abubuwan da take yi, addu'a ce kawai zata gyara ta.
Salma kuwa kayan su ta hau hada masu har da na Salwan, bayan ta kammala ta zauna a qasa, ta ja wayar ta, hotunan ta ta fara dorawa a IG, kamar qiftawar ido kuwa ruwan comments da hearts suka fara yawo, whatsapp DP din ta tasauya da na ango da amarya, status din ta ma haka ta cike shi da hotunan bikin, ba daya na Salwa ko Khairat da suka je bikin tare.
Status din mutane ta shiga gani itama, kamar yanda ta kula ana ta rububin ganin nata,da damar hotunan qawayen ta na net take reply, na dangi kuwa ga shi tana gani, wasu ba lfy, wasu anyi haihuwa, wasu rasuwa, haka zata gani ta tsallake, ba sannu balle Allah sawaqa.
1
Sai dare suna cin abinci, kowa ya nutsu, sai masu magana qasa2, Salma ke ta taba qafar Salwa, tana sanar mata ta fada masu gobe zasu tafi, banza tai da ita, sai da uncle Ibraheem ya kammala zai tashi sannan Salwa tai masa maganar, zama ya gyara yana kallon su.
"Is there any promblem i should knw about?
"No no pls, ba wani matsala, dama sati daya muka ce zamuyi, and gobe ne zai cika sati dayan, mun yi ma Ammi alqawarin zamu dawo nan da sati daya, musamman yanzu da take buqatat taimakon mu na aikin gida, she need some rest"
"To Allah ya muku albarka, Allah ya kaimu goben, kuma muna godiya akan ziyarar d kuka kawo mana, muma muna nan tafe inshaa Allahu,"
"Allahu ya sha'a, muma mun gode sosai da qauna da kuke nuna mana"
"Na zaci zaku dan jima, tinda Abban ku ya qi yadda ku ci gaba da koda HND din ne, amma ba komai, Allah ya tabbatar d alkhairi, haka ma mun gode, khairat zata yi kewar ku, amma yaran nan sai sunfi kewar ki Salwa,"
Kallon su tayi taga yanda jikin su ya sake, sunqi ci gaba da cin abinci, kiss ta musu da bakin ta, sannan tace,
"Kids kar ku damu, dana koma na aje wannan qatuwar zan dawo muyi ta wasan mu,kunji?"
Murna sukai tayi, Salma ta harare ta, haka aka tashi cin abincin masu murnar Salwa zata dawo nayi, wanda suka gane wayo ta masu ran su sam bai masu dadi ba.
Cikin dare Salwa taji dariyar Salma qasa2, a tsorace ta tashi? Ta kunna fitila, ganin Salma tayi nade cikin bargo tana mutsu2.
Budewa tayi, ta gan ta tana dariya, juyawa tayi dan ganin wa ya bude ta, ganin Salwa ne ya sa ta hau mata nuni d hannu akan ya sake mata abun rufan ta, da taga taqi ta fizge ta koma ta rufu, ta ci gaba da hirar ta,
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
All there life Salwa bata taba ganin daya daga cikin su na waya bayan 10 na dare ba balle har a kai sha biyu da wani abu, sake duban gogo tayi taga 12:13Am, pillo ta dauka ta dora saman kujerar dake dakin ta dau abun rufa ta kwanta, dariya da motsin Salma ba zai bar ta tai bacci ba.
Hira suke sosai ta Whatsapp call, ita da Handsome, muryar shi ta ji dadin ta fiye da yanda ta zaci zata samu muryar tashi, ta bangaren shi ma haka, ya yaba sosai da zazzaqar muryar ta, yau suka fara waya.
Basu gama waya ba saida Salma ta fara jin bacci, in yayi magana yaji shiru, daga qarshe ya kashe wayar.
Da asuba ta tashi, sai da Salwa tayi mamaki, ba wanda ya tashe ta, ko kallon mamakin da Salwa ke mata bata kalla ba, ta shirya,ta yi sallah, ta zauna ta ja wayar ta, ta kira Ammin su, tin zuwan su yau ne ta kiran da ta mata na uku.
Bayan sun gaisa take fada mata yau zasu dawo, addu'a da fatan alkhairi ta musu, sannan ta miqawa Salwa wayar, itan ma gaishe ta tayi, sannan ta gaida Abban su.
Qarfe takwas nayi Ubaidullah na tsaye yana jiran fitowar Salwa, wadda yara ke ma Allah ya kiyaye, Salma sai tsaki take dokawa, Ubaidullah y yi iya qoqarin shi wajen danne tsakin da Salma ke jera, amma ya gaza.
"Kin san bakin ki ya sake tsaki sai na fasa shi kafin ku isa Gombe ya kumbure?"
"Bismillah,"
Shine abinda ta furta a hankali,
"Sake ki gani"
Ya juya ranshi a mugun bace, tare da daga hannun shi, yana jiran tace fit ta ji fat.
Hango Daddyn su yayi, yayi saurin sauke hannun shi, murmushin mugunta tayi, sannan ta sake wani mugun tsaki ta juya ta shige cikin mota, Ubaidullah idan shi yayi jawur dan tsabar takaici, budewa ya yi a hasale, ya ce,
"Kin san Allah? Ba zaki tafi a motar nan ba, akwai driver zai kai ki tasha, na rantse maki baki isa ki min rashin kunya sannan na ja ki ba, fito ko na targada ki,"
"What is going on here?"
"Daddy yarinyar nan yanda ka san ba 'yar uwar Salwa ba, gaba daya halin Salwa da ka sani mai kyau, Salma sabanin shi gare ta,daga na mata magana tana ta tsaki,kar ta sake, sai da taga ka fito ta min tsaki ta shigen mota, nayi rantsuwa ba zata bi mota ta ba, sai dai driver ya kai ta, in kuma ta bini sai na tsaya a hanya na fidda ta na mata dukan tsiya, yarinya qarama da ita amma jin kan ta take kamar wata uwar mata,"
"Calm dwn Ubaidullah, tinda ka rantse Salma zo nan, Khairat ki kai su tasha, in ka na so ka bi su a taka motar,"
Daga masu hannu iyalin gidan suke tayi, Mummy na maimaita godiya wajen Ammi, da ta kai mata gyada, tsaraba kuwa ba laifi sun sha ta, Uncle din su ya ba su kudi, Salwa da kyar ta amsa, saboda tana ganin ba sai ya basu komai ba.
Ubaidullah sai da ya raka su har tasha, kafin mota ta cika, sun sha hira da Salwa mutuniyar shi, Salma kuwa ko kallo bai ishe ta ba, Khairat ta so su dan yi hira amma ta share ta, Jadwa ke online,tana sanar da ita yau zasu wuce Dubai, ita da mijin ta, sai murna take taya ta, tana fada mata ta turo mata hotunan honeymoon din nasu.
Wayar ta ce ta fara ringing, ta duba taga Handsome a saman screen din, murmushi tayi ta amsa.
"Hey handsome,"
"Hi beauty, ya kk?"
"Lou, and u?"
"I am gud, kina ina ne naji hayaniya haka?"
"Ina tasha zamu komo gida yau,"
"Tasha kuma? A motar haya zaku tafi?"
Dan murmushi tayi, haka nan taji bata son ta masa qarya, tsabar yanda take ji game da shi.
"Eh ta motar haya muka zo, kuma ta nan zamu koma, kar ka damu bamu saba tafiya hakan ba,"
"K Allah ya kawo min ke gida lfy Allah ya kiyaye hanya,"
"Ameen"
Limshe idon ta tayi, anya zata iya jimawa bata fada masa me take ji game da shi ba kuwa?
A gaskiya abinda take ji mai girma ne, kuma mai nauyi je a qirji, dan kuwa ji take in bata masa magana ba na rana daya ba zata iya numfashi ba.
Wata zazzafar qauna da soyayyar shi ce a zuciyar ta,
'Dole na sanar da shi me nake ji a rai na a yau dinnan, ba zan jurewa ba,'
Mutane sun cika Sukai ma juna sallama.
Ubaidullah ya mata sallama ko ba komai gaba yake da ita, ba zai biye mata ba.
Murmushi ta kalato ta masa tare da daga masa hannu, yana juyawa ta saki siririn tsaki tare da murguda baki, salwa ce ta kada kai tare da motsi da bakin ta, ban ji me ta ce va dai.
Kamar yanda duka zo, haka suka koma, su biyu a baya.
Tafiya tayi nisa sun shiga daji sosai, motar su ta taka wani mugun birki, drivern ne y so gewaye mutumin da ke kwance a saman titin, dan tsoron kar ko 'yan fashi ne suka hada masu gadar zare, nan da nan salma ta fara masifa.
"Irin wadannan 'yan iskan mutanen, kyau ana bi ta jan su,tinda mutuwa suke nema, in ba iskanci ba taya za ai mutum ya zauna a tsakiyar wannan babban titin haka?"
1
"Wai ke me yasa baki iyawa bakin ki? Ki fadi alkhairi ko kiyi shiru, yanzu kk san me ya sa mutum dattijo kamar wannan kwantawa a nan?.da hankalin shi d lafiyar shi kina tinanin zai kwanta a saman titi ne,mtsss"
Dikkan nin su zuqatan su a dadi suke kallon yanda mai motar ya daga dattijon, ya maida shi tsallaken titin, ya miqa masa sandar shi, zama yayi a bakin wani dutse dake kusa da wajen yana maida numfashi, Salwa ta so fita Salma ta tina mata sanda ta taimaka ma wani ya amshe kudin hannun ta ya bace, tsoro ne ya kama ta ta koma ta zauna.
Kafe su da ido dattijon yayi lokacin da drivern ya tsallaka ya koma motar, kamar a na masu rada sike jin magana, kuma suna kallon bakin dattijon na motsawa.
"Salwa Allah ya maki albarka, Salma kibi duniya a sannu,"
Basu sake ganin kowa a wajen ba, har motar su ta juya, ta fara tafiya suna waigen wajen, kallon juna sukai, nan suka kada kai a tare, da sauri suka rungume juna, Salwa ta fara karanto addu'a a bakin ta, saboda tabbas ba qarya aljani suka gani, amma na cikin motar a hirar da suke suna nuna har yanzu su suna ganin dattijon,
Har suka isa Gombe basu dawo nutsuwar su ba.
Salwa ta sanar da Ammin su dik abinda ya faru, nan ta sa su sikai wanka sukai alwala, sukai sallah, sannan ta miqa masu qur'anai dan suyi hakaratu, kuma ta kunna masu ayoyin ruqya a waya, nan da nan Salma ta fara wata iriyar jijjiga...................
Toooooooo
Hankalin kowa ya tashi, musamman yanda suka ga idon ta na qafewa, daukan ta Ammi da Salwa sukai, zuwa motar da ke a je a gidan su, saboda irin wannan emergency, Ammi ke jan motar sai asibiti, tinda suka fara tafiya nimfashin ta ya fara koma wa daidai, a hankali ta daina girgizar da take, idanun ta ta bude, taga yanda Salwa ke rizgar kuka, tana qanqame da ita,
"Ammi ina zamu je?"
Da sauri Salwa ta daga fuskar ta, tagan ta fess, maida ta tai jikin ta, tana ma kan ta kiss, cikin murna take magana,
"Ammi kin gan ta taji sauqi, kamar ba ta taba ciwo ba,"
"Alhamdu lilLAAH zamu je asibiti still,bamu san wanne irin ciwo ke damun ta ba,"
"Ammi lfy t qlou, ni ban ma san yaushe na shiga mota ba, shin ba karatu muke ba da?"
Shiru sukai, dan ba wata amsa da zasu iya bata, tafiyar minti ashirin ce ta kai su babban asibitin, nan da nan suka kammala abubuwan da ya dace dan ganin likita, sai da suka jira aka zo kan su sannan suka shiga gabaki dayan su.
Bayanin komai Ammi ta bama likitan, shi kuma ya tambayi Salma akan me da me take ji, shiru ta masa dan sai taji wani irin takaicin shi da ya mata magana,hararar shi tayi t kauda kai,
"Baki ji ana tambayar ki? Meke damun ki? Wani waje na maki ciwo?"
"Tin a hanya nace maku ba na jin komai, ban san dalilin da yasa kuka kawo ni wajen wannan mayen matan ba"
Subhanallahi, da sauri Ammi ta kame bakin ta tana zaro ido, ta kalli Salma sannan ta kalli likita, likita kamar ruwa ya ci shi, tabbas yana da son mata, amma ai bai nuna mata ba,ya akai ta sani, da sauri Ammi ta duqa tana ba likitan hakuri, Salwa da Salma ne suka daga ta tsaye, shi kuwa kamar ruwa ya cinye shi, daga baya Salma ta fice ta tafi mota tai zaman ta, tare da rufe idanun ta.
Ammi jiki ba kwari ta tattara qarfin da ya rage mata suka fita, tinda mara lfyr ma ta bar wajen balle su?
A mota suka same ta tana ta muzurai.
Idanun ta gaba daya sun sauya kala daga asalin kalar brown zuwa kalar idon mage, fuskar ta tayi jawur, kamar wadda aka barbadawa barkono.
Ammi kallon ta tayi sai taji gaban ta ya fadi.
Tada motar tayi suka dau hanyar gidan, ko da suka shiga gidan Salma ta toge a bakin gate, tace bazata shiga gidan ba, sai an je an kashe karatun da aka kunna,
"Iko da daukaka na ga Allah mahalicci, yau kuma karatun ne baki so Salma? Salma n me ya same ki, ya Allah ka sauqaqa min ko me zai same mu, da wanda yake tare damu,"
Kuka sosai Ammi ta fashe da shi, mai gadin su ya ruga da gudu ya durqusa.
"Hajiya lfy?"
"Dalla tashi ka ba mutane waje, gulmamme kawai, ko wani ya kira ka?"
Tabbas dama ya san ta ba kunya ta cika ba, amma ba ta taba masa haka ba,anya lfy take kuwa? Suna hada ido ya sauke kan shi qasa,
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, hajiya, Salma bata da lfy, a gaggauta nema mata magani kafin abu ya kai da gagara,"
"Me kk fada ne Malam Mansur?me ya same ta?"
"Hajiya kin dai san mu mutanen karkara ba mu cika zama haka ba, musamman mu da muke gadi, hajiya tabbas Salma na dauke da baqaqen aljanu, ya kamata a nema mata magani, kuma a...."
Wani hadadden mari ne ya kifar da shi, sannan Salma ta bi shi ta taushe, ta dinga naushi a fuska, sai ihu yake yana bata hakuri, amma inaa, sai da bakin shi da hancin shi suka hau jini,
"A'udhubi kalimatillahi taammat min sharri ma khalaq×3"
Ammi na yi Salwa na yi, nan ta silale ta kwanta, da kyar suka daga ta suka mayar daki, jikin ta yayi nauyi sosai, Malam Mansur da kyar ya tashi jiki ya masa mugun tsami ya shige dakin shi dan jinyar jikin shi.
1
Kwantar da ita sukai, karatun ya kar qarshe ya mutu da kan shi, wayar Salman ke ta haske tana ringing, dubawa Salwa tayi taga an rubuta Handsome, kamar ta daga sai kuma ta sa a silent ta kifa ta aje.
Zama tayi kusa da kan Salma ta dafa saman kan ta, tana ta mata addu'a, yau in ta tabbata aljanu gari Salma ya zasu yi?
'Ya Allah ka shiga lamarin mu kar ka barmu da kan mu, ba zamu iya ba'
Kuka mai cin rai ta sake, dik zuri'ar su bata taba jin mai aljanu ba, anya Malam Mansur bai fadi gaskiya ba.
To a ina tai gamo da aljanu? Tabbas akwai wani abu, ko wannan dalilin ne ya sa sanda zasu tafi ta dinga jin faduwar gaba, kuka ta sake saki, Salwa ce ta kwanta a bayan ta tana shafa hannun ta, tare da bata baki.
Da kyar ta samu ta daina kuka, Salma kuwa bacci kawai take sha, Salwa ta tofe ta da addu'o'in bacci.
Kula da lokacin dawowar Abban su yayi ne ya sanya Ammi tashi, ta dauki abincin da ta gama dafawa tin kafin su dawo,ta fara jerawa saman dinning, tana aje plates da spoons, hawaye na zuba mata, sai da ta gama ta tafi bayi dan yo wanka, tana wanka tana kuka, aljanu a zuri'ar ta? Kaiii wannan jarabawa mai tsauri ce, Allah ya bata ikon cinyewa.
Dan kuwa taji rauni sosai ya shige ta.
Kwalliya ta sha abun ta kamar ba abinda ya faru, tasbihi kawai take a ran ta, hakan ne ya sa ta samu sauqin radadin da take ji a zuciyar ta.
Bata jima da shiga dakin su Salman ba suka ji motar Abban ta dawo, Salwa ce ta qarasa shafa kwalli ta aje, ta fita dan tarbar shi kamar yanda suka saba, sai da ya rungume matar shi ta masa kiss a kuncin shi sannan ya rungume Salwa, itama ta mashi kiss a kuncin shi, sai murnar ganin juna suke,
"Ina gimbiya Salma, ko sarautar ta motsa ne?"
"Muna dawowa ta hau bacci, muje ciki, Abba muci abinci, yunawa nake ji, nace ba zan ci ba sai ka dawo,"
"Ohhh my baby, muje ciki to,madam ya akai naga dik kin wani sake? I am sorry ban dawo da wuri ba, aiki yayi yawa, wannan aikinnn, kin tuna shi? Shine ya tsai da ni, na so kafin su dawo an kammala,"
"Oh oh oh na tuna, kar ka damu kan ka,muje ciki ka huta,"
Abinci suka zauna suka ci, yaso a tashi Salma itama aci gaba daya, sunyi iya qoqarin su na danne damuwar da suke ciki, sai da ya riga su gamawa ya tafi wanka Ammi ta sa kuka, har ya gama wanka bata je ba, yayi ta mamaki, kayan da ya ga ta fidda masa ya dauka ya sanya.
Ya koma, zaune take a parlour tana kuka, da wani irin sauri ya je gaban ta ya duqa, Salwa na ganin haka ta fita ta basu waje, fadawa jikin shi tayi, tana kuka tana sanar da shi me ya faru, cikin tsananin damuwa ya fara qoqarin kwantar da hankalin shi dan kar ta sake shiga damuwa, dan kar ya karya mata dik qoqarin da tai na kwantar masa da hankali.
"Taso muje mu gan ta, ki hakuri ki daina kuka, waman yatawakkal alallah fa huwa hasbuh, inshaa Allah Allah zai duba mana kinji? Allah ya miki albarka, ya yaye maki dikkan baqin cikin duniya da lahira,kamar yanda kk qoqarin kare dikkan wani abun da zai bata raina"
"Ameen, "
jiki ba kwari dikan su suka shiga dakin, kwance take yanda suka barta, sunyi sunyi su tada ta taqi tashi, waje ya fita, ya yi waya wani limamin masallacin da yake zuwa sallah a unguwar,
Sanar da shi komai dake faruwa yayi, yace bari zan kawo maku wani mai ruqya, malam Hussaini, in yazo zai ga ko akwai ko babu...........
Allah to ya sa kar ka daku Usai.
Mallam Hussain ya zo, ya taho da magungunan da ake sanyawa masu fama da matsala ta jinnu, inda ya hade su waje daya, ya yi masu addu'a, ya bama Ammi ta shafa mata a qafar ta, da kuma hancin ta sai hannayen ta, har aka gama shafawa a qafar ta da hannayen ta bata farka ba, ana sawa a hanci ta bude idan ta da suka koma jajawur, da dikkan alama ko ma wake tare da ita yaji zafin maganin da kuma ayoyin qur'anin da ake ta karantowa, Salwa ta sabunta alwala da umarnin malam,Ammi na da alwala ita da Abba.
Nan ya umarci matan da su fita, shi da Abba suka zauna ya dinga mata ruqya, amma taqi magana, sai qunjin kuka da take yi, sallah kawai ke tada su su koma, har qarfe takwas na dare, Salma na nan ana abu daya ba ci gaba.
Ammi tayi kuka har ta daina fidda hawaye, dan idan Salma ta kwada wani ihun da kiran wayyo Allah sai Salwa ta riqo Ammi, dan kuwa zabura take ta miqe tace zata shiga dakin nasu.
Hakura Malam HUssain yayi, yace zai tafi dan gaba daya shi ma a jigace yake, har Abban ma sun gaji.
"Alhaji kaman yanda ka gani ko wanne aljani ke tare da ita yana da taurin kai, amma muma ba zamu gaza ba, zamuyi ta taimaka wa har qarshen rayuwar mu, Allah ya bata lfy."
"Ameen ya Allah, Malam na gode sosai"
Kudi Abba ya bashi ya qi amsa, da kyar da sidin goshi ya amsa.
Suna godiya ma juna suka rabu, Abba ne ya ga Mansur mai gadi ba riga jikin shi dik ya ji ciwo kamar wanda yayi fada da zakanya, fuskar nan ta sauya gaba daya saboda ta haye, cikin tausayawa ya isa gaban shi,
"Malam Mansur ya jikin?"
"Hummm gani nan dai, jiki banda tsami ba abinda ya qara, kan nan nawa da kat nake juya shi Alhaji, ina me tabbatar maka Salma in ba hada ta akai da malamai irin nami ba zai wahala ta warke, saboda baqin aljani ne kawai zai iya fidda baqin aljani"
"Kaga Mansur, na gode maka sosai da ka gano aljanu gare ta, amma hakan ba zai sa na dau qafa naje inda za ai shirka ba,Allah daya san halin da muke ciki ya tsare mana imanin mu wajen neman lfy kar mu kauce hanya ko da akan rashin sani ne, domin ba abinda yafi shirka zunubi a wajen Allah"
(Tabdi jam, wata ma ba ciwo ba komai zuwa take ai mata duba da bugun qasa,balle masu kishiya da sai su bayar da komai suka mallaka dan su mallake mijin su kadai dan baqar mugunta su bar dayar ana mata azaba suna jin dadin faruwar hakan, kamar sun manta aure raine da shi, walau asiri ya kare a sake su suje inda aka ninka su a asiri ko a ka mallake mijin da kyautatawa su su koma a wulaqance, ko mijin ya mutu ma ta rasa mashinshini gaba daya)
1
Ranar dai sai bacci barawo amma haka suka kwana kowa ido biyu, baccin ya gagare su dan haka sukai alwala Abba ya jasu sallah, bayan sunyi raka'a wajen shidda bibbiyu,(ba qa'ida bane dole sai shidan, haka suka ga dai zasuyi, ko raka'a biyu kikai/kayi, dn neman biyan buqata sun isar, abinda ake nema shine ikhlasi)
Addu'a Abba ya dade yana kwararawa suna amsawa da Ameen, sannan Salwa ta masu sallama ta shiga dakin su, xaune taga Salma ta dafe kanta dake mugun sara mata, idanun ta na tsiyayar da hawaye, da sauri ta isa gare ta ta rungume ta, wani kuka ne itama ya tokare mamata maqoshin ta, kallon juna sukai,
"Salwa me ya same ni? Dik jikina ciwo yake, musamman nan qasan hammata ta da kaina, kamar wadda aka matseee,"
Cikin kuka Salwa tace mata,
"Salma ki riqe Allah, ki riqe ibada komai ya same ki Allah zai yaye inshaa Allahu, now get up and pray, ki jero azahar la'asar, magrib, isha'i, ko a zaune ne, kar ki damu, yanda zaki iya dai,"
Qoqarin tashi tayi, taji jiri na diban ta, kama ta Salwa tayi, ta zaunar da kyau, tace tana zuwa.
Kitchen taje ta hado tea mai kyau ta kawo wa Salma,
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 17