Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bada
murni ya ce ."Tazo".
Da sauri Jidda ɗin ya juyo ya nufoshi,
hannu yasa ya amshi allurar,
kana ya ɗan kalleta a fakaice yace.
"Zo nan".
A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi.
A take kuma bugun zuciyarshin ya fara tsananta Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da
yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta.da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin
da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa.
"Ya Rabb"
A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso,
yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya,
still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai
saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa rumtse
idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, hannunshi yanada masifar zafine,
Da ƙarfi tace.
"Wach Allah na zafi-zaffi."
Wani irin azaba taji lokacin daya fara sakar mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa
hannu damanta ta damƙe hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka
da sauti tace. "Wayyoo Allah na Zafi nake ji, bugun zuciyarsa ko tsananta yake, ya kusan hallakashi lokacin
data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi. Sannan ya miƙe tsaye,
sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje.
Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Jidda ɗin ya fice daga Office ɗin...
da sauri Jidda ta riƙo hannuta suka fice ɗaga Office ɗin. Ta kaita ɗakin ta kwantar da ita nan take bacci ya
yi awon gaba da ita...
Sultan da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai
kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi...
Bacci Sai Sultana ta yi sai ƙarfe Shidda ta farka, ba ɓata lokaci suka wuce gida, har gida Jidda ta kaita, sai
lokaci ta tuna da wayar ashe cikin mota tabarta, Miss Call ɗin Mami da Kaka. Da Abba ba iyaka... lokacin
da suka iso ƙofar gida Sultana ta kalli Jidda ta ce," me yasa zaki kai wajen Ɗan is..... "ya isa Sultana Jidda
ta yi sauri dakatar da ita," to in ba iskanci ba zai sani a gaba yana mun tambayoyi, wannan sam bai dace da
zama likita ba ɗan jarida yafi dace wa dashi... "Kai Nikam me Dr Sultan ya yi Miki kika tsaneshi haka,
karfa ƙiyayyar da kike mai ta kowa so! Wata rana, " Allah Ubangijin ya tsare ni ko shine Autan maza a
duniya Bazan zaɓa Auren sa ba!"
(Ni dai nace Humm😅).
Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar,kana tace,"Allah ya kyauta"
Ƙala Sultana bata ce mata ba ta fice daga motar ta nufi cikin gida...
Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata
zama babu al'wala.
Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga.
Tana kokarin fitowa falo Meena na ƙoƙarin shigowa da sauri Meena ta zaro ido tare da cewa.
"Yaushe kika dawo?".
Hararanta ta ɗanyi tare da cewa.
"Ban sani ba"
Cikin tausayawa Meena tace. "Sorry Anty Sultana
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace. "Ya jikin naki Anty Sultana!"
"Naji sauƙin"
"Na dawo a guje fa, wannan Sultan ɗin hannunsa zafi.
Zaro ido na mamaki Meena tayi tare da cewa.
"Anty Sultana Shida kanshi ya miki?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Cikin taɓe baki tace.
"Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke".
Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Sultana tace.
"Ba doleba Ko don mugutar da ya yi min dole na warke,
Dariya Meena tayi tare da cewa.
"Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai".
Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira. "Wai ina Mami da Kaka, "Barci suke, sai
gab magriba kaka ta farka daga Barci ruwa ta watsa don taji daɗin jikinta...
"Sultana ya jiki"
"Lafiya lau Mami, tun ɗazu na dawo ai. su Khalil basu dawo ba har yanzu, "Mami Kinsan yau hadda
suke sai 8 zasu dawo..."
"Na manta Sam"
A hankali Meena ta wuce ɗaki don yin Sallah, Sultan ta nufin ɗakin Kaka , koda ta shigo tana Sallah zama
tayi tana karanta Askar a wayarta bayan ta kammala ta kunna Data tana chatting da Jidda dake tsokanarta..
Kaka ko bayan ta sallame sallah taci gaba da Addu'oi...har zuwa bayan Isha'i, ƙarfe 8:15 su Khalil suka
dawo a gajiye,bayan sunyi Wonka suka ciki Abinci,kana kowa ya wuce ɗakin sa.....,
Sultan bai samu dawowa gida ba sai bayan magrib...haka kuwa ya shigo gidan rai a hade saboda tsabar
gajia da yayi...driver na shigowa ya samu wuri yayi parking sanan ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya
zagaya ya bude mishi kofa mai Security yazo ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sultan bai iya ce mishi
komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi cikin gida a yayi da fusakarsa zai baka daria sosai...ya
lumshe idanunsa tareda dora kanshi shoulder din Mommy murya can kasa cikin yace"Mummy na gaji ta
shafa kanshi fuskanta daukeda murmushi itama tace,"welcome back son..akwai gajiyan aiki koh"...ya ɗan
tauna lips dinshi kana ya ce "Akwai gajia sosai Mommy.. "ina Salma da Salim?"
"Sunyi Bacci tun ɗazu" je ka watsa ruwa kazo muci Abinci, jiki a mace ya wuce ɗakinsa ya watsa ruwa
ya fito ya shirya cikin lallausar jallabiya yana zuba kamshi, ya fito palon ruwan tea kawai ya sha ya wuce
ɗaki......
Haka Sultana ta kwana ranar cikin takaicin Sultan da jidda da duk ta tattara laifin a kan Jidda da ta kaita
wajen Sultan ɗin, Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi Jiya da yau Abun ya tsaya mata a
rai da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda
jininin tana, Jidda tuni ta kama kanta don ko a Asibiti bata sakar mata fuska ba....
Washegari ya gama shirya kanshi cikin suit kaman ko yaushe ya nufi parlon Mummy don yin breakfast, A
Gurguje ya yi Breakfast ya wuce Office. Cikin ƙanƙanen lokaci ya iso, bayan mintuna 5 Sultana ta iso
kallon motarsa take tanan dalla mata Harara tare da jan tsaki.. kana ta wuce....
A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. cikin ƙanƙanen lokacin Sunan Sultan ya
kaɗe duniya saboda kwarewar Aikinsa. Kowa yasan Dr Sultan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan
aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana idon ma kaga yana
doguwar magana Murmushi to a gida ne, Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar girman kaine bisa ga
ɗaukakar da Allah ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai
aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga
Dr Sultan sam ba haka baneba ko a nan Asbiti ƴan mata da dama sun nuna mai so. Duk yanda matan ke
binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko
family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. yanda yake gudanar da Rayuwarsa Allah ya ɗaukakashi a duniya a
dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da
aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan Allah shine mai komai da kowa.
A ɓangaren Sultana ma sosai ta maida hankali ga Aikin ta...
A dayan ɓangaren kuma Al'ummar musulmai tana faman shirye shiryen Azumin watan Ramadan...yau
Azumi sauran kwana biyu, Daddy tun Azumi saura sati ɗaya yake rabon kayan Azumi da mabuƙata, A
ɓangaren Abba ba'a barshi baya ba....
Washe garin washe gari.
Da daddare watan Ramadan ya bayyana.
Haka yasa dukkan ɗauka cin Musliman duniya suka cika da farin ciki tare da yin niyan ɗaukar azumin
watan Ramadan ɗin, kana kowa yana shirya bukatunsa dan miƙa su ga Ubangiji Mabuwayi...✍️
Ina ma kowa Barka da jumma'a 🥰💖
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗


*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*


https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*The beginning*
*Page 23-24*
_____ Alhamdulillah an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar Allah da yardarsa. Kowanne
musulmi na ƙwarai yana cike da farin cikin shigar wannan wata mai tarin Albarka dake zuwa mana a cikin
watanni goma sha biyu na shekara sau ɗaya kacal ya wuce.
Randa aka kai azumi na goma Daddy ya gama shirya maganar Umrah da sukan kanje duk shekarar,
tafiyar baifi saursa kwana uku ba Kaka ta kwanta Zazzɓi, hakan yasa Mami ta fasa tafiya,
Amsar passport ɗinsu Daddy yayi musu komai su duka,.Haka kawai sai Sultana ta tsinta kanta da rashin
jin ɗokin zuwan, duk da kuwa tana matuƙar son rayuwa a ƙasar saudia saboda karon nan da sultan Za'a tafi.
Ranar Ta samu Kaka a ɓoye ta roƙeta akan ita bazata je ba karon nan, ita batason zuwa batajin daɗin
jikinta. Harara Kaka ta watsa mata tana taɓe baki. Batare da tace mata Uffan ba a zancen ta ɗauke kanta ta
maida ga karatun Alkur'ani da take karatu.
“Kaka dan Allah Sultana ta faɗa cike da shagwaɓar data saba yima Kaka tana kwanciya mata a gefen
kafaɗa.
Ture mata kai Kaka tayi tana faɗin, “ da Allah jacan Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar
Allah ce ma baƙyason zuwa saboda Sultan zaije ko yaya?
Baki Sultana ta sake kumburawa tana faɗin, "Kaka don Allah fa"
Kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan Allah idan kunga juna ke da Sultan ku mutu Ni bansan me yaron
nan ya tare Miki ba, haka ranar naji kina zaginsa don ya yi Miki Allura.
Sultana bata sake tankawaba, dan ita ɗaya tasan damuwar da take ciki.
Washe gari Jirgi su Sultan ya ɗaga tare da su Ihsan, Salma, Salim, Mommy,.
Bayan shan ruwa suna zaune a Palo, Sultana na kwance saman cinyar Kaka Lafiyarki kuwa Sultana? Kina
tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”.Kaka dake zaune a falo tana duba ta faɗa tana kallonta. a hankali ta
kiƙe saune ɗora kanta gefen kafaɗar Kaka ɗin. “Kaka kaina ke ciwo fa yau tunda safe,. Shiru Kaka tai
kawai tana kallon Sultana, dan gaba ɗaya a kwanakin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta.
Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai.
Jin Kaka batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci.
Sun jima a haka, kafin Kakada taji Sultana ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi
take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar
tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Kaka
ɗin.
"Mama lafiya take kuwa?” Abba ya ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Sultana. Ɗago ido Kaka
tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Sultana.
“Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun ya yi yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To
Alhamdulillah, "Abban Haydar har ka foto, Mami ta faɗa lokacin da ta fito daga Kicin tare Meena. "Zanje
gidan Nuraddeen, Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu'ar dawowa lafiya. "Amin
ya amsa ya yi gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin su Arif ba,
" Sunyi bacci tun ɗazu.....
★★★
Yau Azumi 15, yaune Kuma su Sultana zasu wace Umra. Kaka ta Zaunar da ita Kaka tayi tai mata doguwar
nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba
shashanci ba. Tsaf Sultana ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan in sha Allah zata zama mai
himma. Ƙarfe 10:40.jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Ta tafi cike da kewar Kaka da Mami da Jidda..
_____________________
*SAUDI'A*
Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu na sauka.Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan
cika alƙawarin da taima Kaka akan kama kanta. A hankali suka fito. Sanye take cikin Abaya mai masifar
kyau, an ma rigar ado da duwatsu manya da ƙanana, sai veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda
ƙuruciyarta da ƙyawun da Allah ya bata. Farar ƙafar ya haska tana sanye cikin Black ɗin takalmi da yayi
masifar mata ƙyau. Sai ƙaramar jakarta itama dai Black ɗince. Kallon agogon dake ɗaure a hannunta tai
lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai
dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Sultan dake tsaye jikin mota sanye
cikin Jallabiya ta masa ƙyau.sosai, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba,
Sultan da ya yunƙuro saboda hango Daddy dake a gabansu da yayi yaja ya tsaya cak lokacin da
idanunsa suka sauka akan Sultana ƙirjinsa ya yi matsifar bugawa , ya kasa motsi balle ɗauke ido daga
kallonta har suka ƙaraso inda yake. Abba ko sai kallo su yake,"sultan ya ibada ya Abba ya faɗa tare da
kallon sultan ɗin. sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya,ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Sultana da ta ɗauke
kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. "Alhamdulillahi Abba da ƙyar ya janye Idanunsa
daga kallon Sultana. "Daddy sannu da zuwa, "Yauwa my Boy, Meena ta nufi wajen Sultan ta rungumesa
tare da faɗin,"Ya Sultan ya ibada?, "Alhamdulillahi Aminatu!" wani irin tsam take ji a jikinta duk lokacin
da ya kira ta da sunan, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa rugumersu Haydar, kana suka shiga Mota,
Sultan kam rabin hankalin na'a tuƙi ne rabi akan Sultana da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa
ba. A haka suka iso gidan nasu a mai ƙyau da tsari da Daddy ya saya musu Saboda Aikin Ummra da yake
zuwa duk shekara. Sai da ya Parking motar inda ta dace kafin su fita shi da Haydar ya buɗe musu Mota
suka fito, Sultana a kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan ta yi da duk shekara suka sai sun tarar
da An sabun tasa, zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Sultan, duk yanda tai tunanin zata daure sai
ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin
fiskewar.
dai dai lokacin kuma su Salma da Salim, suka iso wajen A guje tare da Rungume Sultana,"Anty Sultana
oyoyo, suka faɗa tare cike da tsantsan farin ciki, "Anty Sultana I miss You!
"Miss you too my baby's ta faɗa tare da shafa kumatun su, kana suka nufi wajen Abba,"Abba ina Mami da
Kaka? Me yasa basu zo ba?, "Salma kaka ce ba lafiya shiyassa basu zoba"
Marairaice fuska Salma ta yi tare da faɗin,"Allah ya bata lafiya Abba"
"Amin Ummul Salma!"
Ƙirjin Sultan ne ya yi matsifar bugawa.cikin wani irin yanayi ya lumshe idanusa kana ya buɗe akan
fusakar Salma yana mai jin tsakanin Sonta a ransa.
"Ya Haydar, Ya Khalil Ya Arif ya Hanya?"
"Lafiya lau little Sis, Sunan da Sultan ke kiran wani lokacin..
Daddy ko kallon yayan nasa yake cike da so da kyauna...
Sultan ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, cewar Daddy ya yi musu jagora shine mai gida suko baƙi ne
Sultana ita ce ƙarshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga daga bugun
zuciyar da takeji..
Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. cikin tsananin farin ciki
Mommy ta musu sannu da zuwa, "Oyoyo Anty Sultana. Karan farko Sultana ta saki wani lallausan
murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Mommy, a
hankali Sultana ta janye jikin, ,"Anty Yara ya jikin Mama!"
"Alhamdulillahi Mommy taji sauƙi sosai,
Gabaki ɗan su suka Rungume Mommy, "Arif Autan Abba ina Mami," Arif ya yi Murmushi kana
yace ,"Lafiya lau take Mommy, Mommy ta maida kallon ta ga Ihsan kana tace,"Ihsan kai musu kayan su
ɗaƙi," Mommy Nidai a ɗakin ki zan zauna Nana ta faɗa cike da shagoɓa,"TOH shike nan..," Mommy Nima
a ɗakinki zan zauna, taso ki koma ɗakin Ihsan, Kafinma Mommy ta rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan
zauna anan tare da ke Mommy.
da ga Mommy har Daddy kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Mommy
tace dole sai taje. Abba Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa.
Murmusawa Mommy tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Sultana komai.
Sultan Kafeta yayida idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa..
Har ɗaki Mommy ta wuce da Sultana. Kana ta dawo Palo, Daddy ya kalleta cike da zolaya yace ," Kinga ya
yanki kin manta da ni ko?"
Kai ta sunkuyar cike da kunya Sultan dake zaune a Palon, tuni su Meena sun wuce ɗaki tare da Ihsan..
"Ya hanya?" Mommy ta faɗa cikin girmamawa. "Alhamdulillahi"
"Bari muyi sallah ko, "Toh sannan suka fice atare kai tsaye masallacin suka nufa cike da nutsuwa da
kuma kamala suka gabatar da Sallah da karatun Alkur'an..
Bayan sallah la'asar suka wuce Kicin don haka kayan buɗe baki.Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk
aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba. Cikin ikon Allah shida da Rebi suka gama kan
aikinsu.
Sultana , ta jerasu a Foodflaks, Nan duk suka wuce ɗaki.
Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu su Daddy,Koda aka kira sallah
ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallah magriba ,tare suka shigo gida, Ihsan ta
kalli Sultan da gaba ɗaya hankalinsa akan Sultana yake. Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe
tace, “Ya Sultan Barka da shan ruwa Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. "Lafiya"
Nan suka shiga gaida iyayen nasu.
Dai dai lokacin kuma Massage ya shigo a wayar Sultana, a hankali ta ɗaga wayar ta karanta massage ɗin,
*Barka da shan ruwa Sweetheart, Allah ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS*
taɓe baki tayi a hankali tace ɗan
wahala kayi ka kagama, Cikin sanyi Murya Meena ta ce ,"Nas ne halam? Kai ta ɗaga mata....
A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci komai. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka
suka wuce massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci...
Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar
watan Ramadan ɗin.
A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna suka ci gaba da shuɗewa da kaɗan-kaɗan.
Yau wunin azumi na 20 kenan. Da safe duk su Daddy sun wuce masallaci wajen tabsir, Sultan Ya dawo
daga sallar Azahar ya shiga gida sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin
ƙaran sokali . Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da daffen kwai. Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta
ɗauke da sokali totse da abinci.
Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin
yadda ta ke cin uban abincin nan da gani Zaiyi taji sosai ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan.
dai dai lokacin Kuma Meena ta shigo Palon riƙe da wayar Sultana,"Anty Sultana Jidda ta kira Video call,"
Ya Sultan Sannu da zuwa , " Lafiya lau ya bata amsa fuska a sake, a hankali mike tare da barin Palon,
"Anty Sultana kiran zai katse fa, "idon na kammala zan kirata, haka ko akayi bayan ta kammala ta kirata
bayan sun gaisa daga can ɓangaren Jidda tace,"Daughter wlh Asbitin nan ba daɗi Dr Sultan baya nan ke ma
baki nan duk dai Dr Aryan na iya ƙoƙarinsa da Dr Nasir! Gaban Sultan ne ya yi mugun tsinkewa," Nasir
kuma? "Daughter Lafiya kin san shi Hlm?" A'a ta faɗa da ɗan sauri. "Sabon Dr ne bayan ta fiyar ku da
kwana biyu ya fara aiki a Asbitin nan.." Toh"
daga suka ci gaba da hira, sun jima suna waya. Bayan sunyi sallama Sultana ta kira Mami Video call bayan
sun gaida Mami ta miƙa ma Kaka wayar suka ci gaba da hiya cike da kewar Juna....
Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Meena da Sultana
Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai.
Kafin shida ta cikama sun gama komai...
Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari.
A wurin al'ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta.
Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur.
A kwana a tashi Babu wahala wajen Allah , dan gashi yau saura kwana biyu kacal sallah, kowanne yanki
na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan
Yayinda su Sultana keta shirin dawowa suma a ranar sallah.
Bayan Isha'i tana zauna a palon tana waya da Jidda Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta.
Tana ba Jidda Labarin NAS dake Turo mata massage duk safiyar Allah..
A haka bacci yayi awon gaba da ita.
Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta.
Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace.
"Ba Aiki sai kallo da bacci".
Jin haka yasa ta gyara kwanciyar tare da murguɗa baki.
Shi kuma tuni ya wuce ɗikinsa...
Can kuma ta miƙa ta nufi ɗaki ta ɗan kwanta kafin lokaci sallah tuhajju tayi....
Washegari Mommy ta tamusu ƙunshi jan lalle irin na larabawa..
Washegari haka suka niyi suna aiki tuƙuru ..
Washe gari aka tashi da azumi na talatin. Allah cikin ikonshi aka kaishi lafiya.Watan Shawwal ya baiyana
Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana,
Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi.A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku
sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim.
Sultan ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya
ga ya wulgawa a idonshisa. Zuciyarsa tayi mugun buguwa da ƙarfin gaske. A hankali ya dai dai ta
natsuwarsa kana ya ci gaba da ɗawafi
Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu.
Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi.
Zuciyarshi nike da mamaki.Haka yaci gaba da ɗawafin.Saida sukayi. Kana suka wuce gida gabaki ɗayan
su.
Washe gari da safiya.Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.Manya da yara
duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya.
A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.ko waccesu sanye cikin Aba mai matsifar kyau,
Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo.
Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi
gefen maza. Lokaci da aka kammala salla sosai Sultan ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin
amman ina..
(Shiko wannan waye?)
Kai tsaye suka wuce gida, suka ci Abinci cikin kwanciyar hankali, "Kuyi sauri mu kammala ƙarfe 1:30
jirginmu zai ɗaga, cewar Daddy. Dai dai lokacin muka massage ya shigo a wayar Sultana..
*Aminci Allah ya tabbata a gareki yake farin ciki raina! Ina fatan kinyi Salla lafiya, Allah ya mai mai ta
Muna, Allah kuma ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS!!.*
A karon farko Sultana ta saki Murmushi lokacin da ta kammala karanta saƙon, a karo na farko ta maida mai
da Amsa.
*Amin Na gode!*
(Haba Sultana daga ganin Sarkin fawa sai miya tai daɗi😉,)
Nan suka soma shiri.karfe ɗaya dai dai suka wuce Airport..Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar
Nigeria wanda zai sauƙa a kano.A hankali ya zauna. Ya Meena na gefenshi. Riƙe da hannunsa
Kasan cewar yana kusa da

Please Login or Register in order to submit comment