Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka kawai suka tafi, Ubaidullah hankalin shi na kan su, dan ya kula akwai rawar kai a tare da su, Sudais ne ya nuna masa ya barsu kawai ai su ba yara bane. Sanda suka iso matasa maza da mata suna tsakar gida ana ta hira ana maida yanda akai, wasu na ta hotuna, kowa dai da abinda yake, sai qoqarin fita take taji motar a rufe,juyawa tayi a fusace ta kalle shi, "Ka buden na tafi," Iska ya shaqa ya lumshe ido, sannan ya kalle ta, "Salma in kk yanke hukunci cikin fushi zaki yi dana sani, kina so na, ina son ki, kuskure ne na aikata, na baki hakuri, ashe ba zaki iya hakuri da ni ba inna aikata ba daidai ba? Haba Salma,Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, ki yafe min, kuma zan nemi gafarar Allah, na yi na damar abinda na yi tsakani na da Allah ba dan wai kinji haushi na ba," Bude mata yayi yana jiran ta fita, shiru tayi, kafin ta ce, "Na yafe maka, amma sai ka kawon ice cream qatoto guda hudu," You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Fita tayi tana murmushi sosai, shi din ma murmushin yake ta zabgawa, tana fita shi ma ya fice, sai tsokanar ta ake wai dadi miji, ta maqale masa tin kan a kai ta, hararar su tayi ta shige, tana zuwa dakin su ta tadda amaren a ciki da ma sauran sa'o'in su, sai hira ake, caaa aka yo mata, amma ta yi shiru ta fada bayi, sai da ta gyara jikin ta tayo alwala sannan taje tayi sallah. "Wa zai sha ice cream?" "Niiii" ."ku jira a kawo, wadda dik ta tsokanen ba zan sammata ba" Nan sukai ta mata fadanci, tana ta dariya, lokaci zuwa lokaci in ta tina abinda ya faru tsakanin ta da Huzaifah sai taji wani abu na mata yawo a cikin ta, sai ta lumshe ido wani lokacin harda murmushi, da ta ji haka maza take bude ido ta fara istigifari,saboda ta san sabo suka aikata tinda ba a daura masu aure ba, tana son sanar da Salwa me ya faru tana tsoro. Bayan awa biyu Huzaifah ya shiga gidan da manyan ledeji a hannun shi, wanda suke dauke da Ice cream. Ya kira Salma a waya, ta leqa, ta amsa sannan ta mashi murmushi dan tabbatar masa ta yafe masa, "Yessss" Cikin dakin ta koma ta sa Sumayyah sauka ta dakko masu qananan bowl din ice cream da spoons, nan sukai ta diba suna sha suna hira, Ammi ce ta leqo taga yanda suke ta lodar sanyi, fada ta yi ta masu ta kwashe ta fita, qananan yaran gidan ta bawa, tace su shanye, "Allah ya so ni na sha da yawa" "Ni ko ina cokalin farko aka amshe," Dariya sukai ta wa Salma ita ce mayyar sha dama. Kusan raba dare akai ana hira a gidan, gwanin ban sha'awa, kamar kar a rabu ko bayan bikin. (Dangi da dadi wallahi) 1 Washegari da misalin qarfe 12PM aka daura auren wadannan matasan samari da 'yan matan, kowanne akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, mutane marasa adadi ne suka shaida daurin auren, wanda ya hada da abokan Huzaifah da suka zo na musamman dan halartar daurin auren, abokan Daddy na waje ma sun samu halartar bikin. Mata na can gida suna yini, inda da yamma za a yi dinner, daga nan kuma sai kai amare gidajen su. Tin ana yini Salma da Salwa ke kuka, su da za a kai su Abuja, Khairat ma kukan ta ke dan anan za a barta,Nabeelah kuwa sai dai tai kukan barin gidan iyaye tinda iyayen ta na nan gari daya da ita. Da kyar aka samu sukai shiru bayan Sallar magrib aka cancada masu ado, da dogayen riguna wanda aka dinka masu daga Abuja, na wani material mai sheqi, kalar gold, masha Allah, amare sun yi kyau ba na biyun su, ga qamshi da ke tashi, ko ta wanne kusurwa ta jikin su. Dinkin iya fuskar su da hannayen su ya fidda dan kuwa har wuyan su an mishi wani ado ta yanda zai rufu. Hannayen su a cikin na mazan suka shiga wajen event din, wanda ke a cikin Sharaton, ranar Mawaqan Nija musamman namu na Arewa sun baje basirar su, Salma ta sha rawa, Salwa kuwa tsayawa tayi kawai tana rangaji, ita da Ubaidullah, kowa ya gan su sai sun bashi sha'awa, saboda kowa ya shaida su ba masu hayaniya bane, dik da su Salma ma sun yi kyau, amma su kowa ya san 'yan hayaniya ne. Qarfe tara na dare aka tashi, mota daya aka sanya Salma da Salwa dan wucewa da su asalin gidan su na iyayen su, Nabeelah ma haka sai Khairat da aka maida Family house. Tinda su salma suka sanya qafa a gidan su, sukai ido shida da Ammi, suka tafi da gudu suka rungume ta, sai kuka, Ammi kuka su kuka, Abba ne ya dafa bayan su, yana lallashin su, "Habaa Ameenatou, ya zaki sanya yara a gaba kuyi ta kuka kamar wanda aka wa auren dole? Plss ku daina, nan da lokaci kadan za a zo daukan su, zuwa Abuja, na so a bari sai gobe ido na ganin ido, amma Yayah yace a jirgi ne su je kawai yau, so kuyi sallama kafin lokaci ya qure," Sake qanqame juna sukai kamar za a raba su, cikin qarfin hali Ammi ta zame jikin ta, ta miqe zuwa dakin ta, wata takarda ta dakko ta damqa masu, da jaka wadda qur'ani da hadith ke ciki, sannan ta zauna. "Da farko ina godewa Allah da ya nuna min wanna rana ta auren ku, Allah na gode maka da ka bamu ikon aurar da su lfy, Allah ka zaunar mana da su lfy a gidan mazan su, dikkan abun qi Allah ka kare mana shi, Allah ka basu zuri'a mumina saliha,....ga qur'ani nan, na hore ku da yawan karanta shi, domin waraka ne kuma kariya ne ga dikkan musiba,ku yawai ta tasbihi, sannan ku na yawan karanta hadisin nan domin gane hukunce2n islam da kuma sanin tarihin rayuwar Annabi da sahabban shi, na umarce ku da karanta wasiqar nan a washegarin da aka kai ku gidajen ku, ku karanta ku da mazan ku, Allah ya muku albarka," "Ameen Ammi, mun gode maku, Allah ya saka maku da alkhairi, Allah ya sanya ku a aljannah, kun yi mana dikkan abinda iyayen kirki ya kamata su wa yarn su, har ma da qari, Allah ya saka maku da alkhairi, mun gode," Ammi ce ta miqe, Abba ya ci gaba da masu nasiha, cups ne ta dawo da su, manya, madara ce ta shanu da ta zuba niqaqqen ridi da dabino da aya, sai kayan qamshi, sai zuma, ta basu suka shanye, Sunji dadin abun sosai, brush ta sa suka yi, sannan ta sa suka watsa ruwa, wanka sukai da ruwa mai qamshi, sukai alwala, sai ta sa sukai sallah, suka sanya wani material mai laushi, dinkin riga da skirt, mai matuqar kyau, ta nade su da laffaya, suna zama 9:43pm, sai ga mota, Huzaifah da Ubaidullah ne ciki, sai driver, suna kuka Ammi da Abba suka fidda su, suka shiga, Huzaifah ne a baya Ubaidullah a gaba shi da driver, dan haka Salma ce ta zauna kusa da shi, sannan salwa ta shige, suna ta dagawa juna hannu, suka bar harabar gidan, Salma sai kuka take, Salwa da Huzaifah na bata hakuri, cikin ran ta tana ganin ta bama iyayen ta wahala a rayuwar da tai da su, ga shi sun aurar da ita cikin so da qauna, ji take da za a maida hannun agogo baya da ta zama mutuniyar kirki kamar Salwa. Sai da suka isa Airport ta nutsu, jirgin su ya tashi zuwa Abuja. Amare a sha love lfy sai gobe kuma inshaa Allah zan ci gaba.....MY NOVELS 1K 58 2 by Haermeebraerh Following Share 1-*WATA UWAR* 2-*'YAN ABUJA* 3-*'YAR RAWA* 4-*RIKICHIN KISHI* 5-*MIJIN YA TA KO MIJINA* 6-*DA SANIN SU* 7-*DAGA TUSHE* 8-*MAZAUNA GIDA* 9-*BIYAYYAH* 10-*KUN MAKARO* *11-MUGUN MIJI* *12-MUGUN HALI* *13-AURI SAKI* *14-SANADIN FYADE* *15-KALAN DANGI* 16-*ALMAJIRI NA* 17*ALBASA BATAI HALIN RUWA BA* 18-*TAUBASHI (COUSIN)* 19-*A GARIN MU* 20-*MAHWISH ( KYAKKYAWA KAMAR WATA) *DAGA HAERMEEBRAERH*KALAN DANGI.....PAGE 32 1.8K 103 18 by Haermeebraerh Following Dare ya yi sosai lokacin da suka isa, driver yayi bacci bawan Allah,wayar Ubaidullah ta tada shi, cikin magagi ya miqe, maza ya tada mota yaje inda suke, "Yallabai sabon gida zamu wuce ko" "Kwarai da gaske" Murmushi drivern yayi, shi ko Ubaidullah, yana ayyanawa, 'Ji mutumin nan har ma sai an sanar da kai,ai da gani ba bu tambaya' Unguwa ce ta masu hannu da shuni, mai kyau da tsarin kallo, a bakin daya daga jerin gidajen motar su ta tsaya, horn driver ya danna, ba a jima ba sai ga gate ya bude, mai gadi na ta washe baki, haka ma Huzaifah da Ubaidullah, Salma da Salwa kuwa jin su suke kamar suyi tsuntsuwa su bace, qirjin su sai bugawa yake saboda tsoron abinda zai je ya zo. Akwatinan su marasa nauyi mazan suka ja, su kuwa dauke da handbags din su, sai raba ido suke, ko ina haske ne wajen kamar rana, dan haka komai suna gani, gidaje ne biyu a hade da juna,kowanne qofar shigar shi daban, sama da qasa, kallon matsakaicin gidan ya shagaltar da su Salma, saboda kyaun da ya masu, g shi ba wani babba ba, amma tsarin ginin abin kallo ne. "Shall we?" Huzaifah ne ya radaw Salma a kunne, ta dan zabura tayi baya, tana raba ido, kallon Salwa tayi, ta fara kyabe baki zatai kuka, Salwan ma neman agaji take, Ubaidullah na ganin haka ya sake akwatin hannun shi qasa ya daga Salwa cak zuwa hanyar shiga, dan baya son ma ya tsaya lallashi ko raba su. Salma na ganin haka ta bare baki, "Habaa sweet, me ne ne na kukan? Dan Allah kar ki sa masu aikin gidan nan su sa mana ido, dan in kina kuka hankalin su kaf kan ki zai dawo, in suka sa mana ido ba zamu more daren yau ba" Shiru tayi amma hawaye na zuba a idon ta, dik da a mafarki da bayyane Irfaan yana zuwa mata ta san me za a yi amma wannan karon sai take jin komai daban, wannan karon ji take kamar bata san ma me zai faru a ciki ba in sun shiga. "Wai kuna tsaye har yanzu?Huzaifah kana ruwa " Cike da tsokana ya dau akwatin su yayi gaba, yana daga ma qanin nashi hannu, "Sai da safe" Banza Huzaifah ya masa, "Baby kinji ko? Ki ga yanda yake tsokanar mu, pls mu je ciki, ko kina so na dauke ki kema?" Qoqarin aje akwatin yake ta sa sauri ta shige gidan, bakin ta dauke da a'uziyya da basmala, sannan tana addu'ar fatan samun alkhairin dake cikin gidan, kuma tana neman tsari da sharrin da yake cikin gidan da mai gidan. Murmushi Huzaifah yayi "Lallai ne ina ruwa in yarinyar nan bata sake ba, tabbb, ni na zaci ba zan wahala ba?" Ayatul kursiyyu yayi a qofar gidan kafin ya rufe, tsaye ya gan ta ta sake baki tana kallon tsaruwar gidan, shi kan shi ya yi mamakin ganin wasu abubuwan n katakwaye da aka sauya, kamar su dinning table, da center table, sai side tables, (Aikin Uncle Jalal ne wannan) "Wowww" "Masha Allah" Kallon juna sukai suka saki murmushi, kama hannun ta yayi sannan yace, "Muje mu ga sauran, dan dai ni ban saka wadannan abubuwan ba, naga an sauya abubuwa" Cike da zumudi ta bishi, daki biyu ne a qasa guda daya da gado dayan kuma katifa ce irin qatuwar nan, dakin dake dauke da gado ,gado ne madaidaici da zi dau mutum biyu, tana gani ta san aikin Abban su ne, dan tsaruwar gadon ya tabbatar mata harda sa hannun Abban su a aikin shi,shi yasa wataqila ganin shi yayi wahala. You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Sama suka hau, nan ma daki biyu ne, kowanne daki dauke da makeken gado, wanda ya sanya Salma zubar da hawayen farin ciki, a qasan ranta tana zabgama iyayen ta addu'a, sun gama mata komai, kallon Huzaifah tayi kawai sai ta fada jikin shi tana murmushi mai dauke da hawaye. Shiru yayi , sannan daga baya ya rungume ta shima, a hankali ya fara shinshinar qamshin ta, maida wuyan ta tayi dayan bangaren, saboda yanda taji yana sinsinar wuyan ta tare da goga hancin shi da lips din shi, yana aika mata wani irin saqo a jikin ta gabaki daya. Tsayuwar na neman gagarar Salma, dan kuwa dik qafafun ta rawa suka dauka, daga ta yayi ya kwantar a saman gadon su, ya kwanta a gefen ta,shafa jikin ta ya fara, sannan ya kai lips din shi saman nata, yana wasa da shi, kafin ya fara kissing din ta, wani irin dumi take ji na fita a jikin su, na tsananin buqatar juna, sake manna kan ta tayi a nashi. Sun yi nisa sosai, Huzaifah ya janye, cike da kasala ya daga ta, ya miqa mata hannayen shi dika biyun, tashi tayi tsaye bayan ta kama hannayen nashi, idanun ta a qasa, fara warware mata laffatar ya yi, yana gamawa ya tsaya yana kallon lungu da saqo na jikin ta, riga da skirt din sun dame dik wani sashe na jikin ta, qirjin ta ya bayyana, da sauri ya ja hannun ta zuwa toilete, ya mata umarni da tayi alwala yana zuwa. Sai da tayi tsarki sannan ta daura alwala, tana kallon kanta a madubi, tayi murmushi, samun kanta tayi da daukan brush ta wanke bakin ta, sannan ta fita. Huzaifah kuwa kitchen ya sauka ya shige, nan ya duba fridge ya fiddo gasasshiyar kazar da ta sandare, ya saka a oven, ya dakko fresh milk, ya aje a a saman trey, qananan glass cups ya dora, yana tsaye yana jiran kaza tayi, sai doka murmushi yake, shafa gemun shi yayi sannan ya lashi lips din shi. Qarar oven ne ya dawo da shi daga duniyar tinanin da ya fada, ciro kazar ya yi ya dora a plate ya samu wuqa ya yanka yanda zata masu sauqin ci, sannan ya dauka zuwa sama, Sallah ya tarar tana yi, ya ajiye ya koma dayan dakin ya yi alwala shima ya gyara jikin shi, tare da sanya kayan bacci, yayi brush, ya sa turaruka kala2 masu dadin qamshi, sannan ya yi sallar dake kan shi. Yana idarwa yayi addu'a sosai ya shafa, sannan ya nufi dakin Salman, zaune ya gan ta, sai kallon kazar take, 'Salma bata wasa da cikin ta' 1 Zama yayi ya ja abincin gaban su, ya zuba fresh milk a glass cups din, sannan ya fara bata a baki, ba wasa tini ta kurba, sai da ta dan sha ta kauda kai, kazar su suka ci sosai, suka qoshi, sannan suka shiga toilete suka wanke bakin su suka fito, Gani tayi ya tsaya a kan sallaya, ya umarce ta itama ta tsaya bayan shi zasuyi nafila. Ba musu ta tsaya a bayan shi tare da sanya hijabi, sallah suka gabatar ta nafila raka'a biyu, bayan sun idar Huzaifah ya kashe Salma da mamaki, addu'o'in da yake ta zabgawa kamar baqin balarabe ya bata mamaki, ta san ya na da ilimin addini, amma bata zaci ya iya irin wannan addu'o'i ba da larabci. Sai da suka gama, ya kula har wannan lokacin kayan ta na da ne a jikin ta bata sauya ba, bai ce komai ba ya nufi wardrobe ya buda, ya fara dubawa, wata rigar bacci ya samo mai haske sosai, fara sol, mai santsin gaske, ya rufe ya dauki turare dake kan mirrow ya feshe rigar da shi, sannan ya kashe fitila, ya bar masu ta gefen gado, kallon shi kawai take, a hankali ya aje rigar a gefen gadon, ya manna ta da jikin shi, wasanni yake mata sosai wanda ya sa ta kasa jurewa ta fara maida masa itama. Da kan shi ya cire mata kayan jikin ta ya sanya mata na baccin..... Salma ta gurzu wajen Huzaifah, haka ma Salwa, sun nuna ma juna soyayya, ranar nan mai cike da tarihi ne a wajen mutane takwas, Huzaifah,Ubaidulallah, Ameer,Sudais Salma, Salwa, Khairat da Nabeelah. Sun sha amarcin su, wanda ba zasu taba mantawa ba a rayuwar su, dan kuwa kowanne da irin salon soyayyar da suka zuba a nasu. Sin yi ma iyayen su godiya saboda tarbiyyar da suka basu baki dayan su, ba mazinaci, ba mai shaye2, ba barawo, haka ma matan, sun sami matan su kamar yanda ya kamata a samu kowacce mace budurwa. Ana tashi da shagwaba mata, wannan karon a gidan Huzaifah abun sauyawa yayi, dan kuwa shagwaba ya dinga yi wa salma, dan ya kula in ba haka ya mata ba ruwa ma sai ya tauna mata, shi kuwa ya fi ta son a lallaba shi. Tare sukayi wanka suka shirya cikin shadda iri daya, suka sauka qasa, dan samarwa kan su abun karyawa, wayar Mummy ce ta tsaida Huzaifa daga yanka albasa da ya fara. Bayan ya gaishe ta ta fada masa saqon da zata fada, yayi godiya ya kashe wayar,murna yayi ya kama kafadun Salma ya ce, "An hutar da mu Mummy tace Haule zata kawo mana abun kari ba sai mun siyo ba" Bari na fada ma Yah Ubaidulallah," Ubaidullah tinda sukai Sallar asuba da kyar saboda gajiya da bacci, suka koma baccin su, ya dora Salwa a saman qirjin shi, yana lallaba ta a haka tai bacci, fuskar ta ta kumbura saboda kuka, dan kuwa bai mata da sauqi ba. Cike da muryar bacci ya ke magana, "Hello?" "Mummy tace ba sai kunyi abincin safe ba, wait bacci kuke?" "Eh meye?" "Hahahhhaaa ba komai, sai anjima" Kashe wayar yayi, "Kinga bacci ma sike muma mu koma kinji honey" Yana fada yana aika mata da wasu saqonnin da ba dan zafin da take ji a qasan ta ba da ta amince sin koma, amma inaa dole ya hakura ko kwana biyu ne ya bata ta warware. Zamewa tayi ta koma parlour ta zauna, "Yunwaa nake ji ni" "Karki kuka yanzu za a kawo abinci, ko na dumama maki ragowar kazar jiya ki sha da fresh milk kafin a kawo?" Daga kai tayi, bai bata lokaci ba kuwa wajen kawo mata ta fara ci tana bashi, haka suka samu suka toshe yunwar da suke ji, sannan suka haura sama. Koda Haule tazo basu sani ba,nan ta gyara masu abubuwan da suka bata, ta jera abincin a dinning table, sannan ta je wajen su Ubaidullah wanda suma baccin suke, su basu bata komai ba,amma dik da haka sai da ta yi goge2 sannan ta s drivern d ya kawo ta ya maida ta. ******************* A can gombe kuwa Ammi ta kwana da kewar yaran nata, amma da safe bai hana ta tashi ta dafa ma Khairat farfesun naman kaza ba, ta soya mata chips da kunun gyada, sai kwai da ta soya ta zuba ta bama Mansur ya kai musu. Nabeelah kuwa daga gidan Baba Isa aka kai masu abun karyawa. Komai Ammi take sai ta dinga ayyana da su Salma na nan da sun yi abu kaza, lura da halin da take ciki ne ya sa Abba ranar yace ba zai je aiki ba, shima hutawa zai tinda akwai gajiya shima a tare da shi na aikin kayan gadon da yayi na amaren. Dik da ya dade yana yi ba lokaci daya ya yi su ba amma qarasawar ya bashi wahala, musamman ga hidimar bikin ga kuma aikin kayan gadon. Ranar sai da ya sa Ammi taji kamar itama sabuwar amarya ce, soyayya suka zuba sosai kamar ba su aje Salma da salwa ba. "Kin gani Ameenatou dama na fada maki, in sun tafi zamu fi sakewa, ba ruwan mu da tsoron yara zasu gan mu" "Still ina kewar su Abban su" "Nima ina kewae su sosai,yau ba qira'ar Salwa, ko kuma tsiwar Salma, gidan shiru" Dan murmushi tayi ta fara tina masa wasu abubuwa game da yaran nasu. ***************** Bayan shekara biyu salma da Salwa sun haifi yan biyu, Salma ta haifi maza dika, Salwa kuwa mace da namiji, Khairat har yanzu bata haihu ba qaramin ciki gare ta, sai nabeelah da ta haifi namiji an saka mashi sunan Uncle Ibraheem, suna ce masa khaleel, yaran salwa kuwa, da Ameenatou suna kiran ta Meenaah sai Uncle Jalal,da Jalal little suke kiran shi ko suce little, sai yaran Salma da aka sanya Usman da Ahmad. Familyn ya qara cika da kuma samuwar albarka, Salma a yanzu bata da qawa ko daya,qawayen ta sune dangin ta, da wahala ma ta hau social net yanzu, samarin yaran ta basu bari, ga qaramin cikin da bata san tana dauke da shi ba, wanda uban gayyar ya kula yayi shiru gudun daru...... ... Hahhhhaaa maza kuna sha'anin ku, Allah ya sauke ki lfy Salamn Irfaan Maleek, opsssyy🙊🙊Salmn Huzaifah Ibraheem,🤣this is the end of my Tory, not salma and salwa's, rayuwar su ta ci gaba da kasancewa cikin zafi, sanyi, damina, kamar yanda rayuwar mutane da dama take...... KALAN DANGI Marubuciya Hamida Sunusi Ahmad (Haermeebraerh) | 09031416423 Compiled by Shuraihu Usman An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private

Chapter 16 of 17