cikin amincin shi"
"Yauwaa Ammi na, su daddawar tsakar gida ai ta kai kawo tsakanin daki da kitchen"
"Gwanda ni aikin lada nake ke fa sai yawon KALAN DANGI yawon cusa kai ba kwarjini,"
"Ai kema sanin kan ki ne nafi qarfin ace ina cusa kai banda kwarjini, ki duba da kyau yarinya ko baki gani bane? Ido ba lfy ne?"
"Dalla matsa mara abin yi kawai"
Dariya Salma ta sanya tabi Salwa tana tura mata haushi.
Salwa banza tai da ita, ta dau qur'anin ta dan yin abinda ta qudurta.
Ita kuwa shirya wa tayi a cikin kayan da bata taba zatan ma zata sa wai dan bikin wata Heedaya ba, kyau iya kyau tayi shi,
Kamar yanda suka saba shiga, doguwar riga ce milk an mata ado da brown, ta dan kama ta daga sama, daga nan ta dinga budewa har qasa, fadin ta ya sa tai layi layi daga qasa, ta yafe kan ta da brown mayafi, mai stones sosai, rigar ma taji stones, brown, lipstick kawai ta shafa a lips din ta masu danqo da riqe vaki, sai idon ta da ya sha kwalli ta masa layi mai kyau, girar ta ta taje ta ta kwantar, Salwa tsaida karatun ta tai tana kallon Salma, cikin dariya da tsokana kuwa ta ce mata
"Ammata ya ne, kin ga me cusa kai ba kwarjini zata ta make amaryar daga kujerar ta ko? Ya kk ga wankan zuma bama na sukari ba"
Rufe bakin ta da ya bude tayi, ta dora idon ta kan ayar da take karantawa, tai banza da Salma, sai da Salma zata fita ta sake bude ido ta kalle ta, purse din ta da takalmin ta milk ne masu stones a jiki an watsa stones brown a jiki.
Dakin Ammi ta leqa, Ammi ta kalle ta daga sama har qasa, tace
"Masha Allah, barakallah, Allah na gode maka da ka min kyauta kamar wannan, Allah ya kiyaye,kar ki manta kiyi addu'a kan ki fita, ko dai Mansur ya kai ki? A wannan gayun ai an hau mota ko?"
"Karrr ki damu Ammi, Masur banda surutu da gadi me ya iya, ko ke da kk bari ya ke tuqa ku ina ganin kasadar ku sai na dawo, bana son na kai yamma"
Dariya Ammin tayi, ta na jinjina rashin ji irin na Salma, tare sa fatan shiriya a garesu dika.
Adaidaita sahu ta samu ta shige, tace y dauke ta ita daya zata biya, waya ta zaro ta kira Heedaya, ta mata kwatance da kyau, ta ba mai adadaita yaji wajen, shiru yayi, dan ya san nisan wajen.
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Tafe suke taga shiru kamar za a bar Gombe ba a isa ba, sai da suka yi tafiyar kusan awa guda kafin su isa, katafaren gida ne kamar masarauta, jikin ta ne ya bada wani irin yarr, sauka tayi ta sallame shi,
Hayaniya kawai take ji amma ba alamar kowa a wajen, ganin girman gidan da kuma kyaun shi yasa ta ayyana maybe baqin na ciki.
Da yanga ta qarasa gate din ta dau wayar ta ta danna kiran Heedayah, nan da nn kuwa ta hau murna tace bari a bude mata ta shiga.
Babban gate din ne ya fara ja da kan shi, ya bude, mamakin irin haduwar gidan su heedayah take, lallai ta debo gidan masu akwai da ya wuce su Jadwa,
Mutane ta dinga gani jefi2 masu matuqar kyau, wasu 'yan mata ne suka jere gefe da gefe, da dan kwando a hannun su, da flower a ciki kalar ja, tana taka qafar ta ta gaban su suka fara zuba mata flowers suna duqar sa kawunan su, wasu mata ta gani jere masu kyau suma daidai misali, suna da yawa dan sun haura dari da ganin su bikin suka zo suma, kowaccen su da harara take bin ta, a ran ta dariya tayi,
'Dibe su guzumomi da su, kishin ganin gayu na ya sa su harare2'
Kama baki ta danyi ta sosa hanci kar a ga dariyar ta.
Wani katafaren parlour ta shiga, ya sha ado irin na sarauta, nan da nan kan ta taji ya fara juya mata, sakamakon son tinawa da in da ta ga wajen, bata gama tinani ba ta ga matashin ya fito cikin shiga mai kala daya da ta ta, baki ta bude tana son yin magana ta dayan bngaren wani dattijo kyakkyawa shima ya fito tare da masu take masa baya, da masu mashi firfita da maficin da aka yi shi da gashin dawisu.
Nan take ta sulale a wajen ta fadi, da sauri matashin ya isa gare ta kamar qiftawar ido kanta fada jikin shi, hura mata iskar bakin shi yayi, nan da nan ta bude ido.
Cikin in ina ta ke nuna shi da yatsa tana kiran sunan shi.
"Iiiiirrrfaaaannn, Maaaalleeekk?"
Kada mata kai yayi da wani irin murmushin da ya jefa zuciyar ta a wani irin halin sabuwar so d qaunar shi.
Tafi suka ji ta bayan su, Irfaan ya juya yana murmushi, dan kuwa ya san wace ce mai tafawar.
Miqa mata hannu yayi ta miqe tsaye, ta na bin kowa da kallo.
"Heedayah? Me kk yi anan, a gidan su Irfaan?"
"Subhanallah"
"Keeeeeee"
Gaba daya idanun mutanen wajen ne yayi jawur, fuskokin su ta yi jawur, suka zuba mata ido, da wani mummunan kallon da ya sa ta kwalla qara ta durqusa a wajen, ta ji tsoro ainun, a cikin murya mai hadin baki taji ana magana,
"Ahir din ki da fadin wannan kalmar a cikin gidannan"
Kada kai ta dinga yi hawaye na zuba a idon ta da sauri, ganin ta razana ne yasa fuskokin su suka dawo daidai, Irfaan ya rungume ta, yana lallashin ta.
Lafewa kuwa tai jikin shi sosai.
Maleek ne ya bada izinin a fara daura auren Irfaan da Salma.
1
Nan da nan kuwa wasu takwarkwasassun tsoffi suka bayyana suka hau wani yare suna yarfa masu wani ruwa a kasko ruwan baqiqqirin a zaton Salma ko zai maqale a kayan ta kalar, ko mai babu na alamar ya bata mata kaya.
Ana gamawa tsoffin nan suka bace, tafi aka dauka a wajen, Maleek dake zaune a kujerar Sarauta, kowa na duqe a qasa, ya fara magana.
"Salma, a yanzu kin zama godiyar mu, kuma mata a wajen da na babba, Yarima Irfaan, da ga yau ke ce sarauniyar shi, har sai in mun ga kema baki haihu ba kamar sauran matan shi sai mu kwace sarautar Sarauniya da muka baki, ya nemo wata matar da tai makon Heedaya, a sake masu aure"
"Na amince sannan ina godiya da wannan karamci,"
Damqe bakin ta tayi, saboda bata san sanda take maganar ba, sai ji tayi kawai tana fita.
Hawaye ne ke zuba a idon ta sosai.
1
Sallamar su Maleek yayi bayan mutane da dama sun miqa godiyar su wajen sarkin nasu, harda matan Irfaan sai da sukai godiya b dan sun so ba.
Salma gani take kamar gidan na qaruwa ne da girma, dan yanda tagan shi awaje a ciki ya fi girma da kyau.
Kowacce mace a cikin su tana da bangaren ta kuma katafare.
Dik yawan matan gidan kowana da mahalli a gidan, yanda ta kula ita kadai ce mutum a gidan.
Kuka take kamar zata shide, 'yan mata na take msu baya suna zuba masu flowers.
Sai da suka kai bakin qofar wani waje babba,Irfaan ya tsaya, Salma na mnne a jikin shi, ya daga ma su hannu,suka juya, wasu suka tsaya a bakin qofa, kansu duqe, hannyen su riqe a bayn su.
Qofar mai fadi ce ta sha ado da jajayen wasu abubuwa masu kyalli, suna shiga Salma ta saki siririyar qara, wannan dakin take gani a mafarkin ta.
Murmushi ya mata, ya jata saman cinyar shi bayan ya zauna a kan wata shimfida mai laushin gaske,
Mayafin ta ya shiga cirewa a lokaci daya kuma yana sunbatar kuncin ta, jikin ta dik ya sake, tsananin so da qaunar shi na narkar da ita a hannayen shi.
Bata san ya akai ba Irfaan ya gama cire mata dik wani kaya dake jikin ta, romancing din ta yake kamar yanda suke yi a mafarki, wannan yafi zama gaske, jin komai take yana faruwa da gasken gaske, Irfaan bai samu daga Salma ba sai da ya samu gamsuwa da ita, kukan da tai ba shi da iyaka, Ammin ta da Abban ta da Salwan ta take hangowa, in suka san ta aikata zina dik da ance an masu aure ita a wajen ta zina ne, dan kuwa wannan ba aure ba ne a wajen ta, aure da aljani? Dan koda ba su tabbatar mata da su din ba bil'adama bane ta san ba mutane bane,
Irfaan wani irin son Salma ke sake shigar shi, lallai in haka bil'adama suke mazan su na morewa, basu da hadi da kowacce halitta.
Salma ba ta bar gidan nan ba sai da tai sati biyu.
*************
A bangaren su Ammi kuwa, tinda Salma ta fita ta bar gidan taji gaban ta na wani irin bugu,zuciyar ta kamar zata fito a qirjin ta, ko dankwali babu a kan ta ta falla haravar gidan a guje dan ta kira Salma tace ba zata je ba.
Salwa da gudu ta bi ta dauke da hijabi a hannun ta, jikin Ammi na matuqar rawa da ta bude gate taga Salma ta shilla ita da mai a daidaita, kwala mata kira ta hau yi idanun ta na zubar sa hawaye, Salma ba su ji ta ba, Salwa ce ta sanya mata hijabi, Mansur na rakube yana ganin ikon Allah.
"Hajiya fada kk mata ta bar gidan ne? Naga ta fice cikin nishadi ba wata matsla,"
"Ko mai zan fada maku ba zaku gane ba, ni uwa ce, i can feel it, i can feel it, ina ji a jiki na something bad is going to happen to my child"
Kuka ta fashe da shi,
"Habaa Ammi, kar ki wannan tinanin mana, da izinin ki, da amincewar ki ta tafi, kuma cikin farin ciki, dan Allah think positive, nothing is going to happen inshaa Allah, sai alkhairi,"
Rungume juna sukai, Mansur sai ya dakko gane me suke fada sai su batar da shi a hanya in sukai turanci, oho koma dai me ne ne, Allah ya kawo masu da sauqi.
Hankalin Ammi bai kwanta ba, tinda Salma ta tafi, tasbihi kawai take ga Allah,har dare bata dawo ba, kafin nan Ammi ta sha kuka har ba iyaka, Abba ma hankalin shi ya tashi ainun, ina to ta tafi? Wayar ta bata shiga ma sam.
A lalace sai da akai sati biyu ba Salma, Uncle Ibraheem da iyalan shi sun zo, suna zaune a gidan su na gado da ya gyara shi yake sauka a nan da iyalan shi in sun zo, kuma anan ake family meeting, Uncle Isa da Uncle Usman suma ba a bar su a baya ba wajen neman Salma, gidan redio da TV dik an saka ta mujallu da yanar gizo dik labarin batan Salma ya zaga........
KALAN DANGI...PAGE 14
953 90 8
by Haermeebraerh
Following
Ba kowa a gidan sai Salwa, duk sun tafi Family house, in da ake tattauna yanda za a bullowa lamarin batan Salma, Salwa na zaune jigum, ta gwada dik wata no d ta ke da,ta qawayen Saalma sun ce ba su san inda take ba, hawaye ne ke ta kwaranya a idanun ta, tana share hanci da hannun ta.
Ba sallama ba komai haka ta ga mutum a saman kan ta, idanun ta sun kode sunyi jawur, gata kamar wadda ta fito daga wata masarautar, alkyabba ce mai tsananin kyau a jikin ta, sai tashin qamshi take, rigar da ta fita da ita na qasan alkyabbar, ita kan ta Salma da za a tambaye ta tin farko ina taje, sannan daga ina take ba zata iya fadi ba.
"Salma!!!"
Cikin layi Salma ta zube a wajen, wani nannauyan bacci ya dauke ta, kuka Salwa ta sa ta fita da gudu waje, ta kira Mansur, matsanancin tsoro ne ya kama Mansur daya ga Salma, ta ina ta shiga gidan? Yana fa zaune bakin qofa bai ga shigar ta ba, baya ya ja da sauri ya rabe a jikin qofar dakin nasu, ya qanqame jikin knob din gamgam, kamar mai jin tsoron za a ja shi gaban Salma.
1
"Kira Hajiya, kira Alhaji,"
Shi ne abinda yake maimaitawa, yana sakewa.
Hannun Salwa na rawa kuwa ta dakko waya ta kira Ammi, bakin ta na rawa da muryar ta take fada mata ga Salma ta dawo, jikin Ammi har kyarma yake, tana tuntube,
"Abban su ta so mu tafi Salma ta dawo, Alhamdu lilLAAH Allah na gode maka"
Sai ta durqusar da kan ta a tafin hannayen ta ta fashe da kukan farin ciki, Abba bai ji nauyin rungume ta gaban 'yan uwan shi ba yana bata hakuri, cikin sauri kamar wadda take tsoron kar Salman ta koma haka ta fita daga babban Parlourn da suke taruwa dika iyalan.
Bayan ta suka bi dika, suka shisshiga motocin su suka dau hanyar gidan Jalaluddeen.
A bangaren su Salwa kuwa, fita tai dan debo ma Salman ruwa ta dan sha, Mansur ya kwasa waje da gudu, ya tsaya a parlour, bai yarda a barshi daga shi sai Salma ba, bai san irin dukan da zai sha ba kuma in ta farka ta gan shi.
Koda Salwa ta dawo dauke da Cup a hannun ta, mamaki ne ya sa ta tsaya a bakin qofa da tsoro, nuna hanyar gadon su ta dinga yi tana in ina, tana ma Mansur magana.
"Sasssasalmaaa...waaawaayee... ya daga ta??"
Leqa kan shi yayi, ya gan ta kwance a saman gado, an sa mata pilo ko ta ina, ga shi an cire alkyabbar da ta zo da ita, ba alkyabbar ko sama ko qasa.
Mansur bai tsaya a ko ina ba sai a wajen gate, dan a cewar shi zaman cikin gidan ma tsautsayi ne, ba a san ta inda za a diro ba indai ana iya kawo salma from no were.
1
Yana nan waje ya nade hannayen shi a qirji yana mamakin abubuwan da ke faruwa, da tinanin zuwa qauye ya samo wasu layun da tsari, (Allah ya shiryu masu daura laya).
1
Motar su Abba ta sawo kai cikin layin, da gudu ya wangale gate, nan motar shi ta shige, ta sauran kuwa a waje suka aje saboda wajen ba zai dau motocin su ba, dan gidan ba irin qaton nan bane sosai.
Koda suka shiga sun samu Salwa na zaune a daya daga kujerun parlourn tana ta rera karatun qur'ani dan ruwan ma ga shi nan aje wajen qafar ta, ta kasa shiga,Mansur da take ganin babba ne zai tsaya ta ya gudu.
Tana ganin Ammi ta tashi da gudu ta rungume ta, cikin kuka da tsoro ta zayyana masu dik abinda ta gani, nan suka samu suka shiga dakin.
Kwance Salma take sai bacci take, karatun qur'ani aka kunna a waya aka sanya mata gefen inda take kwance, Ubaidullah yana tsaye yayi downloading App na Ruqya sai da ya gama shiga ya kunna, ya aje mata.
Baccin ta take ta sha kamar ba abinda ya faru,fita sukai suka bata waje, dan sun kusan awa daya a wajen amma bata farka ba.
(Illar aljanin da yake auren matan bil'adama kenan, wasu ba zama suke a jikin ka ba, sai da su zo su tafi, dan haka sai sun gama birkita ka su tafi, ai ta ruqya a ji shiru, sai in Allah ya yi dubun su ta cika, a samu suna nan fitar ta gagare su, ya Allah ka kare mu ka nesanta mu da su).
1
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Sallar magrib sukai, saboda har lokacin Salma na kwance, suna nan ana tattaunawa, Ammi da Salwa suna girki, ba su gama ba, kusan dik minti biyar zuwa goma sai ta leqa Salma, sai ta gan ta tana saukar da numfashi a sauqaqe kamar ba abinda ya ke damun ta a duniya.
Ubaidullah ke dan taya su wasu aikin, saboda ya kula dik yi kawai suke amma hankalin su ba a jikin su yake ba.
A taqaice dai har goma na dare Salma na bacci. Uncle Isa ne yace.
"Yah Ibraheem ko za a tashe ta ne? Ni fa na fara jin tsoro, wannan baccin yayi yawa"
"Ammin su ta gwada tashin ta, amma bata tashi ba, kar ku damu tinda dare yayi zaku iya tafiya, in Allah ya kaimu ta tashi sai na sanar daku, komai dare zan sanar da ku inshaa Allahu,"
"To shikenan, Allah ya sa muji alkhairi, Allah ya yaye mana wannan musiba da ta kunno mana kai cikin zuri'a, tinda muke a zuri'ar mu bamu taba fuskantar irin wannan tashin hankali ba, Allah ya fitar damu, ya bamu ikon cinye jarabawar nan"
"Ameen yayah"
Nan sukai Sallama suka kama hanyar tafiya gidajen su, Ubaidullah anan zai kwana, dakin baqi na gidan Salwa ta gyara masa, motar shi ya je ya dakko laptop din shi da sauran abubuwan da suke ciki na buqatar shi.
Shayi ta kai masa, dan yana son shan shayi da dare.
Gani yayi dik bata da walwala, damuwa ta sa dik ta rame, idan ta kamar wadda bata samun bacci mai kyau.
Har zata rufe masa qofa ya kira ta, ta juya, suka hada ido,murmushi ya sakar mata, wanda taji baqin cikin zuciyar ta ya ragu sosai, itan ma bata san sanda ta maida masa da murmushin ba, rabon ta da murmushi ko dariya tin randa Salma ta bace.
"Zo, shigo ciki"
Komawa tayi ta zauna dan nesa da shi, daga qasan gadon da yake kai,
"Salwa na sani batan Salma ya daga hankalin ki, amma ki sani komai yayi zafi maganin shi na wajen Allah, dik abinda ya dami bawa ba zama zai ya sa a ran shi ba har damuwa ta ci qarfin shi ya yi developing wani ciwo a jikin shi ba, miqawa Allah lamarin shi zai, yayi addu'ar Allah ya kawo masa mafita a lamarin shi, dan haka kinga saboda tsananin addu'a da muke ga shi Salma ta dawo, in muka ci gaba da roqon Allah sai ya yaye mata kome ke damun ta, kin gane? Ki dai na wannan kukan bana so,"
Share hawayen ta tayi ta share hancin ta, ta dan qaqalo murmushi,
"Yah ubaidu ina kukan murnar bayyanar Salma ne, a da na zaci ta bata kenan ba zan sake ganin ta ba"
Ta sake fashewa da wani kukan, dafa kan ta yayi ya daga fuskar ta, ta kalle shi, idanun ta na zubar da hawaye, share mata su yayi, yana girgiza mata kai da murmushi, sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi itama,
"Ko ke fa, kinga yanda kikai kyau yanzu? Ki daina sa damuwa, kuma ki tabbata kin ci abinci kan ki kwanta, dan na san baki ci ba, dik kinbi kin koma qashi da rai, wuya ya maki zololo,kamar na raqumin agadez"
Dariya ce ta kama ta, ba tare da ta shirya va, ta jima rabon da kunnuwan ta suji sautin dariya balle ta yi da kan ta.
Sallama ta masa ta fita xuwa dakin su, shi kuma daukan shayin shi yayi yana sha, dik da ya ma yi sanyi akan yanda yake so, bude laptop din shi yayi yana aiki akan kayan da duka shigo da su.
Salwa ta dan ci abinci kamar yanda Yah Ubaidu ya umarce ta da ta yi, sai taga in batai ba kamar ya na ganin ta.
Ammi taqi sam ta bar dakin, so take ko Salma zata farka ta farka akan idon ta.
Abba na zaune a parlour, ya lumshe ido, yana jiran shima yaji ance diyar tashi ta farka.
Kowa bacci ya dauke shi, sun nan zazzaune suna jiran farkawar Salma, tsakiyar dare ta farka, ta fara kalle kallen inda take, tinani ta fara a hankali ta fara tina me ya faru.
Tin ran da aka daura masu aure da Irfaan Maleek a masarautar su, ya kaita turakar shi yake saduwa da ita, ba gajiyawa, tin tana jin dadin abun har ya ishe ta, tayi kuka ta kuma, amma ba mai ceton ta, rasa yanda zatai tayi sai ta fara roqon shi akan ya maida ta gidan su, nan ma qi yayi, sai da ya tabbata ta na daukeda cikin shi sannan ya shirya ta ya dawo da ita da kan shi.
Ya so ya zauna ya dinga kula da ita, amma yanda yaga dangin ta sun dage da saka karatun qur'ani da ruqya ya sa shi guduwa, dan kuwa gaba daya fuskar shi ta fara qonewa ta gefe, dole sai ya je yayi jinya, nannauyan bacci ya sanya ta dan ta huta, saboda yayi alqawarin komai rintsi komai wuya zai kare abinda ke dauke da Salma na cikin shi.
Dik matan da ya ke aurewa daga bil adama zuwa jinsin shi na jinnu bai taba samun haihuwa ba,yanzu ya samu Salma n dauke da cikin shi ko mezai faru zai kare wannan cikin.
Kuka ta dinga yi qasa2, dan tinawa da asalin waye Irfaan Maleek da tai, a tinanin ta mutum ne kamar ita, amma ba mutum bane ashe aljani ne, gashi tana matsanancin son shi, bata taba son kowa ba sai shi, ga shi mafarkin ta na mallakar shi a matsayin abokin rayuwar ta ya tarwatse, dik da a shirmen shi yana ganin ya aure ta, ita kam gani take bata auru ba, kuka take da shassheqa na tsananin jin matsananciyar soyayyar Irfaan dake huda dik wani sashe na jikin ta tana sake ninqaya ta kwanta.
Cikin baccin Ammi ta ji kuka, a hankali ta bude ido, ta kunna fitila,ganin Salma zaune tana kuka ya sanya ta isa gaban ta da sauri ta rungume ta.
"My poor baby, my child me ya same ki? Ina kk je? Ina ke maki ciwo? Wani ya taba ki ne?"
"Ammi Ammi Ammi plsss, ki kwantar da hankalin ki, ba abinda ya same ni, ni kaina ban san me ke
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 17