Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani Malami da Malam Hussain ya hada su, wato Hassan din shi, Hassan din shi ba qaramin mai ilimin sanin yanda ake fidda aljanu bane, dan haka da ya ji ya kasa, sai ya masa magana, ya hada shi da Jalaluddeen, dan haka sun gama shirya yanda zasuyi tafiyar a goben maganar hatsarin Huzaifah ta riske su. Sameer ne ya kawo Salwa asibitin, dauke suke da basket wanda ta zubo flask din abinci, da kuma abubuwan sha, koda ta je ta sha mamakin irin kallon da Mummy ke bin ta da shi, gaishe ta tayi, ta ga ta amsa cikin sakin fuska, tare da furta mata kalmar godiya. Qana nan carpet suka shimfida masu a qasan dakin da Huzaifan yake, nan suka zauna suka ci abincin, lokaci zuwa lokaci suna duba Huzaifan ko ya tashi. Har akai isha'i bai farka ba, nan Ubaidullah ya umarci Sameer da ya maida su Mummy gida shi zai kwana a wajen Huzaifan, da kyar Mummy ta amince ta bi Sameer. Sai sha biyu saura Huzaifah ya farka, nan da nan kuwa Ubaidullah ya kira likita aka duba shi, sannan ya ce zai iya bashi abinci yanzu, hada masa tea mai kauri da zafi ya yi, sannan y dakko masa kwanon da ake wanke baki, ya wanke bakin shi, kafin ya fara bashi tea din, bayan ya shanye tea ne zai zuba masa abinci ya ce ya qoshi. "Ka ci ka qoshi, akwai albishir mai faranta rai,ba dan khairat na son sanar da kai ba da na riga ta," Murmushi Huzaifah ya dan yi, amma cikin ran shi yana ayyana wanne irin albishir ne da ya wuce yaji Mummy ta daina qin auren su? Shine kadai zai faranta masa......... KALAN DANGI....PAGE 26 876 94 6 by Haermeebraerh Following Share Zuwan malam Hassan da Abba ya kawo sauqi a lamarin Salma, dan kuwa a ranar har tashi tayi tayi sallah, Abba da ya ga da sauqi akan yanda Ammi ke vashi labari sai ya wuce asibiti wajen Huzaifah, dan ganin yanayin jikin shi, tinda Malam Hassan ya je ya bada wani hayaqin magani a yi wa Salman, kuma ya bada na shafawa a shafa mata, ta samu har magana tana dan yi. A yau ne za a fara yi mata ruqya sosai, dan haka Salma tin asuba gaban ta ke faduwa, ji take kamar ta gudu ta bar gidan, hankalin ta ya tashi sosai, tsabar shiga damuwa ko kukan ma ta kasa, a bangaren Irfaan kuwa ya san waye Malam Hassan, domin a jinsin bil'adama da Aljanu dole akwai sananne wanda in sun shahara ake sanin su, to haka Malam Hassan ya shahara a wajen aljanu, saboda barna da yake ma mugayen cikin su da ke cutar da bil'adama. Tayo alwala a qarqashin kulawar Ammi, inda ya umarci dika kowa yayi alwala, wasu daga mutan gidan sun yi makaranta, wasu sunje asibiti, wasu kuma ba makarantar dan haka suna gida, Khairat na cikin 'yan zuwa asibiti, saboda tsoron ta ba zai barta zama gida ba. Da sallama Abba da Malam din suka shiga dakin Salma na daga ido ta kalle shi ta fara qoqarin guduwa, tin a jiyan Irfaan ya so guduwa amma Malam din ya daure shi a jikin Salman, Maleek ya yi iya qoqarin shi saboda magajin shi kar ya halaka amma sun kasa kunce Irfaan. Dan haka yanzu ga Malam ga Irfaan, ga kuma Salma a gefe. Da sallama malam ya fara yi ma Salma magana, tana ji tai shiru, malam yace, "Ba da kai nake sallama ba, da Salma nake, saboda kai baka san ma'anar sallama ba," Salma ce ta bude baki ta amsa Sallamar malam, sannan ta fara roqon shi akan ya yi hakuri ya kyale su,tana son Irfaan "Ba ke kk son shi ba, shi ke son ki, shi yasa kk ji kamar kina son shi, shine ya sanya kk jin soyayyar shi ta hanyar sihiri irin nasu, amma ba wai son Allah kk masa ba, yanzu ke salma kina musulma, diyar musulmai, kuma jikar musulmai me zakiyi da aljani? Aljanin ma baqin aljani mugu? Ko baki ga yanda ya nesanta ki da Allah ba, in baki sa a ran ki kina son rabuwa da shi ba, maganin da za ai ta maki a banza ne, ko kina son ki qare rayuwar ki ba aure? Ko ko kina son ki qare rayuwar ki ba ki bautawa Allah, ki zama daga cikn kafurai Allah ya azabtar dake? Ki zabi daya, dik wanda kk zaba da shi zan aiki ba ruwana" Shiru tayi, cikin bacin rai Malam yace, "Ina maka gargadi ka bari nayi magana da mara lafiya da nazo domin ta, zan dawo kan ka" Salma ce cikin kuka ta ke kada kai, alamar bata son abubuwan da aka lissafa su kasance a kan ta, "Bana son Allah yayi fushi da ni,ni kai na bana son rashin sallah da nake yi amma innaje zan yi sallah sai naji jikina ya mutu,ko naji bacci,ko kuma na dinga hango Irfaan, daga nan sai ya fara min soyayya har sai lokacin sallah ya fita amma kuma ina dungurawa kamar ina sallah saboda kar a ga bana yi" Ammi ce ta kama baki tana salati, ashe dama kenan ba sallah take ba, "Ya salam, yanzu dan Allah to me ne ne amfanin dungurawar da kk? Ke a jikin ki bakijin gajiyar dungurawar ba tare da kina gabatar da ibadar ba? Dungurawar ba ta maki wahala ba sai yin ibadar? To inda zaki gane shi Irfaan ba masoyin ki bane so yake ya kai ki wuta, yanda ya kafurce ma Allah kema ki kafurce ma Allah, a yanzu sai kin amince kin yarda baki son Irfaan kina son rabuwa da shi sannan wannan ruqya zatai tasiri akan shi, kin amince?" Da sauri ta daga kai, ba bata lokaci kuwa Malam ya zauna a qasa ya ce Abba ya xauna ya riqe Salman, addu'a ya fara akan Allah ya tsare shi daga cutarwar aljanu, akan shi, da ahalin shi, da dukiyar shi, da mutanen gidan baki daya, sannan ya fara rera karatun qur'ani cikin ayoyi na ruqya da suka inganta a islam, tare da debo wani ruwan magani wanda yaji ayoyin Allah, yana yi yana watsa mata, ihu ta fara dan kuwa Salma ji tayi kamar ana zagwanye fatar jikin ta, kamar zata suma. You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Haka suka dinga yi sai da sukai wajen awa biyu sannan Malam yace a sake ta a huta, "Dan Allah ka tsaya kaji malam, ni fa ba laifi na bane, ita ta ganni ta ce tana so na, tinda ta ce tana so na nima naji ina son ta shine na aure ta" "Kafin ta ce tana son ka a ina kuka fara haduwa? Domin na san hali irin naku,mutum bai san da zaman ku ba, kuce zaku gwada shi ku ga ko mutumin kirki ne, sai kace ku kuka halicci mutum" "Zan fada maka gaskiya, amma dan Allah ka barni na koma wajen iyali na da mahaifa na" "Iyalin na ka da dik rabi matan bil'adama.ne. da ka sace iyayen su na nan na nema? Kaiii ka san na san ka ko? Kuma mahaifiyar ka aljanar kirki ce, amma kai da mahaifin ka aljanun banza ne,ka ban labari kar ka min qarya, in ka min qarya zaka wahala" "To na maka alqawarin fadin gaskiya ta, shekarar da ta wuce ne, na fito ina shawagi sai na hadu da Salma da wata qawar ta Jadwa sai Salwa, a gidan mahaifin Jadwa wanda muke yi wa hidima irin ta aljanu da mutane, muna masa sihirin da yake maida jinin mutane dukiya,a ranar da suka isa gidan Salma ta cire mayafin da suka lullube kan su, daga zuwan ta gidan, gashin ta mai tsaho da kyau ya bayyana, ga qirjin ta mai kyau ya bayyana, kawai sai naji sha'awar ta ta kama ni, sun kai dare a gidan. Sai da zasu tafi ne na fito a siffar mutane a tinani na zasu tausaya min, saboda ganin yanayin talauci a jiki na, daga nan sai mu fara qawance da ita har ta so ni a matsayin da naje mata da shi, na aure ta, sai na kula ita halayyarta daban da ta Salwa, tana da girman kai, ina son hakan, tana da qin talaka, ina son hakan, tana da KALAN DANGI sai masu kudi da aji da dukiya take bi, ina son hakan, sannan tana da wulaqanta dangin ta ta girmama dangin wasu, ina son hakan,dan haka ko da Salwa ta nuna tausayawar ta a kaina, ita zagi na tayi saboda ta ganni talaka mai neman taimako. Tin daga ranar na bude account a Instagram, na samu suffar bil'adama kyakkyawar siffa na samu muka dau hoto da 'yan uwa na, na dora a IG,Salma kuwa akai sa'a ta gani, kyau na da alamar hutun dake jikina shi ya ja ra'ayin ta, daga nan muka fara gaisawa, da soyayya mai qarfi da na sanya mata ta hanyar sihiri, Lokacin da Salma zasu koma Gombe, na bata dama dan ta daina halin da take na tsanar talaka, amma sai naga halin qin talaka ko wane ne ko da tsoho ne kuwa a jikin ta yake, dan yanda ta sake fadan baqaqen maganganu akai na, ya harzuqa ni, nan take na shiga jikin ta, na ci gaba da gana mata azaba da soyayya ta da kuma wahal da jikin ta, ta hanyar sanya mata ciwuka da qin yin ibada, Na fada maka komai tsakani na da Allah, ka ga har zalunta ta akai, aka kashe min d'an da muka samu da Salman, bayan ban taba haihuwa ba, qanin ka shine ya zalunce ni," "Auuu har kana da bakin ka kira an zalunce ka? Kai zalunci nawa ka aikata? Ka raba ta da Allah, ka raba ta da kowa, gashi za ai mata aure ka toshe zuciyar ta kar ta so dan uwan ta, bata ganin kowa sai kai, zan baka zabi, na san halin ka na taurin kai, da naso zan iya karanta ayar Allah, Allah ya qone ka, amma ba zan zalunce ka ba ba tare a na bk zabi ba, ka fita ta dadin rai, ko kuma nahada ka da Allah ya mana maganin ka" Shiru yayi sai gurnanin azabar da aka masa yake, jikin shi dik ya qone, jini na zuba, Shirun da yayi na sama da minti ashirin ya tabbatar ma da Malam me yake nufi, dan haka ya so ma karatu tare da kunto jakar shi ya dakko wani magani liquid a roba, Irfaan na arba da maganin nan ya fara tsalle ya na bada hakuri, Salma kawai suke ganin tana ihu tana tsalle, dik qoqarin su Abba wajen riqe ta abun ya gagara, dadin ta kawai an rufe dakin, dan Ammi ma waje aka ce taje. "Na shiga uku, Ammi naaa, Ammi kar ki bari su kashe ni, Salman ki ce, ba Irfaan bane," Ammi da ke waje tausayi irin n d'a da uwa, kuka take sosai tana jin kamar taje ta hana, Salwa ce ta dafa ta tana bata hakuri, "Ammi ba Salma bace, so yake ki katse su a bar abinda ake masa ya samu ya gudu" "Allah ya shine maki Salwa, muguwa, da na zaci kina da tausayi, ashe muguwa ce ke, shine kk so a kashe ni,Allah ya tsine maki," "To kai ka san Allah ne?Allah ba zai tsine mata ba sai dai ya mata albarka" cewar Abba. Lokacin Sallah ya yi, an fara kiran Sallahr azahar, wani qayataccen murmushi Salman ta sake, tinda Malam ya kula shima sai ya sakar mata murmushin, dan ya gano murmushin me take, Ammi na gama bin kiran sallah tai addu'ar da ake bayan gama jin kiran sallah, sannan tai salatin annabi, ta fara nemar wa Salman sauqi da kuma sauran addu'o'i da ta saba. Maganin Malam Hassan ya diba a hannun shi ya shafa ma salman a fuska ya watsa mata a qirjin ta da qafafun ta, ya ba Abba ya bude bayan ta aka shafa mata, wata iriyar qara da shidewa take yi, ana shafa mata Malam na ruqya, ihun salma dik mai imani sai ya koka in ya jiyo shi, saboda ihu ne na wanda yake cikin azaba da halaka. Ana haka ta dinga miqewa, tana wata jijjiga, malam na sake shafa mata maganin tare da ci gaba da addu'a, diba yayi a sirinji ya faki idon ta ya watsa mata a hanci, nan take kuwa ta buga qatuwar atishawa, ta zube a wajen, kamar matacciya, "Salma....Salmaa... malam me ya faru,Salma fa kamar bata da rai a jikin ta," Jin haka ne ya sa Ammi ta dinga buga qofar dakin a kidime, Salwa na biye da ita, kuka suke sosai, Mala neya bude .asu qofar suka shiga, ganin Salma sukai a kwance shame2, Abba idan shi ya rufe da hawayen da ya cika mashi su, kunnen shi har wata qara yake ji kamar an kunna gidan redio, shuuuuuuu Ammi sai jijjiga ta take tana kiran sunan ta, Malam bai daina karatu ba kuma bai kula su ba, Salma kuwa na nan kwance ko d rai, ko ba rai? Nima dai ban sani ba yar kallo ce,wataqila sai gobe zamu san a wanne hali take ciki Wayyyooo Salma karki tafi ki bar su Abbaaaa, ga Huzaifah masoyin gaskiya😢😢😢KALAN DANGI.....PAGE 27 953 79 8 by Haermeebraerh Following "Zata farka ku daina damun kan ku haka, Alhaji aje ta kan gado, dan na san dik sanda ta farfado jikin ta zai mata ciwo sosai" Cikin azama Abba ya dauke ta ya aje ta saman gadon dake dakin, Salwa kuwa waje taje ta debo ruwa zata yayyafa mata, Malam Hassan ya miqa mata na addu'ar da yake ta amfani da shi, "Shafa mata wannan" Cikin ikon Allah ana shafa mata ta bude ido a hankali, tare da sauke ajiyar zuciya mai qarfi, daya bayan daya take bin su d kallo, har sai da ta gama zagaye su, sannan ta maida kan ta akan Ammi, wadda ta ci kuka ta gode Allah, sai hamdala take bugawa ganin Salma a raye. Wasu hawaye ne masu zafin gaske ke zubar ma Salma, jikin ta dik inda ta motsa zafi yake mata musamman haqarqarin ta, qoqarin tashi tayi ta zauna, amma ta kasa, Abba ne ya taimaka mata ta zauna, tare da jingina mata pillow, ruwan addu'ar still aka bata ta sha, sai da ta qoshi, Malam Hassan ne ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana da Salma. "Malama Salma sannu ko, ya kk ji yanzu?" Da kyar murya qasa2 take magana, "Jiki na ciwo yake, kamar an dake ni, ko an matse min jiki na" "Sannu Allah ya baki lfy d dikkan musulmi, kin san dai me ya same ki ko?" Daga kai tayi, alamar Eh. "Da kyau, ki sani a dalilin wulaqanta talaka, da son sai kinyi hulda da mutanen social media wadan da baki sani ba, sama da 'yan uwan ki, da dangin ki, shine hakan ta same ki, dan sarkin aljanu na wannan yankin naku ya aure ki, mai suna Irfaan Maleek,ki sani, komai na tafiya da hali da dabi'a ne, ya same ki a wacce take da son wulaqanta na qasa da ita, da KALAN DANGI, tare da son masu arziqi koda baki san su ba, shi yasa ya qara maki wannan halin, kuma ya sanya kk son shi sosai ta hanyar sihiri, amma yanzu kina jin son shi? Kar ki boye man dan zan gane," "Ni bana son shi, ko da ma ban san ya akai na fara son shi ba" "Masha Allah, inshaa Allahu indai kin riqe dokokin da zan sanar dake yanzu zaki rabu da jinnu har abada, kinga dai na farko ki kama Allah, ki ji tsoron Allah a dik inda kk, hotunan ki marasa kyau da mijin ki ko maharramin ki ne kawai zai gani da kk sanya a social media dik ki goge,domin waje ne wanda har aljanu na hawa, sannan ki dage da azkar kina yin lahaula wala quwwala illa billah ba adadi a rana, da hasbunallahu wa ni'imal wakeel, ki yawaita yin su ba iyaka, kina azkar na safe da maraice, sannan qur'ani ya zama abin karantawar ki a koda yaushe, ya zama abun sauraron ki, da dare in zaki kwanta kinji wannan ruqyar da naji an samaki randa nazo, ki na kunnata ki sata a repeat, ki tabbatar kina da caji sosai ko ki saka karatu daga baqara ki baccin ki, karkina wasa da addu'ar bacci, Sannan kina girmama na gaba da ke ko kin san su ko ba ki san su ba, karki wulaqanta kowa dan baki san da wa kk magana ba, wataqila wanda zaki wulaqanta ya taimake ki a inda baki sani ba a rayuwar ki, sannan ga magunguna zan bari da addu'ar da zaki na yi a ruwan shan ki, ga hayaqi, har hanyar da Irfaan ya maki a jikin ki ya shiga ta kulle,in ba haka ba wasu zasu iya shigar ki,tunda sun ga hanya" "Na gode wa Allah daya bani lfy, na gode maka malam, inshaa Allahu zan gyara dikkan abinda nake yi mara kyau," Haka malam ya tattara suka je sukai sallah, yaci abinci ya koma Gombe a ranar, Abba kuwa da yamma daukan su yayi a mota har asibiti wajen duba Huzaifah, koda suka isa Huzaifah gani yayi kamar Salma ta fada, kafe ta yyi da ido, yana zana kyaun fuskar ta a zuciyar shi, fuskar shi dauke da qayataccen murmushi, kallo daya ta masa ta yi murmushi itama ta maida kan ta qasa, tare da wasa da hannun doguwar rigar ta. You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Sun jima sosai a asibitin kafin su koma gida. ********************* Irfaan jina jina ya koma fada, yana zuwa ya zube yaraf a turakar shi, matar shi da ke kwance tana hutawa a dakin ce ta gan shi, sam bata gane waye ba da fari, tsabar qonewa da yayi, ihu ta sanya, cikin abinda bai fi qiftawar ido ba Maleek da sauran mutanen gidan suka bayyana a dakin, ganin halin da Irfaan ke ciki ya tsorata kowa da kowa, rasa ta ina ma za a kama shi a daga sukai, saboda ko ina rauni ne, quna ce da ta shiga cikin jikin shi ainun, Maleek idanun shi sun kada sunyi jawur, saboda bacin rai, wani irin baqin hayaqi ke fita a bakin shi d hancin shi, kowa ya tsorata, dan haka suka durqusa akan guiwowin su, su kai shiru, numfashin Irfaan ke fita kadan kadan. "Na rantse da d'ana Irfaan, sai na ga bayan zuri'ar wannan bil'adama da ya maida min magaji haka kamar matacce,in ban ga bayan su ba nayi alqawarin barin gadon mulki na Irfaan ya hau," Ba wanda ya san ta inda ya bace, ya bar dakin zuwa gidan uncle Ibraheem, su kuwa matan Irfaan kowacce aljana tana qoqari wajen bashi gudunmawa da qarfin da Allah ya hore mata, matan bil'adama da ya sata ya kai can ya aje kuwa, sai kuka suke, saboda dik ya sihirce zuqatan su da tsananin soyayyar shi. ********************** Ko TV a gidan ba wanda ya kunna, in ko an kunna sai dai a kunna karatun qur'ani, dan haka Maleek da ya iso rasa ta ina zai samu ya shiga gidan yayi, ya sha qoqarin shiga ta jikin wasu halittun kamar su kyankyaso, qadangaru, ko beraye, hatta da quda sai da ya qoqarta shigewa gidan ta jikin shi amma ya gagara. A haka ya kwana a waje, yana jiran dama, yayi alqawarin ko da yaushe ne sai ya shiga gidan kafin nan kafin auren Salma ya wulaqanta ta, ya mata azabar da basu taba yi wa wani dan adam ba. ************************ An sallami huzaifah ya dawo gida cikin qoshin lfy, ba inda ke masa ciwo yanzu sai ciwon son Salma, wadda ya kasa gane komai game da ita,tana son shi ko bata son shi, a bangaren Slama kuwa, tin da hankalin ta ya dawo jikin ta, take qoqarin sanya son Huzaifan a ran ta, amma shiru, sai dai bata qin shi, sannan tana jin ko a haka zata iya auren shi, su zauna tare, ko ba komai shi din yana son ta. Zaune yake a dakin shi, yana nazarin ta yanda zai samu Salma ta fara son shi,shawarar abinda zai yi ce ta fado masa, da sauri ya miqe, ya shiga wanka, ya yo alwala, ya yi sallar la'asar, sannan ya sake shiryawa, turaruka masu sanyin qamshi da dadi irin na maza ya sanya, ga wani glass mai daukan hankalin mai kalla daya maqala, gemun nan nashi ya sha gyara yana ta daukan ido, kyau iya kyau Huzaifah ya yi shi, kyakkyawan bafulatani ya sha shadda kun san sai dai kawai ace masha Allah😃 Dakin da Ammi ke ciki yaje ya kwankwasa, Salma ce ke shan magani tana ta shagwaba, a jikin Ammin, Salwa na tsokanar ta da qatuwar banza, bayan sun masa izinin shiga ne, ya samu waje ya zauna, Salma kuwa tashi tayi tana kame2 ta koma gefe, dariya sosai Salwa ke yi, "Da ki ci gaba da shagwabar mana, qatuwar kawai" "Nawa Salman take da zaki kirata qatuwa? Tayi shagwabar ta yanda taso, ai ita ce qarama ko?" "Ehhh kace wani abu Yah Huzaifah, abun son kai ne kawai na gano,...to ba wannan ba, irin wannan gayu haka, ko dai zance zaka je ne?" Cikin faduwar gaba ya kalle ta kamar wadda tayi sabo, ina shi ina zuwa zance, ya dafe qirji tare da zaro ido waje, ba Salwa ba hatta Ammi sai da ta dara, Salma kuwa harara ta bankawa Salwa, "Ohhhhh sweetheart meye na harara ta, ina nufin zance yazo wajen ki? Ko kuwa kin zata a wani wajen nake nufi zashi zancen," Murmushi Salman tayi tare da danna yatsanta manuni a

Chapter 13 of 17