Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka nufi wajen Maryam, Murya a dishace Maryam tace ," Kaka
da gaske ya Maleek ya yarasu!?"
Jinjina kai Kaka tayi cike da tausayawa cikin raunin Murya tace," Ki Dena kuka Maryam kiyi mishi
Addu'a Kinji!"
Girgiza kai tayi tare da cije lips ɗin ta kana ta runtse idanunta cikin wani irin mummunan yanayi mai wuya
tace. ," kaka shikenan na rasa Ya Maleek! Kaka shikenan Ya Maleek ya tafi ya barni? Wayyo!! Allah ya
Maleek me yasa zaka min haka?" Sai kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, cikin wata irin
raunan'nanyar murya taci gaba da kiran Ya Maleek!! a karo na Barka tai,
Kallonta Kaka tayi cike da tausayawa yanin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kaman zata fasa
ƙirjinta......da sauri ta runtse idanunta da masifar karfi Zuciyarta naci gaba bugawa da ƙarfi....
Mutsu mutsu ta kaman wata zautacciya hawaye Masu bala'in zafi na zubo mata..
"Ya Maleek me yasa ka tafi ka Bar....ni kasa ƙarasa Maganar nan take ta fashe matsanancin kuka a take
Numfashin ya sake ɗauke......
Likitoci suka sake duƙufa a kanta suka shiga bata taimakon gaggawa da kyar da bone suka samu ta
farfaɗo still tana ci.gaba da surutai haka yasa Dr ya yi mata Allurar Bacci nan take bacci wahala yayi a won
gaba ta da ita....
Ajiyar zuciya suka sauke," ɗaya daga cikin nurse ɗin yace halam," Mahaifiyarta ne?" ba wanda ya kulashi ,
Ina ga tunda ta samu Bacci a barta ta huta Insha Allahu idon ta farka zata samu natsuwa,
Jiki a mace suka fice daga dakin ," Abdullahi Ya kamata kaje gida Kodan masuwa gaisuwa," TOH Mama!!"
kana ya wuce tare da Atiku, sai lokacin ya samu damar duba wayar shi Kasan cewar a silent take miss call
ne ba a daɗi koda suka iso gida mu tane cike tam, ɗaya ba yan ɗaya suka riƙa jajanta mishi sai wuraren 10
ya samu damar shiga gida, tuni su Haydar sunyi Bacci koda yaje daƙinsa kwance suke suna Bacci hankalin
kwance.....
Ɗakin sa ya wuce ya watsa ruka ya canza kaya kana ya wuce Asbiti, har yanzu Maryam bata farka ba.
Sosai Kaka tayi Mamakin ganinsa,"Abdullahi Meya dawo da kai? " Mama kona zauna gida ba bacci zanyi
ba!" ga wannan nasan baki ci komi ba!" Kaza ce da Youngaut mai sanyi," Abdullahi ka koma gida kasamu
ka huta, kaji Kaka ta faɗa cikin tausayawa," da kyar Kaka ta shawo kanshi kana ya wuce gida cike da
damuwa, Ranar dai Haka suka kwana a zauna cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya,
A ɓangaren Abdullahi ma haka ya kwana cikin wani irin yanayi na kewar matarshi.....
Kiran farko na Assalatu a kunnen Maryam, a hankali ta fara buɗe idanunta da suyi bala'in hauyi ta sauke su
kan Kaka dake zaune a wajen hannuta rike da tazzabaha idanunta a bushe alamar ko runtsawa bata yiba,
Cikin wata irin raunan'nanyar murya tace ," Kaka!" Kallonta Kaka tayi cikin ƙarfi hali da danne damuwar
ta tace," Na'am Maryam"
ya yinda Zuciyarta ke ci gaba da bugawa da matsifar ƙarfi tace ," Ya Maleek!" cike tausaya Kaka tace ,"
Maryam kiyi haƙuri Kinji" kiyiwa Abdulmalik Addu'a kinji,
Jinjina kai tayi tare da sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, tashi muyi sallah Kinji kiyiwa Abdulmalik
Addu'a!"
tare da taimakon Kaka Maryam tayi Alwalla kana sukayi salla a tare bayan ta sallame sallah ta daga
hannayen ta sama ta soma Addu'a tana Kuka, Kaka ma Hawaye ne taf a Idonta cikin dubara tasa hannuta ta
goge Hawayen.....
Wuraren karfe 8:30 Dr ya shigo, " Masha Allah jikin da sauƙi zaku iya zuwa gida, ƴan rubuce rubuce yayi
kana ya miƙawa Kaka ,"Ga wannan a saya mata maganin zai taima kamata sosai Allah ya bata lafiya,"
Amin likita mun gode," ba komi Mama!"
"Bari na kira Abdullahi Azo a ɗauke mu, nan Kaka ta nemi wayar ta rasa, cikin tsananin tashin ta fara
neman waya a ɗakin ba wata ba madadinta, sai yanzu ta tuna tunda Iya ta kirata ta sanar da ita Amrasuwar
Abdulmalik wayar ta faɗi Ƙasa bata koma binta kanta ba, tana tsaka da tunanin Atiku ya shiga hannusa
dake da Basket mai matsifar kyau, " Mama ina kwana ya mai jiki," Cikin sanyi Murya Kaka tace ," Jiki
Alhamdulillahi har an sallame mu"
Mutafi gida kwai"ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce gida,ƙofar gida cike tab da jama'a, ya yi parking
Abdullahi ya nufi wajen su ," Ina Kwana Mama!"
" Lafiya lau Abdullahi ya ƙarin Ha ƙuri"
" Angode Allah, Mamana ya jiki!" Murya a disashe Maryam tace ," naji sauƙi Abba!" Nan Abokan
Abdullahi suka shiga yiwa Kaka gaisuwa, kana suka wuce gida da gudu su Haydar suka sheƙo tare da
Rungume Kaka da Maryam, Kaka ta kallesu cikin tsananin tausai yaro kenan, mutane ne cike cikin palon
matan Abokan Abdullahi ne sai masu aiki, da ƴan uwan Kubra, cikin girmawa suka gaida kana Haydar yaza
Hannuta suka wuce ɗakin su, nan suka tarar da a kwatin su, Wonka Kaka tayi, bayan ta fito Maryam ta
shiga sosai taji daɗin jikinta koda fito a shirya musu Lafiyanyen Breakfast, Kaka kam ruwan tea kwai tasha,
Maryam haka,
Ranar dai Kaka suka yini har zuwa dare ba wata walwala a tare da su kawo da abinda ke damunsa, bayan
Isha'i kowa ya watse ƴan gida dai aka bari, Abdullahi koda ya shigo yaran duk sunyi Bacci Hadda Maryam
saboda cikin maganinta ta akwai na bacci ciki,
Kaka ce kwai zauna ta saka yaran a gaba tana kallo, " Mama bakiyi bacci ba?" Abdullahi ya faɗa cikin
sanyi Murya," Ajiyar zuciya Kaka ta sauke kana ta kalli Abdullahi, " Banyi ba Abdullahi"ya kamata
kikwanta ki kuhuta," Abdullahi kona kwanta Bazan iya yin Bacci!"
Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, " Mama wannan yaro dake zuwa gidan ki shine ya rasu!?"
"Shine Abdullahi!"
"Baida lafiya halam?"
"Lafiya lau yake jiyama kafin mu ta so tare muke dashi, hatsarin mota sukayi nan Kaka ta shiga bashi
labarin Abdulmalik tun farkon haɗuwarsu"
" Ya Salam! Mama me yasa tun lokacin baki sanar dani ba na ɗauƙi nauhin karatun sa, Kaka ta sauke Ajiyar
zuciya," Abdulmalik ba irin yaran nan ne masu matattar zuciya Abdulmalik yaro ne mai son neman na
kasanta ba yadda banyi dashi akan ya bari na taima ka masa yaƙi!?"
Abdullahi ya fesar da iska mai ɗumi kana yace " Allah ya gafar ta Nishi!"
"Amin ya rabbi"
"Saida safe Mama ya kama ki kwanta"
Bayan tafiyar shi Kaka ta jima zauna kafin nan Bacci yayi a won gaba da ita......
★★★★..........
*BAYAN SATI ƊAYA*
Rayuwa ta juya musu izuwa kunci da baƙin ciki musamman Abdullahi, Kaka Maryam, cikin satin nan daya
sunyi wani irin masiffen ramewa, kallo ɗaya zaka musu kasan kusa cikin tsananin damuwa musamman
maryam gabaƙi ɗaya ta fita cikin Haiyacinta duk ta dawo Shuru Shuru....
Tuni mutane sun watse su Haydar tuni sun fahinci Mahaifiyar su bata cikin gida lokacin da suka matsa
tambaya Abdullahi ya faɗa musu Mahaifiyarsu ta rasu basu wani shiga damuwa saboda yarinya dake
damun su, Haydar ne ma ƴa dan shiga damuwa Kasan cewar ya ɗan fisu wayo, daga baya kuma ya saki jiki
sukaci gaba da wasar su......
★★★★★.....
A hankali ya fara buɗe idanunsa cikin wani irin mummunan yanayi da kyar ya tattaro duk ƙarfin ya miƙe
zaune ya jingina jikin dutse a hankali ya riƙa bin dajin da kallon ko'ina tsit sai kukan tsuntsaye dake tashi,
da sauri ya dafe kanshi dake sarawa da matsifar ƙarfi,ƙoƙarin tashi tsaye yake gabaki ɗaya jikinsa ƙarkarwa
yake, ga wani irin masiffen kishin ruwa da yake ji, cikin wani irin yanayi a fara tafiya yana faɗuwa kaman
yaro mai koyon tafiya daga ƙarshe ya dawo rarraye haka ya riƙa rarrarehe batare da yasan ina yake tafiya
ba a hankali ya fara jin kukan motoci a karon farko ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar ha ya riƙa rarrafe
har ya iso saman titin cikin wani irin yanayi ya kiƙe tsaye yana tal gal tal gal kaman zai faɗi magana yake
son yin ya kasa saboda masifar bushewa da maƙoshin yayi yana tsaye a waje wata mota ta wuce da masifar
guda fuuuuuu. Ƙasan cewar ba ƙarfi a jikin sa wannan isar motar yayi sanadiyar faɗa warshi a' tsakiyar
titi...
Hakan yasa motar dake tafe ta taka burƙi da ƙarfi har motar na bada wani sauti tsuuuuuuu" direban ya
sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, mutumen dake zauna a bayan ya yi sauri safe kanshi yana faɗi" Innalillahi
wa'inna Ilahi rajiu'n!!! kana ya sake Ajiyar zuciya.... Motoci dake bayan su suka tsaya da ƙarfi, wasu kattan
maza kusan guda huɗu suka diro daga cikin motar ko wannen su riƙe da bindiga da sauri suka nufi matar
dake gaba, suka zagaye ta...
"Doga duba ga yaron na yare!" Allah ya ƙarama lafiya mutafi kwai yanzu haka shirin miyagu ne! mutumen
dake zaune bayan motar Ya yi Murmushi kana yace" duk Abinda ya faru da bawawa daga Allah ne! Koda
mugaye ne Allah bazai bari su cutar damu Saboda da kyakkyawar niya muke,
Dogo Direba ya sauke Ajiyar kana yace ," gaskiya ranka ya daɗe hankali bai kwanta ba shiyassa bana son
mota ta ta zama itace gaba,
"Dogo da gaba da baya da tsakiya duk Allah ne ke kare su!" Dogo Direba ya yi Murmushi kana ya buɗe
motar gaban shi na faɗuwa, ɗaya daga cikin security ɗin yabi bayan shin da sauri dogo Direba ya dawo
wajen mota ,"Ranka ya dade Yaron nan a sume yake.... Ɗaukoshi muje Asbiti, " Ranka ya Daɗe..... da sauri
ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu jiki a mace ya koma suka tallabo suka saka shi cikin mota.
Kana suka wuce da gudun Gaske......
Tafiya suke da gudun Gaske kicin cikin ƙanƙanen lokaci suka iso Kano kai tsaye suka wuce Asbiti. nan
take aka soma basu Agajin gaggawa, kasan cewar tare yake da ƴan sanda yasa sukayi gaggawar amsar shi,
nan take likitoci suka fara gudanar da aikin su tsawon awa huda kana aka wuce dashi ɗakin hudu, bayan ya
biya su kudin su ya wuce gida tare danƙa Amanar a hannu litaka kana ya tattabar mai cewa zuwa Anjima
zai dawo....
Suna barin Asabiti akai tsaye suka wuce Nasarawa tun kafin ya iso aka wangale mishi gate wani katafaren
gidane mai matsifar kyau da ɗaukar ido gaba ki ɗaya motoci suka dannan han hancu nansu cikin farfajiyar
gidan sukayi Parking, a parking space da sauri ƴan sanda suka nufo motar shi kana suka buɗe Mishi, kai
tsaye suka wuce cikin gida, dai dai lokacin kwata Kyakkyawa mata fara sol doguwa mai matsifar kyau
sanye take wani tsadadden lass doguwar riga ta zauna mata ɗas a jikin a hankali taci gaba da sauko saman
bene ɗin fuskarta dauke da murmushi.....✍️✍️✍️✍️
*More comments and share pls*
*Sadeeya Ka'oje ce*
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

*( THE BEGINNING)*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬




Bismillah........ ✍


Tallah ! Tallah !! Tallah!!!

Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a
littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI*

yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN
ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai
karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi
kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number
08103884440
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*Page 11-12*
_______fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙara so wajen sa tare da Rungume sa. A hankali ya sauke
sassanyan Ajiyar zuciya. tare dai lafe a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, Lumshe ido tayi kana
ta buɗe a kan kyakkyawar fuskansa, cikin Murya mai kama da raɗa tace ,"Sannu da zuwa Habibi!"
A hankali ya Lumshe idon kana ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, cikin sanyi Murya yace," Yauwa
Habibity!"A karon karfo ta saki murshi Mai ƙawatarwa, kana tace "Ya hanya? Numfashi ya ja kana ya
fesar, cike da gajiya yace ," Alhamdulillahi!"
"muje ciki kawatsa ruwa"
Kana suka wuce ɗaki rike da hannun juna, kallon ɗaya zaka musu ka fahimci tsantsan so da kyauna da
shaƙuwa mai ƙarfi, Masha Allah wani haɗaɗɗen daki suka shigo mai matsifar kyau, cikin tsananin kewa ya
rungumeta nan take suka faɗa duniya masoya, kana sukayi Wonka tare, bayan ya gama shiri ta kallesa,"
Habibi ina zuwa kuma?"
A hankali ya sake Ajiyar zuciya kana yace ," Gidan Abdullahi zanje nayi Masa gaisuwa!"
"Gaskiya kam ya kamata kaje karya yi fushi da kai, ya ɗanyi Murmushi," Abdullahi bazai yi fushi dani ba
saboda yasan Uzurin da ya riƙe Ni!
" Wannan Gaskiya ne Habibi ba mai shiga tsakanin ku" tare suka fito daga ɗakin kai tsaye suka wuce
darning,da kanta da riƙa ciyar dashi Saida ya ƙoshi kana ya shiga bata ita ma gwanin burgewa,
"Yauwa ki haɗa min Abici mai ɗan ruwa ruwa zai kai Asbiti,
"Subuhalillah Habibi waye ba lafiya?"
Nan ya bata labarin abinda ya faru ,"Ya Allah ya jikin nashi"?
Numfashi ya fesar kana ya ce ," Alhamdulillahi zanje gidan Abdullahi daga can zan wuce Asbiti"
"Allah ya tsaye!"
", Amin ya rabbi Habibity ya faɗa tare da manna mata Kiss a hankali ya Lumshe idon, har bakin
mota ta rakashi cikin girmamawa security suka Gaisheta fuska a sake ta amsa musu.
"Barka da fitowa ranka ya dade!"
"Yauwa Dogo, security suka buɗe mishi mota kana yashi a tsake suka fike daga gidan, kai tsaye suka wuce
GRA,
Suna isowa mai gadi ya buɗe musu gate a tsanake Dogo ya danna hanci matar cikin gida, dai dai
lokacin Abdullahi ya iso fuskar ɗauke da murmushi ƙarfin Hali,
"Sannu da zuwa Abdullahi ya faɗa cikin sanyi Muryar, saukar yaushe?"
Batare da ya bashi amsar tambayar shi yace, " Ya ƙarin haƙiri!?"
"Alhamdulillahi mun gode Allah!"
"Allah ya gafar ta mata! cikin raunin Murya Abdullahi yace," Amin!"
Kana suka wuce cikin gida kai tsaye suka wuce ɗakin Kaka,
"Mama!!"
Abdullahi ya kira sunanta cikin girmamawa"
Kaka dake kwance saman lallausar Katifa ta mike.murya a disashe tace ," Abdullahi ƙara so mana"
Kai a sunkuye ya shigo ɗakin ,"Barka da war haka Mama!"
"Yauwa Abdullahi"
"Mama ga Nuraddeen can Palon yazo gai sheki"
Kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana tace ,"wannan Abokin ka da kake bani Labarin?"
"Ehh Mama shi koda aka yi rasuwa yana india dawowar shi kenan daka India"
"Masha Allah"
Tare suka fito daga ɗakin fuskar Kaka ɗauke da murmushi har suka ƙarasa cikin palon Abdullahi mai
matsifar kyau,
Suna isowa Alhaji Nuraddeen ya durƙusa har ƙasa ya gaida Mama cike da girmamawa da sauri Kaka ta
dakatar da ta hanyar daga ƙafaɗun sa Kana ta zaunar dashi saman Sopa masu matsifar laushi,
Fuska a sake Nuraddeen ya soma gaida Kaka tare da jajanta mata rasuwar Kubra, " Allah ya jikanta da
rahama Allah yasa ta huta !"
Suka Amsa da "Amin" Kana Kaka tace ya Iyali? " Lafiya lau mama"
Mama ai Matar ce wannan dake kawo Abin tunda akayi rasuwar" cewar Abdullahi,
"Allah sarki Allah ya yi Albarka, Allah yasa a gama Lafiya!"cikin tsananin farin ciki da Addu'ar suka
amsa da "Amin"
"Naji gidan shiru ina yara halam?"
"Ina suna ɗaki Abdullahi ya bashi amsa"
Dai dai lokacin Nana ta shigo Palon fuska a tsuke hannunta riƙe da tap ta yara," Kaka Kinga Khalil ya goge
min Gama ɗina" sai kuma ta fashe da Kuka," zo Nan Nuraddeen ya faɗa tare da riƙe hannunta kana ya
zaunar da ita saman ƙafafunshi, " Ki Dena kuka Kinji ya faɗa tare da kai Hannusa yana share mata
Hawaye,
sai gasu sun fito ga baki ɗayan su, da sauri Haydar da khalil suka ƙara so wajen tare da rungumeshi cikin
tsantsan farin suka soma faɗin," Oyoyo "Daddy sannu da zuwa!" a hankali Maryam ta zauna kuka da
Kaka,
"Daddy yaushe kazo?" Cewar Haydar, "Banjima da zuwa ba" Daddy Ina kaje kwana biyu mun Dena ganin
ka? " Tafiya nayi yau ɗin nan ma na dawo!"
"Daddy Ina Mommy?"
"Tana gida tace na gaishe ku gaba ki ɗayan ku, kuma tace yaushe zaku kuzo mata weekend? "Daddy yau
Monday ran Friday zamu zo Weekend"
"Yauwa Allah ya kaimu"
"Amin Daddy"
A hankali Kaka ta cewa Maryam je kicewa Azumi ta haɗo mata ruwa, a hankali Maryam ta kike kana ta
wuce Kicin,
"Abdullahi wannan kuma wace?"
a hankali ya fesar da Numfashi kana yace ƴar Ibrahim ce Ƙane na!"
"Allah sarki kasan ban santa ba Allah ya jiƙansu da Rahama!"
"Amin ya Allah"
Dai dai lokacin Azumi ta iso hannunta dauke da tire mai matsifar kyau kayan drinks ne ƴa ƴan itatuwa
masu sanyi,
"Sannu da zuwa ranka ya daɗe cewar Azumi"
"Yauwa ya aiki"
"Alhamdulillahi yanka ya fade" kana ta wuce, sosai yasha kayan marmarin kana suka ci Baga da hira
zuwa na dan wani lokaci, Lokacin cinda zai tafi ya ba Su Haydar kyautar 100k Azumi kuma 10k kana ya
yi musu sallama, har bakin mota Abdullahi ya raka shi nan yake sanar dashi daga nan Asbiti ya nufa ,"waye
ba Lafiya. Nuraddeen?" Nan ya sanar dashi abinda ya faru, cikin tsananin damuwa ," Abdullahi yace Allah
ya bashi lafiya ," Amin" kana ya shiga Mota suka fice daga gidan kai tsaye suke wuce Asbiti, tare da likita
suka wuce ɗakin da aka kwantar dashi har zuwa yanzu bai farka ba, kallon yaron yaro cike da tausayi a
Ranshi yake faɗin wa wanne hali yan uwanshi suke cike oho....
"Ranka ya daɗe ga kuje ka zauna" cewar Dr,
"Bazai farka yanzu ba kenan? "Ranka ya dade da wahala gaskiya Allurar Bacci ka mai saboda ya nayin
jikin sa yana bukatar Hutu sosai!"
"Okay ba dawuwa Allah ya tasheshi lafiya!"
"Amin"
"Yauwa ga katina koda za'a buƙaci wani abun bana kusa" a hankali Dr ya karɓi katin tana kallon da sauri ya
aware manyan idanunsa yana kallon sunan dake jikin katin NURADDEEN MAI NERAH! Cikin tsananin
Mamaki yaci gaba da kallonsa mutumen da sunanshi ya kewaye da duniya,tabbas shine" a hankali Alhaji
Nuraddeen ya ɗago ya kallonsa," Shi kowa sam Baisan Maganar ta fito ba,
ya miike tare da barin ɗakin kai tsaye suka wuce gida.....
Nuraddeen da Abdullahi tare sukayi jam'iya Nuraddeen Mahaifinshi Babban Attajiri ne kuma dan Kasuwa
ne a Kano Nuraddeen shi kadaine ɗanda suka haifa Nuraddeen yana Ss3 Allah ya yiwa Mahaifiyar shi
rayuwa, farkon shigarshi jami'a Allah ya haɗashi da Abdullahi kasan cewar Course ɗinsu ɗaya wasa wasa
shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su Nuraddeen yaro ne mai kirki da kyauta ga tausayi ga son taimako,
yadda yake rayuwar shi da mutane sam ba Zaka dauka ɗan masu kuɗi bane rayuwar shi yake kaman kowa,
shaƙuwar su tayi karfi sosai a makaranta ba wanda bai sannu ba baru wansu da ƴan mata karatun su suka
saka a gaba, bayan sun kammala jami'a sukaci ga da zumunci su, Abdullahi baida wani Aboki a duniya
kaman Nuraddeen haka shima Nuraddeen baida wani Aboki kaman Abdullahi duk abinda zasuyi sai sun
shawarci junan su, Mahaifin Nuraddeen haka ya dauki Abdullahi kaman ɗan cikin sa, Mahaifin Nuraddeen
mutum ne mai matsifar son yara, Haka Nuraddeen ma kusan halayen sa ɗaya da Mahaifinshi...
Nuraddeen can waje yawacen ya wace shi ƙauyuka wajen taimakawa ta takkawa Allah ya haɗashi da
Ummul khairi bafulatanar daji kyakkyawan da ita wasa wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu ba bata
lokaci Akayi Auren bayan Auren su ya saka ta Kamaranta yaƙi da jahilci cikin ƙanƙanen lokacin ta fara
waye a bangaren ilimin Addini ma har gida malami ke zuwa koya mata karatu, bayan Aure su da shekara
Biyu Allah ya yiwa Mahaifin Nuraddeen rasuwa, Nuraddeen ya gaji duk a binda ya mallaka, tsawon
shekara goma sha biyar kenan da sukayi Aure, Allah bai taɓa basu haihuwa ba, likitoci sun tabbatar musu
da duk lafiyar su lau lokaci ne kwai bai yi ba, tun abin na damusu har suka barwa Allah, hakan yasa shida
Matar shi suke tsananin son yara, zuwa yanzu Nuraddeen baida kowa sai matarshi da Abdullahi da ya
kasance tamkar dan uwanshi haka ya dauƙi ƴa ƴan Abdullahi tamkar ƴa ƴan cikin sa wani lokaci a gidan shi
suke hudu ko weekend. Kubra har ta raru basa shiri da Ummul khairi, saboda ƙashi da hassada da tasawa
kanta ganin yadda Ummul khairi ta ke sharhiliya da dukiyar mijinta tare da ƙanwarta Ummul Kulsum,duk
da ta kasance ƴar Attajiri matar Attajiri, Abdullahi duk da ya kasance mai kudi Nuraddeen ya kereshi shi da
komai.....
Wannan kenan....👌🙌🤗
Gab da maggariba ya shigo gida Kai tsaye ya wuce masallaci dake cikin gidan Saida kayi Isha'i kana ya
wuce cikin gida cikin tsastsan farin ciki ta rungumeshi tare da manna shi hot kiss a kumatu, "Sannu da
zuwa Habibi ya mai jiki ina fatan yaji sauki?"
Ya sauke Ajiyar zuciya kana yace jiki da sauki!"
"Masha Allah, Allah ya tashi kafaɗunshi Allah kuma ya baka ladan taimako, "Amin Habibity!!"
Tare suka ci Abinci kana suka wuce daki, sukayi Wonka a tare bayan suna gama shirin suka kwanta
rungume da juna nan take bacci ya yi awon ya gaba su......
*BAYAN KWANA HUƊU*
Zaune suka a Palo suna hira Kaka ta kalli Abdullahi cikin sanyi Murya tace "Abdullah ya kama mu koma
gida! Kodan makarantar Maryam kusan kwanan mu goma sha ukku kenan"
Abdullahi ya sake Nannauyan Ajiyar kana yace," Mama don Allah karon nan ki dawo nan da zama Ko dan
yaran nan! Kafin na samu mai kula dasu.don Allah Mama," nan take Idanunsa suka shiko da kwalla, Su
Haydar suka haɗa baki wajen faɗin "Kaka don Allah karki koma ƙauye! Murya a disashe Maryam tace "
Kaka Nima Bazan iya zama ƙauye ba tunda Ya Maleek baya nan! Nan take maryam ta fashe da kuka,"shike
nan ya isa ki Dena kuka nan zamu ci gaba da zama insha Allahu Kaka ta faɗa cikin sanyi Murya" tare da
sharewa Maryam hawaye, " Nagode sosai mama Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" cewar
Abdullahi,
"Amman ya kamata mu naje ƙaraye ko don nayiwa maƙotana sallama"
"shike nan mama ko yanzu zamu iya tafiya! " kaka Ni kam ba zanje ba cewar Maryam" Nan take Kaka ta
shirya suka wuce tare da Abdullahi"
*ƘARAYE*
Suna isowa kai tsaye suka wuce gidan cike da kewar Abdulmalik da ke mata gizo a tsakiyar gida, isowar
keda wuya Mutane Unguwar suka fara shigowa tare da yiwa Kaka Gaisuwar Abdulmalik da Kubra, nan
take Mutuwar ta dawo mata sabuwa, cikin dauri ta shiga amsa musu tare da faɗa musu zasu koma birni da
zama, kowa sai tambatayar Maryam yake, haka Kaka ta shiga rarraba kayan Abincinta ga duk wanda ya
shigo gidan, kana ya shiga haɗa musu kayan su da duk wani Abin mafani aka saka a motar Hilux dasuka zo
da ita, "Abdullahi sai batun gida ya za'ayi dashi kasan idon aka bashi ba kowa zai nakkashe miye shawarar
ka," Mama ina ga kwai ki kyautar dashi ga duk wanda kikega dama,
"Bana da sauran dengi a duniya kaman yadda kaima baka saura kowa a duniya. sai Ni, da iyayen
Hauwa'u suna rare sune suka fi cancanta dana mallakawa gidan!"
Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana yace Hakane Mama! Barinsa haka zai sa ya lalace ko bata garin su
samu wajen aikata barna"
"zan mallakawa Malam liman idon har ka amince, " Haba Mama miye saina wani Abince damu da gidan
duk a ƙarƙashin ikon ki muke duk wanda kika ba banda matsala!"
"Allah ya yi maka Albarka!"
"Amin Mama"
Bayan sun gama kwashe duk wani abinci mai mahimmanci suka wuce gidan Malam Liman, bayan ya fito
suka gaisa kana ya yi mata gaisuwa, a hankali Kaka ta miƙa mai makullin gida, batare da yasan na miye ba
karɓa,
"Malam Liman zanmu koma Kano da zama Insha Allahu, wannan makullin gidan muna na mallaka mashi
halak malak, cikin tsananin Mamaki Malam liman ya waro ido yana kallon Kaka,
Murya na rawa tace ," Mama kin mallakamin gida, saiga waye shar a fuskar malam liman har ƙasa ya
duƙa tare da yiwa Kaka godiya, Kaka tayi sauri dakar dashi," Haba Malam liman miye abin godiya anan,
da sauri ya nufi cikin

Please Login or Register in order to submit comment