Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ka'oje ce* ✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*
💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 15-16*
_______Lokaci ɗaya su ka iso ta re da Dogo Deribe, ya na ga ma Parking su ka buɗe motar cikin tsananin
farin ciki har wa ni tsalle su ke saboda mur na, dai lokacin Ummu Kulsum ta fi to cikin mota ta re da wa su
kyawawan Yara gu da Ukku kusan kama su ɗaya Ummul Kulsum ga baki ɗayan su suka nufi palon,
Sunyi nisa sosai da kallon tv Alhaji Nuraddeen ji kwai ya yi a rungumeshi a hankali ya juyo da fusakar
karab Idanunsa suka sauka kan Abdullahi dake tsaye murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa, Alhaji
Nuraddeen ya sauke sassanyan murya tare rungume Abdullahi yana faɗin ,"Sannu da zuwa Aminina irin
wannan bazata haka?"
Bayan sun zauna Mommy ta kalli Abdullahi cike da girmamawa ta ce ,"Abban Haydar sannu da zuwa yasu
Mama?"
"Duk lafiya lau su ke tace a gaishe ki,"
,"Amin ina mai sunan Mama!"
"Tana gida ba yadda banyi da ita ta zo muje ta ce a'a saboda karatun Hadda da take!"
"ma sha Allah!, Allah ya ƙara basira mai Albarka"
"Ga ba ki ɗaya su ka Am sa da "Amin"
"Ina yaron Nawa?" Abdullahi ya tambaya murmushi na ƙara faɗaɗa akan kyakkyawar fuskarsa,"
Cikin girmamawa Sultan ya ce ,"Abba Barka da zuwa"
"Yauwa My boy ya gida"
"Alhamdulillah Abba!"
"Daddy waye wannan Haydar ya faɗa tare da nuna Sultan,"Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi tare faɗin ,"
Yayan kune Sultan! " Daddy ban taɓa ganin saba"
"Ehh a school yake last Month ya dawo daga yanzu ku riƙa kiransa Ya Sultan! kaji"
"Toh Daddy"
"Yauwa my Boy!"
"Meenah Zo non Mommy ta faɗa a hankali yariyan ta ƙara so wajen ta zauna ƴar kimanin shekara goma
sha sha biyu, "Meya sameki?"
cikin raunan'nanyar murya ta ce ,"Mommy kaina ke ciwo!," Cike da damuwa Mommy tace ,"Ayya
sorry Mamana!" Shiko Sultan sai kallon yarinƴar yake, Yana mai jin. tsakanin son a Ranshi, ga baki ɗaya
hankalin sa nan kansu, ,"kinci abinci?" A hankali ta gyaɗa kai, "Yauwa to je ɗaki ki watsa ruwa kizo na
baki magani,"toh Mommy kana ta wuce ɗaki,
Ummul Kulsum ta sake Nannauyan Ajiyar zuciya,"Anty dole Kanta Ya yi ciwo jiya a zauna kuma kwana
reshin barci ne ya sakan mata ciwon kai nan, jiya tunda ƙannen magariyi suka zo gidan a suna faɗamin na
tattara kayana na bar musu gida, tun a lokacin ta ke ta na kuka! haka muka kwana zaune"
"Mommy ta fesar da Numfashi mai zafi, cikin tausasa halshe ta ce ,"Allah ya jiƙan Aminu sam basu
hali!"
"Ya isa hakan nan cewar Alhaji Nuraddeen,.. In sha Allahu daga yau wannan matsalar tazo ƙarshe!"
"toh Allah ya sa hakan shine Alheri Mommy ta faɗa cikin wani irin yanayi," ga baki ɗayan su suka Amsa da
Amin,..
Sai lokacin Sultan ya samu damar gaida Ummul Kulsum,"Ina kwana Mommy!" Lokaci ɗaya su ka juyo da
Ummul khairi, ko waccen su furkarta ɗauke da murmushi," shima murmushin ya sakar musu," Ummul
Kulsum haka kawai ta tsinci kanta da kallon Sultan..
"Wai bakiji yana gaishe ki ba da sauri Ummul Kulsum ta janye hannunta,"Kana ta ce ,"Lafiya lau!"
su Haydar kam sai guje guje suka a Palon suna wasa,
"Mommy nayi Wonka"
"Yuwa Mamana muje na bakin maganin tare suke wuce ɗaki bayan ta bata bamagani ta Kwantar da ita
tare da lulluɓeta da laulausar blanket nan take Barci ya yi won gaba da ita.
Ranar dai haka suka yi cikin tsastsan farin karfe Abdullahi sai bayan isha'i ya wuce gida..
Sultan ma tunu ya wuce ɗakin sa tare da Haydar da Khalifa...
"Anty wai Nikam ina kuka samo yaro nan?" cewar Ummul Kulsum,"Mommy bata ɓoye mata komi,"Kai
gaskiya Anty ya Nuraddeen nada kirki Allah ya saka Mishi da Alheri, shiko Sultan Allah yasa ya zame
muki ɗan Halak duk da dai naga bashi da matsala"
"Amin ya rabbi!"
Kinga Saida safe wlh Barci nake ji sosai jiya ga baki ɗaya ban runtsa ɓa"
"Allah ya tashe mu tafiya lokaci ɗaya suka miƙe ko waccen su ta nufi ɗakinta, Ummul Kulsum koda ta shi
Meenah na zaune a tsakiyar gado ta dafe kai, da sauri Ummul Kulsum ta nufi wajen ta zauna tare da
Rungume ta kana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar cikin raunin Murya tace," Mamana lafiya mike da
munki?"
Murya a disashe Meenah ta ce wannan mafarkin na sake yi! da sauri ta Ummul Kulsum ta waro manyan
idanunta cikin raunin Murya ta ce ," Yau kuma?" Mamana! Kai ta gyaɗa mata, a hankali ta rumtse idanunta
ta na mai jin wani irin Radaɗi a Zuciyarta, "Mami Yauwa cewa sukayi Zasu ta fi da.....Ya isa Mamana tayi
saurin da katar da ita," idanunta duk a rufe take Maganar," Mamana Kodai baki Addu'a ba?"
Mame Wlh nayi harda Alwalla nayi kafin na kwanta"
a hankali ta riƙa shafa kanshi ita ko sai ƙara shigewa jikinta take, a hankali ta Kwantar da ita ta re da
tofa mata Addu'oi, tana sauke Ajiyar zuciya, haka dai har Barci ya yi awaon gaba da ita....
a hankali ta gyara masu kwanciya kana ta kwanta cike da ruɗu da tashin hankali ta ɗau tsawon lokaci a
haka sai faman juyi take, har wuraren karfe 2:20 kana wani Nannauyan Barci ya yi a won gaba da ita..
Washe gari bayan sun suyi sallah suka kowa Barci sai wuraren 12:10 suka farka, ta re su ka yi Breakfast
ga ba ki ɗayan su, lokacin da suka gama Alhaji Nuraddeen ya mikawa Ummul Kulsum ATM dinsa, ga
wannan a je a sewa su Meenah kayan sawa da duk Abinda ya dace gobe Monday zasu fara zuwa
makarkata" yana kai ƙarshen Maganar ya bar Darning ɗin.
Ya..
Ummu Kulsum da Mommy sai kallon kallon suke,
"Anty a da ya bar kuɗin sa kwai muje a kwaso kayan su a gida."kedai kawai kiyi a binda ya ce,"
Bayan sallah Azzuhur suka wuce kasuwa ga baki ɗayan su Hadda Sultan...
"Abdullahi!"
"Na'am Mama!"
"Zaman ka a haka bazai yiwu ba ya kama kasamu Mata kayi Aure! Kodan tarbiyyar ƴa ƴan ka, kagani sai
ƙara tsufa nake ba komai zan i ya yi yanzu ba sanan ba'a bar masu Aiki da tarbiyyar su ba, Abdullahi ya
sauke Nannauyan Ajiyar zuciya Kana yace ," Ina sha Allahu Mama zanyi ƙoƙari!"
"Yauwa haka nake son ji Allah ya yi maka Albarka! Allah ku ma ya haɗa ka da mata da mata ta gari!
"Amin Mama nagode sosai da Addu'a!"
"Yaushe su Malam Gwani zasu dawo?"
"Insha Allahu yau zasu dago gobe Monday Akwai makaranta"
"Allah ya dawo dasu Lafiya"
"Amin Mama!"
"Ina Mamana ?"
"Tana ɗaki tana Karatu" daga haka sukaci gaba da hira.....
Sai bayan Isha'i suka dawo gida da kaya niƙi niƙi ko wanne su a gajiye haka suka zuɓe gabaki dayan su a
Palo, dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya sauko daga sama bene fusakarsa dauke murmushi ya ƙara so
cikin palon, cikin sanyi Murya ya ce ," Kun dawo ,"Ehh"
"Yauwa A shiyama su Haydar zan maida su gida gobe Monday!" Nana kaman ta yi Kuka," Daddy Nidai
bazan koma ba!" Alhaji Nuraddeen ko sai kallon ya yan nashi yake,"Kuyi haƙuri ku shirya muje gida kunji
Ɗazu ma Abban ku ya kirani Mama Zatayi Magana daku tace Mishi kunje kasuwa!"
"Daddy Amman Next Week ma zamu dawo"
"Ba damuwa Allah ya kai mu!"
"Amin"
tare suka tattara kayan suka shigar dasu ɗakin Ummul Kulsum, bayan sun dawo gaba ki ɗayan su suka nufi
Darning Abcin suka ci cikin kwanciyar hankali da natsuwa....
Ƙarfe 9:30 Su mommy suka raka su har bakin Mota tare da kayan tsara da ta haɗawa Kaka turame guda
uku masu matsifar kyau da tsada da turare... cike da kewar Sultan da Ihsan, Arif, Meenah dan kwana dayan
da sukayi har sun saba da juna musamman Sultan.....
Suna barin gidan kai tsaye Alhaji Nuraddeen ya wuce dasu super market ya yi musu seyayya kayan sweet
kala kala dasu ice cream kana suka wuce gida...
Koda suka iso gida su Kaka na zaune a palon suna kallo, da gudu suka nufi wajen Kaka tare da rungumeta
cikin tsananin kewar su ta ƙara rungume su tare da sha bayan su, dai dai lokacin Maryam ta shigo polon a
hankali ta sauke sassanyan Nunfashi kana ta nufi inda suke cikin sanyi Murya ta gaida Alhaji
Nuraddeen,"Yauwa Mamana ya karatu," Lafiya lau Daddy!"
"Kuje ɗaki ko kwanta ko dare nayi"
Bayan tafiyar su Kaka ta kalli Alhaji Nuraddeen ta ce ," Ya su Ummul khairi!"
"Lafiya lau take Mama ta ce a gaishe ki ga wannan ta ce a kawo Miki!.
Cikin tsastsan farin ciki Kaka ta karɓi Ledar tare da buɗewa wani irin sanyi yaji a ranta,"Allah ya yi muku
Albarka! Allah ya baku zuri'a mai Albarka! gaba ki ɗayan su suka amsa da Amin hira sukayi danyi zuwa
ƙarfe goma ya yi mu su sallama har bakin Mota Abba ya rakashi, bayan ya shiga Mota ya ɗan kalli Aminin
nashi kan ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya," Abdullahi mike damun ka?" tun zuwa na gidan nan na
fahimci kana cikin da muwa miye matsalar?"
Abdullahi ya dago da kansa cikin wani irin yanayi ya ce," Ba komi Nuraddeen!"
Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi gefen Baki kana ya ce ,"Abdullahi duk duniya bayan Mama banyi
tunani akwai wanda ya fini sanin halinki ba!" Tabbas akwai abinda ka ke ɓoye min!"
Abdullahi ya fesar da Numfashi kana ya ce ," Ba komai fa"
"Uhmm Abdullahi kenan shike nan tunda ka ce ba komai yanzu na san yadda ka ɗauke Ni!" Nan take
Jikin Abdullahi ya yi sanyi"
cikin wani irin yanayi Alhaji Nuraddeen ya tada motar yana ƙoƙarin barin wajen Abdullahi ya yi saurin
da katar dashi, "tsaya kaji zan faɗa ma!" a karo na Barka tai ya yi ƙoƙarin da katarshi amman ina tuni har
ya kai baƙin gate, Abdullahi ya yi tsaye a bakin gate ya hana mai gadi ya ɓude Mishi gate... Shi ko Alhaji
Nuraddeen sai hon ya ke, fuska a turmuƙe ya sauke Glass ɗin motar shi a fusace yace ,"Salihu Kaje a buɗe
min gate na wuce dare na nayi, Abdullahi ya saki Murmushi kana ya nufi wajen mota tare da faɗin idon har
kaga ka bar gidan to mun gama maganar da muke!" Wacce magana kuma? Gaga haka na fa ɓata min
lokaci!"
"Haba Habibin Ummul khairi! Haba Babibin Habibaty! Nan take Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi ta
re da Lumshe idanunsa kana ya buɗe su akan fusakar Abdullahi"
"Mugu ta wannan hanƴar ka ɓullo ko? ya ƙara sa maganar murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa,
Abdullahi ya sake sassanyan Nunfashi Kana ya kalli Alhaji Nuraddeen," Wlh Mama ce ta sani gaba akan
maganar Aure!"
"Kai Amman wallahi Mama ta yi dai dai to miye a bin tada hankalin a nan? Mama Gaskiya ta faɗa kodon
tarbiyyar Yaran nan ya kamata ka yi Aure Mama ta tsufa yanzu tana buƙatar Hutu sanan masu Aiki ba zasu
kulamar ya da yadda ya dace ba! duk da dai naga Mai Aikin tana da natsuwa Amman wallahi abu mafi
muhimmanci shine kayi Aure! Abdullahi!"
Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar kana ya ce ,"Nuraddeen ba na son na koma gidan jiya bana
son na sake Auren mata mai irin halin Kubra Nuraddeen bana son Na Auro matar da zata sake rabani da
Mama da Maryam! Duk lokacin da na buɗe idona na ganni a kusa da Mama na kan ji sanyi a raina, ba ma
wannan ba Su Haydar sun saba sosai da Kaka yanzu bana son Abinda zai raba su! Ya ƙasara maganar cikin
tsananin damuwa...
Alhaji Nuraddeen ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce, wannan gaskiya ne Abdullahi Nima bana
fatan Abinda zai sake rabaka da Mama!.
"tunda ta matsa ka yi Aure ya kama ka nemo Mata Abdullahi!
Nuraddeen wlh tsoro nake ji!"
Alhaji Nuraddeen ya ɗan yi shuru na ɗan wani lokaci kana ya ce ," Na baka shawara!"
da sauri Abdullahi ya ɗaga kai,"Ina jinka Aminina!
"Me zai hana ka Auri Ummul Kulsum ƙanwar Ummul khairi na tabbata zaka samu duk natsuwar da ka
ke buƙata, Ummul Kulsum bata da matsala kusan halin su ɗaya da ƴar uwarta na tabbata idon ka Aure
zakayi farin ciki har ƙarshe yayuwar ka! Tsawon shekara ɗaya kenan da rasuwar mijinta Aminu mutumin
kirki ne, ƴaƴanta Ukku Amina, Ihsan, Arif na tabbata zata riƙa ma zuri'ar ka da Amana! na tabbata duk
matar da zaka Aura ba lalle bane ka samu kaman Ummul Kulsum ba! Wannan shawara ce idon har ka
Amince!"
Abdullahi ya ɗan kalle shi sai kuma ya yi shiru," dare na yi fa zan wuce gida"
Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana ya ce,"Kana ganin zata Amin ce dani!"
"Me zai hana duk fa zaurawa ku ke ya faɗa cike da zolaya.
"Allah yasa Ha kan shine Alheri! "Amin ka Amince kenan?"
"Bazan ki zaɓin ka ba!"
"Shike nan Allah ya yi muna zaɓi na Alheri!
"Amin ya rabbi haka su ka ci gaba da tattaunawa sai warren 11:30 Alhaji Nuraddeen ya wu ce gida ci ke da
ƙwarin Quiwa, ko da ya iso gida :12 har ta gota...
Koda ya shigo ɗakin zaune ya sa meta sanye sa Kayan Barci sunyi matsifar yi ma ta Kyau ga wani
fitinannen khamshi da ta ke, da Sauri ta faɗa jikinsa tare da rugumeshi," murya a shogoɓe ta soma
magana," Habibi ina ka tsaya haka"
a hankali ta ƙara lafewa a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi,
janye ya yi daga jikinsa suna fusakar juna hannayen sa ya ɗaga sama, ta san mi ya ke nufi a ta fara
gwaɓe kayan jikinsa, "Haɗo min tea kafin na matsa ruwa, bai jira mi zata ce ba ya wu ce toilet ya yi
Wonka da ruwan dumi, ya na fitowa dai dai lokacin ta shigo hannu dauƙe da Mug ɗin Black tea mai zafi sai
tururi ya ke fitarwa saman Centre table ta aje Mug ɗin ,bayan ya gama shirinsa ya zauna suna fusakar
juna,a hankali ya soma shan Black tea ɗin yana Lumshe ido, ita ko sai kallonshi take, a hankali ya aje Mug
ɗin saman table, cikin tsokana ya ce "irin wannan kallo ha Habibity!"
Kana ya yi gyaran Murya, Hankalin da natsuwarta ta maida a kan, "wani aikin lada na ke son ki ta yani
ai watarwa wanda zai amfane nu ga baki ɗaya!"
ta sauke sassanyan Nunfashi tare da faɗin," Allah ya sa wanda zan iya ne Habibi!" Nan ya taba labarin
yadda su ka yi da Abdullah...
A hankali ta sauke Ajiyar zuciya kana ta fesar da Numfashi," cikin tausasa halshe ta ce ," Haba Habibi ai da
ni da Ummul Kulsum duk a ƙarƙashin ikon ka mu ke, zaɓin ka shine na mu, na amince da wannan haɗi,
Allah ya ƙara danƙon zumunci, " Amin ya rabbi"
"Sai ki san yad da zaki shawo kan ƙanwar ta mu, " Ina sha Allahu!"
Mommy ko har Allah, Allah ta ke gari ya wa ye..
washe gari bayan su Meenah su wace Makaranta, Mommy ta wu ce ɗakin Mame, "Anty Ina kwana?"
"Lafiya lau"
Zama ta yi su na fuskarta ju na, Ummul Kulsum! Mommy ta kira sunanta ci kin sanyi Murya,.
"Na'am Anty!"
"Daman Baban Sultan ne ya zo min da wata Magana ji ya!" a takaice ta sanar da ita duk Abinda ya faru,
Ummul Kulsum ta fesar da Numfashi,cikin wani irin yanayi tace ," Anty! Ba zanƙi zaɓin Yaya
Nuraddeen ba! Na san ba zai zaɓin abinda zai cutar da Ni ba!"
Mommy ta sauke sassanyan Murmushi,"kin Amin ce kenan?"
cike da kunya ta gyaɗa kai" Masha Allahu, Allah ya tabbatar mu na da Alheri!"
★★★★★......
"Habibi kaga ikon Allah ko komi yazo da sauƙi ko?"
Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi kana ya ce ,"Ai daman shi Alheri ha ka ya ke Allah dai ya tabbatar
muna da Alheri!"
"Amin Habibi"
Nan take Alhaji Nuraddeen ya kira Abdullahi ya sanar da shi, cike da zolaya ya ce,"koda ma can kuna so
juna? Naga Abin ya zo da sauƙi ha ka! An ya Abdullahi!"
daga can ɓangaren Abdullahi ya ce ," Ba na son sa ido fa,
"Ba wa ni sa ido gaskiya na faɗa"
Anjima zan shigo muyi Magana da Mama!"
"Okay Allah ya kai mu"
"Amin"
Kaman yadda Alhaji Nuraddeen ya faɗa wuraren ƙarfe Biyu ya wu ce gidan Abdullahi ya yi Kaka bayanin
komi sosai Kaka ta yi Murna..," Allah ya sanya Alheri, "Amin Mama!"
dai dai lokacin su Maryam su ka da wo da ga school da gudu su Haydar suka ƙara so cikin palon su na
faɗin "sannu da Daddy! Daddy munga su Meenah da Ihsan da Arif a school ɗin mu!... Daddy Ina Ya
Sultan?"
"Ya na gida, "Daddy Muna gaida shi,
"Wai waye Sultan ɗin nan tunda su ka dawo hirar sa su ke" cewar Kaka,
Abdullahi ya yi saurin ce wa "Ɗan Nuraddeen ne Mama" ita ko Kaka a tunanin ɗan Uwan Nuraddeen
tunda ta san bai taɓa haihuwa ba,
"Allah sarki tunda su ka dawo kullum cikin hirar sa su ke, Murmushi su ka yi ga ba ki ɗayan su,
Nuraddeen ya jima a gidan Kana ya yi musu sallama ya wu ce gida,
Lokacin da ya isa gaida haka su Ihsan da Arif su ka faɗa mai sunga su Haydar a makaranta....
★★★★........
Bayan Isha'i Abdullahi na zaune a ɗaki wayar shi ta fara Ringing a hankali ya ɗaya wayar ta re da Manta ta
a Kunna," ka shirya ka zo gida na yanzu," Me Zanyi?"
"Bana son Munafurci kaman ya me za ki yi, "Nuraddeen!!!.. "Yanzu don Allah da girman nawa zanje ta
ɗi?"
"Au Ashe kasan Abinda za ka yi"
"Allah idon baka zo ba zan fa sa Ni daga yau ma na dawo Mahaifinka tunda Ni ne waliyin Ummul
Kulsum! Ya ƙarasa maganar cike da zolaya,"Auw ta nan ka ɓullo!"
"don Allah mu aje maganar wasa ya kamata kazo taɗi, "za ka rani idon nazo?"
"Ina matsayin Yayan ta zan raka ka taɗi"
"A matsayin Abokin Ango zaka rakani"
Mommy na zaune ta na jin duk Abinda suke faɗi sai Murmushi ta ke, a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin
Ummul Kulsum dai dai lokacin ita ta fito da Wonka," Shi ke nan ma abu ya zo da sauƙi ki shirya Abdullahi
na nan tafe"
Da sauri ta waro manyan idanunta tana kallon Mommy," Anty wlh Kunyar sa na ke ji, "Kedai a ke ji
Kinga tafiya ta,
Koda ta tadawo dakin sun kammala waya,. Ba tare da tace Mishi komi ba ta buɗe durowa ta sauko wani
tsadadden lass mai matsifar kyau tare da gyale color less ɗin da turare mai matsifar khamshi ta wuce ɗakin
Ummul Kulsum, "ga wannan ki saka, ita ko duk kunya ce ta ce, Mommy ta taimaka ma ta ta shirya "Masha
Allahu madarar kyau Mommy ta faɗa! a hankali ta sunkuyar kai....
★★★★★★.......★★
Abdullahi suna gama wayar ya faɗa toilet ya yi Wonka kana ta fito ya shirya sanye da wata tsadaddiyar
shedda sky Blue sosai kayan suka yi mishi kyau abinka da farin Mutum ga wani irin fitinannen khamshi da
ya ke, a hankali ya fi to da ga ɗakin, dai dai lokacin kuma Kaka ta fito da ga cikin, da sauri Abdullahi ya
sunkuyar da kai cike da kunya, kaka kasa ɗauƙe Idonta ta yi akansa saboda kyau da ya yi mata yau
kamanninsa sak da na Mahaifinshi da dan uwanshi Ibrahim, a hankali ta sauke sassanyan Nunfashi,
"Mama baki Barci ba?"
"Yanzu nan zanci na zo ɗaukar Ruwa ne kasan Nana kullum dare saita farka shan ruwa"
Bata tambaya ina zashi ba shi ko bai bai ga ya ma ta ba duk da ranta ya na bata ina zai tafi.
Bayan ta fiyar Kaka ya fice daga palon Kai tsaye ya wuce gidan Nuraddeen lokacin da ya iso ya kira
Nuraddeen ba jima ya fito Abdullahi sai wani ɗari ɗari ya ke ha kwai gidan ya zamo mishi kaman sabon
zuwa, kai tsaye suka wuce palon baƙi Alhaji Nuraddeen sai murmushi ya ke,"Abokin irin wannan kyau ha
ka Kodai A ɗaura Auren yanzu ka tafi da matarka, dai dai lokacin Mommy ta karaso da Ummul Kulsum da
kanta ke sunkuye ga baki ɗaya a kunyace ta ke, Abdullahi ko ga baki ɗaya ya kasa ɗauke idanunsa kanta
wani irin kallo yake binta dashi mai cike da ma'anoni
"Sannu da zu wa Ango cewar Mommy bayan sun gama gai sa wa Mommy da Alhaji Nuraddeen su ka
wuce,
A hankali ya Abdullahi ya sauke sassanyan Nunfashi kana ,"Ya gida Kulsum!" A hankali ta Lumshe
idanunta ta buɗe akan fusakarsa cikin sanyi Murya ta ce," Lafiya lau"
"Ya su Mama!"
"Alhamdulillahi"
Bada ɓata lokaci ba ya sanar da ita abinda ke ta fe da shi,
cikin Ikon Allah ko buƙatar shi ta karɓi hira suka sha sosai cike da so kaman waƴan da suka shekara a ta
re. Wuraren karfe 10:30 ya yi mata sallama ta re da bata Number wayarshi, har bakin mota ta rakashi baiko
bi ta kan Aminin nashi ba...🤣🤣
Bayan ta fiyar shi Ummu Kulsum ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya tare da yi wa Allah godiya fuskarta
ɗauke da murmushi ta wu ce ciki gida wuraren 11:10 ta kira shi tare da tambatayar ya iso lafiya nan fa suka
barke da hira sun jima suna waya kana su ka yi sallama..
Ranar da haka su ka kwana cikin farin ciki....
Washe gari Abdullahi ya sha tsiya wajen Alhaji Nuraddeen 🤣
(Haba Abdullahi tun ba'a je ko'ina ba ina ga idon Anyi Aure zai manta da Nuraddeen 🤣🤣🤸)
★★★★★
A bunka da manya cikin ƙanƙanen lokaci suka fahimci juna duk wasu shirye shiryen Aure sun kammala
Abinsu, lehe ma tuni ta haɗa abinda tare da Mommy gyara na Musamman Mommy ta yiwa ƙanwar ta ta A
ɓangaren Alhaji Nuraddeen ba'a bashi a baya ba sosai ya gyara Aminin nasa... Ranar jumma'a kaka daura
Aure gagarumin buki aka shirya na gani faɗa. Bayan Isha'i Amarya ta ta re ɗakinta... tarba ta Musamman
Ummul Kulsum ta samu daga wajen Kaka...
Washegari Abdullahi ya gabatar da ita a wajen ƴaƴansa, "wannan sun Nan Mama ga reta Maryam,zo nan
mai sunan Mama!" Fuska a sake Maryam ta nufi wajenta,"Kina Lafiya?" Lafiya"
"Abban Haydar yanzu kowa da Sunan Mama yake kiran ta ba sakayawa? Gaskiya Bazan yadda a
riƙa kiran sunan Mama kai tsaye ba" ta yi maganar cikin gaskiya da gaskiya,"Kaka ko sai kallo su ta ke
tana Murmushi har ga Allah Ummul Kulsum ta

Please Login or Register in order to submit comment