Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
isa. Gidane babba mai danneman kyau, sanda suka isa mai gadi ya bude masu gate suka shiga, Salma sai murna take a qasan ran ta, irin gidannan take son tana zuwa , kullum ta zo sai tayi hotuna dama, wannan karon taga an sake gyare, lallai zata bada kala, murmushi ne ya subuce mata, qannen su da suka zo tarvar su sai sukaji dadin ganin murmushi a fuskar ta, dan bata saba sake masu ba. Amsar kayan su yaran sukai, matasan sukai ta masu sannu da zuwa, yaran gidan sun kai goma. Salwa na son kowa, kuma tana zumunci da kowa, musamman Khairat, da Ubaidullah, amma Salma kuwa ba wanda ya ishe ta kallo dik gidan, gwanda ma in khairat ta ishe ta da surutu tana amsa mata, ko kuma in taga wasu kaya masu tsada da kyau tana son aro tai hoto to a ranar zasuyi mutunci da Khairat din. Mummy ce ta sakko daga saman banen, tana yauqi, mace ce gajera fara sosai, har wani ja take yi, tana da yalwar gashi, tana da qiba madaidaiciya, tafe take tana waya. Sai da ta gama ta zauna a daya daga cikin kujerun dake zagaye da parlourn tana masu murmushi, "Baqin Gombe sannun ku da zuwa, maraba," "Yauwa Mummy, ina fatan mun same ku lfy?" "Muna lfy qlou, ya Ammin da Abban naku?" "Suna gaishe ku sosai d sosai," "Salma ba magana," "Ina wuni?" "Lfy" "Yunwa take ji, kun san bami iya karyawa in zamuyi tafiya, shi yasa" "Allah sarki Salame sai kice yunwa kk ji," Kallon Abdurra'uf tai ta zabga masa harara, dariya sukai ta mata, Khairat ta dawo daga aje masu kayan su a dakin da suke sauka in sun zo, ta ce. "Ku zo ku ci abinci, dan na san hali, ko wanka zaku fara?" A son Salwa zata so tai wanka kafin taci abinci, amma ko dan saboda 'yar uwar ta bari tafara cin abincin. Sai da Salma ta faki idon su ta ma abincin hoto, abinci ne mai tsinka yawun mai kallo, ci sukai suka qoshi sannan suka je dan yin wanka,waya Salwa tai ma Ammin su, suka sanar da ita sun isa lfy, hankalin ta ya dan kwanta, ta masu addu'a, sannan suka kashe. Abban su suka kira shima suka sanar da shi sun isa lfy. Bayan sun yi wanka sun sauya da wasu dogayen riguna na qasar larabawa suka yafa mayafin, ta baya Salma ta fita kambun gidan, ta hau hotuna, daga nan ta je qofar gidan ta yi hotuna tare sa yin snapchat, qawayen ta da suka san waye yayan Baban nasu a siyasar qasar mu nan d nan suka dinga fasa mt kai, ji ta dinga yi ba wani wayayye a IG sama da ita, ko akwai ba su hadu ba tukunna. Sannan ta koma ciki ta zauna, tana chatting da Jadwa, tana fada mata sun iso sai gobe zata zo a sa lalle da ita, dama itama batai komai na kwalliya ba. Nan Jadwa ke fada mata in tazo ma sai suje saloon tare. Haka akai kuwa washegari bayan an gama karyawa a makeken table din cin abincin, Uncle Ibraheem ke sanar dasu sun yi waya da Abban su, yace zasu biki ko, amsa masa sukai, nan yake sanar dasu to driver zai kai su dik inda zasu. Salwa ce tai godiya sannan Salma, ya nuna masu ba sai sunyi godiya ba, nan din gidan su ne. Ko da suka shirya dan zuwa gidan su Jadwa, Salma cewa tayi su sanya atamfar su mai tsada saboda kar a raina su, Salwa kada kai kawai tayi tn mata fatan shiriya a ran ta. Uncle din su ya basu kudi wai koda zasu buqata, Salwa tana ah ah, saboda an basu a gida, Salma ta amshe tai godiya. Khairat ma ta shirya tsaf dan bin su, "Ni gaskiya ban fada masu zamu je da yawa haka ba, haba dan Allah," 2 Ran Khairat ya sosu, amma ta dake, "Ke sai ki fasa zuwa mu muje a madadin ki," Tsaki tai ta shige gaban motar, suka zauna a baya, driver ya ja su sai gidan su Jadwa........ *Ayi biki lfy* by Haermeebraerh Following Koda suka isa gidan su Jadwa dikkan nin su sai da suka sake baki dan kyau, rasa wane ne uban ta a Nigeria Salma tayi, anyaba gidan yankan kai ska zo ba, mazewa tayi kar su Salwa su gane halin tsoron da ta shiga,wayar ta ta zaro ta kira Jadwa, bata jima tana ringing ba tadaga, "Qawata kin iso?" "Eh mun iso, nida sisters dina ne,amma na ga gate din naku akwai msu tsaro da baqaqen kaya, ya zamu yi mu shiga?" "Kar ki damu, bari na yi waya za a bude maku yanzu, ur wlcm my freind" Basu jima da gama waya ba suka ga gate na budewa, drivern shiga yyi ya parker motar, motoci ne a cikin gidan iya ganin mutum, wata matashiyr budurwa ce yar qarmasassa ta fito sanye da qananan kaya, kanta ba gashi sosai ta yi parking din gashin irin na gefe dinnn, wayoyi ne masu mugun kyau d tsada a hannun ta, kyaun ta sai a hankali, Salma ta kalli gidan, tabbas nan gidan take ganin ana Jadwa na hoto a ciki,amma wannan kamar ita kamr ba ita ba, wadda take gani a IG tafi wannan kyau d cika, (aikin technology😂) rungumar da Jadwa ta ma Salwa ne ya tabbatar mata lallai wannan itace Jadwa, ikon Allah, amma waya shegiya ce, dibe ta azahiri, kamar wata baqauyar da ta waye. 1 Salwa ce ta dan yi murmushin yaqe ta nuna Salma, 'Banza ko meye na nuna ni, so take nima a dadime ni yanda aka mata, ohhh Allah, tinda nake qawance a media yau ne na daga wrong number' 2 Da sauri ta miqawa Jadwa hannu, dan gaskiya haka nan take jin bata son su hada jiki, cikin qayataccen murmushin da ta qaqalo lokaci daya ta miqa mta hannu tare da cewa, "Salma Jalaludden Hussain" Itama miqa mata hannun tayi tare da qanqame hannun sosai cikin nata tsabar murna yau ga ta ga Salma, "Kina tare da Jadwa, ur highly wlcm my queen" Murmushi sukai dika, Salwa da Khirat kuwa dariya ce fall cikin su, amma sun qunshe ta, cikin gidan suka shiga, masu aiki ga su nan kala2, kowa da abinda yake yi, Salma sake tabbatarwa tayi tabbs wannan gidan su Jadwa ne, dan in ba a qasar waje tai hotuna ba anan gidan take ganin hotunan ta, dan nunnuna masu gidan tayi kamar wanda suka je ganin gidan, sannan suka zaun a wani qayatacce parlour, nan da nan kuwa aka jere masu wajen da kayan ciye2 da na sha. Salma ba fulako, nan ta hau cin abincin hankali kwance, Salwa da Khairat kuwa ko ruwa ba su sha ba,Jadwa ce ta ce bari taje ta shirya su je saloon, in sun dawo mai gyaran jiki zata zo a masu, a cewar ta iyayen ta basu nn sun yi tafiya a gobe da asub zasu dawo. Ta jima sosai kafin ta dawo, sai da suka yi hotuna sosai suka saka a IG sannan suka fita, Salma ta ga yanda Jadwa take ta qarawa kan ta hips da boobs da kyau ma gaba daya, dik aikin technology ne da aka samu ci gba yanzu ta kowanne fanni. Wani qayataccen Saloon suka je, da gani sai wance da wance ke zuwa, Salwa da khairat sun so suyi gardama, Salma ta hna, ta dinga mintsinin Salwa akn ta daina bata kunya, nan aka shiga masu hidimar gyara, daga kai zuwa hannaye zuwa qafar su, dik an gyara masu, Jadwa sai da tai qara ganin gashin su Salama da Salwa har ma Khairat, "Amma gaskiya kuna da kyau, ba qaramin dagan daraja zakuyi ba a biki na, dan kuwa ba safai muke da kyawawa a dangin mu haka ba, dama qawaye na gaskiya" Salma an zo wajen, wani murmushin isa da qasaita tare da jin kai ta sake, vedio Jadwa take ma Salma, saboda kowa yaga yanda aka gyara su sai sun bashi sha'awa yaji dama qanne , yayu, ko 'ya'ya, ko kuma qawayen shi ne. "Amma ke da twin din ki in ba mutum yayi d gaske ba ba zai gane ku ba, hatta da dankunne iri daya kuke sakawa, a gskiya kun hadu" "Kar ki damu, yanzu daga nan ki kaimu shoping mall, ina son zamu siyi kayan da zamu saka, kin ga mun zo a qurarren lokaci, sai ki zabar mana kalar da kukai anko, sai mu sanya," "Kar ki samu damuwa, da kai na zan kai ku, ai dole ne ma muje shopping inna yi baqi bamuje shopping ba ji nake kamar banda lfy" Cike da murna a ran Salama suka wuce wani shopping mall da ke kusa da wajen, wasu tsadaddun riguna dogaye purple Jadwa ta zabar masu, masu kyalli da walwali, dogaye ne sosai dan har qasa suke ja, ta baya, mayafai sirara da zasu hada suka dauka, dan ta kula Salma na son rufe halittar da Allah yamata, (Tarbiyyar iyayen ta kenan). Sun hada harda purse da takalma, dan kunne da agogo, da wasu kayan ma, dik Jadwa ke diba, can qasan ran Salma tana roqon Allah ya sa Jadwa ta biya,dan basu da kudin siyan wannan uban kayan, dik kudin jakar su ta san sai sun qare indai su zasu biya, nan d nan ta fara hana Jadwa diban kayan,tana kiran sunyi yawa. "Dan Allah karki damu, wasu ma a baza munzo mun sai kaya dasu balle ke? Mu diba nima akwai abubuwan da na ke so nima" Suna ci gaba da dibn kayan wayar ta tayi ringing, amsawa tayi ta kashe, "We have to go home, mai gyara ta je gida tana jiran mu" Wajen biyan kudi suka je, Jadwa ta miqa msu card din ta, ta ci gaba da latsa wayar ta, aka hade masu kayan a ledoji suka wuce motocin su, Salma na tare da Jadwa su kuma su Salwa suna motar su, sun yi dariya sun godewa Allah, ashe da ma haka Jadwan take? Har suka isa gidan suna tina abubuwan da Jadwan take yi, kamar ma masu kudi ba, kwata2 batai kama da su ne ke da wannan arziqin ba. Su kuwa suna can mota Jadwa na mata bayanin abubuwa da za ai a dinner din, sannan take sanar da ita da an daura aure zasu wuce london da mijin nata, abokin baban ta ne,kuma ba yaro bane, yana da kudi dai,shi yasa take son shi, ita bata son auren talaka komai kyaun shi kuwa, nan take sanar mata ta gayyaci wasu daga qawayen su n IG manyan 'yan matan da hotunan su ke yawatawa a IG da wasu daga cikin manyan 'yan film. Salma ta sake jinjina aiki irin na Jadwa. Sanda aka gama masu gyaran wajen tara n dare yayi. Taso su kwana,amma inaa dole su koma b tarbiyyar gidan su bane hakan. Salma ce a gaban motar su Salwa na baya suna tsokanar ta,tai banza d su,sai shafa hannun ta take tana taba yanda yayi laushi. Wata qara motar su tayi tare da cin burki mai qarfi,sai da kan Salma y bugu, saboda rashin teat belt, cike da fushi ta daga kanta dan ganin mene ne ya so sawa suyi hatsari,gaban tane y mugun faduwa.......... Wani matashi ne, sanye da wasu irin kaya a yage,kai da ganin shi ka san ya ji rayuwa, tsabar tinani ne na babu ko wata damuwar ta sa shi tafiya bai san inda yake jefa qafar shi ba, motar na tsayawa shima ya tsaya ya juya yana kallon su,dik gemu buzu buzu yarufe masa fuska, ga gashin kai ya tara, dik wanda ya gan shi yana iya kiran shi mahaukaci direct. Salma cikin tsananin fushi ta bude motar ta isa gaban bawan Allahn nan, ta daga hannu zata zabga masa mari Salwa ta riqe hannun ta, "Kai wanne irin baqin mahaukaci ne? Zaka tsorata mutane sannan ka sa a bige ka ka jawa mutane musiba, in kana da matsala da rayuwa ka kashe kan ka a wani wajen mana amm ba ka zo saman titi inda mutane ke wucewa ba," "Salma wai me yasa ke a rayuwar ki ba ki san meye tausayi ko mutunci ba? Yanzu fisabilillahi wannan bawan Allahn in baki tausaya masa a yanayin da yake ciki ba har kin masa fada?.....bawan Allah lfy kk? Baka ji ciwo ba ko?" Cikin murmushin shi daya bayyana haqoran shi wasu kala da mutum ba zai iya cewa ga kalar su ba ya furta. "Babu damuwar komai, kuje kawai, Allah ya kiyaye hanya, ke kuma ki bi rayuwa a sannu, rayuwar nan da muke ciki ta qunshi abubuwa kala2 masu ban mamaki," "Sai ka fara ban mamakin na sha kafin na san ya rayuwar take, aikin banza kawai, in talauci yayi ma mutum katutu sai ya dauka shi kadai ya san Allah," Kada kai wannan mutumin yayi, ya wuce, Salwa ta bude jakar ta tabi shi da gudu ta miqa masa kudi, juyawa yayi ya kalle ta, dauke da murmushin da ya mata dazu, "Na gode SALWA, ALLAH YA CIKA RAYUWAR KI DA FARIN CIKI, YA BAKI MIJI NA GARI MUMINI SALIHI, WANDA ZAI KULA DAKE KAMAR YANDA KK KULA DA IYAYEN KI DA 'YAN UWAN KI, DA DIK WANDA ALLAH YA HADAKI DA SHI, ITA KUMA SARKIN KALAN DANGI, INDAI DANGI TAKE SO DA GA YAU ZATA SAME SU HAR TA GODEWA ALLAH" 1 Da kudin da ta miqa masa da shi din bata san ta inda suka bi ba, a kidime ta koma mota, Kahairat dake hango su ta ja ta jikin ta tana son ta tambaye ta, ita kuma a kidime tana nuna masu wajen da abun ya faru, bakin ta sai rawa yake da hannayen ta, da jikin ta ma gaba daya, muryar ta na rawa take furta, "Ba mutum bane,.....baaa mutum baneee...,salma ba mutum bane wancan" Daga idon ta tayi daga wayar ta da ta fara downloading hotunan su na dazu da Jadwa ta fara turo mata, kada ido tayi sama ta kalli Salwa dake tsananin cikin tashin hankali, tace, "Dama ta yaya wancan mutumin zai zama mutum, ai sai dai ya fito a dangin aljanu," "Salma she is telling the trueth, ni kaina ina nan ban hango ta inda ya bi ya bar gaban Salwa ba" Driver na jin haka ya tada mota, goshin shi tini ya fara tsattsafo da zufa, gamo sukai kenan? A guje yake tafiya, bai tsaya ba sai a gidan Uncle Ibraheem, Salwa da Salma sai musu suke daga baya Salma tai banza da su, gashi kamar an mantar da Salwa abinda ya fada mata, dan gaba daya ji tai ba zata iya tuna me ya fada mata ba, ta dai san sunyi magana, kuma ya amshi kudin hannun ta, ba ta ga sanda ya amsa ba, kama hannun ta tayi ta sa a bakin ta tana ta tofa masa ayatul kursiyyu da dik addu'ar da ta sawwaqa. Koda suka shiga gidan qarfe goma na dare tayi, Mummy da Daddy na zaune suna kallon NTA, da kallo Mummy ta bisu , Salma gaida su tai ta wuce dakin su, Salwa kuwa da Khairat zama sukai suka ba su labarin me ya faru, dariya Daddy yayi, "Yara kenan, kuna da abin dariya, ta ya zaku ga mutum har ya tsaya kuyi magana sannan kuce aljani ne, dan Allah ku cire wannan a ran ku, nan Abuja bariki ne, akwai masu rufa ido, akwai mutane kala2, wasu dan su cutar da 'yan uwan su kawai suke zuwa Abuja, wasu neman kudi, ke gashi nan dai kala2, so kar ku damu kan ku, da aljani ne da bai karbi kudin hannun ki ba, dan rufa ido ne dama" You'll also like The Other CEO by ivojovi The Other CEO 46.7M 1M Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P... So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin So I Married A Rockstar - Season 3 48.1K 1.8K After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last... Overdrive by HTEllis Overdrive 132K 3K When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As... Western Heat by MustangSabby Western Heat 358K 14.8K A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f... Puck You by FlynnNovak Puck You 21.9M 588K SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra... Unholy Matrimony by xxinlove Unholy Matrimony 40.1M 1.6M Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ... The Cursed Archer by howtosellmysoul The Cursed Archer 46.2K 1.5K The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l... Cikin sauke ajiyar zuciya mai qarfi Salwa ta fara dariya sosai harda hawaye, saboda ba qaramin tsorata da tayi ba. Dariya iyayen suka fara mata, can qasan ran Uncle Ibraheem ya ji dadin samun kwanciyar hankali diyar dan uwan shi, mai son sanya kowa farin ciki, ya fada mata haka ne saboda kawai hankalin ta ya kwanta, amma shi kan shi labarin ya bashi tsoro. "Gurls, kar ku sake kaiwa dare, dik inda kuka je magrib ta gabato ku dawo gida, in gida kuka je na wasu ku tabbatar kun yi alwala kafin ku bar gidan, in zaku fita kuyi alwala, kuma kuyi addu'ar fita, haka in kun dawo kuyi addu'ar komawa gida, saboda aljanu na biye da mutum in ya fita, in bai addu'ar shiga gida ba zasu ce yauwaa yau mun samu wajen kwana, amma in kayi addu'a zasu yi baqin ciki suce yau basu da wajen kwana" "Inshaa Allahu Daddy zamu kiyaye, sai da safen ku," "Kun ci abinci ne?" "Salma dai taci, amma mu bamu ci komai ba, zamu bi kitchen mu samu abinda zamu ci muguwar yunwa muke ji, " inji Khairat. Sai d suka bi ta kitchen suka ci abinci suka qoshi sannan suka dau hanyar dakin su, suna tafe suna hirar abubuwan da suka faru yau din, a shirye suka gan ta, ta dakko ma Salwa kayan baccin ta, tana ta danna wayar ta tana murmushi, kamar wadda ta ga wanda take so. Ko magana basu mata ba Salwa ta shiga wanka, bayan ta fito khairat ma ta shiga, ta fito daure da towel, ta tafi dakin ta ta dakko kayan bacci da babban bargon ta, dan yau tare zasu kwana tsoro take ji, gadon babba ne, Salwa na zama kusa da Salma ta leqa wayar ta, wani dandasheshen matashi ta gani zagaye da wasu mutane masu kama da shi, mata da maza, suna ta murmushi, kamar a duniya ba su da damuwar komai, comment din da taga Salma ta tura ne ya sanya ta kallon ta. "Wowww beautiful family" "Ohhh ina kuma kk san wannan din?" "Ina ruwan ki? Wai me yasa kk son leqan waya ne? Ni ina shiga sabgar wayar ki ne? Bana son haka raina na baci sharewa kawai nake, ki daina min haka bana so" "Allah ya baki hakuri Uwar KALAN DANGI," "Bana son kalmar nan ta KALAN DANGI d kk yawan fada min," "Wannan kuma baki isa na baki hakurin ta ba dan kowa da ya san ki ya san daya daga cikin manyan halayen ki kenan" Duka Salma ta kai ma Salwa mai qarfi Allah ya bata sa'a ta goce, tana dariya ta dasa ma Salman duka ta sauka daga gadon da gudu, da sauri ta aje wayar ta bi ta suka hau zagaye dakin, ta kasa kama ta, "Ga shegiyar tsokana ga gudun tsiya, kamar dan ibro, (Allah ya jiqan shi)" "Ke sunan Daddy ne fa," "Banza to sunan Daddyn dan Ibro? Ba sunan shi Ibraheem ba," "Eh haka ne 'yar gidan Jalaluddeen" Nan fadan ya koma kan Khairat, sai da suka yi kaca kaca da dakin sannan suka zube a gado, suna maida numfashi, gyara kwanciyar su sukai, Salwa da Khairat sukai addu'ar bacci suka shafa, sukai ma junan su sai da safe, suka kwanta. Salma kuwa a lokacin kasuwar ta ke ci,dan kuwa socil net ta fada tsundum, daga wannan peji ta fada wannan peji sunan family din wannan kyawawan ta dauke, ta shiga Twiter ta gano su, a facebook ma ta gan su, nan dai ta koma IG ta dinga duba su, a nan ta fahimci mazauna Gomben su ne ma, wani murmushi ta sauke mai qayatarwa. "Woooww i ma so lucky i swear, garin mu daya da su, ai ko gidan uban wa suke sai mun qulla abota da mutan gidannan, irin wannan kyau haka, ga kudi, dan da ganin kayan jikin wannan babban ka san nera ta zauna," Qasa qasa take maganar, ta ci gaba da dubawa, nan ta ga yana ta replying comments din mutane, saboda kula da sabbin reply da tai suna shiga, data duba sai taga hoton babban su ne a jikin mai reply din, ta tabbata kuwa shine ya bude shafin. Zaune take tana mugun jin bacci amma dake messages din na da yawa, ba a zo kan ta ba, har ta fara gyangyadi kamar an tashe ta, ta duba wayar ta, sai taga message din shi ya shiga,ya mata reply, hannu na rawa ta duba. "U ar a beautiful gurl as well," Hoton ta da ta saka ta sake dubawa, lallai ne ba wanda zai gani bai so son ya sanya ta a idanun shi ba a ainahi, murmushi tayi, tini baccin idon ta ya wattsake. "Thanks handsome" Yarfe hannu ta fara, tana cizon faratan da babu su ma dan an yanke dazun, dabi'ar tace kawai in tana cikin damuwa ta ci hannun ta, 3 'My god me ya sa na amsa mashi harda kiran shi handsome, kar fa aji na ya yi qasa,bari na basar' Dm ta duba taga da sabon message. "Beautiful baki bacci ba?" "Hansome ban bacci ba,," 'Wayyyooo what is wrong with me? I have to sleep,kafin na kwafsa' "But i am about to" "K gud nyt, hope za a yi freindship da ni?" "Why not? U ar handsome anyway" 'Ya salammm' Da sauri ta sauka, ta kashe wayar gaba dayan ta, qirjin ta na bugawa tana jin wani irin abu na ratsa ta, wanda bata taba jin irin shi akan kowa ba, ta rintse ido, sake kunna wayar ta tayi, ta kashe data, ta shiga whatsapp, ta dinga duba messages din qawaye da kuma yan uwa, a haka bacci ya dauke ta, (batai addu'ar bacci ba, the last thing she did was karanta messages din social net). 2 *Toooo mu bari sai ta tashi daga kwana ko????zuwa anjima inshaa Allahu sai mu dora, inna ga comments din ku sun min dadi i promise u zaku samu new update anjima, infact page biyu zan dinga sambada maku kullum inshaa Allah.* by Haermeebraerh Following Ko da ta tashi daga barci, ko sallah ba tai ba ta kunna waya taga time, lokacin sallar ma ya wuce, duba labulen dakin tayi, wanda ke kadawa a hankali, sakamakon bude window da Khairat tayi, miqa tayi, sannan ta kunna data ta sauka daga gadon, Salwa ce ta shigo, dauke da waya a hannu, ganin ko sallah ma batai b ne y sa tace, "Ta shiga bandaki, in ta fito zata kira ki Ammi," Ci gaba sukai d gaisawa, sannan suka gaisa da Abban su,Salma cikin kasala ta tada sallah, nan d nan hr ta idar, ji take wani baqon lamari na ziyartar ta, dan dai ba halin ta bane qin yin sallah da nutsuwa d khushu'i, ko addu'a ba tai ba ta miqe ta dau wayar ta, Salwa ce tace mata, "Kina da matsala gaskiya, wai ace kina ji fa nake waya da Ammi amma ba zaki iya bude baki kimin magana ba, bayan kinga har wajen nan na shigo dan na hada ku a waya," Kallon ta tayi kamar zatai magana ta fasa, dan jin ta take tana cikin wani irin qunci, "Kuma daga idar da sallah kin rarumi waya,an hana ki an hana ki kinqi dainawa, meye amfanin irin wannan rayuwa ne? Ga mu muna son ki, ke 'yar uwar mu ce amma kin gwammace ki mu'amala d mutanen da baki ma sani ba" "Enough!!! Habaa, wai meye matsalar ki ne? Ina ruwan ki da ni? Tin da na tashi sai wani damuna kk da surutun ya kamata bai kamata ba, karki batan rai...so kk na kula ki? Na kula ki ko?" Zuwa tai cikin fada fada ta ringume Salwa,ta mata kiss a kunci,Salwa ture ta tayi, ranta

Chapter 2 of 17