Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIO*

*LITTAFI NA ÆŠAYA*

*PAGE 1*


Bismillahir-Rahmanir-Rahim


NIGER STATE

*Abayi close* fitacce ne kuma sananiyar unguwa a cikin garin na *Minna*, unguwace
dake dauke da nau'ikan mutane kala kala
ƙabilu dabam dabam
musulmai,cristain, talakawa, masu matskaicin ƙarfi,da ma manya masu hannu da shuni,
hakan yasa unguwar ke cakuɗe da gidaje maya da ƙanana.

Misalin karfe biyu na sulisin dare, ruwa ake tsugawa kamar da bakin kwarya, ko ina
ya dau sanyi bakajin
ƙarar komai sai na yadda ruwa ke sauka a saman kwanukan gidajen mutane da mugun
karfi haÉ—i da walkiya tare da razananiyar tsawa mai firgita mai sauraro tare da
wani iska mai ƙarfi dake kadawa jefi jefi, hakan yasa gaba ɗaya garin ya ɗauki wani
irin sanyi mai ratsa jiki.

A É—aya daga cikin gidajen talakawan dake unguwar, kwance *AL AMEEN* yake cikin
É—an madaidaicin É—akin shi dake zauren gidansu a kan yar madaidaiciyar katifar shi,
kuÉ—undune yake cikin bargo idanun shi a lumshe, a kallo É—aya zaka dauka barci yake,
sai dai ko kaÉ—an ba haka bane, yadda yake sauke numfashi a wahale da yadda zufa ke
karyo masa duk da matsanancin sanyi da iskar dake kaÉ—awa a garin ne zai tabbatar
maka ba lafiya yake ba.

Cike da tsananin azabar ciwo ya buÉ—e rinannun idanun shi ya sauke akan wani jaka
dake rataye jikin hangar dake manne a bangon ɗakin, so yake ya miƙe ya isa ga jakar
domin ya dauki magungunan shi da ya musu kyakyawar buya a cikin jakar , sai dai
inaa! Bazai iya ba domin Ko kwakwaran motsi baya Iya yi balle har akai ga batun
miƙewa tsaye, idan kuwa yace zaiyi wani motsi mai karfi a halin da yake ciki, komai
zai Iya faruwa da shi ciki harda rasa numfashin shi. Ci gaba yayi da kallon jakar,
ji yake da yana da dama da ya kira jakar daga kwancen da yake, sai dai shi kanshi
yasan hakan ba abune mai yuwuwa ba,


A hankali ya mayar da idanun shi ya lumshe, cike da tsananin azabar ciwon maran da
ke neman hallaka shi, ya riga ya sani a duk sanda za'a wayi gari cikin irin wannan
weather ko makamancin sa, to kuwa shi a ranar bashi da sauran lafiya, yau kimanin
shekara hudu kenan yana fama da wannan lalurar, tun daga lokacin da yakai munzilin
balaga, lokacin yana da shekaru sha takwas a duniya ya fara fuskantar wannan
matsalar, tafi tafi abu ya fara ƙamari wanda har sai da ya danganta kanshi da
likitaba tare da sanin kowa ba, shi ƙadai yake gwagwarmaya da faɗi tashin shi ba
tare da kowa ya sani ba, ciki harda mahaifiyar shi wacce duk duniya bashi da kamar
ta.
Cikin karfi hali irin nashi na jarumin namiji ya shiga, ambaton Allah a zuciyar
shi domin ya kawo mishi
É—aukin gaggawa, yayin da ya kai duka hannayenshi biyu ya dafe marar shi dake mishi
wani irin matsanancin ciwo tare da daurewa kamar jijiyoyin gurin zasu tsinke.

Kimanin awa É—aya da rabi ya dauka ba tare da bakin shi ya gaza da ambaton ALLAH ba,
a hankali cikin hukucin ubangiji ya ji komai na lafa mishi.

A hankali ya miƙe hannunshi ɗaya dafe da marar shi, yana tangaɗi ya isa gaban
jakan da maganin shi ke ciki, hannu ya saka can kasar jakar tare da dauko sacet din
magani, guda data ya ɓalla ya maida sacet din, komawa yayi bakin katifar shi ya
zauna tare da jawo jug din dake gefe cike da ruwa babu bata lokaci ya afa maganin
ya kora da ruwa, ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa ya kwanta rigingine yana
sauke numfashi.


*Washe gari*


**********

6 Am dai dai Alarm É—in agogon dake ajiye akan bed side drowan dake kusa da gadonta
ya fara ƙara yana girgiza, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta tare da miƙa hannu
ta kashe alarm É—in, kusan minti biyar ta kwashe a kwance kafin ta yaye bargon da
ke lullube a jikinta ta miƙe zaune tana tattare dogon gashin kanta daya barbaje ta
ɗaure shi a baya, yunkurawa tayi ta miƙe akan kafafunta, mika tayi tare da dogon
hamma baki bude tana furta "in Jesus name" cikin zazzakar muryarta, kayan bacci ne
riga da wando masu kauri a jikinta saboda yanayin da ake ciki yau na sanyi a garin,
cike da kasala ta fara takawa a hankali Kamar wacce bata da laka a jiki ta nufi
wani ɗan ƙofa ta buɗe ta shige.

Kusan minti 30 ta kwashe, sannan ta fito daure da dan ficilin tawel iyakarsa
cinyoyinta, jikinta da gashin kanta na É—igan ruwa, gaban mirron dake shake da kayan
shafa na mata da turaruka ta tsaya, hand dryer ta kunna ta fara busar da gashin
kanta bayan ta gaba ta shafe shi da mayukan gyaran gashin kusan kala uku masu kyau
da tsada take ya dau kwalli da sheki, taje shi tayi kafin ta tattare shi tayi
parking din shi a gefen kai.

Body lotion dinta mai kamshi da tsada ta shafa, tare da turarukan ta na jiki,
fuskarta ta gyara batayi wani dogon kwalliya ba hoda kawai ta shafa da lip gloss
sai maskara data karama Zara zaran lashes dinta.

Gaban makeken wadrob mai kofa shida dake dakin ta tsaya Wanda set ne da gadon da
mirron dake dakin, kofan farko ta bude, inner wears ne shake a wurin kalakala kamar
za'a bude kantin sayar da su, pant da vest da sock ta dauka ta maida kofar ta
rufe, kofar dake kusa da na farko ta bude, school uniform dinta ne a goge a ninke
kusan kala goma, É—aya ta Zara tare da madai kofar ta rufe cikin Sauri ta shirya
cikin farin riga mai dogon hannu tare da skirt sky blue damamme iyakarsa cinyanta,
tayi stokin,farin sock ta Sanya dogo ta dauki wani farin both a cikin jerin
takalmanta dake cikin abin jera takalma sunfi a kirga ta saka a kafarta, agogon ta
dauka a cikin wani dirowa ta daura a hannuta, daga haka bata kara komai ba ta
sunkuci gabjejen school bag dinta ta fice daga dakin.

Sauri sauri take saukowa daga kan stairs ta iso wawakeken falon dake kasa, a share
yake tsab sai tashin kamshi yake babu abin da ke tashi sai sautin TV dake kunne a
tsahar eagle TV wani babban pastor na wa'azi cikin karadi da tsoratarwa, da alama
ma,aikatan gidan masu alhakin kula da tsabtar falon har sunyi aikin su, bata bi
takan TV ba ta ajiye jakanta akan daya daga cikin kujerun dake kewaye da falo ta
fice.
Hanyar dining Wanda ke kusa da makeken kitchen din gidan Wanda shine general
kitchen na gidan a nan ake duk wani girki ta nufa, abin mamaki a shirye tsab ta
tarad da dining din shake da warmers kala kala ga flask da kayan tea da sauran su.

Bata bata lokaci ba gurin Jan daya daga cikin kujerun dining din ta zauna tana mai
duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, motsin da taji daga stairs ne yasa
tayi saurin daga kanta ta kalli hanyar gurin, kamar yadda tayi tsammani iyayen nata
ne biyu mom and papa ke saukowa cikin shirin su ta tafiya aiki hannayen su sarke
cikin na juna , mom sanye cikin dogon rigar less kanta babu dankwali, gashin dokin
data kara a kanta a bayyane, papa kuma sanye cikin suit ash da kagansu kaga
tsofafi masoya ya boko.

A tare suka sakar mata murmushi, itama babu bata lokaci kyakyawar fuskarta ta
yalwatu da farin cikkin ganin iyayen nata.

Mikewa tayi tun kafin su ƙaraso tanufe su , jikin papa ta fara faɗawa ta bashi
kyakkywan runguma tana cewa "gud morning my papa" shima zagayeta yayi da hannayen
shi yana É—an bubuga bayanta yake cewa "morning dear how ar U how was ur n9t." Ta
amsa mai da "fyn papa." Sannan ta sake shi ta dawo jikin mom dake kallon su tana
ta sakin murmushi, itama gaisawar sukayi kamar yadda sukayi da papa, kafin duk
suka dunguma suka karasa kan dining.

Suna zama kuku ya futo daga kitchen da alamar dama tsaye yake yana jiran fitowar
su, cike da girmamawa ya gaishesu, kafin ya shiga serving dinsu, abinci ne
lafiyayyu akayi shi kusan kala bakwai kai da gani kasan a kwai almubazzaranci a
lamarin.

Kusan duk a tare suka miƙe ba tare da sun ci abin kirki ba, Jakarta ta dauko a falo
bayan ta shiga kitchen ta cikashi da chocolate da sauran kayan kwalama nau,i nau,i
suka dunguma zuwa compound din gidan, ma,aikatan gidan ne suka Shiga kwasar
gaisuwa, da sauri drivan dake kaita school ya fito da mota, duk da school din nasu
ba wani nisa gare shi ba cikin anguwa ne amma kullum a mota ake kaita a dawo da ita
tsabar gata.


Mom ce ta kalli driven cikin harshen nasara ta ce "Peter ka barshi kawai yau ni zan
yi dropping dinta tunda ina da aikin safe, kai kuma in sun tashi sai kaje ka dauko
ta." A ladabce ya amsa da "yes maa." Sallama suka kara yi da papa ya sunbace ta a
kumatu bayan ya sake hugging dinta a hankali yake gaya mata ta kula mishi da kanta
cikin shagwaba take amsawa a sangarce.

Daga cikin gidan zuwa school din kwata kwata tafiyar 15 minute sukayi har cikin
school mom taso shigar da ita amma ta nuna bata so saboda gudun bacin ranta yasa
mom ajiyeta a get, suna daga ma juna hannu har motar mom ya bace ma ganinta.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuci Jakarta ta goya, saida ta yi tsayuwar minti
biyar a bakin get din ganin babu Wanda ya ganta yasa ta juya cikin sauri sauri gudu
gudu ta bar bakin get din, dai dai zata shiga wata kwana dake bayan katangar school
din taji ance " *JOY JAMES* " da ƙarfi, koda bata juya ba tasan me wannan muryar
hakan yasa ta juyo ido huÉ—u sukayi da juna ta maka mai harara tare da kallon
gargaÉ—i kafin ta juya ta runtuma da gudu, "Joy!! Joy!!" Haka David ya dinga kwala
mata kira amma a banza dan bata juyo ba balle ta tsaya, ƙwafa David yayi kafin ya
kinkimi jakar shi ya shige cikin school din.


*********
*AL AMEEN* kiran sallan Assalatun farko a kunnen shi saboda sabon da yayi da
tashin asuba ko a wani iri hali yake idan har asuba tayi ko da kiran sallah ko
babu zai farka, babu laifi yaji sauki sosai amma duk da hakan ciwon bawai ya gama
sakin sa bane, lallaɓawa yayi ya mike yana yamutsa fuska alamar ciwo, ya dauki
butar shi guda ɗaya dake ɗakin ƙofa ya nufa ya zare sakata tare da buɗe wa, wani
sanyi ne ya doke shi wanda yasa yayi saurin rintse ido, danne zuciyar shi yayi ya
zuro ƙafafun shi waje, a haka yana mammatse jikin shi ya nufi cikin gidan, tsakar
gidan madaidaici ne mai dauke da daki babba guda daya ciki da falo, sai makewayi da
madafi dake daga gefe.

Ƙofar ɗakin Ummi ya nufa kamar kullum duk asubar duniya shi yake tashin su, sai da
yaji Ummi tayi gyaran murya alamar tana farke, sannan ya lallaɓa ya nufi toilet,
ruwa ya kama, ya fito ya daura alwala da sauri sauri ya koma É—aki yana rawar É—ari,
ranar kasa fita sallar asuba yayi yana ji yana gani aka tada sallah a masallacin
kusa da gidan su amma bazai iya fita ba domin yana tsoron abin da zaije ya dawo
bugu da ƙari kuma dama ba wai ya gama wartsakewa bane, komawa yayi ya kwanta bayan
ya idar da sallah, a maimakon tilawar alƙur,ani daya saba yi kullum bayan sallar
asuba har gari yayi haske, dalili kuwa, saboda jiya bawai ya samu isasshen barci
bane.

Ummi sai da tayi sallarta ta idar kafin ta ƙarasa kan karamin gadon dake uwar ɗakin
ta, a tausahe ta kai hannu tana tsashin *FATIMA* Dake barcinta hankali kwance, ware
ido fatima tayi akan Ummi, ganin ta buÉ—e ido yasa Ummi cewa "'ki tashi gari yayi
haske, koda ba sallah zakiyi ba ki dauro alwala kizo kiyi arkar É—inki." tashi tayi
tana cewa "to Ummi" ganin ta tsahi yasa ummi komawa taci gaba da azkar É—inta.

Alwala Fatima ta dauro ta zo ta zauna ta gabatar da azkar da addu'ointa kamar yadda
ummu ta sabar mata koda kuwa tana jini ne bata yarda ta barta ta zauna haka kara
zube ba .

Bayan ta idar miƙewa tayi taje gaban ummi ta tsuguna tace "ina kwana ummi." sai da
ummi ta shafa adduar da take yi sannan ta juyo ta kalli fatima tace "lafiya ƙalau
fatima, fatan kin tashi lafiya." ta amasa da "lafiya ƙalau ummi." "To
alhamdulillah, maza ki tashi kije ki gaida yayan ki sai kizo ki amshi kuÉ—i ki sayo
gawayi asaka ruwan wanka a dama kunu." "to ummi" fatima ta amsa tana miƙewa

ÆŠakin dake zauren gidan ta nufa, tafi matukar mamakin jin yau bata jiyo sautin
zazzaƙar muryar yayanata ba, haka dai ta daure tayi sallama abakin ƙofar da
mamakinta shiru taji ba amsa kusan sau uku tana sallama taji shiru abinda ba
kasafai ya cika faruwa ba, hannu tasa ta dan turo ƙofar dakin ta leƙa don duk
atunaninta baya ciki ne, ga mamakinta ta hango shi kwance kan gadon shi ya
ƙudundune waje ɗaya cike da mamaki ta juyo ta dawo cikin gidan, ganin yanayinta
yasa ummi tambayarta lafiya, cikin dan damuwa tace "ummi me yasa mu yayana yau
yake barcin bayan asuba ko bashi da lafiya ne." kallonta ummi tayi kafin tace
""barci kuma? cikin sigar tamaya gyada mata kai fatima tayi ta ƙara da cewa "na
leƙa ɗakin shi na ganshi kwance ƙudundune cikin bargo" ɗan jim ummi tayi ita kanta
ta cika da mamaki can kuma tace "eh to wata ƙila baiji daɗi bane, bari naje na duba
shi ki dauki dari biyu cikin pos ki siyo gawayi ki hura wuta."

Bayan tafiyar fatima tashi ummi tayi taje ta duba Al'ameen, kamar yaddz FATIMA ta
fada haka ta same shi, cike da alhini ta ja mishi kofar ta koma cikin gida.

Ko da Fatima ta dawo kitchen ta shige ta hura wuta dakyar ya kama saida ta ɓata
lokaci kasancewar gawayin yayi sanyi, tana gamawa ta haÉ—a wanke wanke, koda ta gama
ta samu ruwan baiyi wani zafi ba haka ta zauna tana fofitawa har ummi ta gama
lazuminta ta fito ta same ta, ganin haka yasa ummi cewa "har yanzu baki Shiga
wankan ba Bintz kinsan yayanayin makarantar Ku basu da sauki idan aka makara fa"
"Wlh ummi gawayin ne jikakke wutan baici sosai." Bude ruwan ummi tayi ganin zai
isheta wanna idan ta juye duka yasa tace "je ki dauko bakitin wanka ki juye duka
kije kiyi in kin tafi ni da yayanki sai musa muma muyi tunda mu babu Indi zamuje"

Bayan ta juye ruwan, ruwan kunu ummi tasa gani har bakwai ta gota, da kanta ta
zauna tana fifita wutan, koda Fatima ta fito wanka É—aki ta wuce ta ciro kayan
makaranta cikin sif a goge tsab, da sauri sauri ta fara shiryawa, cikin farin Riga
mai dogon hannu da skirt sky blue sai dai nata dogo ne ya sauka har kaurinta
kasancewarta musulma ta daura dankwali tare da madaidaicin hijabi daya rife mata
kirjinta, Jakarta ta dauko ta fito tsakar gidan bayan ta saka takalmi da safa, nan
ta tarar ummi ta gama dama kunun koko, ganinta yasa ummi cewa yawaa Binta miko
robar siga da ledan kulikuli in baki naki ki karya ki tafi, ajiye jakar tayi ta
koma É—aki dauko sugar da kulin ta fito tana zare ido ganin yadda lokaci yaja.

A gurguje tasha kunun bata ma shanye ba saboda da zafi ta ajiye saura ta sunkuci
Jakarta, ummi tace "ki dauki nera hamsin a pos." Da Sauri ta shige dakin ta dauko
tana fitowa tsakar gida *JOY* na kwada Sallama cikin gurbatacciyar hausarta, dai
dai time É—in kuma Al'ameen ya fito daga dakin shi sanye da singlet fari da dogon
wando a jikinshi,turuss joy tayi gabanta na wani irin dokawa da mugun karfi take
jikinta ya dau rawa lokacin da idanun Al'ameen ya sarke cikin nata.....



More comment more typing


Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ÆŠAYA*

*PAGE 2*


Turusss Joy tayi gabata na wani irin dokawa, take jikinta ya É—auki rawa lokacin da
idanunta ya sarƙe cikin na Al'ameen, wani irin mugun kallo ya shiga jifanta da shi
kallon gargaÉ—i da tsantsagwaron tsana wanda ita kaÉ—ai ke ganin hakan , ta rasa
dalili a duk lokacin da idanunta zai haÉ—u dana yayan Fatima ta kan rasa nutsuwarta,
ta kan shiga firgici, da tashin hankali kwarjini yake mata kamar zaki, yanzu ma
gani ta yi duk ya cika wajen, zata iya rantsuwa da yesu almasihu bata taɓa ganin
murmushi a fuskarshi ba.


Cikin rawar muryar ta ce " good morning Yaya Elameen." Bata yi zaton zai amsa ba
don bai cika amsa mata gaisuwa ba, sai dai ga mamakin ta dauke kai yayi daga
kallonta ya ce "morning." tare da rabawa ta gefenta ya shige toilet ya turo ƙofa
garam.

Daga ita har Fatima da Ummi da kallo suka bishi, bata san ta lula tunani ba sai da
ta tsinkayi muryar Ummi na cewa "A'a Joy kece, baki tafi abinki ba kika tsaya
biyoma Fatima salon ki ƙara makara, oya maza Ku tafi kar ku tsaya wasa Allah ya
tsare." Sallama suka ma Ummi suka fice jikin Joy a sanyaye ko martanin murmushin da
Fatima ke sakar mata bata iya mayar mata ba.

Da kallo Ummi ta bisu a ranta ta rasa wannan wani irin haÉ—uwar jini ne tsakanin
Fatima da Joy, ba yadda bata yi ba don ta raba wannan alakar tun abin baiyi nisa
ba, amma ina!!! abin ya ci tura tayi dukan tayi faÉ—an ta daure fuskar amma duk a
banza karshe dole ta hakura ta fawwalawa Allah bayan ta gane tsakanin Joy da Fatima
hadin Allah ne.

Motsin fitowar Al'ameen daga toilet ne ya dawo da ita hayyacinta, da kallo ta
bishi har ya ajiye butar dake hannun shi, ranshi gaba É—aya a jagule, ga ciwon daya
kwana dashi yanzu kuma ga bacin ran ganin arniyar yarinyar nan mai fistari a
tsaye a gidan su, tsugunawa yayi a gabanta cike da ladabi yace "Ina kwana Ummi."
Amsa mishi tayi cike da kulawa tana nazartar yanayin shi, kwarai ta hango rashin
nutsuwa a tattare da shi ga idanun shi ya dan fada, "Tabbas a kwai abin da ke
damunshi don banza bata kai zomo kasuwa" ta fada a ranta, mikewa yayi bayan sun
gama gaisawa ya nufi hanyar Zaure, murmushi tayi ta Riga ta sani dama bazai taba
fada mata damuwarshi ba ita ta haife shi tafi kowa sanin zurfin cikin shi.

Har ya kai bakin Zaure ya ji tace "*AMINTACCE*." Sunan da take Kiran shi da shi
kenan a wasu lokutan, zai Iya rantsuwa tunda ya mallaki hankalin kanshi bai taba ji
Ummi ta kira sunanshi ba yayan Fatima tafi kiran shi sau da yawa, cak ya tsaya tare
da juyowa, kallon juna sukayi cikin ido da sauri ya sauke kan shi ƙasa, a sanyaye
tace "Meke damunka." Bai yi mamaki ba don yasan yadda Ummi tasan shi ciki da bai
duk yadda taga sauyi a tare da shi sai ta gane.

Ba tare da ya dago kanshi ba ya ce "Ba koma Ummi jiya da zazzabin mura na kwana da
ciwon kai amma Alhamdulillah zuwa yanzu ya sauka na ji sauki dan nasha maganin tun
cikin daren." Cikin da nazarin yanayin shi ta ce "Ka tabbata." Ya gyada kai tare
da ce wa "Eh Ummi." Ta ce "Allah ya kara sauki." Ya amsa da "Amin Ummi." "Kazo ka
juye ruwa kayi wanka zaka ji karfin jikinka sai ka sha kunu ka kara shan maganin."
"Toh Ummi."ya ce tare da juyawa ya nufi inda botikin wanka yake ranshi duk a ɓace.


*********

Suna fitowa Fatima riko hannunta tare da maka mata harara cikin harshen nasara
Wanda shine yaren da Joy ta fi iyawa ta ce "why Bestie me yasa kike son saka kanki
cikin damuwa ne sabo da ni." Kallonta Joy tayi ta sakar mata murmushi Wanda har sai
da dimple dinta ya loza, cikin jin haushi Fatima ta ce "OK dariya ma na bakin ko."
Fari ta mata da idanu ba tare da ta amsa ba hakan ya ƙara hassala Fatima, take ta
hade rai kamar bata taɓa dariya ba sake hannun Joy tayi ta kama hanya zata wuce ta
barta, ganin haka yasa Joy saurin shan gabanta rike kunnayenta tayi cikin
marairaice fuska ta ce "sorry my Teetee." Jin sunan da ta kira ne yasa Fatima
kwashewa da dariya tare da kai mata dundun wasa, itama dariyar ta kwashe da shi,
tana kaucema dundun Fatima, sai da suka natsa, Fatima ta ce "kin san dai mun
makara, sai ki shirya amsan punishment." Ba tare da wani damuwa ba ta ce "Ai na
shirya." Fatima ta ce "OK I see." Da haka suka kama hanyar school hannunsu rike
dana juna suna fira suna kwasar dariya cike da nishadi hankali kwance, duk da ita
Joy tsoron al'ameen bawai ya gama sakin ta bane, da ka gansu zaka hango yadda suke
tsananin kaunar juna.

Kamar yadda suka tsammata kuwa sun tarar ana kama late comer a bakin get ana musu
bulala, sosai Fatima taji babu dadi a ranta dama abin sa take gujewa Joy kenan,
amma ta lura ita Joy din babu alamar damuwa ko nadama a fuskarta.

Koda suka Isa class har teachern da zai dauke su first period ya shiga class
kasancewar sa ba mai tsauri ba yasa excuse kawai suka dauka ya basu izini suka
shiga ciki.
Suna shiga idanun Joy ya sauka akan na David daya zubo musu ido yana kallo yana
gyada kai, harara ta maka mai tare da dauke kai daga kallon shi, sit din su suka
nufa Wanda yake a layin gaba suka zauna su biyu, dama bibbiyu ake zama a kowane
sit.

Haka sukai ta daukan karatu cike da himma da kwazo don dukan su ba baya ba wajen
kokari, wannan malamin ya shiga wannan ya fita har har zuwa break time, Joy ta
fito musu da su chocolate da biscuit din da ta zuba a jaka suka zauna a class suna
ci suna hiran karatu, sai jin tsayuwar mutum sukayi a kansu, kusan tare suka dago
suka kalle shi, harara ya fara watsama Fatima wanda itama bata yi kasa a gwuiwa ba
wajen ramawa kafin cikin wani yare wanda Fatima bata ji ya fara ce wa "dama nasan
gidan su wannan matsiyaciyar zakije kuma ki rubuta ki ajiye daga wannan karan kinyi
na farko kinyi na karshe don sai na gayawa papa halin da kike ciki a makarantar nan
kin san kuma abin da zai biyo baya, wannan ai zubar mana da Kimar family kike yi."
A harzuke ta ce da harshen turanci don shi tayi ji fiye da yaren su da David ke
mata magana da shi "David ka fita harkata babu ruwanka dani kayi harkan ka nayi
nawa a cikin makarantar nan." Ya ce "bazan fita a harkar taki ba, kiyi abin da
zakiyi." Kwafa tayi ta ce "to ka ci gaba da shiga zan yi maganin ka." "Ni dai ne
zan yi maganin ki, wawiya kawai Mara kishin kanta da addininta." Yana gama fadin
haka ya juya ya fice daga class din, joy taji zafin zagin ta da yayi hakan yasa a
zafafe ta mike zata bishi don ta rama, da sauri Fatima ta rikota tana bata hakuri,
batasan takamaimai abin da suka faÉ—a ba tunda da yare ne amma ta fahimci a kanta ne
suke wannan cacar bakin, kamar yadda ta bangarenta Joy ke fuskantar barazana da
kiyayya a wajen yayanta, haka take fuskantar kiyayya da kyamata daga wajen duk wani
ahlin Joy uwa uba iyayenta.

David dan uwan Joy ne cousin dinta ne, mahaifiyar shi kanwar papa ne uwa daya uba
daya.

Rarrashinta Fatima ta shiga yi tana bata hakuri, da kyar ta hakura ta koma ta zauna
don Joy akwai zafin zuciya idan ta fusata, basu fita ko ina ba har aka dawo break
aka ci gaba da lesson, har kuma akayi closing bata daina hararan David tana kwafa
ba, Fatima dai sai aikin rarrashi take kasancewar tasan halin kayarta.

Tare suka fito daga cikin school din kamar yadda suka saba hannun sakale da juna,
sarai Joy taga driventa peter yazo daukarta amma ta yi fuska ko kallon inda yake
bata yi ba saboda tana so ta jera da Fatima ,sau da yawa takance Fatima tazo su
Shiga mota su sauke ta amsa ƙememe take ƙi saboda gargadin ummi.

Peter bai damu ba don Inda sabo ya saba da hakan, rana daddaya ne idan yazo daukan
ta take yarda ta bishi.

A hanyar su sai da Fatima ta san yadda ta yi, ta mantar da Joy ɓacin ran da take
ciki na David, sai gata tana dariya har da kyakyatawa.

Wani me sai da yalo ne ya zo wucewa yana talla a bairo, har sun gifta shi Fatima
ta ce "laaa Joy bari na sai ma yayana yalo." Kafin Joy ta amsata har ta juya ta isa
gare shi, hamsin din da ummi ta bata ta mika mishi ya bata na hamsin.

Dawowa Inda Joy take tsaye tana jiranta tayi cike da farin ciki ta ce "nasan yayana
zaiji dadi sosai don yana son yalo kamar me." Taɓe baki Joy tayi tare da cewa
"Wanna yayan

Please Login or Register in order to submit comment