Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
"Here, na san har da yunwa, tinda rabon ki da abinci tin daren jiya, shanye sai ki je sallar,"
Ba musu ta shanye dan sai a lokacin taji wata yunwa na taso mata, ta aje mug din, sannan ta yi qoqarin tashi, Salwa ta taimaka mata taje tayi alwalar ta dawo, ta mata shimfida ta zauna ta fara rama sallolin da ke kan ta.
Ita ko salwa da taga dakin su Ammi an kashe wuta.sai bata sanar da su ta tashi ba.
Ta wuce kitchen ta dafa ma ta fev din ta wato indomie da kayan lambu da kifi.
Nan da nan gida ya dau qamshi, Ammi ce ta bude qofa ta fita, sanye take da rigar baccin ta har qaurin ta, sai ta saman wadda take ja da qasa saboda tsaho, sanye kanta yake cikin hula kalar kayan.
Tayi kyau sosai, ta daurs rigar da igiyar ta tace
"Salwa girki da tsohon daren nan? Qarfe biyu da kwata fa,"
"Ammi Salma ta farka, yanzu haka sallah take, shine naga ta dade rabon ta da abinci, ya kamata ta ci, ko kan zai daina mata ciwo, dan ina zaton harda yunwa ma,"
Kwalla ce ta taru a idon Ammin, ta dafa kafadar Salwa, tare da sakar mata kiss a kuncin ta,
"Allah ya miki albarka, maza to ki kammala ki kawo, sai na bata taci, kin san taurin kan ta akan abinci, lfy qlou ma balle kuma ba lfy,"
"Haka ne Ammi, Ameen na gode"
Dakin su Ammin ta shiga ta zauna bakin katifar su, tana kallon Salma dake sallah cike da kasala.
'Ikon Allah, Salma mai son ibada,ita ke sallah haka, tabbas akwai matsala, ko mai munanan halayen ta na san ita yarinya ce mai ibada'
Tana cikin tinani Salwa ta shiga ta aje abincin, ta zuba ma Salma ido itama, sun dan ja wasu mintoci kafin Abba ya biyo sahun matar shi,ganin Salma na sallah,sai yayi murmushi, tabbas akwai sauqi kenan.
Zama shima yayi ya dafa hannayen salwa dake matse hawaye, tausayin twin din ta ya gama karya zuciyar ta.
Sai da ta ida dika sannan ta juya, ta gaida Abban, ta hanyar fadawa jikin shi, ta fashe da kuka, shima hawayen ne ke zubar masa, yanzu kam jarumtar shi ta qare.
"Abba ban da lfy, jikina ciwo yake min, kamar an matsemin haqarqari nake ji, kaina tsananin ciwo yake min,Abba ka min addu'a plsss"
Kuka kawai suke a dakin, haka bata taba samun wani a gidan ba.
Sake qanqame ta yayi yana kissing kan ta, tare da fadin
'As'alallahal azeem, rabbul arshil azeem an yashfiki,"
Ya kasa sanya su a lips din shi sai a zuciya, Salwa ce ta daure tace,
"Allah ya baki lfy, taho ki ci abinci sai ki kwanta ki bacci na tabbata zaki samu sauqi,"
Kada kai tayi alamar ta qoshi, Abba ne ya zauna yace,
"Salwa je ki dakko mana abincin nan, dama yunwa muke ji gaba dayan mu, bamu ci abinci ba, in zamuyi ciyayya ne to, kici namu muci naki, ko kowa yaci tuwon gidan su? Wanda kk zaba"
Dariya suka dan yi, Salma tace,
"Naji kowa yaci tuwon gidan su, dan yanda naga Ammi na hadiye yawu ta kama Indomien nan banjin zan samu loma biyar kyawaw"
Dariya sosai suke yi, wannan itace Salman su, mai barkwanci, in taso, in bata so ba kuwa,za a ga baqin hali.
Abincin su suka zauna suka ci bayan salwa ta kawo masu, cikin nishadi kamar komai bai faru ba, Salma kuwa tini ta ware, amma dai haqarqarin ta na ciwo.
Bayan sun gama suka masu sallama suka wuce dakin su, Salwa ta tattara kayan ta koma, sai da ta tofe ayatul kursiyyu har a qofa da ko ina sannan ta kwanta, tayi addu'a ta shafa, tana kula da Salma qiwar yin addu'ar take, bata ce komai ba ta kara hannayen ta a baki, ta fara da ayatul kursiyyu uku,falaq uku, nas uku, iklas uku, sannan tai fatiha uku ta shafe ma Salma a jikin ta, bata hana ta ba, sai ma gyara kwanciyar ta da tayi,
"Ina waya ta?"
"Ga ta can, amma ba zaki dauka ba sai da safe,i don't want to see that phone near u, sai da safe, kinji ni ko?"
"Yes Ammi,"
Murmushi sukai Salwa daga baya ta fara bacci, Salma na ganin tayi bacci ta miqe cikin sanda ta dakko wayar ta, ta kunna data, bama ta da isahmsshen caji, messages ne rututu suke ta shiga.
IG ta leqa, nan ta tadda messagez din Handsome kala2, yana neman ta, dik ya damu, bai san meke faruwa ba, ya kira yafi sau a qirga, sannan ya mata messages ba reply.
Amsa masa ta fara yi, tana jin wani irin dadin damuwar da yayi dan bai ji ta ba.
Tana gama ansawa taje whatsapp, tana missed calls din shi harda vedio call, sannan ga saqonni,
Diba saman wayar ta tayi taga nan ma ga missed calls nan, tana shiga taga sunayen qawayen ta dana Handsome din nata.
Ta ji dadi sosai d damuwar da yayi akan jin ta shiru da yayi.
Amsa masa message din whatsapp tayi, kawai sai taga fuf ya na online.
"Salma oh my gudness,ina kk shiga? Na kira ki ya fi a qirga amma baki amsa va, me ya faru?"
Hawaye taji na xuba mata,anya zata iya boye mas rashin lfyar ta,tana tsananin jin son shi a ran ta, ba zata iya masa qarya ba,
"I was sick, ban san inda kaina yake ba, yanzu amma naji sauqi,"
"Ya salam, Beauty na meke damun ki, wayyo Salma ina ke maki ciwo? Do u need anything? Kina son wani abu ne?"
Murmushi tayi mai dauke da hawayen jin dadi, bata san sanda hannun ta ya rubuta masa wannan magic words din ba.
"I love u Irfaan Malik, I love u so much,"
"And i love u more Salma Jalaludden"
Wani kukan dadi ne ya sako ta gaba, ta damqe vakin ta ta hau yin shi, wayar ce ta mutu gaba daya, tai maza ta sa a caji, dan bazata so gobe ta tashi ba caji ba, bata san me zai faru va gobe.
Rintse idon ta tayi dan yin bacci, mafarki ne mai dadin gaske ya shigo mata.
Zaune take a wani katafariyar masarauta, ita da Irfaan, suna cin kayan marmari, suna kallon juna, a matsayin shi na dan sarki, wai ita ta kai masa ziyara dan su zanta su fahimci juna, auren su ya gabato, Maleek mahaifin Irfaan ya sa a kira su fadar shi, Irfaan ne ya mata jagora ta hanyar riqe mata hannu, wanda ta ji riqewar kamar wani maganadisu ke jan ta,gare shi.
Kan su a qasa, Sarki Maleek ya sha nadi, fada ta amsa sunan ta fada, mulki kuma ake zubawa, sai wanda ya gani,
"SALMA wadda muke sa ran nan da sati daya zaki zama Saurauniya Salma, sakamakon soyayyar ki da ta kama Yarima Irfaan, ina fatan kin amince da wannan hadin da za a maku? Dik da ko baki amince ba ma, mu in dan mu ya gani yana so, sai mun bashi, yanzu haka matan shi dari ba daya, ke ce zaki zama cikon ta dari biyun,"
"Na'amince Allah ya ja da zamanin ka,"
"Zaku iya tafiya,"
Irfaan ne ya dan sake duqar da kan shi qasa,
"Godiya nake Abbana,"
Daga kai kawai Sarki maleek yayi, Irfaan ya miqawa Salma hannu ta tashi, suka nufi wani daki a cikin jerin dakunan d ta gani wanda ba zata iya qirga su ba.
Suna shiga ta sake vaki dan tsabar tsaruwar wajen, komai jane a dakin, sai ratsin baqi kadan, labulaye ne kawai farare masu tsananin haske, da kwalliyar ja.
Irfaan jan ta yayi a jikin shi, ya qura ma lips din ta idanu, wani lumshe ido take kamar mai jin bacci, itan ma lips din shi ta fara kalla,a hankali suke kusantar da fuskokin su ga juna su, wata iriyar sumbata suke ma junan su mai matuqar gigitar da su, Salma tinda take a duniya bata taba jin irin wannan lamarin ba, Irfaan da yake da mata kala ji yayi a duniya kamar bai taba sanin ya ake kiss ba.
2
Sun jima a haka, sannan suka raba tsakanin su, suna cike da maida numfashi Salma tace, zan tafi, lokacin Sallah yayi, nan da nan fuskar Irfaan ta sauya daga mai haske da annuri, zuwa jajawur kamar kayan dakin wajen, idanun shi suka qara girma.
Shi baya son yawan Sallar ban da take, janta yayi a jikin shi, ya hau shafa ta, dadin da take ji tini ya mantar da ita Sallar d zatai.
Salwa ce ta farka jin kiran sallah na ratsa dakin su, lallai yau ta makara, dan kuwa har an shiga.
Jijjiga Salma ta hau yi, amma shiru, tayi dik me zatai dan ta tashi shiru, tabbas da ran ta amma wannan wanne irin bacci ne haka?
Addu'a ta fara ma Salma sosai, tana tofa mata, can cikin baccin Salma kuma cikin mafarkin ta taga Irfaan ya sake ta ya kwalla qara yana riqe vayan shi, don kuwa ya kwanta a saman salma, yana ta romancing din ta,gantsarewa yayi ya tashi daga jikin Salma, a sannan ne Salma ta tashi.
Gaba daya jin ta take wani iri, mafarkin da tai take son tinawa amma inaaa ta kasa tunawa.
Alwala ta shiga yi, wajen kama ruwa taji ta jiqe kamar wadda take cikin tsananin sha'awa, Irfaan ne ya fado mata arai,
'To kk hirar da mukai da shi ne jiya ya sa ni haka?'
Kama vaki tai ta zaro ido, me muka ce da zan ji wannan irin abu a jikina? Ya salam, in Ammi ta sani na mutu.....
Hummmmm, ya kuka ji wannan page? Ya yi maku dadi kuwa? I want to knw ur feedback, more comments more typing less comment a ga dan qundun......lalaci😂😂
KALAN DANGI...PAGE 12
1K 87 1
by Haermeebraerh
Following
A hankali Salma ta fara developing sha'awa mai qarfi akan Irfaan, har abun na bata mamaki, kuma gashi kullum ta kwanta ta tashi sai ta yi wanka, koda kuwa baccin rana ne, a waya ko a chatting bai taba yi mata maganar da ta danganci zina ba,
Kwance take tsakanin la'asar da magrib, tana danna wayar ta, hoton qawar ta da suka taba haduwa a wani group ta dora a DP din ta, Heedaya.
"Woww wace ce wannan?"
"Qawata ce why"
"Ohhh qawar ki ce? Na zaci sistern ki ce da nace ta fiki kyau"
Wani irin abu taji ya tokare mata qahon zuciya mai ciwo, da sauri ta je ta dauke hoton a DPn ta, ta sanya nata mai kyau sosai,
"The most beautiful gurl in all"
Hoton ido yayi sama dinnan ta tura masa, dik da taji dadi amma zuciyar ta bata daina mata suya ba na yabon Heedaya da yayi, tinda take ko hoton Salwa bata sawa a DP ko status, saboda bata son mutane masu iyayin qanwar ka ko yayar ka ta fika kyau su yaba.
Ta gwammace ta sanya hoton wadda suka hadu a social.media ko qawayen ta na makaranta 'yan gayu, hakan ke sawa a dinga ganin itan wata hadaddiyar yarinya ce.
Sun hadu da Heedaya a wani group saboda laben da suke aka ta masu masifa daga qarshe aka cire su, tin daga nan Heedaya ta mata magana privately suke gaisawa, daga nan suka zama qawaye.
Fushi take sosai akan yabon da Irfaan yayi wa Heedayaa, dan kuwa ta kashe ma wayar ta kar ya neme ta, tana daga kwancen bacci mai dadi ya fara diban ta, cikin baccin ta, ta hadu da Irfaan kamar yanda ta saba.
Hakuri ya ke ta bata tana kaucewa saboda kishin da take ji, romancing din ta ya fara sosai, da zafi2, tin tana qi har ta biye masa, sunyi nisa sosai ya zame jikin shi a nata,
"Ga Ammi nan zuwa,anjima zamu hadu a waya, bye i love u"
"Plss kar ka tafi,"
"I have to"
"Plsss"
Irfaan tini ya tafi daga mafarkin ta,sai magana take tana karya tafi,
"Iiiirrrfaaaann plsss"
"Ke, ke Salma, ke da waye kk magana haka?"
Maganar ta kamar ta mai maye,cike da shauqin so take maganar, miqewa tayi ganin Ammi, da sauri ta gyara zaman ta tana muzurai, tana kalle kalle.
Dafa kuncin ta Ammi tayi tana son su hada ido, Salma taqi yarda, kauda kai tayi, dan kuwa kunyar Ammin take ji,
"Salma ki dinga yawaita addu'a koda kwanciyar baccin rana ne ko na safe, ko na wane lokaci,ba dole sai da dare ake addu'ar bacci ba, shaidanun aljanun nan ba ruwan su da lokaci, ki kiyaye kan ki sai Allah ya kiyaye ki, tashi ga Salwa nan tafe ku kwashe kayan dakin nan, ku fidda katifa,Abban ku na hanya,suprise din ku na kusa da isowa,"
"Ammi me ne ne?"
"Inna fada bai zama suprise va kenan,maza ki tashi yace sun kusan zuwa."
A kasalance ta tashi, tana hade qafar ta taji ta a jiqe ta qasan ta, da sauri ta kalli Ammin ta, ji take yi kamar zata gane halin da take ciki, Salwa ce ta shiga dakin, ta fara kauda abubuwan da ya kamata, ita kuwa toilete ta shiga, ta wanke jikin ta, ta fito, suka fara dauke katifar,suka kai parlour, ba su jima da gamawa ba, Ammi ta fito sanye da Hijab, ta masu umarnin sanya hijabs din su, za a shigo, dakin ta ta kira su tace suje su taya ta gyara dakin ta,
Basu jima da shiga dakin Ammin ba maza sukai ta shiga da katakwayen gado, ana hadawa, gado ne babba mai tsananin kyau, wanda Abban su da kan shi yayi masu shi.
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Sai washe vaki yake, yana hango yanda zasuji dadi in suka ga sabon gadon nasu, an maida kafita an saka masu zanin gado, an maida komai da suka fitar, ba datti ne dama a dakin ba tinda suna gyara abin su.
Bayan samarin nan sun tafi Abba ya bude dakin Ammi yana murmushi, da sauri su salma suka je gare shi, suka rungume shi,
"Sannu da dawowa Abbanmu"
"Yauwa, sannun ku da aiki 'yan Abbansu, kuzo muje na nuna maku wani abu"
Dikkan su jikin su ya gama basu gado aka sake sanya masu,saboda qarar bige bigen da suke jiyowa, amma dai basu tabbatar ba, tinda basu gani ba, ba su taba zaton kyaun shi ya kai haka ba, koda suka isa dakin baki suka bude, saboda mamaki, da gudu suka kwasa zasu dale gadon Ammi ta bude murya ta kira su,
"Ba ku isa ku karya wannan bama, ashe ma baku horu ba ko kwana a katifa, da girman ku da komai ku dinga tsalle a gado, ba xan lamunci wannan shashancin ba, wanan gadon da hannun shi ya yi maku shi, so in kuna ganin zaku balle wahalar da ya sha bismillah"
"Ammin su ki bar su suyi murnar su na yau ne kadai, nima ba dan kin cikan ciki da abinci na zama qato ba dani za ai tsallen ai,"
Wani kallon na gaishe ka ta masa, ta kada kai ta bar masu dakin tana murmushi, shi ma bayan ta yabi kafin ya dawo ya yi magana qasa2,
"A yi murna a hankali, kuka balla gadon nan yanzu mai ceton ku sai Allah, ba ruwana"
"Mun gode Abban mu, Allah ya qara maka lfy da imani, da arziqi mai yawa mai albarka, zamu kiyaye, dama wancan ma Salma ce ta balla"
"Kaiii kaji baqar qarya yaushe na balla, ba ke kk balle shi ba kk ce kar na fada,"
Nan kowa ta dinga bama kowa laifi, har ya gaji da jin bayanin wanda ya balle gadon ya ja masu qofa ya rufe su yana dariya.
Kokawa ce ta kaure, sukai ta tumurmusa gadon, sai da suka gaji suka kwanta kan su na kallon sama, ya dan sauka daga kan gadon, hannayen su riqe dana juna,
"Salwa i am in love,"
Da sauri Salwa ta daga ta kwanta a gefen hannun ta na hagu tana kallon Salma cikin zumudin son jin da gaske ne abinda ta fada?
"Yeh i am so in love with Irfaan Maleek,"
"Waye haka? Amma gaskiya yayi sa'a tinda kyakkyawar sister na take son shi,sace zuciyar ta sai jarumi,"
Salma ma dagowa tayi daga yanda take kwance tana kallon Salwa, cikin murmushi da jin kanta ya fasu ta ke magana,
"Salwa na rasa gane wane ne Irfaan, saboda....."
Ringing wayar ta ta fara, hannu ta kai ta dauka, sunan Handsome ta gani, murmushin ta ne ya bayyana, tini ta manta maganar da suke da Salwa, Salwa kuwa ta dasa mata duka a baya ta sauka daga gadon ta fita parlour, bata ga su Abban ta ba ta san suna ciki yana wanka, abinci ta hada mashi a dinning, tana dakko zobon da suka hada mashi ita da Ammi ya fito, hannun shi riqe da na Ammin su,ganin Salwan ya sa suka janye, zama yayi, Salwan ta tsiyaya mashi zobon ta aje mashi, addu'a ya mata ta amsa cikin jin dadi, sannan ta kama hanyar komawa dakin su, hira ta tarar Salma nayi, nan da nan ta ji itama ina ma ace ta samu wanda zata bashi soyayyar dake danqare a zuciyar ta, tana dauke da so da qauna masu yawa, amma ba wanda ta mallaka wa, abinda ta sani kawai shine dik sanda tai tinanin so, ko masoyi, Yah Ubaidullah kawai take hangowa a idon ta, amma ta san ba zai aminta da soyayya da ita ba, ta san ya mata nisa sosai, shi da yake hulda da mata kala2 har daga qasashen waje, yanayin kasuwancin shi ba a iya Nija ya tsaya ba, qasashe kala2 fita yake, suna shigo da kayan abinci da na marmari, irin na qasashen waje, dan haka qauyukan da biranen turai da qasashen larabawa ba inda baya zagawa, tabbas ta san indai mata ne ko matar aure yake so ba zai bige da auren ta ba, wani irin abu mai zafi taji ya soki qirjin ta,bata san hawaye na zuba ba sai da Salma ta dafa ta cikin damuwa sannan ta share mata hawayen, da sauri itama ta fara sharewa da kan ta.
"Me ya same ki?"
" ba komai,"
Bandaki ta fada, kafin Salma ta mata wata tambayar,
"Ikon Allah,"
Kuka ta ke yi sosai, kuma ta rasa na meye,
'Kuka kk saboda kina tinanin wanda kk da crush akan shi ba zai zama mallakin ki ba'
Zuciyar ta ce ta bata wannan amsar, kallon kan ta tayi a dan madaidaicin madubin dake toilete din, idan ta yayi ja sosai, wanke fuskar ta tayi, ta tsaya, tana sake kallon kan ta, me ta rasa to? Yah Ubaidullah bai taba mata maganar da ta danganci soyayya ba, a qanwa ya dauke ta, qanwar da yake so sosai,
'Nima zan ci gaba da daukan ka a matsayin yayana da nake so sosai, Allah ya bani miji na gari da ya dace da ni, wannan dik shirme ne abinda nake ji game da kai Yah Ubaidu'
Ji tai ana kiran sallar magrib, alwala tayi ta fita, Salma dake bakin qofa tana jiran fitowar ta ce ta kama kafadun ta.
"Salwa akwai abinda zaki iya boyen dama? Me ye ya saki kuka haka nan ana zaune lafiya?"
"Shin mutum ba zai kuka ba in ya tina da farin ciki ko baqin ciki?"
"Zai yi in abun ya kai a masu kuka, so tell me, me ya saki kuka?"
"Lokacin sallah na wucewa, nima in muka idar ki van labari akan Irfaan Maleek"
Wani murmushi ne ya bayyanar da irin so da farin ciki da take dauke da shi akan Irfaan,
"K muyi sallah tukunna,"
Ko da suka idar Salwa qur'ani ta dauka, tafara karantawa byn tayi azkar n yamma, tin Salma najiran ta har ta fara jin kn ta na mata ciwo saboda karatun da Salwa ke yi,fita tayi adakin ta nufi can wajen gidan, a kusa da motoci biyu da ke gidan nasu akwai inda suka aje round table da kujeru na roba, zama tayi,ta hau hotuna, bayan ta gma ta saka a IG a sai ta rubuta 'Hijab suwag'
Mansur ne ya hango ta, hasken tsakar gidan ya haske ta, yana son ya mata magana tafito da magariba waje yana jin tsoro, kama bakin shi yayi d hannun shi daya,
"Kaga mansur, wajen surutu kake jawa kan ka masifa,"
Yana gama fadin haka ya shige dakin shi ya zauna yana leqa ta ta taga.
Sai d ta tabbatar Salwa ta gama karatun ta koma,
"Daga ina kk?"
"Ina can waje a kujera, kai na ke ciwo shine naje na dan sha iska,"
"Allah y sawaqa, kar ki qara fita waje da yamma haka"
"To Ammi, Ammi yunwa nake ji"
"Je ki kira Salwa tazo a ci abinci,"
Dakin ta koma ta ga Salwa kamar bat taba samun damuwa ba a duniya,
"Kizo mu ci abinci"
"Ohk"
Wayar Salma ce tayi ringing, Heedaya, ce ke kiran ta, dag wa tayi, dik taji ta rage son ta ma saboda kawai Irfaan ya yaba hoton ta.
"Hello Salma, ya kk?"
"Dadai, ke fa?"
"Me too, nakira ne na sanar dake, biki na jibi ne, i am so sorry na fada maki aqurarren lokaci, abubuwa ne suka min yawa,amma zaki samu zuwa ko?"
"Inshaa Allah, da ba gari daya muke ba d sai dai na biki da addu'a, tinda kusan kullum muna chat ba ki taba fadan an kusan auren ki ba sai yau"
"Kiyi hakuri na san ban kyauta ba, na amshi laifi na,"
"Ohk zamuyi magana an jim, inshaa Allahu zan zo,"
Suna cin abinci ta sanar da zuwan ta bikin, iyayen su basu da tsanani akan fitr su,amma ba su sake masu ba yanda zasu dinga yawo anyhow.
Salma na cike da farin cikin wannan ranar biki, saboda plan din da suka hada da Irfaan, na haduwa da zasuyi..........
KALAN DANGI...PAGE 13
1K 90 12
by Haermeebraerh
Following
Ammi tace indai Salma na son zuwa bikin ta na qawar media sai dai su je da Salwa, Salwa kuwa ranta ya gama baci wannan karon, Salma na son sawa a sanya ta yin abinda bata da niyya,
"A gaskiya Ammi ni ba zan je ba, yarinyar nan shegen shige2 ne da ita, ba fa ta san ta ba a social media ta san ta, amma in kk ga rawar kan da take akan ta sai kinji mamaki, ta gama da Jadwa yanzu ta koma Heedaya, banda wadan da ta yiyyi, ni kenan ina da abin yi fisabilillahi sai ace sai na raka ta bikin KALAN DANGi? Ammi yau target dina na haddace ayoyi goma inshaa Allahu, inna je biki taya zan haddace a wajen da ake cashewa,gaskiya Salma kina shiga haqqi na, ba fa zama na kenan in kinyo gamje gamjen qawayen ki na dinga maki rakiya ba"
Ammi shiru tai tana nazari maganganun diyar ta ta, Salma sun riga sun san tin usul halin ta daban dana kowa ma a dangin, to ya zasu yi, a qalla tana da tarbiyyar da ba kowacce yarinya ke samun irin ta wajen iyayen su ba, and she want to show them that ta yarda da su, bata son yaran ta su ji bata basu yarda ba, tana fatan hakan ya zama alkhairi, kar su kunyata ta.
"Ammi ni fa dama bana son 'yar rakiya, tai ta bina kamar wata jela, kawai in kin amince min zan tafi ni daya, kafin yamma na dawo,"
"Na amince maki, kije cikin amincin Allah ki dawo
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 17