zuwa aiki sati daya bayan auren shi, Ubaidullah ya so shima yana zuwa aikin saboda yaron ya dame shi, kamar shi bai matsu a yi auren ba, kullum sai ya masa lissafin kwanakin da suka rage, sai yana aikin shi zai sallama kamar abin arziqi sai ya amsa sun gaisa sai ya balle da zance, yau ma kamar kullum Ubaidullah har rufe dakin shi ya yi d key, amma Huzaifah sai da ya kwankwasa, ya jima yana bugawa Ubaidullah ya shafa kan shi,
'Huzaifah in maye ne ya kama maka kurwa sai ya ga har bargon ka, yana abu kamar dan shekara ashirin ko yawan qannen shi baya hangowa'
"Waye ne haka? Aiki nake aje a dawo anjima,"
Maqale murya Huzaifah yayi,
"Mummyn ka kk cewa ta dawo anjima? Shikenan bari naje anjima na dawo din,aikin ka yafi ni mahimmanci"
Cikin sauri Ubaidu ya sa jallabiyya, ya fara murda qofar, Huzaifa yayi baya yana dariya, yana ganin ta bude ya wuce ciki yana ta dariya, leqawa Ubaidu yayi baiga Mummy ba, kama goshin shi yayi yana murmushi.
"Wai kai dan Allah baka girma ne?"
"Ni da abokai na inda zaka ga me muke lokacin ina can sai ka yi ta mamakin anya muna da hankali, is normal kawai share,dama naji ka shiru ne yau bamu gaisa ba nace bari na leqo naji qofar rufe da alama key ka sa"
Ubaidullah cire rigar shi yayi ya aje ya zauna ya ci gaba da tsara yanda zasu shigo da wasu kayan, sannan ya ce,
"Aikin nan nake son gamawa na san halin ka, in ka zo ba zaka bari na gama.ba, saboda kai dan zaman kashe boxer ne daga wannan ka sauya wancan"
Dariya sosai Huzaifah yayi,
"Ai ya qare inshaa Allah, nan da sati biyu, yanzu sauran kwana bakwai auren mu, inna gama angwancewa na fara zuwa aiki, i will be a bery responsible man, i promise u, zaka ce na fada maka"
"Really?"
"Yeh sure, zaka gani"
"Ok oo, Allah ya kaimu, wata qila kuma sai kun samu baby zaka nutsu,dan ba zai yu baby na shirirta kaima na yi ba dame uwar zata ji?"
"Yah ubaidu easy mana, ni yanzu wa zai kallen ya ce ban da hankali dan Allah,"
"Gani"
"Sai fa kai din"
"Tashi ka fita,"
"Tam ina jiran ka ka gama muyi shawara,"
"Akan me?"
"Akan maganin mata,"
"Ban gane ba"
Komawa yayi ya zauna, ya nade qafafun shi a saman gadon, yana kallon Ubaidullah, tare da dora pillow saman cinyar shi,
"Na kula an ware mu, mu ba mai bamu maganin matan, amma yau kusan sati da wasu kwanaki inajin Mummy suna waya, Mummy sai tace "kina dai basu maganin mata ko?" Ban san me ake cewa a can ba sai naji Mummy tace,"yauwa ko wannan ma suna da kyau kuwa, a basu su sha sosai,"
"To ni abun na damu na, in aka basu muma ai ya kamata a bamu, an kai su ana ta gyarawa mu ba abinda ake mana, aboki na dake qasar Saudiyya yace min in za ai ma maza aure ana kai su a gyara su suma kamar ya da ake ma mata, komai yi masu ake,"
Ubaidullah kallon Huzaifah kawai yake, yama rasa ta ina zai masa magana, da ace shine dan farin ma ba a san wautar da zai ba, shirirtar nan da mata ta dace, amma yana namiji yana abu kamar soko,
"Tashi ka fita,"
"What??"
"Yeh get out"
"Me na fada ba daidai ba? Shawara ce fa? We have to do something, su kadai ne zasu burgemu? In ba zakai gyaran ba nima zan duba google naga me ango zai dinga yi nayi, dan na birge mata ta,"
"Get out Huzaifah,"
"Ko kunya kk ji?"
Dariya Huzaifa ya fara, ganin yanda Ubaidullah ya zaburo kan shi ne ya sa shi fita waje da gudun tsiya, amma dik da haka sai da yayi nasarar make qeyar shi, yana rufe qofar shi ya dafe kan shi da hannu bibbiyu,
"Yaron nan wawa ne fa, wai maganin mata, ina ma laifin maganin maza? Me ya hada mu da shan maganin maza ko na mata, kaiiii yaron nan Allah ya sa ya fara shiga mutane lafy ya gane nan ba turai bane, "
Shiru Ubaidullah yayi, can ya yi sauri ya qarasa aikin da yake, Google ya shiga shima, ya fara duba me angwaye ya kamata su yi kafin aure har zuwa aure, a islam? Nan da nan kuwa ya dinga samun amsa, a qalla idean Huzaifah is not too bad, ga shi ya samu wasu tips masu amfani a musulunci wanda bai sani ba da, nan fa Ubaidullah ya samu abun yi, ko da aka aiko kiran shi cin abinci.bai kashe ba ya fice, Huzaifah ya fito daga dakin shi ya leqa ya kira shi su wuce ya ga laptop kunne ba Ubaidullah, dan duqawa yayi ya kashe masa yaga me Ubaidullah din ke gani, dariya kamar ya suqe, sai da ya dau abun a wayar shi ya fita.
Cin abinci yayi nisa, masu hira nayi masu danna waya nayi, Huzaifah ya tabo Ubaidullah, ya daga kai cikin jin kafa damen, sai ya daga masa gira alamar meye?
Nuna masa hoton laptop din shi yayi da inda ya ke dubawa a google, da sauri Ubaidullah ya zabura zai karki wayar Huzaifa, boye wayar shi,ya ci gaba da cin abinci kamar bai komai ba, yana dariya qasa2, Daddy ne ya kalle su,
"Huxaifah da Ubaidullah kuna ban mamaki, ku fa ba yara bane, meye haka kuke yi? Abu kamar kokawa, me zakai da wayar shi in ka amsa? Ku maida hankalin ku, bana son na sake ganin wani na danna waya ana cin abinci, ko kuma hira, wajen cin abinci ba wajen da za a na nuna rashin da'a bane"
"Ok Daddy inshaa Allah zamu kiyaye"
"Allah ya muku albarka"
"Kai kawo wayar nan taka,"
Cikin bata rai da umarni ya ma Huzaifah magana, miqa masa yayi yana qunshe dariya, kowa mamaki ya kama shi meye wai haka suke yi, sai da ya goge hoton ya bashi tare da masa kallon zamu hadu ne.
Dariya fal cikin Huzaifah ashe shima yana son ya burge amaryar shi, shine ya kawo shawara yake nuna masa baida wayo.
3
Bayan sun gama cin abinci suna zaune, suna kallon tashar Iqra wasu na wasa yara na guje2, Daddy yace.
"Who is ready for shopping?"
Kowa
"Niiiiiii, Daddy ni, Daddy zani"
"Ok to kowa zashi, Huzaifah da Ubaidullah in baku komai ku kai qannen ku su zabi abubuwan da suke so, na bikin nan, jibi zamu wuce Gombe inshaa Allahu,"
"YEEEHHHHHHH"
Yara da manya sai murna ake, Huzaifah ya shiga cikin su ana ta ihun murna,Ubaidullah kada kai yayi ya haye sama.
"Yaron nan sai addu'a dik ya sa yaran nan yanzu suna gani na kamar dodo, da kuwa komai ni, amma wai yanzu ni suke ce ma mai fada,ko san bana shirme irin na shi oho", wata rawa da ya hango Huzaifan yayi sai da ta bashi dariya shima"Huzaifah kenan, i love my brother, he is cute"
Ranar yara sun kwashi kayan da suke so, na kwalliya dana sawa, qananan manyan suka dauka masu, a qatuwar motar su mai daukan su dika suka tafi,
Sai gab da magrib suka dawo, alwala sukai sukai sallah, suka ci abincin dare, sannan suka shiga daki aka fara kwasar kaya. Ana hadawa na tafiya, sai da suka yi yanda zasu iya sannan aka hau hira kowa na fado sunan qawar shi da yake so ya gani,kusan kowa Aunty Salwa da Salma suke son gani, dan kuwa kan su Salma su koma ta samu shiga wajen wasu daga yaran, sauran da suka mallaki hankalin su in suka tina me take masu da na rashin mutunci sai siji gaba daya bata masu.
YAHHHHHHH INA SON BIKI, AMMA BANA SON ZUWA😂😂😂 WA ZAIJE BIKIN SU SALMAAAA??????KALAN DANGI....PAGE 30
967 63 0
by Haermeebraerh
Following
Mota uku sukayi, kowacce anyi mix tsakanin yara da manya, Khairat tayi kyau sosai, sai tsokana take sha wajen qannen ta su Sumayyah, ita kuwa hankalin ta na kan qawaye kuma 'yan uwan ta Salma da Salwa, ji take kamar sunyi shekaru basu tare, angon ta ya cika ta da messages na murnar zuwan ta da yake.
Koda suka isa gidan ya cika harda wasu 'yan uwan na jiki sosai, hayaniya kamar an ma fara bikin, Salwa da Salma da gudu suka fito dan taran Khairat, kan su ba ko dankwali saboda an shafa masu kayan gyaran jiki a fuskar su, tayi yellow, riga da wando ne a jikin su, wanda ba su kama su ba,yadin wani material.mai santsi,kalar yellow shima, gashin su ya sha gyara a daure a bayan su, ba qaramin kyau sukayi ba, dik da fuskar su tayi kalar dodo, suna haduwa suka rungume juna suna ta tsallen murna.
Huzaifah ne ya dan tura hular shi gaban.goshi ya zuba hannaye a cikin aljihun wandon shi, da baqin glass a idon shi, sai baqin agogo da ya daura mai kyau, farar shaddar ta dace da hular da ya sanya, an masa irin dinkin zamani mai siririn aiki rigar tabi jikin shi iya qaurin shi, sai baqin takalmi sau ciki.
Tsayawa yayi daidai saitin Salma, tana ta murna, ya yi magana a hankali,
"Lallai ma, ashe dama ba ni kk murnar gani ba Khairat kk son gani ko? Me kk ce man dazu da na ce maki ga shi mun kusan shigowa?"
Sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya, ta saci kallon shi,
"To ai ba yanzu nake nufi ba sai munyi aure,"
Dukan qirjin shi yayi ya lumshe ido,yana murmushi,
"Kwana nawa neeee yarinya?"
"Akwai saura dai"
Haka suka jera suna hira gwanin ban sha'awa, har cikin gida.
Salwa kuwa tana hada ido da Yah Ubaidullah taga ya hade fuska, ta masa murmushi taga bai maida mata ba, hannun shi ya sanya akai yana nuna mata ina ankwalin ta? Kuma shi a ganin shi kayan sun kama ta, kowa ma kallon ta yake, su Ameer da Sudais, ga matasan samarin family kowa na ganin ta a haka, wani iri yake ji kamar ya sa mata hijabi da niqabi kar kowa ya kalle ta.
Da sauri ta zame ba wanda ya gan ta ta je ta wanke fuskar ta ta shafa man da aka hada masu na kwakwa, man ridi, man dalbejiya kadan amma, sai man habbatussauda, man karas,da man zaitun, aka zuba madarar turare mai qamshi, fuskar nan kamar ta jarirai, hijabi ta samu kalar kayan ta ta sanya, sannan ta fita.
Ko da ta fita suna baje a parlourn qasa suna gaishe da Ammi da matan su Uncles din su, Mummy da Daddy na zaune suma ana kwasar gaisuwa wajen su, Uncle Jajal ya leqa companyn shi, Uncle Usman ma haka yana office? Yaje yayi signing wasu takardu, Uncle Isa ne kawai a gidan.
Koda Ubaidullah ya ga shigar da Salwa ta koma tayi wata iriyar qaunar ta da girman ta ne ya qaru a ruhin shi, murmushi ne da ke tafiya da imanin dik wanda tsautsayi ya sa ta kalla, da sauri ta rufe idon t ta shiga kitchen, Khairat Nabeelah, da dai sauran 'yan matan suka bi ta, nan suka fara debo abincin da aka tanadar ma baqin, dama mutan gidan baki daya, Mummy da Daddy sun shiga ciki dan watsa ruwa su fito a ci abinci, daki daya mazan manya sosai suke, dan haka angwayen dik suna a tare sai Umar shi kuwa ba aure zai ba a wanan lokacin, dan gidan Uncle Usman ne, idon shi na kan Sumayyah.
Hira suke ta yi sosai, Huzaifah ya basu labarin Ubaidullah da Google, sun sha dariya sosai, Ubaidullah tin yana bata rai nam shima ya biye masu suna ta dariya,
"Yaron nan ba a sirri da kai, shi fa ya matsa dai mun koyi ya ake zaman aure tinda matan ma ana koya masu, amma kunji ya na min sharri"
"Ai dan ka goge hoton ne da sun ga shaida"
Kwankwasa akai, Umar ya bude, 'yar qaramar yarinya ce qanwar shi da ake kira Ummee,
"Daddy ya ce in kun gama kuzo a ci abinci"
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
"To Ummeen Baba gamu nan zuwa"
Da gudu irin na yara ta sauka, cikin sauri suka gama shiryawa suka sauka, da'ira da'ira akai ana cin.abinci anyi shimfida,an hada kowa girma2, iyayen ne a kan table, sai da suka gama cin abincin su Ubaidullah suka gaida si uncle Jalal.
Bayan an gama matan suka gyara wajen? Manyan suna qaramin parlour, yaran na babban, sai hira ake kamar kasuwa, ta message Ubaidullah ya yi ma Salwa magana ta je ta same shi a waje, tashi yayi ya fita, ba a jima ba kuwa ta bi shi.
Yana tsaye a jikin qofar fita daga parlour ta waje, ita kuma sai ta tsaya daga dayan bangaren, suna fuskamtar juna.
"Thank u"
Daga idanun ta tayi da suke tsananin son ganin shi, cikin wata iriyar muryar da take kwadayin yi ma.masoyin ta magana tace,
"Da akai mi?"
"Da kk bin umarni na koda ke baki so,"
Murmushi tayi,
"Ai wajibi na ne, ko da ba zaka zama mijina ba na bi umarnin ka, balle kuma kai din inshaa Allahu miji na ne,"
"Hijab din nan ya miki kyau, wai dan Allah da me kuke wanka? Kinga yanda kk koma kuwa? Gaba daya kamar ba ke ba, kinyi wani irin kyau, kyaun da in kika fi haka gaba bana jin idona zai iya dauka, sai an min gilashin rage ganin kyau😂"
Dariya sosai ya bata, gaba daya ya shagala wajen kallon ta, suka ji ana kiran sallar la'asar, shiru sukai dan bin kiran, sai da suka gama bi sannan sukai addu'a a tare yace,
"Me kk roqa?"
Murmushi tayi,
"Na roqi qarin tsoron Allah da imani, sai aljannah dana roqa mana, sai kuma immm nace immm.."
Hannu ta sanya a bakin ta ta dora qafa daya a bakin qofa, sanan ta riqe labulen qofar,
"Cewa nayi Allah ya mallaka min kai"
Da gudu ta shige ciki, ya bi bayan ta da kallo, dauke da wani irin murmushi mai tattare da tsantsar so da qauna a cikin shi.
Shafa kan shi yayi ya fita zuwa masjid.
Salma kuwa da ke zaune a bakin gadon dakin su, tana qoqarin shiga bandaki tayi alwala, sai ta zauna cire hijabi tare da kashe datar wayar ta.
Qwanqwasa akai sau biyu, ya leqa kan shi, suna hada ido suka sakarma juna murmushi,
"In shigo?"
"Ka riga ai ka shigo,"
Duba kan shi yayi sai yagan shi a dakin,dafa goshin shi yayi kamar wani mace.
"Kashhh, wani irin maganadisu ne a tattare da ke, shi yasa bana sanin sanda nake bin ki,"
Tashi tayi tsaye tana nade hannun rigar ta,
"Ya kamata kam ka iya daina bina a wannan lokacin, saboda tsaro,ni kaina ji nake kamar n dinga bin ka dik inda ka shiga"
Shigewa toilete za ta yi ya kama hannun ta, da sauri ya sake yana zaro ido, itama da sauri ta janye jikin ta, tana matse hannun nata a dayan hannun, kallon ta yayi ya kalli hannin shi, a tare suka ce
"Shoking"
Sake kai hannu sukayi dan taba juna, wani irin maganadisu ke jan su, hannayen ta jin su yake kamar yana taba audiga dan laushi, idanun su sarqafe da na junan su, a hankali ya fara takawa gaban ta, itan ma bata san tana matsawa ba, sai da ya qarasa daf da ita, cikin sauri kamar wadda aka kwadawa mari ta ja baya sosai, suna hada ido ta sauke na ta, janye hannayen ta tayi a nashi ta shige bandaki ta rufe qofar, numfashin ta na fita cikin sauri, lumshe idon ta tayi, tana jin baqon lamarin dake shigar ta, ta yi soyayya da Irfaan, har sex tayi da shi dik da cewa aljani ne, amma bata taba jin irin wannan abun da taji a wajen shi ba a iya tabin hannu kawai, Huzaifah da kyar ya ja jikin shi ya fice sakamakon hayaniyar 'yan matan da yaji suna qoqarin hawowa saman.
Dakin su ya shiga ba kowa sun tafi masallaci, kwantawa yayi ya rintse idon shi, wani irin yanayi yake ji a jikin shi, wanda bai taba ji ba, mata ba su gaban shi, bai taba zina ba, ya dai taba shan sigari, rufe idon shi yayi ya juya ya kalli ceiling, hoton yanayin da Salma ta shiga yake, ta yi mashi kyau sosai, anya abinda sukai ya dace kuwa???
Shine tambayar da sukai ta yi wa kan su har sukai sallah.
Wayar ta ta dauka, ta fara masa message,
"Hey my baby, y kk?"
"Good, missing u"
"Mee too"
"Hummm to ki zo waje na,"
"Nop"
"Why?"
"Bana son mu sake maimai ta abinda mukai dazu, ba kyau, haramun ne, mace da na miji su kebe kafin aure,dazu ba dan Allah ya kiyaye ba da shaidan ya fi haka yin nasara akan mu, mu yi hakuri da ganin juna a kebe muna haduwa cikin mutane"
Yaji dadin kalaman ta sosai d sosai.
"Inshaa Allahu ba sa a sake maimaitawa ba my dear"
"Allah ya sa love"
"Kina ina?"
"Ina dakin mu"
"Ok, pls muje qasa i wanna c ur beautiful face plsss baby"
"Oh okkk gani nan ina zuwa"
Sauka yayi online ya sake fesa turare, ya fita,ita ma shafa powder tayi, ta shafa turaruka sannan ta fita.
"Sai ina sist?"
"Zan je qasa ne ina ce kuma sauka zakuyi?"
"Ni dai ina nan, zan dan yi karatu, kunyar Yah Ubaidu nake ji na rasa me yasa"
"Kinji da gulmar ki dai, zai cire maki kunyar ai"
"Khairat na rasa ina kk koyi zaro manyan zance haka,"
Nuna Salma tayi da sauri,
"Niiiii? Khairat kiji tsoron Allah, ni da magana ma da kyar nake yi,"
Dariya suka kwashe da shi dika, suna nuna ta, murguda baki tayi ta qarasa shiryawa ta sauka.
Mutane na ta zuwa saboda samun damar halartar bikin wannan family mai albarka, kowa ka gani cike yake da farin ciki, masu aiki suka qara, saboda a samu aiki yayi sauqi.
Yau ranar qunshi ne, kowa ka gani ya sha lalle, wasu suna layi, sai fullanci ke tashi a tsakar gidan, amare aka fara yi wa, an masu jan lalle da baqi, zuwa yamma xa a yi Kamu, qawayen Salma wanda suka saba sosai a social net sun mata alqawaein zuwa, Jadwah ba ta qasar, dan haka Salma ke ta tura mata hotunam lalle.
Salwa ce ta ja ta gefe,
"Salma ya kamata ki rabu da qawayen nan na net, kin dai ga dauki ba dadin da aka sha, kusan a gidan su Jadwa muka fara haduwa da bala'in, amma shine kk ta tura mata hotunan ki, kinga dai mijin ta abokin baban ta n muka sani ko shima kudin jini gare shi? Kk tura hoton jikin ki? Plss go back and delete all the pix, ki nitsu,"
Maganganun sun mata tasiri, godiya tayi ta je ta goge hotunan dika, Jadwah na ta mata masifa akan bata gama gani ba, haka ta share kawai, suka tafi wanka, dan a fara kamu da wuri, ba su son magrib tayi ba a gama ba.
Wanka sukai, sannan suka dauraye jikin su, sannan suka sake wanke jikin su d ruwan jiqaqqen lallen da ya sha madarar turare masu qamshi,ko da suka fito sai zabga qamshi suke, jikin su akwai ragowar ruwa suka shafa humra iskar fanka na kadawa ya fara bushewa, humrar tayi naso dik jikin su, tiraren garwashi aka sa suka yi, suka tirara har qasan su da turaren wuta na HQ, sannan suka sanya na gashi,
Wani irin qamshi ke fita a jikin su kamar jikokin larabawa.
Shigar sudanis aka masu, aka fara kamu, irin na sudanis, wata qawar Mummy ce ta tsara irin kamun, (Hafla) masha Allah, amare sun yi kyau sosai d sosai,mazan ma sun sha kyau, sai qamshi suke, ba a jima ba kuwa aka fara gabatar da kamun.
Biki yayi biki, hasken wayoyi kawai kk ganin na tashi, ga kida irin na soyayya wanda ake yi da larabci irin waqoqin sudanai.
An ci an sha, wanda suka zo kowa yabawa yake dan kuwa sun tafi da tsarabobin biki hannu cike.
A gajiye aka tashi daga kamun, Huzaifah ya kasa jurewa, koda Salma suka zo fita, kawai taji an jata, taso ta saki ihu ya damqe bakin ta...
HummmmmmmmmmmKALAN DANGI......PAGE 31
935 73 5
by Haermeebraerh
Following
Motar shi mai rufaffen gilasai ya tura ta, sannan ya zagaya ya shige, rufe qofofin yayi ta kowanne bangare, fahimtar waye ya dauke ta da tai ne ya sake tada mata da hankali, ba dan komai ba sai dan tsoron abinda zai je ya zo, abinda ke cikin idon shi ba qarami bane, cikin rawar murya da baki ta fara magana, amma ya katse ta,
"Ka maida ni gida plss,kar......
Wani irin mayunwacin kiss ya sakar ma lips din ta, bakin shi har rawa yake, wani irin dumi jikin su ya dauka na tsantsar sha'awar junan su, tin tana daurewa itama ta fara maida masa da martani, cikin jin dadin da suke wani irin tsoron Allah ya shige ta, da sauri ta janye lips din ta da suka sauya kala zuwa jajaye, cikin maida numfashi da sauri2, ta kalle shi, hawaye na gudu akan fuskar ta,Huzaifah idanun shi sun sauya zuwa launin ja, hannun shi har rawa yake saboda tsananin sha'awar da yake ji, qamshin jikin ta ke qara susuta shi, bai qi ya same ta a wannan lokacin ba.
"Yah Huzaifa ka maida ni gida, bana son ka, bana son ka, na tsane ka, in ka ga na aure ka sai dai in na mutu, a yau ba sai gobe ba zan sa a janye maganar auren mu"
Cikin wani irin tashin hankali yake bin ta da kallo,
"Ka ji me na ce ai, ba zan aure ka ba, bana son sake bude ido na gan ka, ka buden mota ko a adaidaita sahu zan koma gida,....wayyoo Allah na, Allah ka yafe min, Allah na tuba, na shiga uku...Yah Huzaifah ka cuce ni, ka sa na aikata zina,"
Kife kan shi yayi ya fara hawaye shima, a hankali sha'awar da yake ji ta fara lafawa, kuka sosai yake yi,
"Salma dan Allah kar ki guje ni, na tuba ga Allah ki yafe ni, tsananin son kasancewa da ke ne ya sa na aikata haka, Salma kuma kuna da laifi, wannan irin qamshi da kwalliyar da kukayi shine ya sa na kasa hakuri, amma dan Allah kiyi hakuri,kar ki guje ni, in kk barni mutuwa zan yi,"
"Shi Yah Ubaidu ba mutum bane? Ko kana nufin ka fishi zama namiji ne? Ka fadan kawai ya fika imani da tsoron Allah,ina son ka, amma ban taba zaton zaka min haka ba, bude min na tafi"
"Dan Allah salma ki yafe min, na san ban kyauta ba, amma ina neman afuwar ki, ba zan sake ba, dan Allah ki yi hakuri, ki rufan asiri, kk fasa aure na me za a ce? Me mutane zasu ce?"
"Ohhh damuwar ka me mutane zasu ce ko? Ka manta da Allah ya fi ganin ka sama da mutane, ka iya aikata abinda kayi amma shine kk zancen mutane? Mutane na da wuta ne? Ko aljanna gare su? Ka buden nace ba zan aure ka ba, na fada maka, ka sani, ko gobe baka ji an daura aure da kai ba ka sani ni salma na fasa auren ka"
Cikin kuka da tashin hankali ya ja motar zuwa gida.
Can tinda suka ga basu ga Salma ba, basu ga Huzaifah ba sun san tabbas suna tare, dan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 17