Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bakin ta, tana dan cizawa, "Ni ba ruwana bakiji nace maki komai ba" "Zama ki fadi gaskiya ne, dan in kk tsaya kallon ruwa wannan bafulatanin sai dai kiji wata ta kamu da son shi, tinda ke kince baki sn shi" "Inji wa ya ce maki ban son shi? Ko ni da ke mukai hakan" Huzaifah bai san sanda ya sake zama dabar a qasan dakin ba, dauke da wani irin farin ciki a ran shi, "Salma kema kina so na kenan?" Ammi ce ta miqe zata fita, dan abun ya fara bata kunya, taga gaba daya sun ma manta tana wajen, Har ta bude baki zatai magana ta ga Ammin zata fita, zumbur ta miqe ta bi bayan ta, "Ina zaki?" "Binki zan ki ban maganin" "Hummm Salma kenan, kin tafi baki fada masa yanda kk son shi ba?" "Ammiiiii" Cike da shagwaba da buga qafa ta fadi hakan, ba qaramin kyau tayi ba, ba Huxaifa bane kadai ya ga kyaun da tai,saqala hannayen ta tayi a wuyan Ammin, tana ci gaba da shagwaba kamar wadda za a goya. "Kin ga saken wuya dan Allah, Salma kina raina nauyin ki, dik sai ki tarawa mutum gajiya" "Ammi har nawa nake ni din" "Biyar kk ke din" Dariya sukai dika, Huzaifah kuwa har yanzu jira yake yaji me Salma zata fada. "Ammi dan Allah ki aramin 'yan matan nan muje shopping" "Ga su nan ko na huta nima, amma kar ku kai magrib, ka ga har yanzu ba a gama jinyar Salma ba" "To Ammi na gode, gurls lets go shoppinggh" "Yehhhhh" Cike da hayaniya suka fita da gudu zuwa dakin su, Khairat da Sumayya na zaune suna hira, "Wa zai je shoppinggggg????" "Niiiiii, dan Allah Adda Salma zani" "Sumayya shirya muje, ai kece ta hannun dama na a gidannan" Da murna sosai suka fara shiryawa, dikkan su shigar dogayen riguna sukai, kowa da kalar ta ta, mayafan su suka yafa kiruf ba mai ganin ko ina a jikin su, daga fuska sai hannaye, da qafa, Salma sai da ta shafe jikin ta da ruwan addu'a, ta shafa mayukan ta da akai addu'a a ciki da garin magani, hadin Habbatussauda da man tafarnuwa, da man za'afaran, koda suka sauka qasa Huzaifah ya gan su da yawa, ran shi bai so ba, yaso ace daga shi sai ita, su sha soyayyar su, amma ba komai, a hakan ma ba za a fasa ba. "Lets go gurls" Cike da murna suka yi ma Mummy sallama, tana zaune tana kallon tashar saudiyyah, ta sakko yanzu akan qin auren, amma har yanzu zuciyar ta bata gama son Ammi ba dari bisa dari, sai ta fara daina jin haushin ta, abu daya sai ya maida ta ruwa, abun kuwa shine hassada, tana jin haushin soyayyar da Jalaluddeen ke nuna ma Ammin. (Wai qarfin hali barawo d sallama, ba mijin ku daya da mutum ba, amma in an masa abu wai ku dinga jin hassada da baqin ciki, bayan kun san masu hassada aikin su wuta ke cinyewa, kuma ba su ci gaba a rayuwar su sam) 1 Bayan sun yi addu'ar fita daga gida, suka shige motar Huzaifah sai shopping mall, Maleek tinda ya dora idon shi kan salma, yunqura da azama dan shigewa jikin ta ya illata ta, amma wani hucin zafin azaba ya mayar da shi baya, ya so yin taurin kai dik da zafin da yake ji ya shige amma inaaa, zafin ba na wasa bane, dan haka ya koma baya, "Ina nan tare da ke, kafin auren ki in ban samu galaba akan ki ba na aje rawani na" Wani babban mall suka je, Huzaifah ya dinga zagawa da su wuri2, musamman wajen kayan kwalliya, da ado na mata, Salma wai kunya take ji, Salwa ke daukar mata abu, tinda dana komai nasu iri daya ne, Daga haka Huzaifah ya gane dik yanda akai ta fara son shi, soyayya ke kawo kunya ai. Hannu ta kai zata dauki chocolate, dan tinda suka shiga tsinke bata dauka ba, sai da taga zaqi, shima hannu ya kai zai dauka, hannun shi da nata na kusa dana juna, ido ya kafe ta da shi, itan ma shi take kallo, sin jima a haka, kafin Khairat ta katse masu kallon da suke ma junan su, "Ni dai in ba zaku dauka ba ku bani waje na dauka" Da hanzari Salma ta juya baya, ta rintse ido, kunyar duniya ta gama shigar ta, yanzu zai ga kamar tana mugun son shi, 'To ai da gaske salma kin fara son Yah huzaifah' Zuciyar ta ke sanar da ita hakan, cikin jin kunya ta fita da gudu ta samu wasu kujeru a wajen ta zauna.........KALAN DANGI...PAGE 28 1K 87 11 by Haermeebraerh Following Mahaifiyar Irfaan ta zo duba shi, ita da Heedayah, yanayin da suka sami jikin shi ya daga hankalin su kwarai d gaske, sun so matuqa su dauke shi su maida shi qasar su dan ayi jinyar shi amma ya qi amincewa, har yanzu jikin shi na zubar da jini, saboda qunar ta shiga jikin shi sosai d sosai, yana nan kwance a turakar shi, matan shi da hadimai na ta hidimta mishi, "Ina Maleek yaje, ya barka a cikin wannan mawuyacin halin Irfaan?" "Mahaifi na ya tafi daukar min fansa, lokacin da ya tafi ko magana ba zan iya ba, da zan iya da na hane shi, amma dik da haka nayi qoqarin hanashi zuwa, na kuma aika masa dan saqo akan ya dawo yaqi dawowa" "Da kai da Maleek kuna da taurin kai sosai, in kuka sanya kan ku abu,ba kujin bari, Allah ya ganar da ku gaskiya," Nan da nan Irfaan ya bata rai, saboda shi ko sunan Allah baya qaunar a kira a inda yake, wannan dalilin ne yasa baya zuwa inda mahaifiyar shi take, in kuwa sun zo lokacin ibadar su yayi ta musulmai gidan su suke tafiya,wanda yake a nesa sosai da nasu, in sun kammala suna buqatar komawa su koma. Suna zaune suna jimanta abinda ya faru suka ga dan aike ya fado yana haki, "Ran yarima Irfaan ya dade, Sarki Maleek ya tinkari yarinyar nan, kuma daga nesa ina hango yanda in ya kusance ta yake jin azaba, amma ya dage yau tinda ta fita sai ya daukar maka fansa" Kafin qiftawar ido Irfaan ya bace, Heedayah da mahaifiyar su sun bi shi. Salma na zaune tana ta murmushi ita daya, Huzaifah ya biyo ta ya tsaya daga nesa yana daukan ta a hotuna, dan ta yi matuqar kyau a wajen kujerun da aka dasa bishiya mai flowers kalar red, wani dattijo ne dauke da leda a hannun shi, sai kyarma yake kamar zai fadi, da sauri Salma ta miqe tare da cewa. "A'uzoobillahi, sannu baba, baka ji ciwo ba dai ko?" Baya Maaleek yayi a kidime saboda wani irin azabar zafi da yaji ya dake shi, Huxaifa da ke nesa da su kadan ya qaraso da sauri shima, a daidai lokacin su Khairat da Salwa suka qaraso suna masifar an barsu da biyan kudi yaji kunya ba zai tsaya ya biya ba zai basu su biya, ganin meke faruwa ne yasa suma suka qarasa. "Subhanallah, Baba baka ji ciwo ba ko? Ina ne motar ka mu kai maka kayan, " Maleek sai zufa yake saboda sunayen Allah da suke ta ambata, ga addu'ar fita daga gida da sukai, ga azkar din safe da sukai, sannan ga alwala dake jikin su, ya rasa yanda zai ya dau fansa, sannan ya rasa yanda zai ya kubuta, dan ba zai yu ya bace haka kawai ba, Cikin shigar da Heedayah ta saba dora hotunan ta a social net ta bayyana ita da mahaifiyar su, Irfaan na tafe, jini na diga, sai qoqarin riqe shi suke yana qi, so yake ya gargadi mahaifin shi, kamar yanda mahaifin shi ke son shi, shima yana matuqar qaunar shi, baya son abinda zai cutar da shi. Salma da ta saba ganin su a da ita kadai ta gane su, cikin wata iriyar razana ta furta, "Lahaula wala quwwata illa billah,A'udhu bi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq, Yah Huzaifa sune, Irfaan ne da Heedayah ban san su waye sauran ba" Ganin ta gama gane su ne ya sa Maleek miqewa daga takwarkwashewar da yayi, yana nishin wahala yana tunkarar ta, Irfaan ne ya je ya rungume shi ya na kuka, yana roqon shi su koma gida,da kyar Maleek ya juya cikin tsananin fushi idanun shi kamar an kwaba yaji a zuba. "Ke bil'adama, kar ki taba zaton hakan a matsayin gazawar mu, mu aljanu bamu mantuwa, kuma bama yafiya, ko shekara dubu zuri'ar ki zatai a doron qasa, indai zuri'ata na raye sai mun dau fansar abinda kikai ma Yarima Irfaan" "Kaii dai kk ganin zaka dau fansa, amma mu mun yafe mata har abada, saboda ba wanda ya aike shi shiga jikin bil'adama, Allah bai halicci mutum da aljan ba sai dan su bauta masa, amma mu jinnu muna zaluntar su saboda basu ganin mu, bayan su basu zalintar mu, qalilan ne daga cikin su suke janmu dan mu yi masu aiki, dan haka ni mahaifiyar shi, ga qanwar shi, mun yafe maki, muna nema masa afuwa da ki yafe masa" You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Salma cikin kuka da tashin hankali baki na rawa ta furta, "Irfaan da farko soyayya ce ta hada mu, na so ka sosai, amma kaci amanar soyayya ta kasancewar ka ba mutum ba,kuma ka sani ba soyayya tsakanin mutum da aljan, na yafe maka dik abinda ka min a baya, indai kayi alqawarin ba zaka sake cutar dani ba,ko zuri'ata," Cikin shaqaqqiyar murya irin ta marasa lfy yake magana, "Na miki alqawari ba zan sake cutar da ke ba, har abada, ina son kaina nima ai, mai zai dawo dani wajen ki in ba qarar kwana ba" Hankalin mutane dik ya fara taruwa akan su, wadannan dawa suke magana, dan ba kowa yake iya ganin su Irfaan ba, sai mutane wanda aljanu suka bude ma ido, ganin idanun mutane ya fara yawa ya sanya Irfaan kama Maleek da kyau suka bace, Heedayah ta juya ta yi ma Salma murmushi na bankwana, suka bace ita da mahaifiyar su, kamar wanda suke jira kuwa, haka suka bazama zuwa mota, ko bayan mota basu tsaya budewa zuba kaya ba,a cinyoyin su suka shiga da su. Koda suka isa gida, suka sanar da me ya faru, kowa mamaki da tsoron Allah ne ya qara kama shi, tabbas ba mai karewa sai Allah, dikkan bawan da cuta ta riske shi ya sani jarrabawa ce daga Allah, kuma baiwa ce, dan ba kowa Allah ke azurtawa da hanyar samun lada ba, wani hanyar samun zunubi ne yake a bude a gare shi. Bangaren su Irfaan kuwa Maleek kulle kan shi yayi a daki, yaqi fita, kuma ya bada sanarwar ba zai fito ba sai ranar da Yarima Irfaan yaji sauqi, a ranar zai yu murabus, ya miqa sarauta wajen Irfaan kamar yanda yayi alqawari. Irfaan yaji dadi da mahaifin shi ya hakura da daukan fansa, saboda yana ma mahaifin nashi soyayya mara misali, ba zai so ya shiga cikin uqubar da yake ciki ba, da ya qara minti daya a jikin Salma a ranar da aka masa ruqya ya sani da mutuwa zai, Maleek kuwa yanda yake da taurin kai, in yayi nasarar shigar salma zata wahala, shima zai wahala, ba zai bari ayi nasara akan shi ba, sai dai ya mutu ana bugawa da shi. Sati biyu bayan haduwar su Salma da Maleek a mall, Ammi zata koma gida da yaran ta, domin fara shirye2n biki da ya qarato, Jadwah tazo da maigidan ta, amma Salma ta yanka mata qaryar bata Abuja, tana qauyen su dake Gombe, kamar kuwa yanda ta sani ne, Jadwah ba zata taba zuwa qauye ba, dan haka tace dama gobe zasu koma, taso in tana nan ne su gaisa, bayan sun yi Sallama, Salwa ta kalli salma tayi murmushi. "Meye?" "To iya masifa karki huce haushin rabuwa da Yah Huzaifah akaina" Dan murmushi Salma tayi ta juya ta kalle shi, ya jingina da jikin qofar fita, hannun shi dauke da akwatin ta, ya turo baki irin na shagwababbu, Daddy na tsaye a bayan shi ya harde hannayen shi yana jiran yaga iya gudun ruwan shi, zai tsaida su ne yana kallon salma ko zai hada cunkoson layi ne? Sun jima tsaye, Ubaihullah yaga alamar baida niyyar matsawa, ya zira hannu ta gefen Daddy ya gasa masa mintsini, cikin wata qara kamar ba namiji ba ya sake akwatin ya dawo wajen qofar yana zaro ido, tare da sosa wajen, dariya kamar ta siqe su khairat, Salma kuwa harda hawaye, gane wanda yayi mintsinin ne ya sa ya kada kai, cikin girmamawa ya fara dan duqa kai, yayi gefe alamar Daddy ya wuce,kada kai kawai Daddy yayi ya ce, "Yaran zamani, kuna da abin mamaki" Dan sosa kan shi yayi tare da cije haqoran shi, ya kashe idanu, "Ka tsaya kallon soyayya mun kusa minti uku bayan ka, wai baka san me ake bama, yaron nan kamar kai kafi kowa soyayya" "Yo in wasu sun fini me yasa basu nunawa?" "Mu fulani ne muna da kunya ba turawa bane mu," Dariya sukai sannan suka fara sanya akwatunan su Salman a bayan mota, Mummy ce ta fito dauke da 'yar qaramar leda guda biyu, da alama komai dake ciki iri daya ne, duba da yanayin su, miqa kowacce tayi hannun surukan nata, tana murmushi, "Ga wannan, a qara a kayan gyaran jikin amare, dik da na san sai dai ku gyara kayan ba dai su gyara ku ba, Allah ya muku albarka,ya kare ku daga dikkan sharri" Cikin jin kunya suka amsa suna mata godiya, Ammi taji dadi sosai na ganin sauyi mabayyani a wajen Mummy, lokaci daya kawai ta sauya, Allah ya sa is for the best. Driver ne ya shiga, Salma zata zauna gaba Huzaifa ya riqe hannun rigar ta, kallon shi tayi, ya kada mata kai, "Ki zauna a baya, bana son ki zauna a gaba, kin san ba kya gani ki kyale" Dariya tayi, "Kar ka damu Sweet love, nayi hankali yanzu, ruwan da ya dake ka ai shine ruwa ko?" Daskarewa Huzaifa yayi, saboda yanda ta furta Sweet love din, da alama ba wanda ya ji sai shi, rufe qofar tayi ta zauna tare da sakar masa da murmushin da yake tabbatar masa da abinda yaji shi ta fada, da sauri ya shiga gida yana murna, kowa binshi yayi da kallo, Ubaidullah na ta bin Salwa da kallo qasa2, dikkan nin su suna jin kunyar manyan dake kewaye da wajen, a hankali ya motsa labban shi ya kalle ta, "I love u" Murmushi tayi ta kauda kan ta, wani irin dadi ne ya ke tsarga zuciyar ta, da kuma zafin rabuwa da shi da zatai, Motar su ce ta fara ja a hankali, ya qura mata ido ko zata dago, Salma na kallon qofar gidan ko Huzaifah xai fito, amma shiru, sama ta kalla wajen dakin shi ta window ta hango shi yana ta hura mata kisses, yana daga mata hannu, a hakali ta sanya hannun ta a baki ta mishi kiss ta hura mishi, Ammi da ta ga me take ta rankwashe ta, "Salma baki da kunya fa" "Ammiiii" "Maza ayi addu'a" "Bismillahi tawakaltu alaLLAHi wala haula wala quwwata illa billah," Ammi ci gaba tayi da tasbihi, Salwa kuwa wayar ta ta lalubo, ta nemo sunan Yah Ubaidu, nan da nan ta fara tapa masa message, ta tura, tare da dake murmushi ta rufe fuskar ta, kamar yana ganin ta, kwantar da kan ta tayi jikin Ammi ta rintse ido, Kowa ya shige ya barshi yana jin haushin Salwa bata kalle shi ba, yaji qarar saqo,kamar ba zai duba ba, ya bude, yana ganin sunan ta a jiki kamar yanda ya rubuta mata. *Hayatee* Cikin sauri ya bude, "Nooree, na fara kewar ka tin dazu, sai naji kamar kar mu tafi, a daura mana aure a barmu tare da junan mu har abada, amma ba damuwa, lokaci ne qalilan zai sake hada mu, ina son ka Yah Ubaidullah, kai kadai, har qarshen numfashina" Ubaidullah ya karanta saqon nan yafi sau biyar, "Yah broth, ya akai ne? Dad is calling u," Da sauri ya boye wayar shi ya fara magana kamar mra gaskiya, "Nnna"am? Toh to muje" Kallon anya ba abinda kk boyewa Huzaifah ya masa, qoqarin amsar wayar Huzaifah ya fara, Ubaidullah ya dinga boyewa tare da zaro masa ido, "Kai kaii kana hauka ne,me za kai da waya ta, ban waya ta, Huzaifah zan saba maka fa, baka da kunya ko," Huzaifah na amsar wayar ya ruga da gudu yana kallon saqon, dariya ya dinga yi, "Ohhh kaga Salwar nan kamar mumina, dan Allah ji kalaman love, chaiii," "This is it, give me back my phone, or...." "Or what?" Da kyar Ubaidullah ya samu Huzaifah ya bashi wayar shi, "Stupid boy, Allah ya sa ma ba a Abuja za a sama maka aiki ba, kana mugun damuna, da a Nigeria kai karatu ban san irin ukun da zaka shigar dani ba yaron nan" "Habaa dan uwa wasa ne fa, muje Dad na son muje gidan da zamu zauna, za a fara gyara da zuba kayayyakin da muke buqata, ni dai sai na nuna mata ta waya ta zabar mana, kai fa," Wani kallo Ubaidullah ya masa sannan suka fara shiga gidan.... Ayi man afuwar shirun da kuka ji kwana biyu, banji dadi bane.KALAN DANGI...PAGE 29 949 67 3 by Haermeebraerh Following Amare sun sha gyara, dan kusan Ammi tattarewa tayi ta koma family house, da yaran dika har Nabeelan Uncle Isa amaryar Yah Sudais din uncle Usman, dik take ma gyaran tare, yaran fulani sun ji kayan gyara irin su kurkum, dilka, dukkhan, da su hadin lalle, su cucumber, su dankalin turawa, da dai sauran su, sai abubuwan ci da sha wanda ya zama fruits kamar inibi, tufa, ayaba, da kankana, ayaba na da matuqar kyau jikin mace, ga mangwaro bata wasa da basu shi, dik da ba lokacin shi bane sai da ta sanya Ubaidullah aika masu da shi, wanda yake shigowa da su daga qasashen larabawa. Ga farfesun naman kaji da su tantabara da naman zabuwa da yake shan kayan qamshi, (kayan yaji ) da wasu itatuwan na mata, wani lokacin bama ta saka wani iccen haka nan take dafa masu ta basu su ci da kayan qamshi. Yara sun yi kyau kamar ka kira sunan su da yaren qasashen waje. Ga Ammi ta hada kai da Haule suna koyar da su grike2n gida dana waje, dan samun matsayi a wajen mazan su, Nabeelah bata iya lafazi mai dadi ba, yaba magana take dik yanda taga dama, amma zama da su ba wanda ya tsangwame ta da kan ta ta fara gyarawa, saboda abun sai ya mata nauyi yanda take watso magana ba taunawa. Qarar motar Abba ce ta sanya Salma tashi da sauri ta bude qofa tana dariya, sai da ya fito daga motar ya baro harabar gidan ta isa da sauri ta amshi jakar shi tana masa sannu, "Salman Abba ya dai? Naga kina ta murna da washe baki," "Abba kullum inna gan ka sai indinga jin farin ciki, Abba bana son nai aure dan kar na daina ganin ka kullum," Dakatawa yayi, ya kalle ta, dan shi har yanzu bai gama yarda aljanu sun bar ta ba, "Salma fadan gaskiya, ko dai wani aljanin ne baya son ki aure?" Dariya tayi sosai, sannan ta bata rai ta fara zaro ido tana lanqwasa hannaye tare da juya idanu, tini ya amshe jakar shi ya riqe ta, yana fadin, "Ya salam, dama na san har yanzu ba su sake ta ba dika, bari na kira malam Hassan" Cike da dariya ta miqe har duqawa take, "Abba dan Allah ni kar ka kira min mutumin nan, wallahi tsokanar ka nake, Abba kaga idon ka kuwa?" Wayar ta tazaro ta tsaya kusa da shi bakin shi bude ya kalli wayar ta basu kyassss Ta kwashe da dariya, ta amshe jakar ta yi ciki, tsaye yayi yana jinjina shaqiyancin salma, ta shammace shi, amma yaji dadin yanda ta sake kamar ba ita ba, yanzu kowa na ta ne, yana shiga ya tarar har ta gama bada labarin abinda ya faru, sai dariya ake, ga hoton da ta masu ta kanne ido daya shi kuma ya zaro nashi, Salwa ce ta je wajen shi tana mai sannu da zuwa tana dariya shima dariyar ya yi ya zauna, Nabeelah na ta kallon su cike da sha'awa Uncle Isa kamar wani zaki, ina suka isa ya masu wasa haka, tabb zasu ci uwasu dik wanda ya kuskura ma ya mai hoto. "Ammi kina ganin su ko? Ni dai gaskiya wannan tsarin bai min ba, an barni kamar maraya, kin tare wajen yaran ki, baki da lokaci na sai nasu, gaskiya ni dai a sauya wannan tsarin," Miqa masa juice din hannun ta tayi mai sanyi daidai misali, ya yi bismillah ya kurba sau daya ya ajiye, zama tayi a qasa dan aikin tane cire masa takalmi da sucks tin da can, ko yaran zasuyi baya so, murmushi tayi ta ce, "Kar ka damu, yanzu is there time, kwana nawa ne ganin su ma zai mana wahala, (sai ta sassauta murya sosai) zai rage daga ni sai kai," Tare da lumshe idon ta guda daya cikin wani irin salo, ta matsa qafar shi da ta gama cirewa safa guda daya, ta kai bakin ta tai kissing a hankali, murmushi yayi ya maida kan shi ya jingina da kujerar, shiru tayi ta qarasa me take, Nabeelaah na kallon ikon Allah, lallai dole Uncle jalal yaji da Ammi, tinda take bata taba ganin Maman su ta damu ma da Baban su ba balle ta bashi kulawa haka, daga yawan fada zai kushe juna. You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Can Abuja kuwa, Uncle Ibraheem ya samawa Huzaifa aiki a ma'aikatar da yake, tare da albashi mai tsoka, an bari zai fara

Chapter 14 of 17