Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ƙi ko da kallonta, Wayar Mommyn ce ta fara ruri Ta ɗauka gami da sa hands free yadda Husnee za ta ji ko me za a ce, Daddy ne ko sallama bai yi ba ya fara surfa faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, da Mommy ta gaji sai ta ce masa ga Husnee ɗin ta miƙa mata wayar ta tashi ta bar musu Parlorn. Ba Irin kuka da magiyar da Husnee ba ta yiwa Daddy ba amma ya kanne idanunsa, bai katse wayar ba sai da ya tabbatar mata gobe za su shuɓigar da ƙara Kotu dolen doliya sai an raba Auren, a cewarsa ba zai kai ƴarsa inda za a dinga ciyar da ita da Haram ba. Ko da Muddassir ya jewa Malam Kabiru da tambayar sai da ya haɗa masa da Shaidu waɗanda a gabansu aka ɗaura Auren sannan su ka haɗu su ka yi masa bayani, nan fa ya ƙara burkicewa ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa, shi ba abin ya dinga kurma ihu ba ko ya samu sauƙi. Ma'u na kicin tare da Iya da Talatu su na girke-girke Yazeed ya shigo kamar an jefo shi. da sauri Iya ta ce "Lafiya kuwa Yallaɓai?! ya ɗan sosa ƙeya kafin ya ce "Don Allah ku ɗan ba ni wuri mana." Iya ta komaɗe baki Zuciyarta cike da saƙe-saƙe, kafin Iya ta miƙe Talatu da Ma'u sun miƙe, Iya ta ce "Ke ƴar nan kamani in miƙe mana." Ma'u ta temaka mata ta tashi sannan su ka nufi hanyar fita, jikin Ma'u na rawa sai gaggawa take yi don ta yi ta fita kar ya ce mata wani abun. Caraf ta ji ya damƙo hannunta, a firgice ta juyo ta na zazzaro masa ido, ya marairaice kamar zai yi mata kuka "To Ma'u kika tafi ki ka bar ni da wa zan yi magana? dominki fa na zo." da kyar ta fizge hannunta daga riƙon da ya yi mata cike da baƙin ciki ta ce "Ni ban ga abinda za ka yi mini ba Yallaɓai, indai Abinci ka ke so ka nemi Iya mana sai dai in zalumci ne ya kawoka". wani irin sakin baki ya yi galala ya na kallonta kafin ya ce "na yi miki kama da Azzalumai Ma'u?? to in ma haka ki ka gani ni ba haka ce a Zuciyata ba, ki je ki shirya ki raka ni." "Ni ba zan je ba!!" ta faɗa a masife kamar za ta hau kansa da dukan. wani lallausan murmushi ya saki Gami da cewa "Dama kin iya faɗa? sai naga kin yi kyau a cikinsa; ke sai fa kin je ko kuma in ɗauke ki da kaina in zuba ki a Mota, wata cikal-kal da ke har wani hargowa ki ke yiwa mutane? to ki gaggauta shiryawa in ba haka ba zan ɗaukeki ko babu gyale." Ba ta ce masa komai ba ta fice daga Kicin ɗin ta na kuka ta nufi ɗakinsu. Iya da Talatu na zaune sun ci gaba da hirar da su ke yi ta shigo ta na kuka, Iya ta riƙe haɓa gami da cewa "Oo! Duniya, me ya yi miki ki ke kuka haka?? ni fa ina ji miki tsoron yaron nan, me ki ka ci masa me yake ta zawarcenki??" Cikin shashshekar kuka ta ce "Ba abinda na yi masa haka kawai yake mini haka, wai yanzu ma in shirya in raka shi, ni dai ba zan je ba ko me zai yi mini." Talatu ta yi karaf ta shiga zancen da cewa ''Ke wallahi ki bi shi ki ga inda zai kai ki, ai dai ba zai sayar da ke ba ko." cikin takaici iya ta zabga tsaki gami da kaiwa Talati duka ta na cewa "Ja'irar gora, to in bai sayar da ita ba ai zai rabata da darajarta, ki na gani in uwar ba ta nan yadda yake yo safarar Mata ya na kawowa gidan." Talatu ta ce "Eh kuma fa haka ne..." Ma'u kuwa ƙara fashewa ta yi da kuka jikinta sai tsuma ya ke yi gabaki ɗaya ta ƙara firgicewa. Sun ɗauki lokaci a nan Talatu da Iya su na maida yadda aka yi Ma'u kuwa ta na razga kuka....... Kamar daga sama su ka jiyo muryarsa ya na ƙwalla mata kira, ta ƙara sautin kukanta cike da tsoro da firgici. Iya ta rausayar da kai kamar marigayin zakara kafin ta ce "To Allah i tsare sai ki tashi ki je, amma ki dinga Addu'a." Talatu ta na jin haka ta tashi ta ɗakko koɗaɗɗen Hijab ɗinta ta fara ƙaƙaba mata, ta na turewa ta na komai amma sai da ta sa mata shi sannan ta ɗakko mata takalmi ta ajiye mata ta na cewa "Gwara ki bi shi ta maslaha kar ki yi masa abunda zai cuceki a banza, sai ki dinga Addu'ar." Sai da kyar da siɗin goshi suka lallaɓata ta fito wujiga-wujiga da ita sai murza kuka take yi kamar an yi mata wahayinsa. Shi dai ba abinda ya ke iya yi banda kallonta, har cikin ransa ba ya jin daɗin kukanta amma ita ta kasa ganewa. A wani rafkeken Super Market ya yi Parking, ido ya ƙara zuba mata kamar zai cinyeta, kanta ya na ƙasa har lokacin ba ta dena kuka ba. Cikin wata karyayyar murya ya ce "Ma'u me yasa ba za ki saki jiki da ni ba? ba zan iya cutar da ke ba Ma'u hasalima burina a koda yaushe in ga ki na farin ciki, kuma ina so farin cikinki ya ɗore har Abada, ki temaka ki gaya min damuwarki domin ina so in zamo miki Bango." Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, ai kuwa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan filll, cikin shashsheka ta ce ''Ba zan iya ba!!" "Yau na ji ikon Allah, kuka na ƙara sa ki? to Allah i ba ki haƙuri na dena, ki kwantar da hankalinki, Nasan ki na tunanin wasu halaye nawa ke ba ki yi kama da irin waɗannan matan ba, ke mace ce wadda ya kamata a yi kishinta, ki zo mu je to, sayayyar kaya zan yi miki sai ki zaɓi abinda ki ke so." "Ni ba zan je ba" ta ba shi amsa cikin kuka. Bai matsa mata ba ya wuce shi kaɗai, bayan wani lokaci ya dawo ɗauke da tirƙa-tirƙan ledoji guda biyu wanda aka shaƙesu da kaya, bayan ya zuba a Motar ya shiga mazauninsa sannan ya ja ta. Har su ka dawo gida Ya na zuba mata surutu ita kuwa ba ta da aiki sai kuka, muryar ta shi ma duk ta gaji da ji; ji take kamar ta kashe shi ta huta. Talatu jiki na rawa ta fara zaro kayan ta na dubawa sai murna ta ke yi kamar ita aka bawa. Dogayen Ruguna ne wanda yawancinsu Abaya ce, sai riga har ƙasa me wando, sai kayan ciki su pant, da su turaruka, da Alewoyi da chocolate kala-kala . Iya da Talatu sai yabawa su ke yi yayin da Ma'u ta ke jin Zuciyarta na wata irin ƙuna, lokaci guda zazzaɓi ya rufeta bayan ta gama masifa da cewa ba za ta yi amfani da komai a ciki ba ta haye yamutsatstsiyar shimfiɗarsu ta kwanta, ba abin da ke ɗaga mata hankali idan ta tuna sama da surutan da ya dinga yi mata a hanya kamar mahaukacin da ya ƙwato da ga gidan Masu rangwamen hankali. Sai da su ka gama gani sannan su ka mayar su ka ajiye mata, ita kuwa ko wajenda kayan suke ba ta ƙara kalla ba. Washe-gari Ranar litinin kenan, Ranar jirginsu Abhi da Jaafar ya ɗaga zuwa Saudi Arabia, hakan ya mugun yiwa Akhiee daɗi ya san duk rigimar da za a yi za ta ƙare kafin Abhi ya dawo. Gidan Su Husnee Komai ya yamutae lokaci guda ta zamo tamkar Mujiya a cikinsu kowa ya ƙi saurararta hatta Khausar in ta kulata sai Mommy ta doka mata tsawa, Faɗa kuwa ba irin wanda ba ta sha ba Muneeb har da kai duka. Cikin kwana ɗaya ta wani zuge ta zube ta yi zuru-zuru ta dawo tamkar tsumungiya, ga wani ciwon kai da ya sakota gaba ko abinci ta kasa ci, Ta rasa inda za ta sa kanta ta ji daɗi. Wata Zuciyar ce ta bata shawarar kiransa ta sanar masa abinda ke faruwa don haka ta ɗakko wayar ta lalubo lamba ta tura kira. Ya na tsaye a kan wani tsauni hannayensa harɗe a bayansa, sai ƙarewa ko'ina kallo ya ke yi Zuciyarsa cike maƙil da tunane-tunane, jin motsin wayar ta shi ya dawo da shi hayyacinsa ya ɗauka ba tare da ya ce komai ba. Cikin Dasashshiyar muryarta ta ce "Akhiee!!" "Asma'u ki na lafiya? waye ya taɓa ki?" goge ƙwalla ta yi kafin ta ce "Ba wanda ya taɓa ni kawai ina cikin tashin hankali ne, iyayena da ƴan uwana duk fushi su ke yi da ni, na fahimtar da su na basu haƙuri amma duk hakan bai yi tasiri ba, kuma sun ce sai sun rabamu." ƴar ƙaramar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Asma'u Calm dow........" kafin ya ƙarasa faɗen abinda ke Zuciyarsa ya ji anyi masa wata muguwar runguma ta baya wadda ta sa Numfashin da Zuciyarsa su ka dena aiki na wucin gadi, ya rintse idanunsa da ƙarfi gami da cije gefen leɓensa. Ya na jin Husnee na kiran sunansa gami da tambayar lafiyarsa amma ba zai iya ce mata uffan ba a wannan yanayin. a hankali sautin kukanta ya fara karaɗe kunnuwansa hakan ya sa tsigar jikinsa su ka hau tashi. katse wayar ya yi gami da sakinta ta faɗi ƙasa, cikin wata irin rikitacciyar murya ya ce "Raziahh!!!!!" Cikin shashshekar kuka ta ce "Kai fa Mijina ne Risslan me ya sa za ka haɗa ni kishi da wata? ka san kai kaɗai nake so kuma ina kishinka shine za ka je ka auri wata? me yasa ni ba za ka so ni ba?" Cikin wata irin murya me matuƙar gusar da hankalin duk wanda ya ji ta take maganar, a sannu ya zagayo da ita gabansa su na fuskantar juna ya jefa idanunsa wanda su ka canja launi cikin nata, kamar wanda aka tilastawa yin magana ya ce "Amma duk da ke matata ce wajibi ne na nemawa kaina Abokiyar rayuwa, kin sani dai ba jinsinmu ɗaya ba, babu ɗorarren aure tsakanin Mutum da Aljan, ko ba ma haka ba Asma'u ta cancanci hakan, ki yi haƙuri" Sake ƙanƙame shi ta yi ta na cusa kanta cikin ƙirjinsa gami da sake wani sabon salon kukan, cikin wata shu'umar murya ta ce "Nima zan zamo Bil-adam domin na rayu da kai, idan babu kai a rayuwata zan sha wahala, Don Allah ka dena guduna Mijina ka amince mini mu rayu tare, ina azabtuwa da banzatar da ni da ka ke yi; ka sa Uban Dawa ya ɗaure ni kawai sabida ina kasancewa tare da kai, idan laifi na yi maka ka hukuntani ta wata hanyar amma ba ta wannan ba Don Allah!!!!!!" Ta ƙarasa maganar ta na kwallan idanunsa da ke cikin nata. dukkan hannayensa ya sa ya rungumeta tsam gami da tura fuskarsa cikin wuyanta, cikin fitar hayyaci ya ce "Ni ma ba a son raina hakan ta ke faruwa ba, sai dai ni ba na buƙatar mace a rayuwata dole wata rana za ta hana ni yin abinda ya dace, amma ni ban taɓa ƙin ki ba hasalima ko da yaushe ki na cikin Zuciyata!!!" SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 AN FARA PAYMENT *©️INDO* [8/29, 5:41 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 20 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *Wannan shine Last Free Pages* LAST FREE PAGE Da sauri ta ɗago ta zuba masa blue eyes ɗinta ta na murmushi me matuƙar ƙara mata kyawu da jan hankalin me kallonta, cikin sassanyar muryar da ke ƙara sa shi fita daga hayyacinsa ta ce "Indai da gaske ka ke ka yi min Alƙawarin za ka kasance tare da ni har abada, kuma za ka rabu da wadda ka Aura." idanunsa ne su ka ƙara girma, tamkar aradu ta rikito masa aka haka ya ji saukar kalaman nata, laɓɓansa har karkarwa su ke yi wajen cewa "Impossible! Razia idan ki ka rabani da Asma'u tamkar kin rabani da garkuwar rayuwata ne, ban na son rabuwa da ita kuma ba na so ta cutu, akanta na shiryawa komai ko da mutuwa ce, ta na da muhimmanci a rayuwata kuma kema ki na da shi, zan so ku rayu a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba tare da cuta da cutarwa ba." "Ba zan iya haɗa Mijina da kowace ɗiya ba, kuma ma ka rasa wadda za ka haɗani kishi da ita sai Bil-adam, ba ka nemi zaman lafiya ba, kuma ka na ji ka na gani zan kasheta ko kuma na nakastata!!" Ta yi maganar a fusace. zafi da ƙuna kawai Zuciyaraa ke yi, ture ta ya yi daga jikinsa gami da juya mata baya cikin ɓacin rai ya ce "Tinda na fahimtar da ke kin kasa fahimta zan ɗauki tsatstsauran mataki akanki da zarar kin cutar da ita, ko meye ya sameta ki sani zan ninka shi akanki, ko kasheta ki ka yi sai na yi miki azabar da za ki gwammace ke ma mutuwa ki ka yi, tinda na gaya miki gaskiya kin kasa fahimta." Ta na shirin yin magana Russlan ya diro a wajen, ransa a matuƙar ɓace, ya na sauka ba tare da wani tunani ba ya ɗame kwari-da-bakar hannunsa ya na shirin harbawa Razia, wani gwauron tashi Akhiee ya yi ya dira a kansa ya bangajeshi su ka faɗi can gefe su ka fara mulmulawa kamar ƙwallo, cikin sa'a Akhiee ya yi nasarar ƙwace kwari-da-bakar ya yi wurgi da ita zuwa gefe, rai a ɓace ya ce "Me ta yi maka?" Russlan ya tunkuɗeshi gefe sannan ya miƙe ya na cewa "Sabida ta raina mutane a dinga faɗa mata magana amma ita kamar shaiɗaniya? yanzu gashi ta sa Uban Dawa sai faɗa ya ke yi mini a ganinsa ko me ta yi laifina ne, gwara kawai na harbeta mu je mu yi jinya da wannan fitinar ta-ta." Dogon tsaki Risslan ya ja kafin ya ce "Amma ai Matata ce ko? kuma wurina ta zo ba wani wurin ta tafi ba." "Waye ya bata izinin fita to? kawai ka ƙyaleta ta karɓi hukuncin abinda ta yi, ka riga ka san halinta kaima. "Ba fa zan bari ka cutar da ita ba, laifi na yi mata kuma ta na da right ɗin da za ta nuna ɓacin ranta, ka je kawai zan dawo da ita da kaina." Cikin takaici Russlan ya ce "Sai ka amsa Kiran Father kai ma nemanka ake yi." Daga haka ya tashi sama ya basu wuri. Akhiee ya maida kallonsa kan Razia da ke durƙushe ta na kuka magashiyyan, a hankali ya taka zuwa gabanta ya durƙusa, tausayinta ya cika masa Zucuya taf, cikin tattausar murya ya ce "Razia! gardamarki ce ta sa ki ke fuskantar ɓacin rai a kodayaushe, ba kya jin magana gashi ba kya aikata abu me kyau, Lokacin da za'a ƴantaki ya kusa amma a bisa wannan laifin da ki ka yi na san dole Uban Dawa Zai Ƙara miki lokaci, ba kya kiyaye ɓacin rai, ba kya ɗaukar shawara, ni a yanzu ba zan iya yin komai a kai ba don nima hankalina ya fi kwanciya idan aka killace ki, fitinarki ta yi yawa musamman a yanzu da ki ka ƙara burkicewa, ki tashi mu je." Ba ta iya cewa komai ba sai kuka, Zuciyarta tamkar ta tarwatse, ji take da Allah zai haɗata da Husnee a yanzu ba abinda zai hana ta kasheta in yaso sai ayi mata ɗauri me dalili. Hannunta ya kama su ka ɓace daga wurin. A Fadar Uban Dawa su ka sauka, yayinda Da yawa daga cikin ahalinsu sun taru a wurin su kaɗai ake jira. Russlan da Arsalaan da Hidaya da sauran yara su na durƙushe a gaban Tafkeken gadon Sarauta na Uban Dawa, anan Razia da Risslan su ka durƙusa su na miƙa gaisuwarsu. Sai da lokaci ya ɗan ja sannan Uban Dawa ya yi gyaran murya ya fara da cewa ''Risslan Labari ya iso mana na cewar ka Auri wata Ƴar Bil-adam ba tare da iyayenta sun Amince ba, meye dalili?" Da sauri ya ɗago kansa cike da tsoron ta yadda Father zai Karɓi Abin, Mother ya kalla cike da son ƙwarin guiwa daga gareta, ta sakar masa sassanyan murmushinta gami da lumshe idanunta . Ƴar ajiyar Zuciya ya sauke gami da yin ƙasa da kai ya ce "Sabida ta na sona ne, kuma idan ba na tare da ita komai zai iya faruwa da ita, shi yasa na yi hakan, a gafarceni Father." Uban Dawa ya jinjina kai cikin dattako gami da manyance ya ce "Ba ka yi tunanin hakan akwai kuskure ba?" "Ba na tunanin akwai kuskure a ciki, amma ban sani ba ko kun hango abinda ni ban hango ba." Father ya yi murmushi hakan ya sa duk sauran na wajen su ka murmusa, cike da ƙauna da kulawa ya ce "Kar ka sake wani ya rabaka da Ita, nima zan so ganinku tare." Da sauri Razia ta ɗago rinannun idanunta ta zubawa Uban Dawa gami da cewa "Father!!" cikin kaɗuwa da tashin hankali. Oum Razia ce ta yi saurin tarar numfashinta da cewa "Kul!! kar ki ƙara sako baki cikin maganar manya." Uban Dawa ya ce "Razia ba sai kin neme ni ba ni zan nemeki da kaina domin kin yi mini laifi, indai fa ba za ki koyi jin magana ba to ba za ki dena karɓar hukunci ba, Yanzu kin ninkawa kanki Shekaru a ƙarƙashin Hukunci, Arsalan maza a maida ita." ya ƙarasa maganar ya na kallon inda Arsalaan ya ke Razia ta ƙara rushewa da wani azababben kuka ta na magiya gami da bada haƙuri, amma ba wanda ya ce uffan har shi wanda ya yanke hukuncin, Akhiee kuwa rintse ido kurum ya yi don kuwa sam ba ya jin daɗin kukan nata. Cikin sanyin jiki Mother ta ce "Father! don Allah a yiwa Razia afwa, wani lokacin Zuciya ce take ruɗarta da aikata abinda ba daidai ba." "Idan ba a nuna mata kuskurenta kuma ta yaya za ta fahimci yadda rayuwa take??, idan ta gama hankalta babu me ƙara hukuntata; idan akwai wanda zai yi magana ana saurarensa." Miƙewa Akhiee ya yi gami da cewa "Ni kam zan fita ana nemana." Da kai kowa ya amsa masa, sannan ya fice. Hajiya Laure Yau har ƙagara ta yi gari ya waye Sabida mafarkin Boka Barore da ta ke yi, ko ta farka da zarar ta koma sai ta ci gaba. Tin ƙarfe bakwai na safe ta ɗauki waya ta turawa Hajiya Saudah kira, a ɓangaren Hajiya Saudah ma wayar ta na hannunta ta na shirin kiran Hajiya Laure ta sanar mata, cikin sauri ta ɗauki kiran gami da kara wayar a kunnenta ta na cewa "Hajiya Laure kema kin yi mafarkin ne?" Hajiya Laure ta ce "Hmm! na yi manaaa,, ba me daɗi ba ma kuwa, ai ni gaskiya mu shirya tin wuri mu je mu ji abinda zai ce don wallahi a tsorace nake." "To ai nima dai hakan take a nawa ɓangaren, har na ji ma ina tsoron zuwa wallahi don mafarkan da na yi ba kyau" Hajiya Saudah ta faɗa murya ƙasa-ƙasa, da sauri Hajiya Laure ta ce "A'ahh! da ke mu ka je da ke za mu koma, ni kinsan ba sanin kan abinsa na yi ba, ko hanyar ba lallai in gane ba, kar kuma mu ƙi komawa ya yi mana wani mugun abin, don na lura azzalumi ne" ta ƙarasa maganar cikin nuna tsoronta a sarari. Ƙulululu!!!! cikin Hajiya Saudah ya ƙara juyawa, jiki na ɓari ta ce "Kuma fa haka ne, to ki shirya mu je da wuri." Da sauri Hajiya Laure ta ce "Ai tuni na shirya dama ke kaɗai na ke jira, na fa cika da tsoro wallahi. Hajiya Saudah ta kasa cewa komai sai ma katse wayar da ta yi ta na sauke wani gwauron nishi, yau ɗaya dai ta yi danasanin raka wani wajen Boka Barore. Dolenta ta shirya, Hajiya Laure ta zo ta zabareta su ka yi gaba, cikin su biyun ba a bambance wadda ta fi shiga tsoro da firgici. Muddassir na cikin driving kamar an tsunkuleshi ya gangare Motar gefe ya tsaya, wayarsa ya zaro ya lallatsa ya tura kira: Sai da na farko ya katse wani ya shiga sannan aka ɗauka, Bakinsa har karkarwa ya ke yi wajen cewa "Oga Dazginabu ina cikin tsaka me wuya fa". a ɗaya ɓangaren Dazginabu ya yi magana cikin kakkausar muryarsa wadda ta ke nuni da rashin imani da tausayi da bushewar Zuciyarsa, "Me ya faru??" "Sahun Keke ya auri Ƙanwata, kuma wadda na fi ƙauna, ban san yadda zan yi ba wallahi" "Hhhhhhhh!!" ya shiga ɓalɓala dariya irin ta mugayen mutane, Maddassir dai ya na saurarensa har ya yi me isarsa sannan ya tsagaita ya ce "Kar ka damu Mafaraucina, wannan dama ce ta zo mana wadda za mu ƙara wasa ƙwaƙwalwarsa, za mu dinga yi masa abinda bai yi tsammani ba kuma ba zai taɓa zarginka ba, yanzu ko me mu ka yi masa ruwa ta sha, zai dinga kallonka a matsayin yayan Matarsa, yayin da mu kuma za mu dinga cin dunduniyarsa, ka ga ranar nan ya kashe jama'ata to yanzu tinda haka ta faru ka ci gaba daga inda ka tsaya ni kuma zan dinga tura masa wasu domin kawar da hankalimsa daga kanka." ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ina Fatan kisan da aka yiwa yaran nan guda Biyu ya taɓa Zuciyarsa sosai." Muddassir ya ja wani dogon numfashi ya sauke shi tare da wata zazzafat iska me tiriri, murmusawa ya yi cikin jin daɗin kalaman Ogan nasa, shi da duk bai yi wannan tunanin ba, amma kuwa tinda abin ya zama haka ba shakka shi me goyon bayan auren ne ba zai so a raba su ba. da wannan tunanin ya ce "Gaskya kanka ya na kawo wuta Oga!!" Ya faɗa cikin sigar yabawa da koɗawa. Dazginabu ya yi wata shu'umar dariya. Muddassir ya ce "Ai nake gaya maka ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, har yanzu ban ƙara jin ko ɗuriyarsa ba, da haka za mu sabauta shi har sai ya haukace sannan mu kashe shi, lokacin Ƙanwata kuma za ta dawo hannunmu." Dazginabu ya ƙyaƙyata dariya cike da farin ciki ya ce "Yau duk waɗanda su ka ba ni aiki akansa za su sha kyakkyawan labari, ka ci gaba da Fito masa a

Chapter 13 of 19