Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 16 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun jiya." Daga haka bata sake bata
dama sun yi magana akan abinda ya faru jiya ba sai ta canza akalar hirar da gaya
mata cewa cikin Wannan month d'in Papanta zai dawo kuma sun dai-daita yanzu ya kula
da ita kamar yadda yake yi da, da yake Fatima ta san komai game da tsakaninta da
Papanta.


************

Da misalin karfe goma sha daya Maman Amira ta shirya ta shiga wajen Ummi, tun jiya
a d'okance take da tazo ta labarta mata abin farincikin dake shirin wanzuwa a
tsakanin su.

Gyara zama Maman Amira ta yi bayan sun gama gaisawa da Ummi tare da tambayar
lafiyar iyalai harma da d'an ta6a hira, tace "Wai nikam Ummin Fatima ko kin hangi
abin da na hango?" Cike da rashin fahimta Ummi tace "Name kenan Maman Amira?" "A
game da yaran nan Al'ameen da Amira, sai nake ganin kamar a kwai wata alak'a a
tsakanin su." Dariya Ummi ta yi , tace "Maman Amira na dad'e da fahimtar hakan, sai
dai rashin tabbaci yasa na bar maganar a zuciyata, don su y'ay'an yau ba'ayi musu
katsalandan a irin wannan lamarin, nasan dai komai dad'ewa idan zargina gaskiya ne
zasu bayyana kansu, to ashe kema kin kula." Mama da fara'ar fuskarta ta kara
fad'ad'a tace "Hmmm na kula Ummi lamarin yaran zamani sai a barsu." Ummi tace "In
dai haka be sai muce Alhmdllh! Don wannan abin farin ciki ne." "Kwarai Ummi Fatima
zan iya cewa nafi kowa farin ciki da hakan." "A'a fa Maman Aysha, na fiki farin
ciki domin kuwa amira diya ce yar albarka duk wacce ta sameta matsayin rusuka ta yi
dace." Mama ta amsata da shima "Aminullahi haka." Sun dad'e suna raha kamar na
masu shirin zama surukai ba kafin Maman Amira ta yi sallama da Ummi ta
tafi............



Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 38*


Mikiya Writer's Association.


*NOTE*
Jiya na yi mistake wajen saka number, instead of 37 na sake maimaita 36, so yanzu
zamu je 38 da fatan kun fahimtaπŸ‘Œ



A kwana a tashi ba wuya, musamman a wannan zamanin da muke ciki ta karshen duniya
yadda lokaci ke gudu kawai ya ishi bawa tsoron Allah. Tsakanin Al'ameen da Amira
komai ya k'ara daidaita soyayya suke gudanarwa mai tsabta, kyautatawa tare da
kulawa had'i da girmamawa sune manyan makaman da Amira ta yi amfani da shi wajen
kafa kanta a zuciyar Al'ameen, bugu da k'ari yadda take nunawa Ummi da Fatima
tsantsar soyayya da kulawa ya k'ara mata kima a idanunsa, wani babban matsayi na
musamman ya ware mata a zuciyarsa, da fari ya k'arbi, soyayyar ta ne saboda Fatima
sai kuma tausayinta da yake ji, sai dai da tafiya tayi fatiya rashe ya juye da
mujiya, don a halin yanzu idan ya ce baya sonta to tabbas ya yi babban karya.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya kamata yasan da maganar soyayyar su da ya rage bai
sani ba, kama daga dangi, makota, yβ€˜an uwa, da abokan arziki, tuni kawunan Amira
suka fara maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa idan da gaske yake, lamarin da
ya yi masifar d'aga masa hankali, bashi da kud'in aure yanzu bai ajiye ba bai baiwa
wani ajiya ba, hasalima d'akin da zai sakata kango ne bai kai ga k'ark'are ginawa
ba.

Cikin kwana biyu kacal da samun wannan sak'on duk ya gigice ya shiga damuwa, tabbas
yana buk'atar mace a rayuwarsa, musamman a halin yanzu da ya kai gargarar da tablet
d'in da yake sha sam! ya daina yi masa aiki, ko da kuwa zai shanye sachet biyu ne a
take, k'arfi da ya ji ya koyi, istimna'i, (Biyawa kai bukata) wanda a duk lokacin
da hakan ya kasance yakan kwana ne yana kuka tare da neman gafarar Ubangijinsa,
sarai ya san abinda yake aikatawa sa6o ne babba haramun ne , kuma cuta ne ga
lafiyarsa, sai dai shi hakan ya fiye masa a kan ya aikata zina, yana kyamar zina,
haka yana tsananin tsoron aikatawa domin ya dad'e da sanin bashi ne, idan kaci sai
ka biya, shiyasa yakan yi taka tsantsan wajen ke6ewarsa da Amira, saboda
kasancewar ta ma'abociya son gayu da kamshi, a cikin yan kwanakin nan, hirasu ta
waya ya fiye masa alkahiri bisa ga ace sun ke6e, domin a duk sanda hakan ta
kansance ya kan shiga wahala da garari.

Misalin karfe biyu na sulisin dare, zaune yake a bakin kafifarsa, ya rafka taguma
da duka hannayensa biyu, idanunsa ya yi jajur, hankalinsa a tashe nadama da kaico
kwance k'arara akan fuskarsa,ya tabbata idan mutuwa ta riskesa a wannan halin la
shakka zai gamu da fishi da azabar Allah, take wani irin tsoron Allah ya dirar
masa, zuciyarsa ce ta karye, take hawaye ya shiga kwaranya daga idanunsa, ya dad'e
yana kuka, banda "Astagfirullah Allah na tuba Allah ka yafe mini." Babu abinda
yake maimatawa a zuciyarsa, ganin zaman da yake yi da najasa a jikinsa bashi da
amfani yasa ya tsagaita da kyar, ya mik'e yana layi tamkar wanda ya yi tatul, daga
shi sai gajeran wando a jikinsa, sif ya bude ya dauki, wani wandon wankakke, ya
kuma dauki babbar butarsa dake ajiye a gefe cike da ruwa ya fito, kamar yadda ya
saba kullum cikin sand'a da taka tsantsan ya nufi toilet.

Cikin takaitaccen lokaci ya tsarkake jikinsa ya fito sanye da wankakken wandonsa
yayinda ya riko daya wandon da hannu hagu cike da kyamkyami, gabansa ne ya yi wani
irin yankewa ya fad'i lokacin da idanunsa ya hadu dana Ummi da ke rike da buta
wanda ta gama zuba ma ruwa a ciki yanzu yanzu, da sauri ya yi kasa da kansa gabansa
na ci gaba da wani irin dokawa, take ya ji wani irin sanyi na kada shi, da yana da
hali a lokacin da babu abin da zai hana yace kasa ta bud'e ya shige tsabar
kunya.

Kur! Ta kure shi da kallo zuciyar ta na tsinkewa, ba yaune karo na farko da ta ta6a
kamashi yana wanka ba musamman ma a cikin yan kwanakin nan da abin a shi ke neman
shallake tunaninta, sai dai basu ta6a yin gaba da gaba ba sai yau, ita kanta bata
san yana tailet d'in ba da batta yarda ta fito alwalan ba, ta bari har sai ya gama
ya shige d'aki.

Yi tayi kamar bata gane komai ba, ta ce "A' a Amintacce hala kaima zafin nan ya
dame ka, da sauri ya ce "E wallahi Ummi, na kasa barci sai da na fito na watsa
ruwan sanyi." Tana nufar toilet d'in tace "Hmmm! Allah dai ya saukaka mana." Daga
haka ta shige toilet, da sauri ya bar tsakar gidan.


Ta dad'e a kan darduma tana kai kukanta gurin Allah tana hawaye, tun jiya da
maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa ya risketa take cikin matsanancin tashin
hankali, shin wa zai wakilci lamarin auren nan, shin wa zata nuna musu a matsayin
dangin mahaifinsu, tabbas lokaci yayi da zata waiwayi wadancen azzaluman Ahlin,
lamarin Al'ameen ya fara bata tsoro ita kanta zata so ya kasance da mace a kusa,
domin dai ta riga ta gama fahimtar shi din mai tsananin bukata ne.
Da safiya kasa hada ido ya yi da ita, duk da yadda ta yi iya kokarinta wajen ganin
ta nuna mishi bata fahimci komai, shi yasan ta fahimta d'in domin dai ita ba
yarinya bace duk da babu wanda zai ganta ya ce ita ta haife shi Indai ba wanda ya
sani ba, haka jiki a sanyaye ya shirya ya fice daga gidan.


School ya nufa don yana da lecture, karfe goma ya fito daga school, jikinsa duk a
mace kansa ne ke masa matsanin ciwo kamar zai rabe biyu baya jin yana da kuzarin
iya fita aiki yau, hakan yasa ya kira Aliyu ya ya ji ko yana gida, samun tabbacin
yana gida yasa kai tsaye ya tari dan acaba ya nufi gidan su Aliyu.

Ganin shi a sanyaye yasa Aliyu tarar shi da cewa; Lafiya Ameen mekefaruwa." Zama ya
yi a kan kujera 2 sita dake d'akin Aliyu ya dafe kai, yana sauke numfashi.

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, ya zauna kusa da shi, sun fi minti biyar a haka,
Al'ameen bai ce komai ba shima Aliyu bai matsanta mashi ba, sai da ya gaji don kan
shi ya dago idanun da suka kara rinewa ya kalli Aliyu. Ya ce "Aliyu ya zan yi?
Nutsuwa Ali ya kara yi ya maida dukkan hankalinsa garesa, ya ci gaba da cewa;
"Iyayen Amira sunce na turo, Aliyu bani da halin aure ban ajiye ba ban ba wani
ajiya, kuma ina bukatar aure Aliyu ya zan yi? Murmushi mai sauti Aliyu ya yi a
zuciyarsa ya ce anzo wajen.

Wani irin kallo Al'ameen ya shiga bin Aliyu da shi ganin yana murmushin, ganin
irin kallon da yake masa yasa ya dafa kafadar shi, ya ce " Abokina a kwai mafita."
Tamkar wani soko ya ke bin Aliyu da kallo kafin ya ce "Akwai mafita kace Aboki?"
Gyada kai Aliyu ya yi ya ce "kwarai kuwa a kwai mafita."..............




Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 39*


Mikiya Writer's Association.


"Menene mafitar?" Al'ameen ya tambaya idanunsa cikin na Aliyu. Nannauyar ajiyar
zuciya Aliyu ya sauke, cike da kwarin gwiwa ya ce "Dr Abdul Hafiz ." Wani irin
k'ank'ance ido Al'ameen ya yi, a hankali ya maimaita sunan da sigar tambaya "Dr
Abdul Hafiz S Alto?" "Kwarai shi nake nufi." Aliyu ya fad'a shima yana kafe
Al'ameen da ido.


Bacin rai ne ya bayyana k'arara a fuskarsa take, a kausashe ya ce "Menene had'in
ka da shi?" Dakewa Aliyu ya yi daman yasan hakan zai iya kasancewa, ba tare da
shayin komai ba ya ce "Zumunci." Gyada kai Al'ameen ya yi, ya ce "Zumunci ko? Very
gud." Daga haka ya mik'e bai kalli side d'in da Aliyu yake ba ya fice daga d'akin
jiri na kwasarsa.

Murmushi Aliyu ya saki a yayin da ya raka bayan shi, da kallo, taurin kan Al'ameen
ya wuce tunanin mai tunani, idan ya riga ya kau da kai a kan mutum da wuya ya k'ara
waiwayarsa ko shi waye, sai dai ya lashi takobi zai yi iya 'kokarinsa wajen ganin
komai ya daidaita.


*********


*JOY*

Tun daga ranar da Fatima ta sanar da ita batun soyayyar Yaya Ameen da Amira, bata
sake yarda wani hira makamancin wannan ya sake shiga tsananinsu ba domin ta san
baza ta iya jurar ji ba, zuciyar ta baza ta iya d'auka ba. Haka suka ci gaba da
harkokinsu ba tare da ta bari Fatima ta fahimci komai game da abin da ke lullu6e a
zuciyarta ba, ta bi ta toshe duk hanyar da Fatima zata fahimci a kwai wani abu a
zuciyarta game da Ameen, tun da ta fahimci kamar Fatin na zargin hakan, sai dai duk
wani walwala da kuzarinta ya ragu, sam! ta daina tambayar Fatima game da Al'ameen
kamar yadda take yi ada, idan ma Fatima ta dauko hirar shi, da dabara za ta dakatar
da ita ta hanyar sako wani hirar dabam ta shashantar da wancen hakan ya saka
zuciyar Fatima a wa si wasi a kan zarginta, har ta samu kwanciyar hankali, don ta
yi imanin cewa; Joy baza ta ta6a boye mata wani sirri na rayuwarta ba, sai ta
watsar da zargin da ta ke yi suka ci gaba da sabgarsu na yau da kullum babu wani
sauyi.

Joy kuwa kwantan 6auna ne kawai ta yi, don zuciyarta cike ta ke taf da kaunar
Al'ameen, ita kad'ai ta san irin famar da take da zuciyarta, duk daren duniya sai
ta sha kuka ta gode Allah, musamman da ta fahimci yadda ya ke kaunar Amira da kuma
yadda itama Amiran ta mace a kaunar shi, ganin haka yasa ta gama sadak'arwa ta rasa
Al'ameen domin dai da idanunta take ganin zallar soyayyar Amira a tattare da shi,
hakan yasa take jin wani irin mahaukacin kishi da haushinta na babu gaira babu
sabar, har yau ta kasa bata fuska su dinga ko da gaisuwar mutunci ne, ba yadda bata
yi don ta tausasa zuciyarta a kan hakan ba abin ya gagara, Fatima da ke tsakanin
su, sai ta bar hakan a kan cewa jininsu ne bai hadu ba.

A duk sanda ta zo gidan ta yi rashin sa'a da katarin ganinsu a tare, ranar takan
wuni ta kwana da mugun ciwon kai, bata ta6a zaton duk wadannan abubuwan da take ji
shafar mai ba ne, sai yau da suke k'ule a uwar d'akin Ummi, Fatima na sanar da ita
cewa iyayen Anty Amira sun ce Yaya Ameen ya turo magabatansa a zo ayi zancen
aurensu. Kamar saukar gudumar wuta haka zancen ya daki zuciyarta, da sauri ta kai
hannu ta dafe saitin zuciyarta da ya yi wani irin dokawa da mugun k'arfi, a dan
gigice Fatima ta kalleta tare da cewa "Ar u ok." "yes I'm ok." Ta fad'a da sauri
tana ya mutsa fuska jin gefen kanta ya fara sara mata, sannu Fatima ta shiga jero
mata, ta gyada kai tare da mik'ewa tsaye, Fatima ta kalleta da mamaki ta ce "Ya dai
friend ina zaki je ?." "Teetee I want 2 leave now." Ta fad'a cike da wani irin
rauni a muryarta, mik'ewa Fatima ta yi ta riko hannayenta tana kallon cikin
idanunta, cikin k'asa-k'asa da murya ta ce "Ki gaya min dan Allah, menene?" Tsura
mata idanu ta yi, na yan sakanni take hawaye ya ciko a kwaurin idanunta, can kuma
kamar an tsikareta ta fisge hannayenta da sauri ta fice daga d'akin tana sharar
kwallah.

Wani irin tafiya take yi tana layi kamar yar caburos, duk in da ta samu jefa
kafarta kawai take yi ba tare sa kula ba, gaba daya idanunta sun kulle bata ko
ganin gabanta, tuni hawaye ya gama wanke mata fuska cikin kankanin lokaci.

Babu zato babu tsammani ta ji an ca6e hannunta, yana yin sauyin bugun zuciyarta da
kuma kamshin turaren shi ya tabbatar mata da cewa shi ne, hannun shi da ke rike da
nata ta kalla, kafin a hankali ta d'ago kai ta sauke idanunta a fuskar shi.
Wani irin kallo yake binta da shi, mai dauke da ma'anoni daban-dabam, d'ago idanun
da ta yi, ya ba shi damar sauke kwayoyin idanunsa a cikin nata, wani irin kallo
suke bin juna da shi mai kama da kallon kuda, hawaye ne ke zurara a kumatunta,
hawayen zallar so da kauna, yayinda shi kuma na shi idanun suka kara rinewa jajur,
zakarar wuyar shi na motsawa yake alamar yana hadiyar wani abu wanda shi kad'ai
yasan ko menene, dawowarsa kenan daga wajen Aliyu zai shiga gida ya ci karo da ita,
ganin yana yin da take ciki yasa ya kasa bari ta wuce, domin da gani ba lafiya ba.

Kamar an wuntsilota daga sama ta bayyana a gabansu, wani irin abu ta ke hanga
kwance a idanuwansu su duka biyun wanda bata fatan ace gaskiya ne, shin ina ma
mafarki take yi' cike da matsanancin tashin hankali, cikin rawar murya ta ce "Yaya
Ameen." Sautin muryarta ya daki kunnuwansu baki d'aya, sai dai ko da wasa Al'ameen
bai dauke idanusa daga fuskar Joy ba kuma bai saki hannayenta ba.

Yayinda ita kuma ta d'ago manyan jik'akk'un idanunta ta sauke su a kan fuskar Amira
dake tsaye tana binsu da kallo hankali tashe, suna had'a idanu ta ji wani irin
k'ululun abu ya tokare mata makoshi, wani irin kuka ne ya taho mata daga can kasar
zuciyar, da mugun k'arfi ta fisge hannunta daga rik'on da ya mata ta juya da gudu
ta bar wajen.

Ba shi da kuzarin tsayar da ita domin jin damuwarta, shi kan shi cikin matsanancin
damuwa yake, Sai dai ganinta cikin damuwa ya so mantar da shi ta shi damuwar.

"Yaya Ameen." Sautin muryarta a karo na biyu ya ratsa kunnuwarsa, a hankali ya
dauke idanunsa daga hanyar da Joy ta bi, ya sauke a fuskarta, hawaye ya gani kwance
a kwaurin idanunta, tsabar wutar kishi da tashin hankali kwance karara a idanunta.

A halin da yake jin kansa bai san mai zaice mata ba, sai kawai ya samu kansa da
cewa; Ban san menene ya saka ta kuka ba, bansan me yasa na damu da damuwarta ba
abin da na sani kawai ina jinta a zuciyata misalin yadda nake jin Fatima a raina,
bana son ganin hawayenta kamar yadda bana son ganin hawayen Fatima.

Kasancewarta mai tsananin wayo, yasa ta yi murmushin yak'e wanda aka ce yafi kuka
ciwo, tana share hawayenta da bayan hannu a fakaice ta ce " Wata kila hakan nada
nasaba da yadda suna shaku da Fatima ne, tabbas nima ina kaunarta a raina kamar
yadda nake kaunar Fatima." Tsura mata idanu ya yi, shin da gaske take abin da ta
fada ya ke tambayar kansa, yayinda maganganunta suka maimaita Kansu d'aya bayan
d'aya a kunnuwansa.

Ganin haka yasa ta ra6a ta fice ta gefensa ba tare da ta sake kallonsa ba.


************

Ragwab! Fatima ta koma ta zauna a kan gadon Ummi, hankalinta a tashe, shin' me
abinda Joy tayi yake nufi, wannan shine karo na biyu da shigen irin haka ya faru,
kar dai ace zargin da ta dade da cirewa aranta ne ke shirin tabbatuwa, zumbur ta
mik'e, ya zama dole ta tabbatar kafin ta zartar da wani hukunci da mugun sauri ta
biyo bayanta, a zaure suka yi kicibus da Al'ameen, kallon tuhumar daya jefe mata
yasa da sauri ta ce "Yayana ka had'u da Joy a waje." Girgiza mata kai kawai ya iya
yi ya bude d'akinsa ya shige,yana tambayarta Ummi ta dawo? A sanyaye ta amsa mashi
da "A'a Taya." Kafin ta juya jiki a sanyaye ta kima cikin gida zuciyar t ciek da
tunani kala-kala.



Sai da Joy ta kwashe kwana biyar bata je gidansu Fatima ba kuma bata je school ba,
tana gida tana fama da mikin zuciyarta don sai da ta kwashe kwana biyu kwance tana
fama da zazza6i da ciwon kai, lamarin da sai da Mom ta kira Dr solo ya daura mata
drip kafin ta ji dama dama, wannan shurun na Joy ya saka Fatima a cikin
matsanacin damuwar da ya kasa 6oyuwa a tattare da ita duk kuwa yadda ta so
boyewar, Al'ameen ne ya fara lura, ritsata ya yi a d'akinsa ya tambayeta meke
damunta, bata 6ata lokaci ba wajen sanar da shi damuwarta ba, san da ta ambaci Joy
sai da gabansa ya fad'i, tun Daga ranar da abin nan ya faru da tunanin ta yake
kwana yana tashi, taurin kai da dakiya ce kawai irin ta shi yasa bai bude baki ya
tambayi Fatima ba, dakewa ya yi ya shiga bata baki a kan ta cire damuwa a ranta
domin dai lafiya ita ke 6uya.


Ranar Monday kamar wasa Fatima na shiga class ta tarad da ita, da gudu ta karasa ta
rungumeta ya baya, ranar basu maida hankalin kan darusan da aka koyar ba, saboda
yadda sukayi kewar juna, Fatima ta so ta tuhumeta a kan abin da yasa ran nan ta
fice ta barta daga ta yi mata zancen Yaya Ameen da Amira sai kuma wani tunani ya
fado mata ar rai wanda tilas ya sakata fasawa.

**********

Ajiyar zuciya Zainabu ta sauke bayan ta gama sauraren jawabin Amira, kallon Amira
tayi da ke kuka sha6e sha6e ta ce "kin tabbatar da abinda kike fada kuwa Amira."
Cikin shessheaka ta ce "Tabbas na tabbar da idanuna na hango tsantsar soyayyar
Arniyar yarinyar na kwance a cikin kayan idanunsa dan Allah Zainabu ki bani shawara
ya zan yi wallahi zuciyata zata tarwatse."............



Afuwan masoyaπŸ™




Oum Ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 40*


Mikiya Writer's Association


*Masu facebook ku yi following wannan account Ι—in domin samun damar cin giveaway
Ι—in da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*

https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL



Kwantar mata da hankali Zainabu ta yi, tare da ba ta shawara a kan ta yi kunnen
uwar shegu da abin ta cire shi daga zuciyarta ta yi kamar bata fahimci komai ba
tunda dai hasashe ta ke yi bata da tabbas a kan lamarin. Cikin kuka ta ce "Wallahi
Zainabu da idona na gani ya rik'e hannayenta, suna bin juna da wani irin kallo,
kollon da bai ta6a yi mini irin shi ba, irin kallon da nake fatan samu daga gare
shi koda a mafarki ne. Ta6e baki Zainabu ta yi ya zuwa yanzu lamarin Amira ya fara
bata haushi, cike da jin haushi, ta ce " Ke dai Wallahi an yi raguwar banza, yanzu
haka ma fa ba abin da ki ke tunani ba ne shegen kishinki ne yasa ki ke ganin hakan,
ta yaya Ustaz kamar Al'ameen zai tsaya soyayya da wata arniya mai fistari a tsaye,
ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, ni kam ko duk jikina kunne ne ban yarda ba."
Murmushin takaici Amira ta yi, ta na kallon Zainabu a zuciyarta tana cewa; Hmm!
Zainabu don dai ba ki san so ba ne shiyasa ki ke cewa haka, "Kallon fa?" Zainabu ta
fad'a tana dan zaro mata ido had'i da d'an hararanta, girgiza kai ta yi tare da
sakin murmushin yak'e wanda ya fi kuka ciwo.

Amira ta dauk'i shawaran Zainabu don kuwa koda wasa bata yarda ta yima Al'ameen
maganar Joy ba haka ma Fatima duk irin yadda abin ya tsaya mata a rai kuwa.

A haka tafiya ta mik'a a ka kwashe satittika, har zuwa lokacin kuwa Al'ameen bai
tura magabatansa wurin kawunnan Amira ba kamar yadda suna buk'ata kuma bai ce musu
komai ba, ganin shirun nashi ya yi yawa yasa d'aya daga cikin k'annen marigayin
mahaifin nata kiran Al'ameen har gida.

Tare suka shirya da Aliyu suka tafi gidan nasa bayan sallar isha'i, d'aya daga
cikin samarin gidan ya musu iso har falon kawu Basiru kamar yadda suke kiran shi,
bayan gaisuwa aka gabatar musu da ruwa da abin motsa baki, sai da suka d'an ta6a
hira da Aliyu kasancewar kawun mutum mai yawan magana sai dai mafad'aci ne na
karshe, haka ma Alin shima magananne ne ba laifi idan ya samu waje. Al'ameen kam
kansa na k'asa yana saurarensu gabansa na fad'uwa ya k'agu ya ji kiran me a ka yi
masa.

Sun dan d'auki lokaci a haka kafin kawu Basiru ya yi gyaran murya ya ce "Am!
Aminullahi." D'agowa Al'ameen ya yi ya kalle shi tare da sake yin k'asa da kai cike
da surukuta, "Abinda yasa na kira ka, mun ji shirunkaya yi waya, yau kimanin wata 3
da aka yi maka magana ka turo magabatan ka amma har yanzu shiru, to mun gaji da
gafara sa kuma har yanzu bamu ga k'aho ba, domin dai yarinya cikin y'an uwanta wani
ya ganta kuma ya nuna yana so , to kaga gida bai k'oshi ba ba'a kai waje ba, sai
dai kasancewar mu ba k'ananun mutane bane yasa jiya muka zauna ni da y'an uwana, a
kan maganar, yanzu dai an umarceni kasancewar nine k'arami a cikinsu suka wakiltani
a kan na kira ka na shaida maka, an baka nan da sati d'aya idan har da gaske ka ke
muji wani motsi idan kuma ba haka ba, to gaskiya komai zai iya faruwa, wannan shine
mak'asudin kiran da na yi maka da fatan ka fahimce ni."

Tun kafin kawu Basiru ya kai aya a maganarsa, tuni gumi ya tsatsafowa Al'ameen a
gaban goshi, banda dukan uku-uku babu abin da zuciyarsa ke yi, sai Aliyu ne ya yi
karfin halin amsawa kawu Basiru da cewa; Na'am kawu mun fahimta." Ya ce "Toh dama
kiran ke nan idan kuna da abin fad'i kuma ku fad'i ina saurara." Aliyu ne ya sake
amsawa da "A yi hakuri kawu, in sha Allah zaku ji mu kafin satin." Da haka suka yi
sallama da kawu basiru, Aliyu ya ajiye masa naira dubu uku suka fito.


Daga Alin har Al'ameen an rasa mai karfin halin cewa wani abu, har suka yi nisa da
k'ofar gidan, shi Aliyu ganin halin tashin hankalin da abokinsa ya shiga ne ya
sanyayar masa da jiki hakan ya tabbatar masa da akwai wata matsala, yayinda A
bangaren Al'ameen yake hasaro irin tashin hankalin da Ummi ta shiga ranar da ya
fara sanar mata da cewa; Iyayen Amira sun nemi ya turo, wannan na d'aya daga cikin
abin da yasa har yau bai sake tayar da maganar ba, bawai don ya rasa naira dubu
goman da za'a kai a matsayin kudin gaisuwar ba, kwarai ya hangi firgici da tashin
hankali a cikin kwayar idanunta, wanda har ya kai ta ga son yin su6ul da baka a
gabansa ta furta wasu kalamai da suka hana shi rintsawa a daren ranar.

Aliyu ne ya katse shirun da cewa; Abokina ya kamata fa ka yi wani motsi a kan
lamarin nan, ka dai ji abinda kawu ya fad'a, kar ka yi sakacin da zaka rasa Amira
domin na lura kiris suke jira shi yasa suka yi maka wannan daurin talalar, duk da
nasan kai ko da ta subuce makan ba damuwa zaka yi ba tun da ba wani sonta kake yi
ba" Ajiyar zuciya ya sauke, da wani irin sanyin murya wanda Aliyu bai ta6a jin ya
yi irinta ba ya ce "Aliyu ina son Amira, wallahi ina kaunarta ina fatan ta zame
mini uwar y'ay'ana, sai dai ina jin tsoron wani abu, ina ji a jikina a kwai
gagarumar matsala." "Wacce irin matsala? Aliyu ya jefa masa tambayar cikin dan
tashin hankali, cike da wani irin k'unci ya ce " Dangin mahai...." Sai kuma ya yi
shiru ya girgiza kai, Aliyu ya dafa kafadarsa ya ce "Dan girman Allah kar ka boye
mini matsalarka abokina, idan kamin haka zaka saka zuciyata cikin zullumi." Shiru
ne ya ratsa tsakaninsu na yan sakanni, kamar bazai ce komai ba, can kuma ya sauke
nannauyar ajiyar

Please Login or Register in order to submit comment