Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 16 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Kaka ta bita harta
zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Sultana tai zaune ta
riƙo hannunta. Kaka Wallahi inhar baku aura masa niba saina gudu na bar muku gida!.
Mami da Meena da Jidda gabaki ɗaya jikinsu ya yi sanyi, basu taɓa tunanin ƙiyaryar da Sultana take wa
Sultan takai haka ba.
Run gumeta Mami tayi Cikin hikima da wayo Mami ta riƙa yi mata nasiha da ƙara ƙarfafa mata gwiwa
harta daina kuka, cikin wani irin yanayi ta nufi ɗakinsu ta kwanta,cikin raunan'nanyar murya ta soma faɗin"
Ya Allah ina mai ƙara roƙonka ka bani haƙuri da juriya tare da wadatar zuciya a kan dukkan a binda zanci
karo dashi cikin rayuwata na jin daɗi ko a kasin hakan ka kuma bani ƙarfin Zuciya da zan iya tafiyar da
ita akan hakan....
Ranar dai da kyar Sultana ta iya yin Bacci,....
Washegari Tun kiran sallar farko wasu daga jama'ar gidan da makusantansu suka tashi aka fara ƙaƙainiyar
ɗaura abinci. kaka ta nufin Ɗakin su Sultana ta tada ta don tayi Wonkan lalle,a hankali ta buɗe ɗakinsu
Sultana. Babu wanda ya tashi a cikinsu, dan mafi yawansu basuyi barici da wuriba, Kaka ta kunna fitilar
ɗakin tana kiran sunan "Sultana ki tashi kiyi Wonkan lallen ki, Meena ce ta fara farkawa saboda bata da
nauyin barci sam, ta tashi zaune da ƙyar tana murje idanunta,
"Ina sultana?"
"Kaka ƙila tana toilet? Bakin toilet ɗin Kaka ta nufa tana ƙoƙarin buɗewa taga ƙofar a buɗe, "bata ciki fa?
Fita kaka tayi daga ɗakin, bakin ƙofa taci karo da Mami ," Kulsum kodai Sultana tana ɓangaren ki?"
"A'a Mama bata can"
Lungu da saƙo na gidan Mami da Kaka suka shiga namen Sultana,
Sosai hankalin Abba ya tashi lokaci da Kaka take sanar dashi Sultana bata gida....
Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Sultana bata gidan,
Kamar wasa saiga ƙarfe 10:30 babu Sultana babu labarinta, kowa jikinsa ya yi sanyi..
Meena ta nufi ɗaki tana hawaye, a hankali ta zaune saman gado karab Idanunta suka sauwa kan takarda,.ta
ɗauki ta kartada ta nufi wajen su Abba,
Assalamu alaikum Abba!!
Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wallahi Abba bana son
Auran Sultan Nas zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga
yarda, amma wallahi ina masifar son Nas fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku
wajen ɗauramin Aure da wanda bana so! Abba bana son na zama sanaɗiyar rugujewar zumunci ku kaida
Daddy, ga Meena nan da Ihsan da Jidda duk wanda yake so A aura masa, Na muku alƙawarin idan komai
ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Nas. Na barku Lafiya!!!,
Daga ɗiyarku Maryam Ibrahim Gwani......
Tsit palon yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Abba sai faman kaɗa kai yake
"Wallahi ni dai ban yardaba, sai dai idan wani Azzalumi ne ya sacemin jikata". Kaka ta faɗa tana fashewa
da kuka.
Tashin hankali, 🙆
*SHIN WA SULTANA ZATA AURA??*
*SHIN WANI HALI SULTAN ZAI SHI GA??*
*SHI WAYE NAS??*
*SHI WANNE IRIN MA FARKINE SULTAN YA KE DA MEENA??*
*SHIN WANE IRIN RUƊANI NE KE TATTARE DA RAYUWAR SULTAN??*
*SHIN YAUSHE SULTANA ZATA GANE ABDULMALIK SHINE SULTAN??*
*SHI WANNE IRIN MATAKI ABBA ZAI ƊUAUKA A KAN SULTANA??*
*SHI YAU SHE KAKA ZATA HAƊU DA ABDULMALIK??*
*SHIN WANNE MUTUM NE SULTAN YA GANI A UMMURA?*
Amsarku na a cikin Littafin DR SULTAN.
A nan na kawo ƙarshen Book 1, sai mun haɗu a book 2 in sha Allahu
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment