Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tula a jaka, sannan su
ka fita sabon driver'n Mom ya d'auke zuwa school.

A cikin mota ta samu damar yin kukanta, kwantar da kanta a jikin kujera ta yi tana
shesshekar kuka kasa-kasa, David dake gefenta ya kalleta yayi murmushi, cike da
izgili ya ce "Yarinya ki kwantar da kai a gabana ki roke ni abin da kike so, zan
taimaka miki." Harara ta watsa mishi ta dauke kai wani irin mugun haushin shi take
ji. D'age kafad'a ya yi ya ce "kin huta."

Yau ma kamar jiya babu abin da ta tsinana a school d'in har sukayi closing.

Koda su ka koma gida yau ma bata huta ba, haka Anty Esther ta sakata a gaba kamar
jiya, ko garden ta ki bari ta fita ta sha iska, wayarta take bukata ta kira Papa
amma tsoro ya hana ta tambaya, tana ji a gabanta Anty Esther da Mom suka yi waya,
amma Mom bata ce a bata ba, sai ma cewa ta yi wai a ci-gaba da tsareta kar a barta
fita ko compound ne idan ba school zata je ba, kuma koda wasa kada a kuskura a bata
waya, har sai ta dawo, daga nan kuma suka ci-gaba da wasu maganganu wanda tuni ta
daina fahimtar komai saboda kukan da ya ci karfinta.

Kamar jiya tana samun kanta tuni ta manta da duk halin da take ciki, ta tsunduma
tafkin begen abinda zuciyar ta ke bege.


**************

Bayan wasu kwanaki.

Sosai Amira ta dage da zuwa daukar karatu wurin Al'ameen, sai dai hakan ba abinda
ya kareta da shi sai wani irin mahaukacin kaunar shi, a duk sanda zasu zauna karatu
zuciyarta sake narkewa take da soyayyar shi, haka zata yi ta kallon shi wani bin
sai Fatima ta ta'ba ta zata yi firgigit ta dawo hayyacinta, zuwa yanzu Ummi ta soma
fahimta wani abu game da Amiran sai dai ta bar abin a zuciyar ta a tunda hasahse ne
kawai take bata da tabbas. Shi kam Yaya Ameen bai fahimci komai ba, saboda kwata
babu wata aba wai soyayya a gaban shi, sai dai ya kan rasa wani irin kallo ne
yarinyar ke yawan bin shi da shi haka.

Ita kam a bangaren ta sosai lamarin ke damunta, duk wani salo da iyayi da zata yi
don Al'ameen ya gane halin da take ciki ta yi amma a banza, hakan yasa ta sake
tarar Zainabu da maganar, zee ta bata shawara kamar yadda ta saba, ta yi na'am da
shawarar don a yanzu yadda take jin soyayyar shi, bata ki kowa ya sani ba don ta
k'una bata tsoron kauri.



Yau ma kamar kullum ta shigo gidan bayan sallar isha'i, kasancewar an wuni ruwan
sama gari yayi sanyi, yasa Ummi basu zauna a tsakar gida kamar yadda suka saba ba,
a falo ta same su gaba dayan su harda Al'ameen d'in da dawowar shi gidan kenan, ya
mutsa fuska ya yi lokacin da ya ji sallmarta, baya jin dadin jikin shi tunda rana
karfin halin kawai yake yi, ga wani sanyi-sanyi da yake ji yana shigar shi.

gaban Ummi ta zube ta kwashi gaisuwa, sannan ta juyo bangaren sa, cikin wata irin
narkakkiyar muryar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen." Ya amsa da "Lafiya kalau." Yana
dauke kai daga gareta don take kamshin wannan mayataccen turaren nata na ran nan ya
mashi sallama, dafe kanshi daya fara Sara mishi ya yi.

Fatima ce ta gaisheta, ta amsa cike da kulawa kafin ta samu waje kusa da ita ta
zauna, ta saitin shi yadda zata samu damar satar kallon shi hankali kwance.

Ya fi minti uku a haka kafin ya dago, carat idanunsu ya sarke dana juna ba tare da
ta ankara da zai dago ba, da sauri ta kawar da kanta don bazata iya jurar hada
idanu da shi ba, muryar shi ne ya dawo da ita hayyacinta "Amm! Amira ki yi hakuri
kike gida yau baza mu saka yin karatu ba, Bana jin dadin jikina."

Jin haka yasa Ummi kallon shi da sauri, ta katse shi da cewa "A'a yayan Fatima baza
ayi haka ba, tunda ta riga ta zo, ka koya mata ko kadan ne."

Shiru ya dan yi kafin ya amsa da "To Ummi." Baya iya mata musu matukar akan abinda
bai fi karfin shi ba ne.

Mikewa yayi ya kalli Fatima ya ce "Ku muje dakin zaure taskar gida a kwai sanyi."
Daga haka ya fice, Ummi ta so tsayar da shi suyi karatun a falonta ganin ya riga ya
fice yasa ta kyale shi.


Fatima ce a gaba Amira na biya da ita suka shiga dakin bayan ya amsa musu sallama,
lumshe idanu Amira tayi lokacin data shaki daddadar kamshin turarensa da take
maitar son ji kullum. Dakin tsab da shi a tsabtace kamar ba dakin saurayi ba.

Cike da karfin hali da jarumta ya fara koyar da su, sai dai ko minti goma basu
dauka ba ya fara neman fita hayycinsa, rintse idanu ya yi, yana jin yanayin shi na
canjawa, gefe daya ga wani shu'umin kamshin turaren da yake shaka na neman hallaka
shi.

Babu shiri ya dakata, ya kalli Amira da kyar ya ce "Amira kije kawai gobe ki dawo,
bana jin zan iya karatu yau, na so na koyar da ke kamar yadda Ummi ta saka ni amma
bana jin zan iya."

Cike da matsanancin tausayin shi ganin yadda idanun shi suka rine, ta ce "Toh
Yaya, Allah ya saukawake." Da kai ya amsa mata don baya jin zai iya bude baki ya yi
magana, a rude Fatima ta shiga jeromai sannu, da kai ya ke amsa mata, tuni idanunta
ya ciki da kwalla, da hannu yayi musu alamar su tafi kawai, jiki duk a sanyaye suka
mike, har sun kai kofa, cikin wata irin wahalalliyar murya ya kira sunan Fatima,
duk dakatawa suka yi, ya ce "Kar ki gayawa Ummi halin da nake ciki bana son hankali
ta ya tashin, kin ji ko. " ta gyada kai tana sharar kwalla, cikin shesheka ta ce
"Yayana to kasha magani." Ya ce "zan sha yanzu nan." Ta amsa da "Toh ."suka fice.

Da kyar Amira ta tafi gida ranar, barci kuwa kaurace mata ya yi juyi ta dinga yi,
tana ji kamar ta koma ta kara duba shi duk da dare ya tsala, karshe dai ta lallaba
tayi alwala ta yi nafila ta shiga nema mishi sauki a wajen Allah, tare da mika nata
kokon baran.

Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai taba tashi da
karfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi
sumewa a cikin daren nan.....



*Jama'a masoya masu bibiyar littafin JOY, pls Ku kara hakuri da ni, wallahi kwana
biyu nan nayi busy da yawa, amma insha Allah zuwa ranar Monday komai zai daidaita
daga ranar zaku dinga samun update kullum, harda weekend bi iznillah na muku
alkawari ni dai kawai comment dinku da addu'ar Ku nake bukata, sai kuma shearing
fisabilillah* 🙏
[12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN
*AyshaNalado*👉

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writers Association*


*PAGE 21*

Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai ta6a tashi da
k'arfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi
sumewa a cikin daren nan, wani irin hank'oro had'i da jijjiga jikinsa ke yi masa,
babu abin da yake muradi irin ya samu biyan bukata, rashin samun hakan ya haifar
masa da mummunar zazzabi, tare da matsanancin ciwon mara, duk dauriya da jarumtar
Al'ameen sai gashi yana zubar da hawaye yana mulmula a tsakar d'aki, tare da rok'on
Allah ya d'auka ranshi ya huta.

A 6angare d'aya kuma shaidaniyar zuciyar na masa zuga tare da bashi
gurbatacciyar shawara akan ya ta shi kar ya yarda ya hallaka kanshi, ya samarwa
kanshi sauki ta kowacce hanya, ta shiga zano mashi hanyoyin mafi sauki da zai bi ya
samu cikar muradin gangar jikinsa.

Dakyar da taimakon Allah wani wahalallen barci ya sure shi ba tare sa zato ko
tsammani ba.

Kimanin awa biyu ya kwashe yana barcin wahala, wani irin azababben murdawar da
mararsa tayi ya tilasta masa farkawa a zabure, cikin fitar hayyaci da rufewar idanu
ya rarumi sacet din maganin shi da ke yashe a gaban katifarsa, guda uku ya 6alla ya
watsa a baki, daga kwancen da yake ya d'auki ledar ruwa ya kora. Komawa yayi ya
kwanta lamo ya lumshe rinannun idanunsa yana sauke wani irin wahalallen numfashi
mai fita tare da hucin zazzafar zazzabi, hannyen shi duka biyu dafe da mararsa.
Jinsa yake kamar a duniya, kamar matacce kamar yarayye shi sai gashi na, sai dai
duk da haka bakinsa bai yanke da ambaton Ubangiji ba.

Wani haske ne ya mamaye idanunsa, da sauri ya rintse idanu saboda sun gaza daukar
hasken, bayan wasu sakonni ya bud'e su a hankali har ya gama waresu, bai san
tahowarta ba bai san ta ina ta shigo d'akin ba sai dai kawai ya ganta a agaban shi,
sanye da fari kar d'in dogon riga mai sulbi da taushi. Fuskarta ya kurawa idano
yana son gane ko wacece, amma ya kasa saboda rufe shin da tayi da farin mayafin
rigarta kamar nikab, banda kwayoyin manyan sexy eyes din ta babu abin da yake iya
gani, a gaban shi ta tsuguna, tare da sanya kwayar idanunta cikin na shi, a hankali
da wani irin tattausar murya ta furta cikin rada "I Luv u Ameen, zan kareka da
dukkan karfi da iyawata, ruhina da naka suna tare tun fil azal, zamu rayu a tare
bakin rai bakin fama nice cikon farin cikin rayuwar ka kuma nima kaine farinciki
na." Wani dakowa zuciyar shi ta shiga yi har ya kai ga kirjin shi na sama da kasa
kamar mai shirin barin duniya, kallonta ta mayar kan kirjin, na wasu sakonni, a
hankali ta dago hannunta masu dauke da Zara zaran faratuna ta daura akan kirjin shi
ta shiga balle boturan rigar.

Wurgi tayi da rigar bayan ta zame shi a jikinsa, faffadan kirjinsa ya bayyana mai
dauke da tattausar kwantaccen bakin gashi.

Kamar an kwato zancen daga bakin shi cikin rarrabewar harshe ya ce "Wa ce ce ke?"
Murmushi ta saki a hankali ta ce "FARHAT."
Bai yi aune ba ya ji ta fada jikin shi gaba daya tare da bashi wata irin runguma,
wani irin karkarwa jikinsa ya shiga yi.

Sark'ewa nunfashinsa ya fara yi lokacin da ya ji tattausar tafukan hannayenta a
gadon bayan shi tana shawafa, wani irin karfi ya ji ya ziyarce shi, yunkura yayi
ya yi wani juyi, ya mirginata kasan shi ya dawo samanta kamar mayunwacin zakin daya
dade bai ci abincin ba, ya samu daga sama haka ya shiga yamutsarta, laushi hadi da
taushin fatar ta tare sa wani irin mayataccen kamshin da jikinta ke fitarwa suka
hadu suka kara zautar da shi, cikin zafi da fitar hayyaci ya ke bin duk wani sakon
jikinta da wani irin romance wanda bai san yaushe ya koya har ya iya ba. Lokacin
daya isa inda yake muradi, ihu ya takarkare ya yanka saboda jin shi a wata duniyar
da gangar jikin shi ya dade yana muradi, da taimakonta ya samu satisfaction koro na
farko a rayuwar shi.

Cikin karkarwar jiki da gushewar hankali ya juye mata duk lalurarsa. Kwanciya
yayi lamo a jikinta tare da kamkameta kamar zai maidata cikinsa, ya shiga maida
wahaltaccen numfashi, jin shi yake sakayau kamar jariri sabuwar haihuwa.

A lokacin ya farka daga nannauyan barcin daya kwashe shi bayan ya yi overdose!

A hankali ya ware idanun shi, yana bin dakin da kallo, akan labbansa ya furta
dream! Tabbas mafarki yayi, mafarki mai cike da rudani.

Abin mamaki Normal ya farka babu wani ciwo a jikinta sai rashin kwarin jiki, don a
lokacin ko dan yatsarsa akace ya daga bazai iyaba.

Lamo ya kwanta brain din shi na sake tariyo masa mafarkinsa, me yasa baiga fuskarta
ba, mai yasa duk irin abinda ya faru nadin fuskarta ko gezau bai yi ba, wacece ita.
"FARHAT."
Zuciyar shi ta bashi amsa, "FARHAT." Ya sake maimaitawa sunan a bayyane, wani irin
damuwa yaji ya mamaye zuciyar shi, kar sai ace aljana ce ta Aureshi. Tabbas! Abin
tayi kama da apmara ko tasuniyar gizo. kafin yayi aune ya ji ladan ya rangad'a
kiran sallar farko.

Ga al'adarsa ta yau da kullum, da anyi Kiran sallar farko yake tashi, yau ma bai
bari shaidan yayi tasiri akansa ba, bakin shi ya samu da furta adduar tashi daga
barci tare da Karin wasu addu'oin, wani karfi yaji ya shige shi, yunkura yayi ya
mike zaune, rass! gaban shi ya fadi, ta yaya zai gusar da najasar jikinsa ba tare
da Ummi ta sani ba yana matukar kunyarta baya so ta yi wani tunani akan shi, take
duk karsashin daya ta shi da shi ya ji ya ragu.

Jiki babu kwari ya mike tsaye, cike da kyankyamin jikin shi ya dauki buta da
jallabiyarsa wankakke da short ya dauki kuma extra leda da zai saka short din
jikinta idan ya cire, daga haka ya fice daga dakin zuwa cikin gida, ya saba buga ma
su Ummi kofa kullum daya fito amma yau direct toilet ya wuce, cike da kyankyami da
taka tsantsan ya kwabe short din jikin shi ya saka a Leda ya kulle, sannan ya cire
riga.

Duk sanyin da akeyi bai ji ba haka ya rintse idanu ya tsarkake jikin shi, a hankali
cikin taka tsantsan don kar kwarafniyar shi ya farkar da Ummi ko Fatima.

Jallabiyarsa ya sako baya ya kammala wankan, sai da ya gabatar da alwala a tsakar
gida, ya mayar da butar shi da kayan shi daki, sannan ya tukarin dakin su Ummi,
kamar ya kyale su ranar don gani yake kamar zasu iya gane wani Abu, dakewa yayi ya
karasa bakin kofar ya bubbuga musu, sai da Ummi ta amsa sanna ya tafi masallaci.

Koda suka idar da sallar subh, samun waje yayi a masallaci ya zauna yayi addu'oinsa
tare da karatun alkurani, don ya tabbata idan yake gidan ya kebe tunani bazai bar
shi yi ba, sai da gari ya fara haske sannan ya fito ya nufo gida.
Sallamar shi ya fito da Fatima sake kitchen tana wura charcoal da sauri, cikin
raunatacciyar murya ta ce "Yaya Ina kwana ya jikinka, tun dazu nake duba dakin ka
baka dawo ba." Murmushi ya sakar mata tare da matsawa gabanta ya kama kumatunta ya
dan ja da sigar wasa ya ce "Fatiman Yayanta." Dagowa ta yi ta kalleshi da idanunta
da sukayi yi raurau da hawaye ta ce "Jiya dakyar na yi barci saboda tunanin halin
da na barka ciki Yayana." Cike da so da kulawa ya ce "Na ji sauki sosai kanwata
baki gani ba." Ta gyada kai hawayen daya taru a idanunta na sakkowa, ya ce "Kukan
fa Bintan Ummi, oya share wahayenki," da Saudi ta share ya ce "then smile."
Murmushi ne ya subuce mata, shima murmushi tayi ya ce "Da fatan baki gayawa Ummi
ba." Ta girgiza kai alamar A'a ya ce " Yawwwwa! Gud gal! Ci gaba da aikin ki bari
in gaisa da Ummi inzo in tayaki." Daga haka ya nufi dakin Ummi, a falo ya sameta
karamin kur'ani ne a hannunta tana karanta suratul kahfi. Wuri ya sama ya zauna
yana saurrenta wani natsuwa na huda zuciyar shi, sai da ta kai karshen surar tayi
addu'arta ta shafa sannan ta juyo ta kalle shi da kulawa, murmushi dauke a
fuskarta.

A ladabce ya duka gabanta ya sunkuyar da kai, ya ce "Ummina ina kwana."
Cike da alfahari da kasancewarsa d'a a gareta ta ce "Lafiya kalau alhmdllh
Amintacce, da fatan kai ma haka." Bayan gaisuwa zama yayi su ka dan taba hirar
duniya.

kallon agogon yayi ganin bakwai da rabi ta yi, ya mike ya ce "Ummi bari na je na
kimtsa yau ina da lecture safe." Ta ce "Allah ya taimaka, Allah ya yi albarka ."
ya amsa da "Amin Ummi." Sannan ya fito, sharar tsakar gida ya tarar Fatima na yi,
ya ce ta kawo ya karkare ta kama wani aikin kememe ta ki yarda wai ya je ya huta
bashi da lafiya.

Yana saka kai a kofar shiga zaure su ka zabga karo. Taga-taga ta yi zata fadi, da
sauri ya rikota, Zazzare idanu Amira ta shiga yi cike da kunya, bata taba tunanin
zata same shi tsaye haka akan kafafafun shi ba, saboda yadda ta barshi, tun asuba
take son shigowa ta ganshi tana tunanin idan shigo, ta ce musu meya kawota, yanzu
tana zaune ta ji mamanta zata yi aike wajen Ummi tayi caraf ta amsa ta ce bari ta
kai.

Sake ta yayi ta tsaya akan kafafunta ya ce "Ki dinga kula mana, ina kike kallo
haka?."Cikin inda- inda ta ce "ina kwana Yaya Ameen, ya karfin jiki." Babu yabo
babu fallasa ya amsa mata da "lafiya jiki Alhmdllh." Ya rabata ya shige dakinsa,
yana shiga daga bakin kofa yaji ya taka Abu kamar takarda, kallon shi ya kai wajen,
paper ne a nannade, da mamaki ya tsuguna ya dauka tare da budewa da sunan ta idanun
shi ya fara tozali. Cike da dumbin mamaki ya furta "What!!! Amira!".........


Ga mai bukatar shiga group ya tuntunbeni kai tsaye.

09116099486.
[12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


~FARHAT~


DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*


ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiyi Writer's Association*
*PAGE 22*

Dunk'ule paper n ya yi bayan ya gama karanta abin da ya k'unsa, ya dafe goshi cike
da takaici, ko kad'an bai ji wani karsashi ko shauk'i game da kalamanta ba, sai
ma ganin tsananin wautarta da shirmenta da ya yi, dama he is wonder yadda ta ke
yawan kallon shi ashe da dalili, guntun tsaki ya ja, ran shi duk ya 6aci, cike da
takaici ya ce "Yara tun baku tafasa zaku k'one!" Wurgi ya yi da paper'n ya shiga
kimtsa d'akinsa, tattara komai ya yi, ya shere d'akin tass! kamar yadda ya saba,
wurin tattara shara ya sake cin karo da paper n kamar ya share da shi ya zubar sai
kuma ya dauka ya warware ya linke, zai ajiye saboda evidence, gurin da tarin
littfansa suke ya nufa, ya dauki wani babban textbook da yake saka paper's ya bud'e
da nufin ajiye wa a ciki, karaf! ya bud'e dai-dai page d'in da ya ta6a ajiye letter
n Joy, gaban shi ne ya yanke ya fad'i, kurawa latter n idanu ya yi, brain din shi
na tuno masa abin da ya faru tsakanin su rannan' lokacin da take sand'a da za ta
shiga gidansu, yadda ta firgice daga jin muryarsa kadai, yadda ta riko kafafunsa
tana rokonsa, yadda ya fisge kafarsa da k'arfi ta fad'i ta fasa goshi, yadda ta
mik'e tana hawaye ta kakka6e jikinta, ta tashi tana tafiya a slow, bin bayanta da
ya yi, guduwan da ta yi ta barshi a tsaye rik'e da handkerchief, k'ak'k'arfar
ajiyar zuciya ya sauk'e. Hakan na nufin bata yafe masa ba fa kenan, take jikin shi
ya yi mugun sanyi, hakika ya cutar da ita, kuma he regret, zai yi kok'ari ya gyara
kuskurensa.

Latter n ya d'auka ya koma bakin mattress d'insa, ya warware yana bi da kallo
tare da sake karantawa, yana maimaitawa, zuciyarsa na k'ara shiga matsanancin
tausayin yarinyar kamar yadda ya fassara lamarin.


Bai san adadin lokacin daya 6ata a haka ba, ya tsinkayi sallamar Fatima a k'ofar
d'akin shi, da sauri ya linke wasikar, ya tura karkashin pillow, sannan ya bata
izinin shigowa, kayan breakfast d'in shi ne ta kawo, guri ta samu ta ajiye, godiya
ya mata, sannan ya tsareta su ka yi breakfast d'in tare. Yana ta so yayi mata
zancen Joy zuciyar shi na hana shi, a haka su ka kammala, ta kwashe kayan ta mayar
cikin gida shi kuma ya d'ibi ruwan wanka ya shiga.

Har ya yi wanka ya shirya tunanin Joy ya ke, da kyar ya yakice ta a rai ya samu ya
fita, school ya tafi daga can kuma bai dawo gida ba, ya ta fi harkar kekensa.

Karfe takwas ya shigo gida, as usual su Ummi na tsakar gida, nan ya zauna su na
shan iska, a nan ya ci abincin suna sauraren shirin kwarmato! A redion Ummi abin
mamaki ranar Amira bata shigo karatu ba, Ummi ta ce "Wai ni kam yau banga Amira
ba tun safe ko lafiya? " Fatima ta ce "Nima Ummi wallahi tun d'azu abin ke
raina."Ummi ta ce "Allah dai yasa lafiya, da safe idan Allah ya kaimu sai Ki dubo
mana ita." Al'ameen na jin su bai saka musu baki.

Hira suka shiga yi, sai sha d'aya saura suka ta shi lokacin tuni Fatima ta yi
barci. Shi ya kwashe tabarman bayan sun ta shi, sai da ya d'aura alwalar barci
sannan ya nufi d'akinsa, shafa'i da wutiri ya gabatar, ya rage kayan jikinsa ya
haye katifarsa, sai dai me! Tunanin yarinyar ne ya yi wa kwakwalwarsa kawanya, ya
rasa me yasa ya damu da ita cikin y'an kwanakin nan, tun ranar da abin nan ya faru
bai ta6a wayar gari ba ta fad'o masa a rai ba koda sau d'aya ne, tausayinta ya ke
ji kamar me, sai dai ya alakanta hakan akan abin da ya gifta tsakanin su ran nan,
hakan yasa ya daura damaran gyara kurensa, ya dauki tsawon lokaci kafin barci ya
d'aukesa.

Cikin barci yaji yanayin shi ya fara sauyawa, tun yana d'aurewa har sai da da ya
kai ga bud'e idanu, "Allahumma ajirni fi musabati! Hasbunallahu wa ni'eemal
wakeel!" Ya shiga maimaitawa, iya hasashe babu wani abu daya faru cikin abubuwan da
ke tasar masa da ciwonsa, babu ruwan sama babu sanyi a garin hasalima zafi ake yi
saboda kwallara ranar da akayi a yinin ranar, bai shaki wani abu makancin kamshi
ba, bai ga wani sura ko wani abu da zai iya daga mashi hankali ba, to menene
dalili?

Jin abin na k'ara yawa yasa ya yi ta maza ya d'auko maganin sa ya 6alla sai dai ko
gezau, sai ma ci gaba da hauhauwa da abin ya k'ara, hankalin sa ya ta shi mak'ura,
abin da ya lura yanzu tab! 'Din ya daina mishi aiki ma, kardai maganar Dr Abdul ne
ya tabbata.

Tuni ya fara ficewa a hayyacinsa, sharkab ya had'a gumi, jikin shi na karkarwa
tare da soma daukar zafi, gefe guda ga mararsa da yayi wani irin kumburi ya yi
tauri had'i da k'ullewa, numfashi ma dakyar ya ke iya ja da saukewa.

Cikin lalube da malelekuwar da yake yi, hannun shi ya sauka akan sachet din
maganinsa, kamar jiya, wawura yayi ciki rufewar ido ya 6alli uku ya watsa a baki.

Da farko kamar ya k'arawa ciwon karfi, don sai da ta kai shi ga fara mirgina a
tsakar d'aki.

Kimanin 15 minute ya kwashe a haka, kafin kuma ciwon ya fara lafawa, dakatawa ya
yi da mirginan ya yi lamo yana sauke numfashi, a hankali komai ya tsaya cak! Kamar
an yi ruwa an d'auke, kumburin maran ya sace, sai dai duk da haka jikinsa na nan da
zafi rau, a haka wani wahalallen barci ya kwashe shi.

Kiran farko ya farka as usual, Alhmdllh! Zuwa lokacin zazza6in ya sauka, babu wani
alamar ciwo sai idanunsa ne kad'ai su ka nuna, zaune yayi a bakin katifarsa
zuciyarsa cike da damuwa, sachet d'in maganin shi dake yashe a k'asa ya dauka ya
tsurawa idanu yana kallo, tsakanin jiya da yau ya sa guda takwas, abin da ake shan
d'aya d'aya, kuma ba kullum ba don da sai yayi sati biyu uku bai sha ba, hakan na
nufin d'aya ya daina mishi aiki ke nan, tabbas akwai gagarumin matsala, dole ya
koma wajen Dr Abdul, amma kafin nan yana bukatar shawara, yana bukatar shearing din
matsalarsa da wani, wayar sa ya d'auka ba tare da la'akari da lokaci ba ya dan nawa
Aliyu kira.

Ringing biyu Aliyu ya daga, tare da sallama, Al'ameen bai taba kiransa a irin
wannan lokacin ba, cikin dan tashin hankali ya ce "Ustaz lafiya, hankali ya ta shi
da naga kiranka a irin wannan lokaci." Numfashi ya sauke kafin ya ce "Aliyu ina
cikin damuwa."

"Subhanallah! Me yake faruwa Ameen? Bai amsa mishi tambayar shi ba, ya daura
mishi da wata "Yaushe zaka dawo? Maganar bata waya ba ce." Jim! Aliyu yayi kafin
ya amsa da "Zan kai karshen wata, ka fa'di ka d'an daga damuwar ka abokina zaka ji
sauki." Girgiza kai Al'ameen yayi kamar suna kallon juna ya ce "Sai dai ka dawon
zan kira ka." Daga haka su ka yi sallama jikin Aliyu duk a mace, ya san halin
Al'ameen ba tun yau ba, tun da ya bukaci su tattauna akan matsalarsa to ya tabbata
babbar matsala ce, zai yi duk yadda zai yi ya samu ya koma gida a karshen watan don
su zanta kuma zai taya shi da addu'a Allah ya kawo ma shi d'auki.


Tun daga wannan rana kusan kullum sai ciwon shi ya ta shi, walau da sanyi ko babu,
taimakon shi daya bai tab'a tasar masa da rana ba, sai dai wani lokacin tun da
yamma zai fara jin alamun shi, da yaji haka ranar da wuri yake komawa gida da ya
yi isha kuma yake shiga d'akin shi ya kulle.

A bangare daya ga damuwar FARHAT zuwa yanzu kusan sau hudu yana yin mafarki da ita,
tana maimaita masa kalamanta na ran nan, sai dai har zuwa yanzu bai yi nasarar
ganin fuskarta ba duk irin kwakwanshi da son ganin hakan, lamarin yana matukar
damun shi. Duk wannan matsanancin yanayin da ya shiga bai manta da Joy ba, sai dai
idan bai samu sarari ba sai ta fado masa a rai, ya kan alakanta hakan da cutar da
ita da ya yi ran nan kuma yana fatan ya samu damar da zai nemi yafiyarta.



*****************


Kamar yadda Al'ameen ke

Please Login or Register in order to submit comment