Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari tunda safe Abba ya wuce Asbiti tare da Breakfast ɗin su, Alhamdulillahi koda ya shiko ɗaki
jikinta da sauƙi sosai, Office ɗin Dr ya wuce, bai jima ba ya dawo. ya maida hankali ga Sultana da Kaka
take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta
cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan
kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.
Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan Allah a'a banaso”.
"To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har
yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai"
Kanta ta sake jinjina masa. kaka da batace musu komaiba taci gaba da bata Abinci Batafi spoon huɗu ba
su tace ta ƙoshi, kwanan Sultana Huɗu a Asbitin aka sallamesu... Alhamdulillah jikinta yayi ƙyau sosai, sai
dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu
a cikin tsananin damuwa. a ɓangaren Sultana sam bata son mike faruwa ba,
Lokacin da suka dawo Mami ta taimaka mata tayi Wonka, saboda Kaka ma na bukatar Hutu, taci abinci da
magungunanta ta kwanta danta huta. Sosai Sultana ta yi barci Kiran sallar magriba ne ya saka Mami
shigone ɗakin Sultana ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata
tayi tai alwala,
Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan ta ɗauƙi
wayarta, miss call ɗin Nas ne da massages ɗin sa ba adadi, Sultana ta sauƙe Sassanyan Nunfashi, a hankali
ta riƙa bin massages ɗin tana karantawa.
"Anty Sultana ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi Meena"
"Nas ya yi takira lokacin da kike Asbiti, Anty jidda ma ta kira ba adadi.
"Allah sarki My Mommy nayi kewarta Sosai, bayan sun gama waya da Nas ta kira Jidda sun jima suna
waya..
____________★★★★
A ɓangaren Sultana kuwa tunda daga ranan da Abba yayi mata maganar aure ta watsar da maganar
kasancewar Kaka da Mami ma basu sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa
bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Kaka ko kullum cikin ya mata Addu'a take Sultan
al'khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al'khairi idan kuma ba al'khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi
al'khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al'khairi....
A ɓangaren Sultana kam Soyayyarsu suke Sha hankali kwance ita da Nas...
Tsawon sati biyu kenan da zuwan Sultan wajen Sultana, tun lokacin ko bai sake sakata a ido ba, ka a
Asbitin ba sake haɗuwa ba.. Sultana duk wata hanya da zata haɗa ta Sultan ta daƙileta...
A hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, yau sati ɗaya kenan da akayi sallah layya, haka suka gudanar
da bukin sallar su cikin kwanciyar hankali.
Ƙarfe Shidda suka tashi daga aiki, lokacin da suka fito jidda ta nufi Motarta ta wuce gida, Sultana ta nufi
motar,ta tada motar taƙi tashi kusan minti 20 tana abu guda gabaki ɗaya a gajiye ta, wayar Abba ta kira ta
sanar dashi, daga can ɓangaren Abba yace mata baya gida, Su Haydar ma basu dawo ba ga hadari kuma
gari har yasoma duhu mamana nasan Abin hawa zai Miki wahala, bari naki Sultan idon bai wuce ba ya
dawo dake gida, gaban Sultana ne yayi Masifar tsinkewa tana ƙoƙarin magana Abba ya kashe wayar, a
hankali ta ɗaga kanta ta kalli sama hadari ta ko'ina yana batun haɗewa,
A ɓangaren Sultan ko yana ƙoƙarin barin Office kiran Abba ya shigo, Cikin girmamawa ya gaida Abba,"
Yauwa Sultan ƙanwarkace motar ta taƙi tashi shine nake son ka maida da gida...Shiru Sultan yayi tun
lokacin da Abba ta ambaci sunan Sultana ya nemi nutsuwarsa ya rasa sam baya.
Son wata alaƙar da zai haɗa sa da ita..Jin yayi shiru Abba yace ,"Kana jina Sultan?"
da sauri ya ce ,"Ehh Abba"
"Yauwa na gode".
"Ba komi Abba"
A hankali ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya nufi farfajiyar Asibiti,
A natse ya nufi matarsa ya shiga
Cak Sultana ta tsaya ganin motar Sultana tafe nanda nan ta nemi natsuwar ta ta rasa
A hankali ya yi parking kusa da ita, buɗe bayan mota tayi ta shiga. lumshe idanu Sultan yayi ba tare da
yaja motar ba. Sun kai kusan minti huɗuahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai, har a
fara iska da ƙarfi, ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Sultana ta ɗago Idanunta ta kalli madubin
cikin motar, idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna.
Cikin sanyi Muryar da bai san yana da ita ba,"Halam Ni direban ki ne ?"
Jikinta har yarawa yake ta fito , gaban motar ta buɗe ta shiga dai-dai lokaci Ka ɓarke da ruwa kamar
da bakin ƙorya, Suka.fice a guje .Tunda suka shiga motar babu wanda yace da ɗan Uwansa komai kowa da
irin tunanin da yake Aransa kana ga abin hawa da suke giftawa da ɗan gudu kasancewar maghariba ta
gabato gashi har yanzu ana tsula ruwa...
jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa.
Suna cikin tafiyar aka wani walƙiya mai masifar haske ,
Atsorace tace.“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.Ta gefen ido ya kalleta Sultan ya Kalleta.
Gudu Sultan yake sosai, Sultana ko duk ta tsorace,cikin Suɓutar halshe tace "Don ka rage gudu bana so!!"
Ƙala Sultan baice mata ba.
Ƙawar da kai gefe Sultana tayi tare da watsa masa Harara kana ta murguɗa baki, A hankali tace ,"Mugu
kawai"
Cikin Wata irin murya yace.
"Idan kika sake tura min bakin nan, zan tsikeshi🤣" haka dai sukaci gaba da tafiya
Suka cikin tafiya aka saki wata irin tsawa mai firgitarwa Cikin wani irin tsananin tsoro Sultana ta saki ƙara
mai razanarwa tare da faɗawa jikin Sultan ta mishi wata irin Runguma
Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin
taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta ƙamƙamesa, ta kife kanta
afaffaɗan ƙirjinsa, .
Wani irin masifaffen tsuma jikin Sultana keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya
sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.cikin
wani irin yanayi ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi,
Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta.
Lokacin da aka kuma sakin wani irin tsawa,
Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi , Sultan wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin
Nannauyan Numfashi.
Sultana numfashi ta shiga saukewa akai-akai tare da sake manna kanta ajikin damtsen hannunsa.
Ahankali ya juya ya kalli yanda rabin jikinta ke kansa cikin wata Sanyayyar murya, "Sultana!! Wannan
shine karo na biyu arayuwarsa da ya taɓa kiran sunanta,"Sultana!! ƙara lafewa tayi a jikinsa, tana shaƙar
dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi,
Buɗe idanunsa yayi da kyar murya a sanyaye ya ce, "sauka a jikina!".
Cike da tsoro da kuma sanyin jiki ta janye jikinta daga garesa kana ta sauƙe ajiyar zuciya...
"Nidai tsoro nake ji, kayi sauri ka maidani gidan mu"
Harara ya watsa mata kana ya cigaba da Driving ɗin sa batare daya tanka taba yana isa ƙofar gidansu yayi
Parking cikin sauri ta buɗe motar ta fita da gudun Gaske, kai tsaye ya wuce gida saboda har yanzu ruwan
basu ɗauke ba ....jiki a mace.. Sultan ya wuce gida....
________★★★★
Bayan sati ɗaya, suna zaune a palon Abba ya killi Kaka cikin sanyin Murya yace ," Mama ya batun
maganar Auren Sultana naji shuru, gashi Nuraddeen kullum sai ya yi min maganar, Kaka ta sauke Ajiyar
zuciya kana tace ,"Nima maganar ta tsaya min rai, Saida kuma matsalar da Sultana ɗin ke mafa dashi, ya
kama abita cikin lalama," Haka ne Mama!" Saboda matsalar yasa nake goyen baya ta Aure Sultan shine zai
zame mata jigo a rayuwarta kasan cewar Likita! "Wannan gaskiya ne.
Suna tsaka da Magana Sultana ya shigo Palon, "Mamana zonan" a hankali Sultana ta nufi wajen su ta
zauna, Abba ya fesar da Numfashi mai ɗumi .
Palon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga Abba yafara nasiha, sannan yaɗora da faɗ'in wannan zama
yashafi ki Sultana, Batun Auren kine da Sultan ina maganar ta kwana ?"
Cikin raunan'nanyar murya tace ,"Abba wlh banza Aurenshi ba! Abba wlh ɗan isk.....Abba ya yi sauri
ɗakarta da ita ta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya Sultana ta yi. "Abba wlh bana sonsa Abba ina da
wanda nake so!!!
ABBA ya dubeta rai Ɓace, waye ne zaɓin baki? Kuma yasa baki taɓa gabatar da shi ba ?"Kintaɓa yi masa
magana? Wanene zaɓin naki? Kin taɓa sanar dani kinada wadda ki keso ne?
Kai ya Sultana a ƙ'asa tana sauke numfashi da k'yar, saboda damuwar datake ciki, gawani Abu dayazo ya
tokare mata mak'oshi saboda tashin hankalin, ta girkiza kai
Shiru yayi bata komaiba.cewa ƙanana.
Wannan ya k'ara hasala Abba, ya ce Sultana kabud'e baki kayi magana ta ɗ'ago idanunta jajur
tazubasu kan Abba,
Babu wanda ya lura da halinda yake ciki . Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya
sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta ana zubama ta ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma
ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.
Kaka ta aza Hannu saman kai tana faɗin ,"Shike nan ta mutu!!!"✍️
(Nima na aje biyo ina hawaye )😥
Yanzu Aka soma wasan kudai ku zance da Sadeeya Ka'oje don jin ya zata kaya!!!.
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce ✍️*
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗

*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 33-34*
_______Hankali a tashe suka wuce da ita Asbiti, An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Sultana take
ciki.
yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Sultana hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma
sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al'amarin
ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har huɗu sun ƙaru bayan na farko. Sai faman yin
ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu...."
Cikin ƙarfin hali Abba ya dubi Dr yana faɗin, "don idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar
mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku".
Dr Sadiq ne ya tada kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa Ranka ya dade, ba muna ɓoye
muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha Allahu zakuji komai nanda ƴan
mintuna kaɗan" Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen
Dr Sadiq ba.
Kaka dake zaune a hankali ya jingina jikin kujera ta lumshe.ta faɗa duniya tunani.
Tun da suka iso Asbitin har zuwa yanzun zuciyarta a ruɗani take. Motsin da taji a kusa da ita ne ya
sakasa ta buɗe idanunta da ƙyar.Abba ne ta gani tsaye. "Mama muje gida ki huta ko" Duk da halin da
take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yayi magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun
jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ta Zaunar da
shi.
"Abdullahi inaji a jikina karon nan mutuwa Sultana Zatayi , a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar
wannan al'amarinba!!" Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba
ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe kanta
dake mugun sarawa.
Haka sukaita hawaye har sai da baba Abba ya fahimci Kaka na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa
yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi
da iya ƙarfinsa. Mami ta ƙara so wajen su da saurin tare da rungume Kaka tana kiran Sunanta.... da saurin
Abba ya kira Dr suka duba kaka Allurar Bacci akayi mata kana nan take bacci ya yi Awon gaba da ita....
Wuraren 12:40am Doctors ya buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. suka shiga office ɗin, aka bar Kaka
kawai a ɗakin.
Dr Halima ta ɗanyi gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata
alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku
damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya
yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi
ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a
samu mafita. Muna Bukatar Babban likita da zai dubata, matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin
hankalin musamman da ya kasance yana Aiki a Asbitin kansa dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji
ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira ɗaya daga cikin ya ransa yanzu
haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan
bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar
tata dan shima babban likita ne”.
Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “Allah yasa a dace” tare da musu godiya
sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a
cikin ransa...
Mami ta kalli Abba Murya a raunace tace ,"Abban Haydar bazu kaita Asbiti n Sultan ba inaga haka zaifi"
Murya a disashe Abba ya ce, saidai mu bari mu ga yadda hali Zaiyi!!"
wasa Wasa har gari ya waye amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin
basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani
lokaci. lokacin sallar Azzuhur ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake
fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace ,"Abba Haydar ya kamata Mama ta koma gida ta huta tana
buƙatar hutu sosai, Abba ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace," Na kira Haydar yazo ya kaita gida,
yana rufe bakinsa Haydar na isowa, fuskarsa cike da damuwa ya gaida iyayen nasa,da kyar Abba da Mami
suka shawo kan Kaka ta yadda suka wuce gida.... Bayan ta fiyarsu lokacin ɗaya Abba da Mami suka sauƙe
Nannauyan Ajiyar zuciya, haka suka shafe tsawon Awa ɗaya zaune a wajen ba wani labari....
"Abban Haydar da zaman jiran tsammanin nan da muke da mun wuce Asbitin Sultan tunda duk private
hospital ne. "Ina ga haka za'ayi tashi mu tafi" Abba na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor Halima, sai
kuma ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta ɗauke da murmushi.
Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya
fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo wajen su...
Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka
iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Sultana da ke a hannunsa yana dubawa. ga wani irin ƙwarjininsa da
cikar haiba, Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Black color,
Dr Aryan na gefensa Doctor Halima na daga gefen damarsa, da alama bayani take masa akan matsalar.
Sai Nurse Yusra dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Nasir da wasu likitoci biyu da Nurse guda
biyu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abba bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa
a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Sultana ke ciki suka ja birki, su Abba da duk suka zuba
nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin
hankalinsa nakan file ɗin...... Daga shi sai Dr Halima da Dr Aryan suka shiga .
A hankali ya ƙarasa gab da gadon da Sultana take kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta,
bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo
kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin bugawa zuciyarsa tayi ba da
sauri ya janye Glass ɗin idonsa ya ƙare mata kallo. da sauri ya maida
na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na karkarwa har gadon kansa
na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi
Doctor Halima a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman
shima matakin ƙarshe, A Rayuwarta 😥
(Allah ya baki lafiya Sultana)😥
Cikin ɗauriya yace ," Su waye suka kawo ta?" duk suna waje,
Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Sultana, sai kuma yayi saurin ɗauke kansa batare da nasan
dalilin yin hakan ba. Juyawa yayi zai fita. Doctor Halima tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye suka fita....
Kai tsaye ya wuce Babban Office ɗin ta aka tanada saboda manya baƙin lokitoci ake gaiyata aiki... komai
tsab yake, dan tunda Dr Halima ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama
ƙa'ida kullum sai an share an goge. Gudun a girshe su... A hankali ya zauna sannan ya kunna Computer ɗin
da ke a gaban sa . Yanda yayi matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a
ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Halima ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, Batare
da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin Aiki yanzun,
dan haka ku shiryata zuwa theatre room”. Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan
mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice...
Cikin girmamawa ta ƙarasa wajen su Abba Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu
nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”.
Cike da jin daɗi suka shiga faɗin "Alhamdulillah Allah mun gode maka!!"
Da ga haka ta buƙaci magana da Abba Babu musu ya bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu
da Dr Sultan ya sanar mata, jikin Abba bar karkarwa yake ya ƙarɓi file ɗin ya saka hannu.....
Bayan Abba saka hannun da Dr Sultan da wasu likitocin biyu sai Dr Halima ta uku suka shiga theatre
room da Sultana da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata....
(Dr Sulta Allah yasa ayi aikin cikin nasara!!!💔🤲
Tsawon lokaci suka ɗauke a theater room ɗin Sai kusan ƙarfe takwas na dare dai-dai su Sultan suka fito,
duk su Abba suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki? Su Doctor Halima ne kawai suka tsaya musu
bayani, dan Sultan yana ɗakin bai fito ba...
A tare suka shiga faɗin Alhamdulillah Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai
Sultana samu sauƙi ba,
Su Dr Halima da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka
sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Sultana a yanzu, hasalima ba'a
buƙatar kowa a gareta.
Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Sadiq... "Kulsum mu tafi gida ko zuwa
anjima sai Mudawo.... Jiki a mace suka wuce gida ...
______★★★★★★_______
Abba ya kalli Kaka Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa
cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, " an
kammala Aiki cikin Nasara Mama, ki Kwantar da hankali ki!!" inason mu ɗauƙi komai matsayin
jarabawa,
Ƙwallar da suka cika mata idanu haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Allah ya
bata lafiya!!"
“Amen ya rabbi” ya amsa mata shima.
Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa,.
Washe gari tunda safe Sultan ya iso Asbitin ko da yaje ɗakin da Sultana take har yanzu kwance take tana
bacci cikin wani irin yanayi. tsowan mintuna goma Sultan na tsaye yana kallonta... A hankali ya sauke
Nannauyan Ajiyar zuciya kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida...
★★★★★★★
sai Kusan ƙarfe Ukku na rana Sultana ta farfaɗo. Dr Sadiq dake tare da ita dan duty ɗin rans ne da
shi yay saurin kiran Dr Sultan ya sanar dashi,
Cikin ƙanƙanen lokaci ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses
da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin saTunda ya shigo asibitin baiyi magana da
kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa
ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin....
Ɗakin da Sultana ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sadiq da Nurses guda
biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa.
Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sadiq hannun suka
gaisa..
A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kanta
Sultana ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar
saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Sultan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin
idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara
ganesa ba.
Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura
zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, "Wayyooh kaina!’.
Sultan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike
da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka
Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sadiq Sultan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta
ƙasan ido. Yanda duk suka so Sultana ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Sultan ɗin ya sake dawo mata da
komai,
“Live her.” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yayi maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika
umarninsa, amma tausayin Sultana fal ransu. Dr Sadiq ya yi ƙoƙarin riƙo hannun Sultana data riƙe kanta da
shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata.
Sosai mamaki ya kama Nurse's Sultan ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba.
Sai tura tattausan nasa hannun yayi ƙarƙashin kan Sultana da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman
filon.
Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu

Please Login or Register in order to submit comment