Reading JOY by Aysha Nalado Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi bai, kara cewa komai ba
ya nufi dakin shi, Fatima kuma ta nufi kitchen ta dauki abincin shi tabi bayan shi
da shi.

Abincin ya ci ya koshi, bayan ya gama yasha ruwan sama, kishingid'a yayi a katifar
shi ya lumshe idanu, da ace shi wani dan gata ne da kwanciya zaiyi ya huce gajiyar
daya kwaso na tafiya, amma yasan haka ba Abu ne mai yuwuwa ba, idan ya kwanta wa
zai basu su ci,wa zai kula da mahaifiyar shi da kanwar shi, wa zai dauki dawainiyar
rayuwar su, wa zai biya musu bukatunsu na yau da kullum???, "Babu." Ya ba kan shi
amsa a bayyane, shine gatan su da shi suka dogora da Allah suka dogora, tunanin
yadda yasha gwgwarmayar zuwa da dawowa school yau ya shiga yi, zai Iya cewa daga
zuwan har dawowar kusan da kafa yayi saboda halin babu, duk abin da ya roro ba ta
kan shi yake yi ba, ta Ummi da Fatima yake yi, sune a gaban shi, da wannan tunanin
ya yunkura ya mike ya canja kayan jikin shi ya fice daga dakin.

Cikin gidan ya shiga ya ma Fatima sallama sannan ya fice, daga gidan, direct
unguwar Sayako ya nufa gidan Alhaji bala baka shot, in da yake zuwa daukar keke
napep, ya na fatan Allah yasa akwai keken a kasa, cikin sa'a ya samu har biyu a
kasa, take aka bashi wani form yayi singing, singing din da kulli yaumin idan zai
yi sai gaban shi ya fadi ya rasa dalili, amma haka yake daurewa domin bashi da
wata hanyar da zai samu kudi a saukeke sai wannan, yana dan tana sana'ar hannu,
amma aikin nashi ne ba ko wani lokaci yake samu ba, haka ya dauki keke daya ya
kama aiki da bismillah.

Tafiyar Al'ameen babu dadewa Ummi ta dawo,dauke da buhun bakko, Fatima ta tare ta
ta amsar mata kayan, tana mata sannu da dawowa "yawwa Fatima sannu da gida," ta
karashe maganar tana zama a kan kujera, " matso da bakkon nan Fatima mu gani."

Matso mata da shi gabanta tayi, kwancewa tayi ta shiga fito da kullin ledodi a kasa
buhun kuma ta fito da doya manya guda uku, kallon Fatima da tayi kasake tana
kallonta tayi ta ce "kwashe wannan ki kai mana kitchen wannan kuma ta fada tana
nuna mata ledodin gabanta ki bud'e robar da muke ajiye kayan abinci ki sassakasu
ciki shinkaface da wake, Fatima da mamakin Ummi ya gama kasheta tace "Ummi kasuwa
kika je? Ita kanta bata san sanda tambayar ya subuto mata ba ganin dai tunda suke
Ummi bata tana zuwa kasuwa ba komai yayanta ke kawowa, komai za'a siya shi yake
siyowa dagowa Ummi tayi ta kalleta kafin ta ce "ba kasuwa naje ba." "To ina kike je
waya baki wadan nan kayan abincin?" Ta fada a zuciyarta a zahiri kuma ta ce "Oh ai
na dauka can kika je na ganki da kayan abinci." Ummi bata amsata ba, sai ci gaba da
kokarin kwance ledan shambo da tarugu da take yi ta juye a kwando.

Cefane Ummi ta dawo da shi ba na wasa ba , harda su mai da maggi da busasshen kifi,
sai da suka gama Adanawa tsab ta kalli Fatima ta ce "ba na son yayanki yayanki ya
san da maganar kayan abinci nan ko da wasa." "To Ummi amm....." "Kinji abunda na
fada ko baki ji ba." Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "naji Ummi insha
Allah bazai ji ba." Murmushi Ummi tayi ta ce "yawwa fateetee ngd,." Fateeteen data
fada yasa Joy ta fado mata a rai, cike da dan damuwa ta ce "Ummi yau joy bata zo
school." Ummi ta ce "Allah sarki kila ta samu wani uzurine yau din." Fatima ta ce
"ummi Joy fa bata fashin makaranta, ni dai ina ji a jikina kamar bata lafiya, tun
dazu da na tuno ta gaba na ke faduwa." Ummi ta ce "Assha! To kiyi ta addua, koma
menene Allah ya takaita." "Amin Ummi" Fatima ta amsa yana mikewa zuwa kitchen dan
ta hada wutar sanwar dare.


Karfe Tara dai dai Al'ameen ya maida keke nape gidan Alhaji bala baka shot, kamar
yadda yayi singing sanda zai dauka haka yayi singing da ya mayar bayan alhajin da
kan shi ya duba lafiyar keken, yaga babu wata matsala, 3k Al'ameen ya bashi cikin
cinikin dubu hudu da dari biyu da yayi, amsa yayi yana washe baki sabanin da da
fuskarshi yake murtuk yana jiran yaji da wannne ya dawo dan yanzu kafin shi mutum
biyu da suka dawo da kekuna har yanzu gasu nan ana kes, daya ya samu accident gefen
keken ya lotsa dayan kuma dubu biyu yakawo sabanin dubu uku da yake a ka'ida idan
mutum yayi fitar rana zuwa taran dare zai kawo.

Sallama yayi musu ya tafi bayan yabar alhaji bala na ta bala'i a biya shi ko ya
hada su da polie don shi akan kudi babu sani babu sabo ne.

Sai gurin goma saura ya iso gida, a tsakar gida tarad da su, Fatima ta tare shi
tare da karbar ledan biredin daya siya musu a hanya.

Ummi ya tsuguna ya gaisar kamar yadda ya saba kullum, ta amsa mishi tana "Alhmdllh
yayan Fatima jiki yayi warware dama tunda na dawo Fatima ta ce ka fita aiki nace to
jiki ya yi dauki kenan." Murmushi yayi ya ce "eh ummi wlh jiki Alhmdllh." Nan ya
zauna Fatima takawo mishi abincin ya ci suna ta hira, gefe daya kuma iska na
kadawa hadari na haduwu,

Sai gurin sha daya saura Ummi ta ce su ta shi haka gobe da makaranta, dari takwas
din daya rage mai a aljihu ya kwaso duka ya mikawa Ummi, ya ce "Ummi ga wannan ki
rike a hannunki a sai wani abin." Kallon shi tayi tana murmushi ta ce "A'a
Amintacce ka bar shi kaima ka rike a hannunka kayi hidimar makaranta ni akwai kudi
a hannuna kuma a kwai abincin da zamu ci gobe ka fini bukatarsu, Allah yayi
albarka." Tana gama fadin haka ta mike ta shiga daki ta turo kofarta don karma ya
tsareta da magiya,

Iska da hadarin daya taso gada gadan ne yasa shi sauri ta shi yayi hanyar dakin
shi, gaban shi na dokawa wanda shi kadai yasan dalilin haka.

Kamar jira ake yi su ta shi a tsakar gidan, take ruwa ya kece da wani irin karfi
mai ban mamaki, kudundunewa yayi cikin bargo bayan ya lafta kaya masu nauyi a jikin
shi, kwance yake kawai yana jiran tsammani, amma zuciyar shi cike take fall da
tsoro, fatan shi daya kar ciwon shi ya tashi, shiru yayi a kwance yana sauraren
sautin ruwa da haka barci barawo ya kwashe shi ba tare da sanin shi kasancewar
dama a matukar gajiye yake.

Kusan raba dare akayi ana tsuga ruwa, can cikin barcin shi ya fara jin sauyi a
jikin shi, ji yayi wani irin sanyi na ratsa kasusuwan jikin shi, babu abin da yake
bukata a lokacin sai dumi, duk da kasancewar a cikin bargo yake a kudundune, dumi
yake bukata ba irin dumin bargo ba, sannu a hankali tsigar jikin shi ya fara tashi,
kafin daga bisani wani irin feeling ya lullubeshi, rasa Inda zai saka kanshi yasa
ya cusa duka hannayenshi cikin wandon shi, ya matse abin shi dake ta mishi wani
irin honkoro, yana ambaton innalillahi wainnailai rajiun a zuciya, magani yake son
sha , amma har yanzu abin bai kai matakin da Dr ya ce idan ya kai ya hadiyi
maganin ba, kuma baya fata ya kai stage din, sai dai fatan shi bata karbu ba, dan
cikin abinda baifi minti biyu ba maran shi tayi wani irin kullewan da yasa babu
shiri ya yaye bargon ya mike ya nufi jakar nan, ya zaro sachet din maganin shi
balla yayi ya jefa a baki kafin ya bi da ruwan buta ya koma ya kwanta yana
nunfarfashi.

Da asuba da karfin shi ya tashi ba kamar wancen ranar ba kasancewar bai bari ciwon
ya shige shi sosai ba ya sha magani, kamar kullum saida ya kwankwasa masu Ummi kofa
kafin ya wuce masallaci, koda ya dawo zama yayi ya gabatar da azkar da sauran
addu'o'inshi Inda ya roki Allah ya kawo mishi dauki game da wannan matsalar da
kullum kara gaba take yi a gare shi, bayan ya gama kuma ya daura da karatun
alkur'ani mai tsarki cikin daddadar sautin kira'ar shi wanda ya karade ko ina na
gidan hatta da gidajen makota na kusa, Amira tana daga tsakar gidan su ta na
aikace aikacenta tana sauraren shi zuciyarta gari tass.

Seven fourty Fatima ta gama shirinta na schools, sai dai yau ma kamar jiya har ta
fito gida babu Joy babu labarinta, jiki a sabule ta k'arasa class, tana fatan Allah
yasa ta cimmata a can , sai dai nan ma wayam, haka ta isa sit din su ta zauna jiki
a mace.
Yau kan damuwar data shiga yafi na jiya haka kawai jikinta ke bata ba lafiya ba, ta
kudiri aniyar zata tambayi David ta ji ko mekefaruwa tun da shi dan uwanta ne bazai
rasa sani ba.

Da aka buga break time, ta yi sauri ta isa sit din David da har ya mike yana goya
jaka da harshen nasara ta ce "Sannu David." Wani banzar kallo ya mata ya dauke,
bata damu ba ita dai fatan ta taji halin da Joy ke ciki ta sake ce ma shi "me yasa
Joy bata zo school ba kwana biyu." Share ta yayi kamar bada shi take magana ba bata
yi zuciya ba ta sake cewa "ko bata da lafiya ne dan Allah ka gaya min na damun
sosai da rashin ganinta?" D'agowa yayi wannan karon ya ce "ha'ahh! Wai ke mayya ce
ne? To nima ban sani ba kije gidan su ki duba."daga haka ya fice ya barta tsaye a
wurin.

Haka Fatima ta koma gida cikin wani irin yanayi, tana isa kuwa labarin yau ma Joy
batta zo school ba ta fara ba ummi da yadda sumayi da David, tausarta Ummi ta yi
akan kar ta damu in sha Allah joy tana lafiya ai lafiya ke buya, ta dai ji ne kawai
amma ba wai hankali ta ya kwanta ba.

Ranar har Yaya Ameen sai da ya fahimci tana cikin damuwa daya dawo da daddare,
shima cikin damuwar yake amma ya danne nashi, koda ya tambayeta damuwarta kin fada
ta yi sai hawaye da ta shiga zubarwa sharr! Ummi na jin su bata saka baki ba, don
abin na Fatima ya fara wuce makadi da rawa, har kullum bata gajiya da mamakin irin
shakuwa da kaunar dake tsakanin Joy da Fatima.

Da kyar Al'ameen ya lallabata ta sanar mashi da damuwar tata, tabe baki bayan ya
gama sauraranta, shi bai ga abin damuwa akan wannan ba, hakan yasa bai bama damuwar
tata mahimmanci ba, sai ma canza akalar hirar tasu da yayi.

Washegari daya kama friday ma bata sake zani ba still Joy bata je school ba, zuwa
yanzu kuwa ta gama yanke shawaran bin abinda zuciyarta keta azalzalanta akai wato
zuwa gidan su Joy ...............



Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


*PAGE 8*


ASSALAMU ALAIKUM

KUYI HAƘURI DA JI NA SHIRU DA KUKA YI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI
DALILI MAI ƘARFI , AMMA YANZU NA DAWO INSHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA,
FATAN DAI BAKU MANTA LABARIN AL'AMEEN DA JOY BA KUCI GABA DA BIBIYA AKWAI
FAƊAKARWA, WA'AZANTARWA RIKICIN KABILANCI, TARE DA ZAZZAFAN SOYAYYA MAI TAƁA
ZUCIYA.


A bangaren Joy kam jinye take yi hankali kwance, daga Mom har Papa wani irin so
da kulawa suke nuna mata na musamman, sai dai kamar yadda Fatima ta shiga damuwa
saboda rashin ganin ta, haka itama ta shiga matsanancin damuwa saboda rashin ganin
Fatima, hakan yasa ranar Friday ta shirya don zuwa school amma ƙememe Mom ta hana
ta zuwa ta ce ta bari sai Monday badan ta so ba ta haƙura saboda kar Mom ta zargi
wani abu, ta bari idan ta wuce aiki sai ta saci jiki ta je gidansu koda Ummi ne ta
gani, da wannan shawarar ta koma ɗaki ta cire uniform ta yi shirin zuwa gidan su
Fatima, sai dai ga mamakin ta ranar Mom ƙememe taƙi fita ko bakin get har wurin sha
ɗayar rana, kamar tasan abin da take ƙullawa, gajiya tayi ta miƙe taje ɗakin ta, a
kwance ta sameta bata da alamar fita, zama ta yi a bikin bed ta ce "Mom yau baza
ki je aiki ba ne." kallon ta tayi kafin ta amsa da "Yes daughter yau na ɗauki
excuse zan huta sai on Monday." har ranta bata ji daɗin wannan lamari ba don ta
sani in dai ba yau ba to bata da damar fita daga gidan sai ran monday, ita kuma
bata jin zata iya jurewa har zuwa ranar ba tare da ta saka Fatima a idanunta ba,
haka ta bar ɗakin Mom jiki a sanyaye, ranar haka ta wuni sukuku duk ranta babu
daɗi.

Kamar yadda Fatima ta ƙudiri aniyar zuwa gidansu Joy yau, bata yi ƙasa a gwiwa ba,
la'asar nayi tayi shirinta na hadda, cikin dogon zumbulelen hijabi ta ruwan toka,
ko jiran Ummi ta shafa addu'a suyi sallama da kyau bata yi haka bata biya gidan su
Amira su jera da yara gidan kamar yadda suka saba jerawa ba ta wuce.

Direct haryar gidan ta kama tana sauri don kar ta ci karo da idon sani.Sai da ta
tsaya a gaban tangamemen get ɗin gidan sannan gabanta ya fara faɗuwa take wani irin
tsoro ya shige ta, tsoron mahaifiyar Joy , sau ɗaya rak ta taɓa ganin matar wata
rana an tashe su school, tun daga irin kallo ɗaya data mata tsoronta ya ɗarsu a
ranta, sai dai bata jin duk da haka zata iya komawa batare da ta san halin da Joy
ke ciki ba don ta tabbata baza ta iya rintswaba idan hakan ta kasance.

Ta fi minti goma kafin ta daure ta miƙa hannu tayi knocking ɗin ƙaramin kofar get
ɗin a hankali, bata zata za'a jiyota ba balle har a buɗe mata sai dai ga mamakinta
taga an buɗe get ɗin wani baba iyamuri da ko zo in kasheka da hausa bai sani ba ya
leƙo. Suna haɗa ido gaban ta ya faɗi amma ganin ya sakar mata murmushi, yasa taji
hankalinta ya ɗan ƙwanta, cikin harshen nasara daya caƙude da yaren igbo ya ce "My
daughter who ar u looking." da sauri itama cikin harshe da ya mata magana ta ce
"I'm looking 4 Joy, ni ƙawarta ce naga kwana biyu bata zo school bane shi ne nazo
in dubata ko lafiya." ɗan jim ya yi kafin ya ce "kom in." tare da buɗe mata ƙaramin
get ɗin, jiki a saɓule ta bi bayanshi gabanta na dakan uku uku.

Gurin zama ya nuna mata daga gefe, ya ce ta jira shi ya na zuwa yama Joy ɗin
magana, idan ya shiga wa za'a ce mata, ta ce "Fatima Husain." "Ok." ya amsa mata
tare da ficewa.

Farfajiyar gidan Fatima ta shiga bi da kallo, bata taɓa shigowa gidan ba sai yau,
take ta ji ta raina kanta, ashe girman gidan da tsaruwar shi daga waje duk shafan
mai ne akan cikin, baƙauyiya tukuf ta koma tana bin ko'ina da kallo baki sake ,
tare da tunanin wani irin dukiya mahaifin Joy ke da shi haka, manyan motocin dake
fake a parking lot ta ringa kallo tana al'ajabin yanzu duk wannan na mutum guda ne.

Get man direct entarance ɗin first plat na gidan ya nufa, tare da danna doorbell,
dai dai lokacin Mom na zaune a main falon tana cin cake, tasowarta kenan daga barci
yunwa ya korota ƙasa, ɗaya daga cikin hause maid na gidan waɗanda ke da zarafin
shiga cikin part ɗin, ta kira ta ce ta duba wayake knock,dubowa tayi ta dawo ta
sanar mata get man ne, umarni shigowa ta bashi, ya shigo ya zube a gabanta ya
kwashi gaisuwa duk da ya girme mata nesa ba kusa ba don zai Iya haifarta ma, cike
da fariya ta amsa, ya ce "Wata ce ta zo neman Joy yar school din su ce, ta ce
sunan ta Fatima Husain wai taga kwana biyu batta zo school ba shine ta zo ta gani
ko tana lafiya." Bata rai tayi tare da hade girar sama da ta kasa, ko bata
tambaya ba tasan wannan tsinanniyar Muslim girl din ne dake shirin warware mata
aiki, wato har abin bai tsaya Iya school ba shine har gida zata biyo ta, aiko zata
ci ubanta yau sai ta gwammace kida da karatu a fusace ta mike ba tare da bi ta kan
get man ba ta fice daga plat din, bayanta ya biyo da sauri yana tambayarta ko
lafiya, Bata saurare shi ba, ta wuce kamar kububuwaa'aikan gidan tuni kowa ya shiga
taitayin shi suka bits da kallo, a zaune ta tarar da Fatima in da get man yace ta
zauna ta shagala da ka kallon flawers bata san karasowar Mom ba sai dai ta ji
saukar gigitacen mari a kumatunta, a firgice ta mike tsaye, tare da sauke idanunta
akan mahaifiyar Joy take gabanta ya yanke ya fadi, firgici da tsoro suna bayyana
karara a fuskarta, shakar wuyar hijabinta Mom tayi cikin zare ido ta ce "Me ya kawo
ki gidan na, Me kike nema a gidan nan,menene tsakanin ki da yata, abin naki har ya
wuce school shine kika biyota har gida ko, ina da labarin komai akan gurbata mata
tarbiya da kike yi da canza mata akida, to ina miki warning da babbar murya daga
yau sai yau na miki tsakani da Joy babu ke babu ita, ba a gida ba, ba a makaranta
ba, ki rabu da ita kar ki sake kulata idan kuma ba haka ba na miki alkawarin sai na
batar dake a garin na daga ke har zuri'ar Ku gaba daya." Daga haka ta shiga janta
keee kamar kayan wanki ta nufi get da ita.

Hayaniyar Mom yasa Joy dake kwance a dakin ta cike da damuwan rashin damun famar
zuwa gafan su Fatima saurin mikewal ta daga labulen window tare da lekawa idanunta
ya saka a kan Mom rike da wuyan Fatima tana ja, gabanta ne ya yanke ya fadi, da
wani irin mugun gudu ta nufo downstairs tana tsallakewa bibiyu ba tare da ta kula
ba, tun daga bakin kofar part din ta shiga ce wa "Stop Mom Stop Stop please."
Amma ina bata jita ba, ta bude get din tare da hankada Fatima wacce tuni ta fice a
hayyacinta Wuyan hijabinta ya yage ya zame kasa, dankwalinta ya fadi kasa gashin
kanta ya bayyana waje. Wani irin hankada ta mata mai mugun karfi da biyu niyarta ta
tura ta bige da palwayan dake kofar gidan irin na kasan nan, sai dai kawai tajita
caraf jikin mutum, wanda ya diro kamar daga sama, dai dai time din Joy ta iso wajen
su a guje tare da rike hannun Mom tana kuka.....
[12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


*PAGE 9*


Gaba ɗaya Fatima ta gama sadaƙarwa ta bugu da falwayan nan dan har ta rintse ido,
sai dai babu zato ko tsammani ta jita a jikin mutum, turarensa ne ya tabbatar mata
da cewa shi ne, take ta ƙamƙameshi tare da fashewa da wani irin kuka mai ƙarfi.

Rintse idanu Al'ameen yayi zuciyar shi na tafarfasa, zai iya jurar komai amma
banda taɓa tilon kanwar shi, zai iya yin fito na fito da ko waye akanta, ita kaɗai
ce wacce zai iya bugu ƙirji ya nunawa duniya a matsayin ƴar uwarshi.

Lokacin da ta fito daga gida tana shan kwanan gidan su Joy yana ɓullowa bata
ganshi ba amma shi ya hango bayan, kamar ya kwala mata ƙira sai wata zuciyar ta
raya mishi cewa ba ita bace, tunda yasan ba nan bane hanyar haddarsu wata ƙila
daya daga cikin yaran maƙota ne da suke zuwa hadda ɗaya, sai dai shigan sa gida ya
tabbatar masa da ita ɗin ce, don gaba daya ya tarar da yaran makotan nasu a tsakar
gida wai sun biyo mata su tafi hadda, yana ji Ummi ta amsa musu da Fatima ta riga
ta wuce bata biya musu bane" Gabanshi ya faɗi, ke nan ita ɗin ce ina zata je??? ya
jefawa kanshi tambaya, tsoro ne ya shige shi lokacin da zuciyar shi ta raya ma shi
wani mugun tunani, ta ke ya kawar da shi ya na girgiza kai, kasa kwanciya hankalin
shi yayi hakan yasa ya biyo bayanta da sassarfa ba tare da ko Ummi ya sanar wa
mekefaruwa ba, kwata kwata bai kawo gidan su Joy aka ba, sai dai ganin ya shanye
kwanar ya shiga wata bai ganta ya fara zargin ko can ta je, take hirarsu ta jiya da
dare ya dawo mai, tabbas yadda yaga ta damu da rashin ganin Joy yasan zata iya zuwa
gidansu don ta duba lafiyarta, take ya kama hanyar gidan cike da yaƙinin ganinta
sai dai yana isowa Mom na hankaɗo ta waje kamar wata barauniya.

Sautin kukanta ne ya tilasta ma shi
buɗe idanun shi waɗan da suka rine kamar gauta saboda ɓacin rai ya sauke su a kan
get ɗin gidan, daidai lokacin da Mom ke banko ƙarami ƙofar bayan tayi nasaran tura
Joy ciki dakyar.

Hannu ya saka ya janyo hijabinta ya rufe mata kanta dake buɗe, a hankali kuma ya
shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi ba tare da ya iya buɗe baki ya furta mata
koda kalma ɗaya ba.
A hankali sautin kukanta ya fara raguwa, daga bisani kuma ya dauke gaba ɗaya, sai
shessheƙa da ajiyar zuciya, ganin ta ɗan samu nutsuwa, ya raba ta da jikinshi tare
da kama hannunta suka bar ƙofar gidan ba tare da ya ƙara yi ma gidan kallo ɗaya ba.

A bangaren Fatima mari da hankadar da Mom ta mata bai daga mata hankali ba, kamar
yadda kalamanta suka daga mata hankali, tana jin Joy a jikin jinin jikinta da
bargonta, jinta take yi kamar wata bangaren na jikinta, kwatankwacin yadda take jin
Yaya Ameen haka ta ke jin Joy a zuciyar ta, shin me yasa Mom take son raba su, ta
karashe tunanin sabbin hawaye na silalowa daga idanuwanta.

A haka suke iso ƙofar gidan su ba tare da Al'ameen ya iya buɗe baki ya ce mata
ƙala ba, domin ran shi a maruƙar ɓace ya ke idan ya ce zai yi magana a lokacin
bazai faɗi alkhairi ba.

A zaure ya dakatar da ita, ya shiga ciki ba jimawa sai gashi da dayan hijabin
haddanta a hannunta shi, buta ya dauko ya bata ta wanke fuskarta, sannan ya bata
hijabin ta saka, ya sake jan hannunta, bai tsaya da ita ko ina ba sai haddarsu,
hakuri ya baiwa malamin su akan lattin da ta yi, sannan ya juya ya tafi ba tare da
ya kalli Inda take ba, sai lokacin shirun na shi ya fara daga mata hankali, ta san
sarai shirun nan na yayanta ba alkhairi bane akwai abin a yake shiryawa, magantuwan
shi yafi alkhairi sau da yawa fiye da shirun shi.

*********

A bangaren Joy dakyar Mom ta samu ta turata cikin gidan ta maida get ta rufe,
zubewa ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka, cikin kukan take cewa "why Mom me
yasa zaki yi mata haka, me yasa kika koreta Mom, me yasa kika daketa." Mom dake
wani irin huci ta dago ta watsawa ma'aikan gidan da suka yi cirko -cirko suna
kallonsu wani mugun kallo take duk suka dare kowa ya kama gaban shi, tsugunawa ta
yi gaban Joy a tausashe ta riko hannayenta ta ce "Ki daina kuma daughter ban yi
haka don na bata miki rai ba nayi ne dan kare martabarki data addininmu, na mata
haka ne saboda ta rabu dake don ke ba sa'ar kawancenta bane," katseta ta yi da
cewa "Amma ai na miki alkawarin ni da kaina zan rabu da ita, me yasa zaki
wulakantata." Mom ta ce "To naji kiyi hakuri ki share hawayen ki, kinga baki da
isasshen lafiya." Mikewa ta yi ba tare da ta kula Mom ba ta wuceta fuuu ta shige
plat din su haurawa sama ta yi ta fada dakinta ta bugo kofa ta murza key. Nan ta
silale bakin kofar ta ci gaba da rera kukanta ji take kamar ta yi tsunstuwa ta
ganta a gaban Fatima, me zata ce mata da wani ido zata kalle ta, uwa uba Yayanta
shin da wani baki zata fahimtar da su ce wa bata laifi.

Biyo bayanta Mom ta yi ta tura kofar dakin ta ji shi a rufe, knocking ta shi ga yi
tana kiran sunanta, tana ji taki tankawa, babu irin magiyar da Mom bata mata ba,
karshe dole ta kyale ta, gajiya ta yi da kukan ta mike ta shi ga toilet ta wanke
fuska ta dawo kan bed dinta ta kwanta, wuraren karfe goman dare ta jiyo muryar Papa
a bakin kofarta yana kiran sunanta, ta shi tayi ta bude tare da fadawa jikin sa ta
fashe da sabon kuka, rarrashinata ya shiga yi, cikin sigar nasiha ya ce "Akan me
zata damu kanta dan kawai wata Muslim kanwar ta tazo Mom dinta ta ce bata nan, ai
wannan ba abin damuwa bane Mom tayi haka ne don ta kareta daga sharrin terrorism.

Daga yanayin kalaman shi ta fahimci bai san ainahin abin da ya faru ba, kawai karya
da gaskiya da son rai Mom ta sanar mishi. Shi ya lallabta har ta dan sake ta samu
ta ci abinci.

A haka weekend days suka tafi

Please Login or Register in order to submit comment