Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikinta kaɗawa. dai dai lokacin Dr
Aryan ya fito daga ɗakin da sauri ya durƙusa kasa ya tattara takardun ya maidasu cikin File kana yamiƙawa
Sultan, cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai ya ce,
“Biyoni!”.
Kaman wata soloɓiyo ta bi bayan sa har zuwa Office ɗin sa,.Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta
ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace.
Tsawon lokacin Sultana na tsaye a Office, ƙanta ta ɗago ta kalli Sultan dake zauna a saman lallausar
kujerarsa yana danna laptop, "Nifa na gaji da tsayin nan"
Ƙoƙarin fice wa ta yi daga Office ɗin,"Come Back"
da sauri ta juyo ta kallesa kaman bashi ya yi maganar ba, a hankali ya mike ya nufi ƙofar fita, sai muka ya
juyo ya kalleta," ki biyo da file ɗin can, ya faɗa a hankali,
"A kwai aikin da Zanyi" Sultana ta ka tseshi daga kallon walaƙanci da yake jifanta dashi..
Shut up" Sultan ya katse Sultana da tsawa.
Hannu Sultan ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you,
ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"
Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Sultan shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama
sadakarwa Sultan marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.
"Aikin banza" ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Jidda ta bi bayanta tana kiran sunan ta.
Ta shiga wani ɗaki amma kafin ƙofar ta rufe Jidda yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga,"Daughter
Lafiya?"
"Nida ɗan renin hankalin can ma ya Kaini Office ɗin sa ya tsayar dani kaman wata kunki." Oh ni jidda
Daughter wai mike tsakin ki da Dr Sultan?"
"Mtsss Sultana taja tsaki
"Daughter pls ki daina fushin nan mana, Allah ɗazu ba ƙaramin dacewa da juna kikayi ba. ta ƙara sa
maganar tare da nunama Sultana video da tayi musu ɗazu,
da sauri Sultana ta fisge wayar da niyar goge video Jidda yayi sauri saka wayar a key, "Allah Bazaki goge
ba Daughter, wlh baki ga yadda mukayi matuƙar dacewa ba ina a ce ki Auresa!"
Juyowa da saurin Sultana ta yi tana kallon Jidda ,"Allah ya kiyaye, Ni matar Nas ce da yarda Allah!
"Nawa ba irin na kowa ba ne
Batun nayi bayani ko jawabi akan sanda zuciyata take masa hakan ba Abu ne mai sauƙi ba na sai san ina
son sa domin ya kasance na mummunan a rayuwata hakan yasa na kulle ƙofa daga kansa ba wani a
gabansa kuma ba wani a bayansa!
Jidda da ta tsura mata ido tana kallon ta kaman ta samu tv.
Sultan Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da
abinda ya keyi.
"Lallai Daughter kin kamu da Soyayyar Nas, to wai Daughter kintaɓa haɗuwa dashi, kai Sultana ta gyaɗa
mata alamar A'a, Jidda ta sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya kana yace ,"Daughter Anya bakiyi kuskure ba?
Yanzu duniya ta sauya Daughter Mutane ba Amana!"
"Nas baya ɗaya daga cikin Mutanen da kike tunani"
"Daughter ya kamata ki....."
"Mommy ya isa pls! Bana son mu samu matsala"
"Shiken Daughter Allah ya tabbatar muku da Alheri"
Fuska a sake tace "Amin Mommy na koke fa"
Jidda ta sauke Ajiyar zuciya. haka suka ci gaba da aiki a ranar har zuwa lokacin tashi kowa ya nufi gida....
Washe gari ta kasance Weekend ne Sultana basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mami takawo
musu breakfast sukayi,
Mami takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya kuje shoprite,
To suka fad'a suna mik'ewa, Sultana tasaka wando da Riga sannan ta ɗaura After dress sunmata k'yau
sosai,
Meena na rik'eda ATM d'in Abba tare da Nana suka fice daga gidan.
Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Sultana ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali,
basuwani ɓata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Sultana ce rik'eda keken🛒tana zaɓa tana
sakawa,
Bugun zuciyarta ne yatsananta, waige-waige tafara, Dan lamarin yafara tsoratata, babu wani alamar abinda
yashafi rayuwarta awajen, Dan haka ta dake tacigaba da duba abinda take buk'ata.
Sanye yake cikin ƙananan kaya sun masa kyau sosai. Taku yakeyi cikin nuna shinfa jarumine mai
wadataccen jini, kasaitarsa da kwarjini sun taka rawar gani wajen bayyana kwarjininsa, dasuka k'ara haska
farar batar sa mai matuk'ar taushi da d'aukar idanu, k'asumba tad'an taru masa afuska, hakama kansa akwai
Y'ar kwantacciyar suma, hakan yanada nasaba darashin lokacin kai, Dan aiki ya cakud'e masa sosai a ɗan
kwanannan.
Yana tafiyane kunnensa manne da waya, magana yakeyi ahankali kuma cikin nutsuwa, Wanda baisaniba
saiya d'auka da matarsa ko budurwarsa yakeyin wayar, fuskarsa babu walwala, yanayi yana duba abinda
yad'auka, saiya d'an karanta kafin yajuyo yasaka a keke.
Wannan salo nasa yayi masifar tafiya da y'an Matan wajen,
Dukda zuciyarta Na masifar harbawa hakan baisa tadamu da kallon waɗanda ke bayanta da gabantaba,
anutse takai hannu zata d'auki wani turare , shima yakai hannu. Akan nata hannun yaɗora nashi, da sauri
kowa yajanye danjin wani masifaffen shock daya jasu atare, lokaci ɗaya suka zubama juna idanu,
burkitattun idanunsa masu girma da haske suka shige cikin Na Sultana manya masu yalwataccen gazar-
gazard'in gashi.
Da sauri Sultana ta janye idonta cikin nasa.
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya tareda jan tsaki afili, yacigaba da ɗaukar abinda yakeso.
"Ya Sultana Meena ta kira sunansa cikin tsananin farin ciki, tare suka iso wajensa da Nana, ba kunya ta
faɗa jikinsa ta rungumesa hannu bibbiyu ya sa shima ya rungumeta tare da Nana, yan matan dake tsaye a
wajen ko waccenta ta tsuke fuska 🤣,
A hankali ta janye jikinta, "Ya Sultan ina Mommy da su Salma," Murmushi ɗauke a fusakar yace ,"lafiya
lau suke , " ya Sultan ina nan tafe Weekend ka gaya Mommy idon ka koma gida. Kai ya gyada mata, haka
suci gaba da seyayyar su,
Awajen biyan kud'i suka iske Sultana, Sultan ya miƙama Meena ATM ɗinsa, aiko da sauri ta miƙa ma su
Aiki..
tare suka fito daga shoprite ɗin. Kowa ya nufi motarsa Meena da Nana na yiwa Sultan Bye bye...
Ahaka suka k'arasa gida, suna shiga harabar gidan taci karo da motar Daddy, da sauri suka wuce cikin gida
nan Palo suka tarar da su gabaki dayan suna hira," Daddy sannu da zuwa, suka faɗa a tare ,"yauwa my
Daughter's, daman wajen ku nazo, Mommyn ku tace nazo na ɗaukeku kuyi Weekend a gida, wani irin farin
ciki ne ya lulluɓe Meena da Nana," don haka kuje ku haɗo kayan ku," Daddy Nidai Bazan je ba! Sultana ta
faɗa cike da Shogoɓa," wani irin kallo Abba ya watsa mata, nan take ta kama kanta, ,"Abba ga Atm ɗinka
cewar Meena," Banji debit Alert ba har yanzu. "Abba ya Sultan ne ya biya muna"
"Toh ma sha Allah, maza kuje ku haɗo kayan ku, da sauri suka wuce ɗakin , Sultana na kumbure
kumbure, jim kaɗan suka fito, Kaka ta kalli Sultana cikin tsokana tace idon kunje ina gaida Sultan, wani
irin kallo Sultana ya yi kaka tare da murguɗa mata baƙi... Har bakin Mota Mami ta raka ƴa ƴan nata, dai dai
lokacin kuma Motar Haydar ta jigo. Yana gama Parking suka fito gabaki ɗayan su, "Daddy Abba Ina wunin
ku, "lafiya lau Haydar,"Khalil ya kalli Sultana," Anty Sultana ina zuwa haka ?"
Ya Khalil gidan Mommy zamu tafi Nana ta bashi amsa.
"Allah ya tsare sai mun shigo"
"Amin"
"Ina Arif halam ko bada shi za'a je ba?"
"Ya Haydar bacci yake kansa ke ciwo,
Saida suka wuce sanna su Haydar suka wuce cikin gida.
Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidan Daddy Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu
tamfatsetsen gate din.
Aɓangaren Sultan bayan ya dawo daga shoprite
Side ɗinsa ya wuce,
Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo blue mai taushi ya zira, tare da
fesa turarensa mai masifar ƙamshi,
System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar kamshi
turarensa ya mamaye ko'ina
A hankali yake taku wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar
fatarsa.kai tsaye ya nufi babban palon ya zauna,
Cikin wani irin farin ciki Sultana ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken
kayan marmari suka zagaye gidan, Da sauri ta juyo da kallonta kan Meena tare da cewa. "masha Allah wai
daman haka gidan yake da kyau? gaskiya yayi kyau sosai"
ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers,y
"Anty Sultana yanzu kam kin Dena fushi ko? Kinga gida mai kyau?"
"Wallahi Meena gidan nan ya yi kyau sosai komai kuma ya burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda
ilahirin gidan ke fitar da wani Daddaɗan ƙamshi,har Naji ina son yaruwa a gidan nan!"
Meena Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa,
Tunda sukayi sallama su Salma da Salim dake falon suka taso da gudu suka rungume Sultana
Meena gefe takoma tana kallonsu cikeda birgewa, saida suka gama murnarsu sannan suka lura da Meena da
Nana , suma suka rungumesu tare da Nana.
"Maraba da baƙi" cewar Mommy.
Lokaci ɗaya suka juya suna kallonta karab Idanunta ya sauka kan Sultan
zaune akan sofa, dagashi sai wando 3quter idonsa a wayarsa yana danne-danne.
Rumtse ido Sultana tayi gabanta Na fad'uwa, bak'aramar firgita tayiba daganinsa haka, Dan damtsen
hannunsa yamugun tsoratata, tai saurin kauda kanta daga kallonsa.
Har yanzu idonsa nakan waya, tare suka wuce tsakiyar palon suka zauna.
Kafeta tayayi da idon nasa, wannan yasakata gaza koda kallonsa,
"Mommy Ina ihsan?"
"Tana ɗaki bansa uban me take kitsawa a ɗakin, kullum tana ɗaki kaman wata Amarya.
"Sultana kun gaisa da Sultan, cewar Mommy. Kai ta gyaɗa a lamar a a'a, bazaki gaida Ogan na Kiba?"
"Mommy nan ai ba Asbiti ba ne" ta yi maganar tana kallon Sultan,
Mommy tayi ya yi Murmushi kana tace," Oga oga ne a duk inda yake Sultana,
Batasan sanda bakinta yasuɓuce tace kamarya? Banda waje na ?, tak'arashe maganar da murgud'a baki.
Aransa yace akwaifa rashin kunya sosai awajen yarinyarnan..
Afili kuma saiya gallah mata harara.

, harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye
idon nata,
Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi
bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu
macen data taɓa kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa
kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa,
kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na yan sakannnu kawai saikaga jikinta
narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba.
Amma yau ga yarinya k'arama, ta kalli tsakkiyar idonsa.
Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Daddy kallonsa.
"Sultana kuje sama kukai kayan a ɗakina.
"Mommy yau a ɗakinki zamu kwana wajen Anty Sultana, Salma da Salim suka faɗa, "Salma a zaku takure
a ɗakin ku barsu Kinji, ,"nan ta ke ta marairaice fuska kakam Zatayi Kuku, Mommy ki barsu zamu kwana a
tare, "A'a sai dai Salma ta kwana tare da kuku, Nana taje ɗakin Ihsan su kwana tare,
"Mommy Nifa".
"Kaje ɗakin Ya Sultan ka kwana, dai dai lokacin kuma su Haydar suka iso da Khalil da Arif, "Yauwa ga Ya
Arif nan ma yazo zamu kwana a tare..
Nan take palon ya ƙara hargitse wa da hayaniyar su, kafinan suka ci Abinci na musamman da Mommy ta
girka musu. Sai bayan Isha'i Ihsan ta fito daga ɗakin fuska a tsuke, sama sama suka gaisa dasu Sultana,
Ƙarfe 8:50 su Haydar suka wuce gida haka a bar Arif.. bayan ta fiyarsu Sultana ta wuce ɗakin Mommy tare
da Meena, "Anty Sultana karku rufe ɗaki ina nan tafe, ,"sai kinzo...
Suna shiga ɗakin Meena ta wuce toilet Wonka tayi ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta nan take bacci ya
Awon gaba da ita.
Bayan tafiyarsu, Salma bata jima ba ya yi Awon gaba da ita, koda Sultan ya shiga palon tana kwance,
kashe Tv ya yi kana ya ɗauke a hankali, kansan cewar bacci nata baryi nisa Sosai ba, ta buɗe idanunta a
hankali, cikin muryar Barci tace ,"Ya Sultan kaini wajen Anty Sultana...
Sultana Meena na fitowa daga toilet ɗin itama ta shiga Wonka tayi ta fito
bayan tafito tashirya cikin wando dogo da Riga Na cartoon kalar Pink sunmata kyau.sosai, tana gaban
mudubi tana tufk'e gashinta Dan bataso tayi barci dashi ahaka, yaturo k'ofar yashigo, da sauri Sultana
tajuya tana kallonsa.
'Dauke yake da Salma a kafad'a, saɓanin d'azun yanzu yasaka doguwar jallabiya, Salim nabiye dashi
abaya, da'ala shi baiyi barcinba.
Ko kallonta baiyiba yad'orata a gadon Mommy, saida yagyara mata kwanciya sannan,
sannan yamata addu'ar barci ya shafa mata, Salim yace Ya Sultan ni awajenka Jan kana.
"Arif na can na jiran aka palon ɗakin ka Zaiyi barci.
Taɓe baki Sultana tayi,
Duk abinda takeyi ya Sultan Na kallonta ta k'asan idonsa, bakinsa yataɓe ya kauda kansa daga kallon nata.
yafice abinsa, batareda ya nuna yamasan dawata hallita a d'akinba.
Da uwar harara Sultana taraka bayansa harya fita.
Yana fita ta kace wutan ɗakin ta kwana, nan take Barci ya ɗauke ta...
_Washe gari_
Har 8:30am Sultana bata tashiba, tuni su Salma da Meena sun tabar ɗakin ita kad'ai taketa juye-juyenta
ƙaton gadon Mommy
Kowa ya hallara a dining har Daddy kasancewar weekend ne,
Mommy takalli dukkan yaran babu Sultana da Sultan ,
Meena tashi kakira Yayan ku, kekuma Salma kira Anty Sultana.
Da to suka amsa.
Babu dad'ewa saiga ya Sultan sunfito shida Meena rike da Hannun juna har k'asa ya durk'usa ya gaida
iyayen nasa, k'annensa suka gaisheshi.
Yaja kujerar ya zauna, Sultana suka fito, da alama saida Salma tasha dagama wajen tashin Sultana, dan
kayan barcinema ajikinta sai hijjab data d'ora iya ƙirji a saman kayan barcin, daka kalli idonta kasan yanzu
tatashi a barci, saboda akwai ja acikinsu, gasukama sun k'ara zama manya, durk'usawa tayi tagaida Daddy,
ya amsa cikin fara'a,
"Mommy Ina kwana"
"Lafiya lau Anty Yara"
Daddy yace tashi kizauna d'iyata yanuna mata kujera d'aya data rage wadda take kusada ya Sultan .
Jitayi tamkar tafasa ihu, amma babu damar hakan, dan Daddy kallon mahaifi take masa.
Mommy ta haɗawa Daddy Abincisa dasu Salma da Salim. "Sultana tatashi ha had'a masa shima,
bak'aramar kid'ima zancen Mommy yasakataba,
Babu yanda zatayi tahad'a masa komai, yanata danna waya abinsa tamkar baisan mi'akeyi a dining
d'inba,
Kowa yagama zuba abincin Daddy yayi bismillah, kowa yayi aka fara break, Sultana dukata takura, sai
juya cokalin takeyi, shiko a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance,
bayan sun kammala break fast Sultana tazare jikinta zuwa kicin taya masu aikin gidan Aiki Abinci....
Bayan La'asar, Sultana ta nufi gadin, tafiya take a hankali kai a sunkuye
batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata
tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba
ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wata lallausan kujera, yana Danna lap-top ƙirar kamfanin apple
dake akan wani ƙaramin table Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran cike da ƴaƴan
itatuwa masu in ganci. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da
zuwanta ba.
A hankali ta kawar da kanta gefe tana kallon gwaiba. Matsawa tayi a hankali, tsalle tayi da niyyar
tsinkowa dan bishiyar na da tsayi sosai.
tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.
"Ki bar nan".
Sassaanyar muryarsa mai sanyi ta daki kunenta. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya
tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata
ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba'a amsa masa
ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago manyan idanunsa masu haske ya sauke a
kanta. Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son
lumshesu..
A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Sultana ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen
idanunta , "Ansa dokar shika nan ne?"
Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a
kanta ba har yanzu, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar
jini.
Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba'a kansu take ba.
Kai tsaye ta wuce cikin gida fuska a tsuke ta nufi ɗaki ta kwata cike da takaicin Sultan, da wannan takaici
barci ya yi Awon gaba da ita, sai gab da maggariba ta farka, ruwa ta watsa tare da Alwalla kana ta fito, dai
dai lokacin Meena na shigo ɗakin," Anty Sultana kinsha barci yau. Harara Sultana ta dalla mata, "yi haƙiri
karki sauke barin nan a kaina, Saida suka Isha'i suka fito Palo.... Koda suka shigo palon Salim na kuka
Miya faru kake kuka Salim?.
Cikin kukan ya nuna Salma, ta Sultana ta maida kallonta kan Salma ita ma tana niyyar kukan.
" Meki kamasa?"
" Anty Sultana biscuit d'ina da yana Sultan ya bani shine ta kwace min." "Anty Sultana jiya tare mukaci
nawa"
Bata k'arasaba taji Salim ya fusge hannunsa anata yakwasa aguje.
Juyowa tayi da sauri Dan ganin itama Salma tagudu.
Kasa ya duk'e suka shige jikinsa, bataga fuskarsaba saboda sun kare, amma jin yanda kirjinta keta
harbawa taji ajikinta shine, dak'yar tacira k'afa danufin Darning..
Tare sukaci Abincin, bayan sun gama Daddy ya kalli Sultan, "idon sun gama ka maida su gida gobe
Monday, wani irin farin cikin Sultana taji.... ai da sauri ta wuce ɗaki ta haɗa kayanta ta fito Palon Meena
da Nana har ga Allah basa son barin gidan,
Lokaci da zasu tafi Daddy ya basu 200k su sa kati. da farko ƙin ƙarɓa Sukayi Saida Daddy ya yi musu
jan ido kana suka ƙarɓa tare da yi masa Godiya. Har bakin mota suka raka su.
Meena ce a gaba Sultana na zaune gefen Meena, har suka iso gida Sultana Ƙala bata ce ba, suko sai hirar
su, suke gwanin burgewa.suna isa ƙofar gida Sultana ce farko fita.
"Ya Sultana kazo muje cikin gida ka gaida Mami, Ya Sultan ni banma taɓa ganin kazo gidan nan
ba,"Ameenatu! dare ya yi Zanyi na san duk sunyi Bacci next time zan shigo in sha Allahu. Ya Sultan.... Pls
tayi maganar cike da Shogoɓa, kai ya gyaɗa mata alamar A'a, jiki a mace ta fife daga motar...
Saida yaga shigar su cikin gida kana ya wuce...
Waje gari, da safe Sultana ta wuce wajen Aiki...
A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. A ɓangaren Sultana da Nas Soyayyarsu suke
Sha hankali kwance.
Yau ta kasance Weekend, tunda safe Sultana ta wuce gidan su jidda
Kaka ko yau tunda safe ta tashi da matsanancin ciwon kai. Bayan La'asar Mami ta bata maganin ciwon kai,
tana sha bada jimawa barci ya yi a won gaba da ita...
Sai ƙarfe Shidda Sultana ta dawo.
Duk da takalman data gani na maza a ƙofar palon Daddy bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su
gama amsa mata ta shige dan duk zatonta Su Haydar a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta
buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan
fararen idanunta waje cike da al'ajabi.....!"✍️
*Har yanzu dai muna cikin Book 1*
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍


PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗

*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 29-30*
______Sultan dake zaune sanye da ƙanan kaya sun yi masa Kyau sosai, kallon nata yake cike da mamaki,,
ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi.......
" Oyoyo Anty Sultana ”. Salma ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda Salam take, har yanzu
mamakin ganin Sultan ɗin bai barta ba,
Sosai mamaki ya kume Sultana, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Sultan
daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa..
"Shigo mana Sultana"
A hankali ta ƙara so cikin palon, "Daddy sannu da zuwa"
"Yauwa yar Albarka"
Kana ta zauna tare da su Salma.
"Toh shi Sultan bazaki gaida hiba?" cewar Abba.
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Sultan ɗin da yayi tamkar baisan da zaman kowaba a palon ba
tace, "ina wuni".
Sarai yajita, amma sai ya share tamkar bejita ba,
"Ya Sultan Anty Sultana ya gaisheka" Salma ta faɗa a hankali.
Ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin
ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Sultana tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa.
Shima ɗan lumshe nasa yayi ya buɗe cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, "Lafiya lau"
"Jeki kawo musu ruwa".
A hankali ta miƙe ta nufi cikin tare da Salma, kayan drinks ta haɗo musu masu sanyi,
wani irin Murmushi yayi , tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira,
harar ƙofar da Sultan yabi ya fice ta gefen ido.
Jim kaɗan mai gadi ya shigo, a bakin ƙofa ya tsaya, yana kiran ,"Sultana"
Miƙewa ta yi ta nufin wajensa, tsaye ta tarar dashi rike da 🎁, "gashi"
A hankali ta kai kallo da Sultan dake waya yana faɗin ,"Haba Aziz kasan irin da muwar da najiga reshin
samunka a waya da nayi, taɓe baki Sultana tayi, tayi, yauma dai Flower ce mai masifar kyau da kamshi da
yar takarda,
*Zan Kasance cikin Son ki har Abada*
*kalaman bakina sun gaza furta adadin yadda Zuciyata* take* kyaunarki kin zamo tamkar Numfashin da
nake shaƙa kece rayuwarta ina Son ki Sosai wallahi ban san na linda zan shiga ba In don na rasa ki ba kece
Abar be gena safe da yamma daga Nas*
Wani irin sassanyan Nunfashi ta sauƙe lokacin da tagama karatun,
tafiya take kai a sunkuye
Karo sukayi, goshin Sultana ya bugu goshin Sultan, Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja
kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Sultana bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon
Abba dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi.
Sultan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo
jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yayi
sauri ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe,
Cikin tashin hankali Sultana ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma
yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu,
cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen tsiwa.
cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa

Please Login or Register in order to submit comment