din,"
Nan sukai ta hirarraki akan yanda zasu samar da ci gaba a zuri'ar su, kafin daga baya kowa ya tafi su bar Daddyn shi kadai.
Da misalin qarfe sha biyu na rana suka tashi zuwa Abuja.
Ubaidullah ya so zuwa dauko su amma yanayin aikin shi ya hana, ana da buqatar shi a wajen aikin, Huzaifah shine wanda ya dakko su, ya kaisu gida,
"Ya kamata ka fara zuwa aiki Huzaifah, zaman banzan ya isa haka, daga wannan film ya qare a sauya tasha, hira cikin mata kuwa har ka fara tafa hannu baka sani ba"
Dariya sosai suke ma Huzaifah Ammi tace,
"Gaskiya kam Yayah ya kamata ya fara xuwa aiki, kar tsabar zama da mata yayi aure a rasa wace matar waye mijin"
Huzaifah yaji kunyar maganar ta a ran shi yace,
'Ga shi kuwa Salma dama abubuwan ta sun fi kama da na maza ba'
Koda suka isa gida, yara na islamiyya, sai murna manyan suke, Salwa kuwa harda kukan farin cikin ganin iyayen nasu kamar wata qaramar yarinya, ko ina Ammi ta sanya qafa itama nan take aje ta ta.
Mummy ta sakko sun gaisa tana ta bude hanci, sai dai fuskar ta dauke da murmushi, wanda da ka gani kasan bai kai zuci ba,
Wani abun da Daddy bai son tana yi, dik da ya hana amma taqi hanuwa, zama ba mayafi a gaban qannen shi, Ammi bata taba zama ba hijab ko mayafi gaban shi, amma ita ko wanne irin dinki ne jikin ta ba ruwan ta, zata zauna gaban qannen shi haka.
Abinci suka ci sannan Daddy yace in Ubaidullah ya dawo za a samu yin taro.
Ammi da 'yan matan ta har da khairat ma da Sumayyah sun haye sama dakin da Salma ke kwana, nan sukai ta hira da bata labarin Abuja, kallon Salma kawai take, cikin jin dadin ganin yanda Salman ke surutu yanzu, wato ba yan samun lafiya da tayi har da hira ta koya, hamdala ta yi tayi a ran ta, ga shi tai qiba ta murmure kamar ba ita ce suka kawo ta qashi da rai ba.
Shafa fuskar Salman tayi cikin kulawa tace,
"Salma ya jikin ki?"
Khairat na ganin haka ta taba Sumayyah da qafar ta, suka miqe, zasu fita, Ammi ta basu umarnin su koma su zauna, su din 'ya'yan ta ne halak malak, dik abinda zata fada gaban su salma zata fada gaban su, ba wani wariya,
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
"Ammi jiki da sauqi sosai, magunguna na ma sin qare,kuma kinga na ji sauqi"
"Masha Allah, Allah ya qara maki lfy, ya kare ki daga sharrin shaidanun aljanu,da dikkan nin ku ma"
"Ameen suka amsa gaba dayan su"
Labarin Gombe ta basu itama, da shirmen Mansur dan salwa na shan dariyar shirirtar shi sosai, kwankwasa qofar akai, Huxaifah ne ya fara leqa kai,a hankali Salma tace,
"Na mata na mata ya zo"
Ubaidullah shima ya shiga, durqusawa yayi ya gaida Ammi, juyawa tayi gaba daya tana amsawa, Ubaidullah wai kunyar ta yake ji, sai wani sosa qeya yake, yana sunkuyar da ido qasa, dariya dakin ya dauka da shi, inda Salwa itama take kauda kai, cikin jin kunya.
Ammi ta kula da hakan, nan da nan tinanin hukuncin da aka yanke ya shige ta, anya ba matsala a wannan hadin da akai kuwa?
"Salwa xo ki kawon abinci na"
"Yah Ubaidu bari ni na kawo maka"
Wata harara ya makawa Salma dake tsokanar shi, dan ta kula kamar da biyu yake cewa Salwa ta kai masa abinci dan suyi zance ne su kadai.
Dariya suka sanya ita da su Khairat suka tafa.
Bayan fitar shi Salwa na son ta je ta kai masa abincin tana jin kunya, Ammi na kallon ta, so take ta tabbatar da zargin ga shi yasa taqi tai magana,
"Ki je ki kaiwa Haerbeebeen naki abinci manaaa Salwa"
Duka ta kai ma cinyar Khairat amma ta goce, tana dariya,
"Tabb dana bari wannan hannun naki mai zafi ya sauka a cinya ta sai na yi ruwan qanqara dan sanyaya wajen,"
"Wai me ke faruwa ne? SALWA bakiji yayan ku ya ce ki kai masa abinci ba, ko dama haka kike in an saki aiki kiqi zuwa?"
Da sauri ta kalli Ammin tana kada kai alamar ah ah.
"To ta shi mana kije yana jiran ki,"
Sumi sumi ta tashi ta fita, dariya su salma suke mata, Huzaifah ne yace,
"Ammi baki san me ke faruwa ba shi yasa,"
"Zan so sanin me ke faruwa kuwa yaron Ammi"
Dariya nan ma su Khairat suka kwashe da shi, dan yanda Ammin tai magana kamar shi din dan jariri ne,
"Wato Ammi Salwa da Ubaidullah akwai wani babban al'amari a tsakanin su, ina nufin suna son junan su da aure"
Dimm Ammi taji a qirjin ta,
'in ko haka ne an yi kuskure babba, ya kamata na sanar da magabata dan a gyara maganar hadin auren nasu'
"Tooh ikon Allah, ita kuma Salmaaa wa yake son ta a gidan?"
Cike da murmushi ta fadi hakan, Huzaifah na jin haka in inar da bai san yana da ita ba ta kama shi, haka kwai ya amsa kiran da ba ai ba a waje ya miqe zai fita,
"Dawo ka zauna ba mai kiran ka, yanda ka fadi na Ubaidullah kaima sai ka fadan naka, kasan ni kamar qawa nake a wajen ku, komai kuna iya sanar dani"
Sosa kai ya fara yana qiqqifta idanu, Salma ya kalla wadda take ta daure fuska, sauke kan shi qasa yayi a hankali ya furta.
"Salma nake so Ammi"
Yana gama fada ya fita daga dakin, Salma kuwa wani irin gurnani ta sake kamar wata dabbar dawa, nan da nan idanun ta suka sauya kala zuwa jajawur, fuskar ta tayi ja alamar bacin rai mai yawa,
Khairat kafin kowa ya farga ta bar dakin, Sumayya ce ta tafi kiran Salwa, Ammi taba Salman tayi tana son jin ko lafy? Ture hannun ta tayi, sannan ta miqe tsaye, ta nuna Ammi da yatsa, cikin kakkausar murya take magana,
"In kk bari aka daura aure tsakanin mata ta Salma da wani namijin bil'adaman zaki rasa 'yar ki, kin san inna dauke ta kuwa wannan karon ba zan dawo maku da ita ba, saboda Salma mata ta ce, ina son ta, ba zan yarda ku hada ta da wani bil adama ba, in aka daura auren su zaku shiga cikin masifa da bala'i"
Daidai nan Ammi ta kai qarshen ayatul kursiyyu, ta hada da a'uzubi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq, ta tofa ma Salma a fuskar ta, wata iriyar qara Salma ta sake ta fara shafa fuskar ta, ai kafin Ammi ta kamo ta har ta kai qasa, kan ta ya bugu da jikin gado, nan da nan ta suma,dakin ya cika da mutane, Huzaifa ne ya isa gaban Salma ya daga ta ya dora saman gado, inda ta buge har ya tashi, fuskar ta ta bashi tsoro sosai, wasu irin quraje ne suka feso, kamar borin wuta ta qona mutum, nan aka yayyafa mata ruwa, addu'a suka ci gaba da yi mata, ana tofa mata, Salwa kuwa ruwa ta samu tana tofa ayoyin ruqya iya wanda ta sani, sai da ta gama ta miqawa Ammi aka shafawa salman a jiki, aka bata ta sha da kyar, nan da nan fuskar ta da yanayin ta ya dawo normal,sai numfashi take saukewa alamar bacci ya dauke ta, fita sukai gaba dayan su, tare da kunna mata ruqya a waya.
Zaune suka tadda Mummy qafa daya kan daya, Khairat na zaune kusa da ita daff, tana ta cin farcen hannun ta,tsabar tsoro idanun ta sin sauya dik sun fito waje, tashi tayi d sauri taje gaban Salwa ta na tambayar ta ya Salma,
"Taji sauqi yanzu, dan ta samu bacci ma"
"Allah ya qara lfy"
Mummy ce ta miqe tsaye, ta kalli Mutanen wajen, wanda ya hada harda Abba da Daddy, ana jajanta ciwon na Salm, saboda da suna murna taji sauqi ashe ana nan.
"To Ibraheem, ka dai ga wadda kk son dan ka ya aura ko? Yarinyar da da ita da mahaukaciya ba su da maraba.....
"Keeee dakata, kar ki kuskura ki sake danganta min yarinya da rashin hankali, Allah ya nesanta ta da rashin hankali da dikkan ahalin mu ma baki daya, wanne irin qi kk min ne ni da yarana? Ciwon jinnu in Allah ya qaddara bawa zai yi shi wa ya isa ya tsallake? Kar ki sake zagin yara na akan son zuciyar ki, yaran nan suna son junan su meye naki a ciki, ko ke zaki zauna masu da matan? Ban taba fada ki fada ba saboda ke gaba kk dani, amma ba zan zauna ki na fadin magana akan yara na ba,"
Fuuuu Ammi ta haye sama, shiruu wajen ya dauka ba mai magana har Mummyn da ta miqe dan yanka rashin mutunci, yaran ma daya bayan daya suka bar wajen, daga Jalaluddeen sai Uncle Ibraheem,
"Yanzu baki ji kunya ba? Nace yanzu bakiji kunya ba? Matar da ke girmamaki kamar ke din kin haife ta ne yau ta daka maki tsawa saboda shashancin da kk yi, ke da Salma waye yanzu baida hankali munji ita lalura ke damun ta ta aljanu ke me ke damun ki?ina baki shawara da ki sauya hali tin kafin lokaci ya qure kiji kunya,"
Bar mata wajen sukai shi da qanin nashi, jikin ta yayi sanyi sosai saboda yanda abun ya juye mata.
Salma ta farka tsakiyar dare tana neman ruwan da zata sha, Ammi wadda idan ta yake biyu tana kan sallaya ta miqe taje gaban ta ta na tambayar ta me take so,
"Ruwa zan sha Ammi"
"To"
Ruwan ta fita ta debar mata, ta kawo mata, bata bata ba sai da tayi addu'a a ciki, ta shanye,
"Ko na kawo maki abinci?"
"Ah ah, sallah zan yi banyi magrib ba da isha'i"
Taimaka mata Ammi tayi ta shiga bayi, dauke da addu'a a bakin ta, sai da ta wanke bakin ta sannan tayi alwala ta fito, sallah ta gabatar ta kwanta wajen ta ci gaba da bacci.
Sai da Ammi ta idar da addu'ar da take ta tada ta suka haye gado.
Salwa taso kwana da su Ammi tace taje can inda ta saba kwana ta kwanta,
Da safe a wajen karyawa Huzaifah sai neman idanun Salma yake ya kalla ko zai ji dadi, amma ko da wasa bata daga idanun ta ba, gaba daya ya damu, ko baccin kirki bai ba,lura da hakan ne ya sa Ammi ta sake tabbatar da wake son wani a tsakanin yaran hudu.
A qaramin parlour suka taru bayan kammala karyawa, Daddy ya sake jaddada hadin da akai na auren su Ubaidullah, nan Ammi ta bayyana ma su abinda ta lura da shi, tambayar su Daddy yayi suka tabbatar masa da cewar haka ne yanda Ammin tace, dan haka ba bata lokaci Daddy yace kawai a sanya ranar auren, in yaso ko ta waya ne a sanar da sauran 'yan uwa indai yin auren nan kusa shine zai cire Salma daga cikin lalurar ta.
Nan Daddy ya sanya ranar auren su wata biyu masu zuwa.........
Irfaan kuwa zai yarda wannan aure ya dauru?
1
Mummy fa?
KALAN DANGI....PAGE 25
936 86 2
by Haermeebraerh
Following
Tin daga ranar da Daddy ya sanya ranar auren su, iyayen maza da mata suka fara shirye2n auren, sai dai a bangaren Mummy kuwa shirye2n yanda za a fasa auren take, ta kira yaran nata ta gargade su akan auren su Salma, amma sun nuna mata in ba su suka aura ba ba za su yi aure ba har abada, dik ta inda ta bullo sai ta samu hanyar a toshe take.
Irfaan kuwa yana fada wajen Maleek suna tattaunawa akan sha'anin mulki ya samu labari daga 'yan leqen asirin shi, ya taho, ranar mutan gidannan sun ga tashin hankalin da basu taba gani ba, dan kuwa Salma fashe2n abubuwa ta dinga yi tana bi ta kan su tana takawa, ba qaramar wahala Irfaan ya bata ba, Khairat tin tana jin tsoron Salma sai da ya kai ta rungume ta tana kuka tsabar tausaya mata,Ammi kuwa da suke shirin komawa fasawa sukayi, Salma bata ci bata sha ga tsananin ciwon kai da baya, ga qafafu sun kumbura sosai, saboda kwalaben da ta farfasa sun shiga mata qafa, likita aka kira har gida ya mata magani, ba dama a sanya karatun qur'ani a gidan zata firgice ta sake take ciwon qafar ta ta.
A cikin ran ta kuwa ji take ina ma mutuwa ta dauke ta akan wannan azabar da take sha, in ta bude ido sukai ido hudu da Huzaifah ji take kamar ta shaqe shi ya mace kowa ma ya huta, Huzaifah kuwa da shi ake jinyar ta,Mummy sai qara nuna masa illar auren Salma take, amma ya toshe kunnan sa.
Kamar koda yaushe Salwa ta kawo ma Salma abinci, tayi tayi Salman taci saboda yau kwanan ta hudu kenan bata ci komai ba, sai allurai da ake ta mata da qarin ruwa, jikin ta dik ya mace ba qarfi, idon ta ta yi zuru2,Salwa ke ta lallaba ta amma taqi ci, kawai sai ta fashe da kuka, itan ma kukan take son yi amma ba zata iya ba, Huzaifah ne ya shiga dakin, ya amshi abincin dan ya gwada bata ko zata amsa, tana hada ido da shi ta zabura ta miqe ta zauna, mamakin ina ta samu qarfin tashi suke, kafin su gama mamaki ta kai hannu zata zubda abincin dake hannun Huzaifan, Allah ya sa ya gani, ya janye, ajiyewa yayi a gefe, sannan ya kama hannayen ta, ihu ta dinga yi tana son fizge hannayen nata,jin su take kamar wuta a jikin ta, addu'a sosai ya dinga tofa mata, tin tana ihu har ta daina sai ido, tana girgiza masa kai, a hankali ta samu ta daina ihun da komai ta kwantar da kan ta, tare da kulle idanun ta,
"Salma...Salma...Salmaa,bude idon ki ki kalle ni, "
A hankali ta sauke idanun ta a nashi,
"Salma karbi abinci ki ci kinji, in baki ci abinci ba zaki iya rasa ran ki, ba bawan da yake zama ba tare da abinci ba ya rayu, ko me ke tare dake ba masoyin ki bane, maqiyin ki ne mai qoqarin kashe ki, ki bude idon ki Salma karki bacci karbi ki ci kinji,"
A hankali ya fara bata tana amsa har ta ci mai yawa sosai, hamdala kowa yayi Ammi kamar ta taka rawa dan murna.
Bayan ya gama bata ya fita ya tadda Mummy a bakin qofa, kiran shi tayi zuwa dakin ta, zuciyar shi ba dadi ya bi ta, dan ya san labarin nata bai wuce akan ya bar Salma kar ya aure ta, shi Ubaidullah ta daga masa qafa amma shi kullum sai ta masa magana akan karya auri salma.
Koda ya shiga dakin tsaye ya gan ta tana kaiwa da kawo wa, cikin damuwa, dik ta fada saboda ta sawa kan ta masifa.
Cikin girmamawa ya zauna a gefen gadon ta, ya ce
"Mum in kinai wa Allah ki daina cewa kar na auri Salma, yanzu ba mu cikin qarnin da Iyaye ke zabawa 'ya'ya mata, matan ma an daina zaba masu maza yanzu su suke zaba da kan su balle maza, Mum na sani nayi rayuwa ta kaff a turai, da ace ban samu ilimin addini ba kema kin san ba zaki dinga tinkara ta da wannan maganar ba, dan Allah ki daina maimaita min magana daya kamar karatu, idan kina da matsala da mahaifiyar yaran nan ne ni jinina ne su, ba abinda zai hana ni auren su sai mutuwa"
"Lallai kuwa gwanda ka mutu da ka auri ragowar aljanu, Huzaifah ashe baka da mutunci? Ni kk farfada ma irin wadannan kalaman? Kana ganin yarinya ita da aljanar ma ba maraba, ita kk so ta zama suruka ta"
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
"Ehh ita nake so ta zama surukar ki, plsss Mum don't push it, i have heard enough"
Cikin fushi ya bar dakin, ya dauki mota ya fice daga gidan, gudu yake sosai a babban titin garin Abuja, tafe yake yana shafa kan shi saboda damuwa, kawai ya ga kamar mutum ya gilma ta gaban motar shi, wani wawan burki ya taka, ya hau dube2 amma bai ga kowa ba, tada motar yayi, ya sake diban ta da gudu, nan ma ya sake ganin wani tsoho zai tsallaka titin, ga shi ya zo daf da shi kamar zai take shi, a qoqarin shi na kaucewa tsohon ya kauce hanya ya daki wata motar dake gaban shi, nan da nan kuwa kan shi ya bugu da sitiyarin motar, saboda bai saka seat belt ba, mutanen dake gefen titin ba su da wani yawa, a haka aka samu wasu suka kai shi asibiti, wayar shi aka duba last call din shi Yah Ubaidu, nan aka kira k sanar da shi inda yake da kuma abinda ya faru.
Cikin tashin hankali Ubaidullah ya kira gida ya sanar, shi kuma ya damqa ayyukan da yake gabatarwa wajen mataimakin shi ya wuce zuwa asibitin.
Yanda ya ga Huzaifan ya dan samu kwanciyar hankali, kan shi ne kawai a rufe da bandage ta gaban kan shi, nan ya samu likitan da ya kula da shi, sukai magana aka sanar da shi meke damun shi, ciwo ne kawai ya samu a goshin nashi, ta dalilin rashin saka seat belt da bai ba, amma sun auna BP din shi sun ga jinin shi ya hau, tambayar Ubaidullah likitan yayi ko yana da wata matsala ne? Ko kuwa hatsarin ne y daga masa hankali har ya samu BP?
Shiru Ubaidullah yayi, dan ya san tabbas daga masu hankalin da Mummy ke yi akan auren su shi zai jawo wannan matsalar.
Ubaidullah ya gama da wajen Likita ya fito, ya ga su Mummy na tambayar wata nurse inda Huzaifah yake, tana kan tambayar su sunan shi, da abinda ya same shi suka hango Ubaidullah zai shiga dakin da Huzaifan yake, da sauri suka nifi inda ya ke, ita da Khairat da Sumayyah.
Koda suka shiga dakin Huzaifah ya farka, Ubaidullah ya juya ya ga yanda Mummy ta firgice,
"Na fada maka ka rabu da yarinyar nan, auren ta kamar kisan kai ne, dibi yanda ka samu hatsari, ba dan kiyayewar Allah ba me kk tinanin zai same ka"
Cikin bacin rai Ubaidullah ya kalle ta,
"Idan auren Salma bai kashe shi ba Mummy maganganun ki zasu qarasa shi, kin san me ke damun shi yanzu da kk wadannan maganganun? Jinin shi yayi hawan da ake gudun vata ran shi yanzu haka, jinin shi ya yi hawan da gab muke da rasa shi, dan Allah Mummy in ba zaki so wannan auren va ki sa albarka ki shiru, ki qi abun a ran ki, ki bar mu mu auri wanda muke so, lalurar Salma Khairat ko wani daga cikin qannen mu ba su wuce Allah ya dora masu ba, dan girman Allah Mummy ba dan mu yaran ki bane ki daina nuna qiyayyar ki akan wannan lamarin, meye asalin matsalar ki ne? Me bayin Allahn nan suka maki da suka cancanci irin wannan zazzafar qiyayya a wajen ki? Dan Allah ni ina son dan uwana, bana son na rasa shi, in ke ba......"
Wani hadadden mari ta sauke wa Ubaidullah, wanda ya sa Huzaifa ya fara nishi kamar wanda ake shaqewa, Ubaidullah da ya qame a wajen, tsabar mamaki, ne ya maida hankalin shi kan dan uwan nashi, Mummy kama hannun ta tayi da tai marin ta fara kuka, tare da dafa hannun Huzaifa dake fama da numfashin shi.
Likita Khairat ta dawo da shi, nan da nan suka ma shi wata allura, sannan suka sa mashi oxygen, umartar su yayi da su fita yana buqatar hutawa.
Waje suka fito Ubaidullah ya zauna a kujerun dake manne da bangon dakunan asibitin, tare da sanya fuskar shi a hannayen shi, hannun shi ya sa ya shafa inda Mummy ta mare shi;ya daga kai ya kalle ta, dana sani ne kwance a fuskar ta, baya son ganin hakan a tare da ita, zuwa yayi gaban ta ya durqusa, mutanen dake wucewa na masa kallon mamaki, da sauri ta fara qoqarin daga shi dan bata son mutanen su ci gaba da kallon su, amma yaqi tashi,
"Me kk yi haka Ubaidullah tashi, tashi ka zauna"
"Mummy ba zan tashi daga nan ba har sai kin yafe min, sai kin sanya ma auren mu albarka Mummy, ban damu da mutanen dake kallona ba, ke mahaifiya ce, albarkar ki kawai muke nema, fushin ki a gare mu musiba ne"
Cikin kuka da karyewar zuciya ta durqusa ta daga shi, tare da cewa,
"Ubaidullah Allah ya sanya albarka a rayuwar ku bki daya, ya sanya albarka a wannan auren da zakuyi, ka yafe min marin da nai maka, raina ne ya baci da naji kana neman ka nuna bana son d'a na, ina son ku gaba dayan ku ta yanda ban san wa nafi so a cikin ku ba, ahalin Jalaluddeen ne kawai bana so"
"Mummy ahalin Jalaluddeen muma muna ciki, abinda yayi jalaluddeen shi yayi Daddyn mu, Mummy me suka maki da zaki tsane su haka? Ubangiji baya son mutane masu nuna qiyayya ko soyayya ba domin shi ba, sabon Allah suke aikatawa da kk tsane su tsana mai yawa haka?"
Shiru tayi, dan kuwa va hakan bane, haka kawai ta tsane su dan son zuciyar ta.
"Shi kenan Ubaidullah magana ta wuce, Allah ya sanya alkhairi ya ba Huzaifah lfy"
"Ni xan fara mishi albishir kuwa"
Murmushi Mummy tayi tare da shafa kan Khairat din.
Har yamma suna nan zaune Huzaifah bai farka ba, Daddy da baya qasar yayi waya yafi sau biyar, Uncle Jalaluddeen da ya koma tin ranar da Daddy ya yi tafiya, shima alqawarin zuwa yayi, a washegari, dan yana son su zo da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 17