Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *DR SULTAN*
(A heart touching love story)
_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬


Bismillah........ ✍
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
_Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!!! Godiya ta tabbata ga Allah, Ina mai Ƙara Jaddada
Godiya ta Ga Allah da ya bani Rai da Lafiyar fara Rubuta wannan littafi Nawa Mai suna *DR SULTAN*
Allah ka bani Ikon Kammala shi Lafiya, dani da Masu karatu, wannan Labarin Ƙirƙirarren labari ne, Ina
roƙan Allah ya bani ikon gamashi cikin kwanciyar hankali da Salama Amin_
*WANNAN PAGE NA SADAUKAR DASHI GA AYIYA GENERATION ALLAH YA ƘARA MUNA
DANƘON ZUMUNCI! ALLAH YA JIKAN AYIYA DA RAHAMA!! ALLAH YASA TA HUTA*😥

_The Beginning_

*Page 1-2*
*Book1*
_____Hayani ya ce ke tashi ta ko'ina Mutane kowa na Harkan gaban shi, Wani kyakkyawan Saurayi ne
tsaye a gaban wani ƙaton shago suna saukar da kaya a moto, Jikin shi duk a jiƙe da Zufa, " Sannu da Aiki,
Ya yi Murmushi tare da Faɗin "Yauwa Oga, Haka suka riƙa sauƙe kaya a mota suna shigar da su cikin
Shago, Gama warshi ya yi dai dai da Kiran Sallah Maggariba, Alwalla Ya yi suka wuce Masallaci, Saida
Akayi Isha'i suka dawo Shago, "Oga zan wuce gida Ya yi Maganar kai a sunkuye, "Har zaka tafi Maleek"?
"Eh Oga"Toh ga wannan ko sai Allah ya kaimu gobe, "Oga Nagode Sosai, "Miye Na godiya Maleek
Hakƙen kane fa, Murmushi mai ƙawatarwa Ya yi, tare da barin shagon, Kai tsaye ya nufi cikin garin cikin
ƙanƙanen lokaci ya iso Unguwar su , daga can Nesa ya han geta tsaye, Sai faman Kalle kalle take, ganin shi
tafe yasa ta ruga da gudun Gaske ta nufi inda yake, durƙu sawa yayi ƙasa tare da buɗe mata Hannu ta faɗa a
ƙirjinshi ya rungumeta, "Ya Maleek! Tun ɗazu nake neman ka Ya Maleek ina Ƙwai da kwai na? Ya Maleek
Ina Arake na? Ya Maleek ina.... Yayi saurin da katar da ita a hankali ya janyeta daga jikinsa, ya tsura wa
kyakkyawar fuskantar ido, "Irin wannan tabbaya Haka Maryama ta!"? "Ya Maleek kaifa kace zaka siyo
min, tayi maganar tana Turo ɗan ƙaramin bakinta mai launin pink color, Numfashi ya fesar cike da gaji, a
hankali ya Buɗe lumsheshin idanuwansa da suka ƙara sakayi jajir saboda gajiya, "Kinje Islamiya"? Kai ta
ɗaga Mishi, "Bazaki bani Amsa ba? A karo na biyu na sake ɗaga Mishi kai, "Shike nan tunda Baza kiyi
magana ba ruwa da ke kwai da kwai Ma Bazan baki ba daman Kaka kawai na saya....tayi sauri rufe Mishi
Baki da iya ƙarfinta da laulausar fatarta kaman ta jariri sabon haihuwa, dariya ta bashi sosai ya yi saurin
gimtse ta, ƙoƙarin janye hannunta yake sam taƙi bashi dama, ƴar ƙaramar ƴarinƴa da Ida sai shegen ƙarfi,
"Uhmm Uhmm ya fara ya jujjuya kai ita ko sai kallonshi take, "Bazato ba Tsammani yaga hawaye na zubo
mata a kan kyakkyawar furkarta, janye hannunta tayi daga bakinsa tana ƙoƙarin barin wajen, da sauri ya
riƙo hannuta tare da juyo da ita suna fuskantar juna, a karon farko ya saki Murmushi, "cikin sanyi Muryar
ya soma faɗin, "Meye a bin kuka a nan"? Kina son Nima nayi Kuka"? a hankali ta girkiza kai almar A'a,
"Toh ki Dena kuka bana so Kinji,hannunsa yasa yana share mata Hawayen, " Ya Maleek da gaske Kaka
kawai kasaya wa kwai da kwai"? "A'a wasa nake ga wannan ke kadai na sayawa, wani irin daɗi taji, "Ya
Maleek komai da komai ka saya min,"Ehh" Ya Maleek Nagode," hannuta ya riƙe suka wuce gida,
Koda suka shigo zaune take a tsakiyar gida saman tabarma, da sauri ta saki hannun sa, ta zauna saman
tabarma, "Kaka Kinga Abinda Ya Maleek ya kawo min Ni kadai bada keba,"Kaka Barka da dare, "Abdul
Maleek Barka kadai an dawo lafiya,"Lafiya kau Kaka, "Madalla ya Kasuwa," Alhamdulillahi Kaka, "Allah
ya taimaka, "Amin ya faɗa cike da gajiya,
"Maryam tashi ki ɗauko masa Abinci sa, "Kaka bari na gama cikin kwai da kwai na, "Bana son
shashanci maza tashi, "A'a Yayi saurin ka tsayeta Kaka ki barta kwai zan ɗauko da kaina, bai jira mi zata
ce ba ya wuce cikin ɗin, "wai yaushe zaki girma Maryam, shekara Goma sha biyu har yanzu ba ki sa ciwon
kan kiba"? dai dai lokacin ya dawo a hankali ya zauna gefen tabarmar ya fara cikin Abinci cikin natsuwa,
lokaci lokaci yakan ɗago ya kalle ta har ya kammala cikin Abincin ya maida kwananan cikin, " Kaka Kinga
sallamar da Oga ya bani yau dubu Biyar ne, "Kai Masha Allah, Allah ya ƙara buɗi Mai Albarka Abdul
Maleek, "Amin Kaka A kwai Abinda kike Buƙata, "A'a Abdul Maleek Allah dai yayima Albarka, furkarshi
dauƙe da Murmushi ya ce "Godiya nake Kaka" Idon Kin gama cikin kayan kwadayin ki ɗauƙo littafin ki
muyi karatu kafin na wuce, "Abdul Maleek idon ka biye mata sai ka kwana a gidan nan bata kammala ba, "
Ni Wallahi kin saka min Ido da yawa Kaka, tayi maganar cike da Shogoɓa, Aure ma zanyi na huta da
wannan ɗumin Naki, lokacin ɗaya suka kwashe da dariya, "Ya Maleek ba kai kace zaka min Au.... "Kinga
kina ɓata min lokacin, zumbur ta miƙe tare da barin wajen, " Allah ka shirya min ƴarin ƴar nan cewar
Kaka, "Amin ya faɗa a hankali,
"Yau Ni zan fara yin karatun idon magana sai ka ƙaramin, " wannan saurin Allah yasa kin iya a bin
kwarai Kaka ta faɗa cike da zolaya, "Babu Ru wanki da Ni, tayi maganar tana ƙoƙarin zama, " Abdul
Maleek ga wannan idon tayi kuskure ka zane ta, ƙarɓan balar ya yi ya na Murmushi, "Ni na san Ya Maleek
bazai da ke ni ba, littafan boko ta fito dasu Nan tashiga yimai bayanin Abinda aka koya musu sosai yaji
daɗin yadda take mai bayani komi dalla dalla ko wanne subject, harda Assignment ya nuna mata yadda
Zatayi, tana gamawa ta fara karatun Alkur'ani cikin zazzaƙar Muryar ta mai sanyi, tunda ta fara karatun ya
lumshe ido yana saurarenta harta kammala, ya ƙara magata, tunda suka fara karatun Kaka ta tsura musu ido
tana kallon su, cike da Sona da kyauna, bayan sun kammala hira sukayi ƙaɗan, Maryam sai hamma take,
"Kaka ni zan tafi Saida safe, "Toh Abdul Maleek Allah ya tashe mu lafiya, "Amin Kaka, cikin murya Bacci
Maryam tace, "Ya Maleek Saida safe, Murmushi kawai ya sakan mata, sannan ya fice daga gidan, Kaka ta
rufe gida, tadan yin kakkace kakkacen sanan suka wuce ɗakin, Suka kwanta, Nan take Bacci mai daɗi ya
dauƙe su,
★★★
Yana barin gidan kai tsaye ya nufi ɗan ƙaramin ɗakinsa irin na samari, ya watsa ruwa yaji wani irin iska
mai daɗi na shiga jikinsa, a hankali ya zauna saman katifarshi, karatu ya soma yi da ɗan rubuce rubuce
bayan, yana gamawa ya fara karatun Alkur'ani na ɗan wani lokaci, Addu'a yayi sannan ya kwanta nan take
bacci mai ɗaɗin gaske ya yi a won gaba shi cike da mafarkai masu ɗumbi da ɗi da rudarwa,
★★★
Washe gari Tunda Assuba ya farka Alwalla ya yi ya wuce Masallaci, bayan ya dawo ya yi karatun
Alkur'ani sannan ya yi Wonka ya shirya, ya gyara ɗakinsa tsab kana fice daga gidan kai tsaye ya nufi gidan
kaka....
"Maryam tashi kiyi Sallah karki bani na same a wajen, ko motsi batayi ba, "Wai ba magana nake ba, a
hankali ta Buɗe Idanuwanta ta sauke su kan Kaka dake zaune a tsakiyar ɗakin, "Ga ruwan Zafi can cikin
bokiti saura kuka ki tsaya shirita ta, A hankali ta fice daga ɗakin, tana gama Wonka ta fito a tsiyar gida ta
duƙa tana Alwalla a hankali ta janye hular kanta nan take gashin ta dake kwance har gadon baya ya
bayyana baƙi wul da shi sai sheƙi yake, tana kammala Alwalla ta wuce cikin ɗaki Kaka na Zaune tana juya
mata Shayi ɗon yayi sanyi, bayan ta shirya ta saka Unifrom farar riga da Blue wondo sai hijabi fari ɗan ma
dai daici sosai Unifrom ɗin sukayi mata kyau sun zauna Das a jikinta," Ta yi Sallah, a tsanake ta soma shan
shayin , dai dai lokacin ya shigo gidan," Kaka Ina kwana"? "Abdul Maleek lafiya lau shigo Mana,a hankali
ya shigo ɗakin ya zauna, "Ya Maleek ina kwana"? "Lafiya lau"
"Ga Naka Abdul Maleek, "Nagode Kaka a tsanake ya soma cin abinci, lokaci ɗaya suka Kammala,"
Tashi mu tafi karmu makara, a hankali ta miƙe tare da ɗaukar jakar Makarantar ta, "Kaka zamu tafi, "Allah
ya kiyaye Abdul Maleek Allah ya bada Sa'a, "Amin Sannan suka fice daga gidan, Tafiya suke a natse yana
riƙe da hannunta Suna hira gwanin burgewa har suka iso makaranta," Toh ni zan tafiya kiyi karatu Kinji,
"Toh Yaya me zaka seya min? ta ƙarasa maganar tana Murmushi, "duk abinda kike so, "Kasiyi irin na jiya,
"Shikenan kiyi sauri karki makara, yana tsaye a wajen yana kallon harta shige Ajinsu, A hankali ya sauƙe
Ajiyar zuciya, dai dai lokacin mai mashi ya aje wani Malami, "Malam tafiya ne "? Wacer ɗan Ajaɓa, "Ehh
kasuwa zaka Kaini, "muje" yana hawa suka wuce,
Suna isowa ya sallami mai mai Mashin ya wuce shago, "Oga ina kwana, "Lafiya lau Maleek" Nan
ya shiga gaida mutan dake kewaye da shagon Abokan Ogan shi, yana shiga shagon ya fara kakkance
Kakkance tare da fitar da Abu marar Amfani bayan ya gama ya share Shagon har zuwa gaban shago ko'ina
tsab, Haka ya suka yini a kasuwa suna hadada da Mutane har zuwa Bayan Isha'i, sannan ya wuce gidan
yauma kamar jiya da gudun Gaske ta iso wajen sa, ya rugumota, "Ya Maleek sannu da zuwa, "Yauwa kina
Lafiya"? "Ya tsaraba na"? "Gashi nan" ya faɗa a ɗan fusace, "Rau rau da ido ganin ya ɓata rai, "Ya Maleek
kayi haƙuri, "ALLAH Idon na sake kiyi Miki magana kika share Ni Bazan ƙara saya Miki wani Abuba,
"Kayi Haƙuri Ya Maleek!!" Kama Hannuta yayi suka wuce cikin gida,
Yauma kamar kullum zaune take a tsakiyar gida suka shiga Yayi Sallama ta Amsa Mishi, "Abdul
Maleek Sannu da zuwa, "Yauwa Kaka ya gida, "Lafiya lau' " Tashi ki ɗauko Mishi Abinci, bayan ya
kammala cikin Abinci sukayi karatu Sannan ya wuce gida,
"Kaka kaman Wayar ki Na Ringing, tashi ki ɗauko tun bata tsinke ba, da sauri ta nufi ɗaƙi lokacin har
kiran ya yenke tana dauƙar wayar wani kira ya sake shigowa, "Abba Abdullahi ne ɗaga wayar tayi, "Abba
Barka da Dare, daga can ɓangaren aka Amsa da "Mamana Kina lafiya? Ina Mama? "Lafiya lau muke Abba,
Abba yaushe zaka kaimu birni nida Kaka, "Abba ka maida mu Birnin tare da Ya Maleek Abba K..... "Ya isa
haka Mamana Ina Mama"? "gata Abba, cikin Sanyi Murya Kaka ta kira sunansa,"Abdullahi Ya gida"? Ya
Iya linka"? "Lafiya lau suke Mama ɗazu da Safe na kira baya zuwa, " Ehh ɗazu sabin din ya ɗauƙe, Dariya
Maryam tayi,"Kaka service Ake cewa ba Sabin ba, duka ta ɗan kai mata tayi sauri kaucewa tana dariya,
"Yauwa Mama gobe zan aiko da Direba ya kawo muku kayan Abinci ina fatan ba wata Matsala, "Ba komai
Abdullahi Nagode sosai Allah ya yi maka Albarka," Amin Mama ki ƙara Haƙuri har yanzu Abubuwan sai
Addu'a Nasara gane mike da mun Kubra, " Ba komi Abdullah Allah dai yayi maka Albarka tare da zuri'ar
ka, " Ya su Nana "Lafiya lau suke, sun ɗan jima suna hira kafin nan sukayi Sallama, Tuni Maryam tayi
Bacci, da kyar Kaka ta kaita ɗaki suka kwanta,
Washe gari yau ta kasance Weekend ne, Zainab na zaune a tsakiyar gida tana Aiki zane zane nenta, sai
faman Murmushi take, "Kaka Kinga na zana Ya Maleek, tayi Maganar tana nuna mara zanen da tayi," Dai
dai lokacin Akayi sallama, "Kaka kaman muryar Direban Abba, "Aiko shine ji kice ya shigo, da sauri ta
nufi wajen gidan," Kaka tace ka shigo, Binta yayi a baya har inda Kaka take zaune, "Mama ina kwana,
"Lafiya lau Atiku ya Hanya"? "Lafiya lau Mama" suna gama gaisawa ya wuce waje ya shigo da kayan
Abinci da yazo dasu, Maryam sai faman tsalle tsalle take tana jin daɗi, "Sannu da aiki Atiku ga ruwa ka
sha ,"ba musu ya ƙarɓa ya sha tare da yi mata Godiya, "Ga wannan nan yace a baki 50k cike da farin ciki ta
karɓi kuɗin tana mishi godiya, sallama ma yayi masu har ƙofar gida suka rakashi, sai lokacin Kaka ta samu
daman kallon kayan, kayan Abinci ne kala kala da duk wani Abin buƙata yau da kullum, sai kayan saka
kusan kala goma ita biyar zainab Biyar sai su sabulaiya da turarukka masu daɗin gaske, "Ya Allah kayi wa
Abdullahi Albarka Allah ka kare a duk inda yake, ta ƙara sa maganar tana share hawayen da suka zubo
mata,"Kaka kukan me kike? Murmushi ƙarfin hali tayi," Ba kuka nake ba Maryama, "Kaka me yasa duk
Abba ya Aiko muna da kaya sai kiyin Kuka"? Nan take ya nayinta ya sauya, ta sauke Nannauyan Ajiyar
zuciya mai zafi....
★★★★
"Ya Maleek Sannu da zuwa, Ya Maleek Abba na Birnin ya aiko muna da kaya, "Kiyin kyau Maryama ta Ya
faɗa a hankali sun kuyar da kai ta yi, "Uhmm Maryama An girma Kunya kike ji"? Murmushi ya sakan mata
da taune Lip ɗin sa na ƙasa ya ɗage mata gira ɗaya da Lumshe idanunsa ya buɗe a kan fuskarta ya danyi
murmushi tare da tsurawa furkarta ido, " Ya Maleek kayan nan Abba ya aiko min su, "sun Miki kyau sosai,
"Nagode, A karon karfo ya saki Murmushi murya. sanyaye ya ce," Maryama ta an girma? Murmushi ta yi ta
ɗan marairaice fuska cike da kula ta ce," Ya Maleek bai kai ne ka ce na rage yin surutu ba"? Suka ha ɗa Ido
a karo na biyu, da ƙarfin zuciya taso janye Idonta Amman bai bata daman hakan ba cike da ƙwarewa ya
Lumshe idanunsa ya buɗe a tsakiyar kwayar idonta, tsabar lamarin yazo mata a bazata tai saurin Janje
idota, wani irin kwarjini ya yi mata....
Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi ya ce ,"Muje gida, a hankali ta sauke Numfashi tare nema duk
kan natsuwar, tana gaba yana biye da ita har suka iso cikin gida, ganin Kaka bata tsakiyar gida suka wuce
ɗaki, ya yi Sallama, ta basu izinin shiga, koda suka shigo tana zaune a saman tallausar carpet ɗakin na fitar
da wani irin fitinannen khamshi mai daɗin gaske,
Cikin sanyi Muryar yace," Ina wuni, "Lafiya lau Kaka, " Zauna mana, a hankali ya zauna tare da
lonƙosa ƙafarshi,ta hagu, kwanukan Abinci dake gefenta ta aje Nishi a gaban sa, "Sannu da Aiki Kaka!"
Murmushi ta sakan mai, "Ya Maleek Ni ba zaka min sannu da aiki ba, tare mukayi girkin, "kwaɓe fusaka
yayi cike da zolaya ya ce,"ke ɗin"?.sai kuma yayi dariya mai sauti, da ce wa, " Maryama an girma!"
hakannen yasa Kaka Murmushi, " Kaci abin cikin ka Abdul Maleek" kwaɓe fusaka Maryam ta yi tana
turo baki gaba tana ce wa," Ai Bazan ƙara ta yaki aiki ba, A hankali ya buɗe kwanon abinci wani irin
khamshi mai daɗi ya daki hanci sa, Wani irin sassanyan Nunfashi ya sauke tare da Lumshe idonsa, "Ya
Rabb" tuwon shimkafa ne da miyar taushe taji nama da kifi, sai man shanu, nan take ɗakin ya gauraye da
ƙamshi, a tsanake ya riƙa cin abinci har ya kammala,
Juyowa ya yi ya watsa mata narkakkun Idanunshi sa da bata iya gano mike cikin su, turo baki tayi
tare da sunkuyar da kai ta murguɗa baki, "Taso muyi karatu, ba musu ta dauko littafanta sukayi karatu
kaman yadda suka saba, "Kaka Nagoge zan wuce gida, "Ji mana Abdul Maleek!" a hankali ya zauna,
"Abdul Maleek ya batun karatunka"? Nunfashi ya ɗan fesar cikin sanyi Murya ya soma faɗin," Kaka kuɗin
ne bai gama kammalawa ba! kaka Makarantar tana da tsada sosai, " Abdul Maleek idon ka biye wa sai
ranar da ka tara kuɗin da zasu isheka ba zaki karatu yanzu ba! Komai a hankali aka farashi, baka san me
Allah zai yi nan gaba ba, yanzu nawa ka tara"? Nannauyan Ajiyar zuciyar ya sauke, " Kaka! dubu Ashirin
ne a hannun yanzu, "Abdul Maleek, kana nufin tsawon lokacin nan da ka dauƙa kana aiki iya abinda ka tara
kenan?, Rau Rau ya yi ido Kaman zaiyi kuka, "A'a Kaka! "Toh ya akayi suka zama 20k"? "daman kwanaki
koda na dawo da shago na tarar da An ɓalle ɗakina! "Subuhalillah" kai ya jingiya cikin ya nayin da muwa
yace," Wallahi Kaka duk kudin da na tara sun kwashe!" Nannauyan Ajiyar zuciyar Kaka ta sauke, "shine
baka gaya min ba"? "Kiyi haƙuri Kaka!", "Allah ya tsare gaba ɓarayi sunyi yawa a unguwar nan, cikin yana
yin Natsuwar sa da ya zame mishi jiki, yace "Haka ne Kaka, Allah ya shirye su! "Amin" " Kayi ƙoƙarin
Abdul Maleek kar shekarar nan ta ƙare baka shiga makaranta ba, In sha Allahu Kaka zanyi ƙoƙarin, "Allah
ya taimaka idon ka tara ra gowar sai na cika ma, "Nagode Kaka cikin yana yin natsuwar sa da ƙasaitarsa
ya kalli inda Maryam take zaune,ya Lumshe ido ya buɗe a kan fuskarta, cikin sanyi Murya ya ce,"Kaka
Saida safe, "Allah ya tashe mu lafiya, "Amin"
Kai tsaye ya nufi ɗakinsa, ya watsa ruwa, a hankali ya fara jin natsuwa na saukar masa, karatun Alkur'ani
ya yi kana ya yi Addu'a ya kwanta nan take bacci ya yi awon gaba dashi, can cikin Bacci ya fara ganin
wani gaske mai bala'i ƙarfi ya kewaye wani ka tafaren wajen, wasu muta ne sanye da Fararen kaya za gaye
da wannan hasken, daga can gefe wasu kyakkyawan ƴan mata ne tsaye ko wacce furkarta ɗauke da
murmushi, ɗaya daga cikin ƴan matan ta soma kiran sunanshi ciki wata irin zazzaƙar Muryar mai cike da
natsuwa," Abdul M.....!" dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa
ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa,
ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar mai ɗumi ya juya gefen hagu ya kwanta ta re da yin Addu'a ya sake
juya hannu izuwa dama ya yi Addu'a...
Sam bacci ya ƙi zuwa sai faman juyi yake cikin wani irin mummunan ya nayin da ke faruwa dashi duk
lokacin da ya yi irin wannan markin da yake duk bayan shekara, karatun Alkur'ani ya riƙa cikin sassanyan
murya mai cike da kasala.. cikin ikon Allah ya samu bacci ya yi awon gaba da shi......✍️✍️✍️
_More comments and share_
*Sadeeya Ka'oje ce*✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬


.Bismillah........ ✍
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
*Page 3-4*

_______ Washe gari , gaba ki ɗaya yinin wannan Rana haka ya yini a kasalance, komai a hankali yake
yinsa, zaune suke a tsakiyar gida, suna hira, Kaka ta kalleshi cikin sanyi Murya ta soma magana,
"Abdul Maleek mike da munka"? cewar Kaka, " sassanyan Nunfashi ya sauke, " Ba komi Kaka, gaji ya
kawai ke da muna, " Ka tattabar ba komi"? A karon farko ya saki Murmushi,"ALLAH Ba komai Kaka!,
"Shikenan, "taso muyi karatu, ya faɗa yana kallon Maryam dake kwance, a hankali ta mike ta nufi daƙi ta
dawo dauke da jakar Makarantar, nan suka soma yin karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, kana ya yi
musu sallama, bayan ta fiyar shi Kaka ta rufe gida kana suka wuce ɗaki suka kwanta,
Washe gari ma haka ya tashi ba wani kuzahari, jikin sa ya musu sosai da mafarki, duk da ba wannan ne
karo na farko da ya fa irin wannan mafarkin, tawon sati guda kenan yana fama da kasala, Kaka tayi
tambatayar duniya ya ki ya faɗa mata,
Bayan Isha'i kamar ko yau she tana tsaye a ƙafar gida, tana jiran da wowar shi, ta ɗau tsawon lokaci
tsaye a ƙofar gida tana jiran da wowar shi, " Maryam wai miki ke a waje"? " Kaka Ya Maleek nake jira!"
Ajiyar zuciya Kaka ta sauke, tare da faɗin Allah ya sa yaron nan lafiya yake? bai taɓa kai irin wannan
lokaci ba, "Allah ka tsare shi a duk inda yake"
Cikin tsananin da muwa Maryam ta shigo gida, " Kaka ya Maleek bai dawo ba har yanzu ta faɗa kaman
Za tayi kuka, Murya na rawa tace" Kaka muje mu nemo shi Kaka!" Bata jira me Kaka zata ce ba ta wuce
ɗakin ta ɗauko jiha bi da fitala, kana suka fice daga gidan hankali a tashe, saboda bai taɓa kar War haka ba,
"Kaka ko zamuje Kasuwa ƙila yana can, Maryam ta faɗa a hankali, "Bana tunanin yana kasuwa wani
lokacin idon Oga ya riƙe shi a kasuwa, yakan kirani da wayar Oganshiya ya sanar dani, " Kaka ƙila ya ƙira
ba Network, "da wuya idon yana Kasuwa, ganin Maryam ta matsa sai sunje kasuwa,hakan ya sa suka wuce
kasuwa, Nan mai shagon ya sanarda su tun bayan Isha'i ya wuce gida, cikin tsananin tashin hankali da dake
tattare dasu, suka baro kasuwar,Nan suka ruƙa neman shi cikin Unguwa,duk sun san baya zuwa gidan
koma ha salima ko aboki Baida idon ka ganshi tare da wani to Maryam ce, " Kaka ko zamuje ɗakin sa"?
cewar Maryam, "Anya wuya yana ɗakinsa, "Kaka muje mu duba, Haka suka ɗunguwa zuwa ɗakinsa, iso
warsu ya yi dai dai sakin wata irin ƙara mai razanarwa, nan take jikin Maryam ya soma
ƙarƙarwa,"“Innalillahi wa innailaihi raji'un!! Abdul Maleek ta kira sunansa a rauna ce, da sauri ta nufi cikin
ɗaƙin, tana kiran Sunanshi" Abdul Maleek! Abdul Maleek!! tsawa tayi cak, tuni Abdul Maleek ya suma
babu a lamar Nunfashi atare dashi, Rungumeshi Kaka tayi tana kiran Sunanshi, cikin tsananin tashin
hankali Kaka ta fashe da Kuka tana kiran Sunanshi....
A Ɓangaren Maryam tuni ta fita haiyacinta,
jikin Kaka sai karkarwa da kyar ta tattaro ƙarfi ta, kana ta janye shi daga jikinta, ta zuba Nishi ruwa, ya
sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya shiga karanto Addu'oi cikin ikon Allah hankalinsa ya fara
dawowa jikinsa, a hankali ya ɗago da idanunsa da suka kaɗan sukayi jazir ya kalli Kaka ya yi ƙasa da
kanshi, Murya a dishace ya ce "Kaka! zasu tafi dani sai kuma ya fashe da Kuka, A razaje Kaka ta ɗago ta
kallesa Zuciyarta na bugawa da ƙarfi idanunta a kansa, "Suwa ye zasu tafi da kai Abdul Maleek!" su tafi da
kai su kaika Ina?"
Kai ya gyaɗa mata cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya fashe da kuka mai tsuma
zuciya, Murya a dishace yace,"Kaka wlh tafiya zasuyi dani Kaka bana son rabuwa daku! "Kaka Ina
Maryama ta!"
Wani sabon Kuka Kaka ta fashe dashi tana girkiza kai" Abdul Maleek ba inda zasu kai ka, Abdul Maleek
sam baya cikin Haiyacinsa sai sabbatu yake,
Maryam dake baƙin ƙofa tana sauraren sabbatu da Abdul Maleek yake, ta durƙu she a wajen ta saki wanin
irin marayan kuka,
Kwallnshi kaka keyi cike da tausayawa ganin yadda ya takure a waje ɗaya yana sabbatu, cikin
raunan'nanyar Murya Abdul Maleek yaci gaba da fadin "Kaka gasu nan zasu tafi dani, Wayyo Allah na!!
nan Kaka ta shiga tafa Nishi Addu'oi, a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya, Nan take jikinsa ya sake, sai
lokacin Maryam

Please Login or Register in order to submit comment