Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 15 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da daukin wayewar garin Monday, sai dai cikin rashin sa'a
ranar karatu ta yi musu zafi, kuma da aka yi closing Mom ce da kanta ta zo
daukarta, ba don ta so ba ta bita suka wuce gida da kudirin koma menene gobe baza
ta rabu da Teetee ba sai ta gaya mata......
[12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 35*


Washegari tun six thirty ta gama shirin school saboda gand'oki, a gaggauce ta
sauko dining, a shirye ta same shi tsab! Kamar yadda ta tsammata, sai dai tea da
cake kadai ta iya sha shima kad'an, sake kallon agogon dake daure a tsintsiyar
hannunta ta yi, ganin bakwai saura yasa ta naima waje a parlour ta zauna tana
kallon cartoon a tv duk da kallon kawai take amma hankalinta baya gurin, karfe
bakwai dai-dai ta nufi upstairs, direct d'akin Mom ta nufa, tura kofar ta yi ta
shiga ba tare da knocking ko excuse ba. Mom bata falo dama bata yi zaton ganinta a
nan ba, kai tsaye ta nufi bedroom, muryar Mom da ya daki dodo kunnenta ne, ya
dakatar da ita daga karasawa cikin d'akin.

Cike da tabbatarwa ta ke cewa "Kar ki damu Esther bani da kowa a duniyar nan bayan
ke, ke kad'ai ne iyayenmu suna haifemu tare mu biyu kuma a yanzu basa raye, ki sani
ita d'in ba komai bace a gareni fa ce tsanin cikar burina, lokacin dana dibar mana
na daf da k'aratowa, sai na tabbatar da ya mallaka mata komai nasa daidai da tsinke
bai bari ba, zan kashe shi, sannan daga baya ita......" Sauran zancen ne ya mak'ale
lokacin da idanunta suka sauka a kan Joy rik'e da k'ofa, da alamar ta ji me take
cewa' Jikinta ne yaso daukar rawa, amma tuna wacece Joy yasa ta dake rainonta ce,
ta fi kowa sanin halinta bata da shiga sabgar da bai shafeta ba. "Excuse me." Ta
fad'a tare da sauke wayar daga kunnenta, sakar mata murmushi ta yi, cike da
wayancewa ta ware mata hannayenta tare da cewa; "Come to me my dearest princess."
Martanin murmushi ta mayar mata ta k'arasa ta fad'a jikinta suka jungume juna,
"Morning my lovely Mom." Joy ta fad'a tana zare jikinta daga na Mom, rike hanayenta
Mom ta yi ta na kallon ta cikin ido don son karantar yanayinta ta ce "Morning my
Happiness, har kin shirya? "Yes Mom har ma na yi breakfast." "Auh! Shine babu jira
ko gud." Dariya ta kyalkyale da shi, "I'm sorry Mom na tashi da yunwa ne." "Ok no
prblm." Mikewa ta yi tana cewa; "Bye bye! Mom till I came back." "Ok princess nima
yanzu zan shirya na tafi gidan antynki Esther, tana can tana rigima da Mr Moses wai
sai ya sake ta, yanzu ma da ita nake waya kika shigo Esther bata jin magana
lamarinta ya fara isa na." Ta karashe maganar tare da dafe kai cike da takaici,
"Ki yi hakuri Mom ki ci gaba da abin da kike yi na alkhairi zaki samu lada." Tana
gama fad'in haka ta fice, a parlour n k'asa ta dauk'i jakarta ta fito compound,
already Peter na jiranta basu 6ata lokaci ba, ta shiga ya tukata zuwa school.

Da biyu Mom ta fad'i wannan magana, don ta kauda hankalin joy daga zargi ne, hakan
kuwa ya yi tasiri, da farko kalmar kisan da ta ji a cikin maganganun Mom sun saka
ta a shakku, sai dai jin zancen Esther yasa ta yi watsi da lamarin don bata kaunar
abin da zai had,a ta da tilon kanwar uwartata, tun a bedroom d'in Mom ta watsar da
batun, ko kafin su isa school ta shafe babin batun a ranta.

Shiganta aji da mintuna kad'an Fatima ta iso, kasancewar babu teacher a ajin yasa
ta tashi da gudu ta tare ta suka rungume juna, dakyar suka saki juna suka k'arasa
sit suka zauna, sauran student na masu dariya masu jin haushin kawancensu kuma na
ta6e baki da zund'en su.

"Teetee tell me about him, ki gaya min mana sai ja min rai kike yi." Dariya Fatima
ta saka ta ce "Sai during break." Fushi Joy ta yi ta juya mata baya, magana Fatima
ta dinga mata amma ta share da gaske fushi ta yi sosai don harda guntun kwallah ta
share ba tare da sanin Fatin ba.

Abin da ya ba Fatima mamaki da kuma dariya ana ringing bell, Joy ta kalleta tare da
cewa; "Oya tell me." Dariya Fatima ke son yi, amma sanin halin Joy na saurin fushi
yasa ta danne, ta yi abinta a ciki, narai-narai Fatima ta yi da ido ta koma kalar
tausayi kafin ta ce "Zan gaya miki amma sai kin saki fuskarki, kinji my beautiful
friend." Murmushi ta saki, Fatima na dariya ta ce "Ba irin wannan ba gaskiya, idan
ba haka ba kuma bazan fad'a ba." Ga mamakinta sai ji ta yi Joy ta kyalkyale da
dariya. Gimtse nata dariyar ta yi tana binta da kallon mamaki, gira Joy ta d'age ta
ce "A kan Yaya Ameen komai zan iya yi domin nima a yanzu shine komai nawa." Rass
gaban Fatima ya fad'i da sauri ta kauda tunanin da yazo mata zuciya, jin Joy din ta
ci gaba da cewa; "Shine ya bani matsayin kanwa, ya zame mina Yaya dan uwa abin da
na nake tsananin kewa shekara da shekaru, ina jinsa har cikin bangon zuciyata."
Murmushi Fatima ta yi ta ce "Umm! Kaji masu yayyi muma Allah ya bamu." "Amin!" Joy
ta amsa mata a gatsile. Fatima ta ce tana murmushi, "To albishirinki." "Goro fari
kal!" Ta amsa mata, "kawo kunnenki kiji." Matso da kunnenta ta yi fuskarta a washe
yau dai finally zata ji abin da Teetee ke ja mata rai a kai kwana da kwanaki,
Fatima ta kama kunnen ta matsa da bakinta cikin rad'a ta ce "Yaya Ameen ya yi
budurwa very soon zai yi Aure, zai auriAnty Amira....." 6at tattausar murmushin
dake kwance a kan fuskarta ya ba ce within second, kamar saukar gudumar wuta haka
kalaman Fatima suka daki zuciyarta take idanunta suka fara juyawa, wani irin
dunkulallen abu ya tokare mata kirji, take numfashinta ya shiga sama da kasa kamar
mai cutar Asthma.

Jin shiru yasa Fatima kallon ta, a tsorace ta zaro idanu tare da furta "Na shiga
uku." A bayyane "Joyyy!"ta kira sunanta da karfi tana jijjigata, suuu! Ta ta tafi
zata fad'i, da sauri Fatima ta rikota cikin tashin hankali take kiran sunanta da
karfi tana jijjigata, lamarin daya jawo hankalin yan tsirarun student d'in dake
ajin, da gudu wasu suka yo kansu suna tambayar menene, ya yin da wasu suka tafi
kiran class teacher d'in su. Wata cikin yan ajin ne tayi dabarar fasa pure water
mai sanyi da ke hannunta ta shiga antaya mata daga kai zuwa fuskarta, wani irin
ajiyar zuciya mai karfi ta shiga saukewa tana kokawa da numfashinta tare da kokarin
hadiye kululun daya tokare mata wuya amma ina! Abin ya ci tura. Tuni Fatima ta
dad'e da fara kuka, hannayenta bisa kai, ta ke cewa; "Na shigo uku! Joy dan Allah
kar ki mutu ki barni, wasa nake yi miki." Ana cikin haka class teacher ya shigo
bayan shi nurs na school d'in ne cikin uniform d'in su, d'auke da first aid
box.....

Kishin balbal😱



***********


A karo na babu adadi ya sake trying lambar, yana kallo har kiran ya katse kamar
koda yaushe ba'a d'aga ba, text ya shiga rubuta ma shi na ban hakuri, tare da
tabbatar mashi a kan lallai yana so su had'u a kwai story.

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin da ya gama duba sak'on, ya tabbatar ya zuwa
yanzu abokin nasa ya yi laushi, zai jaraba sa'ar shi wata kila ya dace. Replay ya
yi ma shi cewa; Zai shigo after magrib.


Karfe bakwai da yan mintuna a k'ofar gidansu Ameen ta yi Aliyu, zama ya yi a kan
dakalin wajen ya zaro waya da niyyar kiran shi, sai ga shi, babu yabo babu fallasa
Aliyu ya ba shi hannu suka yi musabaha, zama ya yi kusa da shi yana murmushi, ya
dafa kafad'ar shi ya ce "Timekeeper nawa, har yanzu kana nan da dabi'arka ta r'iko
ko?" Ba tare da ya kalleta shi ba ya amsa da "E kamar yadda kaima dabi'arka ta
kafiya bata canza ba haka nima." Murmushi ya sake yi ya ce "Baka ce min ya jikina
ba." Dage kafad'a Aliyu ya yi ya ce "Naga ai ba ka damu da lafiyar taka ba bare aje
yi maka ya jiki." Dariya ya yi ya ce "To naji baka tambayeni ya jikin My Meerah
ba." "Wacece haka?" Aliyu ya tambaya, amsa mashi ya yi da cewa; Masoyiyata mana
Amira wacce kake fushi da ni saboda ita." Sai lokacin Aliyu ya d'ago ya kalle shi.
Ajiyar zuciya Ameen ya sauke a nan ya kwashe duk abin da ya faru bayan wucewar shi
ran nan har zuwa yanzu. Ya daura da "Aliyu ina matukar tausayinta, na amince zan
zama maji6ancinta zan rayu da ita koda a zuciyata babu d'igon soyayyarta." "Bare ma
baza a rasa ba." Aliyu ya fad'a yana hararanshi, murmushi kawai ya yi ba tare da ya
tanka ba, sun dad'e suna hira, sosai Aliyu ya nuna mishi jin dadinsa game da
amicewarsa da Amira ya k'ara da nusar da shi alfanun hakan ga shi karankanshi, sai
dai koda wasa bai sako zancen Dr Abdul ba, don so yake ya bi komai daki-daki.

Tare suka yi isha'i bayan sun dawo daga masallaci ne, Aliyu ya shiga gida suka
gaisa da Ummi, ya ce "Ummi ya mai jikin nan na kwanaki." Fara'ar fuskarta ce ta
fadada ta ce "Hmmm! Aliyu mai jiki ta ji sauk'i sai hamdala, kar kaso ka ganta
yanzu kamar ba ita ba." "Masha Allah, Ubangiji ya k'ara mata lafiya." "Amin Amin
Aliyu nagode sosai." "To Ummi ni zan tafi a gayar da Fatima idan ta tashi." "To
zata ji Aliyu a gaida mutan gida."

Tare suka fito da Al'ameen don yi masa rakiya, "Aboki ya kamata ka kira Amira mu
gaisa, ka gabatar dani a matsayin babban aboki tun yanzu." Harara Ameen ya watsa
masa, ya ce "Dalla Mallam muje na raka ka, matata mai tsada ce ba'a ganinta haka a
arha." Rik'e ha6a Aliyu ya yi ya ce Ya ce "Da bamu san asalin balbela ba da sai
tace mana daga saudiya take." Had'e rai Ameen ya yi ya ce "Me kake nufi."dariya
Aliyu ya yi ya ce "Naga dai bada wani yare na yi magana ba ko?" "Kai dai ka sani
ja'iri." Haka suka yi ta raha suna wasa da dariya har ya rako shi bakin Babar titi
a nan suka yi sallama kamar kar su rabu.

Direct gidan su Amira Al'ameen ya nufa, ta sheka wanka da kwalliya tana jiran shi,
jin sallamar shi yasa ka yin wuf ta mike, kallon da Mama ta watsa mata yasa ta yi
saurin k'asa da kai, Aysha dake kallon abinda ke faruwa sai dariya take mata,
hararar ta ta yi ta gefen ido tare da yin kwafa.

Shiga falon ya yi ya zauna bayan ya risina ya gaisar da Mama, Aysha da sauran
kannenta suka gaishe shi, da gefen ido ya saki kallon side d'in da take, jin
idanunta na yawa a kan shi, gaba d'aya ta shagala da kallon shi, Mama jin kowa ya
gaishe shi banda ita yasa ta kallonta, ganin yadda ta shagala yasa ta cewa
"Amira." Ina sam bata ji ba, don ta yi nisa Sam bata jin kira, ganin haka yasa Mama
sake kiran sunanta a karo na biyu a tsawace "Amira!!!!" Firgigit ta yi ta kalli
Mama, wani irin kunya ce ta lullu6eta sai kawai ta tashi da gudu ta bar falon, tafa
hannaye Mama ta shiga yi tana sallallami.

Juyowa ta yi da zumar yiwa Al'ameen magana, sai dai wayam! babu shi babu mai kama
da shi a falon sam babu wanda ya kula da sanda ya sudad'e ya fice, ai sai ta sake
rafka salati tana rik'e haba take cewa; Aysha kin ga abin da na gani kuwa, dariya
Aysha ta kyalkyale da shi, cike da nishad'i, "Ikon Allah, yaran zamani ka haifesu
baka haifi halinsu ba ai kuwa banga ta zama ba ni hafsatu, wannan abin farin ciki
har ina." ta fada tana mikewa tsaye............



Comment and share masoya


Oum Ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 36*



A firgice Mom ta shigo cikin makaranta, tana gurin aiki kirata same ta daga
principal na school d'in Joy babu lafiya, office d'in principal ta nufa bayan
gaisuwa principal da kanta ta yi mata jagora zuwa d'an karamin clinic d'in
makarantar in da Joy ke kwance tana hutawa, don koda nurses suka tambayeta cewa ta
yi kanta ke ciwo maganin ciwon kai kawai suka bata na kwaya ta sha, daga nan kuma
suka bata bed rest kafin a iyayenta su zo.

Tun da ta kwanta idanunta ke lumshe, da gaske kanta ke yi mata ciwo, bayan ciwon da
zuciyarta ke yi mata, har zuwa lokacin babu abin da ya ragu dangane da abin da take
ji a zuciyarta,wannan kululun na nan tokare a kirjinta, babu abinda ke amsa kuwwa a
kunnenta sai maganganun Fatima, babu yadda bata yi ba, don hawaye su zubo daga
idanunta ko zata samu sassauci a zuciyarta amma abin ya faskara sai kukan zuciya
take wanda irin wanda ke kara ma mutum kunci.

Cikin wannan yanayin Mom da principal suka iso d'akin, sarai ta ji su amma ta kasa
bude ido ta kallesu, tana ji d'aya daga cikin nurses d'in wajen na yima Mom bayanin
cewa kanta ta ke ciwo kuma sun yi mata abin da ya kamata sun bata magunguna, godiya
Mom ta yi musu, ta matsa gaban gadon tare da dafa kanta, kan da d'umi, ga jijiya
nan a goshinta sun tashi alamar dai ciwon kan mai yawa ne, kallon principal Mom ta
yi ta ce "Dama tana da larurar ciwon kai tun tana k'arama, ina ga shine ya tasar
mata, amma kuma gaskiya ya dad'e bai tashi ba don tun tana da shekara bakwai muka
fitar da ita kasar Mexico ta ga wani babban likitan kwakwalwa shikenan bai k'ara
tashi ba sai yau." Cike da Alhini principal ta jajanta lamarin. "Zan tagi da ita
gida sai na kira Dr ya sake dubata." Cewar Mom, "Ok ba damuwa hakan dama shine
daidai." Matso da mota Mom ta yi har bakin clinic d'in, da taimakon nurses ta samu
ta isa motar don da ta mike jiri ne ya ringa dibanta dole a ka suka rirrik'eta suka
taimaka mata.

Har a ka tashi Fatima kuka take yi, ta firgita sosai da yadda Joy ta yi, tunda suke
tare bata ta6a ganin ta cikin yana yin makamancin wannan ba,ta yi nadamar fad'i
mata wannan maganar yafi sau shurin masaki, sai dai taki baiwa zuciyarta damar
gaskata zarginta na cewa Joy tana son Yaya Ameen ne, duk wani kofa da zai bata
damar gasgata hakan ta toshe, har suka yi closing bata fahimci wani teacher da
wani teacher bane suka shigo class d'in bare tasan me suka koyar, itama da nata
kamashon ciwon kan ta koma gida, sa'arta d'aya Ummi bata nan, dama Yaya Ameen ta
san baza ta same shi a gida ba daidai wannan lokacin sai da wani kwakkwaran dalili.
Sallar azahar ta gabatar ko abinci bata iya ci ba, ta sha paracetamol ta hau gadon
Ummi ta kwanta, babbar damuwarta rashin sanin halin da Joy ke ciki, gashi ko giyar
wake tasha baza ta iya taka 'kafarta zuwa gidansu ba, haka ta yi kwanta cikin
damuwa tana tunane tunane cikin sa'a barci ya yi awon gaba da ita mai cike da
mafarkai barkatai.


**********

Dr Solo ya kalli Mom bayan ya gama duba Joy ya yi mata duk abin da ya makata ciki
harda alluran barci don ta samu hutun zuciya da kwakwalwa, ya ce "Ciwon kan ta ne
ya yi kokarin ta shi dalilin wani yanayin tashin hankali da ta shiga, amma zuwa
yanzu da sauk'i, sai dai a kiyaye shigarta cikin irin wannan yanayin, gudun samun
matsala." Cike da damuwa Mom ta ce "ok Dr mungode kwarai." A ranta tana mamakin
wani irin tashin hankali ne Joy ta shiga haka. Sallama Dr ya yi ma Mom ya tafi tare
da alkwarin sake kira zuwa dare yaji halin da ake ciki. Tare suka five da Mom daga
d'akin don yi mashi rakiya.

Duk abin da Dr yake fada tana ji domin kuwa idanunta biyu, sai dai fitar su daga
d'akin bai fi da minti biyar ba wani nannauyar barci ya yi a won gaba da ita.

Awa bakwai cur! Ta kwashe tana barci, kafin ta farka lokacin karfe shidda daidai na
yamma, a hankali ta bud'e idanunta da suka mata nauyi, ta ji sauk'i sosai don
wasai take jin kanta babu d'igon ciwo, haka ma nauyin zuciyarta ya ragu kaso hamsin
cikin d'ari, a hankali ta lalla6a ta mik'e zaune, tankwashe kafa a tsakiyar
gadon tare da rafka tagumi da hannayenta bibbbiyu.

Maganganun Fatima ne suka shiga dawo mata filla-filla, "Yaya Ameen ya yi budurwa
very soon zai yi aure, zai auri Anty Amira." Kalmomin da su ka yi ta amsa kuwwa
kenan a kunnenta suna neman rikitar mata da kwakwalwa, da sauri ta saka hannu ta
toshe kunnenta da hannayenta tare da fashewa da kuka, take hawayen da take muradin
fitarsu tuntuni suka samu hanya, a guje suka shiga wanke mata fuska.

Kuka tayi sosai don a kalla ta kwashe kusan awa guda tana yi, a hankali ta ji
kuncin dake zuciyarta na yayewa, ajiyar zuciya ta shiga saukewa akai akai hadi da
shessheka, ita kanta baza ta ce ga dalilin kukan nata ba abin da ta sani kawai
umarnin zuciyarta take bi, sam! Zuciyarta baza ta iya jurar jin Kalmar Yaya Ameen
yana son wata mace ba, balle har a kai ga batun aure, tabbas a duniya tana ganin
babu abin da yafi wannan tashin hankali a gareta, a halin yanzu ita kanta bata san
meke damunta ba, bata kishi ba domin ita kadai ta tashi gaban iyayenta abin da ta
sani kawai soyayya, shiyasa abin da ya faru da ita yau bata san da mai zata
kwatantashi ba.

Shigowar Mom ne ya katse tunaninta, da sauri Mom ta k'araso ganin ta a zaune, zama
ta yi a kusa da ita ta kai hannu tana tatta6a goshinta zuwa wuyanta,salam! Babu
zafi ajiyar zuciya ta sauke tare da godiya da abin bautarsu. Cike da kulawa tace
"Princess ya jikin, yaya ki ke ji yanzu, ina ne ke yi ma ki ciwo?" "I'm fine Mom
babu in da ke min ciwo, naji sauk'i." "Ok bari na kira miki Papanki ku gaisa tun
dazu yake ta kira yana son yaji muryarki." Da d'unbin mamaki a fuskarta ta ce "Papa
kuma?" "Yes Ur Papa." Zun6ura baki ta yi ta ce "Ya daina sona yanzu ai." Murmushi
Mom ta yi ta ce "Who tell that, a duniya babu abin da Mr James yake kauna sama dake
tillon y'arsa,ina tabbatar miki yafi kaunarki fiye da ni dana kawo ki duniya." Ta
karashe maganar cike da d'aci a muryarta, amma sam Joy bata fahimci komai ba saboda
kakanun shekaru, "Na sani Mom a da Papa yana sona amma cikin yan kwanakin nan ya
canza min, abin ya dame ni amma na yi masa uzuri, nasan aiki ne ya sha kan shi."
"Of course princess haka ne, jiya ya kammala duk aikin sa ya kaishi kasar Canada,
yanzu hankalin sa gaba daya ya waiwayo kan little princess d'in shi, tun safe yake
min waya yana neman ki,. Ta kai karshen maganar tana mika mata wayarta da ta yi
dialling lambar Papa.

Cike da shauk'in so irinta tsakanin da da mahaifi ta kara wayar a kunnenta tare da
cewa; He'll My Papa." "My Joy My everting." Ya amsa mata cike da soyayya, sun Dade
Suna waya ta yi mai korafi akan shareta da yake yi kwana biyu hakuri ya bata da
cewa shima bai san mai ya same shi ba cikin kwanakin nan, sun dad'e Suna waya kafin
su yi sallama.

Mom ta amshi wayarta tana sakin wani shu'umin murmushi wanda ita kad'ai tasan
ma'anarsa.......

Ko kunsan ma'anar murmushin Mom, ni da ban sani ba😒


Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 37*



Mikiya Writer's Association



No editingπŸ™

Washegari a sanyaye Fatima ta gama shirin school, gaba d'aya bata cikin walwala har
sai da Ummi ta kula da yanayinta ta tambayeta ko bata da lafiya ne. Al'ameen dake
wanki a tsakar gida lokacin da Ummi ke mata magana ya d'ago ya kalleta, tabbas
shima ya hangi damuwa da rashin walwala a tare da ita, hakan yasa ya ce mata "Idan
baza ki iya zuwa makarantar ba ki barshi kawai gobe Sai ki je" da sauri ta ce "A'a
Yaya zan je." Ci gaba ya yi da wankinsa ba tare da ya sake cewa komai ba, sallama
ta yi musu ta goya gakarta ta fice.

Da sauri ya dauraye hannayensa ya bi bayanta, girgiza kai Ummi ta yi ba tare da
tace komai ba, tasan dama bazai iya barin ta tafi ba sai yaji damuwarta, idan ba
haka kuwa a cikin damuwar zai wuni.

Kasancewar ya hada da sassarfa, ita kuma a sanyaye take tafiya yasa ya cimmata a
zaure, jin k'arar taku ya sakata saurin juyowa ganin shi yasa ta shagwa6e fuska, a
gabanta ya tsaya ya kafeta da ido sannan ya jeho mata tambayar "Meke damunki?"
Take ruwan hawaye ya cika mata mata kaurin ido, "shiii!!!." Ya yi mata tare da
daura yatsa a lips dinsa ya ce "Kar ki kuskura ki zubar da hawayen nan." Kokarin
shanye hawayen ta shiga yi don cika umarnin shi, amma ina sai da su ka zubo.

Ganin haka hankalinsa, ya k'ara tashi, riko hannayenta yayi ya ce "Kin samu wanda
zaki sanarwa damuwarki wanda ya fini a duniya ko?" Da sauri ta girgiza kai, ya ce
"Oya tell me meke damunki." Cikin shessheka ta ce "Yaya Joy ce." Wani irin yankewa
gabanshi ya yi ya fad'i, "Joyyy?" Ya maimaita sunan cikin sigar tambaya, gyada mai
kai ta sake yi, cikin tashin hankalin da yake kokarin boyewa ya ce "What happend to
her?" "Bata da lafiya ne." Ba karamin jarumta ya yi da bai kai hannu ya dafe
heart dinsa ba saboda wani irin fad'uwa da ya yi, cikin wani irin voice da saida
Fatima ta d'ago da sauri ta kalle shi ya ce "Mekedamunta." Jim! Fatima ta yi
zuciyarta ne ya so shiga rudani, kasancewar ta mai azabar wayo yasa ta yi gaggawar
boye yanayinta ta ce "Ji ya ne school ta dinga yin wani abu haka kamar ta sums
numfashinta ya dinga sizing idanunta ya juya har saida a ka bata bed rest, kafin
Mom d'in ta tazo ta dauketa su ka wuce gida, ni yanzu bansan halin da take ciki ba
tun jiya." A sanyaye ya ce "Addu'a zaki ta ya ta da shi na kuka ba Fatima, ki yi
mata addu'a Allah ya bata lafiya." Ta gyada kai alamar to, ya ce "Share hawayenki."
Babu musu ta share, naira dari ya ciro a aljihunsa ya cika mata tare da cewa; Maza
ki wuce kar ki yi latti." Amsa ta yi da hannu biyu ta ce "Nagode Yayana."

Tafiya take tana tariyo abin da ya faru yanzu cike da tarin mamaki, wani irin rauni
hadi da damuwa ta hanga karara a tattare da shi, irin wanda ba kasaifai a ka fiye
gani a tattare da shi na sai a kan abu mai mahimmanci a gare shi.


Bayan tafiyar Fatima k'asa komawa ya yi yaci gaba da wankinsa, gaba daya jikinsa ya
yi san yi kalau, gabansa kuwa har lokacin bai dena faduwa ba, dakinsa ya shigeta ya
lalubi kafifarsa ya kwanta a hankali ya lumshe idanunsa da suka canja launi sabida
damuwa.

Ya dad'e a haka, ya rasa mai ke masa dad'i a lokacin ya rasa ina zai tsoma
zuciyarsa ya ji san yi, tambayar da yake jehowa kansa shine "Meya sameta? Meya faru
da ita? Meke damunta." Abinda ya yi ta maimaitawa a ran shi kenan, har bai san iya
adadalin lokacin daya 6ata ba, kiran wayar shi ne ya dawo da shi hayyacinsa, Aliyu
shine sunan daya bayyana akan fuskar wayar, a matukar sanyaye ya d'aga wayar,
magana suka yi na mintuna uku zuwa hudu kafin ya sauke wayar, message ne ya shigo
wayar, budewa ya yi, My Meerah ita ce ta yi masa sak'on sai da ya saki murmushi
kafin ya bude sakon, kamar kullum sakon Barka da safiya ne da fatan ya ta shi
lafiya hadi da zafafan kalaman soyayya, ya kan yi mamakin a ina ta koyi irin wad'an
nan kalaman, Sam! Bata jin kunyar fad'a masa kalaman soyayya, ajiyar zuciya ya
sauke ko babu komai suna burge shi kuma suna saka shi nishadi a duk lokacin da yake
karantawa.

Kwanciya ya ci gaba da yi sai da Ummi ta gaji ta biyo shi d'akin sannan ya samu
damar mikewa ya je ya karkare wankin ya yi wanka ya shirya ya tafi school inda daga
nan zai zarce wajen kasuwancinsa.

**********


Da sauri Fatima ta karasa sit d'in su, dalilin hango Joy da ta yi zaune, zama ta yi
ta shiga tatta6a goshinta zuwa wuyanya at d same time ta na tambayar ta na cewa;
Friend ya jikin ki? Meya same ki jiya. Ina ke yi miki ciwo?" Rike hannun Fatima ta
yi tana murmushi ta ce "I'm fine Teetee ki bari haka mana." Rau-rau da ido Fatima
ta yi ta ce "Hankalina ya ta shi sosai jiya, ban yi zaton zaki zo school yau ba."
Dan dariya ta yi ta ce "Matsoraciya naji sauki

Please Login or Register in order to submit comment