damuna ba, Ammi dan Allah ki dinga min addu'a, kaina ciwo yake kamar zai rabe biyu, jikina tsami kamar an min duka, Ammi hankali na ya gushe,Ammi da halin dana ke ciki gwanda mutu..."
Toshe mata baki Ammin tayi Salwa da ta tashi a lokacin da sauri ta rungume Salwa ta baya, tana kuka, sakamakon jin kalaman ta,
Abban su ne ya shiga da yaji magana da koke koke,ganin Salma ne ya sanya shi qarasawa da sauri ya zauna a gefen gadon su, kamar wadda aka wurga haka ta fada jikin shi tana kuka,
"Abbaa ku taimake ni, mugaye ne, zasu iya kashe ni, Abba dan Allah ku taimaka min"
Qanqame ta yayi sosai jin yanda take shigewa jikin shi kamar wani zai dauke ta, shi kan shi ya kasa riqe hawayen shi, da kyar suka samu ta daina sambatu da surutai,
Ruwa mai zafi Salwa ta je ta dora, dan Salma ta samu tai wanka ta gasa jikin ta.
Bayan ya tafasa ta juye ta kai mata toilete din su, ta fita, har Salma zata shiga, ta qanqame hannun salwa.
"Kar ki barni ni daya, zai iya shigowa, dan Allah muje ki tsaya ni"
"Wai Salma wa kk magana akai ne? Me kk fada, waye zai kashe ki?"
"Iiiii...........
Tadaaaaa, sai gobe ko anjima zakuji ci gaba inshaa Allahu, stay happy, a dinga addu'a a riqe Allah, kar ai sakaci da ibada itace babban makamin mumini. Much love to u all for ur stars๐๐
KALAN DANGI...PAGE 15
991 93 4
by Haermeebraerh
Following
Ji tayi bakin ta ya kasa furta komai, ga sunan a cikin labban ta da harshen ta da muryar ta dika amma ta kasa furta shi, kuka ta sanya mai qarfi, a cikin zuciyar ta take jin maganar Irfaan, saurarawa tayi tabbas maganar Irfaan take ji,
"Salma ni fa masoyin ki ne, kina so na, ina son ki, in kk fadi me ke tsakani na dake zan iya rasa ki, kema zaki rasa ni, kina son haka ta kasance?"
Kada kai ta fara kamar qadangaruwa, tabbas bata son rabuwa da soyayyar shi, dan kuwa ba abinda ke mata dadi, da kuma zafi a rai sama da son Irfaan Maleek, shiru tayi, tambayar duniya anyi taqi bayani, har suka gaji suka kyale ta.
Salma ta koma silent, bta cika magana ba, kowa ya so ya maida rayuwar shi kamar da amma abun yaqi, saboda watarana zata tashi da bacin rai, kowa sai ya amshi rashin kunya da fitsara, ga yawan kwadayin tsiya da sata da Salma ta koya, in ta ga abu tana so madadin ta dauka ta tambaya sai dai kawai ta sata ta cinye, Ammi tayi nasihar tayi fadan, amma abun yaqi yuwa ta gyara,har Ammi da Abba tana iya nunawa da yatsa ta basu umarni yanzu, ga shga irin ta rashin kunya yanzu da take yi, in an hana ta fita sai fa ta fita, kalan dangin qawaye kuwa sai abinda ya ci gaba, wataran Irfaan zai dauke ta sai ta kwana uku k sama da haka ba a gan ta ba, nan da nan mutane suka fara kiran ta zama 'yar iska, bin maza take, in taje tai kwanaki sai ta dawo.
Ammi da Abba sunqi yarda da hakan, zuqatan su suna nuna masu cewa tabbas akwai wata matsalar da take damun diyar su, kuma ko ina maganin matsalar yake da izinin Allah zasu nemo ta.
Salwa da Ubaidullah yanzu kusan ko da yaushe in suka fara hira a Family group sai su kebe kuma a PC su dasa tasu, Ubaidullah bai san me yake ji game da Salwa ba, amma tabbas ya bata matsayi mai girman gaske a zuciyar shi, ta yanda ba ya iya bacci bai magana da ita ba ko kuma basuyi chatting ba, ko yana gida Nija ko ya fita wata qasar.
Azumi ya gabato ganga ganga, inda kowanne musulmin kirki yake qoqarin samun dacewa a wannan wata mai alfarma da albraka, kowa ke neman ya sake kusanta kan shi da Allah mahaliccin shi.
Wasu kuma ran su a bace yake da zuwan watan Ramadan din, saboda dole zasu aje wasu abubuwan ko ba dan Allah ba, cikin masu wannan dabi'a kuwa harda Salma, dan kuwa ji tayi ina ma ayi tsallaken watan. Ina ma a hana yin azumin kwata2.
1
Heedayaa qanwar Irfaan musulma ce, wannan dalilin ne ma ya sa ita bata zaune da ahalin ta, tana can qasar Iraqi ita da sauran dangin su musulmai, sai lokaci zuwa lokaci suke kai wa 'yan uwan su ziyara, Irfaan Heedaya ya bari akan ta zauna da Salma saboda gabatowar azumin, da kuma cikin shi da take dauke da shi.
Haka kuwa akai, Irfaan na tafiya, sakamakon daure kafurai daga cikin aljanu da ake, har sai bayan azumi a sake su, Heedaya ta maye gurbin.shi,zaman ta tare da Salma sai ya sa Salma nutsuwa ainun, abun har yana bama iyayen na su da Salwa mamaki.
Wannan nutsuwa har tayi yawa.
In Salma ta fara karanta qur'ani da wata qira'a mai dadin sauraro,sai mutan gidan sun tsaitsaya a bakin qofa ana leqen ta, musamman in suka ga da ka take yi, ma'ana ta haddace dika, wanda ko Salwa da take hadda har yau bata kai qarshen qur'ani bango d bango ba, a kwana uku Salma ke karance qur'ani kaf kuma a haddace.
Addu'a sosai Ammi da Abba da dik wani masoyin su, suka dirfafa a wannan wata mai alfarma akan Allah ya bawa Salma lfy, dan tsoro take bawa mutane yanzu, kamar ba mutum ba haka take abubuwa.
Ga aiki in ta fara jikin ta har rawa yake, da ta kama abu yanzun nan zata gama, kuma ba wanda ya isa ya hana ta yi, dan kuwa sai tayi ta ihu tana burgima a qasa.
Tana aiki tana karatu ko tasbihi haka take abubuwan ta, sannan lokaci zuwa lokaci zata dau waya ta shiga social net.
Dik wasu qawayen Salma sai da Heedaya ta raba su, saboda kishi take ji, yanzu ji take ta samu wajen zama, ba Irfaan ba ko mahaifin su bai isa ya fidda ta a jikin Salma ba.
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Halin Salma na sata na nan, dan kuwa kwadayin da take ji irin na masu ciki baya barin ta ta zuana lfy, Heedaya kuwa bata hana ta, in ma ta sato tare suke cinyewa.
Azumi ya zo qarshe, mutanen Abuja sun zo gaba dayan su domin Sallah,gidan su na gado babban gida ne, gashi Uncle Ibraheem da Uncle Isa sun maida shi na zamani, dik da Uncle Isa taimakawa kawai yayi amma Uncle Ibraheem shine qarfin komai, har saman bene aka dora.
Dakuna da parlour guda biyu babba da qarami sannan kowanne daki akwai bayi cikin shi, sai bayi daya a wajen gidan, mai gadi na da daki daya da parlour inda yake zaune da iyalin shi Haule, saboda sai shekara ahalin gidan ke zuwa dikan su ko kuma in za ai wani taro na gaggawa ko biki, ko suna.
Haule na taimaka masu da wanke2 da share2 da kuma goge2, dik da ba ita daya bace amma itan ce kamar shigabar masu aikin in sun zo hidima, kowa yakan taho da mai aikin shi, daya ko biyu.
Gida ya cika da iyali,masu wasa nayi, masu karatu nayi a babban parlour kowa da inda yake karantawa, masu bacci nayi, marasa azumin na can na dafa abinda zasu ci,
'Yan mata ne a qalla zasu kai sha biyar kk shida.
Maza kuwa mutun sha takwas ne gaba daya, sai iyayen su maza da mata.
Gida yayi albarka ainun, ga tarbiyya da kamun kai a wajen yaran.
Yau kwanan su biyu a gidan, Ammi ce ke sanar da masu aikin abinda za a dafa, matar Uncle Isa da Uncle Usman, sai uncle Ibraheem, su na zaune a qaramin parlour inda qofar kitchen ke nan, Salma da bata son hayaniya tana manne da Ammin su, da sun gama su koma dakin su,dan ita a dakin su Ammi da Abba ma take kwana, saboda tsabar bata son ta shiga cikin sa'o'in ta.
Matar Uncle Isa ce ta fara magana qasa2, wanda Salma kamar maciji haka take jin su.
"Na fara gajiya da wanan me shegen iyayin, yanzu tinda muka zo, mune manya, ita ke zuwa ta fadi me za a girka, dik ta san me mazan mu ke so, d an gama su hau wani yabon ta, gaskiya dole mu nuna mata mune manya,"
Matar uncle Ibraheem ce ta amshe,
"Ashe ba ni kadai abun ke ba haushi ba, dik sanda muka so tinda aka auro ta take mana wannan iyayin,abun na mugun damu na, muje mu ce ba za a dafa wanda ta bayar ba muji in ta isa ta sauya me muke so ayi, ai ba gidan ta bane gidan gado ne"
Salma ce ta tako gaban su ta tsaya, idanun ta sun yi jawur, ta kalle su,
"In ga wata 'yar iska me qaramar kwakwalwa taje ta sauya abinda Ammi na take son a dafa, me kuka iya? Me kuka sani a girki banda a dafa a baku ku lamushe a gidajen ku? So kuke kuje ku fe a dafa mana tuwo miyat kuka da azumi? Dan na san shi kadai kuka sani, wata ta tashi ta gani balle har ta tinkari uwata da wata mummunar magana, kun dai san abinda zan iya da wanda ba zan iya ba ko?"
Cikin sauri suke gyada kai, daa tin fil azal da suka ji tana da aljanu suka fara jin tsoron ta, musamman da suka ji labarin yanda nata suke, sun maida ta kamar aljanar ita kan ta.
Ido kawai suke rarra bawa, Mummy matar uncle Ibraheem ce cikin dakiya, dan a matsayin ta na babba bai kamata 'yar cikin su ta zauna tana karanta masu suna haddacewa ba.
"Fitsararriya, in baki ba ai ba za a ce itace Uwar ki ba, 'yar yarinyar ki dake kin yi haddar kissa da munafurci ko?"
Wani wawuyar hambara Mummy taji a bakin ta, sai da jini yayi tsartuwa, ihu da qarar ta ne ya janyo hankalin mutane, kowa ya shigo wajen, nan da nan kuwa wajen ya cika, ana tambayar me ke faruwa, Salma kuwa zuciya da fushi sun sa Heedayah ta rinjaye ta.
Wani gurnanin bacin rai kawai take saki, tsoro ya turniqe mutanen wajen ganin yanda gashin hannayen ta ke miqewa, idan ta yayi jawur, Ammi ce ta taka a hankali, ita da Salwa, suka riqe hannayen Salma da ke rawa.
Addu'a suka hau topa mata, nan da nan ta fara nutsuwa, itama tana bin addu'ar da suke mata, a jikin Ammi ta jingina tana hamma, bacci ya zo, ratsawa sukai ta cikin mutane Ammi ta kai ta dakin ta ta kwantar, suka mata addu'ar bacci suka tofa mata sannan suka fita, Mummy baki ya yi zumbutu ta qasa, yayu ja daidai inda aka fasa din, sai hawaye take zubarwa tana fakaicewa da kukan takaicin rashin kunyar da Salma ta mata ne, anyi anyi ta fadi wacce iriyar rashin kunya aka mata, taqi fada,tace a bar maganar ai Salma 'ya ce a wajen ta ba sai an hukunta ta ba.
1
Haka aka bar ta da me ta fada din.
Ranar sallah kowa ya ci ado na ban mamaki, an yi abinci kala2, iyayen maxa da wasu daga yaran maza sun yi layya, har iyayen mata ma an yanka masu nasu abun yanka, masu aiki kuwa sai kai kawo suke ana gyara nama ana soyawa, wasu daga yaran na taya su.
Ubaidullah da Salwa ne zaune a wata kujera dake parlour, suna hira, Ubaidullah yanzu ya gama amincewa ran shi son Salwa yake, kuma a yau yake son sanar da ita, sai dai gidan cike yake da mutane masu ziyara da kuma ahalin nasu, dan haka yake roqon ta akan ta zo su fita, akwai maganar da yake son fada mata,kunya taje ji sosai, dik da ba wanda ya dan tana son shi, amma ita a ran ta ta san tana son shi, dan haka bata jin zata iya fita da shi, kar taje ta kasa danne abinda take ji game da shi.
"Pretty plss, wani abu zan fada maki, ina gama fada ko kwarzane ba zan maki ba zan dawo dake,in ma tsoro na kk,ni ne fa yayan ki, wanda kk so,"
Da sauri ta daga kan ta, tana zaro ido, in ina ta fara,
"Niiii niii yaushe naceee iiiiinaaa son ka?"
"Jiya"
"Da yaushe?"
"Da daddare"
"A ina?"
"A cikin bacci na, nai mafarkin kin ce kina so na,kuma kin bani mallakin zuciyar ki da ganganr jikin ki, muna zaune a inuwa daya ta ma'aurata,"
Kunya ce ta kama ta iya wuya, rasa inda zata saka kan ta tayi dan kunya, dariya ya tsaya yana yi yana kallon bayan ta, saboda kwantar da kan ta da tai a kan cinyoyin ta tana dariya, gashin ta da ta daure, ta nannade yana zaune dass qasan daurin dankwalin data kafa, yalwataccen bayan ta mai kwantaccen gashi ya bayyana, saboda zamewa da mayafin ta yayi, cikin sauri ya dauke kan shi yana ta'awizi, saboda wani abu dayaji ya ratsa jikin shi.
Qara suka ji an kwalla, da qarfin gaske, tabbas wannan muryar Salma ce ba ta kowa ba,
A kidime Salwa ta tashi ta kwasa da gudu, sai sama, inda dakin su Ammi da Abban su yake, tana shiga taga Salma yashe a qasa, ta ware qafafun ta, tana ihu, ta hada zufa sosai, tana nishi, Ammi dake bandaki tana alwalar azahar itama bata idar ba ta shiga, ganin halin da Salma ke ciki ne yasa Ammi ta rufe qofar saboda kar wani ya shiga, gani sukai ta qanqame zanin gadon da take kai ta sake kurma wani ihun mai qarfi,
Ammi ma kuka ta saka sosai saboda gane me Salma ke yi da tai, wannan wanne irin aljanu salma ke tare da su? Suna nuna masu komai ido da ido..........
Nima ban sani ba, ku tambayi Irfaan Maleek, wa ce zata iya tambayar shi cikin ku๐๐
KALAN DANGI....PAGE 16
937 87 5
by Haermeebraerh
Following
Salwa ce zata isa gaban ta dan rife mata jikin ta Ammi ta dakatar da ita, dan so take ta ga ni shi da gaske diyar ta ta ta rasa budurcin ta ko ya abun yake, zuciyar ta na matsanancin bugawa bakin ta ya qafe dan ba digon yawu cikin shi, haka ta isa gaban Salma, leqa ta tayi tagan ta a hade, ba inda ya samu matsala a gaban ta, zama tai a bakin gadon tare da fashewa da kukan farin ciki, a tinanin Salwa wani mummunan abun ne ya sami Salma har Ammin ke irin kukan nan, zuwa tayi ta durqusa a gaban Ammin tana tambayar ta lfy? Bata iya ce mata komai ba illa tashi da tai ta rarumi wayoyin su, kunna karatun qur'ani tayi a daya, a daya kuma ta kunna ruqya, tayi haka ne dan rage ihu Salma da ke fita har waje, sannan su sami sauqin matsalar.
Wani qara tayi na qarshe, sai tayi baya tana maida numfashi, Irfaan da ke ganin jaririn shi ya iso duniya, zuwan shi kenan dan ya shiga jikin Salma amma ya tarar tana naquda, ga Heedayah na taimaka mata,idanun shi zubar da hawayen farin ciki suke, shima yau ya samu magaji,yaron na kama da shi sosai, Salma ce take magana cikin azabar da ta gama sha.
"Heedayaahhhh, na san kina nan, na san kina ji na, na san dik me yake faruwa, dan Allah na baki amanar abinda na haifa, ki kare min shi da rayuwar ki, na mallaka maki abinda na haifa, ki tabbabar bai tashi a cikin kafurci ba, ki tabbatar ya kafa daular musulunci, ki tabbatar koda ya gaji mahaifin shi a mulki shi a matsayin Maleek musulmi zai zama,in kk min haka na yafe maki dik abinda kk min na cin amanar qawancen mu"
"Na shiga Uku, Salma, Salma magana kk da aljanu kuma, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Salmaa,ke kira min Abban ku, ba zan iya zama da yarinya da wannan lalurar ba,"
Cikin kuka Ammi ke magana, zuciyar ta ta gama karyewa, ina zata saka ran ta, 'yar ta na bada wasici ma aljana, gashi ta gama tabbatarwa ta haihu,ta haihu da aljani kafuri kenan, wayyooo Allah wannan wacce irin musiba ce, kullum cikin kwanciyar hankali suke a rayuwar su, basu taba fadawa wata musiba ba, yau gashi lokaci daya qaddarar Allah ta zo gare su, qaddara mai firgitarwa.
Salwa na bude daki taga Ubaidullah tsaye a jikin qarfan saman, ya duqar da kan shi, dik ya kori kowa, saboda baya son su tsaya jin meke faruwa, dan ya riga kowa zuwa, kusan a tare suka isa da Salwa, jin meke faruwa yasa da Salma ke ihu ya tsaya a wajen, ya hana kowa zuwa kusa da hanyar dakunan ma, har iyayen su mata.
Murmushin qarfin hali ya yi wa Salwa sanda ta fito, tana ganin shi ta tafi da gudu ta rungume shi ta fashe da kuka, wani iri yaji a jikin shi, qoqarin cire ta ya dinga yi a jikin shi amma taqi sake shi, kuka kawai take,
"Salwa....Salwaaa...sake ni muyi magana,sasssalwaa,"
Daga kai tayi a hankali idon ta na ci gaba da tsiyayar d hawaye, baya ta ja tana furta kalmar 'hakuri' ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi, dan kuwa ba zai qarya ba ta jefa shi wani yanayi mai wuyar fassara.
"Yah Ubaidullah Salma bata da lfy, Salma na cikin matsanancin hali, na rasa ya zan na taimaka mata, in ban iya taimakon ta ba sai naji kamar i am worthless sister, dan Allah ya zan yi? Iyayen mu suna cikin matsananciyar damuwa, Salma is in pain"
"U ar also in pain my dear, ki kwantar da hankalin ki zaki taimaka ta hakan, domin in iyayen ku na ganin ku gaba daya ba lfy hankulan su sai sunfi haka tashi, in ya zama kin saka damuwa sosai a ran ki har kk samu wani ciwon kinga jinyar da zasuyi ta zama biyu. Ki zama kwarin guiwar su,ki zama farin cikin su, je ki kirawo Uncle Jajaludden saboda na san Ammi needs hin now"
"Sure"
Da sauri ta fita harabar gidan, inda su Abban ke zaune a kujerun roba, an cika table din gaban su da baqin shayi wanda mai gadi ya dafa masu da hade2 na maza ciki, sai gasasshen nama, da fruits, kafin ta isa sai da ta daidaita nutsuwar ta, ta sanya mayafin ta akai, ta yanda ba lallai ya ga idanun ta ba.
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Durqusawa tayi ta gaishe su, sannan ta sanar da Abban nasu Ammin su na kira, sai da Salwa ta tafi yayun shi sukai ta tsokanar shi,
"To mijin hajiya, hajiya na kira,"
Dariya sukai ta mishi, shi kuma yana jin nauyin su, ji yayi kamar kar yaje saboda nauyin 'yan uwan shi, amma ba zai iya tsallake kiran Ammi ba, (hakkaa, ina son macen da ta san kan ta ta mallake miji aradu,mallaka da kyautatawa ba da boka ko malaman duba ba, ta yanda ko a gaban idon ta ko a bayan idon ta take da mahimmanci da qima da kuma darajar da ba za a iya qetare maganar ta ba kowacce iri ce kuwa, i love love๐)
1
Koda ya je yaga Ubaidullah tsaye idanun shi sun sauya kala, da sauri ya qarasa.
"Me ya same su? Sanar dani kafin n shiga, in wani abu ne ya same su ban san ya zan da rayuwa ta ba, mahaifiyar su ta koya masu boye damuwa, ban fahimci komai a fuskar Salwa ba, amma ganin ka ya tabbatar min ba lfy,"
"Uncle pls calm ur self down, ba bu fa abinda ya faru, kawai ciwon Salma ne ya dan motsa, kuma an samu nasarar yi mata ruqya ya kwanta, yanzu an dai kira ka ne ka ga yanda take,"
Cikin jin kwanciyar hankali kadan ya murda knob din qofar ya shiga, kwance Salma take, tana hango shi ta fara kyabe baki irin na shagwabar nan, Ammin ma haway ne ya zuba mata, gaba dayan su kwantawa sukai a jikin shi har Salman suna ji da junan su sosai,shine qarfin su, shi ke lallaba su in sun karye a zuciya du samu kwarin guiwa.
"Me ya faru?"
Nan Ammi ta bashi labarin me ya faru, ya yi matuqar razana, da jin wai salma ce ta haihu da aljani, aljanin ma kafuri, tabbas dole ne ya fita ya nemi malamai masu ruqya a yi ta ruqyar da zata sa su barta kwata2.
"Ina zuwa, sannu ko babyn Abba,Allah zai baki lfy,"
Fita yayi ya je zai wuce yayun shi,cikin tsokana Uncle Usman yace,
"Me aka aike ka siyowa mijin hajiya?"
Juyawa yayi suna hada ido da dan uwan nasu hankulan su ya tashi, da sauri har suna rige2n isa gare shi.
"Me ke faruwa? Ba dai salma bace ko?"
"Salma ce Yaya,"
"Subhanallah, yanzu ina zaka je baka sanar damu me yarinyar mu ke ciki ba?ka kyauta kenan zaka fita ba tare da ka sanar damu komai ba?"
"Yaya kuyi hakuri, bana son bata maku moment din da muke haduwa muyi building memories masu dadi a cikin shi, sai shekara shekara muke samun haduwa haka,"
"Kar ka sake irin wannan abun da kai, zo nan"
Zuwa sukai suka zauna, suna jira suji me yayan nasu zai ce,
"Kira Malam Hussain, ya zo nan gida, in ma ba halin zuwa sai driver ya dakko shi, koma wajen iyalan ka,suna buqatar ka a kusa, na san yanda kusancin ku yake, in ba kai kusa yanzu zasu shiga cikin damuwa"
Da sauri ya kira Malam Hussain, ya masa bayani, yace za a zo daukan shi, a kawo shi har nan din, ya fadi inda yake, sanar da shi inda yake yayi suka bama drivern Uncle Isa waya, yaji ko ina ne, ya gane waje, dan haka key din
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 17