Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KALAN DANGI Marubuciya Hamida Sunusi Ahmad (Haermeebraerh) | 09031416423 Compiled by Shuraihu Usman Zaune suke a dakin nasu madaidaici, mai dauke da qatuwar katifar da ta sha gyara, sai madaidaiciyar kujerar daki guda biyu, carpet ne a qasan kujerun, ruwan qasa, sai jakunkunan su dake rataye a jikin wani qarfe dake jikin windown dakin nasu. Salwa ke ta danna waya tana comment akan gaisuwar da babban yayan su a dika familyn ya aiko da fatan alkhairi, tin da ta amsa sauran dake maqale suka fito aka fara hira, suna yi sina dariya, Salma ce ta kalli Salwa tace, "Ke dalla malama kun dami mutane da chatting, sai cika ma mutane waya kuke da hira, shi Yah Ubaidullah dinnan in ya fara surutu kamar wani kanari," Ci gaba tai da duba hotunan qawayen ta da ta ke ta kalla a status tana yabawa. Tsam Salwa ta miqe taje gaban ta, leqa wayar da ke hannun ta tayi, taga yanda take ta zubama qawar ta yabo akan hoton da suka dauka da familyn ta a qasa mai tsarki, "Hummm Salma wato kina ban mamaki, wai ace ke ba zaki taba magana a family group ba, amma group din qawayen ki sai ku wuni kuna hirar abin duniya wanda ke baki da shi, amma su sunci sun tada kai, yayun mu da qannen mu suyi ta neman ki, amma ki banza da su kamar baki gani ba, dangin wasu sun fi naki, ji yanda kk ta kwarara wa Ilham yabo tana sa maki hmmm da Koh kina ta surutu ko a jikin ki," "Uban wa yace ki duban waya? Ba zan magana acan din ba, bari ma ki gani," Shiga family group din su tayi, ta shiga Icon, nan da nan ta duba qasan jerin sunayen ahalin nta, ta yi left, 1 "Sai me kuma?" "Sai nace Allah ya shirye ki, dan kuwa kina buqatar shiriya,sau nawa zaki fita a group dinnan ne wai ke?" "Sau iya yanda kk maida ni, me shegen iyayi kawai," "To kaji kun fara? Ni ban taba ganin yaran da abu qanqani ke sa su fada ba sai ku, ga ku 'yan uwan juna, tare kuka zauna a ciki, na haife ku rana daya, seconds ne tsakanin ku amma ji kuke kamar ku shaqe juna akan abu qalilan, ya Allah ya shirya min ku," Salma ce ta bude baki dan yin magana Ammin su ta dakatar da ita, "Salma kin kammala aikin da na saka ki?" "Eh Ammi, na gama tatar, na mayar bokitin kunun yana kitchen na rufe,akwai abinda za a maki ne kan mu kwanta?" "Allah ya maki albarka, Allah ya muku albarka dika, ya shirya min ku hanya madaidaiciya, Allah ya sa ku hada kan ku ku daina yawan fada," "Ameen Ammin mu, ai kema kin san bamu fada sai in an tabo wannan uwar KALAN DANGIN ne akan KALAN DANGIN da take, yanzu zakiji kamar ta daga mana rufin kwanon gidannan" "Kan ki ake ji," Cikin murmushi Ammin su ta masu sai da safe ta rufe qofa ta koma dakin ta. Kwance yake ya yi addu'a yana kallon qofa, ko da ta shigo bakin ta dauke da sallama, ta hau cire dankwalin ta tana ninkewa, tana ci gaba da cire kayan jikin ta take ma mijin nata magana. "Wato halin Salma da Salwa na ban mamaki, ga su dai 'yan biyu amma kowa da halin ta, kuma kowa da ra'ayin ta, gashi akan abu qalilan sai ka ga sun kacame da fada" "Haka Allah ke ikon shi Amina, shi yasa a koda yaushe kk ji ina maki nasiha akan karki gajiya, ki dinga nema masu shiriya wajen Allah, nima ba zan gaji ba inshaa Allahu, ta ho nan na maki tausa, na san kin gaji," Murmushi tayi tare da kallon cikin idanun shi, ya bi jikin ta da kallon so da qauna, dik da shekarun da sukai a tare har yanzu kallon masoyiyar shi daya taba gani shekaru ashirin da uku da suka wuce yake mata, ita din ma haka, rigar baccin dake jikin ta mai kyau ya taba, "Wannan itama sabuwa ce ko? Kina burge ni, kusan ba a yin wata biyu baki sauya sabon abu ba, wataran ma a wata sai ki sauya abu sau biyu, ko uku, a gaskiya ke ta daban ce Amee" Jin ya kira ta da sunan da yake kiran ta tin suna saurayi da budurwa ya qara mata jin dadi da qaunar mijin nata, "Komai nake saboda kai ne my Jalal" Rungume ta yayi, yana matsa mata hannayen ta, zuwa yatsun ta, ba kadan ba taji dadin hakan saboda jikin ta ciwo yake sosai, yau sakwara ta daka masu, ko su Salwa bata bari sun taya ta ba. 1 Washegari Salma tin safe take shiri, gaban ta na faduwar abinda take so ta tambayi Ammin su........ Assalamu alaikum, makaranta novels dina, ga sabo nan ya kunno kai, ku bani kwarin guiwa da comments din ku da votes, inshaa Allahu zaku ga typing kullum, and for those that ar reading my other novels here on wattpad, inshaa Allahu ku ci gaba da bi na, sanda na samu time sosai xan ci gaba fa sabunta maku rubutun inshaa Allahu. Thank u. by Haermeebraerh Following Share Ta rasa yanda zata gabatar d buqatar ta wajen iyayen nata, zaune take gaban jakar da ta hada, wacce kayan ta na can qasan akwati suke ciki, sai cin farcen hannun ta take, tana tinanin mafita, Salwa ce ta shig dauke da jug da qananan cups sai plate mai dauke da qosai, ta ajiye, ta kalli 'yar uwar ta ta da tai nisa a tini, kada kai tayi ta sake ficewa. + Wani plate ne a hannun ta wanda yake dauke da dafaffiyar indomie da ta sha kayan lambu da kifi, sai da faffen kwai a sama, aje wa tayi, still Salma na can duniyar tinani. Dan taba ta tayi tare da shafa gefen fuskar ta, cikin kulawa tace, "Lfy kk kuwa Salma? Meye damuwar ki?" Sanin halin Salwa na tausayi d son ta ya sa tai rau rau da idanu, kamar zatayi kuka, ta ce, "Dan Allah ki taimaka min abarni zuwa Abuja, kinga bikin Jadwa ya taso, kuma jibi za a fara, Ammi ba zata bari naje ba, in banje ba girmana zai fadi wajen qawayena, tinda na dau alqawarin zuwa ya kamata ace ina can yau ko gobe,ki taimaka min" 1 Kuka sosai ta sata rungume Salwa, Salwa da kukan 'yar uwar ta ta ke taba zuciyar ta ta shafa bayan ta tace, "Amma kin san dai ba zasu barki zuwa bikin qawar da kuka hadu a IG ba ko? A gaskiya Salwa ina son ki bana son halayen da kk yi na KALAN DANGIN nan, watarana kar ki fada inda ba zaki iya fita ba" "Amma dai kin san mun fi shekara uku muna tare, ko Ammi ta san ta, tun kan mu gama ND din mu muke tare lokacin itama tana nata karatun, gashi yanzu ta kammala za ai auren ta, ba abinda bata sani ba game dani, nima kuma na san komai nata, dan Allah ki sa baki," "Salma ko na sa baki in Ammi bata yarda ba Ko Abba ya yarda ba inda zaki, kin san d wannan ko?" "Na sani, ke kuma Ammi na jin maganar ki, ki sa baki plssss sweetheart" "K ya isa ba sai kin min dadin baki ba, jiya akan ruf sai da kk min rashin mutunci tsakiyar dare, yanzu zaki wani kirani Sweetheart,oya in kina son na sa baki a tafiyar ki sai ki zauna ki ci abinci, amma dole ki bari tafiyar ya zama zuwa gobe zakiyi ta," "Habaa Salwa gobe kuma? Wanne irin gobe na shirya kaya yau fa," "Ke kk fara fada, ko yau ko gobe, dan haka sai gobe," Tura baki tai ta tura jakar gefe, ta zauna a qasa, suka fara cin abinci, ita ce mai cin indomie, salwa mai cin koko d qosan da ya sha yaji mai dadin gaske, kokon kan shi ya sha madara ga sugar yaji, amma haka Salma take qin sha, wai ita Allah ya kiyaye ta sha koko. Sai da suka ci suka qoshi suka fidda kwanuka, suka hau wanke2, Abban su ne ya fito sanye da dakakkiyar shadda, ya sha hula kalar kayan shi, takalmin shi kalar kayan, sai zabga qamshi yake, Ammi na gefen shi itama ta sha kwalliyar ta daidai misali, kwalliyar safe, doguwar riga ce a jikin ta, ta material wadda aka ma dinki irin na 'yan mata, mace ce bafulata mai kyau, amma bata da hasken fata, mijin ta ne mai haske, dan haka ko Salma da Salwa ma daya tafi daya haske kadan. Riqe take da jakar shi, suna magana, cikin so da qauna, ganin yaran nasu ne ya sa suka raba hannayen su dake sarqafe dana juna, Salma ce da bata gaida Abban ba ta isa gaban shi, ta kama hannin shi tai kissing, sannan ta gaida shi, amsawa yayi cikin fara'a, da qaunar diyar tashi, ya dafa kan ta yana shafawa, "Kin tashi lfy? Meke faruwa yau baki zo gaida mu ba, 'yar uwar ki ce kawai take ta kaiwa da kawowa, ina fatan lfy kk?" "Abba ga ta nan dai, dan kuwa so take taje Abuja, ta rasa yanda zata fada maku, shine take ta damuwa harda su kuka, yau 'yan zumuncin sun tashi," "Masha Allahu, lallai Allah abin godiya ne, ya amsa mana addu'ar mu, Salma da bata son shiga dangi yau ana son zuwa Abuja," "Ehh Ammi, ai sai ma kinga yanda take tayi dazu, sai da na duba ta na tabbatar lfy take," Dariya suka sanya dikan su, Abban ya kalle ta, "Gaskiya naji dadi, dan haka ku shirya ke da 'yar uwar ki kuje, in kunje ku gaida min dan uwana, Allah ya qara maku zumunci, ku kare mutuncin ku, kuji tsoron Allah a dikkan abinda zaku aikata.... "ALLAH YANA GANIN MU" A tare suka qarasa, murmushi yayi, sannan yace, "Zaku ga kullum in zaku fita tin kuna yara ina yawan fada maku hakan, ko bajima ko ba dade zai maku amfani, akwai sanda wani abu mara kyau zai shiga kan ka, amma da ka tina kalmar da ake nanata maka kullum na kaji tsoron Allah, zakaji ka hakura da abun, ni shaida ne, ga ta nan, kullum sai ta fada min in zan fita, kune baku sani ba, amma ni na san amfain kalmar," "Abba amma yau zamu tafi ko?" "Saurin me ake? Sai gobe zaku," Daga hannayen shi yayi ya kalle su, "Kunji me boss tace, dole abi," Dariya suka yi suna rife vaki, Ammi kuma ta hade fuska ga murmushi boye a cikin bata fuskan da tai, ta kalle shi da kallon bana son tsokana. Amsar jakar shi yayi, suka masa fatan alkhairi, ya fice. Motar shi ya shiga ya tada ta sai kamfanin shi da ake sarrafa katakwaye zuwa kayan daki, gado, kujeru, tables,sai bangaren saida katifu, infact dik wani abu da ake sanyawa a gida, daidai misali suna saida shi, SALMA & SALWA FUNITURE. Cikin farin ciki Salma ta ci gaba da aikin gidan, ranta kwal, bayan ta gama ta hau online, ta ke sanar da Jadwa zata samu zuwa bikin ta, amma gidan uncle din su aka yarje mata taje, dan haka ko tazo ba a wajen su xata zauna ba. Jadwa taji dadi sosai, dan tana son Salma ne saboda kyaun ta, da iya daukan hoto da turancin ta, sannan ga muryar ta in suna magana kamar ana busa sarewa, kaii Salma ta hadu a cewar Jadwa qawar kece raini ce, zata fidda ta kunya a qawayen ta da ma wasu 'yan uwan ta. Ranar kuwa tsabar farin ciki haka Salma ta dinga hotuna da kaya masu kyau, da tsada tana sanyawa a IG da status na whatsapp, tana fadin 'Abuja on my mind...' ko ta saka 'Abuja loading...' Wasu daga qawayen ta 'yan qarya da suka hadu a social net mazauna Abuja sai roqon ta suke akan taje masu, tana ta murna, tana jin kan ta wata salamburuti😂 ga messages din yaran Uncle Ibrahim tana gani suna murnar zuwan ta sai ta karanta ta tabe baki ta wuce, ko amsawa bata yi. 1 Salwa ma ta hada kayan ta kusan dik wanda Salma ta diba itama shi ta diba, hatta da abun hannu ko zobe iri daya suke sanyawa, dake hasken nasu ma ba kowa ke gano su ta nan ba, in sukai shiga iri daya. Ammi haka nan taji zuciyar ta na tsinkewa in ta tina yaran ta zasuyi tafiyar nan, abinda bata taba ji ba kenan game da su in zasuyi tafiya, kwantawa ta yi baccin tsakanin azahar zuwa la'asar, mafarki tayi mara kyau akan tafiyar yaran nata, amma ta kasa tantance me ta gani, tayi iya qoqarin ta dan tina me ta gani amma ta kasa, zufa kawai ke yanko mata, miqewa tayi ta nufi dakin su dan ta sanar da su an fasa tafiyar nan.......... 1 Ikon Allah wai na kwance ya fadi... by Haermeebraerh Following Kwance Salma take, tana ta danna waya tana chatting da qawayen ta 'yan gayu, Salwa kuwa na waya da Khairat wadda take sa'ar suce daya daga cikin yaran Uncle Ibraheem, suna magana akan zuwan nasu, Salwa na tabbatar masu da gaskiyar maganar, ta sanya a handsfree, tana zaune gaban Salma, sai alama take mata da suyi magana, ta dauke kai, ita bata son yaran su ga tana shige masu su zaci ko dan sunga uban su nada ariqi ne yasa, (amma zata shigewa bare, koda kuwa haduwa social net ne) jin yanda yaran ke ta murna ne ya dakatar da Ammi, rintse ido tayi dan tana son dai na jin faduwar da gaban ta ke yi,amma har yanzu shiru. 'Ba zan iya hana yaran nan zuwa ba, musamman da Salw ta tabbatar masu da hakan, kowa ya san ta da gaskiya da cika alqawari, zan hakura na miqawa Allah lamarin abinda zai tunkare mu,Allah ka sanya wannan tafiyar ta zama alkhairi,' Komawa daki tayi ta shiga bandaki tai alwala ta zauna tana karanta qur'ani, kafin a kira sallar la'asar. Ta kuwa samu sauqi sosai, sai taji zuciyar ta wasai, dan haka bayan tayi sallah, ta sa ta gyara gyada, ta soye ta mai yawa sosai, matar Uncle Ibraheem Zulfa'u na son gyada, dik da ba wani mutunci suke ba, amma ita Ammi har ran ta tana son dik matan 'yan uwan mijin ta, da 'yan uwan nashi tsakani da Allah. Qiyayyar da suke mata ta samo asali ne ta yanda suka ga mijin ta yana haba2 da ita, akan ta zai iya batawa da kowa, dan kuwa iyayen shi kafin su rasu mutanen Gombe state ne, mazauna nan cikin garin Dukku, iyaye da kakanni dik a cikin garin suke, sun qi auren su sosai, kasancewar su masu hali, ita kuwa dangin ta ba masu hali bane, gata marainiya, a wajen kawun ta take da zama, Jalaludden ya kafe ya nace, aka kada aka rawa, yace shi ita yake so, gashi iyakar primary ta yi bata samu ci gaba bama, sai da sukai aure ya sata taci gaba da karatun, da kyar Yyan shi Ibraheem ya ja hankalin iyayen su suka aura masa ita, wanda ba a jima ba da auren suka rasu sakamakon gobara da ta tashi a gidan su da tsakaddare. Matar Uncle Ibraheem da yaran ta ke kiran ta da Mummy, da matar Uncle Isa, Sai matar Uncle Usman, sunyi naci akan in ma wajen wani malamin take zuwa ta kaisu, suma su samu shiga irin ta ta, ta masu bayani iyakar iyawar ta, akan ba inda take zuwa da ya wuce mata wajen ubangijin ta, wato ibada, da hakuri, kauda kai, juriya, tsafta, iya girki, iya yi ma yara tarbiyya, iya kalamai, shagwaba, da dai dik wani mataki na zama mace ta gari, har yanzu ta kasa convincing din su akan iya abinda ta riqa kenan, dan haka suka hade mata kai, ba safai ma ake abu su sanar da ita ba, sai dai taji wajen mijin nata, sannan a yanda suka dauki rayuwa, da tsauri, ita ba haka abun yake ba a wajen ta. Wannan kenan..... Yau tin da sassafe, Salma ta tashi, ta fesa wanka, Salwa kuwa tana can tana taya Ammin su aikin daya kamata ta mata in basu nan ta huta, cikin sauri ta shige dakin nasu ta fada bandaki, dan yin wanka, zaune taga Salma a kujera, tana ta kashe hoto, sai da tayi masu kyau, sannan ta fara turawa IG, kowa ya gani sai ya yaba, kan ta take ji kamar zai fasa dakin dan girma. A gurguje Salwa ta shirya cikin irin shigar Salma, dogon skirt, mai fadi sosai, da riga mai dogon hannu, sai suka dora wata a sama, wadda ake ce ma boyfreind jacket. Kalar skirt din, sai mayafi da suka rufe gashin su mai kyau da shi, sukai rolling iri daya, ba kwalliya fuskar Salwa, amma Salm tasha ado, sai qamshi mai sanyi ke tashi a jikin su, dan hatta da turare iri daya suke amfani da shi. Takalma masu dan tsini suka saka, kalar rigar su ta ciki, jakar su ma kalar takalman su, kowa riqe take da akwatin ta, suka fito, "Ohhh ni kam ban san ya zan da wannan baqar dabi'ar taku ta qin cin abinci in zakuyi tafiya ba,sai mutum ya zauna da yunwa?" "Ammi kar ki damu, inshaa Allahu da munje zamu ci abinci, na san Khairat ta aje mana abinda zamuci, kar kiji komai," "To Allah ya tsare ku, ya kai ku lfy, ya dawo da ku lfy, kun dai ji na fada maku, sati daya zakuyi, kar a haura, Allah ya maku albarka, ya kare ku daga dikkan abin qi," "Yauwa ke kuma Salma, bikin da kk ce zaki, kar ki sake ki tafi ke daya, ga 'yar uwar ki nan, dik inda kk saka qafa ta aje ta ta nan," "Abbaaaa bafa ta san ta ba ni kadai na san ta," "Sai su san juna,in kuma ba zaki da ita ba ki fadan yanzu mu hana ki zuwa bikin" "Xani da ita" Cikin tura baki ta fadi hakan, "To maza ku tashi muje, na aje ku tasha," Miqewa sukai suka rungume mahaifiyar su, ji take kamar in sun tafi ba zasu dawo ba, har da hawaye taji yana saukar mata, girgiza mata kai Salwa tayi, "Habaa Ammi, sai ki sa muji bamu son tafiyar ai, ki mana fatan alkhairi," "Fatan alkhairi na na tare da ku, a koda yaushe," "Sai mun dawo," A tare sukai kissing kuncin ta suka fice. A tasha Abba ya kama masu kujerun baya dika, yanda zasu sake, sannan ya qara masu kudi akan wanda ya basu, ji yake kamar ya aje aikin komai ya kaisu da kan shi, amma ba zai yu ba hakan, yau akwai aikin da yake gaban shi babba a kampanin shi. Sai da motar su ta tashi sannan ya tafi, suna ta daga ma juna hannu. Isar su tashar Abuja ke da wuya, suka kira Yah Ubadullah, ta dade tana kiran shi yana gani yayi banza da ita, Salwa tace bari ta gwada, itama, ko baya kusa ne? Kira daya na shiga na Salwa ya daga, gaida shi tayi sannan ta fada masa sun iso tasha, sanar da ita yayi su bashi awa daya gashi nan xuwa. "Sabon salon iskanci da rainin wayo, ni na kira shi yafi nawa bai dauka ba, shine ya daga kiran ki ko gama ringin batai ba, can mashi shi ya sani dan rainin wayo," "Salma kina matuqar ban mamaki, shin kin manta akan wa kk magana ne? Yah Ubaidullah ne fa, babba a dika familyn mu, amma ke kwata2 baki da ladabi in zaki masa magana, a gaban shi ko a bayan idon shi, sannan baki sani ba ma ko baya kusa ne daga baya ya isa ya daga a daidai sanda na kira, gaskiya ki sauya hali, abinda kayi shi za a maka, ko bamu da qanne kina da qanne a dangi, in suka raina ki ba zakiji dadi ba," "Dan Allah ni ki daina min surutu a tasha," Kowa kama benci tayi ta zauna, rai bace,kamar yanda ya alqawarta kuwa, awa daya ya isa. A gaskiya makaranta ba zan iya fasalta maku haduwar shi ba, abu daya zan iya ce maku baqi ne shi kuma siri, amma ba sosai ba, kyakkyawa ne sosai, ya aje gemu irin na matasan yanzu, ya sha aski, sanye yake da shadda kan shi ba hula, sai qamshi yake zubawa, ya isa gaban Salwa da tai tagumi tana jiran shi, Salma kuwa sai tsaki take tana kumawa, kama akwatin Salwa yayi, tare da kada masa makullan hannun shi, cikin firgita ta daga ido ta sauke akan nashi, murmushi suka sakar ma junan su,Salma kuwa tana ganin shi ta dauki akwatin ta ta ja zuwa gaban motar shi, ta tsaya, Gaisuwa Salwa ta fara masa ya amsa, yana tsokanar ta, tana dariya, "Dan Allah kuyi sauri ni na gaji," 1 Cikin wani irin kallo Ubaidullah ya kalle ta....... *Hummm Salma a rage hali faaa tammm* Kuda kan ta tayi ta murguda baki, kada kai yayi, ya sa akwatin Salwa a bayan mota, ya kama qugun shi da hannu daya, "Ke mara kunya wa kk aje ma wannan gwangwanin akwatin naki ya sa maki?" Salwa ce tai sauri zata saka ma Salma, ya kalle ta tare da daga mata hannu daya, "Ban saki ba" Cikin fushi ta isa ta saka nata ta koma ta shige bayan motar ta zauna, "Mutum na jin yunwa an wani tsaya surutu ba za ai sauri mu wuce ba" "Salma kin san zaki isa gida a taxi kuwa?" "Sai ka fada kace baka son dauka ta a motar ka tin fari," Zai magana Salwa ta sa baki, "Dan Allah Yah Ubaidu ka rabu da ita, yunwa take ji, and kai babbane nuna mata halin girma, ka manna mata yarintar ta" Kyaci yayi, sannan yace, "Kin ci sa'ar Salwa da ranki ya baci, dan kuwa a taxi zaki isa gidan" Kauda kai tayi ta ci gaba da qunquni, tada motar yayi sukai ta hira da Salwa har suka

Chapter 1 of 17