Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 15 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake
jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare
da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya
faɗa a hankali cikin kunnen nata.
idanunsa ƙyam akan Sultana dake ta juyi a jikinsa, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi.
Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna
biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar
barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi
sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka
ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin
kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
Tsawon mintuna biyar suna a haka,
A hankali ya shimfiɗe Sultana a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya, kana ya fito daga palon
Duk kallon Sultan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake
faɗin, “Abba karku damu aikina ne ai. Insha Allahu zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin
allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita,
“Insha Allahu za'a kiyaye. Allah ya saka maka da alkairi, ita kuma Allah ya bata lafiya yasa kaffara
ne”.
A tare suka amsa da amin, "Ni zan tafi, "A sauka Lafiya ina gaida Daddy ku, 20k Abba yaba Salma
gashi kuma sai Ice cream, Abinka da yaro nan take ta karɓe kuɗin tana murna, suna tsaye a wajen har su
motar Sultan ta fice daga gidan,....
Bayan wucewar Sultan duk suka shiga har falon yadda suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai,
Kwanaki Ukku Sultana tayi tana jinyar kanta, amma Alhamdulillah da sauki, dantana samun kulawa daga
Kaka da Mami,
___________★★★★____________
Yau tunda safe Sultana ta shirya zuwa wajen aiki kwanta huɗu kenan bata je ba.ta fito fes Abinta sai zuba
kamshi take, Kai tsaye ta wuce Asbiti kusan lokaci ɗaya ta iso tare da Jidda,
Gaban Sultana yafad'i lokacin da idonta ya sauka akan ya Sultan dake jingine jikin mota, sanye yake da
Shuit Ash color, yayi masifar k'yau, tunda take yaune karon farko data ƙare mata kallo,Jidda tace woow
wlhy Dr Sultan yahad'u Daughter kin more miji gaskiya! Allah nuna min ranar Auren ku!!"
"Ba Amin ba!"
Dariya Jidda tayi tana fad'in ," Ai tun tuni Allah ya ƙarɓi Addu'ar mu"
Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan
ɗaya, har suka shige cikin Asbitin, daga can ɓangaren Aziz yace ," Bros baka jina? A hankali ya sauke
Ajiyar zuciya kana ya fesar da Numfashi,"Ina jikin ka Bros!"
Aziz yaci gaba da faɗin ," jikin Abie ya tsananta sosai Wallahi! Harta kai ga sai amma sa aiki a zuciya,
Sultan ya sake Nannauyan Ajiyar zuciya tare da farin ,"Allah ya bashi lafiya!"
"Amin Bros! Ya shirye shiryen Aure wai Ni kam har yanzu baka haɗani da matar tamu ba, Murmushi mai
sauti Sultan ya yi tare da faɗin ,"zaka ganta idon lokacin ya yi, " Bros nifa Very Soon Zanyi Auren nan, cike
da farin ciki Sultan yace ,"Allah ya nuna muna!"
"Amin Bros Ina gaida Amarya kuma In sha Allahu Aure saura sati ɗaya zanzo, da ga haka sukaci gaba da
yin waya, zuwa na ɗan wani lokaci kana ya wuce Office...... sai ƙarfe Shidda suka tashi, Sultana na ƙoƙarin
shiga Motarta Jidda ta Kalleta cike da tsoka tace ," Daughter duk yadda namiji yake sonki karki taɓayin
wasa da damarki har kici masa mutunci da rashin kunya, a duk lokacin da nakilli Dr Sultan nakan ga
tsantsan Soyayyarki a cikin idanunsa wanda ke kika kasa ganewa, Sultana ta taɓe baki tare da faɗin,"Aure
mafi daɗi da.kwanciyar hankali, babu kamar Auren wanda kake so yake sonka!!"
Sultan dake bayan su yana sauraren duk a binda suke faɗi, kai kawai ya sunkuyar yaci gaba da tafiya har
zuwa wajen motarsa ya shiga ya yi tafiyarsa...
Jidda tuni ta yi mutuwar tsaye, Sultana ko a jikinta, haka ko wannen su ya shiga motarsa ya wuce gida...
Sultana ya isa gida ta watsa ruwa tayi sallah, woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan
sautin kiran kawai ke shaida mata Nas ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara
magana a waya cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba,
Ido ta lumshe cikin sauk'e ajiyar zuciya tace.
"Hubbyna!"
"Na'am."
Yace mata tare da cewa.
"Sultana kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in banji
muryar ki na awa 3 ba Sultana ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki."
Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa maƙoshi tace
" Hubbyna ka kontar da hankalin ka Sultana taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin raina ko
bacci nake muyarka nake jiki a kunnuwata.
A can Ɓangaren Nas kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana
mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na ratsashi har
cikin k'ahon zuciyarshi,
yayin da ita kuwa Sultana take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar kasan cewa a
haka suna musayan zantukan so masu sanyi,
ji take matuk'ar babu Nas a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita.
Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna, bayan ta gama wayar tayi salla Isha'i kana ta wuce
Palo Abinci suka ci gabaki ɗayan su kana kowa ya wuce makwancinsa......
_*five Weeks Ago_*
Kwanaki nata shurawa, bikinsu Sultan na ƙara matso gab.
Sultana tanashan gyara wajen Mami da Kaka,
Ga Mamie tatsaya akanta wajen koyamata girke-girke dazama da miji,
Tayi k'yau harta gaji, Kaka ma Na koya mata dabarun zama da miji irinna zamaninsu, sosai Sultana take
fahimtar komai daki-daki.
Sati ɗaya kenan da dawowar Mommy daga Dubai wajen haɗo lefen Sultana.
Yauma da kamar kullum Bayan Isha'i Mami ta saka Sultana a ɗaki Mami ta b'alle marfin wani roba sannan
ta jijjiga tare da mik'ewa Sultana d'in cikin tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."
Kai Sultana d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah Mami a barni hakanan." Ba yadda ta iya dole ta karɓi gorar ta sha ye tas,
Mami na fita Jidda da Meena suka shigo ɗakin,
Jidda tace ,"Allah dai ya biya Mami yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da baya
magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Meena ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty Jidda wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Dr Sultan ,"
Haka suka rink'a tsokanar Sultana,
Abba tuni ya kammala kayan ɗakin Sultana da duk wani Abin buƙata a ɓangaren Kaka duk wani Abin
gargajiya ta seya Sultana...
Washe gari Aka kai lefen Sultana, Set shidda, kowa nata yaba lefen Sultana, ba ƙaramar dukiya a ka barke
ba,
A ɓangaren Sultana kowa ba Abinda kecin zuciyar Sultana bai wuce Nas ba, musamman y'an uwanta keta
shirye-shirye da
Duk yadda tayi banza da maganar Auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka
kawai sai tsoro ya shigeta,
Sultana ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta komai nata yasha gyara sai wani
k'amshin mai Daɗi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman,
*Sultan*
Ƙarfe biyar ya nufi Airport, ya na isowa jirginsu na sauka, a hankali wani kyakkyawan Saurayi ya ke
saukowa daga jirgin, tun bai gama saukowa ba Sultan ya nufi wajensa cikin tsananin farin ciki suka
rungume juna..kai tsaye suka wuce Hotel,annan suka cigaba da shagalinsu,
Sultana yau ta wayi wagi cike da mutuwar jiki, a hankali ta mike daga kwancen da take ta ɗauƙi wayar ta
dake ringing ta ɗaga, cikin raunin murya mai haɗe da kuka tace.
"Hubbyna nayi ma al'kawarin ni taka ce har Abadan bazan bari wani yayi nasarar rabamu ba,
nayima alk'awarin zan adana maka kaina zan killace maka jikina ba wani mahaluk'in da zai zama hijabi a
tsaka nin mu."
Sai kuma tayi shiru tare da sheshshek'an kuka murya na rawa tace.
"Sultan zai rayu cikin bak'in cikin rayuwa tunda har ya kasance a sanadin shi za,a rabamu ,
bazai sake samun farin ciki da konciyar hankali ba gidan shi zai zame mai tamkar kurkuku zai rayu cikin
k'unci da bank'in da tashin hankali ta yadda shida kanshi zai sauwa k'amin,
Sai kuma ta saki kuka mai tsuma zuciya,
Nas Kuma lallashin ta yake cikin raunin murya yake cewa.
"Kiyi hak'uri Sultana ki daina kuka ki sani har Abadan kina cikin raina bazan dena sonki ba,
da ƙarfi aka bankaɗo ƙofar ɗakin,
Abba Yayi mata wani irin kallo cikin tarin mamaki da jin zafi a ranshi murya can k'asa yace.
"Mamana! duk wannan kukan kina yinshi ne dan zaki Auri Sultan?
Mamana Ashe har yanzu kina kan bakarki?,
"Abba wlh na tsaneshi Bana sonshi,
Wata irin gigitcciyar ƙara ta saki da k'arfi tare da dafe fuskar ta jin wani irin zazzafan mari da Abba ya
zuba mata cikin huci da zafin rai ya nunata da yatsa murya a hargitse yace.
"Wallahi koda mutuwa zaki sai kin Auri Sultan ina ya so Aiki gawarki a gidan sa!"
Kife kai Sultana tayi a bakin gado ta saki wani irin kuka mai cike da zafi a zuciya kuka mai cushe
zuciya gaba d'aya jikin ta sai karkarwa yake,
Abba ko har cikin ranshi yake jin tsanar Nas tunda a kan Nas ne Sultana take furta kalaman k'iyeyyar kan
ɗan Aminshi da duk duniya Baida kaman sa, haka kuma yake jin zai iya yiwa Sultana ko wanne hukuncin
matuk'ar zatayi wa Sultan d'in rashin mutunci,
Sultana kuka take kamar zata had'iyi zuciya ta mutu,
Mami yayi ta lallashin ta amman ina,
Haka har dere yayi Kaka. kam ko ta kanta bata kuma biba dan inta tsaya kusa da ita tana jin tausayin Jikar
tata,
har dare Sultana tana kuka ne hannun ta dafe da kanta,ta kuma kifewa kan kago ta ci gaba da kukan da
sautin shi baya fita dan muryar ta ta dashe, Meena da Nana duk taisayin Sultana ya cika su,
Washe gari haka ta tashi jiki a mace,
tun da sassafe gidan su yake cike tib da bak'in haka yasa Sultana ta takure kanta cikin d'aki akan gado
kaman ba Amarya ba sam bata da walwala.
Mami dake zaune a ɗaki tana shirin Kiran Sultan ya shigo a wayar ta, ta ɗaga a hankali tace ," Sultan ya
dai?" daga can ɓangaren Sultan," Yace Mommy ɗazu na mata Atm ɗina ina wajen Bazan iya shigowa ba
mutune sunyi yawa a gida," Mommy ta yi Murmushi tare da faɗin ,"lalle Ya tona ya girma,"Mommy ya
kira sunanta cin Shogoɓa," Shike nan bari na ɗauƙo sai naba Salma ta kawo ma,
Bayan ta kammala shirinta ta wuce ɗakin Sultan, a hankali ta buɗe ɗuwar madubi, karab Idanunta suka
sauƙa kan A kwatin Azufar nan cike da mamaki ta riƙa kallon A kwatin, Atm ɗin ta ɗauka dake gefen
Akwatin har takai baƙin ƙofa ta sake dawo wa,
Haka kwai take jin son buɗe A kwatin, cikin wani irin yanayi da bata san namiye ba, ta soma buɗe
Akwatin cikin Sa'a idanunta suka sauka kan hoton dake sama mai Black and write, da sauri ta wace manya
idanunta tana kallon mutanen dake cikin hoton Zuciyata na bugawa da ƙarfi, cikin murya na na rawa ta
soma faɗin,"Adda Sal......ma......✍️
Is sha Allahu gobe idon Allah Ya kaimu zan kammala Book 1
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬



Bismillah........ ✍
PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta
wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number
08149979652. Nagode🤗
*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 39-40*
____________"Adda Sal...Salma, dai dai lokacin a ka Turo ƙofar ɗakin, "Anty Ina key ɗin part ɗin Sultan?
zamu saka kaya a ciki, ganin Mommy bata tanka ba yasa ta nufi wajenta ta sake cewa "Anty Lafiya? Sai
kuma ta kai Idonta ga hoton da Mommy take riƙe da shi, Allah sarki Bappa da Nenne Allah ya gafarta
muku, hawaye ta share cikin raunan'nanyar murya tace ,"Amin"
"Amman Anty Me Hoton su Bappa yake a ɗakin Sultan?"
"Ni ma ban sani ba"
tsaye sukayi a ɗakin sunyi Zugum, kowa da abinda yake tsaƙawa a Ranshi,
A ɓangaren Sultan ko zaune a mota yana jiran Atm ɗin sa shiru shiru har tsahon wani lokaci sai faman kiran
Mommy yake aman ba'a ɗaga ba, hakan yasa ya nufi cikin gidan, batare da ya so hakan ba, tun da ya saka
ƙafarshi a palon hankalin Mutane suka dawo kansa suna faɗin Maraba da Ango" cike tsakanin kunya ya
nufi ɗakinsa, tsaye ya tarar da su sunyi cirko cirko, cike da tarin Mamaki ya riƙa binsu da kallon
Musamman Mommy dake riƙe da Hoto, cikin ƙoƙarin danne abinda ke ranta tace ,"Sul.... Sultan na Barka a
tsaye ko?"
Makom ya bata Amsa, ya jefe mata tambaya ,"Mommy lafiya? mike damun ki?"
A karo na farko ta saki Murmushin ƙarfin Hali Kana tace ,"Ba komi Sultan"
Mami tace ta yi ƙarfin halin faɗin ,"Sultan ina kasan mutanen nan dake cikin hoton nan?"
Nannauyan Ajiyar zuciya Sultan ya sauke kana yace ,"Mami Dengin Mahaifiya tace!!! "
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da su," Mami tace Degin Mahaifiyarka Sultan? Wace
Mahaifiyarka a ciki?"
cikin raunatattiyar Murya yace," Ummul Salma!!!" Nan take hawaye Masu matsifar Zafi suka zubo
Mishi,
Kallon kallon aka tsaya yi tsakanin Mommy da Mami, dai dai lokacin Kuma Daddy ya shigo ɗakin, "Ina
fatan Lafiya? Daddy ya yi maganar yana kallon su,
"Sultan yanzu kana nufin kai ɗan Adda Salma ne!!!"
Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa musu kai,
A karo na Biyu Daddy ya sake tambatayar Lafiya?
Mami ta sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Abban Sultan! Sultan ɗan Adda Salma ne Sultan ɗan
yar Uwar muce.*A DALILIN SO* Muka zamo Tamkar *JINI ƊAYA* Daddy ya sauke Nannauyan
Numfashi kana yace,"Allah mai Iko!!,
Zama sukayi Ga baki ɗayan su, cikin tarin Ruɗu dake tattare da Sultan yace ," Mommy ku fahimtar dani
mike faruwa"
Mommy ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana tace.....
*WAI WAYE A DON TA FIYA*
"Alhaji Abubakar Siddi shine sunan mahaifinmu, haifaffen garin dawakin tofa ne dake jahar Kano,
Asalinmu Fulani ne, Mahaifinmu babban Attajiri mai darin dukiya da garken Shanaye da tumaki, Matarsa
ɗaya a duniya Zainabu yar Gwoggon sa ce, Mu Ukku ne a wajen iyayen mu, Kuma duka mata Ummul
Salma, Ummul Khairi, Ummul Kulsum, mun ta so cikin kyaunar Junan haka muke Rayuwar cikin
kwanciyar hankali da kyaunar juna, wata rana Bappa ya fita da safe zaije masallaci, yaci karo da wani
kyakkyawan Saurayi Mai Suna kwance a ƙofar gida cikin wani irin Mummunan yanayi Ya shigo dashi
cikin gida tare da bashi taimakon gaggawa, kwanansa Ukku yana jinya, bayan yaji sauƙi Bappa ya bashi
masauƙi a gidanmu saboda ya fahimci saurayin Bai san kowa a garin ba, sannu a hankali shaƙuwa mai
ƙarfim ta shiga tsakanin Bappa da saurayin har kiwo yake ma Bappa, ana cikin haka Soyayya mai ƙarfi ta
shiga tsakanin Adda Salma da Abduljalil, Allah ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini. ba wani
ɓata lokaci Bappa ya ɗaura musu Aure, tare da basu muhalli zama, Rayuwar suke cikin so da kyaunar Juna,
Adda Salma ta jima bata haihu, Auren su nada shekara Huɗu aka haifi Abdulmalik, lokacin Ni kuma nayi
Auren Kulsum tana gidana, Abdulmalik nada shekara ukku Kulsum ta yi Auren, itama Saida ta shafe
tsawon shekara Ukku sannan ta samu ciki, lokacin da cikin ta ya isa haihuwa, nazo ta zauna a wajen
Amman Nenne yaƙi yadda haka yasa Kulsum ta koma gida anyi dai dai Adda Salma ma nada ciki, kusan
lokaci ɗaya suka haihu da Adda Salma, Kulsum ta haifi ɗa na miji aman baizo da rai ba, tashiga tashin
hankali sosai, saboda gorin da take sha a wajen dengin mijin da suke kiranta juya,ganin Halin da Kulsum ta
shiga na tashin hankali yasa Adda Salma ta saudakar da yarta ga Kulsum ita ko karɓi ɗa najimin matacce a
matsayin nata... Ranar Suna Yarinya taci Suna Aminatu, da sauri Daddy da Sultan suka maida Kallonsu ga
Mommy dake ci gaba da faɗin, ba wanda ya san da maganar daga Ni dai Adda Salma da Kulsum ɗi,
Lokaci kafin Kulsum ta koma ɗakin ta, Kowa yaga Aminatu sai yace kamanninsu sak da Adda Salma, duk
lokacin da akayi magana Adda Salma takan nuna musu ai ba wani Abu bane don Aminatu tayi kama da ita
tunda duk Jini ɗaya suke, hakan yasa muke samu tsanuwa a ranmu, bayan Kulsum tayi Arba'in ta koma
gidan mijinta... Ranar Kulsum ta cika wata ɗaya da koma a rar faɗa ya caƙuɗe tsakin fulani da makiyaya in
da akayiwa iyayenmu da yanzuwan mu kisan gilla... Washe garin bayan faɗan ya lafa muka wuce
rugarmu,mun shiga tashin hankali sosai, ganin gawar Bappa da Nenne kawai muka ganin, ba irin neman da
bayiwa Adda Salma da Abduljalil da Abdulmalik, lugu da saƙo na rugugarmu mun neme su mun rasa, daga
ƙarshe muka haƙura da neman su, satin mu ɗaya a ruga muka dawo Kano cike da kewar Yar uwarmu da
muke rasa....... Mommy ta ƙara sa maganar cikin raunin Murya.
Wannan kenan🤗
★★★★_________
Meena dake tsaye bakin ƙofa tana jin duk abinda Mommy take faɗin, nan take jikinta ya soma rawa, daman
tare suka zo da Mamk tashi ta shiru shine ta biyo bayanta ashe da rabon taji me suke faɗi, cikin wani irin
yanayi ta buɗe kofar ɗakin ta shiga tare da faɗa wa cikin Sultan ta rugumeshi tana kuka mai tsuma zuciya,
Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa,
Kamar an watsa mishi ruwa.
Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa. Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne
yakeji yana jujjuya mishi
Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi, idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai
sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin. Ita Meena sai ƙara shigewa jikinsa take
tana shaƙar dadɗan khamshi turarensa...
"Allah mai iko Daddy ya faɗa ya faɗa cikin wata irin murya mai cike ruɗu.yanzu da Sultan da Meena uwa
ɗaya uba ɗaya suke, kai Mommy ta gyaɗa mike, Murya a rauna ce Mami tace ," Na jima ina zargin Sultan
nada alaƙa damu duk sanda na kallesa nakan kammanin ya Abduljalil A tattare dashi,wani lokaci kuma ya
kanyi min kama da Adda Salma"
Murya na rawa Mommy ta soma tambatayar,"Sultan ina Adda Salma da ya Abduljalil?"
Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son kubce Mishi yace ,"Ammie na da Abie duk sun rasu!" da gan ya
soma basu labarin rasuwar da sukayi tare da Mahaifinshin kafin ya rasu, Mahaifiyashi kuma bazai iya tuna
komi a kanta, ko da abin ya faru yana ɗan shekara Shidda.
Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciya,"Allah ya jikan su da rahama Allah yasa sun huta!"
"Amin"
A hankali Sultan ya janye Meena daga jikinsa ya share mata hawaye kana ya sakar mata Murmushi ƙarfin
lahi, sai yanzu ya gane dalin da ɗasa yake Masifar kaunar Meena ace jini ɗaya suke....
Cikin tsananin so ɗan Uwan nata tace "Ya Sultan idon an daura Aure zan dawo gidanka da zama!!"
Murmushi ya sakar mata,
"Allah abin godiya! Ina son maganar nan ta tsaya iya tsakanin muna, bana son kowa yaji har sai ranar da ya
ce,
"In sha Allahu Daddy!"
Yauwa a je aci gaba da shirye shiryen, Cikin mutuwar jiki Sultan ya fice daga ɗakin tare da Daddy.
_____________★★★★
Haka a ci gaba da shirye shiryen Ta ko wanne Ɓangaren, yau jumma'a sun safe ake ta shiryen shiryen
walima,. Tsab Sultana tai shiri da kayan da jidda ta kawo mata ɗakin Mami . Lass mai matsifar kyau da
tsada sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa
ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske
da cikar gashi. Turaren ta fesa tana zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da
tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa.Ta saka sarƙa da sauran kayan
adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma
blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Su jidda ma tuni sun kammala shirin su tsab,
Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi
tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani,
Alhamdulillahi, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka yi wa'azi masu ratsa jiki ga ma'abocin
saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin
magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya,
Tunda aka tashi da walima jikin Sultana sai ya sake yin sanyi, Palon Abba ta nufa sallama, daga ciki
suka amsa mata da bata iznin shiga.
“amarya da kanta. Miya farune?”. mami ta faɗa tana murmushi. Kallon Kaka da batace komaiba
Sultana tayi, sai kuma ta duƙar da kanta hawaye na cika mata ido. Mami tace, “Kinga zonan”. mamana!
tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ƙasa jikin ƙafafun Kaka data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan
da shigowar Sultana ba.
"Anty Sultana gobe War haka kina gidan ya Sultan! hawaye suka gangaro mata a kumatu, ta kwantar da
kanta bisa cinyar Kaka tana jan ajiyar zuciya a jajjere.
Dauriya kawai Kaka keyi dama, taja ɓoyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Sultana. “Ke
kuma me ya sameki?
"Kaka don Allah ya gaya Abba bana son Auren, A aura masa Meena ko Ihsan harda Jidda ma idon yana
so!"
Sosai abin ya basu dariya,
cukuykuye ƙafafunta tana kukanta, "Kaka wallahi banaso Sultan!"
Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Ta sake matso hawayen
masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe
“Haba Sultana kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya
a jajajjere.
Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Mami wallahi bana son Auran, "Sultan ɗin ne
baki so!!" kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi.
Mami ta sauke Nannauyan Numfashi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta.
“Kalleni Sultana”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda
kukan data sha ta saukesu akan Mami ”. “Kukan ya isa haka kinji Mamana, kicire komai a ranki babu
abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsanar sa da kike ci zai koma Soyayya ki cire tsanar Sultan a zuciyarki,
kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan Allah ya kaimu, fatanmu Allah ya sanya albarka a al'amarin ya
baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Allah yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da
lahira”.
faɗawa jikin Mami Sultana tayi tana kuka, sake fashewa da wani sabon kukan, “Mami Wallahi ina
sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wallahi saina kashe kaina idon ba'a autamin Nas ba, Mami
wallahi Nas nake so....!
Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata

Please Login or Register in order to submit comment