Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaune a wurin sannan ta iya tashi ta nufi wajen sif ta buɗe, kaya ne a ciki masu tarin yawa kuma duk ɗinsu sabbi ne ba wanda yake nuna alamar an saka shi, bayan ta gama ƙare musu kallo ta riƙe haɓa ta na cewa "Oo!! ikon Allah a ce cikin kayan mutum kwata-kwata ba tsoho? ko dai ya kai wanki ne??" Kasancewar ita kaɗai ce a ɗakin babu me bata amsa ya sa ta rufe bakinta ta ci gaba da burkita kayan don ganin wadda ta yi mata, sai da ta gama ruwan ido sannan ta ɗauko wata doguwar Jallabiya Maroon ita ɗin ma ta yi mata yawa daga faɗin har tsayin, amma da yake abin aro ne haka nan ta sanya sannan ta ɗauki lafkeken hijab ɗinta ta saka ta koma ta zauna jiran shigowarsa. "Abee ka san dai ina da hankali kuma na san ciwon kaina, to don me zan yi abinda ba shi ne daidai ba?, kawai don ba sa son farin cikina ne shi yasa suke cewa haka, ni da Asma'u duk mu na son mu rayu tare, na san kai ma ba za ka so a rabamu ba." Abee ya jinjina kai kafin ya ce "Wannan Gaskiya ne, shi yasa dama sam ban goyi bayan kowa ba don na san mafi yawancin abinda za ka yi me kyau ne." numfasawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa ''Yarda da kai da na yi shi yasa nake maka wannan shaidar kuma na Amince da abinda ka yi, ba na so ka ban kunya ka ji Dattijo?" ya ƙarasa maganar cikin Sigar lallami, gyaɗa kai ya yi sannan ya ce "In sha Allah Daddy." "Ita Matar Aure ba wai abar muzgunawa ba ce ta na da daraja da kima, sannan a riƙe amana kar wani abu ya sa a ci amanarta da iyayenta, sannan a mayar da kai wajen sauke haƙƙinta da kuma kare shi, Allah ya yi muku Albarka." nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke tare da amsawa da ''Amin, bari ta zo ta gaisheka Abee" ya faɗa tare da miƙewa tsaye. Zara ta ce "In zo in raka ka??" juyowa ya yi ya maka mata wani banzan kallo, ta yi saurin sunkuyar da kai gami da haɗe bakinta, ya yi ƴar ƙwafa bai ce komai ba ya fice. Shiru ne ya ratsa na wani lokaci kafin Abee ya katse shirun ya na murmushi ya ce "Allah Sarki Dattijona; Zahra'u labarin me muke yi ma kafin ya shigo??" ta ce "Labarin rashin lafiyata, Wallahi Abee idan mutum ba shi da lafiya sai ya ji ƙunci ka ga ko fita ba na iya yi sai dai in ga kowa ya na ta yawonsa ba me kulawa da ni, don ma yanzu ka dawo." "To ai jikin naki ya yi sauƙi sosai ko?, to ai Zahra'u ciwo ba shi da daɗi ko kaɗan, kin ga ni shekaruna goma sha ina zaune ba na iya tafiya ba na iya tashi komai sai an yi min, don ma Allah ya azurta ni da zuri'a, kuma hakan ya na daga cikin baiwarsa, babu wanda rayuwarsa ba ta tafiya tare da jarrabawa kuma kowa da irin ta shi, sannan a rayuwa abubuwa da yawa suna da silar faruwarsu." gyara zama Zara ta yi cike da al'ajabi ta ce "Wai da gaske Abee da ka na tafiya?" tambayar tata sai da ta sa shi dariya, ba tare da ya dena dariyar ba ya ce "Da garau nake tamkar ke, kamar yadda na gaya miki komai ya na da sila to nima hakan ce ta faru da ni." "To Abee meye silar?" kafin ya yi magana Akhiee ya yi sallama hannunsa ɗauke da Husnee wadda ya rungumeta a ƙirjinsa tamkar ƴar jaririya sai da ya zo gabansu sannan ya direta ya na cewa "Abee gata nan." Abee dai lamarin na Akhiee ya sa shi kasa cewa komai, Zara ce ta yi ƙoƙarin cewa "Ciwo ta ji a ƙafarta ne Akhiee?" idanunsa a ƙasa ya ce "Wai tsoron duhu take ji, kuma ba ta san kan gidan ba shi ne kawai na ɗakkota." Abee ya murmusa ba tare da ya ce uffan ba, zuwa yanzu ya gama gazgatawa kansa ba ƙaramin so Akhiee yake yiwa yarinyar nan ba, indai kuwa haka ne ta cancanci shi ma ya so ta domin alamu sun nuna itace silar farin ciki da kuma sauyawar rayuwar ɗan nasa." (Ma su karatu ba ku ce min ina Husnee ba?" Ai ya na direta ta zagaya bayansa ta ɓuya sabida wata muguwar kunya da ta lulluɓeta, ji take tamkar ƙasa ta buɗe ta shige ciki, da ta rasa abin yi kawai sai ta fashe da wani ɗan marayan kuka. Zahra dai dariya take yi musu, Akhiee kuwa ba tare da damuwa ba ya zame ya koma kusa da Akhiee ya yi zamansa, cusa fuskarta ta yi a cikin hijab ɗinta ta na ƙara sakin wani sabon kukan. Zahra ta na dariya ta ce "Kai Anti Husnee sai ka ce ƙaramar yarinya?, Abee ne fa" Akhiee ya ce "Ƙyaleta in ta gaji da tsayuwa sai ta zauna ko?" Abee ya ce "A'a ba za a yi haka ba, zo nan Ƴata, ki rabu da waɗannan zolayarki suke yi." Kasa motsawa ta yi don har ga Allah ji take tamkar za ta nutse, Abee ya ƙara da cewa "Zo ki zauna kusa da ni; ke ma yanzu Ƴata ce ai, tamkar Muhammad haka kike a wajena, kin ga shi tamkar aboki haka ya ɗaukeni." Har yanzu ba ta da niyar gusawa daga ina take tsaye, a ƙufule Akhiee ya ce "Wai ba kya ji Abee na magana ne? ko so kike sai na ƙaraso da ke da kaina??" ta san zai aikata fin haka ya ƙara mata wani abin kunyar don haka ta salallaɓa can bayan Zara ta lafe, shiru ne ya ratsa wajen na ɗan lokaci kafin Abee da yake ta murmushin farin ciki ya katse shirun da cewa "To Barka da da Dare Ƴata tinda kin kasa magana." Sai a lokacin ta tuna abinda ya kamata ta yi wato gaisuwa kuma ta kasa, murya can ƙasa ta ce "Ina wuni" cikin jin kunya. Ya na fara'a ya amsa da ''Lafiya Lau, ya rayuwa?" ba ta ce komai ba hakan ya bawa Zara damar cewa "Ki fito sarari mana ya kamata Abee ya ga fuskarki kar ya kasa ganeki gobe, kin san idon manya kaɗan-kaɗan suke gani." ta ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, Abee ya yi dariya gami da cewa "Na fi ki lafiyar ido Zahra'u." "To ai Abee naka idanun sun manyanta sosai, dole nawa za su fi kyau. "Na tsofi kuma ai ya fi ƙarko" Abee ya bata amsa. kafin ta ce wani abu Akhiee ya shiga zancen da cewa "Wai ke kin ɗauka Abee Kakanki ne da kike zolayarsa?, Abee ka dena biye mata don Allah." Abee ya rausayar da kai gami da cewa "To!! Dattijo su waye Abokan nawa in ba ku ba?, to a bar zancen dai, Yanzu na dawo kan Ƴata." ɗan tsahirtawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Asma'ul- Husna! ga amana nan ta Ɗana Muhammad Rislan, shi maraya ne ya rasa Mahaifiyarsa tin bai wuci shekaru goma sha ɗaya ko shabiyu a Duniya ba, tin daga lokacin kuma rayuwarsa ta sauya, farin ciki ya ƙaurace masa, ni kuma ina matuƙar sonsa ina son ganin farin cikinsa; za ki same shi a wani irin bauɗaɗɗen Mutum, hakan ya na da nasaba da irin tashin hankalin da ya tsinkaya a rayuwarsa a daidai lokacin da shekarunsa ba su kai ya ga wannan tashin hankali ba, hakan ya bada gudun mawa wajen canjawarsa sosai, ni kaina na sani rayuwa da shi sai da haƙuri sai an jure, a dinga haƙuri da juna a dinga kawaici da juriya, a dinga tausasa zuciya sannan a kyautatawa juna." ɗan jim!! ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Jikina ya bani cewar ke ce silar canjawar rayuwarsa, ya na buƙatar temakonki sosai domin tin da ya rasa mahaifiyarsa bai ƙara samun wata uwa mafi kusanci da shi ba sai ke. Mayar da kallonsa ya yi kan Rislan gami da cewa "Dattijo! ba na son na ji saɓani a tsakaninku, kuma ka sa a ranka indai na samu haka kai ne me laifi." ya gyaɗa kai alamar ya gamsu. Husnee kuwa ta yi tsit!!!! kamar ruwa ya cinyeta , kalaman Abee sun yi bala'in ratsa Zuciyarta kuma sun jefata cikin tunani iri daban-daban, ga tarin tambayoyi da ta rasa wa za ta yiwa su Akiee ɗin ko Abee ɗin?. Nasihu Abee ya yi musu sosai wanda suka ratsa Zuciyar Husnee jikinta ya yi sanyi salam! Zuciyarta ta tsumu kuma ta samu nutsuwa, bayan ya kammala ya rufe da Addu'a sannan suka bar sashin nasa tare da Zara ita ma ta wuce Ɗakinsu. Suna komawa ta haye gado don kuwa ba abinda take buƙata a yanzu sai bacci, Rislan kuwa sai bayan ta yi baccin ya haura kan gadon ya kwanta kusa da ita gami da janyota jikinsa, da haka shima baccin ya yi awon gaba da shi. Daidai lokacin da ya saba fita daga cikin gidan yau ma ya fice ba tare da Husnee ta sani ba hakan ya sa ta yi tunanin bai ma kwana a gidan ba. Da rana tsaka kawai sai jin Sallamar mace ta yi a gefen Ɗakinta, ta zumbuɗa hijab sannan ta leƙo a tsorace cike da shakkar wadda za ta gani. Matashiyar macece fuskarta ɗauke da murmushi "Sunana Rahma Daddy ne ya aiko mu mu kawo miki kaya, da fatan ba damuwa, in kuma da damuwa sai mu koma sai kin shirya domin mun shigo miki gaba-gaɗi" duk da ba ta gane kowacece ba kuma ba ta gane inda zantukanta suka dosa ba sai ta washe baki ta na murmushi ta ce "A'a ba komai, amma ban gane wanda kike nufi Daddy ba , ko dai Daddyna? in haka ne kuma ai ban san ki ba." Rahma ta girgiza kai sannan ta ce "A'a ba Daddynki ba, Mijinki shine Daddy a wajenmu, Kayan lefenki ne da kuma kayan Ɗaki muka kawo, idan ba damuwa za mu shigo da su." Husnee ta cika da mamaki da jin furcin Rahma, cikin alamun mamakin ta ce "To ku shigo ba komai." Rahma ta yi godiya sannan ta koma zuwa waje. Suman tsaye Husnee ta yi lokacin da suka gama dire mata akwatinanta a gabanta, Saiti ne kala-kala masu shida-shida, shidan kuma sau Shida, in an haɗa duka Akwati Dozin uku kenan, guda Talatin da shida. Banda dukan shalugude ba abinda Zuciyarta ke yi, ta matuƙar girgiza da lamarin Akhiee, lokaci guda Zuciyarta tafara yi mata saƙe-saƙe kala daban-daban. Ta na nan tsaye wasu ƙaratan Maza suka fara shigo da Sif, Baƙa ce me yarfin fari irin me shidan nan wadda ta sha kyawun ƙira daga gani Naira ta yi kuka, Madubinsu ma kanshi abin a zo a gani ne, ya sha ado ta ko ina, sai kujeru guda uku Fallatsa-fallatsa masu numfashi, irin wanda ba dai a gidan Malam Shehu ba sai dai me hannu da shuni, ga wasu plowers na adon ɗaki masu bala'in kyau da burgewa. A gefe guda kuwa kayan Kitchen ne aka tsibe su tari guda manya masu shegen kyau, ko makaho ya shafa zai gane an zuba miyagun kuɗi wajen mallakarsu. Husnee dai ta kasa cewa komai sai ido kawai take zarewa kamar an tarfa ɓarauniya a Kasuwa, "Anya kuwa Akhiee ba ɗan fashi ba ne?" tambayar da wani sashin na Zuciyarta ya wurgo mata kenan, yayin da wani ɓangaren ya cafe kalmar kuma ta yi ɗaram a Zuciyarta, don kuwa in ba fashi yake yi ba ta ya zai iya sayen waɗannan maƙudan kayan kuma a lokaci ɗaya? sai dai da yake bai san darajar kuɗin ba tinda sata yake yi. wannan tunanin take ta yi tana daga jikin bango a raɓe tamkar garafuni a jikin danga. Ƙiftawa da bismillah sashin ya cika da tarkacen Matan gida da Yaransu sun zo kashe kwarkwatar idonsa, dandanan wurin ya ɗau cecekuce kowa na tofa albarkin bakinsa, sun kamu da tsananin mamaki da Al'ajabi na ganin irin wannan kirimɓa ta Rislan. Ko kunyar idon Husnee da su Rahma ba su ji ba suka dasa zancen cewa ai ɓarawo ne dama har fashi da makami yake yi, wasu ma cewa su ka yi ƙila shagon masu sayar da kayan ya je ya yi musu fashin kayan ya ɗebo. Laita ta so ta tanka musu Rahma ta hanata don kuwa Inna ta jaddada musu kashedi akan kar su sake su biyewa matan gidan a yi da su. Zara da Ruƙayya da Musa su ne suka temaka musu wajen yin jere da duk sauran aikace-aikacen. Kayan da ke cikin ɗakin waje aka yo da su aka sanya sabbin, da yake Ɗakin da girmansa duk sai da ya cinye komai kuma dama sai da Rislan ɗin ya kimanta shi kafin ya san irin kayan da zai zuba masa. Dandanan ya ɗau kyau ko ina gwanin sha'awa. Duk hassadar su Inna Huwaila su Innajo duk wadda ta leƙa sai ta yaba sai dai ta ciki na ciki, musamman Matan Yayyen Akhiee da suka kasance faccaloli a wurin Husnee sai suka ji baƙin ciki ya ƙara kama su don sun tabbatar ta yi musu fintinkau, da kuwa har sun fara tsegumi akan iyayenta ko tsinke ba su kawo mata ba. Kayan kitchen kuwa a ɗaya ƙaramin ɗakin aka jera su tsaf, bayan an buga kanta doh kuwa da masu aikin suka tawo kafin su gama jeren ɗaki an gama bugata. Komai ya ji banda tsiya in ji maroƙa. Tamkar Macijin da aka zarewa Dafi haka Husnee ta koma, sai ta ji duk gidan ya ƙara matseta ta ji tamkar a kurkuku take sabida abubuwa da dama da suka sha mata kai, tin daga kan kayan har zuwa maganganun da Faccalolinta suke jefar mata. ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ta ga har maƙota shigowa suke yi kallonta lokacin Zuciyarta ta yi karyewar da ba za ta iya jura ba dole ne ta yi kuka ko ta samu sassauci, bayan ɗakin ta zagaya ta zauna a ƙarƙashin ɗaya daga cikin bishiyoyin wajen ta fara mazgo kuka. Sai bayan Magrib su Rahma su k yi mata sallama suka tafi, da za su tafin ne Laita ta ke cewa "Ranar nan Inna sai yi miki nasiha take yi akan haƙuri da matan gidan nan, to wallahi kar ki sake ki yi haƙuri da su, duk wadda ta yi miki ki yi mata mu za mu tare miki, irin waɗannan indai za ka yi musu sauƙin kai to ka shiga uku." Husnee dai murmushin yaƙe ta yi kawai gami da yin ƙasa da kai don kuwa ba ta da abin cewa. Zabira ma ta ƙara da nata nasihun na shiririta, ita dai Rahma aikinta dariya, da haka su ka yi sallama sannan suka tafi. Sai a lokacin ta gane ita cikakkiyar Marainiya ce a yanzu, a lokacin da take cikin tsananin damuwa da tashin hankali, yayin da sawu ya ɗauke ya rage daga ita sai wannan tarin kaɓakin kaya nata wanda in ta kallesu take jin Zuciyarta ta yi wawan zillo tamkar za ta fito ta baki. zama ta yi ta buga tagumi ta na kallonsu, wata Zuciyar ta na zugata akan ta buɗe Akwatinan ta ga meye a ciki wata kuwa ta na yi matsa tsawa akan kar ta buɗe, tana cikin wannan halin ne Zara ta yi sallama a ɗakin, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Ni fa Anti Husnee Allah ma ya sani na zo ganin kaya ne; Allah ya sa mu a danshinku ." ta ƙarasa maganar tana dariya cikin sigar Zolaya. Husnee ba ta iya cewa komai ba sai ta yi ƙasa da kai, hakan bai damu Zara ba ta ƙarasa inda aka jere akwatinan wata kan wata ta fara saukesu ta yi musu ɗaiɗai a tsakar ɗakin suka cika ko'ina sannan ta fara buɗewa bakinta ɗauke da bismillah. Tin Husnee ta na kan gado sai da tashin hakali ya jefota ƙasa, ashe a ɗazu ba komai ta gani ba face shafar mai. dallatsa-dallatsan Atamfofi, Leshika, Shaddodi, Matarial, sun kai kala talatin-talatin, kuma dik cikinsu ba wanda ba a ɗinka ba duk a ɗinke suke, ɗinki kala-kala masu bala'in kyawu irin na manyan mata. Sai jerin su Abaya, da dogayen riguna dangin ƴan kanti, da kayan bacci iri daban-daban su ma kansu yawansu sun fi gaban irgawa. A gefe guda kuma wasu irin kaya ne na saƙi Irin na da, wanda aka yi musu ƙirar kayan Sarakunan Asali, dakakku masu kyau da burgewa. sai takalma da mayafai kowane kaya da nashi, sai hijabai, sai dangin sabulai turaruka kayan kwalliya da sauransu gasu nan barkatai kamar kayan banza. Wata ƴar madaidaiciyar Akwati Zara ta janyo ta buɗeta, idanunta ne suka ƙara girma Zuciyarta ta yi wata muguwar buguwa wadda ta sa ta kusan shiɗewa......... Husnee kuwa da ta yi tozali da abinda ke cikin Akwatin kawai sai ta fashe da wani mugun kuka tamkar an yi mata baƙin albishir da Mutuwar iyayenta.............. *©️INDO* [9/11, 8:40 PM] INDO: *🪻S-K🪻* Ep 26 Jiki na rawa Zara ta fara zaro kayan, danƙara-danƙaran Ababen Ado ne dangin su Sarƙa, Awarwaro, Ɗan Kunne, Zobe. daga yanayin kyawunsu da ɗaukar ido ko ba a faɗa ba za ka gane na zallar Lu'u-lu'u da Zinare ne, wato Gold da Diamond, gasu nan kala-kala kowanne da nashi style ɗin. Ita kanta Zara lokacin da ta kammala fito da su sai da ta kasa jurewa ba tare da ta shiryawa kuka bata fara yinsa. Daidai lokacin Ruƙayya ta yi sallama a ɗakin tare da shigowa gadan-gadan "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!!!" ta faɗa cikin kaɗuwa gami da firgici, cike da rashin sanin abun yi ta ƙarasa kan kayan ta durƙusa, har lokacin bakinta a buɗe kamar ƙofar gari sai jinjina kai take yi ta ma rasa abin furtawa. Zara ce ta fara ƙoƙarin mayar da kayan cikin sauri don kuwa ba za ta so mutan gida su san irin abinda ke cikin Akwatinan ba, sai a lokacin Ruƙayya ta ƙara samun ƙwarin guiwar cewa "Zara! anya kuwa Akhiee ba ɗan Mafiya ba ne???" ta yi maganar cikin tsananin mamaki da fitar hayyaci. Cikin shashshekar kuka Zara ta ce "Haba Ruƙayya! kamar ba ɗan uwanki ba? ko a titi kika gamu da mutum bai dace ki dinga jifansa da irin wannan kalamin ba, Allah shi ya barwa kansa sanin inda ya same su, ban ga amfanin ku zauna kuna faɗen mugayen kalamai akansa ba." Ruƙayya ta taɓe baki gami da cewa "Tab!!! Allah ya sittiri buƙui in ji kishiyar me doro, gaskiya ce dai ba kwa so kuma dole a faɗa, don in ba ɗan mafiya ba banga a inda zai samo waɗannan gwala-gwalai da kayan ba, dama indai shan jini ne ai ya saba, ƙila in ya kashe mutum tsafi yake yi da shi." a fusace Zara ta ce "Tashi ki bar ɗakin nan Ruƙayya!! ba na son ƙara ganinki anan don Allah ki ƙyalemu!!, abinda ya shafemu ne ba buƙatar ki ƙara sa baki a ciki, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce ka faɗi Alkairi ko ka yi shiru." "To Alawadaran naka ya lalace, jakin dawa ya ga na gida." ta faɗa tare da tashi jikinta har ɓari yake tsabar zaƙuwa da son ta je ta bada labari. Tana komawa ɓangaren nasu ta fara ƙwalla kira, "Innajo! Umma! Inna Kulu! Inna Huwaila! Umma Azima! Yaya! Yaya Lantana! duk wadda ta ji ni in bata tsakar gida ta fito." Inna Huwaila dama itace ta aikata don ta gano abinda Zara da kuma Husnee ɗin suke yi kuma ta yi sa'ar shiga, da yake abin boni na iya ne tamkar kiran Allah haka suka gaggauta bayyanowa, Innajo da Umma Azima da sauran yara dama suna tsakar gida. Nan fa suka yi rukuni Ruƙayya ta zayyana musu abinda ta gani, har da ƙara zuzutawa abinda yake ƙarami ta kumbura shi ya zamo babba. Nan fa suka fara magana kowacce ta na gwaɓo tata sobaɗanar, haka suka dinga luliya zancen har wasu daga cikin mazan gidan suka dinga shigowa suna iskar labarin su ma sai a zauna a Zana musu abinda ya faru. Duk wannan abin da ake yi Inna Huwaila ba ta iya cewa komai ba sabida wani miki da ya maƙale a cikin Zuciyarta, ba komai take tunawa ba sai Kisan da Rislan ya yiwa ɗanta, da ya bar shi a raye da tuni ya na nan yana rayuwa amma shi ya kashe shi sannan ya zo ya na tashi rayuwar ba abinda ya sha masa kai. Da wannan tunanin ta gama ƙuluwa ta fara mugayen saƙe-saƙe a ranta. a Ɓangaren Yaya Fiddausi Matar Yaya Aminu, abin ya fi ƙarfin ta yi magana don kuwa wani mugun kishi ta ji ya tokare mata maƙogoro, ji take ina ma itace ta samu irin wannan hamshaƙan kayan daga mijinta?, Da a kaf gidan Mijinta ya fi kowa bajinta, ta fi duk sauran mata sanya tufafi masu kyau da ɗaukar ado, duk itace tauraruwa, amma yanzu gashi wata Yarinya ƙarama kuma Matar wani Banza mara galihu ta zarceta, sai ta ji kamar ta sokawa Zuciyarta wuƙa kawai ta mutu, "Ta yaya ma zan bari wata Faccala ta fini komai? ya zama dole in san abin yi domin duk gidan nan ni ce Tauraruwa domin Iyayena ma masu kuɗi ne, bai kamata wata kucaka ta zo ta nuna mini iyakata ba, gwara ko kasheta ne na yi na kwashi abinda zan kwasa a cikin kayan nata." Wannan tunanin kawai take maimaitawa a cikin Zuciyarta wadda take ɗaci da raɗaɗi. Fuuuu!! ta tashi ta koma ɗakinta don ta gaji da jin maimaicin labarin kayan. Inna Huwaila ta na ankare da ita, duk ta lura da yanayinta don haka ta saki wani shu'umun murmushi don kuwa alamu sun nuna mata ta samu makamin da za ta yaƙi Rislan ta hanyar Cutar da Matarsa, Kakkaɓe zaninta ta yi ta miƙe ta na cewa "Uhm!! mun dai godewa Allah da muka samu haihuwa me rana ba mu haifi annoba ba, Ita dai Hadiza ba ta yi sa'ar zuwanta Duniya ba." A ɓangaren Zara da Husnee kuwa har yanzu Husnee kuka kawai take yi ko motsawa daga inda take a zaune ta kasa yi, Zara ce ta yi

Chapter 18 of 19