Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tsaye Sayako ya nufa
gidan Alhaji Bala ko zai samu keke, don d'azu da safe ya je babu keke a k'asa.
Cikin sa'a kuwa yana komawa ya samu, singning yayi ya dauka ya kama aiki.


*******

A cikin y'an kwanaki kad'an Amira tayi namijin kokari wajen cusa kanta gurin
Ummi, har ta kai yanzu da sun zauna hira Ummi bata da wani zance sai nata, a
6angaren Fatima ma babu laifi don tana kyautata mata sosai tare da jan ta a jiki,
kun san kuma ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata. Sai dai fa har
zuwa yanzu uban gayyar bai san da zamanta ba, iyakar ta da shi gaisuwa, shi ma a
d'arare don bata sakin jiki idan yana waje ta dinga sunne-sunnen kai kenan, kunyar
shi take ji matuka gaya, babu wata sanayya mai karfi a tsakanin su, hasalima duk
sanda zasu gaisa da sunan d'aya daga cikin kannenta yake kiranta alamar bai
tantance ta daga cikin su ba, bare har ya kai ga batun bata wani matsayi na
musammam a zuciyar shi abinda ke matukar ci mata tuwo a kwarya.

Yau a islamiyya bayan an tashi su ka ke6e da k'awarta aminiyarta Zainabu wacce ita
ka'dai ce ta san halin da take ci game da soyayyar Al'ameen, haka duk abinda take
wa Ummi ita ta bata shawarar yin hakan kasancewar ta fita wayau da sanin duniya.
Cike da damuwa ta kalli Zainabu ta ce "Zainabu Ya zan yi Al'ameen ya so ni? ya zan
yi ya kalle ni da kallon soyayya koda rabin rabin wanda nake masa ne? na kusa
gazawa zuciyata ta kusa tarwatsewa da soyyayar sa, Babban b'akin cikina shine yadda
har yanzu ya kasa tantance ni a tsakanin kannaina bare har na samu wani matsayi
na musammam a wajensa, bazan yi ci gaba da jurewa ba Allah ya gani nayi Iya yina
wajen kare martaba da mutuncina na d'iya wajen ganin ban zubar da kimata na fara
furta mashi kalmar so ba, duk wani alama da zan mishi na ma shi ya kasa ganewa, ya
zan yi Zainabu ki bani shawara zuciyata zata tarwatse ki taimakamin plsss zeee."ta
karashe maganar tare da kama hannun Zainabu ta kamkame cikin nata da karfi. Cike da
tausayawa Zainabu ta ce "Na fahimci halin da kike ciki kawata domin nima na taba
tsintar kaina a irin wannan halin da kika shiga, dole zamu sake salo tunda munyi
mashi ta baya bai fahimta ba, ya zama dole ya san da zamanki don baza mu tsaya
kallon ruwa kwad'o ya man kafa ba." Nan suka shiga tsara next plan din su, wanda
zasu fara aiwatarwa a ranar ba sai gobe ba.


********

Lokacin da Peter ya koma gida, Mom na main parlour, hakan yasa bai nemi Miss Joy ba
bare ya samu ya bata sakon ta, har dare basu samu haduwa ba, Mom ta kasa ta tsare
kamar ta fahimci tana aikata wani abu. Wajejen karfe taran dare ta kasa jurewa,
dabara ne ya fado mata , da sauri ta dauki telephone din dakinta takira kitchen ta
bada umarnin a kawo mata juice daki, babu jimawa daya daga cikin ma'aikatan gidan
ta yi knocking, umarnin shigowa ta bata, bayan ta ajiye mata juice din zata wuce
Joy ta kira ta, juyowa yayi cike da ladabi ta tsaya, ta ce mata, tana son ta bin
ta kofar baya na kitchen ta je wajen Peter ta karbar mata sako,idan ta karbo ta
boye sosai yadda Mom ba za ta gani ba ta hado da bottle water ta kawo mata.

Haka ko aka yi, babu bata lokaci, maid din ta kawo mata, amsa ta yi ta mata godiya,
sai da ta maida kofar ta saka lock saboda tsaro, sannan ta koma ta zauna ta shi ga
warware pepen cikin wani irin yanayin mai wuyar fassaruwa, idanunta da hankali ta
kacokam na kan shi pepan Har ta gama warwarewa. Wani irin yankewa gabanta yayi ya
fadi lokacin da idanunta ya saka akan wani unique handwriting mai shegen kyau da
kayatarwa, a fili ta furta abinda ke rubuce a jikin pepan THANK YOU. Sake kure
rubutun tayi da idanu har zuwa lokacin gabanta bai daina faduwa ba, zuciyarta ta ne
ya bata ba rubutun Fatima bane, to amma kuma rubutun yayi kama dana Fatima, sai
dai yafi na Fatima kyau da kayatuwa, to idan ba rubutun Fatima bane na wanenen?
AL'AMEEN, zuciyar ta ya bata amsa, take wani irin tsoro had'i da firgici ya ziyarce
ta, zaro kyawawan idanunta tayi tare da sakin pepen ya fadi kasa.

A dai dai wannan lokacin Al'ameen ya fito daga masallacin unguwarsu, dawowar shi
kenan bayan ya mayar da keke ya tsaya yin sallah, yana isowa kofar gida ya tuna da
letter Joy, dakatawa yayi a kofar gida kasancewar a kwai wutar NEPA ko Ina na
wadace da haske, yasa ya lalubi dakalin dake Jikin gidan su Amira ya zauna tare da
zaro latter a aljihu. A hankali ya warware linkin da aka yiwa pepen, shina kamar
yadda ya faru da joy haka ya faru da shi ras ras! Gaban shi ya fadi,lokacin da
idanun shi su ka sauka akan wani dan rubutu da kwata kwata bai wuce layi goma ba,
babu abin da yafi daukar hankalin shi irin drowning din hearts din dake Kasan
rubutun, samun kanshi yayi da kasa dauke idanun shi akan hearts din. Bai san Iya
adadin lokacin daya dauka a haka ba, sai jin sallama yayi a gefen shi, firgigit
yayi tare da saurin kallon side din da ya jiyo sallamar, Amira ce sanye da dogon
hijabinta daya sha guga har kasa, tana tashin kamshi kamar wacce tayi wanka da
turare, idanun su na sarke wa tayi kasa da kanta teke duk wani jarumta da karsashin
ta ya tafi, jikinta ya d'an fara rawa.

Kallon ta ya yi, ganin tayi shiru ya ce "Aysha ya akayi." (Kanwarta dake binta)
wani bakin ciki ne ya ziyarceta take ta dake , cikin dan rawar murya ta ce "Amira
ce ba Aysha ba ce." Ya ce "Ooh sorry Amiran Ummi ko?" Dan murmushi tayi cike da
farin ciki, ya sake cewa " ya akayi ne?." Dan Jim ta yi kafin cikin dan. jin
nauyin tsareta da yayi da idanu, ta kara yin k'asa da kanta ta ce" Yaya Ameen dan
Allah dama nace idan babu damuwa zan kawo pass questions na waec and neco ka koya
min saboda muna daf da fara exam kuma kuma ni ban samu yin karatu sosai ba." Ta
kareshe maganar a d.arere.

Shiru yayi yana jin wani irin kasala na saukar masa saboda karfin turaren da ke ta
shi daga jikinta.

Ganin yana shirin Shiga wani yanayin yasa ya ce da sauri " shikenan kike idan na
saka lokaci zan neme ki." Daga haka ya mike ya shigo zauren gidan su da sauri ba
tare da ya jira ita ta fara tashi ba.......
Yau na je suna ban wuni gida ba amma dai ga alkawarin da na muku jiya na cika duk
da babu yawaπŸ™
[12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


*PAGE 13*


Yana shiga zaure ya a daddafe ya bud'e d'akin shi ya fad'a, bakin katifa ya laluba
ya zauna yana sauke numfashi a wahalce. Ya rab! Wannan wace irin masifa ce ke neman
yi wa rayuwarsa karan tsaye. Meke shirin faruwa ne? Bai ta6a jin irin wannan
yanayin ba don ya shaki wani abu makamancin turare, Ras! Gaban shi ya fad'i, kar
dai ace maganar doctor ne ya tabbata, kar dai ace matakin ciwon shi ne ya k'ara
daga stage two zuwa four kamar yadda doctor ya sanar ma shi ce wa hakan na iya
faruwa a ko wani lokaci matukar bai d'auki matakin da ya da ce ba. Innalillahi
wainnailaihi rajiun! Ba ya fatan ace haka ne, sai dai kuma a kullum lamarin k'ara
gaba ya ke. Shi mutum ne mai matuk'ar tsantseni da kiyaye addininsa hadi da dokokin
ubangijinsa, tun da ya fahimci lalurar shi, ya kiyayi kanshi da mu'amalantar duk
wata d'iya mace, matukar ba muharraman sa biyu ba. Fatima da Ummi. Yana tsoron wata
rana ya kasa rike kan shi, yana tsoron wata rana ya kasa controlling kan shi, shin
ina mafita? Ya yi zama kusan na awa biyu a d'aki yana sak'awa da kwancewa, batare
da yasan lokaci ya ja haka ba, k'arshe ya yanke shawaran zai kai ma doctor ziyara
gobe kamar yadda ya ce mashi matukar ya fahimci wani sauyi daga matakin ciwon nashi
yayi hanzarin zuwa don a san matakin da za'a dauka a kai. Karar shigowar message
wayar shi ya ankarar da shi nisan zangon da yayi cikin tunani, da sauri ya zabura
ya mik'e tare da yiyowa cikin gida.


Hankalin Ummi da Fatima ya ta shi kwarai ganin har goma ta gota Al'ameen bai dawo
ba, abin da bai saba yi ba, sun shiga damuwa sosai da tunanin ko wani Abu ya same
shi ne, ko ya yi hatsari ko makamancin haka, babu irin tunanin da bai zo masu ba a
rai ba. Suna nan zaune jigumΒ² kamar masu zaman makoki, ya yi sallama, da gudu
Fatima ta mike ta fada jikin shi tare da sakin kukan da take ta son yi tun dazu
Ummi na hana ta, Ummi kam wani wawan ajiyar zuciya ta sauke a ranta ta shiga jero
hamdala ga Ubangiji.

A dan rud'e ya ce "Subhanallahi! Yar gidan Yaya Ameen menene haka meya faru?" Cikin
shagwa6a ta ce "Yaya me yasa baka dawo da wuri ba yau ka dade duk hankalin mu ya
tashi.muna ta tunanin ko wani Abu ne ya same ka" Ya ce cikin kulawa "Ya isa haka
kanwata share hawayenki babu abin da ya samu Yayanki wani dan uziri ne ya rike ni."
Ta ce "To dan Allah yayana idan uziri ya sameke ka ringa sanar mana ko ta wayar
yaya Amira ce, zan amso maka lambarta, tunda wayar Ummi ya lalace." Ya ce "To
shikenan zan ringa gaya muku daga yau insha Allah." Ya karashe maganar yana share
mata hawaye.

Basu yi zaman tsakar gida ba ranar saboda yanayin da yake ciki kuma already dare
yayi, abincin shi kawai ya karba ya koma d'aki, suma suka shige nasu dakin suka
kwanta.

Bayan ya ci abinci, ya mike ya canza kayan shi zuwa T-shirt da dogon wandon jeans
ya nufo katifarsa zai haye, ji yayi ya taka abu kamar takarda, da sauri ya kai
duban shi kasa, lettern Joy ne, samun kan shi yayi da faduwar gaba, wanda ya rasa
musabbabinsa, tsurawa takardan ido yayi na sakanni kafin ya tsuguna ya dauka,
hawaa katifarsa yayi ya kwanta, sannan ya sauke duban shi kan rubutun, a hankali ya
fara karanta abinda wasikar ya kunsa.

Kalaman sunyi matukar daukar hankalin shi, bai san sanda murmushi ya subuce mishi
ba, karantawa yake yi yana sake maimaitawa a zuciyar shi, matuka gaya abin ya
kayatar da shi, sai dai bai wani basu mahimmanci ba saboda Sanin daga hannun wanda
suka fito, ajiyewa yayi da nufin ya kwanta, sai dai zuciyar shi taki bashi wannan
damar, ta ci gaba da kwadaita mishi son kallon kayataccen drowning din jiki, da
kyar ya dake yayi fatali da bukatarta ya samu yayi wurgi da pepan ya rintse ido,
take kuma damuwar matsalan ciwon shi ya dawo ma shi, ranar rana dare ya yi bai san
sanda barci yayi a won gaba da shi ba.

Washegari, da wurwuri ya shirya ya fice daga gidan bayan yayi sallama da su Ummi
akan ya tafi school, sai dai yana fita ya dauki hanyar, S Alto special hospital,
duk da sammakon da yayi sai da ya tarar da layi, zama ya yi a waiting area har layi
ya iso kan shi, a hankali ya tura office din doctor ya shiga, kamar kullum
kyakyawan matashin likitan wanda a kalla zai kai shekara talatin da takwas da
haihuwa ya dago ya zubawa Al'ameen idanun shi dake sanye da farin glass kur kamar
zai cinye shi da idanu, hannun da Al'ameen ya mika mishi ya dawo da shi hayyacinsa,
hannun ya mika mishi sukayi musabaha, tare da nuna ma mishi wajen zama, zama
Al'ameen ya yi a kujerar dake facing din *Dr Abdul Hafiz S Alto* Dr da har lokacin
idanun shi na kan Al'ameen ya ce " Muhammadul-Ameen Husain ko?" Al'ameen ya gyada
kai yana murmushi, Dr ya ce "Sai yau ka waiwayeni ko? To ya jikin naka, dama nasan
zaka dawo ai domin wannan matakin daka za6a ba mai bullewa bane." Al'ameen Ya ce "
Kayi hakuri Dr ba laifi na bane na gayaka tun farko a kwai nauyi a kaina bazan Iya
hada taura biyu ba, jiki kuma sai godiyar ubangiji." Gyada Dr ya ce ya ce "well!
yanzu meke tafe da kai?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwashe abin da yaji jiya
game da shakar kamshin turaren Amira da ya yi, ya d'aura da "Na ji tsoro sosai Dr
kar ace matakin ciwon nan ya kara karfi a jikina kamar yadda ka fada zai iya
faruwa, Dr I can't hold my self idan abin ya fi haka, bazan Iya ba I'm so scare."
Dr dake kallon shi tun dazu ya ce "Then ka yi AURE mana Al'ameen shekarun ka sun
kai ai, U ar 25 years by now." Da sauri Al'ameen ya dago ya zuba mishi idanu, Dr
ya daura da "Tun a baya na sha fada ma ka dat is d only solution of ur prlm. Duk
wani tablet ko injection da zan baka,bazai taba zama total solution a gareka ba,
sai ma ya janyo maka wata illar ta dabam, halittanka ne a hakan, wanda ya hade maka
da lalura, a halin yanzu abin ya taka mataki na gaba ajikin ka, wanda idan ka bari
ya kuma karawa gaba daga haka, to tabbas komai zai Iya faruwa ina tabbatar maka da
bazaka iya controlling kanka ba." Kamar zaiyi kuka ya ce "Dr ka taimaka min bazan
Iya rike mace a halin da nake ciki a yanzu ba, bani da wannan karfin a kwai nauyi a
kaina ni maraya ne."kallon shi Dr S Alto yakeyi cike da nazari, "pls Dr dan Allah
ka taimaka min." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce , "Naji zan taimaka maka amma
kafin nan, kamar kullum yauma ina son sanin who ar u Muhammadul-Ameen." Kallon shi
cikin ido Al'ameen yayi ya e "Bazan gaji da gaya maka cewa ni mayara bane. Bayan
hakan bansan komai a kaina ba." Dr ya gyada kai cike da nazari ya ce " For now ka
koma ka ci gaba da amfani da wannan tablet din, idan abin yayi tsamari dole akwai
wani injection da zan maka, wanda kuma yin shi is very risk ga lafiyar mazan takar
ka, idan akayi either a dace kokuma a ta6e." Godiya Al'ameen yayi mishi gwiwa a
sage ya mike ya nufi barin office din, har ya kama handle Dr S Alto ya kira sunan
shi, jiyowa ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, Dr yaci gaba da cewa "Kayi tunani
sosai akan shawarata AURE shine magananin matsalar ka, kaje duk abin da ka yanke ta
waiwayeni." Murmushin yayi ya fice ba tare da ya amsa ba.

Da kallo Dr Abdul Hafiz S Alto ya bi bayan shi har ya kule, ajiyar zuciya ya sauke
zuciyar shi cike da wani irin yanayin mai wuyar fahimta, ganin yana shirin shiga
wani yanayi yasa ya ba next patient damar shigowa don ci gaba da aikin shi.


Cike da wani irin damuwa ya fito daga asibitin, tafe yake akan hanya amma kwata
kwata baya cikin natsuwar sa jefa kafa yake yi kawai duk inda ya samu ba tare da ya
ankare ba, kamar wani karatu haka ya rin ga maimaita Kalmar AURE a zuciyar shi,
gaba daya kalaman Dr sun rikita shi har yana neman rasa nutsuwar sa, shin ta ina
zai fara jajibo aure a halin yanzu? Shin wa ma zai aura, da wani ido zai Iya
fuskantar Ummi ya gaya mata zai yi aure bayan bata da masaniya akan larurar shi,
kai ina impossible, yana bukatar shawarata, lallai yana bukatar shawarata da
gaggawa, wa zai fadawa matsalar shi ya bashi shawara, Aliyu! Aliyu ne ya fado mai
a rai, a fili ya furta "Yesss! Aliyu ne." Daga nan direct gidan su Aliyu ya nufa,
ba tare da sanin yana gidan ko baya nan ba.


********

Joy kwana tayi rungume da takardan da AL'AMEEN ya bayar aka kawo mata a matsayin
Fatima ce ta bayar, wani irin magadisu ne a cikin takardan dake janta kamar magnet,
ta rasa dalili ta rasa dan mafari, sai kawai ta dangata hakan da kasancewar
takardar ya fito daga hannu Fatima ne. Ta ki yarda ta baiwar zuciyar ta damar cewa
rubutun Al'ameen ne bana Fatima ba, hasalima duk sanda tayi wanan hasashen gabanta
faduwa yake yi.........




Wallahi Ku ringa comment ko kuma sai na bari labari ya dakko dadi Ku nemi sama da
kasa Ku rasa, kun san dai halin , hayyaratata in ji me mata tara😬


Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar amma in kinsman idan kin shigo
baza ki ringa comment ba karki fara yi min magana
09116099486
[12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


*PAGE 14*


Ban yi Editing baπŸ™

Daga hospital kai tsaye Al'ameen gidan su Aliyu ya nufa, yaro ya samu ya aika cikin
gidan kiran shi, sannan ya lalubi dakalin kofar gidan ya zauna, babu jimawa yaron
ya dawo ya ce "Wai an ce Aliyu baya nan yayi tafiya." Jim Al'ameen yayi, kafin ya
amsawa yaron da "Ok nagode." Agogon hannun shi ya kalla, sha biyu saura, ya san
kafin ma ya isa school yanzu an gama lecture yau, kuma baya jin zai iya fita aiki a
halin da yake ciki yanzu don haka kawai ya kamo hanyar gida.

Kamar yadda ya zama wa Amira jiki cikin yan kwanankin nan kusan kullum sai ta
shiga gidansu Al'ameen , yau ma cike da zakuwa ta shiga fuskarta dauke da
madaukakin farin ciki. Jiya da dare dakyar barci ya dauke ta saboda farin cikin
Yaya Ameen ya amince zai ringa koya mata karatu, ko babu komai zata samu lokaci ta
ke6e da shi, zata samu wani dama wanda kuma ta daukar wa kanta alkawari iya wuya
zata yi amfani da shi, zata yi kokarin fahimtar da shi halin da zuciyar ta ke ciki
game da shi, ta hanyar kissa irin ta diya mace idan ta kama zata iya kauda zara ta
kauda wata ta bude baki ta furta mashi kalmar so, domin kuwa ita kadai ta san irin
azabtuwar da zuciyar ta ke yi akan shi.

Tana tsaka da jan ruwa a rijiya, ta cire hijabinta ta rataye a igiyar shanya,
kasancewar gidan su biyu ne ita da Fatima Ummi bata nan, ya shigo bakin shi dauke
da siririyar sallama, gabanta ne yayi wani irin faduwa jikinta ta bi da kallo sanye
take da riga da skirt na atamfa dinkin zamani abinka da budurwa ta yi das da ita
kanta babu adiko kananan kitsonta a bayyane, wani irin kunya ne ya lullubeta, ga
shi ta riga ta zura guga a rijiya,ji tayi kamar ta saki gugan sai dai ta daure ta,
dukar da kanta kasa tare da amsa mashi sallamar da yayi cikin dan rawar murya,
kallo daya ya yi mata da dauke kanshi, yana amsa gaisuwar da ta mishi da " Lafiya."
Ya wuce ta zuwa dakin Ummi, Fatima na kwance ta na game da wayar Amira, ta ji
sallama, amsawa tayi da sauri tana mikewa zaune, ya shigo akan wayar hannunta
idanun shi suka sauka, zama yayi akan kujera daya tal dake falon 2 sitter, cike
dan in'ina ta ce "Yaya sannu da dawowa." Bai amsa mata ba sa cewa da yayi "Wayar wa
ye a hannunki." Ta ce "Na Anty Amira ne." Ya ce "Ki kai mata abinta ki ce na ce
ta rufe gashin ta." Da to ta amsa tare da mikewa ta fice, wayam ta Tatar da tsakar
gidan babu Amira babu mai kama da ita, da mamaki ta shiga kiran sunanta amma shiru,
hakan ya tabbatar ma Fatima bata cikin gidan. Dawoqa tayi da wayar a hannu ta ce
"Yaya ban ganta a tsakar gida ba ganin ta wuce." Ba tare da wani damuwa ko daukar
lamarin da muhimmanci na ya ce "Ki kai mata gidansu, kuma kar na kuma ganin ki da
wayar wani, idan lokacin ki rike wata yayi ni dakaina zan siyo miki." Ta amsa da
"To Yaya."
Tana zura hijabinta a jiki, har ta kai bakin kofa ya ce "Ummi fa? Ko ta kwanta ne."
Juyowa tayi a sanyaye ta ce bata nan da mamaki a fuskarsa ya ce "Ba ta nan?." Ta ce
"Eh." "Ina ta je." Ta ce "Bata fada min ba." Ya ce "ya ce ok je ki kai wayar ki
dawo." Ta amsa da to ta fi ce.

Da sallama Fatima ta shiga gidansu Amira, da sauri Amira da ke zaune a tsakar gida
ta rafka tagumi ta mike tsaye, Fatima ta karaso ta ce "Anty Amira sai kika wuce
babu sanarwa, Yaya ya ce na kawo miki wayar ki kuma ya ce na gaya miki ki ringa
daura dankwali." Wani irin zaro ido da tayi sai da abin ya ba Fatima dariya, ta ce
"Da gaske haka ya ce Fatima?" Fatima na mata dariya ta ce "Wallahi haka ya ce."
Amira ta ce "Na shiga uku." Ba tare da tasan ta furta ba duk ta bi ta ruda kanta,
Fatima cikin dariya ta ce "Wallahi ke babbar matsoraciya Anty Amira." Ta ce " Hmmm!
Baza ki gane bane Fatima, wallahi naji kunya sosai yadda Yaya Ameen ya tarar da ni
daga ni sai Riga da skirt babu ko dan kwali wallahi kamar na nutse a kasa saboda
kunya, sai naga ma kamar ya harareni" Sa ke kwashewa da dariya Fatima ta yi ta ce
"Bari na je na gayawa Yayana wagga batu." Da sauri ta juya zata fi ce, Amira tayi
wuf ta rikota, cikin yanayin tsoro ta ce "Dan girman Allah Fatima kar ki gaya
mishi." Fatima ta ce "To sakeni Anty Amira bazan fada ba." Ta ce. "Ki rantse." Sai
da Fatima ta mata rantsuwa sannan ta saketa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta
yi gudu, cike da al'ajabi Fatima ta fito gidan ta shige nasu, koda ta koma Al'ameen
ya fice data dakin su alamar ya tafi nasa ganin haka ta gane baya son hayaniya don
tafi kowa fahimtar shi, bata nemi shi ba ta shiga kitchen ta daura musu sanwar rana
kamar yadda Ummi ta bar mata sallahu.


*********


Karfe biyar dai dai Dr Abdul Hafiz S Alto ya danna hancin motar shi cikin
kyayataccen compound din gidan sa dake unguwar Brighter, bayan parking kai tsaye
ya nufi asalin cikin gidan, da sallama dauke a bakin shi, da sauri yan yaran da ke
zaune a falo suka kwaso da gudu suna ga Daddy ga Daddy, Daddy oyoyoo Daddy oyoyoo,
suka rungume shi, jin hayaniyar su ya fito da matar gidan daga kitchen, matashiya
ce mai kimanin shekaru 28 zuwa 30 fara tass da ita kyakkyawa, da fara'a ta karaso
ta na mishi sannu sa zuwa, tare da dan runguma,yana murmushi, ya amsa mata da
"Uwar gida ran gida, yaya gida ya yara." Ta ce "Gida da yara lafiya kalau sai
hamdala." Zame hannun shi yayi daga cikin na karamin yaron shi ke kimanin shekaru
biyu, ya ce "Aboki bari na watsa ruwa na dawo ko." Yaron ya gyada kai yana
murmushi, daga nan yayi dakin shi, matar shi ta rufa mishi baya, ruwan wanka ta
hada mishi kafin ta dawo ta taya shi rage kaya ya shige toilet don ya watsa ruwa.
Minti goma ya kwashe kafin ya fito sanye da rigar wanka, bata dakin bai damu ba
don yasan kila tana wani uzirin ne, shiryawa ya shiga yi cikin kananan kaya, yana
gama shiryawa ta shigo da sauri ta, tana ganin haka tace "Oh shirt! Kayi hakuri
wallahi Ina kitchen ne ban gama hada dinner ba shi yasa na barka." Murmushi yayi
yace "Babu komai ai na gama." Ta ce "Nasan halinka yanzu zaka baza kaci abinci ba
ka riga kaci abinci a hospital, amma duk da haka bari na kawo naka dan abin
tabawa." Fita ta yi jim kadan ta shigo dauke da tray da jug cake ne da pineapple
juice da ta hada mishi da kanta ta jawo center table ta daura mishi, godiya ya mata
ya zauna ya shiga ci, ita kuma ta bashi hakuri ta sake ficewa kitchen, bayan ya
gama ya dauki tissue ya goge baki, mikewa yayi daga gaban table din, ya koma bakin
bed ya zauna, wayar shi ya dauka, ya lalubo wata international number da yayi
serving da suna Hayatudden Aboki. Sai da ya kalli agogon bangon dakin ganin biyar
da arba'in, ya tabbatar inda zaiyi kiran yanzu dare ne a wajen su amma haka ya
daure ya yi dialling, lambar yayi ringing sosai kamar baza a daga ba can kuma
lucky yaji anyi picking, daga can bangaren aka yi sallama da wata irin
nutsattsatsiyar murya, kafin a daura da "He'll Aboki." Murmushi Dr Abdul yayi
kafin ya amsa sallamar ya daura da cewa "Hi Aboki." Kamar yadda Abokin nashi ya
fada, duk murmushi suka yi, kafin su shiga gaisawa da tambayar lafiyar juna, bayan
sun gama suka dan taba hira irin ta amintattun abokai, daga nan kuma, Barrister
Hayatudden ya ce "How about d boy, ya sake zuwa." Dr Abdul ya ce "Yes ya sake
dazu shi yasa ma na kiraka." Cike da wani irin karsashi Barrister Hayat ya ce "Me
ya kawo shi? Me ya ce maka? Yaya matakin ciwon shi zuwa

Please Login or Register in order to submit comment