Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin damuwa haka a bangaren Amira, zuwa yanzu ta daina
zuwa daukar karatu kasancewar tuni sun fara exam, sai dai kusan kullum tana gidan,
bata da aiki sai ajiye masa wasika, a mabanbantan wurare amma koda wasa, Al'ameen
bai taba daga ido ya kalle ta ba balle ya nuna ya san da zamata, tuni ta fara rama
a tsatsaye kasancewar so ne take masa mai girman gaske, abin na matukar damunta, ya
haifar mata da damuwa da duk wani wanda yake makusancinta zai lura, baga iyayenta
ba hatta da Ummi da Fatima sun fahimci tana cikin damuwa, sai dai banda Allah! da
Zainabu babu wanda ya san halin da take ciki sai ko Al'ameen, wanda shi kuma
damuwar gaban shi ta sha kan shi, kwata kwata bata gaban shi , don tun yana bude
wasikun shirmenta acewarshi yana karantawa har ta kai ga ya dai na budewa idan ya
gani sai da ya dauka ya ajiye ba tare da ya bude ba.


***************

*JOY*

Cikin abin da baifi wata daya ba soyayya ta gama ragargaza jini da bargon jikinta,
i zuwa yanzu bata ji bata ganin komai sai Yayan Fatima, tun tana karyata zuciyar ta
akan lamarin har ta yi surrender.

Sai dai takan shiga matsanancin damuwa, hankalinta kan tashi a duk sanda ta hango
k'urar dake tafe da lamarin, ta ko ina idan ta hanga ta hango babu sauki, baga
Al'ameen ba baga Mom da sauran ahalinta ba, har Papa bata tunanin a wannan karon
zai kalle ta da idon rahama, a duk sanda tayi irin wannan tunanin takanyi kokari ta
yakice shi daga zuciyar ta amma ina! Abin ya ci tura, kullum sai Dada hauhawa ya ke
kamar farashi.

Gaba daya ta koma so silent, bata da aiki sai rubuce rubucen kalaman soyayya, sai
ko kuka da ya zama mata kamar ibada, tuni ta yi rama ta dishe.

kwarafniyar Anty Esther tuni sun daina gigitata, gani take hargagin Mom da anty
Esther ya fiye mata sauki akan tashin hankalin dake tunkarota, zuciyar ta na daf da
yi mata bore, sai dai ta lashi takobin ko zata mutu bazata ta6a bata dama ba, don
tana ganin yin hakan tamkar tarwatsa rayuka ne, gara ita nata rauyuwar ya tarwatse.

Tuni anty Esther ta bata wayarta, sai dai abin mamaki tunda ta karbu wayar Papa bai
taba kiranta ba itama idan ta kira shi baya dagawa, idan ya daga ma da sun gaisa
sama sama zai kashe gaba daya ya dena nuna mata kulawa kamar da. Bata wani dauki
abin serious ba ta mishi uzuri don a ganinta aiyuka ne suke sha kan shi.

A cikin wannan dan tsukin girgin su Mom ya yi dirar mikiya a 9ja, ko gezau bata
yi, babu yabo babu fallasa a tare da ita, suka dunguma ita Anty Esther, David,
zuwa airport don tarbota, babu wani karsashi ko kewa a ranta su ka iso, lokacin
tuni jirgin ya sauka, da sauri Mom ta iso gareta tare da rungumeta, lamarin ya dan
so ya daure mata kai, amma tuna yadda Mom dinta ke matukar kaunarta, ada kafin ta
soma canzawa yasa ta saki jiki itama ta rungumeta, cikin kunnenta Mom ta rada mata
"I missed u a lot daughter." "I missed u 2 my Mom." Ta amsa mata.

"Ki yafe min abubuwan da suka yi ta faruwa a dan kwanakin nan, kuskurene." Hawaye
ta ci ya ciki mata idananu, "take daskararriyar soyayya ta fara narkewa." Tsaki
Anty Eshart ta za a bayyane, tare da kauda kai zuciyar ta na tafasa, murmushi Mom
ta yi, ta saki joy ta rungume Eshart tana cewa "Oh! I'm Sorry my dear sister. Na yi
kewarta sosai ne shiyasa." Daga haka ta rungume David da shima yake mata sannu da
zuwa, hannunta sarke da na Joy suka shiga mota, Joy na kwance a jikinta har su ka
iso gida.

Duk da izza da dagawa irin na Mom, ma'ikatan gidan sunyi murna da dawowarta, daga
yadda suka dinga zuwa kwasar gaisuwa kowanne baki har kunne zaka tabbatar da
hakan, ko ba komai zasu rabu da masifar Esther.

Ranar Joy na makale jikin Mom din ta, tana lelenta kamar yar five years abinda ta
dade rabonta da gani daga Mom din hakan yasa ta saki jikinta sosai ta wuni da farin
ciki, koda lokacin barci yayi har daki Mom ta rakata ta tayata shirin barci ta
kwantar da ita ta kashe mata wuta sannan ta barta ba yan ta yi kissing forehead din
ta tare da shafa kanta.

Mom na fitowa daga d'akin Joy ta tarad da Esther tsaye tana Binta da wani irin
kallo, hannunta Mom ta kama ta jata su ka bar wajen, d'akinta ta nufa da ita
sunan shiga Esther ta fisge hannunta daga na Mom, tare da watsa mata wani
lalatatcen kallo, ajiyar zuciya Mom ta sauke a tausashe ta ce "I'm sorry Esther. Ba
abinda kike tunani ba ne." Cikin daga murya ta ce "Ta Yaya zan tabbatar da haka ba
yan kina aikata sabanin abin da kika sanar min, na gani lokaci yayi da ya kamata ki
cika alkawari." "Calm down Esther ki saurare ni." Daga mata hannu ta yi a zafafe ta
ce "Bazan saurare ki ba, zan bar gidan nan don bazan zauna bakin ciki ya kashe
niba." Daga haka ta tuya ta fice daga dakin fuuu! A fusace.

Dabass Mom ta zauna tare da rafka tagumi.

Washegari da duku duku safiya Anty Esther ta fito da jakar kayanta ta bar gidan.


**********

*Al'ameen*

Kwata kwata babu sauki a cikin lamuran sai ma kara tabarbarewa da abubuwa ke yi I
zuwa yanzu tab! biyar yake sha kafin ya samu relief........




Ga mai bukatar shiga group.

09116099486.
[12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


~FARHAT~


DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*


ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*


*PAGE 23*
*AL'AMEEN*

Kwata-kwata babu sauk'i a cikin lamuransa, sai ma kara ta6ar6arewa da abubuwa ke yi
i zuwa yanzu tables biyar yake sha kafin ya samu relief, yana cikin matsanancin
damuwa, tuni ya fara rama a tsaye.

Ba Ummi ba hatta fatima sai da ta fahimci Yayanta na cikin damuwa, don gaba d'aya
ya sauya mata, ko magana yanzu bai cika yi ba, haka firan dare, da ya dawo zai
shiga d'aki ya kulle ya kwanta da safe ya fito da idanu jajur kamar gauta a kumbure
idan ta tambaye shi ya ce babu komai, tuni duniyar ya fara mata zafi, take kewar
aminiyarta ya dawo mata sabo fil dama shi ke dauke mata hankali akanta ba wai don
ta manta da ita ba.

Ummi kam damuwar da ta shiga ba'a magana, matsayinta na uwa lamarin ya shigeta
matuk'a gaya, tsoranta Allah kar ace shaye shayen nan na zamani Al'ameen d'in ta ya
fara, a duk sanda ta yi wannan tunanin, takan shiga kololuwar ta shin hankali, har
ta zubar da hawaye, ta zauna da shi ba sau daya ba ba sau biyu ba cikin lalama da
dabara ta naimi jin damuwarsa, amma ya ki fad'a mata, sai dai ya girgiza kai ya ce
mata "Babu komai Ummi, kawai gajiyan aiki da karatu ne, sai mura da ta saka ni gaba
a yan kwanakin nan ki taya ni da addu'a." Ba dan ta yarda ba, dole take hakura, ta
san tunda ya nace a haka bazai fada mata ba ne, ta fi kowa sanin halin zurfin cikin
shi tun yana dan kankanin yaro.

Da misalin karfe takwas na dare ya shigo gida kamar yadda ya saba, sunan zaune
jigum jigum a tsakar gida, duk yadda Ummi take da son sauraren redi'o yau rediyon
nata a kashe yake carbi ne rike a hannunta tana ja, Fatima kam notebook din ta ne
a gabanta data dauko zata yi karatu amma ta kasa, ta ajiye ta rafka tagumi.

Kallo daya Ummi ta mishi ta kauda kai gefe, sai ga hawaye shaaa! Duk yadda taso ta
kauce kar ya gani abin ya ci turo.

Da sauri ya kara sa shigowa, zubewa yayi a gabanta hankali tashe, ya ce
"Subhanallah! Ummi." Daga mai hannu ta yi ta ce "Karka kira sunana Al'ameen ni ba
Umminka ba ce, ka tashi a gabana." Ta karashe maganar tare da fashewa da kuka mai
karfi, Fatima da maganar Ummi ya dawo da ita hayyacinta, rarrafowa tayi ta fada
jikin Ummi ta fashe da kuka itama, cikin kuka ta ke cewa "ki yi hakuri Ummi, ki yi
hakuri ki yi shiru." Rungumeta Ummi ta yi su ka ci gaba da rera kukan a tare.

Kololuwar tashin hankali Al'ameen ya shige shi, zuciyar sa tuni ta shiga wani
irin tsalle kamar zata faso kirgi ta fito, rasa abin yi yasa shi fara zubar da
zazzafar hawaye da , sai kawai ya rungume su gaba daya, cikin zubar hawaye da kunar
rai ya ce "Ki yi hakuri mahaifiyata ki dena zubar da hawayenki a kaina, na tuba
nabi Allah na bi ki." Kalmomin da ya dinga maimaitawa ke nan kamar karatu.

Sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin Ummi ta tattare d'an jarumtarta ta danne
zuciyarta, ta zame su daga jikinta ta dago ta kalle shi cikin ido ta ce "Al'ameen
shaye shaye ka fara?"da wani irin sauri ya kalle ta yana girgiza kai, ta ce "Karya
ka ke yi, idan ba haka ba kuma ka sanar dani damuwar ka, don na tabbata a kwai abin
da ke damunki ji yadda ka koma gaba daya ka lalace cikin yan watanni, bazan jura
ganin ka haka ba Aminullah."

Shiru ya yi yana kallonta bazai iya yi mata karya ba, kuma bazai iya fitowa kai
tsaye ya sanar da ita damuwar shi ba, duk da yasan bashi da kamar ta duk duniya,
yana matukar jin nauyinta, kasa ya yi da kai ya ce "Ki yi hakuri Ummi, bazan iya
yi miki karya ba, kuma bazan iya sanar miki damuwata ba, amma wallahi tallahi bana
shaye shaye, ki taya ni da uddu'a Ummina."
Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ko babu komai ta samu saukin kaso ashirin cikin
damuwarta kashi dari.

Sai dai ko da wasa bata nuna a fuska ba, mikewa ta yi ba tare da ta kalli gefen da
yake ba ta shige daki.

Fatima ma mikewa ta yi zata bi bayanta, har lokacin kuka take yi, da wani irin
raunatacciyar murya wanda basu san shi da shi ba ya kira sunan ta "Fatima."
Dakatawa ta yi da tafiyar ta juyo tana kallon shi tana shesheka, girgiza mata kai
ya yi tare da cewa "Shiiiiii!" Alamar ta yi shiru, sai kuma ya yi mata alamar ta
zo da hannu, da sauri ta karasa gareshi ta fada jikin shi, ta sake fashewa da kukan
da dama ba wai ta dai na ba ne. Rumgumeta ya yi, wani irin rauni na kara kaiwa
zuciyarsa farmaki.

A yau ya kara tabbatarwa, shine cikin farin cikin yar uwarsa tilo, da kuma
mahaifiyarsa wacce itace komai na shi a rayuwa.

Muryarta ne ya katse masa tunani, cikin shesheka take cewa "Yayana ka canza,
yayana ka dawo kamar yadda ka ke da don Allah, da ni da Ummi muna cikin damuwa kai
ne haske ka jagoran rayuwar mu." Bubbuga bayanta ya shiga yi, ba tare da ya iya
bude baki ya amsa mata ba, sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin ya samu ta yi
shiru, sai ajiyar zuciya da take saukewa jefi jefi.

Dagota ya yi daga jikinsa ya shiga share mata hawaye, yana yi yana cewa "Kar ki
sake yin kuka My luv na miki alkawarin zan dawo muku da farin cikin ku ke da Ummi.
Al'ameen din Ku zai dawo Yaya Ameen din ki zai dawo kin ji ko." Ta gyada kai ya ce
oya wuce kije ki kwanta,

Babu musu ta wuce shi jiki a sanyaye, sai da yaga shigewarta daki sannan ya kwashe
tabarman ya jingine, kamar mara laka haka ya nufi dakinsa.

Ranar damuwa biyu ne ya hade masa, ga na azababbiyar ciwonsa gana tunanin halin da
ahlinsa suka shiga a dalilin sa, bazai iya jurar ganin su cikin wannan yanayin ba,
bazai iya jurar zafin zubar hawayen uwa ba, ya san wata kila Ummi ta na fushi da
shi, dole ya tsayar da mafitar da yake ganin ita ce dai-dai.

Ranar yadda yaga rana haka yaga dare.

Da safe kamar yadda ya saba gudanar da komai haka ya gudanar, hankalinsa ya kara
tashi lokacin da ya hada idanu da Ummi, bai taba ganinta cikin irin wannan kamar
ba, gaba daya idanunta sun kumbura sun yi jajur, sai dai bata nuna masa wani sauyi
a fuska ba, ya san ta kwana cikin damuwa, abin da ya fi daga mai hankali ganinta da
ya yi kwance a dai-dai lokacin da kullum yake samunta zaune ta na lazumi tabbas!
Bata da lafiya, kuma yasan shine sila, shikam ina zai kai girman sannan zunubin uwa
tafi gaban wasa,zai iya sadaukar da komai domin ganin farin ciki ta, a koda ya
tambayeta ko bata da lafiya ne, cewa ta yi kalau ta ke.

Ko breakfast bai iya tsayawa yi ba, ya shirya afujajan ya nufi asibitin Dr Abdul
Hafiz S Alto don a nan ne kadai yake ganin zai samu total solution.

Lokacin da ya isa Dr bai iso ba, zama yayi a waiting area shi da sauran patient din
da ke nan.

Sun dauki almost gud 2 hours kafin Dr Abdul ya iso, tun daga nesa ya hango
Al'ameen, boyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tuna wayar da su ka yi da Aboki,
shekaran jiya.

Sama sama ya amsa gaisuwar ma'aikata ya shiga office ya fara duba patient dinsa,
gefe guda kuma zuciyarsa cike da fargabar da me yaron ke tafe fatansa Allah yasa
ya zabi cancanta kar ya zabi son zuciya.


Mutum bakwai ya gani kafin layi ya iso kan Al'ameen, tun da ya turo kofar office
din Dr Abdul ya dago yana kallon shi, shima jemammun idanu shi na kan Dr din.

Guri ya samu ya zauna a inda aka tanada don zama, da wani iron cool voice ya ce
"Dr na dawo gareka ka taimaka ka yi mini wannan alluran da ka ce shine zabina."
Rasss! Rasss! Haka gaban Dr Abdul ya yanke ya fadi, ya san za'a rina dama.

Shiru ya yi yana kallon Al'ameen din ba tare da ya amsa shi ba, gajiya da zaman
shirun ya saka Al'ameen sake cewa "Don Allah Dr ka taimakeni ina cikin matsanancin
damuwa." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Wacce irin damuwa ce sannan data saka
ka kake shirin kashe rayukar a tsaye." Ya ce "Duk abinda kaga ya koro bera daga
rami har ya fada wuta to hakika yafi wutar zafi, ni dai don Allah ka taimake ni."

"Ta yaya zan maka injection irin wannan mai hatsari alhalin ban san matakin
ciwonka ba, kar ka boye min komai ka gaya min gaskiya mekefaruwa?"


Tuni idanun Al'ameen suka kara kadawa, a raunace ya shiga labartawa Dr halin da
yake ciki, ba tare da rage komai ba kamar yadda Dr ya roka.

Tun kan ya kai kar she tuni Hankalin Dr ya ta shi, ranshi yayi mugun baci, bai
taba sanin akwai mutane kidahumai ba a duniya sai yau.

Cike da wani irin bacin rai ya katse shi ta hanyar jiran sunan shi a tsawace
"Muhammad!!!! "........




09116099486.
[12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


~FARHAT~


DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*


ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*


*PAGE 24*


Cike da wani irin bacin rai Dr ya katse shi ta hanyar kiran sunan shi a tsawace
"Muhammad!!! Baka da hankali ashe, five tablets fa ka ce." Komawa ya yi zauna
da6ass "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Ya furta tare da dafe forehead.

Ganin yadda hankalin Dr Abdul ya ta shi yasa Al'ameen yin k'asa da kai, cikin
sanyin murya ya ce "I ha6 no choice, dat is y" Dagowa Dr ya yi idanun shi har sun
kad'a ya ce "Ni ka ke gayawa baka da za6i, shin! haka mu ka yi da kai?" Ya girgiza
kai. "Then y ka yi hakan, kasan me ka aikata kuwa, hakan fa dai-dai yake da kashe
kai." "I'm sorry Dr." D'aga ma shi hannu Dr ya yi , ya ce "Ka rike hakurin ka, ka
tashi ka fice min daga office bana bukatar ganin ka, don babu abin da zan iya yi
maka a halin yanzu." Jin haka yasa hankalinsa kara ta shi tuno yadda ya baro Ummi a
kwance cikin ciwo ya yi, ya sake tuna irin damuwar da tilon kanwarsa ke ciki duk
akan wannan matsalar, sannan ya zo in da yake ganin zai samu maslaha amma yana ji
yana gani ana neman yi masa sakiyar da babu ruwa.

A raunace ya ce "Dan girman Allah Dr ka tausayin min ka dubi maraicina, ka yi mini
wannan alluran, na amince da duk abin da zai biyo baya." Kallon zautacce wanda bai
san ciwon kan shi ba Dr ke mishi i zuwa yanzu, hakan yasa ya baiwar iska ajiyar shi
ya ci gaba da duba tarin files din dake gabansa.

Magiya da ro'ko Al'ameen ya shiga yiwa Dr amma yayi kamar bai san da zaman mutum a
wajen ba, don ran shi a matukar 6ace yake danne zuciyarsa kawai ya yi don tunzira
shi ta ce akan ya ta shi ya dinga sharara ma shi mari, amma yaga alamar yaron na
neman kai shi bango.

Magiyar duniya Al'ameen yayi wa Dr amma bai kalle shi ba, har k'asa ya duka ya riko
kafafusa yana rokonsa, amma kamar da dutse yake, tuni zuciyarsa ta fara tunzira.

Mik'ewa ya yi a fusace cikin tafasar zuciya da matsanancin bacin rai ya ce "Kar ka
yi min mana so what!" Kalmar da ta doke kunnen Dr da ya sa ka shi dagowa da sauri
a kalle shi.


Cikin tsawa da rufewar idanu ya ci gaba da cewa "Wacce irin zuciya ce a kirjinka
Dr? Shin baka da imani da tausayi ne baka san Allah da ma'aiki ba? To shike nan ka
je ka rike taimakon na ka, gari da yawa maye baya ta6a cin kansa! Idan baka taimaka
mini ba akwai dubban irin ka da zasu iya taimaka mini, duk duniya babu wanda na
yarda ya san sirrina ciki da waje sai kai, na gaya maka abin da ke faruwa ban 6oye
maka komai ba, na ce maka na amince da duk abin da zai biyo baya ba shike nan ba,
ina ruwanka jikin ka ko jikina rayuwar ka ko nawa? So kake na fifita wani jin dad'i
na rayuwana akan farin cikin mahaifiyata, to ka sani UK duniya babu wanda ya isa,
bani da kamar ta itace komai nawa, kuma zan iya yin komai dan ganin farin cikin ta,
dukan table ya yi da karfi har sai da wasu takardun dake kai su ka watse ya ce "
Ni muhammadul-Ameen Idan na haifu dan halak na maka alkawarin baza ka sake ganin
kafata a cikin asibitinkada zumar naiman taikamo a wajen ka ba."

Daga haka ya juya a fice daga office din tare da buga koda da mugun karfi.

Tun da Dr ya kafe shi da ido bai sauke ba har ya fice daga office din. Ya fi minti
goma a haka, kafin ya sauke zazzafar huci, fuskar yaron yake sake kallo a idanunsa
maganganun yaron ne ke sake repeating kan su a cikin kunnuwansa, "Ya Rabbi! Kaga
niyyata ka dafa mini." Ya furta a bayyane wayar shi ya dauka ya yi dialing lambar
Hayatuttdeen, kamar yadda ya tsammata kiran bai tafi ba, kife wayar ya yi akan
table, shima ya kife kanshi tare da lumshe idanu.....


***********


Da wani irin fushi hadi da bacin rai ya fito daga asibitin, jefa kafa yake yi duk
in da ya samu, idanun shi a rufe, ikon Allah ne kawai ke rike da shi, bai san ina
yake nufa ba, don zuciyarsa ce kawai ke jagorantarsa kwkwalwarsa kam ta dau zafi a
lokacin da bazata iya tantance komai ba.

Wani irin mugun horn ne hadi da taka burki suka ziyarceshi lokace daya, sai dai
kafin ya yi aune tuni motar ta ture shi, duk da ba wani mugun turi bane don direban
yayi iya kokarinsa wajen kaucewa hatsarin, sai da ya fadi kasa.
Gigitacciyar kara ta saki a matukar razane. ba ta san yadda a ka yi ba, ta shiga
komar tunanin shi kamar yadda ya zame mata ibada, kawai ta ji direbanta ya taka
birki, a firgice ta dogo kafin tayi aune kamar kiftwar idanu taga motarta ya ture
shi.

Ita da direbanta rige rigen fita a mota suka shiga yi, kusan a tare suka isa inda
yake, bata tabbatar shi din ba ne, don duk a tuninta gizon da ya saba mata ne, sai
da ta fito daga mortar ta ganshi ra'ayil aini.

Cikin rawar jiki Peter ya isa gare shi don ya taimaka mi shi ya mike, abin mamaki
da daure kai dakatar sa shi yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin karfin hali da
jarumta ya dafa kasan titi ya mike tsaye, bai ji mugun rauni ba sai dan kujewa,
sai dai ga dukkan alama ya bugu a kafafun shi ganin yadda tsayuwa ta so gagararsa
da fari, amma yayi ta maza ya cije lips ya tsaya cak.

Tuni ta fashe da wani irin kuka tare da karasawa garesa, a gabansa ta tsaya cikin
kuka take cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi
asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun
shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba daya ta rude bata cikin hayyacinta......



Ku yi manage pls.

Masu comment nagode kwarai ina alfahari daku, jiya kun faranta min sosai dana bude
data naga ruwan comment na shigowa group di na pls Ku ci gaba hakan shine karfin
gwiwata ina sonku sosai masoya mabiya.
[12/29, 2:41 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


~FARHAT~


DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*


ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*



*PAGE 25*



Fashewa ta yi da wani irin kuka, da gudu ta k'arasa gare shi, a gaban shi ta tsaya
cikin kuka da kid'ima ta ke cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri,
Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a
jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba d'aya ta rud'e bata
cikin hayyacinta.

Duk da yana cikin halin ciwo, sai da ya ji Yarrrr!!! A jikinsa lokacin da
hannunta ya sauka a kan nasa, da sauri ya saka hannusa d'ayan ya 6an6are hannunta
daga nasa.


Jin haka yasa ta dago da jikakkun idanuta ta sauke a fuskar shi, karaf! Suka su ka
sauka cikin na shi kaifaffun idanun da suke rine, tuni zuciyarta ta shiga wani
irin dokawa da wani irin speed,wasu irin sinadarai masu kama da surkulle ke fitowa
daga idanun shi suna shiga na ta direct ba tare da wani shamaki ba, kasa janye
idanu ta yi daga cikin na shi, duk da irin kaifin da suka mata.

Kayataccen murmushinsa ya sakar mata, ya girgiza mata kai, murya kasa-kasa ya ce
"I'm ok' ba sai kin kai ni hospital ba thank yhu for Ur care." Daga haka ya juya ya
ci gaba tafiya yana d'ingisa kafarsa ta hagu.

Kamar a sume kuma ba a sume ba, haka ta dinga jin kanta, bata farga da ya bar wajen
ba sai da ta tsinkayi muryar Peter yana cewa "Miss ar u ok." Firgigit ta yi ta
kalle shi, ta sake kallon hanyar da al'ameen ya bi, ji ta yi wani kuka mai karfi
ya taho mata from no where, da gudu ta wuce shi ta bude motarta ta fada tare sa
fashewa da kuka.

Jiki a matukar sanyaye Peter ya bude motar ya shiga mazauninsa, ya tada motar suka
bar wajen, zuciyarsa cike da tausayin uwar dakinsa.



*************


Karfin hali da jarumta ce kawai da kuma taimakon Allah suka karasa da shi gida,
zuwa lokacin tuni kafar ta kumbura, baya son ya tadawa su Ummi hankali hakan yasa
bai nufi cikin gida ba ya tsaya dakin shi.

Karar taba kofar dakin ne ya jawo hankalin Fatima dake tsakar gida, da sauri ta
leko don ganin ko waye tunda dai ta riga ta san yayanta ya fita, kuma muddin ya
dawo sai ya shigo cikin gida kafin ya nufi dakinshi, sai dai ga mamakinta shi din
ta gani tsaye idanun shi a rintse ya cike lips yana kici kicin soka key a jikin
padlock.

"Yayana." Ta furta tana karasawa gaban shi, sai lokacin idanunta suka kai ga
kujewar dake gefen fuskar shi da gwiwar hannun shi da ke zubar jini, zaro idanu ta
yi a rude ta ce "Subhanallahi! Yaya me ya sameka?" Kafin ya bata amsa ta hango
kumburan da kafar shi ta hagu ta yi, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na shiga
uku!" Da sauri ya bude rinannun idanunsa jin zata yi masa kwarmato, cikin karfin
hali ya yi mata alamar shiii! Da hannu, girgiza mishi kai ta yi tana hawaye sai
kuma ta juya ta runtuma da gudu, "Ya Salam!" Ya furta akan labbanasa, ya fahimci
gaba daya ta rude ne kuma yasan Ummi zata je ta gayawa, sam baiso ba sanin da ya yi
Ummi bata jin dadi yau.

Allah sarki uwa! A kwance take amma jin abin da Fatima ke fada tuni ta mike zaune,
kafin Fatima ta kai aya, ta mike kan kafafunta, ta yo gaba, Fatima ta rufo mata
baya.

"Subhanallahi! Yayan Fatima me ya faru haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!"
Ta fada cikin tashin hankali ganin yadda kafar shi ta kumbura, "Fatima amshi
makullin ki bude kofar." Fatima dake sharar kwalla ta amsa key a

Please Login or Register in order to submit comment