Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 18 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mata
allurar barci domin kwakwalwarta ta samu hutu, zuwa safiya in dan Allah ya kai mu
zamu sallameta.

Hamdala Aliyu da Maman Amira suka shiga jerowa, Al'ameen ku wa rintse idanu ya yi
shima yana jero hamdala a zuciyarsa, wani irin farin ciki da kwanciyar hankali na
maye gurbin fargaba da tashin hankalin da ke dankare a zuciyarsa. Yayinda Fatima ta
rungume Mama ta na shessheka tun da dama cikin kuka take.

Aliyu da Ameen ne suka kwana a asibitin, Mama da Fatima kuma suka tafi gida, bayan
sun shiga sun duba Ummi, tana barci kamar yadda likita ya fada.

Bayan tafiyarsu ne Al'ameen ya samu damar baiwa Aliyu labarin abin da ya sani game
da abinda ya faru, yana ba shi labarin zuciyarsa na kara daukar zafi yana sake cin
alwashi a kan kassara rayuwar koma waye wannan mutumin, shi kan shi Aliyu ran shi
ya baci, zuciyarsa ta tashi har yaso yafi Ameen daukar zafi a kan lamarin, ko da
wasa bai ta6a kawo hakan a ransa ba, ya ciji yatsa ya fi sau shurin masaki a kan
rike Al'ameen da yayi har mutumin da ko sunan sa basu sani ba ya samu damar guduwa,
karshe Ameen ne ya koma tausarsa.

Washegari karfe goma a ka sallami Ummi, a lokacin Fatima da Amira ne ke tare da ita
don Aliyu tun wuraren bakwai ya tafi gida da zummar kimtsawa ya dawo, Al'ameen ma
ganin sun zo yasa ya tafi gida don yin wanka.

Sosai makota da abokan arziki sukai ta shigowa yi wa Ummi sannu, yinin ranar bata
samu kanta ba, kallo daya zaka san bata cikin walwala amma haka ta daure ta saki
fuskarta ta dinga amsa gaisuwar yan dubiya.


Ranar da matsanancin damuwa Al'ameen ya kwana, bai iya rintsawa ba, burinsa ya ji
daga bakin Ummi 'shin wanene wannan mutumin, domin baya jin har duniya ta nade zai
iya yafe mishi.

Washe gari da safe ko da ya je gaisheta bata ce masa komai game da batun ba, haka
ya shirya ya tafi makaranta jiki babu kwari, da yamma tare suka shigo gidan da
Aliyu ya biyosa don ya sake gaida Ummi duk da jiya ma yazo, kuma mahaifiyarsa da
matar kawunsa harma da kannensa sun zo suma a jiyan.

A falonta suka same ta zaune a kan dadduma, carbi a hannunta tana lazumi, zama suka
yi suna jiranta, itama ganin shgowarsu yasa ta yi sauri ta kai karshen lazumin,
Aliyu ne ya fara gaisheta da jiki ta amsa cike da kulawa, Al'ameen ma ya sake
gaisheta.


Daga haka duk zama suka yi jugum-jugum daga yanayin fuskokinsu ta fahimci da magana
a bakunansu, ajiyar zuciya ta sauke dama ta san ko ba jima ko ba dad'e wannan
ranar zata zo, bata gama tunanin da take yi ba ta tsunkayi muryar Al'ameen yana
cewa.

"Ummi don Allah da manzonsa ki gaya mini wanene wannan mutumin? Kallonsa ta yi sai
kuma ta yi shiru, ba tare da amsa shi ba, ganin haka yasa Aliyu kar6ewa da " Ummi
don Allah ki daure ki sanar da shi, domin yana cikin matsanancin damuwa ni shaida
ne, saboda ni amininsa ne, muna da kusancin da bazai iya boye min duk wani
damuwarsa ba, nine na ba shi shawara a kan ya zo ya tambaye ki, shi kuma ya ya
dauko ni don na taya shi rokon ki, Ummi don Allah ki fad'a masa menene hadin ki da
shi."

Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu, ta ce "Dama ko baka tambayeni ba Yayan
Fatima yau ne na yi niyar sanar maka su wanene ahlin Alhussain a gare ku da nima
baki d'aya." Aliyu ya ce "Alhmdllh Ummi, Ameen ya dade yana tsumayen wannan ranar
tsayin shekaru." Ya k'arashe maganar cike da tsantsar farin ciki kamar shine Ameen
d'in. Murmushi Ummi ta yi tana sake jinjina amintar dake tsakanin Aliyu da Ameen,
kamar dai Fatima da Joy.

Fatima ce ta shigo d'akin daga hadda take, ganin yayyinta yasa fara'ar fuskarta
k'ara fad'ad'a, ta gaishesu baki d'aya a ladabce, ta wuce uwar d'aka ta ajiye
hijabinta da jakar haddarta ta fito zata wucesu, har ta kai bakin k'ofa, Ummi ta
dakatar da ita ta hanyar cewa "Fatima! Kema zo ki zauna." Bata musa ba ta dawo ta
samu guri kusa da Yayanta ta zauna, zuciyarta na tsinkewa haka kurum take jin
gabanta na fad'uwa.

Mikewa Aliyu ya yi, da nufin tafiya gida don ya basu waje, Ummi ta dakatar da shi
da cewa; Dawo ka zauna Aliyu, domin kuwa kaima d'ana ne, tamkar Al'ameen haka nake
jin ka." Bud'e baki ya yi da nufin yi mata musu, sai dai ganin yadda ta tsare gida
yasa ya kasa, sai dai bai koma ya zaunan ba kamar yadda ta umarceshi, idanunta ta
watsa mishi, irin kallon da take yi wa Al'ameen idan tana son ladaftar da shi,
babu shiru ya koma ya zauna.

Sauke kai Ummi ta yi kasa ta yi shiru duk ido suka zuba mata falon ya dauki shiru
na tsayin mintuna biyu, a hankali ta dago idanunta da suke cika taf da kwallah
cikin wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a junta da irin shi ba ta fara
cewa..............




Oum ummeertah
09116099486

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment