Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu? Ya fada maka shi
wanene? Su waye iyayensa." Dr Abdul ya ce "Easy mana aboki, wadannan irin tambayoyi
haka a jere, koda yake ba wani Abu bane tunda da cikakken lawya me zaman kansa nake
magana." Barrister Hayat ya katse shi da cewa "All, aboki, duka tambayoyin nake
bukatar amsarsu daga gareka."............


Ayi hakuri da wannan, yau bani da naji sosaiπŸ™ masu comment ngd sosai na gani kuma
na yaba much luv 2 u ppl all INA yinku irin totally. Da iya masu comment kadai fa
nake yi atoh!



Ga masu bukatar shiga group.
09116099486
[12/29, 2:36 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€

~FARHAT~


*PAGE 15*


Dr S Alto ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya ya ce "Bai gaya mani komai game
da ahlin shi ba, still yau ma ce min yayi shi maraya ne kamar yadda ya saba fada,
game da matakin ciwon shi kuwa, yanzu abin ya kai mataki na hudu a gaskiya yana
cikin hatsari ." Barrister Hayat cikin sanyin jiki ya ce "Aboki lokaci yayi da zan
dawo 9ja koda kuwa ban gama cike wa'adina a nan ba, ya zama dole na san ko wanene
shi, jikina yana bani cewa mafarkina yana gaf da tabbata." Dr S Alto ya ce "Aboki
ban katsi hanzarin ka ba, sai dai ina mai kara baka hakuri, kayi hakuri ka zauna ka
kammala aikin da ya kaika, kar muyi biyu babu." A dan harzuke Barrister Hayat ya ce
"me kake so ka gaya min, wani irin biyu babu, kafin kowa sani na Abdul idan da
wanda zai karfafa min gwiwa akan lamarin nan baren ka ne, amma sai naga kamar baka
dauki lamarin da muhimmanci ba." Dr ya ce "Ba haka bane Hayat, so nake mubi komai
a hankali, ka tuna fa har yanzu, tsammani kawai muke bamu da tabbaci, kuma har
yanzu idanunsu ba wai ya dauke akan ka bane, kana dawowa Nigeria ba tare da
wa'adin ka ya cika ba, zasu saka maka ayar tambaya duk wani motsin ka zai kasance
a kan idanun su, kayi hakuri ka zauna nayi maka alkawari kafin nan da shekaru biyun
da suka rage maka ka dawo kasarka zan tabbatar na gama duk wani bincike daya
kamata." Ajiyar zuciya B Hayat ya sauke, a sanyaye ya ce "Na yarda da kai Aboki, a
duniya bayan y'an uwana bani da wanda ya fi ka, na san zaka iya, na damka maka
amanar rayuwata ka kulamin da ita." Dr ya ce "in sha Allah na maka alkwari bazan
baka kunya ba." Daga haka ba su yi wani hira ba, suka yi sallama zuciyoyin
kowannen su a jagule musamman Barrister Hayat wanda maganar ta yi mishi fami a
zuciya.
***********

*JOY*

Zaune ta ke a kyayataccen garden din gidan su, yammaci ne mai cike da ni'ima
kasancewar garin yau kwata kwata basu ga kyallin rana ba saboda ruwan da aka kwana
ana tsugawa daren jiya kamar da bakin kwarya. Books ne a gabanta da yawa, ta kwaso
domin tayi karatu saboda gabatowar lokacin fara mid term test wanda ya kasance na
third term ne, wato na canza aji, d'aya daga cikin books din na rike a hannunta
tana dubawa, a zahiri idan ka ganta zaka dauka a gaske karatun takeyi amma a
badini kwata kwata hankalinta baya kan karatun, tunani ne fal zuciyar ta, kallo
daya zaka fahimci bata cikin walwala ko kad'an, yau kimanin kwana biyar kenan data
aikawa Fatima letter, amma har satin ya kare bata je school ba, gashi on Monday
zasu fara mid term test, bata yi aune ba sai kawai ta ji hawaye na zuba daga
idanunta yana diga kan book din da take kallo, Ta na matuk'ar kewar Fatima ji take
kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan su, ta ke ta shiga tunano yadda suke gudanar
da rayuwarsu a baya, yadda suke nunawa juna tsatanin kauna da kulawa babu kyamata
kyashi ko hassada tsakanin su da juna soyayya ce gangariya daga indallahi' ta tuna
ranar data fara haduwa da Fatima, farkon shigowar su SS1, wata rana suna zaune a
class aka kawo musu new comer Fatima Husain, kallo daya suka yi wa juna a tare suna
sakarwa juna murmushi kamar dama sun san juna, lokacin da class Master su yaba
Fatima umarnin ta je ta samu sit ta zauna direct ta nufo kujerarta duk da cewa ga
sauran empty sit nan a class din da yawa kuma ga musulmai nan yan'uwa ta a ajin,
babu musu ko gaddama ta matsa mata ta zauna, ranar ko kalmar A bata shiga tsakanin
su ba, sai satar kallon juna da suke yi kamar wasu munafukai, idan suka had'a
idanu su sakar wa juna murmushi, tun daga ranar farko da suka fara haduwa zuciyoyin
su ya sark'e da soyayyar juna, sun kai kusan kwana uku a haka kullum idan Fatima
ta zo sit d'inta ta ke zama suyi ta kallo juna, maganar farko data fara shiga
tskanin su a rana ta hud'u maths teacher ya shigo ya yi musu lesson bayan sun gama
ya bada class work kowaccensu ta dauko notebook d'inta ta fara solving, Fatima ta
gama nata kamar yadda suka saba satar kallon juna ta juya ta saci kallon na Joy,
zaro ido tayi ganin yadda ta yi solving wrongly, sai dai ta rasa yadda zata gaya
mata, ta zauna tana ta sak'e sak'e , har lokacin data mik'e zata je tayi submit,
har ta fita daga sit d'in ta ji an riko hannunta, juyowa tayi suka kalli juna cikin
ido, cikin inda inda Fatima ta ce "please can I see ur calculation." "Why not." Ta
amsa mata da murmushi tare da mik'a mata, bata ce mata komai ba ta shiga gyara mata
inda ta yi kuskuren tana gamawa ba tare da ta kalleta ba ta mik'a mata tare da cewa
"ki yi hakuri da shisshigina." Sai lokacin ta kula da kuskuren data tafka, murmushi
tayi tare da ce mata "Thanks" Itama ta sakar murmushi ba tare da ta amsa ba. Tuna
wannan yasa Joy sakin murmushi ba tare da ta san tana yi ba, still ga hawaye a
idanunta, Hannu ta saka a aljihun wandonta ta zaro letter n nan na Al'ameen, daya
zame mata kamar wani gold duk inda zata je yana tare da ita da shi take kwana
rungume a jikinta duk daren duniya, ta warware pepan tana kallo, sai dai har yau
bata sauya zani ba a duk sanda zata daura idanu a jikin rubutun gabanta sai ya
fad'i, ba tare da tasan dalilin hakan ba, tana kallo tana ci gaba da hawaye ta ce a
bayyane "I missed u a lot my Teetee." ba ta san isowar Mom ba sai jin muryar ta
tayi akanta, ta na ce wa "Joy what's wrong wit U? me ya same ki, kukan me kike
yi." Da sauri ta shiga goge hawayenta at same time tana kokarin boye letter n
cikin inda-inda ta ce "Nothing Mom, abune ya fad'a min a idanu." Mom da ta gama
karantar rashin gaskiya k'arara a fuskarta ta shammaceta ta fusge letter n, a
bayyane ta karanta abinda ke ciki "THANK YOU." A razane ta kalli Joy data zaro
manyan idanunta cike da fargaba ta watsa mata, k'ank'ance ido Mom tayi cike da
tashin hankali ta ce "Menene wannan Joy?" Ta ce "Babu komai Mom." Mom ta ce "
Wannan letter daga ina." Cikin inda-inda ta ce "Ya dade sosai Mom a cikin textbook
dina, yanzu dana dauko su ina dubawa shine na gani." Mom ta ce "To naji wannan
kukan kuma na menene shi?" Ta ce "Ba kuka na ke yi ba Mom abune ya fada min a ido."
Ko kadan Mom bata yarda da batun ta ba, hakan yasa ba tare da wani dogon nazari ba
ta daga letter n ta kekketa shi. Rintse ido Joy ta yi don ji tayi kamar zuciyar ta
Mom ke ketawa, lura da haka yasa Mom yin gutsi gusti da shi yadda koda ta tattara
pieces din baza ta gane komai ba. Tana gamawa ta ce ki tashi muje ciki kiyi yan
shirye shirye, tafiyar gaggawa ta kamani gobe da sassafe zamu bi jirgi zuwa Oshogbo
. Cike da mamakin me zai kai su Oshogbo tana tsaka da shirin fara mid term test
hankali ta she ta ce "Mom Oshogbo kuma." Mom Ta ce "Yes of course." "Ba sai hutun
karshen shekara Mike zuwa ba? Kuma next week Monday zamu fara text." Mom ta ce
"dat is not my prlm." Cikin shesshekar kuka tace "Gaskiya Mom ni bazan je ba." Wani
mugun kallon ta watsa mata tare da saka mata wata uwar tsawa da gufu ta mike tayi
cikin gida tana kuka.

*********



Tsawon sati guda Al'ameen bai cewa Amira komai game da batun karatun su ba, iya
damuwa ta shiga damuwa gashi tana jin kunyar sake tunkarar shi da maganar, yau a
islamiyya, ta zayyane wa Zainabu halin da take ciki, Zainabu ta ce "Ko dai ya mata
ne?" Amira ta ce "bana tunanin haka." Numfashi Zainabu ta sauke ta ce "Fatima zaki
aika ta tuna masa idan ma mantuwa yayi sai ya tuna." Amira ta ce "nima tunanin da
nake yi kenan k'awata.sai dai nake ga kar yaga kamar na cika gajen hakuri." Zainabu
ta ce "Bana ganin zai ce haka a yadda kike dan bani labarin halayensa, ni nama fi
zargin mantawa yayi."
Amira ta ce " to shikenan yau zan mata gamana sai mu ji mai zai ce, amma wallahi ni
kunyar sa nake."Tsaki zainabu tayi ta ce "wannan kunyar naki wallahi shi zai
kasheki Amira." "Hmmmm wallahi kawa dan dai baki san shi a zahiri bane, kamar zaki
haka ya ke da kwarjini bashi da wasa baya daukar wargi at all.".............



Ga masu bukatar shiga group
09116099486
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


*PAGE 16*


Da gudu ta k'arasa d'akinta ta fad'a kan bed d'inta tana sakin wani irin numfashi
mai zafi, can kuma sai ga hawaye shaaa! kamar an bud'e famfo, wani irin tafarfasa
zuciyar ta ke mata. Yanzu shikenan Mom ta yaga mata wasikarta, shikenan Mom ta
rabata da letter n ta, ji take kamar wani part na jikinta aka yaga mata ba fallen
takarda ba, tana jin son latter n nan sosai a ranta shi kadai me debe mata kewar
Teeteenta. Ranta ya matukar baci da abin da Mom ta mata yau, tun da take bata ta6a
ja'inja da ita ba amma wannan karon ta lashi takobin ko zata yanka ta baza ta bi
ta Oshogbo ba suna tsaka da shirin fara text, Ai ba dole ba ne sai anyi tafiyar da
ita, zabura tayi ta mi'ke tare da d'auko wayar ta dake yashe kan madubi, bata damu
da waya ba don sai tayi sati bata ta6a wayar ba musamman idan Papa yana gari, idan
baya nan dai dama kullum da safe zai kiranta ya ji lafiyarta ko ita ta kira shi.

Lambar Papa da tayi saving da My blood ta laluba ta dannawa kira, lucky ringing
biyu ya d'aga, ta na jin muryar shi ya ce "He'll my lovely princess my Joy." Ta
daddage ta fashe da wani irin kuka mai k'arfin gaske, kamar yadda ta tsammata a
rud'e ya shiga tambayar ta "Menene ? Mekefaruwa ? waya ta6aki? Kina ina ne yanzu?
Ina Mom dinki?" Babu d'aya data amsa sai ma k'ara sautin kukanta da tayi, aikuwa
Papa dake zaune a office d'in abokin shi Mr Jack dake kasar Canada ya mike tsaye,
ya shiga safa da marwa yana mata magiyar ta yi shiru ta daina kuka haka, sai da ta
bari ta gama rud'ashi sannan cikin wani irin shagwabebben muryar mai hade da
shesshek'a ta ce "Papa Mom ne." Wani irin kankance idanu yayi don bai ta6a
tsammanin Mom ce ta saka mishi tilon yar shi irin wannan kukan ba, tausasa murya
yayi dan kar ya kara daga mata hankali ya ce "Mom din ki kuma? Me tayi miki." Sai
da ta gama jan majina ta ce "Ta ce wai gobe in shirya muje Oshogbo kuma On Monday
zamu fara test." Cikin danne bacin ranshi ya ce "Ki ce mata bazan kije ba." "Na
ce mata ta ce wai ban isa ba." Zazaafar huci ya fesar ya ce j "Ok haka ta ce, To ki
kwantar da hankalin ki ni nace baza ki je ba, yanzu dai ki share min hawayen ki
bari na kira Mom din naki muyi magana." Ta amsa da "Toh Papa." Tana share hawaye.

Bayan ficewar Joy daga garden da wani irin mugun harara Mom ta raka bayanta, a
bayyane ta ce "Ya zama dole mu tafi Oshogbo tare gobe goben nan kamar yadda bokanta
ya umarta bazan yi sakacin da aikina na shekara goma sha biyar zai lalace ba, zan
Iya kawar da duk wanda ya ce zai min shamaki da wannan burina kowaye, Ta karashe
maganar tana huci kamar kububuwa. Daga haka kuma tabi bayan fuuuu Joy, sai dai
kuma kafin kai ga karasawa dakin Joy wayar ta ya dauki ruri, ganin lambar Papa yasa
gabanta faduwa kar dai ace yarinyar nan ta kira Mr James ne, shaf ta manta da hakan
da kwace phone din ta, dakewa tayi ta daga cikin kissa ta ce"He'll My O..... Kafin
ta kai ga karashe maganar ta ya dakatar da ita ta hanyar ce wa "Alice!!!!!" A tsawa
ce. Diriricewa ta yi don tsawar ya shigeta, don bata ta6a tsammanin hakan ba,Rabon
da ya mata irin wannan tsawar tun kafin su dawo Niger state da zama, kafin ta dawo
hayyacinta ya rude da fada akan me zata saka mishi d'iya kuka Akan me zata tilasta
ui. Abinda bata so, sai da ya.mata tatass ba tare da ya bata damar amsawa ba ya
daura da kuma "Ban amince miki ki fita ko bakin get da ita ba, ki je duk inda zaki
je na lamince miki amma ban amince ki tafi min da Y'ata ba wannan umarni nake baki,
idan kuma kika ki ji." Ya yi kwata! Bai jira cewar ta ya katse kiran, ya sake
kiran Joy ya ci gaba da rarrashinta.

Daskarewa Mom tayi a tsaye a inda take, tana zazzaro idanu hankalinta a kololuwar
tashe, kar dai a ce aikin da ta sha bakar wuya aka yi mata akan Mr James lalace,
tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, hannu na rawa ta lalubi lambar bokonta
Kubal. ta danna mishi kira, cikin sa'a ya daga muryar na rawa ta shiga kwashe abin
daya faru tana zayyana mai, tsawa ya faka mata shima , a kausashe ya ce "Na gaya
miki matukar baza ki rabata da wad'an nan ahlin ba ba kiga komai ba, duk wani abu
da kika binne ina mai tabbatar miki sai ya tonu." Hankali ta she Ta ce "Na rabata
da su Kubal duk wani tsaro da takumkumi na saka mata, na shata babbar layi a
tsakanin su." Dariya ya kece da shi mai ban tsoro lokaci daya ya gimtse sannan ya
daura da "Wannan bai isa ya raba alakar jini da jini ba, kizo da ita garemu kizo da
ita garemu kizo da ita garemu zamu rabasu rabuwa ta har abada." Ta ce "Mr James ya
hana kubal. ka taimakeni bana son na rasa aurena ba tare da ba samu ci kar burina
ba, ka taimakeni da kai kadai na dogara, tsoro nake ji kar Mr James ya rabu da ni."
Boka Kubal ya a tswace ce "ki taho ke kadai da gaggawa, zamu canza kalar aikin
namu, ki taho da gaggawa." Ka fin ta bashi amsa tuni ya yanke kiran.

A gurin ta zube ta daura hannu akai, ta san idan har asirin data ma Mr James
tsohon shekara sha biyar ne ya karye kashinta ya bushe tabbass kashinta ya bushe,
bata ga ta zama ba, idan ba haka ba ta tabbata zata kare rayuwarta a prison madadin
ta zama daya daga cikin matan da suka yi ficce suka shahara a duniya kamar yadda
take buri, zabura tayi kamar zautacciya ta bar gurin a guje, dakin ta ta shiga ta
fara hada kayanta.

Ranar daga ita har Joy basu samu barci mai kyau ba, Joy kukan bakin cikin rabata
da letter n ta, ta kwana yi, yayinda Mom tsananin tashin hankali ya hanata
rintsawa.


********


Kamar yadda suka tsara da Zainabu hakan ce ta kasance, washe gari kamar yadda ta
saba ta shiga wajen Ummi bayan ta tabbatar Al'ameen ya fita, a tsakar gida ta samu
Fatima na wanke wanke Ummi na daki, dakin ta nifa ta durkusa har kasa ta gaida Ummi
cike da lababi,cikin fara'a Ummi ta amsa tana saka mata albarka daga haka ya fito
ta saka hannu tana taya Fatima dauraya suna hira, cikin hiran Amira ta ce "Wai ni
kam Fatima Yaya Ameen na nan kuwa." Fatima ta ce "Yana nan mana yanzu bai dade da
fita ba." Amira ta ce "Ikon Allah wallahi na kwana biyu ban gansa bane, duk zato na
yayi tafiya ne ." Fatima ta ce "A'a yana nan wallahi." Shiru Amira ta dan yi can
kuma ta ce "To kodai ya manta ne?" Fatima ta kalleta cikin rashin fahimta ta ce
"Ban gane ba Anty Amira." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wallahi rannan nan mama ta
saka na tambaye, wai ko na kawa past question na waec ya dinga koyamin kafin namu
jarabawar ya kara so, ya amsa min da to zai ne me ni idan ya shirya amma na ji shi
har yanzu shiri shi yasa nayi yunanin ko yayi tafiya ne, Ashe yana nan, shine nake
tunanin ko ya manta ne." Fatima ta ce "abin ya kai kwana nawa yanzu." "Ummm! Ina
ga yafi sati fa." Cewar Amira, "kai anya kuwa! Yayana bai cika mantuwa haka ba,
amma dai ki kara tuna ma shi kiji, zai Iya yuwuwa mantawar yayi" marairai ce murya
Amira ta yi ta ce "Fatima dan Allah ki taimake ni ki tuna mishi yau idan ya
dawo." "To me zan ce ma shi?" "Ki ce Yaya Anty Amira ta ce wai ya maganar da
kuka yi ran nan na karatu. Haka kawai zaki ce masa nasan zai tuna." Fatima ta ce
"to shikenan in sha Allah idan ya dawo yau zan dasa masa."


Haka ko akayi a ranar da dare bayan Al'ameen ya dawo suna zaune a tsakar gida kamar
yadda suka saba, Fatima ta ce "Yawwa Yaya Anty Amira ta ce wai na tuna maka ya
maganar da kuka yi ran nan na karatu, wai har yanzu ta ji shiru daga gareka." Dan
ya mutsa fuska yayi, jin abinda Fatima ke fada, sarai yana sane da ita shareware
yayi don shi a halin yanzu yana tsoron kebewa da wata mace wacce ba muharramarsa
ba, bai manta da abin daya faru ranar da tazo tambayarsa ba, common turarenta na
neman zamar masa masifa. Ummi kam jin an ambaci Amira, tuni ta maido hankalinta
Kansu ta ce "Binta me ya samu Amiran?" Fatima ta ce "A'a Ummi babu komai, ta aikoni
wajen Yaya ne akan maganar da suka yi da shi, wai ta tambaye shi zai koya mata
karatun jarabawan su dake gabatowa, ya e mata to zai neme ta amma yau kusan sati
bata ji daga gareshi ba, shine ta ce idan ya dawo na tuna masa." Kallon Al'ameen
Ummi tayi dai dai shima ya kallota suka hada idanu, da sauri ya sauke kai. Ta ce
"Yayan Fatima idan da hali ka koya mata dan Allah, Amira yarinyar kirki ce." Shiru
yayi kadan kafin ya amsa da "Toh Ummi." Sannan ya dago ya kalli Fatima ya ce
"Fatima ki CE mata gobe idan na dawo da daddare tazo sai mu fara karatun." Yana
kallon Ummi ta gefen ido yadda fuskarta ta yalwatu da fara'a. Fatima ma taji dadi
don ba karya tana son Amira kamar dai Ummi.


*******


Washegari Sunday da sassafe Mom ta fito da trolley dinta, cikin shirinta na tafiya,
sai da ta daidaita komai batta driven da zai kaita airport yana zaune a mota yana
jiranta sannan ta nufi dakin Joy, tura kofar tayi da karfi, taga ya bude, bata
zaci a bude kofar ya ke ba, shiga ta yi, a kwance ta sameta idanunta a rintse kamar
mai barci sai dai ba barcin take yi ba, hasalima jin motsin mom din ne ya saka ta
rintse idanu, tsayawa a kanta Mom ta yi ta kare mata kallo, sai da tayi mai isarta,
sannan ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce "Daughter zan wu ce." Sai lokacin
Joy ta bude kumburarrun idanunta amma bata ce komai ba, Mom ta sake cewa "Ba yan
school ban lamunce miki zuwa ko ina ba, zuwa anjima Madame Esther zata zo ta zauna
dake kafin na dawo." Daga haka ta juya ta fice Joy ta rakata da kallo.

Bani da isasshen lahiya banyi editingπŸ™

Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni.
9116099486
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€
~FARHAT~


*PAGE 17*


Tana tsaye jikin windon d'akita tana kallo har motar Mom ya bar compound d'in
gidan, ko kad'an bata ji wani damuwa ko alamar kewa a zuciyarta game da tafiyar Mom
ba , sabanin hakan sai ma wani irin sanyi da farin ciki ta ji yana huda zuciyarta,
wani tsalle ta daka tare da fad'awa kan tattausar katifarta, yau jin ta take yi
kamar sakakkiyar tsuntsuwa, rasa irin murnar da zata yi yasa ta ci gaba da jumping
akan bed d'in tana tambul da adungure, sai da ta ji ta fara gajiya ta dakata tana
sauke numfashi, bayan ta dan huta daga tsalle tsallen murnanta, ta mik'e ta fad'a
toilet ta shek'a wanka, tana yi tana wake wakenta alamar cikin farin ciki take,
gaban mirror ta tsaya daure da mini tawul, tana kallon fuskarta, Zum6ura baki tayi
ta kwa6e fuska, bayyane ta ce "Ji duk yadda nayi baki kamar bani ba, duk Mom ta
gama ramar dani da jidalinta." Kwafa ta yi ta harari mirron kamar dai Mom d'in na
cikin madubin ne, kallon kayan kwalliyar dake shake kan mirron tayi sai kuma ta
saki murmushi ta ce "Bari nayi wa My Teemah kwalliya." Kujera ta ja ta zauna,
cikin gwanancewa ta shiga fesa kwalliya a kwakkwayar doguwar fuskarta.

Bata cika yin makeup ba, shi yasa duk sanda tayi yake zama special a fuskarta,
lallausar gashinta ta tattara tayi paking din shi gefe ta zubo da jelar ta gaba har
kafad'unta, ta yi kyau sosai matuk'a gaya kamar wata y'ar tsanar roba. Mik'ewa tayi
ta isa gaban wardrobe din ta ta wangale kofofin shi, tsayawa tayi tana kallon
kayyayyakin ciki, kaya ne shake a ciki ba na wasa ba, wasu ma batta taba sakawa ba
sai dai duk kanana ne babu wani na mutunci a ciki, idanuta ne sauke akan wani kaya
da Papa ya taba kawo mata daga America lokacin da yayi wani tafiya, kaya ne masu
matukar kyau da tsada irin ta yayan masu jajayen kunnuwa, bata taba sakawa tunda
ya bata ta jera su a sif, zarowa ta yi ta warware kayan. Straight skirt ne mai
dauke da dogon tsagu ta baya red colour da riga karami mai hannun bes White
colour mai V neck a gaban rigar an rubuta JOY cikin wani irin design mai kayatarwa
ya sha stone sai walwali yake, sai dan karamin jaket kalar skirt din, iyakar shi
kasan boobs yana da igiya daga kasa da za'a d'aure ta gaban.

A tsanake ta shirya cikin kayan tsab! Duk da kasancewarta bera dan yanzu take
shiga sha biyar hakan bai hana kyakkyawan surarta kayatuwa cikin shigar ba,
siririyace sosai sai tsayi, sai dai akwaita da faffadan gudu, hakan yasa take da
shape kayatacce, idan ka dauke hakan babu wani abu jan hankali a jikinta, dan y'an
boobs dinta basu fi girman lemon tsami ba samsam basu da girma shiyasa bata fara
saka bra ba.

Takalmi half cover ta saka fari ta daura agogo a tsinstiyar hannunta, daga haka ta
fito daga d'akin ta da sauri har tana had'awa da d'an gudu, direct get ta nufa ko
tsayawa ta yi breakfasts ta kasa, sai dai tana isowa, d'aya daga cikin security
d'in dake bakin get, ya ce "Miss kiyi hakuri madam ta ce kar a bari ki fita, in dai
ba school zakije ba." Bata san lokacin da ta kwaso wani irin mugun kallo ta watsa
mashi ba, take ta fusata kasancewarta dama gwanar saurin fushi babu wuya ta hassala
sai sai tana da saurin sauka. A tsiwace cike da gadara ta ce "Na ce Ku bud'e min
get zan fita." K'asa yayi da kai ya ce "I'm sorry Miss sai dai Ki kira madam ki
sanar mata." A tsawace ta ce "Bazan kirata ba! kuma ina umartanka da ka bud'e min
get kokuma yanzu wallahi a bakin aikin ka." Tsorata yayi ganin yadda ta ke huci yar
karamar yarinya da masifa kamar wata babba, shikam bazai so abinda zai raba shi da
wannan aikin daya samu mai maik'o ba, jiki na rawa ya shiga bata hakuri, ko kallon
banza bai isheta ba, dsauri ya bud'e mata karamin kofar yana mata a dawo lafiya
tana fita ya lalubi lamabr Mom don ya sanar mata, sai dai wayar tak'i shiga
kasancewar jirgin su ya riga ya lula.
Sai da ta fito gida sannan, ta ji wani tsoro na shirin kamata sabanin da da take
cikin farin ciki, da wani ido zata kalli Fatima, da Ummi, uwa uba Yaya
Al.......kasa karasa tunanin tayi don bata fatan hakan takasance fatan ta Allah
yasa zuwa yanzu baya gida, duba agogon dake daure a tsintsiyar

Please Login or Register in order to submit comment