Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda
jiragan ƙasar su jihohinsu suke. Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya
gani.
Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasarsu.
A hankali yake jin zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Hannu Meena ya damƙe sosai. Kana ya sauƙe
Nannauyan Ajiyar kana,
Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar
da fuskar dattijon da yake hangowa.
A haka dai suka ɓacewa ganinshi.
Kana jirginsu ya ɗaga zuwa Kano.....
______________
*Najeriya*
Ƙarfe 7:20 jirginsu ya sauƙa, a hankali suka fara fotowa kai tsaye wajen motocin suka nufa, A tsanake suka
fice daga Airport. Mommy da taga a canza hanya zuwa gida ta Kalli Daddy,"Lafiya?"
Kai kwai ya ɗaya mata. Abban tuni sun kama hanya gida..
Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake
da wutar nepa tamkar rana. Dai dai lokacin kuma suka iso wani tantsamem gida mai matsifar kyau.Dogon
building ne mai matukar kyau da tsaruwa...sannan yanada girman sosai kusan part biyu.. Mommy ta saki
baki tana Kallo cike da mamaki, "Abban Sultan ina ne nan?" tayi maganar cike da damuwa,
"Sabon gidan mu ne!"
da sauri Mommy ta ware manyan idanunta ta kalli Daddy,"Sabon gida kuma?"
Kai ya gyada mata,
"Abban Sultan Amman Ai.... Ya isa. Mommy ta sauke sassanyan Nunfashi tare da faɗin,"shike nan,
Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne,
Ƙaton gidane sosai an ƙawatashi da shuke shuken ƴan ƴan itatuwa kala kala ga ƙasansu kuma, wasu tsirran
fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor's Pink da yellow. da wajen shan iska na musamman
mai masifar kyau da ɗaukar hankali.. Salma da Salim ko sai tsalle tsalle suke a farfajiyar gidan, A ɓangaren
Sultan ma sosai gidan ya masa kyau, kai tsaye suka wuce gidan cikin gida
Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da
kayan wuta, komai na ciki farine.
Numfashi Mommy ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa gidan da lukkunan gidan kallo,
(Hmm sabuwar duniya sabuwar rayuwa🥂🙌💃🥰 )
Ɗaki Ukku ne a cikin palon, ɗakin Salma da komai naci pink color ne ya yi Masifar kyau, sai ɗakin dake
liƙe dashi ɗakin Salim komi blue da kayan wasan shi, daga gefe kuma ɗakin Ihsan ne,suka ƙarasa
madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya.
zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. ɗaki ne mai matsifar da tsaruwa komai na cikin ɗafin fari ne ," Masha
Allah shine Abinda Mommy ta furta. Sultan tsab ya ƙare wa ɗakin Kallo dai lokacin kuma idanunsa suka
sauka kan wani makeken hotonsa dake manne yana sanye da Fararen kaya na likitoci da wata na'ura sarkafe
a kafaɗarsa daga kasan hoton An rubuta *DR SULTAN*. a hankali suka fice daga ɗakin kai tsaye suka
haura sama. Nan ma Wani haɗaɗɗen Palo ne da ɗaki Ukku. Ko'ina ya yi Masifar kyau... Sultan ya kalli
Daddy cikin sanyi Murya yace ,"Daddy Allah ya ƙara Azziki mai Albarka, Allah ya ƙarama tsawon rai mai
Albarka!"
"Amin my Boy!"
Sultan ya gargaɗi ƙannen nasa zuwa palon ƙasa.. aiki Mommy kaman jira take su bar wajen, ta wa Daddy
kyakkyawar ruguma tare da manta mishi kiss. A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a tsakiyar
idanunta. Cikin tsantsan farin ciki Mommy tace ,"Na rasa dame zan saka ma Abban Sultan kamin komi A
rayuwa, ka ilimarta dani! Ka ciyar dani! Ka suturtani ka min muhalli! Kamin gata! Abban Sultan, ina
rokon Allah ya saka ma da gidan Aljana, Allah ya jikan iyayenmu Allah ya ƙarama Azziki mai Albarka ina
roƙan Allah ya shayar da kai ruwan Aljana!" ta karasa maganar cikin raunin Murya, a karon farko a
rayuwarta tun zaman da shi ya Amsa da "Amin!"
A hankali ta sake lafewa a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi. Ɗaukar yayi Cak zuwa ɗakinsa
cike da so da kyau da kewar Juna suka faɗa duniyar ma'aurata....
____________
Wannan littafi DR SULTAN na kuɗine, yana ɗaya daga TITAN'S OF TALENT WRITER'S, idan kana
buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana Zaku biya kudinku acikin wannan asusun na banki👇👇
1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652.
Nagode🤗.....
★★★.......
Tunda suka fito daga Airport ɗin kai tsaye suka wuce gida, da mamaki ya Abba ya riƙa kallon gidan sa
daka sauyawa fenti mai kyau, koda suka shiga cikin cikin gidan ko'ina tsab Motorsu na gama tsayawa
Sultana bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Kaka kira. Da sauri
Kaka dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Sultana Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta
tana faɗin, “Kaka, nayi kewarki ”.Kaka dake murmushi tasa hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta
tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Sultana! Yaushe ne
zakiyi hankali kisan kin girma ne?,"Kaka daga dawota har zamu fara faɗa ko
Cike da shagwaɓa ta karasa maganar tare.da saka kanta a kafaɗar Kaka tana faɗin, “Kaka ni indai ina
gabanki Ni ƙaramar yarince, nayi kewarki ne my Happyness. Ina Mami take?”.
"Maraba da yan Saudiya, Mommy ta faɗa cike da farin ciki da gudu Meena, Nana,Khalil Arif Haydar
suka rungumeta," Mami munyi Missing ɗinki," Nima nayi missing ɗinku. Bayan sun janye jijin daga na
Mami suka nufi wajen Kaka tare da rungumeta gabaki ɗayan su,
"Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace,"An dawo lafiya? Allah ya karɓi ibada"
"Amin ya rabbi,mun same ku Lafiya. "Alhamdulillahi"
Kana suka wuce cikin palon tsawa cak da Daddy ya yi hin an sauya komi na palon i zuwa sabo ya kalli
Mami,"Lafiya? "
Mami ta yi Murmushi kana ta ce ," Aikin Abban Sultan ne bayan ta fiyar ku da kwana ɗaya ya Turo
masu aiki komi na gidan nan an sauya shi izu sabo hadda ɗayan ɓangaren na Uncle Ibrahim..sai yanzu
maganar Daddy ta faɗo mai ɗaya taɓa tambatayar yana da ra'ayin sabo gida nan gaba, ya ce mishi a'a ya
fito son gidan nan tunda ba shike dai keda shiba... Waton da wannan damar ya yi amfani ko, ya faɗa a
hankali. Nan suka shiga jagayen gida. Ko'ina Ma sha Allah gwanin burgewa.
tarba ta Musamman suka samu daga wajen Mami, Abinci sunci Saida suka ture, suna zaune a palon suna
hira, Mommy ta kira Mommy tayi mata sannu da zuwa, bayan sun gaida Mommy ta sanar da ita sabon
gidan da suka koma, cikin tsananin Murna ta taya ƴar uwar Tata murna.jin jima suna waya, bayan sun gama
wayar ta kira Daddy shima ta taya shi murna,
Nan Mami ta sanar da Abba da kaka Abinda ke faruwa, suma sosai sukayi Murna, duk da Abba ya sanda
komi Amman bai haya ya nuna tsantsan farin cikisa ba...sun jima a palon suna hira yaushe gamo.
Bayan sallah la'asar suka wuce gidan Mommy banda Sultana da Kaka.... Sai bayan Isha'i suka dawo a
gajiye ko wannensu ya wuce ɗakin sa...
*SULTAN*
Bayan ta fiyar su Mami, ya dawo ɗakinsa ya yi Wonka ya shirya, a hankali ya zauna gefen gado tare da
ɗaukar wayarsa ya kira babban Aminsa, Aziz kusan sati ɗaya kenan yana kiran sa wayar sa a kashe.yanzu
ma a kashe take, cike da takaici ya wulgar da wayar gefe gado kana ya kwanta tare da Lumshe idanunsa
yana mai jin zuciyarsa na mai nauhi da haka bacci ya yi a won gaba shi...Yauma kamar duk shekara da yake
irin wannan Mummunan mafarkin da yake duk bayan shekara hakan ne ya sake faruwa dashi, sai dai na
wannan karon ya sha babban da saura.. wannan Dattijo da yaga A Umura shine ya gani a mafarkinsa tare
da wata kyakkyawar mata yana zauna a ge fensu da wata matsifar budurwa fusakar da lullɓe da farin
mayafi. A hankali yarinƴar ta fara janye matafiya, dai dai kuma wata mata sanye da baƙaƙen kaya ta shigo
ɗakin da matsifar guda Hannuta riƙe da ƙaruwar yuƙa Idanuwanta sunyi Masifar ja, gadan gadan ta tunkari
Sultan tana zazzare idanunta masu matsifar ban tsoro. da ƙarfi ta ɗaga yuƙar zata soka mishi dai dai lokacin
ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga
saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa......✍️✍️
(To wata sabuwa inji yan caca, ni dai nayi nan🏃🤣)
*Assalamu alaikum! Ina matuƙar godiya da Addu'oi ku, da masu kirana, damu min text nagode sosai Allah
ya bar zumunci!! Don Allah kuma a ci gaba da haƙirin reshin samun Update a Kai a kai. Nagode sosai*
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce* 💋
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗


*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 25-26*
_________cikin wani irin yanayi mai tsanani ya miƙe zaune tare da dafe kanshi, yayi bala'in fita
hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yayi wujiga-wujiga da shi, daga ƙarshema ya yanke
jiki ya faɗi.
A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ɗinsa ƙirjinsa
na sake zafafa, dai dai kuma Daddy ya shigo Dakin da niyar ya faɗa mishi ya kamata ya leƙa Asibiti gobe.
da ƙarfi yaja ya tsaya ganin Sultan kwance a ƙasa ga baki ɗaya baya cikin Haiyacinsa ba abinda ya faɗo
masa a rai sai wannan mafarkin da Sultan yake duk shekara, kusan sau Ukku abun na faruwa a gabansa
lokacin idon ya kai masa ziyara a India.
Duk da Daddy yasan da yanayin na Sultan sai hankalinsa ya sake ƙololuwar tashi fiye da da can.
Wannan al'amari na Sultan na bashi tsoro.. Allah shine yasan gaibu game da matsalar Sultan. To a yanzu
gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma.
Daddy ya nufi wajensa da sauri ya ɗora kansa Sultan samar cinƴarsa tare da shafa kanshi Cikin murya mai
cike da lallashi ya kira sunansa ,"Sultan!".Duk da yana jinsa bai motsa ba, da ƙyar ya miƙa Zaune Daddy da
kansa ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda Sultan yake ke
rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama
tana tasiri ga Sultan ɗin.
★★★
Mommy ko jin shuru Daddy ya jima yasa ta biyo bayansa, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga,aiko da
sauri na nufi wajensu ganin Halinda Sultan ɗin yake ciki.Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo
na Sultan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu, matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar
yanda Daddy yayi masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur Cike da Kasala. ya nufi toilet.
Duk binsa da kallo sukai ita da Daddy, "Abban Sultan mike da munsa?"
"Ina tunanin wannan mafarki ya sake yi,
Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Habiby! Anya kuwa bazamu nema masa
magani ba,
Daddy dake kallonta ya ɗanyi Murmushi yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya
amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune Habibaty, Na jima ina tunani akan haka na tabbata akwai wani babban
Al'amari dake tattare da ɗan naki.
Kafin ta samu damar bama Daddy amsa Sultan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun
fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu ya maida ƙifar toilet ya rufe, jingina yayi a jikinta ya lumshe idanu
zuciyarsa na ƙara bugawa.
Daddy ya Kalli Mommy," Kinga tashi mu tafi yaron naki kunyar fitowa haka yake a gaban mu. Badan
Mommy taso hakanba ta yarda suka fita.
A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu
yana sauraren yanda Daddy ke lallaɓa Mommy akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo
daga baya.
Sultan najin sun fita shima ya fito sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda
Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando black mai
taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije lips ɗinsa, A hankali
ya sauke Nannauyan Numfashi, tare da dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauhi."Ya Allah ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Har rige-rigen shigowa ɗakin Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa
da tambayoyin yaya akai? Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu,
Mommy tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Zama Daddy ya yi a gefe
suka saka Sultan ɗin a tsakiya, Daddy ya fara tofa mishi Addu'oi a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya.a
hankali a hankali ya fara samun natsuwa, haka suka ci gaba da zama a ɗakin har Sultan ya yi barci.....
Washegari
A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe
ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda
ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe goma na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da
kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, Wonka ya yi ya sanya jallabiya ya gabatar da
sallar.Assuba
Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da
Ihsan tana haurawa sama.
Ya Sultan ina kwana" Ta faɗa a hankali
" lafiya" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.
Ihsan ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya.
Wajen Daddy ya nufa
my Boy" Dad ya faɗi lokacin da Sultan ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Daddy Daddy ya shafa goshinsa ya ce "Allah ya ma ka albarka"
Sultan ya amsa da Amin
"Ya jikin na ka?"
"I'm fine Daddy"
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin Daddy".
"Mommy Ina kwana"
"Lafiya lau ya ƙarfin jik?"
"Alhamdulillahi Mommy!".
Tare sukayi Breakfast cikin kwanciyar hankali, ranar dai a gida ya yini har dare...
Washegari cikin ikon Allah ya wayi gari da walwala kaman ba shine a ka sha fama da shi da Daddare ba.
Wuraren ƙarfe huɗu ya leƙe Asbiti tarba ta musamman ya samu daga wajen yaran sa, A ɓangaren Aiki
kuma Alhamdulillah komi na tafiya yadda ya dace sai bayan maggariba ya dawo gida..
Bayan Isha'i Sultana na zaune a ɗaki suna chatting da Jidda, kira ya shigo a wayarta. Kiran na gab da
tsinkewa ta ɗaga ba tare da tayi magana ba, daga can ɓangaren ," Assalamu Alaikum ya yi maganar cikin
wata irin zazzaƙar Muryar mai Amo,da sauri Sultana ta mike zaune tare da faɗin ,"Waye?"
My Sweetheart kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka, "nace waye wai?"
"NAS NE!!"
"Sultana haƙiƙa Ƙaunar acikin Zuciyarta tamkar ta bo ne da yuƙa mai ƙarfi ta yishi gogewar warsa Abu ne
mai matukar wahala ina ƙaunar ki! Bani da burin daƙushe Miki farin cikin ki koda na second ɗaya ni ki
ɗauke cewa yanzu ne kika samu mahaɗin Rayuwarki bani da wani a buri a Rayuwa da wuce na hanki cikin
farin ciki!!!"
Jikin Sultana ya yi sanyi, sosai kalamansa suka ratsa Zuciyarta,
A hankali a hankali NAS ya cigaba da kiran Sultana, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta
surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya
ke. Cinkin ƙanƙanen lokaci sai da ya san yadda ya ja hankalin Sultana har tana ɗan kulashi ta dena ma sa
faɗa idan ya kira. A dayan ɓangaren kullum sai ya Turo mata massage na kalaman soyayya masu ratsa
zuciya katin waya ma sai ta ture duk bayan kwana ukku sai ya Turo mata katin 5k...
( Haba Sultana😡😡)
★★★★
Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa. Jim ƙaɗan Ihsan ta shigo ɗakinsa Tana jin ƙaran
ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna
tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan
ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.
Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani
aiki da Dr Nasir ya turo ma sa. Yana dubawa yana kuɓartea ɗin sa a hankali. Ba laifi Nasir yai ƙoƙari, da
alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba,
sai dai da saura tunda dududu sayi Ukku kenan da Nasir ɗin ya fara ma sa aiki kenan.
★★★★
A hankali soyayyar NAS da Sultana ta fara nisa, domin har Meena da Jidda sunsan komi...
Washe gari bayan ta dawo da wajen Aiki, tana ƙoƙarin shiga cikin gida mai gadi ya da katarda ita, "Madam
gashi yamimama bag🛍 mai k'yau, ta amsa tana tafad'in namiye Baba?. "Wannan yaron ne ya sake da
wowa, aiko da sauri Sultana ta nufi wajen tuni ya Ron ya ɓace, kai tsaye ta wuce ɗaki 🎁bud'ewa sukayi,
flower🌹ce tanata k'amshi, sai zobe Azurfa mai masifar kyau da tsada
Sultana tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka taɓa bata wata ukku
dasuka wuce , da ƴar ƙaramar takarda,
*_kenafi ƙauna cikin matan duniya bani da buri sai muyo Auren dake!*
Wannan shine kawai arubuce, Sultana ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?,Kodai ya
NAS ne? Kai anya kuwa?.
Saikuma turare mai masifar k'amshi, Sultana ta shinshina turaren talumshr idonta.
Jitake tabbas tataɓajin wannan k'amshin, amma a ina?.
Shine abin tambayar.
Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta ta aje su anan..
Koda Meena ta shigo ta bata labarin sosai Meena tayi mamaki,"Anty Sultana nifa ina zargin NAS ne ke
turo Miki saƙon nan gaskiya, "Nima Meena nafi zargin Shine!"
"Aiko Anty Sultana kiyi duk yadda Zakiyi ki gano ko waye. Suna cikin managar kiran Nas ya shigo,"
Yauwa Anty Sultana ki nuna mai sauƙonshi ya iso kin gode, Meena ta faɗa a hankali," mai Sultana ta gyaɗa
mata, "Assalamu alaikum ta faɗa cikin sanyi Murya, " daga can ɓangaren Nas ya sauke sassanyan Nunfashi
kana ya ce," Ina fatan saƙo Na ya samu ƙaɓuwa a wajenki?" da sauri Sultana ta waro manyan idanunta
kaman tana a gabansa tace ," daman kaine?" Nas ya saki Murmushi mai sauti, Meena ga baki daya
hankalin ta kan Sultana dake faman sakin Murmushi kaman gonar Auduga.
"Allah ka shammateni Nas!" Ta faɗa cike da shagoɓa, sun jima suna waya cike da zallar Soyayya....

★★★
"Anty Sultana Kinga Abinda nake faɗa Miki ko, "najina ina zargin shine"
Cike zumuɗi Sultana ta kira Jidda ta sanar da ita komi. Sosai Jidda ta taya murya, tun daga wannan lokaci
so da shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin Nas da Sultana....
(Hmmm 🥱🥱)
*Sultan*
Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na Shuit . Ɗauke da briefcase ɗin sa fito.daga ɗakin sa cikin takunsa
na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je
"Morning Ya Sultan" ya amsa tana ma sa murmushi
Shima Salim da ke gefe ya ce " Good morning Ya Sultan"
"Morning" ya faɗa a taƙaice.
Tea ɗin da ke gaban Salma ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko" ina gai da Mommy da Daddy idon sun
fito..
Yana fita ya shiga matar sa kai tsaye ya wuce Office..
A hankali ta nufi kan step ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Sultan ya fito daga wani ɗaki ya nufi ƙasa, a hankali yake take steps din yayinda
hankalinsa baki ɗaya yana kan file dayake kan hannunsa na dama yana duddubuwa da hannun hagunsa,
bisa dukkan alamu.
Abu mai mahimmanci ne yakeye karantawa.
A dai-dai lokacin kuma Sultana ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun sauri
Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.
Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar Jidda
“Daugter sai yanzu?”.
Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe
dake gefen steps ɗin."Dr Sultan na memanki,
Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da tsiwa tace. "Mezan masa?"
“ oh ho miki Tun ɗazu.yake nemanki”
Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.
"Ba inda zanje
"Kaman ya ba inda zaki je?"
Haka taci gaba da haura saman steps ɗin ba tare da tana kallon gabanta ba.
Wanda kuma dai-dai lokacin Sultan ma ya taka step na ƙarshen bazato ba tsammani taji tayi karo da mutu.
Shi ma Sultan ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi file ɗin dake
hannunsa ya subce ya tafi ƙasa ta kardun suka watse gabi ɗaya
Tagal-tagal Sultana tayi baya zata fadi yayin da shikuma Sultan da ƙyar ya tsaida kansa daga faduwar da
zai yi.
lokaci guda ta rumtse idanunta tare da sakin kara.
Sultan cikin hanzari yakai hannu ya riƙota sai alokacin idanunsa suka sauƙa akan fuskarta ita.
Sultana sassayan numfashi ta ssuƙe jin an riƙeta bata faɗiba yasa ta ɗago kan Idanunta ne suka sauƙa akan
fuskar Sultan, lokaci ɗaya zuciyoyin suka buga da masifar ƙarfi, cikin wani irin yanayi Sultana ta yi
ƙoƙarin janye hannuntata rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata , kana tayi baya baya
zata faɗi, ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani Nannauyan Ajiyar zuciyar
Gaba ɗaya ta sadakar,da faɗuwa,
Jidda da tuni ta fara yi musu video da Snapchat tana Murmushi.
Cikin zafin nama ya janyota da ƙarfi hakan yasa ta faɗa jikinsa.
jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wata irin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har
yanzu bata tsira ba.
Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi da saka natsuwa..
Sultan cikin tsoro da wani irin yanayi abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa zuciyarsa yana mai jin
baƙon al'amuri. a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani, ya ware hannunsa tare da rumtse
idanunsa da masifan ƙarfi....✍️
More comments and share
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗


*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*


https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*The beginning*
*Page 27-28*
_____Cikin sauri Sultan ya janye hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar

Please Login or Register in order to submit comment