Reading Dr Sultan by Sadeeya Ka`Oje Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta aje mishi abincin sa yaci, Kaka na janshi hira har ya kammala, dai dai lokacin Maryam ta
iso riƙe da perpar," Ya Maleek duba ga ki waye wannan?" A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe
akan takardar, da sauri ya runtse idanunsa, wani irin Amitattacen Nunfashi mai cike da yanayi na
Musamman ya fesar da idanunsa suka kan Hoton da jikin takardar, "Ya Rabbi!!" Shine a binda ya iya furta,
a hankali yaci gaba da kallon kyakkyawan Saurayin da ke cikin takardar, Kaka ma zajen take kallo,
"Maryam waye kuma kika zana?"
Wani irin sassanyan Nunfashi ta fesar," cikin sanyi Muryar tace,"Kaka Ya Maleek!! Ne"
Wani irin lumshe idanunsa ya yi, wani irin kallo mai tafiya da dukan natsuwa yake binta dashi tun daga
farko hoton har zuwa sama ina Aka rubuta YAYA ABDULMALIK da manƴan haruffa, hoton shine sak
Maryam ta zana, zane na ɗaya daga cikin bawarda Allah ya yi Maryam, "Maryama ta!" Nina kika zata
haka, ai zanen ya fini kyau, Harara ta zabga mishi, murmushi yayi tare da ƙarɓan zane yana Kallo,
"Maryam ta! Allah zanen nan ya fini kyau!" da sauri Abdulmalik ya juya yana kallon Kaka," Kaka da zanen
nan dani wa yafi kyau!"?yadda yayi maganar da kuma yadda ya marairaice abin yaba Kaka Dariya,"
fusakar Kaka ɗauke da murmushi tace ," Abdulmalik ai kafi zanen nan kyau kaifa kyakkyawa ne! Ma sha
Allah!"
Rau rau Maryam tayi da ido sai kun ta ta tsuke fuska kana tace ,"Ya Maleek kaifa kyakkyawa ne!"
Abdulmalik a hankali ya tauna lips kana yace," Ki bani hoton nan na tafi dashi ɗakina"
Harara ta dalla mishi ,"Allah Bazan Bazan ba daba, Saida na zana ma wani ta karasa maganar cike da
tsiwa da murguɗa baki, Abdulmalik ya yi Murmushi, haka suka kasance cikin farin ciki zuwa bayan Isha'i
bayan sunyi gama karatu suka ɗanyi hira kana ya wuce gida cike da gajiya...
Yana isowa ya ɗan yi yi gyare-gyare a ɗakin.Abdulmalik Gwani ne a fanni tsabta kana ya yi Wonka ya
kwanta nan take bacci gajiya ya yi awon gaba shi....
Washe gari ranar baije kasuwa ba wonki yayi musu kayanshi dana Kaka da Maryam, Maryam na tayashi
gwanin burgewa, "Kinga ki Dena wankin Nan kar lallenki ya goge, "Ya Maleek idon ya goge Kaka zata
min wani, haka suka ci gaba da wonki har suka kammala, ranar gabaki ɗaya a gidan kaka ya yini sai dare
ya wuce gida tare da kayan shi da wonke Kaka sai saka mishi Albarka take.....
A hankali Rayuwa taci gaba da tafi cikin kwanciyar hankali tuni su Maryam sun koma Makaranta, sosai ta
maida hankali wajen karatun, duk abin ya shige mata duhu takan tuntuɓi Abdulmalik, hakan yasa komi ke
zuwa mata da sauƙi, a ɓangaren islamiya ma ba'a barta a baya ba, Rayuwar suke cikin kwanciyar hankali
da ƙaunar juna, zuwa yanzu Maryam Na gaba da cika shekara goma sha ukku a duniya,
A Ɓangaren Abdullahi ma duk bayan wata ɗaya yakan aiko musu da kayan Abinci kaman yadda ya saba da
duk wani abun buƙata, kusan kullum sai ya kira su, Abdulmalik da Abdullahi basu taɓa haduwa kasan
cewar yana jimawa bai zo ƙauye ba saboda yanayin aikin sa, duk lokaci zaizo ko tunda safe yake zuwa
haka zai zauna suyi hira da Kaka harzu zuwa lakacin da Maryam zata dawo daga Kamaranta, kana ya wuce
Kano...
“Kaka Abba ya Kira, kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga, cikin sanyi Murya ta soma magana "Abba ina
wuni ya gida Abba ina su Haydar"? daga can ɓangaren Abba ya sauke Ajiyar zuciya Kana," Mamana Lafiya
lau suke, Ina Mama"? "Gata Abba" tayi Maganar ta re ɗorawa Kaka wayar a kunnen,
"Abdullahi Ya gida"? ta faɗa cike da kewar ɗanta, " Lafiya lau Mama" cikin raɗa Maryam tace "Kaka
ga ki gaya mishi na kusan sauka, ranar walima yazo dasu Haydar" Kaka ta talla mata Harara,nan take
Maryam ta tsuke fuska tana turo baki, haka suka ci gaba da hira gwanin burgewa, Kana kaka ta mikawa
Maryam waya nan ta sanar da shi abinda ta gayawa Kaka," Insha Allahu zamu zo tare, Kafin nan ma zamu
shigo Ranar Assabar tare dasu, wani Irin daɗi Maryam taji, sun jima suna hira tana bashi labari Abdulmalik
da yajima da sanin sunan sa a baki, Kafin nan sukayi Sallama,
cikin wani irin ya nayi mai ɗauke da tsantsan farin ciki.tace , " Kaka Abba ya ce zasu zo ranar Assabar
tare da su Haydar! Allah ya nuna Muna," Amin Kaka..."
Washegari tunda da sassafe Abdulmalik na shigo ta bashi Labarin su Haydar zasu zo, "Ya Maleek karka je
Kasu kaji," "saboda me?"
"ka zauna gida muyi hira tare dasu Haydar"
"Maryama ta! Idon na zauna a gida wazai min aiki na?"
"Ya Maleek don Allah fa nace"
" Shike nan zan zauna Amman idon suka jima basu zoba zan wuce kasuwa kin yadda"
"Ehh Na yadda na san Abba da wuri zai yake zuwa duk lokacin da zai zo"
"Nadai faɗa Miki"
"Naji" ta faɗa cike da tsiwa tare da murguɗa baki"
"Wannan bakin wata rana saina canye shi idon baki dena murguɗa shi ba"
Kallonta Abdulmalik ya yi kana ya yi Murmushi a hankali ya ce ,"Maryama Sarkin tsiwa"
A gurguje suka karaya ganin lokaci na tafiya, lokaci ɗaya suka kammala kana sukayi Kaka sallama kai
tsaye suka wuce makaranta daga can ya wuce Kasuwa.... sai dare ya dawo,
Yau take Assabar tunda sassafe Kaka ke aikin Abinci nan take gidan ya gauraye da ƙamshi mai daɗin
gaske koda 8:30 tayi Kaka ta kammala komi tare da taimakon Maryam suka gyara gida tare da kunna turare
mai matsifsr ƙamshi da saka natsuwa.....
Wuraren 8:46 Abdulmalik ya shigo gidan, "Kaka ina kwana,
" Lafiya lau Abdulmalik"
" Kaka baƙin basu iso ba?"
"Nunfashi Kaka taja kana ta fesar,"muma zaman jiran su muke Abdulmalik"
"Gashi har 9 ta kusa ni zan waje kasuwa" wani irin Kallo Maryam ta watsa mishi"
" Ai kam gaskiya ne ba'a san ranar zuwan su ba ga abincin kanan"
" Nagode Kaka!" A tsanake ya soma cikin Abinci bayan ya kammala ya wuce,
" Wai wannan fushi duk na miye haka cewar Kaka" turo ɗan ƙaramin bakinta tayi "Kaka ba Ya
Maleek ba ne yaƙi tsayi ya ga su Haydar"
Kaka tayi murmushi kana tace," to ai ba laifinshi bane sune basu iso da wuri ba kuma jiya Saida ya gaya
Miki idon basu zo da wuri ba zai wuce kasuwa kike ce kin yadda to miye kuma abin ɓata rai"
"Wallahi ba ruwa dashi bari ya dawo" dai dai lokacin sukaji tsayuwar mota a ƙofar gida, Kaka ta sauƙe
sassanyan Nunfashi, can ƙasan maƙoshi tace "Alhamdulillahi Allah na gode ma da ka kawo su Lafiya"
Cikin tsiwa Maryam tace Kaka wallahi sun iso" da sauri ta mike har tana batun faɗuwa,
"Mamana kiyi a hankali karkiji ciwo!"
A hankali ta Lumshe idanunta kana ta buɗe akan fusakarsa kyakkyawan dottijon dake tsaye a harabar
gidan dogo ne fari sol da sauri Maryam ta iso wajensa tare da rungumeshi "Abba sannu da zuwa!"
"Mamana! Kina lafiya!?"
"Lafiya lau Abba!" A hankali ta janye jikinta daga nashi"Abba ina su Haydar!?" dai dai lokacin suka shiga
cikin gida su Ukku sanye shedda mai matsifsr kyau da tsaya sosai kayan sukayi masu kyau, da sauri
maryam ta iso wajensu ta rungumesu gabaƙi ɗaya tana faɗin ,"Ƴan ƙanne na! Mai ɗan girma cikin su ya
harareta....... duka shekara nawa kika bamu? ya ƙara sa maganar cikin tsokana, " Koma dai nawa ne ai na
girmeku......
A hankali ya nufi inda Kaka take zauna ya durƙusa har ƙasa cikin girmamawa ya gaishe ta,"Mun sameku
lafiya Mama!" Cikin sanyi Murya tace ," Lafiya lau Alhamdulillahi"
Haka suka zage Kaka gaba ki ɗayan su Kana suka Gaisheta, cikin tsananin farin cike ta bi su ɗaya
bayan ɗaya tana shafa kansa tare da sanya musu Albaka, "Malam Gwani ya Makaran?"
"Lafiya lau Kaka"
"Masha Allah ya maman ku?"
"Kaka Momy bata da lafiya! komai bata iya yi sai masu Aiki sunyi mata"
da sauri Kaka ta maida Kallonta ga Abdullahi, murya a dishace tace ,"Gaskiya ne abinda Malam Gwani ya
faɗa? Kai a sunkuye yace ," Jikin da sauƙi sosai"
" haba Abdullahi me saya tun lokacin baka sanar dani ba!"
" ki gafar ceni Mama"
"Ya jikin nata yanzu mike da munta kuma?"
"Cikon sugar ne Mama"
"Allah ya bata lafiya" ga baƙi ɗayasu suka Amsa da Amin, "kira min Ita mugaisa ba musu ya kira, Kaka
tayi mata ya jiki basu wani jima sukayi Sallama Kasan cewar ba shaƙuwa a tsakanin su,
dai dai lokacin Atiku Direba ya shigo gidan dauke da ledoji niki niki, cikin girmamawa ya gaida Kaka kana
ya fice daga gidan,
"Maryam tashi ku kai mishi abinci gaba ki ɗaya su suka miƙe zuwa kicin suka ɗauƙi Abinci kana suka kai
mishi.
Koda suka dawo Kaka ta jera masu Abinci haka suka zauna cikin Abicin cikin natsuwa da kwanciyar, sai
sontin Abinci suke,
Bayan suka gama cikin Abinci suka tattara kayan zuwa kiciin,
Kaka da Abdullahi suka ci gaba da hira yaushe gama, nan yake faɗa mata irin ciki gaban da yake samu a
kasuwanci su dukiyar Maryam ma sai haɓa ka take, Kaka ta yi farin ciki sosai da wannan maganar,
A ɓangaren su Haydar kam sai wasar su suke, gwanin burgewa, Ranar dai haka suka kasance cikin
tsantsan farin ciki, sai gab da maggariba sukayi Kaka Sallama kana suka wuce, cike da kewar zuna, Kaka ta
haɗa masu kayan tsaraba irin na kyauye, lokacin da suka wuce Maryam Hadda kukanta, har ga Allah tana
son Kasan cewar da ƴan Uwanta,
Har bayan Isha'i fusakar a tsuke, Koda Abdulmalik ya shigo gida Kaka na ɗaki, ko inda yake Maryam bata
kalla ba,
"Cikin sanyi Murya ya kira sunanta "Maryama ta!"
Miƙewa tayi tare da barin wajen, a hankali Abdulmalik ya sauke sassanyan Nunfashi tare da fesar da
Numfashi, A karo na biyu ya sake kiran sunanta "Maryama ta! Maryama ta!! Maryama ta!!!" tuni ta shige
ɗaki ,
durƙu sawa ya yi a wajen cikin zazzaƙar Muryar shi mai cike da natauwa ya soma rare mata wakar Umar
M Sharif ( Maryama) wanda duk lokacin da tayi fushi ita yake rera mata,
🎶" Ina kike Masoyiya! na duba gabas ban ganki ba na duba Arewa ban ganki ba naje kudu ban ganki ba
naje Yamma ban ganki ba! Ehya ya ya oh yah yah yaushe zaki yaushe zaki zo! Yaushe zaki zo
Masoyiya!...... naga ƴan mata iri kyawo baza su fiki ba! Kalaman so kashi kashi banji salo irin naki ba
kyan halinki ba'a faɗa baki hanya wuce gaba gata nan tafe🎶gata nan tafe gata nan tafe Masoyiya 🎶gata nan
tafe tana zuwa!🎶 Maryama zo Maryama zo Maryama zo Masoyiya!!! 🎶 Kinza ma Ni nazama ke komi
zanyi done Saida ke banci abinci inbabu ke Nagode Allah daya bani ke! Maryama Maryama ta iya kalliya
Maryama mai kyau da dariya Maryama!!! Lala lalaye Maryama zo Maryama🎶💖💋
Yana mai ƙarshe baiti ta fito ɗakin a guje ta faɗa ƙirjinshi ya rungumeta da karfi Ya runtse idanunsa "Ya
rabb" ya faɗa a ƙasan maƙoshi,
Kanta ta manya a ƙirƙijinsa tare da sa hannuwanta duka biyu ta zagaye ƙugunshi tare sakin sassanyan
Ajiyar zuciya,
Runtse idanu sukayi lokaci ɗaya tare da sakin sassanyan Ajiyar zuciya, "Maryama ta!" Kin Dena
fushin? a hankali ta gyaɗa maishi kai, a hankali ya janye ta daga jikinshi, lokaci ɗaya suka sakarwa junansu
Murmushi.
"Ya Maleek kana fida su Abba suka iso ta karasa maganar cike da Shogoɓa,
"Ayya Maryama ta Allah bai kadda zamu haɗu ba! Amman Insha Allah wata rana zamu haɗe a tare!"
"Abdulmalik an dawo cewar Kaka,
"Ehh Kaka na dawo ya baƙi"
"Lafiya lau yanzu mukayi waya har sun isa gida"
"Masha Allah, Allah ya wutar da hajjiya Allah kuma ya basu ladan zumunci"
"Amin ya rabbi Abdulmalik" ga abin cinka nan, tare suka ci da Maryama suna ci yana tsokanar ta har
suka kammala, kana sukayi Karatu, nan Kaka ta kawo musu kayan marmari da Abba ya kawo musu,
Abdulmalik yana ci yana. Lumshe ido Allah ya sani yana son kayan marmari, bayan sun gama shan kayan
marmarin ya wuce gida.....
A hankali Rayuwa taci gaba da shuɗewa , tuni su maryam sunyi sauka aka haɗa musu gagarumar walima
kusan komi Abba ne ya ɗau nauyi komi ranar walima Malam Gwani da iyayen Maryam sunsha Addu'a,
Ranar walima su Haydar kaɗai suka samu damar zuwa, Abdulmalik ya taka muhimmiyar rawa a wajen
walimar, haka tare ya tashi lafiya,
A ɓangaren kubra ko jikin tana sai ƙara tsauri yake, wani lokacin har gado aka bata Asbiti, gabaƙi ɗaya
Abdullahi baya cikin Haiyacinsa, kullum sai kaka ta kira taji yakinta..... Haka dai kwanaki suka ci Baga da
shuɗewa..zuwa yanzu Maryam ta fara girma,
Kwance a take a tsakiyar gida sai juyi take,"Kaka ƙirjina ciwo yake har yanzu Kaka wlh gobe idon naje
makaranta sai na rama, "Kiyi Haƙuri tunda tace ba da saninta ta buge ki ba, daman idon ana ƙidan degin
hake abu kaɗan saiya taɓa wajen, nidai wlh Kaka saina rama itama gidan dengi take taji irin zafin da
nakeji!"
"Ohni Mairamu" cewar kaka shegen jini nin tsiya ginga tafiya ta, a hankali Kaka ta nufi ɗaƙi, dai dai ya
Abdulmalik ya shigo, da sauri ta mike zaune tana faɗin "Maleek kalli Ubaidah ta ɓararmi da ƙidan dengi
na tayi magana tana ƙoƙarin buɗe gaban rigarta da sauri ya dakarta ita ta hanƴar daga mata Hannu,
"Ya Maleek duba ka gani wlh ciwo suke min da sauri ya runtse idanu wansa cikin wani irin yanayi da
shi kanshi ba zai tantance wani iri ne ba " ya Salam" da sauri ta maida rigarta cikin tsiwa tace ," Ya
Maleek zafi suke min!"
"Ina Kaka?"
"tana ɗaki" kai tsaye ya nufi ɗakin ya gaishe Maryam ta bishi da Harara, bayan sun gaisa tare suka dawo
Tsakiyar gida suka zauna kana yaci Abinci, bayan ya gama ta kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace "gobe
zamuje Kano tare da oga"
" TOH Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Amin Kaka, dai dai lokacin wayar Kaka tayi Ringing a
hankali ta ɗaya wayar "Abdullahi Ya gida lafiya? Ya nayi muryar a haka? Ya jikin Kubra? Daga can ban
ɓangaren Abdullahi ya sauƙin Nannauyan Ajiyar zuciyar murya a dishace yace ," Kaka jikinne ya kara tashi
sosai yanzu haka muna Asbiti, "Subuhalillah Allah Ubangiji ya bata lafiya "Amin"
"Gobe ka aiko Direba yazo ya kaimu na ganata, "TOH Mama sai kushirya da wuri Allah ya kawo ku
lafiya, " Amin ya rabbi, kana sukayi Sallama, kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana ta fesar da Numfashi mai
Zafi, "Abdulmalik gobe muna zamuje Kano matar baban Maryam ce ba lafiya yanzu haka suna Asbiti,
"Allah ya bata lafiya Kaka yaushe zaku dawo kenan goben zamu dawo Insha Allahu, Nima ina tunani
kwana ɗaya zamu kana mudawo, " TOH Allah ya dawo damu lafiya Amin Kaka" Maryam ha kawai
gabanta ya riƙa faɗiwa, Murya a dishace tace "Kaka Nikam Bazan je ba,"saboda me? "Bakomi Kaka"
"Aiko dole kije"
Jiki a Mace Abdulmalik yayi musu sallama ya wuce gida,
Nan Kaka tashi haɗa .musu kayan su,
Washe gari tunda sassafe Abdulmalik ya shigo gidan tuni su kaka ma sun shirya direba kawai suke jira tare
suka karya kana Abdulmalik ya yi musu Sallama ya wuce har ya kai baƙin ƙofa ya dawo "Kaka yau kike
zaku dawo ko?"
"in sha Allahu Abdulmalik yau ko gobe duk yadda hali ya yi bazamu jima ba kodon makarantar Maryam
koda ka dawo baka gobe baku da woba zan a jema makulli kodon dafa abinci " Toh Kaka Allah ya tsare"
"Amin"
"Maryama ta! Bazaki min rakiya ba cikin mutuwar jiki saba ta san namiye ta rakashi har ƙofar gida har ya
tafi ya kira sunan sa "Ya Maleek" a hankali ya juyu suna fusakar zuna da sauri ta faɗa jikinsa ta
rungumeshi, "Ya Maleek Allah ya kaika Lafiya ya dawo dakai lafiya"
"Amin ya Allah Maryama ta! Kinga bari na tafi lokacin na ƙarewa, " Ya Maleek Allah ya sadamu da Alheri!
Nan take jikinsa ya yi sanyi, murya a dishace yace ," Amin" tana tsaye a wajen har ya ɓace mata kana ta
wuce cikin gida,
Jikin a mace ya wuce kasuwa tsawon Awa guda kenan da isawarshi sai yanzu Oga Kabiru ya iso Kana suka
wuce.....
Bayan tafiyar Abdulmalik baifi minti goma Atiku Direba ya iso kana suka wuce, tafiya suka hankali a
kwance kar suka iso Kano kai tsaye ya wuce dasu Asbiti.... Isowar su ya yi dai da likata na sanarda
Abdullahi rasuwa Kubra Haka kaka taji maganar kaman saukar Adaru nan take jikinta ya soma ƙarkarwa
cikin wani irin mummunan yanayi da tashin hankalin murya rana ta kira "Abdullahi da gaske Kubra ta rasu
Abdullahi da tunu ya baya cikin Haiyacinsa sam baiji me kaka ka faɗi ba, Maryam gabaƙi ɗaya a ruɗe
take....... Nan take Kaka Abdullahi ya yenke jiki ya fadi a sume, Maryam ta kwalla wata irin ƙara mai
razanarwa, tare da ƙamkame Kaka jikinta naci gaba da ƙarƙarwa........
*ABDULMALIK*😥
Tunda suka dauki hanyar suna tafiya ba abinda yake ji a zuciyarshi kamar kewar rabuwa da Maryam ya
rasa abinda yasa bugun zuciyarshi take tsananta a kowani dakika na bugun agogo dake cikin motar,lokaci
zuwa lokaci zufa ke tsatsafo masa yana gogewa ji yakeyi kamar tafiyar da zaiyi bazai dawo ba,wata zuciyar
Kuma na raya masa sun rabu da Maryam kenan rabuwa ta har abada,addu'a yakeyi indan yaji irin wanan
tunanin ya fado masa har suka Yi nisa sosai a tafiyar tasu.
Bayan yayi addu'ar ya samu nutsuwa ba'a mintuna kalilan ba yaji kamar yanayin tafiyar motar ya
chanza,bae samu cewa komai ba ya dinga sauraro a tsanake chan dae yaji kamar motar na kara wani irin
kara, da sauri ya ce "Anya baza'a faka a duba motar nan ba kuwa dri......" Ko karasa abinda zaifada baiyi ba
motar ta kwace a hannu driver ta shiga junjuyawa har zuwa jeji sosai yake son rike sitiyarin motar abin ya
ci tura,Wani babban dutse motar ta daka da karfin tsiya ,a take bangaren da maleek yake qofar ta bude
kamar wanda akayi wurgi dashi ya fada cikin dokar daji kansa ya bugi katon dutse nesa da inda hatsari ya
afku. haka motar taci gaba da junjuyawa cikin hunkici Allah ya tsaya cak......
Bayan wani ɗan wani lokaci mutane suka taru a wajen tare da basu taimakon gaggawa, tuni labarin
mutuwar ya kewaye garin ƙaraye cikin tsananin tashin hankali, daga daga cikin maƙotan Kaka ta kiranta
kusan sau ukku gab da kiran zai tsinke Kaka ta daga murya a dishace tace"Iya!
"Kaka ya mukaji da haƙuri Abdulmalik ashe lokacin Yayi! cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa "Kaka
tace wanne Abdulmalik!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Kasan cewar wayar a hand free take nan take
Maryam ta yanke jiki ta faɗi.....✍️✍️✍️
*More comments and share*
*Sadeeya Ka'oje ce✍️*
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

*( THE BEGINNING)*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*


💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬




Bismillah........ ✍


Tallah ! Tallah !! Tallah!!!

Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a
littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI*

yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN
ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai
karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi
kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number
08103884440

*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*Page 9-10*
________ Nan take ta yenke jiki ta faɗi "Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n! Atiku Direba dake tsaye cikin
ruɗu da tausayawa ya yi saurin ƙara so gaban Kaka, cikin tsananin tashin dake tattare re dashi murya a
disashe ya soma magana ,"Mama suma tayi, Kaka tuni tayi suman zaune, "Doctor ku taimaka muna, da
sauri Nurse suka ƙara so wajen tare da ɗaukar Maryam suka wuce da ita.....
Cikin Wata irin dakakkiyar murya mai ɗauke da tarin raɗaɗi ta ƙuna tace," Abdulmalik ɗin ne ya rasu!
Kallonta ta mayar ga Abdullahi dake zaune daɓas a ƙasa kaman wani yaro tare da wani likita Rungume da
shi, dai dai lokacin wata nurse ta iso hannuta dauke da ruwan gora, Dr ya karɓa kana ya buɗe tare da
yayyafawa Abdullahi ruwa dake kwance a jikinsa har so biyu sai a karo na Ukku ya sauke Nannauyan
Ajiyar zuciya, a hankali ya soma buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Kaka, a hankali
Abdullahi ya fara sakin Ajiyar zuciya kana ya shiga maimai ta Addu'oi sannu a hankali ya fara dawowa
haiyacinsa
A hankali ya sake ɗago da idanunsa ya kalli Kaka ya yi ƙasa da kansa cikin raunin Murya ,"Mama da
gaske Kubra ta rasu!?"
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka, ta kallesa Zuciyarta na bugawa da
matsifar ƙarfi murya a disashe tace ,"Abdulmalik ya rasu! jiki a mace Abdullahi ya fara janye jikinsa,
"Mama kubra ta tarasu!"
Kai Kaka ta gyada mishi cikin tsananin tashin da ruɗu ta fashe da kuka mai tsuma zuciya murya na rawa
tace ," Abdulmalik ma ya rasu!!!"Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n"
cikin ƙanƙanen Lokaci Asabiti ya cika da mutane kasan cewar ɗaya daga cikin nurse ɗin kwai ƴar Uwar
Kubra, ko wannen su damuwa fal a fusakar sa, koda aka fito da gwar Kubra da kyar Abdullahi ya iya mata
kallon karshe, kana ya fashe da sabon Kuka, kasa cewa komi ya yi kawai ya fashe da matsanancin kuka
cikin raunin Murya yace," Allah ya jiƙan ki Kubra! Allah ya ƙarɓi baƙunci ki!, Kaka ma tuni hawaye sun
cika tab a Idonta, wani irin tausayin ne ya ratsa duk kan mutanen da ke tsaye a wajen, anan Asibitin aka
shiryata kana akayi mata sallah tare da kaita gidanta na gaskiya,
Jana'izar da tasamu halattar dumbin jama'a yan uwa da abon Azziki....
*ƘARAYE*
tuni an iso da gawarwakin wayan da sukayi Hatsarin nan take gari ya hargitse da koke koke, kasan cewar
sunyi dameji sosai bata ɓata lokaci akayi jana'izar aka gaisu gidan su na gaskiya,.....
*KANO*
Murya a disashe Abdullahi yace " Kaka Mutafi gida ko!" Cikin raunin Murya Kaka tace ," Abdullahi
Maryam tana wajen likitoci!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Cewar Abdullahi ,
*MARYAM*
Likitoci ne suka duƙufa a kanta tare taimakon gaggawa koda wasa bata bata farfaɗo ba, ganin haka yasa
suka ɗauko wata na'ura mai kama da iron suka fara dannan mata a ƙirji... haka suka ɗau tsawon lokaci
Amman ina babu alamu rai a tare da ita.. haka likitoci suka kwace tsawon lokaci don ganin sun ceto
rayuwarta, a karo na Barka tai suka sake danna mata na'urar a ƙirji ta ƙarfi, cikin ikon Allah Maryam taja
wani dogon Numfashi sai kuma jikinta ya sake, a karo na biyu Dr ya sake danna mata na'urar,da ƙarfin
gaske, ta sake jan wani Numfashi, still bata farfaɗo ba, Dr wata irin zufa ce ta riƙa tsastafo mishi, sauran
Dr duk jikinsu ya yi sanyi, a hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe su a kan fuskarta Maryam, da kyar
ya tattaro duk kan ƙarfinshi ya sake danna mata na'urar da karfi, taja dogon Numfashi tare da buɗe
idanunta cikin raunin Murya tace," Ya Maleek!!!"
Lokaci ɗaya likitoci suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar tare da fesar da Numfashi,
Duk da bata cikin haiyacinta hakan bai sa ta Dena faɗin ," Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!! da duk wata
Addu'a data zo mata a hankali ta ɗago da kanta ta kalli Lokacin dake tsaye a wajen, "Ina ya Maleek!!?"
"Ina Kaka!!?"
"Je ki kira ƴan Uwanta" cewar Dr,
tare suka shigo Abdullahi da kaka da sauri

Please Login or Register in order to submit comment