Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
son jiki, amma kinga waccan mai jin kn? Da ta ke ganin kowa a dage, Allah ya shirya mana kwai," "Ameen" Salwa ta dan sauya fuska, dik abinda za a yi bata son a taba mata 'yar uwa, ko bata kare ta ba zaka gane a fuska bata so, ganin haka yasa Mummyn wuce su ta zauna ta dauki remote ta fara sauya tasha danyin kallo, sama suka haye, Khairat na bata labarin yanda sukai da Huzaifah, ganin qofar dakin Salman a bude ne ya sa suka leqa, Huzaifah ke zauna a saman kujera yana kallon Salma na bacci, "Bala'innan, yau in ta farka taga garjejen qato na kallon ta akwai masifa a gidannan, kinga mu lalaba mu shiga, tinda ba zamu iya cewa ya fita ba ko ya kk ce?" A dan tsorace Khairat tace, "Eh muje," Koda suka shiga hannu ya sa a lips yana masu nuni da suyi shiru, su din ma haka suka masa, waje suka samu suka zauna, Khairat na ta bakin qofa, yanayin zaman ta irin na wanda da ance kyat ne ya kyalla da gudu, dan tinda taji labarin yanda aljanun ke ma Salman tsoro ya shige ta, bata taba jin labari irin na Salman ba. Irfaan da ke daga nesa saboda addu'ar da Salwa ta ma Salma takaici dik ya dame shi na kallon da Huxaifa ke ma matar shi. Dan haka zuwa ya yi gaban Huzaifah ya hura hancin shi, nan da nan kuwa wata qatuwar atishawa ta kubce masa har sau uku. Zai ta hudun ya samu dama da kyar yace "Alhamdu lilLAAH" A cikin hanzari Irfaan ya kauce, "Wai su musulman nan komai sai sun kira abin bautar su ne? Ba abinda zasu gabatar ba ibadar su a ciki? Sai wanda bai riqe addinin da kyau ba, mutanen nan na zaci zan samu sauqi na kusantar iyali na amma abun na neman gagara ta, zanyi maganin ku yanzu," Salma ce ta bude ido, sakamakon qarar da taji na atishawar Huzaifa, bude idon tayi sosai ta zauna da kyau, daga ita sai shimi mai kyau wadda saman ta yake da adon lace mai kyau sosai, ta dame ta ta bayyana halittar qirjin ta, Huzaifah wani yawu ya hadiya, bai neman mata ba har ya bar qasar turawa amma yayi shan sigari a baya, kafin ya hadu da wani imam sukai abota. Amma mata da shigar tsiraici a turai ba zaka iya hana kan ka kalla ba koda dau daya be kuwa, bai taba ganin wadda ta masa kyau kamar salma ba a haka. (Niko nace dan kana son ta ne,) Salwa ce ta ja mata vargo zuwa qirjin ta ta rufe, saboda ganin yanda Huzaifan ya kafe ta da ido, ganin an rufe mata qirji ne ya sa yayi saurin sosa kai ya fice. "Ai da kun barni ya gama qare min kallon, ni ban ma san shegen da ya ciren diguwar riga ta ba," 'Irfaaannn' Shine abinda zuciyar ta ta raya mata, murmushi tayi mai sauti, "Kuje waje ni na shirya dalla" "Wai ke meke damun ki ne?" Ai tini Khairat ta kai qofa, "Tinda tace a barta a barta mana anjima mun dawo hira ko salma?" Daga mata kai tayi alamar eh, ta juya tana kallon Salwa, da mata alamar fita mana. Salwa fita tayi ta ja mata qofa, rufe qofar tayi da key, ta fara cire kayan ta ba bismillah ba komai (In mutum zai cire kaya yayi bismillah, ko yace Bismillahi allazi la'ilaha illahuwa) Halittar jikin ta na bayyana Irfaan na bayyana, nan da nan kuwa suka maqalewa junan su, "In ban haka ba ashe ba zan gan ka ba ko? Me yasa kk azabtar da ni ne? Dan ka ga ina son ka?" Bai barta ta ci gaba da magana ba ya kama lips din ta, tini ya mantar da ita me take son cewa, da wani zai shiga dakin zai ga kamar ita daya take qoqarin biyawa kan ta buqata, amma ita a wajen ta Irfaan take gani sosai kamar mutum a gaban ta, kuma take jin tabin shi da komai nashi. Da wani zai ce mata babu Irfaan da zata qaryata shi tace akwai shi, dan kuwa tana ganin shi, tana jin shi, above all tana son shi. Soyayya suke ta zubawa sosai, tin suna dakin suka koma toilete, sai da suka gamsu da juna sannan sukai wanka a tare, suka fita, ya taya ta shiryawa, yace zaije fada, sai da dare zai dawo, ta kula da kan ta, in ta bari aka bata magani ba zai zo ba, ko ta saka wannan maganar da take sawa, "Karatu ne fa ba magana ba" "Amma ai ni magana nake ji, in aka saka ba zan zo ba, kin dai ga yanda yake qona ni, amma in kina son na qone zan qone, indai akan ki ne, ba abinda ba zan ba" Da sauri ta qanqame shi tana kuka, "Ah ah, bana son ka qone plss, i love u handsome" "And i love u more beauty na" Kissing goshin ta yayi kafin ya bace. Buga qofar dakin ta taji ana yi da qarfi.............KALAN DANGI....PAGE 21 994 83 5 by Haermeebraerh Following Gyara jikin ta tayi ta sanya riga sannan taje bude qofar, Salwa ce ta hau duba ko ina a jikin ta, tare da taba wuyan ta,ture ta tayi tana mata wani irin kallon meye haka. "Salma are you ok? Naji kina ta magana kamar mai magana da wasu," "Ban gane me kk nifi ba, nufinki na haukace ko mi?" "Ba haka nake nufi ba Salma, zan wuce naji maganar ki, kuma naga ke daya ce a dakin" "Kuma sai aka ce maki ba waya ko? Mthsss" Shigewa toilete tayi dan yin wanka, Salwa kuwa ta zauna tana mamaki, tabbas taji magana, to wataqila wayar take,dauka tayi dan ganin da wa take waya haka, a kashe ta ga wayar, mamaki ya sake kama ta, Salma is lying,but why? Salma ce ta fito wanka, daure da towel a kan ta, ta daura shi ya mata kyau yanayin daurin, sai wani towel din a jikin ta, "Me wayata ke yi a hannun ki?" "Ba waya kk ba dazu," "Da aljanu nake magana to sai mi?" Zaro ido Salwa tayi waje, "Aljanu fa salma" "Eh da aljanu nake magana, na ce maki waya nake kinqi yarda harda duban waya ga maqaryaciya ko? Yaushe na taba maki qarya? Ni bana son bin diddigi, ina magana wayar ta katse saboda ba caji ta mutu,kuma dole2 sai kinji da wa nake waya?ko dan ke baki da masoyi har yanzu sai aka ce maki kowa ma baida mai son shi," Tana fadan maganar tai dana sanin furtawa, amma a fuskar ta ba komai na nuna danasani. Murmushi mai qayatarwa Salwa tayi, wanda da ka gani ba jin ciwo ko kadan a cikin shi, sai tsantsar farin ciki da murna, tashi tayi ta isa gaban Salma, wadda zuciyar ta ke bugawa sosai, tabbas bata kyauta ba, ko ma me ya faru ba zaka ma mutum magana akan abinda yake nema ba ya rasa, sun kai munzalin aure amma har yau basu da samari, samarin da suke yi yawanci 'yan a sha sha'ani ne, saboda kyaun su ake son su amma ba dan Allah ba. Salwa na zuwa kusa da ita Salma ta fada jikin ta tana bata hakuri, "Dan Allah ki yafe min Sweetheart, ba zan sake ba, da gaske nake waya nake ba da aljanu nake magana ba" Khairat da ta sako kai zata shiga taji ance aljanu ai da wani irin sauri tayi baya ta sauka qasa da gudu, ji take kan ta isa qasan za a ja ta a kaita gaban Salma, tana jin ta sauka qasa inda mutanen gidan ke zauna ta basar ta fara tafiya normal, amma dik da haka Huzaifah sai da ya tsokane ta, 1 "Zabuwa ke da wa?" "Ah ka manta Kaza ce, kai Yah Huzaifan nan ka cika tsokana" Dariya yayi ta mata yana tsokanar ta. Ita kuma tai banza da shi ta dinga kallon TV amma bata gane komai, tinani take da gaske Salma na magana da aljanu? A can dakin kuwa Salwa ce ta zaunar da su dikan su bakin gado, tare da kama hannun Salma, tana murzawa a hankali. "Salma u knw what? Abinda kk fada bai batan rai ba, dama ina son na fada maki cewar ni da Yah Ubaidullah muna son junan mu, kuma inshaa Allahu mun amince zamu yi aure, da ga Daddy ya dawo daga tafiyar da yayi jiya zamu sanar da su abinda ke faruwa" Cikin murnar da Salma ta dade batai ba ta kama hannun Salwa suka dinga tsalle a saman gadon suna dariya, daga baya kuma ta ja ta jikin ta sukai huging juna. "Congratulations sister, i am so so happy for u, Allah ya kaimu lokacin ya sanya albarka" Salwa kallon 'yar uwar ta ta kawai take da wani irin yanayi mai hade da so, qauna, tausayi, da kuma farin cikin ganin yanda ta warware, lallai zuwan su Abuja remedy ne na cutar Salman. You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... "Bari na shirya muje qasa mu sha hira" 'Ikon Allah' Inji cewar Salwa a zuciyar ta, godiya ga Allah ta dinga yi, zama tayi ta zaro wayar ta a gefen wandon ta,no Ammi ta danna,Ammin ce ta dauka cike da damuwa. "Salwa yaushe 'yar uwar ki zata kira ni ne? I am missing her so much here, amma bata damu data amsa kirana ba ko ita ta kira ni" "Caml dwn Ammi, ga shi zaku gaisa da ita" Miqawa Salma wayar tayi, ta amsa cikin murna da kewar Ammin nata. Nan fa sukai ta hira, suna dariya, abun gwanin ban sha'awa. Ranar kowa ya san Salma is in good mode, Mummy ma kan ta sai da ta sakko saboda da Salman akai abincin daren ranar, Huzaifah kuwa sai binta yake mamat dik inda tayi, ita sam bata gane ma me yake nufi ba. Ubaidullah sai dare sosai ya dawo, saboda shigowa da dabino,busasshen inibi,da bagaruwa, da sukai daga qasar saudiyya mai kyaun gaske, manyan super markets ke siya su na gyarawa su sanya a robobi su siyar. A gajiye yake sosai sanda ya shiga gidan, Salwa idon ta biyu, suna ta hira a parlour su hudu, Huzaifah, Salma, Salwa, da Khairat. "Me kuke har yanzu wajen 12 ba kuyi bacci ba?" "Jiran ka ta ke Yallabai mu kuma muka tsaya ta" Kallon wadda tai maganar yayi, Salwa kuma tana dukan kafadar ta akan tayi shiru, dan uwa rabin jiki, yaji dadi sosai da yaga wai salma ke magana, tabbas Allah ya amsa addu'ar su ta samu lfy. Zama yayi a kujerar dake kallon inda suke, "Iyyyeee Salma ke magana yau? To barkan mu,....Salwa dear pls kawon abinci da dan abin sha daki na, na gaji sosai....kai kuma qaton kawai wato ba aikin yi shine ka samu tsakiyar mata ka zauna haka ko? Allah ya dawo da Daddy lfy yana dawowa zaka fara zuwa office yaro, sauran ka daura kallabi kaima" Dariya sukai tayi har Huzaifan, sannan ya wuce sama. Dakin shi ya shiga yaji wani irin qamshi mai sanyi, an gyara dakin sosai, ga shi an sauya masa zanin gado, murmushi yayi tare da limshe ido, ya aje jakar shi ya shige toilete, wanka yayi a gurguje ya yi brush ya fita daure da towel a qugun shi, yana goge jikin shi da daya, yana bude qofa Salwa na bude qofa zata fita itama, da sauri yayi baya ya rufe qofar shi, dan ba zai so ta gan shi a haka ba, kusan tsirara yake, ta jikin mirron da ke wardrobe ta hango shi, dariya tayi ta qarasa fita, shi din ma dariya yayi, a bakin qofa ta tsaya, yana kula da tsayuwar ta sanda ya fita, dan haka cikin hanzari ya shirya, ya sanya turare, sannan ya bude qofar. "Shigo," "Ah ah, zan je na kwanta, dama zan yi maka sannu da dawowa ne" "To gani yi min Sannu da dawowan" "Sannu da dawowa Yah ubaiduna" Kallon ta yake kamar yau ya fara ganin ta cike da so da qauna, itan ma kallon shi take, lips din shi ya lasa ,cikin wata iriyar murya mai tsananin begen wanda ake so. "Yauwa Salwa na" Siririyar dariya tayi mai dadin sauraro, ta rufe bakin ta, tana kallon shi da idanun ta da suka sha kwalli. Shafa kan shi yayi, tare da cewa, "Salwa sai da safe, ba zan iya jure tsayuwar mu ba, son da nake maki na son ya rinjaye ni" Dariya ta masa sosai, ta daga masa hannu ta fara takawa dan zuwa dakin su, a jikin ta take jin yanda idon shi ke bin jikin ta da kallo, tafiyar ta mai cike da daukan hankali taji na neman gagarar ta, qafafun ta na sarqewa dik da wando ne a jikin ta da doguwar riga mai tsaga gefe da gefe, sai mayafi da ta yafa. Juyawa tayi ta turo bakin ta irin na shagwaba, ya gane me take nufi dan haka ya hura mata kiss ya wuce dakin shi, da sauri ta qarasa dakin su, Khairat har tayi bacci, ta qudundune, da alama sanyin AC ya mata yawa, rage sanyin tayi, sannan ta samu mayafin ta ta kade inda zata kwanta sau uku tayi bismillah, hayewa gadon tayi, dan kuwa bacci take ji sosai, bata jin zata iya tsayawa wani sauya kaya, addu'a tayi ta shafa sannan ta kwanta. Salma kuwa ta san yau Irfaan ba zai zo ba, kuma ya mata bayani, dan haka bata damu ba, baccin ta ta kwanta tayi, bayan ta sanya hotunan su na dazu da suka dauka a IG, mutanen ta na ta mata magana akan sunyi missing din ta, haka tai ta amsa wasu wasu tana sharewa, tana riqe da wayar tayi bacci. Da sassafe bayan sunyi sallah, suka shiga kitchen yau Daddy zai dawo, kuma da safen jirgin su zai sauka, dan haka ake ta gyare2 da girke2, ko tafiyar kwana daya yayi haka ake masa wannan gyaran. Mummy ta sha kwalliya kamar mai zuwa biki, an zuba gwala gwalai, sai tashin qamshi take, bakin nan yaqi rufuwa kamar wadda miji yayi wata baya gidan. Suna jin motar shi yara qananan suka fita da gudu, Mummy ta qarasa sakkowa ta tsaya a tsakiyar parlourn. Ya jima kafin ya shigo, yana ta daga yaran yana masu wasa da tambayar ya suke. Koda ya shigo ya kalli Mummy yaga tayi kyau, amma ya dauke kai, ya fara amsa gaisuwar yaran, cikin ran ta bata ji dadi ba, dan ba wanda zai kalle ta ko sarkin hassada yace batai kyau ba, dannewa tayi itama ta isa gaban shi ta dafa bayan shi tana masa sannu da zuwa ture hannun ta yayi yana mata fada da ido alamun yara na kallon su. Cikin fushi ta haye sama, shi kuma ya gama amsa gaisuwar yaran shi sannan ya hau saman, Khairat ta dawo daga kai masa jakar shi ciki, wadda ta amsa hannun driver. A bakin gado ya gan ta, ta zauna ta bata rai, wucewa yayi gaban madubi ya fara cire agogon shi, ya kalle ta ta madubin, "Yanzu dan Allah ke yarinya ce da kin girma baki san kin girma ba? Yara dik na kallon ki amma haka zaki dinga tabani gaban su, na fada maki bana son irin wannan rayuwar a gidannan, in mun shiga daki komai ma zamuyi" "As if a dakin ma u ar romantic, na rasa ya zan da kai, a gaban ka Jalaluddeen ke tarairayar matar shi, su na zuba soyayya da su da yaran su, amma kai da an maka magana ma sai ka nuna bata dace ba gaban yara, balle akai ga taba ka, yanzu ya dace daga dawowar ka ace ran mu na baci? Wanne na miji ke haka?u ar impossible, kamar wanda baya shiga qasashen waje yana ganin ya suke gudanar da soyayya da matan su" Ya san in ya biye ta haka zasuyi ta yi, shi ba irin romantic type dinnan bane, kawai ya san yana son matar shi da yaran shi, amma wata soyayya bata dame shi ba, ba dan matar bata masa komai ba, ah ah ra'ayin shine kawai hakan. Wanka yayi ya shirya a cikin toilete din ya fito, gani yayi ta cirs komai na adon, ta goge su jambakin da dik wani abu na kwalliyar, a qalla zata kai 52,amma ba wanda zai ce ta kai shekaru haka, saboda kwalliya, da gayu, da wayewa. Zama yayi kusa da ita, tare da jingina jikin shi a nata, "Dan Allah ki fahimce ni, kowanne mutum da ra'ayin shi, a lokacin ina ganiyar quruciya ta wanne irin soyayyace ban baki ba? Wanne irin kulawa ne baki samu ba? Yanzu Jalaludden da kk sawa ido da iyalin shi Jalaludden ke kan ki ya zauna a wajen ki kafin yayi aure, matar shi kuwa dikkan ku kun girme ta, ina sane da sa masu ido da kukayi, da jin zafi akan ta, mijin ta daban fa naku daban,zamanin ku kuma kunji dadin nan, suma ku bar su akwai lokacin da zai zo su daina wannan abubuwan" "Banga alamar Jalaludden har qarshen rayuwar shi zai daina nuna ma matar shi soyayya ba, saboda yaran shi yanzu shekarar su ashirin da biyu zuwa da uku, mu kuwa tin bayan da na haifi Khaleefa mai bi ma Huzaifah ka daina nuna soyayyar ka, wanne irin rayuwa ne wannan? Ni ka ga indai wannan maganar ce ba zata qare mana ba, kaje kaci abinci kawai" "Ke fa?" "Na qoshi" "Nima na qoshi" Kallon shi tayi; taga idanun shi akwai yunwa a ciki, in ba ruwa ba ta sani baya cin abincin jirgi, da alama ma bai ci abinci ba kafin su taso, tashi tayi tana kumbura baki kamar yarinya ta maida kwalliyar ta dan kar yara su gane tana fushi da gyatumin su, ta fara gaba, ya na biye yana murmushi. Hira ya tarar Salma da Ubaidullah suna yi kamar wasu abokai ko masoya, Salma na ta dariya kamar wadda akai ma kyautar hajji, daddy murmushi yayi ya zauna.......... 2 ToooooofaaaaahhhKALAN DANGI...PAGE 22 1K 86 6 by Haermeebraerh Following Har suka gama cin abinci Daddy bai daina murmushi ba, kowa ma sai ya kasance cikin farin ciki, hira sosai Daddy ya yi da su kafin ya wuce sama domin hutawa. A nan ya gano kamar akwai shaquwa sosai a tsakanin Salma da Ubaidullah, Salwa kuma da Huzaifah, su kuma ta bangaren su, sun yi ji nauyin bayyana ma shi soyayyar su ne shine dalilin da yasa kowa ya dauke kai ga abin son shi. Koda ya shiga daki ya kwanta a katafaren gadon su, ya ja numfashi wanda ke dauke da iska mai qamshi, ya furzar, fuskar shi dauke da murmushi mai qayatarwa, a haka Mummy ta shiga ta same shi, zama tayi a jikin shi, sannan tace, "Daddyn yara yau wanne irin farin ciki ne kk tattare da shi daya kasa boyuwa a fuskar ka?" "Babban farin ciki ne da dik wani masoyi na in yaji zai yi farin ciki shima, ina zuwa" Miqa hannun shi yayi ya dakko wayar shi, call log ya shiga, no Jalaluddeen ya danna, nan da nan kuwa bata jima tana ringing ba ya daga, gaisawa sukai, sannan Daddy yace, "Ina son nayi wata magana mai mahimmanci sosai da ku, ban sani ba nan zamu zo ko ku zaku zo nan? Da kai d sauran 'yan uwan mu" "Yayah ai sai mu zo, ba sai ka zo ba" "Ah ah ina ganin ni ya fi dacewa na zo, tinda ku uku ne ni ko mu biyu nake son muzo, zamu zo jibi inshaa Allahu" "To Yayah Allah ya kaimu, a gaida iyali" "Zasu ji ina gaida Ameenatu," "Zata ji Yayah" Sallama sukai, Mummy na zaune na jin ikon Allah, wannan irin abu na matuqar bata takaici, kawai dik sanda ya ga dama sai ya yanke hukunci akan abu mai mahimmanci ba tare da shawara da ita ba, yanzu ma da ita za ai tafiya amma ba ta kai matsayin a sanar da ita ba kafin a shirya tafiyar, sai dai taji a waya, (wasu matan da maza ke wa haka ku na hakuri, indai namiji a cikin kashi dari na kyautatawar aure yana baki tamanin ki hakuri da ashirin din ya zama weekness din shi, wata qila nashi kawai kk sani, ke wata qila ma kaso sittin kk bashi ko hamsin, amma bai taba maki magana ba, amma ke daga anyi abu komai qanqantar shi sai kiji an saba maki, an maki b daidai ba, wanda b hk bane, kina da bin diddigi ne wataqila da hango wasu an masu ke ba a maki ba, mata mu dinga nazari) "Dan Allah ki daina kumburar nan, sake hayewa fuskar ki keyi," Cikin dariya ya fadi hakan, aiko ta sake kumburo kumatu, "Kai da wa zakuyi tafiya ban da labari akai?" "Da ke mana," "Yanzu abinda k...." "Ya isa, in muka je zaki ji koma akan me zan magana" "Ikon Allah, kana ban mamaki Ibraheem,yanzu ace wai ni banda ikon sanin abu sai qannen ka sun gama sani? Kuma babban abun takaicin shine da damar lokuta abu akan yarana ne, bazaka sanar dani ba sai anje, ko tamin dadi, ko kar tamin, yarana nawa ke qasarwaje ba da izi na ba, Huzaifah sanda zaka kai shi sai a gaban qannen ka naji,ka min adalci kenan a matsayi na na wadda ta dau cikin su wata tara? Sai naje gaban matan qanne ina bayani, ina nima ban san akan me za ai magana ba kana sake zubar min da mutunci, suna ganin ban isa da gidana ba?" "Dama ai namiji ke isa da gida ba mace ba, dik wadannan dalilan naki ba su da qarfi, ki hakuri zakiji me ne ne silar zuwan namu can in lokaci yayi, shi abun alkhairi boye shi ake sai ya tabbata, dan haka ki bar maganar, ki kwantar da hankalin ki alkhairi ne inshaa Allahu," "Kaima ka fada ne kawai, amma kasan ni da kwanciyar hankali ba su hada wajen zama ba har sai munje naji akan me ka tashi wannan tafiya rana tsaka" You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a

Chapter 10 of 17