Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 1 NA Ayeesha Abdulkareem INDO Marubuciyar.... DOGON YARO TAJMAHAAL IDO HUƊU WATA HANYA A JINI ƊAYA AAMINAT (Bazawara) da sauransu... 4/8/2023 *Mikiya Writer's Association* Bismillahirrahmanirrahim Garin Kano Misalin ƙarfe 03:00am.... Dare mahutar bawa,, a duk lokacin da dare ya tsala sahu kan ɗauke kowane ɗan Adam ya killace kansa a makwancinsa domin samawa ruhinsa salama. a wannan dare yayin da Asbahi ke shirin ƙaratowa daidai lokacin hadari ya fara gangami, cikin lokaci ƙanƙani ya gama haɗowa ya fara sakin iska me ƙarfi gami da walƙiya me tsananin haske ya na wani irin rugugi kamar zai ci babu. Ya ɗan ɗauki lokaci cikin wannan yanayin kafin ya saki ruwa me ƙarfin gaske. Sai da aka kira Sallar Asbahi sannan ruwan ya tsagaita ya koma yaf-yaf a hankali a hankali, ba shi ya tsaya cak ba sai da gari ya fara haske. mamakon ruwan da aka sha ya haddasa lullumi gami da wani irin sanyi me matuƙar daɗi. kasancewar safiyar Lahadi ce ya sa titina har ma da cikin unguwanni babu yalwar jama'a kowa ya nabba'a a gida, tin daga kan ƴan makaranta har ƴan kasuwa, tsirarun mutane ne kurum ke yawo sai ababen hawa na haya su ma ba su gama fitowa ba, domin kuwa yadda ƙasa ta sha ruwa ta jiƙu ga sanyi na ratsa jikkuna ba kowa ne zai so fitowa a irin wannan lokacin ba. HOTORO Hajiya Laure ce zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun Falon, ta harɗe ƙafa ta na danne-dannen waya fuskarta ba alamar walwala, ta haɗe cikin leshi ɗinkin Buba ta doka ɗaurin ture ka ga tsiya, adon nata ya ƙara fito da asalin suffarta ta Hajiyoyi, Jiran shigowar Alhaji Salisu kawai ta ke yi don ta sauke masa buhun masifar da ta kwana ta na ƙissimawa akansa. Yazeed ne ya shigo falon ya na tafe ya na jan ƙafa zagaraf-zagaraf bai bi ta kanta ba ya saita hanyar bedroom ɗinsa, cike da takaici ta ce "Ai ko ba za ka gaishe ni ba ya kamata ka faɗa min inda ka je." fasa wucewa bedroom ɗin nasa ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna idanunsa ƙasa-ƙasa ya ce "Why are u doing this to me?? you're my mother fa kin fi kowa sanin ba yaro bane ni Mummy, maganar gaskiya kin fiye kishi da ni" tsaki ta doka kafin ta ce "Ubanka ne ya lalata ka ba wani ba, na san ba zai wuce daga biye-biyen ƴan mata ka ke ba, inda zan yi kishi da kai kuma ai ba zan ma haifeka ba yaro, kawai don ba ka son gaskiya ne." Taɓe baki ya ɗan yi cikin ko in kula ya ce "Ina Daddy?" a masife Hajiya Laure ta ce "Ka ban ajiyarsa ne?? tin jiya ya yi min alƙawarin zai dawo ya same ni amma ya ƙi dawowa." "Wani gurin ya je??" ''To ai in wani gurin ya je ma da ƙauna, ya na sashinsa, wai wani baƙo zai yi za su tattauna shine har da ce min kar in sake in zo sashinsa har sai ya dawo ya same ni, to ka ga da bai iya cika alƙawari ba ya ƙi dawowa, sai ka tashi ka je gurin nasa tinda dama ai shi kaɗai ya haifeka ni ƴar karere ce, idan ka je kace masa ya fito ina jiransa." Dariya Yazeed ya yi gami da cewa "Gaskiya kina da yawan faɗa Mum, ki dinga haƙuri mana Daddy fa ya na da aiyuka sosai ki dinga yi masa uzuri, kuma ba na so in ji ki na cewa ba na martaba ki ɗinnan Please Mum, martaba ki ya zama dole bayan ke ba ni da wata." taɓe baki ta yi ta juya masa ƙeya alamar ba ta gamsu ba. Tashi ya yi ya wuce sashin Daddy ya na jiyo Hajiya Laure na mita shi kam sai dariya yake don abin nata dariya yake ba shi. Ɗan madai-daicin Parlor ne wanda ya ji kayan Alatu na more rayuwa, an zuba kuɗi wajen tsara shi da ƙawata shi komai ya ji banda tsiya inji maroƙa. Banda sanyin AC gami da ƙamshi ba abinda yake tashi. a tunanin Yazeed ya na shiga zai tarar da Daddynsa a Falon ya na karatun Jarida kamar yadda ya saba don haka ya fara cewa "Dad!!! ka na ina? ka shirya faɗa da Mum don kuwa ta yi fus........" maganar tasa ce ta maƙale a maƙoshinsa, cikin zazzaro ido ya ke kallon jini da ke kwance malala har ya gangaro ƙarƙashin Kujera ya fito kasancewar saitin kujerun a tsakiya suke. cikin tsananin firgici ya zagaya don ganewa idonsa abinda ke zubda irin wannan jinin haka. Ihu ya kurma gami da yin tsalle ya yi baya idanunsa kamar za su faɗo ƙasa sabida zaro su da yayi, dandanan jikinsa ya ɗauki wata irin tsuma, zuffa ya shiga karyo masa duk da irin sanyin AC da sanyin gari da su ke kaɗawa. Baya-baya ya fara yi ya na cewa "No!! wallahi ba dai Daddyna ba, lallai yau na tabbata Jaki, naje na sha giya ta zo tana nuna min Daddy cikin jini haka? Impossible! dole ma in dena shaye-shaye!!" maganar yake cikin fitar haiyaci don kuwa tashin da hankalinsa ya yi ya wuce mizani. Da gudu ya juya ya koma Parlo ya na ƙwallawa Mummy kira, gabanta ne ya yanke ya faɗi Rimmmm!!!!!!! ta yi saurin tashi ta na cewa "Me ya faru??" Yazeed ya na haki ya ce "Daddyyy!!! zo mu je ki gani, na fara haukacewa!!." ya ƙarasa maganar ya na jan hannunta, cikin sauri gami da sassarfa ta bi bayansa su ka koma Falon Alhaji Salisu. Sai da ya danganata da gawar Alhaji Salisu sannan ya saki hannun nata ya koma baya ya riƙe ƙugu ya na jiran ta ce masa ai giya ta sa ya fara gane-gane. ya na kwance cikin jini ko ina a jikinsa raunin wuƙa ne faca-faca anyi masa wani mugun kisan gilla wanda ko Dabba mutum ya ga anyiwa dole hankalinsa ya tashi bare Mutum ɗan uwansa. Hilis Share Mutanena Ƴan Amana😍🌸🌹 Paid Book ne..... 09079885632 ©️INDO [8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 2 NA Ayeesha Abdulkareem INDO *Mikiya Writer's Association🦅* Ihu da kururuwa Hajiya Laure ta fara yi, ba ta bi takan Yazeed ba ta fice ta na ihun neman ɗauki. Yazeed kuwa jin haka ya tabbatar masa ba gane-gane ya fara yi ba da gaske Daddynsa ne aka kashe, jaɓar ya zauna a ƙasa dafa'an murar kwaɗi, gami da fashewa da kuka kamar ƙaramin Yaro ya na cewa "Wallahi ko waye ya kashe min Daddy sai na kashe shi ba zan taɓa ƙyale shi ba." abubuwan da ya ke ta faɗa ya na maimaitawa kenan. Hajiya Laure kuwa ta na fita harabar gidan me gadi ya taso da sauri ya na tambayarta, cike da masifa ta ce "Maza-maza kira min Ƴan-sanda wallahi ba zan yarda ba duk wanda ya aikata da me hannu a ciki sai na yi shari'a da shi kuma sai na sa an kashe shi, maza ka kira min su!!." ta ƙarasa maganar cikin tsawa, jiki na tsuma Tala ya ce "Hajiya ai bansan me zan ce musu ba ne" Kamar za ta cinye shi da masifa ta hayayyaƙo masa ta na cewa "Ka ce musu Alhaji Salisu aka kashe, su yi sauri su zo tin kafin wanda ya aikata ya bar garin su kama shi don wallahi ba zan ƙyale ba ko uban waye shi." Jin furucin kisan Alhaji ya ƙara ɗaga hankalin Tala me Gadi, cikin rawar murya ya ce "To Hajiya ku na da lambar Ƴan-sandan??" tasssss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, jikinta ya ɗauki tsuma sai huci take sabida ɓacin rai gami da tashin hankali da su ka yi karo da juna a cikin Zuciyarta. "In banda kai ɗan iska ne? a kashe Alhajin shine za ka zauna ka na tambayata lambar Police Dan Ubanka? kai ba za ka iya zuwa da kanka ka nemo su ba? Ba akwai mukullin mashin ɗin da nake aikenka a wajenka ba??" Ta yi maganar ta na huci kamar bujimin Sa. Tala Me Gadi ya na jin haka ya juya ɗakinsa da gudu, ba daɗewa ya ɗakko mukullin ba tare da ya dawo gurin Hajiya Laure ba ya zabari mashin ya fice kamar ya tintsira sabida sauri. Har su ka dawo tare da Ƴan Sanda Hajiya Laure tana harabar gidan ta na zagaye, daga ta kai mari sai ta kai gwauro, sai surutai ta ke yi tamkar sabuwar mahaukaciya. Ta na ganin Ƴan Sandan ta yo kansu ta na cewa "Wai kamar ni za a kashewa Miji?? Alhaji Salisun za a kashe?? shekararmu kusan Talatin da Aure amma yau ɗaya a kashe min shi? Inspector lallai ka kama kowaye ya aikata sannan ka tabbatar an hukunta shi, wallahi ko me ka ke so zan baka, kai ko duka dukiyar da Alhaji ya bari ce zan baka ni ban damu da cin gadon dukiyarsa ba kawai Fansar Ruhinsa nake buƙata!!!." Inspector Khalil ya jinjina kai kana ya ce "Mu je ki raka mu inda abin ya faru." kafin ya rufe baki ta juya ta na cewa "Ku tawo." Bin bayanta su ka yi zuwa Falon Alhaji Salisu, har lokacin Yazeed ya na gurin ya na ɓarza kuka tare da faɗin sai ya ɗau Fansa. Har Ƴan Sanda su ka gama bincike-bincikensu su ka yiwa Hajiya Laure da Yazeed da Tala tambayoyi ba abinda su ka fuskanta game da kisan, illa iyaka sun shaida wanda ya yi kisan ba ƙaramin makashi bane don kuwa ba wata alama da ya bari wadda za ta nuna cewar shi ne. Gawar Alhaji Salisu Ƴan Sanda su ka ɗauka zuwa Asibiti, wurin ya rage daga Inspector Khalil sai Constable Saleh sai Hajiya Laure da Tala. Har zuwa lokacin roƙonsa take kamar ta yi masa sijjada akan ya nemo mata wanda ya kashe mata miji. Cikin salonsa na iyayi da kwainane ya ce "Kar ki damu Hajiya ai hakan aikina ne, yanzu kamata ta yi mu je Asibitin mu gani don haka ke ki yi gaba ina zuwa, zan tafi da wannan me gadin naku don ba yadda za'ayi a ce bai san anyi wannan kisan ba dole da sa hannunsa." Hajiya Laure ta sharce ƙwalla gami da majina cike da farin cikin jin furcinsa ta ce "Na gode IP sai kun zo ɗin." kai ya gyaɗa mata kana ya nufi hanyar fita cikin takunsa na ƙasaita da jin kai, Hajiya Laure ta bi bayansa, Constable Saleh kuma ya cukumo Tala me gadi. Har Inspector Khalil ya ɗaga ƙafa zai shiga mota Constable Saleh ya dakatar da si da cewa "Sir!! na yi ƙoƙarin danne abinda ke raina amma na kasa, wallahi da alama ka fara aiki a wannan Office da ƙafar hagu domin da alama SARƘA ta yi Rikicinta a wannan gida." Fasa shiga motar ya yi cikin rashin fahimtar inda kalamansa su ka dosa ya zuba masa idanu kana ya ce "Me ka ke nufi da haka? wacece SARƘA??" "Ba mace ba ne, Sunansa na gaskiya MUHAMMAD RISLAAN MUHAMMAD amma kowa da kalar sunan da yake kiransa sabida ya buwayi duniya, Sir! ina ganin a lallaɓa Hajiyar nan a rufe wannan Case ɗin in ba haka ba kai ma zaman Office ɗinnan sai ya gagareka, na ga irinka da yawa waɗanda su ka zo su ka koma sabida buwayar Yaron nan." Murmushin rainin hankali Inspector Khalil ya yi kafin ya ce "Ina ne gidansu??" Cikin zaro ido Constable Saleh ya ce "Ka yi mini rai ka gafarce ni Yallaɓai kar ka ce za ka kama bawan Allahn nan, wallahi idan ya san ni na gaya maka shi kenan na mutu, Yallaɓai ina da mata da ƴaƴa uku yanzu ma ta na ɗauke da juna biyu, ka temaka min kar ka yi silar zaman iyalina marayu." Inspector Khalil ya dafa kafaɗarsa cikin sigar rarrashi ya ce "Kai fa Jami'i ne akan me za ka ji tsoron wani karankaɗa miyar mutum? kar ka damu ba zan bari ya san kai ne ka faɗa ba, yanzu bani information nashi, a ina za mu same shi?" Jiki na rawa Constable Saleh ya ce "Ban sani ba Yallaɓai shi kamar iska ya ke ba shi da tabbas, idan ka ganshi anan a yanzu za ka ganshi a can, amma ina da lambar Ɗan uwansa malamin wata makarantar Islamiyya idan ka kira ka tambaya tayuwu ya na makarantar amma fa sai sa'a za a same shi." Cike da jin daɗin hakan Inspector Khalil ya ɗan bubbugi kafar Constable Saleh ya na wani irin murmushi me cike da ma'anoni, cikin salonsa na iyayi ya ce "Jami'i me basira, ba ni lambar." Cikin rawar jiki Constable Saleh ya miƙawa Inspector Wayarsa ba tare da ya ce komai ba don kuwa ya hau dokin tsoro da firgici, ya gama sallamawa ya sa a ransa kwanansa ya ƙare. sai da kiran farko ya katse a na biyu aka ɗaga tare da yin sallama, Inspector Khalil ya amsa sannan ya ci gaba da cewa "Ina magana da Sheikh Auwal ne??" a ɗaya ɓangaren Sheikh Auwal ya ce "Eh ni ne amma ban gane me maganar ba." "Sunana Inspector Ibrahim Musa Rano wanda aka fi sani da Inspector Khalil, ina neman Muhammad Rislaan Muhammad ne." dimm!!!! Zuciyar Sheikh Auwal. "Muhammad Rislaan Muhammad?? What Happened??" Sheikh Auwal ya faɗa cike da tsoron abinda zai fito daga bakin Inspector. "I suspect him of murder, so i will arrest him, i need his informations, ina son sanin inda zan sameshi, ka ba ni haɗin kai Ya Sheikh kar ku wahalar da hukuma." wani irin tuƙuƙi zuciyar Sheikh Auwal ta ke yi gami da tsalle tamkar za ta fasa ƙirjinsa ta fito, cikin tsantsar ɓacin rai ya ce "Kar ka kuma tambayata bayanan Akhiee domin ba shi da tabbas, yau dai ka yi sa'a ya zo makaranta, ka zo nan ka same shi." Farin ciki ne ya lulluɓe Inspector Khalil, ya murmusa sannan ya ce "Godiya nake Sheikh Auwal sai na zo ɗin." Constable Saleh ya ce "Yallaɓai na ga ka na murna?" "Na samu inda ya ke cikin sauƙi, ka ga dole ne na yi murna, ba ka sani ba ne dominsa aka turo ni nan aiki ba zan gushe ba har sai na ga bayansa, yanzu Asibitin ya kamata mu je ko Makarantar?" "Yallaɓai na san ana buƙatarka a asibitin nan ko ba za ka yi komai ba ya kamata a ganka, mu je can ɗin in yaso daga baya sai a je makarantar" Constable Saleh ya yi maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka. Dariya Inspector Khalil ya yi sannan ya ce "Ka na da tunani me kyau, ya kamata ka zama babban Jami'i." Daga haka ya shige mota, Constable Saleh ma shiga ya yi a ransa ya na cewa "Bayan ka gama kashe ni tin yanzu" Tala me gadi kuwa banda kuka ba abinda ya ke rusawa ya rasa ma ko bakin magana bare ya ce musu shi bai san anyi kisan ba. Kai tsaye Asibiti su ka nufa don ganin yadda komai ke tafiya a ɓangaren binciken gawa. Babbar Makaranta ce me ɗauke da sassa da ajujuwa daban-daban, makarantar na ɗauke da ɗumbin ɗalibai masu yawa manya da ƙanana, mata da maza, akwai wadatattun malamai masu koyar da ƙira'a daban-daban ba wanda ba'a yi a makarantar indai na Islam ne. a wani babban Aji me ɗauke da mata da maza kowanne gefen zamansu daban, duk ɗinsu sun duƙufa akan karatunsu, daddaɗan sautin karatun Qur'ani ne ke tashi ta ko'ina a ajin gwanin sha'awa. Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa ta Malami ya zuba tagumi da duk hannayensa, tunanin ma irin hukuncin da zai yiwa Rislaan ya ke, a duk iya tunaninsa ba hukuncin da zai iya yi masa wanda ya wuce yi masa shegen duka. Miƙewa ya yi tsaye ya na rarrabawa ɗaliban nasa idanunsa da su ka yi jajir sabida ɓacin rai, "A dakata!" ya faɗa cikin kamilalliyar muryarsa. Shiru ajin ya yi kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa, an kai 10 second cikin yanayin shirun sannan Sheikh Auwal ya ce "Zahra'u Muhammad!" cikin sanyin jiki ƴar budurwar ta miƙe gami da cewa "Labbaika" Ganin irin halin mugun ɓacin ran da ɗan uwan nata ke ciki ya ƙara karyar mata da zuciya, zirrrr hawaye su ka fara sharara akan kumatunta. Sheikh Auwal bai bi ta kan kukan nata ba ya ce "Maza ki hau sama ki kira min Akhiee, sannan ki bi duk ajujuwan makarantar nan ki tattaro min duk Malaman cikinta ina buƙatarsu a yanzu!" Da kyar ta ɗaga ƙafarta wadda ke faman kakkarwa ta nufi hanyar fita, ta na fita kukan da take dannewa ya samu nasarar kufce mata, shi kenan yau Akhiee ya mutu abinda zuciyarta ke ƙissima mata kenan don haka kukan nata ke ƙara ƙarfi. Duk ajin da ta yi katari da shi sai ta shiga ta kira malamin cikinsa sannan ta wuce har ta hau sama.... Tsaye yake hannunsa dafe da ƙarfen kariya na bene... SHARE DOMIN ALLAH Paid Book ne....... *INDO* [8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 3 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *Mikiya Writer's Association🦅* Matashi ne wanda bai wuce shekara Ashirin da Biyu kacal a duniya ba, Fari ne tas tamkar da an taɓa fatarsa wurin zai yi tabo, Allah ya yi masa baiwar kyawu irin na musamman ɗinnan, ya na da dogon hanci siriri kamar ya yi magana, sai idanunsa dara-dara fararen cikinsu karr suke sai kwarjini kamar na Namijin Zaki, bakinsa ɗan madaidaici ne a tsuke tamkar bai taɓa buɗe shi ba ma bare ya yi magana ko cin abinci, fuskarsa a ɗaure tamau kamar wanda aka yiwa Albishir da wuta. Sanye yake cikin Farar Jallabiya tass wadda ta yi matuƙar karɓarsa kyawunsa ya ƙara fitowa tamkar balarabe. a memakon aski sai wani tumemen kitso ne ƙwalli ɗaya tal kamar rai akan nasa, zanen hannu biyu ne an ɗauke shi tin daga gabannin goshinsa har sai da ya sauka a bayansa, ya saƙu ya yi kyau sai ƙyalli da walƙiya yake, dukkan yatsun hannunsa biyar idan aka haɗa da na ɗaya hannun goma sanye suke da wasu arnakun zobuka wanda su ke wani irin sheƙi da walƙiya gami da ɗaukar idon me kallonsu, wasu sirara wasu kuma manya. Gaɓoɓin yatsun kuwa jajir suke da jan lalle sun yi kyau kamar a sace a gudu, ko na wata macen Albarka. a ɗan nesa da shi ta tsaya cikin muryar kuka ta ce "Akhiee! Sheikh Auwal na kiranka" Ko gezau bai yi ba wai da sunan anyi masa magana, ta san ba zai ce uffan ba don haka ta ci gaba da tafiya. Wata ƴar hula wadda ake kira taɓani ka ji hadisi ya zaro a Aljihunsa ya kife kansa kana ya fara takawa saɗaf-saɗaf kamar me tsoron ƙasa. Lokacin da ya gama ƙalelejinsa ya je kiran tuni dukkan malaman da aka kira sun halarta saura shi kaɗai ake jira. Ba tare da shakka ba ya ratsa tsakaninsu ya wuce ya dangana da Sheikh Auwal sannan ya durƙusa ba tare da ya ce cikal ba. Girman kansa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke fusata kowa da shi, ganin yadda ya zo ya durƙusa ba tare ya ko kallesu ba ya ƙara dugunzuma Sheikh Auwal. "Ba ka iya gaida manyanka ba?!!" Sheikh Auwal ya faɗa cikin tsawa. tamkar dutse aka yiwa magana haka Akhiee ya yi. Yasayyadi Jameel ya dubi Sheikh Auwal gami da cewa "Alagafarta Malam me ya faru ne?" "Gashi nan ku tuhume shi, kisan kai ya aikata" Sheikh Auwal ya faɗa bakinsa har

Chapter 1 of 19