stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
"Nace nan da kwana biyu zamu ai bance yau ba"
"Koma yaushe ne"
Tashi tayi ta fice daga dakin, shi kuwa kwanciyar shi yayi dan yayi baccin huce gajiyar shi.
Ba shi ya tashi ba sai 1:24PM, da sauri ya shiga yayi alwala ya tafi masallaci dan yana son sallah a jam'i, ko wata qasar yaje sai ya nemi masjid yake sallah, in bai samu bane yake sallah shi daya, amma in da Mummy suka je sai ya ja su, ko in suna tare da wani musulmi, sai ya ja su, baya wasa da jam'i, saboda dimbin ladan dake ciki.
Bayan ya dawo, ya ga Ubaidullah da Salwa na zaune suna kiran sauran yara a zo a ci abinci, Salwa na kallon Daddy ta dauke kan ta daga kallon Ubaidullah, Daddy zama yayi, suka gaida shi.
"Ni fa ba dan qamshin abincin nan dake inviting dina ba da sai nace na qoshi, dan abincin da kuka cika min ciki da shi dazu bai gama narkewa ba".
Dan dariya Salwa tayi, tace,
"Daddy kaci abinci da yawa ka zama kamar Abban mu"
"Ke rabani da irin jikin Abban ku, har yanzu akwai yarinta a jikin shi, yana da kyaun jikin shi, amma ni da ban kai shi tsaho ba nai murdadden jiki ai sai na koma kamar inyamuri"
Dariya sosai suke yi, Salma da ta dakko jug din zobon da ta hada ma Daddy ta na ta dariya itama, dan dik suna jin hirar tasu,ajiyewa tayi ta dauki plate ta fara zuba masa abincin kowanne kadan, saboda taji yana cewa ya qoshi,
"Daddy ai ko a gida in Salwa tayi abinci ba mai iya cewa ya qoshi, ko ni nan dana fita iya girki bana hakura sai na ci"
Wani kallo salwa ta mata, da kan ta ta fara dariya tana fadin,
"What?? Daga fadin gaskiya, sai ki dinga harara ta? Ko Mummy shaida ce rannan da na dafa mata abinci tayi ta santi, ko Mummy?"
Dan yaqe Mummy tayi, tana zaune a bangaren da kujeru suke, har yanzu bata huce ba,daga kai tayi kawai ta ci gaba da kallon ta, Uncle Ibraheem bai ce mata komai ba dan kar ta kunyata shi gaban su salma, su basu saba ganin mace na ma miji musu ba, shi kuwa in irin haka ta faru har da baqaqen maganganu ana gasa mai, sai in ya yi fushi ya mayar mata da masu zafi shima, wataran har mari yana kaiwa, to a gaban su salma ba zai iya hakan ba, dan ya na sane da irin tarbiyyar da suka samu, shi yasa yake yabon mahaifiyar su sosai, ita Mummy tana son ya mata yanda Jalaluddeen ke ma matar shi, amma ita ba zata iya yi masa kamar yanda matar Jalaluddeen ke masa ba, shima kuwa ba zai zama soko ba.
Abinci suke taci kowa na santi, Huzaifa da Salwa ke gulmar Salma qasa2 akan qaryar da tayi na cewar ta fi salwan iya girki, Salma na ganin haka ta duqa kusa da kunnen Ubaidullah tace,
"Kai wa budurwar ka magana, naga tana magana ta, na san ta da tona asiri, in ta fada na wancan uban surutun wata magana akai na zan mata ba dadi"
Dariya yayi, daboda yanda tai maganar ya san zata iya yi ma Salwa rashin M, suna hada ido da Salwa ya kada mata kai akamar ta daina.
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Khairat gyaran murya tayi
"Kun dami mutane da qusqus"
"Ke fa baki da kunya"
"Kowa yayi shiru mu ci abinci pls, me kuke koyawa qannen ku kenan?"
Shiru sukai, amma Daddy bayan ya gama maganar a ran shi bai so suka daina hirarrakin sun ba, saboda yana sake fahimtar abubuwa a tsakanin su, zargin da yake ya tabbata ainun.
A kullum Daddy sake sa masu ido yake, abinda yake hangowa na qara qarfi a ran shi, ya matsu ma ranar tafiyar su tayi.
Salma kamar wadda batai ciwo ba, saboda hankalin ta ya kwanta, a kullum tana chatting da Irfaan, da dare yana zuwa su sha soyayyar su, in yayi tafiya kuma wataran baya zuwa yana mata bayani, ta dawo da jikin ta tayi haske mai kyau kamar ba ita ba, in suna vedio call da Ammi ta gan ta sai taji dadi ya kama ta, taji zuciyar ta fess, indai zaman salman anan ne zai sa taji sauqi ita kuwa zata hakura da kewar su, Allah ya sa hakan shine ya fi alkhairi.
Ta bangaren qawayen Salma kuwa sai abinda ya qaru, Jadwa na da ciki, ta ce ma Salma ba zasu dawo ba har sai ta haihu, in ta haihu kuwa zata gan ta har Gombe, group in ba 'ya'yan manya, ko dai wasu kafaffun mata Salma bata zama, su kuma manyan da kafaffun matan kyaun ta ke sa su son yin abota da su, dik abinnan da ake Salma bata hira har yanzu a Family group,sai dai yanzu an samu sauyi akan da, shima sai in Salwa ce ta sata a magana, kuma suna kusa in ta roqe ta akan ta ansa sannan take magana.
Ranar da Daddy zasu tafi Gombe,Mummy ta tashi wai kan ta na ciwo, Daddy ya gane sarai bata son tafiyar ne, ya ce suje in sun je a wuce asibiti.
Haka ba dan ta so ba ta bishi, tayi iya yin ta ya sanar da ita akan me za ai magana yaqi, jirgi suka hau, sai Gombe.
Koda suka isa Uncle Usman ne yaje ya dauke su, Family house ya kai shi, nan suka tadda su Jalaluddeen da Uncle Isa, da matan su, bayan gaishe2, da cin abinci, suka hadu a babban parlour, sallama Uncle Ibraheem yayi, ya bude taron da addu'a sannan ya ci gaba da magana kamar haka,
"Na tara ku ne anan, ba dan komai ba sai dan na shawarta da ku akan abinda nake hasashe a tsakanin yaran mu, dan samun qarin danqon zumuntar mu,"
Shiru sikai suna sauraron shi, fuskokin su dauke da annashuwa, sun tabbata komai zai fada alkhairi ne, dan a tsaye yake akan su,a koda yaushe dan ganin ci gaban rayuwar su data iyalan su, ta kowanne fanni na rayuwa.
"Ina tunanin ko zamu hada yaran mu aure ne saboda qaruwar zumuncin mu? Amma shawara nake nema wajen ku ba umarni bane, na dawo na tadda kyakkyawar alaqa a tsakanin yaran mu, Salma da Ubaidullah, kun kuwa san a da irin rikicin dake a tsakanin su, sannan na ga Salwa da Huzaifah ma akwai kyakkyawar alaqa, Khairat kuwa dama kowa ya san Ameer din wajen Usman ke son ta, kuma itama tana son shi, sai dai har yanzu bata fadi ba, amma dikkan alamu sun nuna suna son juna, me kuka gani game da wannan shawara?"
1
Uncle Usman ne yayi magana,
"Wannan shawara taka yaya ai ko Umarni ne ta zauna, shawara ce mai kyau, kuma abar so matuqa, Allah ya sanya mana alkhairi da albarka a ciki, Nabeela ma ta wajen Isa da Sudais dina suma suna son juna, dan shekaran jiyan nan dama yake fadan yace zamu maka maganar yaran, to kuma ga wannan babbar magana mai dadin saurara"
Uncle isa yace
"Alhamdu lilLAAH wannan al'amari yamin dadi sosai,kaga shikenan in an tashi aure sai mu hada gaba daya ayi, kafin na bayan su su taso suma a sake yi, in sun hada kan su, ko in sun samu masu son su a waje, dik yanda akai daidai ne inshaa Allahu"
Shiru Jalaluddeen yayi, saboda dadin da yaji, zuciyar shi tayi rauni, idanun shi cike suke da hawaye, yaran shi har yana tunanin ko suna da baqin jinin masu son su ne, ba wanda ya taba cewa yana son su da aure sai shashanci, yanzu ga shi sun samu maza ababen kwatance, ba abinda zai ce sai godiya ga Allah, kula da halin da ya shiga Ammi tayi, hannun ta ta sa ta dafa nashi tana dan bubbugawa, kallon ta yayi suka yi ma junan su murmushi, mai gamsarwa.
"Yayah na gode maku baki daya, Allah ya tabbatar mana da zumuncin mu, ya kare mana dikkan abin qi"
"Habaa Jalal meye abin godiyar? Ai mu xamu maka godiya, saboda tarbiyyar da kuka bama yaran nan, muma tana mana amfani"
"Dik kun gama? Nace kun gama? To ni na haifi Ubaidullah da Huxaifah, na ce ban amince ba, ban amince ba, sai naga ya za ai ayi wannan auren"...........
Toooohhhh, me kuka ce ku kuma hadin ya maku?
Ubaidullah da Salma
Huzaifah da salwa
Ameer da Khairat
Nabeela da Sudai.KALAN DANGI..PAGE 23
910 83 5
by Haermeebraerh
Following
"Wannan wanne irin magana kk Mummyn Khairat? Dan Allah ki hakuri ki bar daga murya haka, abinda suka yanke mai kyau ne inshaa Allahu, mu sanya albarka a matsayin mu na iyaye mata shikenan abinda yaran mu da mazan mu ke buqata a wajen mu,"
"Dalla matsa ki rufewa mutane baki, tinda yaran ki zasu samu gidan hutu, kuma zasu samu mazan da kan ku nemo sai kun wahala ai dole kice haka, ba wan......"
"Keeeee Mara mutunci, mara da'a da girmama mijin ta, ki min shiru kafin ki sa na aikata abinda ni dake zamu yi dana sani yanzun nan,"
"Ka aikata din, nace ka aikata, ka dade kayi jinkiri baka aikata ba, wannan wanne irin zalunci ne, ni banda ta cewa akan yarana, ni na dau cikin su wata tara, na shayar da su shekara daidai da rabi, sai yanzu sama.ta ka kawai komai zakai ba zakai shawara da ni ba, sai qannen ka sun gama sanin komai sannan nake sani, ko mu sani a tare, su suka haifarmin yaran? Ko kuwa su ska masu wahala har suka girma"
"Ke da kk taqamar za a auri yaran ki gidan hutu da baki auri miji mai arziqi kama ta ba zaki huta? Wane uban ki ko wace uwarki a Nigeria? A wanne irin gida na dakko ki? Salma da Salwa jini na ne su, dukiyata da abinda na mallaka suma nasu ne, ke fa? Yau kina jin inna rabu dake zaki samu sisina? Ki kiyayi bakin ki akan rashin mutuncin da zaki furta, baki san wanda za a mayar maki ba, ki tashi yau yau mu koma, in kuma kk bari raina yafi haka baci sai dai ki koma gidan ku"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Yayah dan girman Allah, da son Annabi ku bar magana haka, in kuna irin wannan a gaban mu wanne misali kuke bamu? Ga yara muna da su, dan Allah kuyi hakuri, idan hadin nan zai zama zai taba zumuncin mu a hakura a barshi hawai shine zai fi"
"Shikenan, ai da na zaci hankalin ka na banza ne, ashe yana aiki a ko ina, maganar ka ita yafi dacewa abi, a hakura da wannan hadin kawai"
"Jajal bana son na sake jin bakin ka a wannan maganar, ni Ibraheem na yanke hukunci, Isa Usman ko bayan raina wannan auren ku tabbatar an daura shi, ba fashi, ko ba ku, ku bar ma wasu wasici, in kika ga ba ai auren nan ba Allah bai hukunta su din mamallakan juna su bane, shashasha kawai, yara qanana sun fiki tinani, dibi yanda macen kirki tai shiru tana jin maganganun da ake zartarwa, ta baki shawarar ki kama harshen ki amma ba zaki iya ba, saboda harshen ki na da kaifi kamar wuqa,sannan ki dinga kishi da jin haushin son da mijin ta yake mata, waye ba zai so mace mai nutsuwa haka ba?"
Cike da fushi Mummy ta tashi, ta dau jakar ta ta fice a gidan, adaidaita sahu ta dauka sai airport, ta gama qudurta a yau din zata auno su salma Gombe, sun gama zaman gidan ta.
Daddy kuwa da bai san me take shiryawa ba, ya zauna ya na ba ma qannen shi hakurin halayyar da suka nuna da shi da matar shi.
Shawara qannen nashi suka bashi akan ya daina biye mata suna kace nace a bainar mutane.
Matan kuwa koda suka shiga ciki sai kowa ta bata rai, suka hade ma Ammi kai, sai qusqus suke bata jin me suke fada, tashi sukai ma dan su bar mata dakin, tare da doka tsaki, matar Uncle isa tace,
"Allah dai ya wadaran naka ya lalace, wai mutum bai da aiki sai kawo matsala a zuri'a,Allah ya mana maganin masu son abin duniya"
"Ameen, Allah ya ganar da ku gaskiya, na tabbata inda cewa akai Ubaidullah ko Huzaifah ne zai auri Saheebah, ba zaki hana ba, murna zaki, dan haka ba zan boye maku ba ina cike da farin ciki da jin dadin wannan hadin, zargin da kuke kuma dan kudi muke son hada zuri'ar nan, kun san mahaifin su ba talaka bane,ko bai kai Yayah arziqi ba ba za a ce mana matalauta ba, mun godewa Allah"
Dik sun san maganar ta gaskiya ne dan haka sukai shiru, ga shi cikin nutsuwa da jera kalamai ta masu maganar amma ta shige su.
Fita sukai suna qananan maganganun da taqi tanka masu, tinda ta fadi wanda ya fi mata amfani.
You'll also like
The Other CEO by ivojovi
The Other CEO
46.7M
1M
Grief-stricken over the death of the boss who was like a father to her, Olivia Bailey is left to deal with the aftermath--the arrival of his dashing but estranged son, P...
So I Married A Rockstar - Season 3 by Bella_Higgin
So I Married A Rockstar - Season 3
48.1K
1.8K
After getting out of an emotionally abusive relationship, Nola Collins sees the chance to reinvent herself after landing a job as PA for rockstar Darius Keller. The last...
Overdrive by HTEllis
Overdrive
132K
3K
When Chef Margot loses her beloved restaurant to her cheating ex-fiance, her best friend, single dad Nathan, steps in with an unexpected offer to help her start over. As...
Western Heat by MustangSabby
Western Heat
358K
14.8K
A fish-out-of-water story about a New York City chef who inherits a ranch, discovers a family he never knew, and finds unexpected love with a fiercely loyal woman. For f...
Puck You by FlynnNovak
Puck You
21.9M
588K
SOON TO BE PUBLISHED BY W BY WATTPAD BOOKS! Grace wants to prove herself by making the men's hockey team at her new school. Will a rivalry with the captain - or an attra...
Unholy Matrimony by xxinlove
Unholy Matrimony
40.1M
1.6M
Tobias and Talia are complete opposites, yet thrown together in an arranged marriage. Can they navigate married life in the wake of a terrible tragedy? ...
The Cursed Archer by howtosellmysoul
The Cursed Archer
46.2K
1.5K
The forbidden romance between a prince and a stable boy is tested once again when dark forces from their ancestral bloodlines are unleashed, threatening not only their l...
Sai bayan azahar kowa ya kama hanyar komawa gidan shi, Jalaluddeen zasu zauna dan Uncle Ibraheem yace ba yanzu zai koma ba, dama in sukai tafiya suka dawo irin haka sukan yi sati kan su koma bakin aiki, dan haka anan zai satin shi, hankalin shi ya kwanta.
Girki Ammi ta masu, ta kai masu nasu,ta dau nata tayi daki, suna cikin cin abincin wayar Daddy tai ringing, ya dauka, miqewa tsaye yayi ya ce,
"Ban gane ta na masifa ba sai su salwa sun bar gidan, dama nan tayo? To ku sani in yaran nan suka bar gidannan ka fada mata a bakin nata auren, ba zan dawo ba sai juma'a, ka tabbatar ka sanar mata, zata bar gidan, suna da 'yancin zama ita ce bata da shi, kai mata wayar ka bude speeker taji"
Da sauri kuwa Huzaifah ya kai mata wayar, ta hargitsa gidan tana ta masifa,kalaman Daddy ne suka daki kunnen ta,jikin ta har rawa yake ta amshe wayar ta buga da qasa........
*Waiwaye*
Ko d ta isa gidan ta tarar Salwa na ma yara home work, Salma kuwa na kwance a doguwar kujera tana chatting da Sabuwar qawar ta mai suna Sa'adatu, tana ta bata labarin India, dan a can take da zama tana karatu.
Huzaifah na zaune kan kujerar dake kallon ta Salman lokaci zuwa lokaci yana tsokanar ta yana mata magana.
Ubaidullah baya nan ya tafi aiki.
Khairat na kitchen tana taya masu aiki girki.
Da qarfi ta bude qofar shiga Palourn, sai da yaran suka tsorata, har da manyan ma, dan kuwa Salma sai da ta hantsilo wayar ta ta fadi qasa.
Daga kai kowa yayi ya kalli inda Mummy ta ke, da sauri Huzaifah ya je gare ta,
"Mummy lfy? Ina Daddy? Me ya same ku?"
Ture shi tayi gefe, taje gaban salwa dake riqe da Pen tana ma Abdulwadood misalin yanda zai Homework din shi,ta amshe pen din ta yi wurgi da shi, sannan ta kama hannun Salwa taje gaban Salma ma ta damaqi hannun ta, ta fara magana cikin bacin rai.
"Tin da nake da Ibraheem bai taba goranta min akan arziqi ba sai yau, a dalilin ku,har kiran waye ubana da uwata yayi, a sanadin ku mijina ya ci min mutunci a gaban dangin shi, dan haka dole ne sai kun bar min gida,ba yanda za ai ku zo cin arziqi ku aure min yara, dama saboda ku auri yarana iyayen ku suka kawo ku? To bari kuji, ba wadda ta isa dna ya aura a cikin ku, gadon munafurci"
(A wannan lokacin Huzaifah ya kira Daddy)
Ko da taji me Daddyn yace shine ta fasa wayar Huzaifan ta haye sama, wani irin zafi qirjin ta yake yi, a hankali ta kwanta ta rufe idanun ta, hango komai da ya faru ta dinga yi, ranta na sauqin zafin da yake, magana qarama ta koma gingimemiya, yau ita ake ma ikirarin zata bar gida, lallai da sakel, yaran Ameenatu da Jalaluddeen sun zame mata musiba a rayuwa.
Hawaye ne masu dumi suke saukar mata, bata taba zaton yaran ta za su bige da auren yaran Jalaluddeen ba, ita dai haka nan bata son shi, ko dan ya fita matsayi wajen mijin ta ne oho, dan kuwa in washh tace Jalaluddeen yace washh sai Uncle Ibraheem ya tabbatar Jalal bai da damuwar komai zai dawo gare ta.
1
A can qasa kuwa Salma har ta haye ta hada kayan ta, idanun nan sun yi jawur, su za a kora ? Indai gida ne ai suna da shi suma koda kuwa bai kai wannan ba sunan shi gidan su salma.
"Salma dan Allah ki hakuri ki koma, kin dai ji abinda Daddy yace ko? Me kk zato zai ji in yaji labarin ke kin qi bin umarnin shi kin bar gidan?"
"Ni fa yau a gidan mu zan kwana, meye kuka aje a gidan ku wanda ake mana wannan rashin mutuncin? Wa yace mata wani na son ku har d ake cewa zamu aure ku saboda wani abu? Ko a qafa aka dauran dayan ku zan kunce na gudu, balle har na so shi, ina da wanda nake so, ina da mijin aure, dan haka ta jiqa ku ta shanye"
Fauuu taji saukar mari a fuskar ta, kama kuncin tayi ta kalli inda marin ya fito, Salwa ce idon ta na hawayen jin zafin marin da ta wa Salman, amma haka ta kauda wannan tinanin ta fara magana cikin hawaye,
"Tarbiyyar da aka maki kenan ki dinga fadin baqaqen kalamai a kan manyan ki? In Ammi ko Abba suka ji kalaman ki kina da yaqinin ba zasuji kin ci mutuncin tarbiyyar da suka baki ba,ko me zaki kina duba kalaman ki, sannan ba in da zaki sai Daddy ya amince mu tafi, ba zamu watsa masa qasa a ido ba ta hanyar qin bin umarnin shi, kowa ya san domin Allah da zumunci muka zo ba dan wani abu ba, dauki muje"
Daukan akwatin Salma tayi idan ta ya kada yayi jawur, tabbas Salwa tayi gaskiya, amma Mummy zata g rashin mutunci iya rashin mutunci.
Koda suka shiga dakin, rufewa sukai, Salwa ta kwanta ranta na mata suya, Khairat tayi ta bugawa akan su barta ta shiga amma basu bude ba.
Dole ta hakura ta koma kitchen, kusan masu aiki ne suka qarasa girkin, dan kuwa hankalin ta na kan 'yan uwan nata.
Sai dare Ubaidullah ya dawo,daidai lokacin cin abincin dare, Salwa tayi wanka tayi kwalliya kamar ba abinda ya faru,Salma ma tayi wanka amma ba wata kwalliya, fuskar nan kamar an yi barin ruwan zafi akai saboda bata rai da tai.
Huzaifah ya rasa me zai ce masu ma, dan gaba daya sai yake jin nauyin su, Khairat kuwa data gan su da sauri taje ta rungume su, Salma tura ta gefe tayi ta xauna akujerar dake kallon ta Mummy, kafe ta da ido tayi, kafin daga baya ta saki wani shu'umin murmushi.
Irfaan da ke taya Salma fushi saboda wulaqancin da Mummy ta mata yana tsaye kusa da kujarar Mummy, sai da aka fara cin abinci kowa ya maida hankali wajen cin abinci Mummy ta fara tari, shinkafa ta wuce mata hanci,ido ya mata jawur, yana zubar da hawaye, ga shi sai tari take tana kaki tana son ta fito abu ya gagara, Salma sai dariya take ita da Irfaan, wanda ita kadai ke ganin shi.
Ubaidullah da bai san me ya faru ba ya kalli Salma cikin bacin rai, ya yi kwafa, 'mai hali dama baya fasawa ai'.
Da kyar aka samu ta dawo daidai, ruwa kuwa sai da ta shanye jug daya, sai haki take, tana faman zubda hawayen wahala, Salwa ce ta kalli Salma tare da yi mata nuni akan ta daina dariyar nan.
Murguda baki tayi ta ci gaba da cin abincin ta.
Ubaidullah dik ya damu, ga haushin Salma da yake ji qiri2 ta nuna bata damu da mahaifiyar su b.
Koda aka gama cin abincin ya koma dakin shi, Daddy ya kira shi, ya sanar da shi dik abinda ya faru, sannan yace ya dora masa alhakin kula da gidan har sai ya dawo.
Mamaki sosai ya kama Ubaidullah, akan wanne hujja Mummy take qin wannan hadin, ai a bun alkhairi ne da farin ciki, miqewa yayi ya nufi dakin ta,
Waya take da matar Uncle Usman,
"Habaaa ke kuwa Rakiya, ya zaki ce na bari a yi wannan hadin? Kina fa ji yace Salma zai hada da Ubaidu, wannan yarinyar mara kunya da mutunci, Huzaifah kuma da Salwa, ni dama Salwan ya ba Ubaidu, dan shi ne babba, kuma ni ban da damuwa da ita, amma kinga wannan mara kunyar, in ta mallake maka da kamar yanda uwar ta tayi ma uban su kai da ka ga dan naka ma sai ta yarda"
Kan Ubaidullah ne ya sara, kodai bai ji daidai bane, wanne irin Ubaidullah da Salma kuma? Salwa da Huzaifah? Annan wanne irin kwado ne????
1
Sai ka jira Daddy ya dawo ka tambaye shi, ka tambayen ni😏KALAN DANGI.....PAGE 24
988 86 3
by Haermeebraerh
Following
Haule ke ta goge2n parlour, bayan ta kammala aje abincin safe a kan qaton table din da mutanen familyn ke zama, Uncle Isa da Uncle Usman sun zo da safen dan a karya da su, sannan su lallashi yayan nasu akan ya koma gidan shi, hakan ai sai ya zama kamar yaji yayi.
Bayan kammala cin abincin su ne suka sanar da shi abinda ya kawo su, murmushi ya yi sannan yace,
"A halayyar da Mummyn Khairat ke nunawa in nai yajin ma ai ba laifi bane, in ina zaune inda take zan iya yanke hukunci a cikin fushi, bana son haka ta kasance, ina buqatar hutu, ko aikin da nake yi bata gani balle a bani farin cikin da zan samu hutu a cikin gida na, ita kuwa na wadata ta da komai, shara wannan bata yi, komai masu aiki keyi, kula da yara masu aiki keyi, sai manyan ke taimaka ma qannen su, me take so?"
"Dik da haka Yayah kai magidanci ne hakuri da juriya kuwa yana wajen mu, dole mu zama masu laushi a dik sanda mata sukai tauri saboda kar tauri da tauri su yi karo, kowanne zai ji zafi, kayi hakuri Yayah,"
Shiru yayi sannan ya daga kai ya kalle su, shi din ma dikan su shi suke kallo, Ammi ce ta shiga dauke da trey a hannun ta ta jera qananun cups na tea, aje masu tayi sannan ta koma gefe ta gaishe da yayun mijin nata, bayan sun amsa ta tambayi iyalan su, sannan ta shiga ciki,
"Wato abinda matan mu gaba daya suka kasa ganewa shine, halayya irin ta Ameenatu ita ta dace da su, amma sun qi koya sun sa ma kan su dan banzan kishi akan ta, Allah ya shirya mana su, kar ku damu yau zan koma in Allah ya yarda, Jajal in ba abinda kk ina son muje da ku, su Salma su gan ku kuma ku gan su, kun kwana biyu baku hadu ba,"
"Yah ba komai, zan je can wajen aiki na naga meke tafiya sai na dawo mu je
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 17