Reading MAR ADAMS BOOK 4 BY AYSHA BAGUDU Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa inda ya iske mami tsaye da alamun itama shirin shiga sallah take yayi mata sallama zashi"

"massalaci ,fuskarta babu yabo babu fallasa tace ""a dawo lafiya!""."

yasa kai ya nufi kofar fita yana takun nan nasa mai matuqar d'aukar hankali kamar baya son taka kasa

"bayansa tabi da kallo gabad'aya sai taga yanayinsa ya canza daga adamcyn data sani zuwa wani dabam ,bai dawo gidan ba sai da yayi sallah isha'i lokacin daya dawo bai isketa a parlour'n ba tana"

"d'akinta a can ya isketa yace mata ya dawo tace ""sannu da dawowa"" taja bakinta tayi shiru kusan minti shabiyar yana zaune ba tayi magana ba bare ma ta kalli inda yake ganin tayi masa shiru ya mike ya fito ya nufi samansa har kusan karfe goma adamcy bai ga alamun za'a kawo masa abinci ba ,dan ya tabbatar da za'a bashi ko baza'a bashi ba ya kirata tana d'aga kiran tace ""uhm !""yayi shiru yana juya kalmar uhm din da tace ""uhm ina jinka?""ta sake maimaitawa runtse idanunshi yayi sannan yace ""sweetheart"

"abinci ?""muryarta a dake tace ""babu!""shi abincin ne babu !?ya furta ahankali sai dai direct kalmar ta shiga cikin kunneta kafin ya sake cewa wani abu ta katse kiran ,shiru yayi zaune rike da waya yana juya wayar yana mamakin canji daya kara samu daga mahaifiyar dake tsananin son shi yasan duk ya samu sauyin ne akan maryama yasan da zai ce mata ya fasa auren maryama zata ji dadi sosai har ma ta sauko daga dokin fushin data hau sai dai ina bazai iya ba dan ba abu ne mai sauki agaresa ya iya hakura daita"

"ba yana mutuwar son maryama soyayyarta kullum sake karuwa take acikin zuciyarsa ."""

"""wallahil azim da zai iya rabuwa da maryama da zai hanzarta barinta kodan sweetheart dinsa ta samu"

"sukuni da natsuwa amman son maryama ajininsa yake ya zame masa jarabawa arayuwar sa, idan ma yayi ganganci barinta yasan yayi gan ganci da rayuwarsa ne ,bare a yanzu da kullum abun karuwa yake har ma ya had'e masa da tsananin sha'awarta .""waje ya samu akan dogu war kujera ya mike tare da d'aura hannunsa d'aya a saman ruwan cikinsa d'ayan hannun kuwa ya dafe goshinsa dashi ya runtse idanunshi ahankali fuskar maryama ta soma masa gezo wai gata tsaye a gabansa bai tsaya wata wata ba ya kai hannunsa ya fixgota ta fad'o jikinsa ya rungu meta tsam tsam yana sauke ajiyar zuciya duk da ba a zahiri yake jinta ajikinsa ba sai daya ji jijiyarsa ta harba da sauri, a natse yayi kasa da hannunsa ya dafe daidai inda jijiyarsa ke kwance tana wani irin harbawa da sauri sauri ji yayi wai ta sake lafewa"

"ajikinsa ,ya sake rikota sosai yana shinshin wuyanta yana kokarin kamo bakinta da wannan imagination"

"din bacci yayi awon gaba dashi a parlour'n."""

******

Washegari tunda ya tashi yayi sallar asuba ya koma bacci bai tashi ba sai around to 12:00 Kai tsaye bayi

"ya fad'a ya jima yana cud'a jikinsa da sabulu sannan yayi alwala dan har an fara kiran sallar azahar ya fito d'aure da dogon farin towel a ™ugunsa,ruwan dake Wigowa ta cikin sumar kansa ya fara gogewa bayan ya gama ya shafa lotion ajikinsa ya shirya cikin wani had'a den yadi dark blue mai matukar kyau da"

"taushi a gaban rigar an rubuta ""TAT""kamar sauran manyan kayansa ."""

kayan ya matseefar kar'bar jikinsa ya d'aura hula a kansa hular daya saka ma ta matukar taimaka wa

"wajen fito da aihinin kyawunsa ya Wau tsadadden links ya saka a bakin hannun rigar sanyayyen turarensa red me sanyin ™amshi ya feshe jikinsa dashi ya sanya takalmi sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito bai iske mami a parlour kasa ba dan haka ya nufi d'akinta inda anan ya isketa zaune akan daddumar sallah tana jan casbaha da alamun sallah ta idar ya k'arasa har inda take zaune ya durkusa a gabanta ya kamo hannunta cikin nashi ya sumbata kamar yadda ya saba sannan ya gaisheta ""sweetheart kin tashi"

"lafiya ?""ya tambayeta yana kallonta cike da tsananin kulawa."""

"muryarta a sanyaye tace ""Alhamdulillah na tashi lafiya ya kai ma ka tashi ?""ya karyar da kanshi gefe"

"alamun lafiya sannan yayi shiru yana kallon yanayinta kwata kwata yanayinta ya nuna masa bata cikin farinciki da walwala ahankali yace ""ina mai k'ara neman afuwarki sweetheart kiyi hakuri ki yafe min ki manta komai ""numfashi ta sauke da kyar tace ""komai ya wuce"". yayi kissing din saman hannunta yana mai sake karewa yanayinta kallon sannan yace ""na gode sosai sweetheart thank you for suppointing my marriage Allah ya kara miki lafiya da tsawon rai mai albarka ."" ""kallonsa tayi na second biyu kafin Ahankali tace ""ameen ""!yace zanje nayi sallah daga nan zan fita sai dai zan d'an jima kafin na dawo ""a dawo lafiya !"" ta fad'a ataikaice fuskarta a d'aure babu annuri bare ta tambayesa inda zashi da kuma abincin da zai bukata idan ya dawo da alamun ma yau haka zata barshi ya kwana da yunwa numfashi ya sauke sannan ya fito zuwa haraban gidansu ya soma taku zuwa massalaci dake cikin estate dinsu bayan"

"ya idar da sallah kai tsaye ATA company direbansa da masu tsaronsa suka nufa dashi bisa umarninsa ."""

"Tun daga haraban ma'aikata yake samun gaisuwar mutane, wasu ya amsa wasu kuma ya d'aga"

"hannu ,wasu kuma ya share a haka har ya kusan karasowa inda sagir pA dinsa yake zaune yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana cewa ""good morning sir !?morning !""ya amsa atakaice ya shige office dinsa ya zauna yana kallon makeken table din gabansa kusan minti goma yana zaune sannan sagir yayi knocking tare da Neman izini shigo ""may I coming sir ?""bayan kamar minti biyar yace ""coming !""ya bashi"

"izini ya shigo ,a natse sagir ya shiga ya tsaya a gabansa cike da girmamawa yana sake gaishesa mr ata bai"

"d'ago ba ,bayan kamar minti goma sagir yace "" sir ""!mr ata ya d'ago ya kallesa a d'age alokcin da yake kokarin ajiye wani file a gabansa ""sir ana bukatar saka hannuka anan."""

"ya fad'a yana nuna masa inda zai saka hannu ""mr ata bai ce komai ba ya d'auki biro yayi masa singn da"

"zanen fuskarsa cike da girmamawa ya d'auki file din yana cewa""sir akwai wasu mutane da suke son ganawa da kai kusan kwana uku kenan suna zuwa basa samun ganinka ""me yasa baka bari nasan da zaman haka ba tun kafin yau ?""im sorry sir naga kwanakin nan ne baka samun zama amman dai yanzu"

"haka suna kasa ""."

shiru yayi na wasu mintuna har sagir ya fidda rai da zai yi magana dan har yana kokarin juyawa yaji

"sautin muryarsa a kasan makoshi ""kace masu su dawo gobe dan yau banzo da shirin ganinsu ba akwai wanda zan gani .""okay sir ya juya da sauri ya fita kmr zai tuntsura."""

Karfe biyar na yammacin ranar a gidansu maryama tayi masa yana zaune a parlour tare da umma

"wacce farincikinta ya kasa boyuwa Allah ya sani tana tsananin kaunarsa ko d'an cikinta sai haka bata sani ba ko dan ta fahimci maryamarta na son shi ne bayan sun gaisa daita ya soma da tambayar maryama umma tace bata nan yayi shiru sai dai acikin ransa ya fara fad'a yau ma kamar jiya fita tayi to Ina take zuwa haka ?""wato ma zata iya fita yawonta zuwa Office ne bazata yi ba bare ya samu ya dinga ganinta akan time ?""kamar umma tasan abinda yake cin ransa tace ""bata dade da fita ba taje nan bayan layinmu ne akwai wata yar makarantar islamiyarsu da zatai aure acikin satin nan dake tana cikin kawaye ai naso tun jiya na hanata kanwance duk da dai ba wai tana ra'ayin yi bane ita firdausi ce ta matsa mata da magiya amman bazata wani jima ba zata dawo ko a kirata ne ? .""a natse yace ""a'a ki barta kawai ya fad'a tare da yin shiru umma ta mike domin kawo masa abun sha bata wani jima ba ta dawo hannunta rike da karamin tray dake d'auke da cincin da drinks, ta aje mashi akan table din gabansa tace ""adamu ga cincin kaci ni nayi da kaina yayi d'an yi murmushi kana yace ""na gode umma !""bayan second biyu yayi gyaran murya sannan ya soma magana ""umma naso ace kun tare a gidanku kafin zuwan wannan lokacin dasu baba zasu zo amman ban sani ko kuna da dalilin ku na rashin son tarewa ba ko kuma maryama ce"

"ke hanaku ?""."

"umma tayi murmushi irin nasu na manya tace ""sam ba maryama bace munyi magana da auntynta itace"

"dai tace abari har ayi auren tukun shiyasa kaji mun yi maka shiru amman ba wani abu bane. numfashi ya sauke da kyar shi dai gasky ya so ace sun tare amman bashi da yadda zai yi dasu kar ya matsa su d'auka ko yana kyamkyaminsu ne ko kuma ya raina muhallinsu ne ,muryarsa a sanyaye yace ""shikenan umma"

"Allah ya nuna mana lokacin sai magana ta gaba wacce kusan itace musababin zuwana ""umma tace ina"

"sauraronka ya d'an ciza lip's dinsa na kasa yace ""mahifiyata tace maryama a gidanta zata zauna amman"

"nasan zaman na wani lokaci ne in sha allahu"""

umma tayi shiru tana sauraronsa domin gasky abun bai mata dadi ba zaman maryama tare da

mahaifiyarsa kasancewar bata sonta amman babu yadda suka iya shi shaani aure sai anyi hakuri kuma ahankali komai zai wuce bare tasan hali maryama bada mutun ba ko da aljanu ne zata iya zama

"dasu ""karka wani samu damuwa wannan abu ne mai kyau Allah yasa hakan ya zama alkhairi maryama"

"bazata ki zama tare da mahaifiyarka ba ."""

"Yaji dadi sosai daman kuma yayi masu kyakkwan zato yasan bazasu ce a'a ba ""cikin 'ya'yan gidan nan kaf"

"Allah yayiwa mryama baiwar hakuri kuma yayi mata baiwar ilimi da hankali da nutsuwa, zakayi mamaki yadda zata zauna lafiya da mahaifiyarka ,da ba dan kar na baka labarin irin rayuwar data fuskanta da irin qaddarorin da suka fuskanceta cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta ba ,to zaka d'auka ko dan maryama tana tawa ce yasa haka, amman gashi tsananin hakurin datayi yasa taga karshen komai wa ma zai ce ta taba fuskantar matsi da Kunci maka mancin wanda ta tsinci kanta ""basani ba kota fad'a maka wanda ta fara aure ?mr ata yayi shiru yana dubanta a tsanake yana saurronta ""d'an cikina maryama ta"

"aura ?""kana ganin idan bansan nagartata ba duk yadda suke dashi zan yarda ne ?""amman hasalima nice da kaina na had'a auren saboda kyawawan halaiyanta amman dake auren ba mai daurewa bane Allah ya kar'bi abunsa dubanta kawai yake kafin ahankali yace ""Allah ya jikinsa !""ya fad'a a fili yayinda a boye yace ""ai mutuwarsa Itace alkhairi arayuwata daman sai wani ya rasa wani yake samu ."" ""ameen !""umma"

"ta amsa tana sauke numfashi ."""

Suna zaune suna tautauna yadda zuwansu baba babba zai kasance a gobe maryama ta shigo sanye cikin

"dogon hijab har kasa kawai taga mutun zaune ,ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki akan fuskarta ,yayi kyau sosai cikin shigar da yayi ,shima ya d'ago ya kalleta sai daya ji wani abu ya caki zuciyarsa ,ahankali ta d'auke idanunta akanshi tana gaishesa""yallabai barka da zuwa"" mr ata yana jinta yayi mata banza .""ta d'an juyo ta kallesa jin bai amsa ba taga idanunshi baya kanta yana kallon wayarsa ne yayinda fuskarsa a d'aure, maryama ta d'an tsorata amman ta danne tsoron da taji ta kalli umma ""sannu da gida umma!"" yauwa maryama sannu da zuwa ya firddausi take ?""tana lafiya tace a"

"gaisheki ,ina amsawa firdausi amarya maryama ta d'an ja tsaki tana cewa ""nifa umma ina ganin bazan iya"

"kwawance nan ba dan bazan iya fita kullum ba ,gashi wai sai anje wajen agwane a ajibose bazan iya ba gsky ba ."""

umma tai murmushi tana duban adamcy dake zaune yana sauraronsu dan tasan za'a rina karshe bazata

"yi ba .""sai dai bata ce mata komai ba ."""

"""Ina yini yallabai ?""ta sake gaishesa ""lafiya !""ya amsa atakaice maryama tayi shiru tana tunanin laifin me"

"kuma tayi masa daya canza mata ya wani had'e rai kamar yaga mutuwarsa har ma zai zo gidansu batare daya kirata ya sanar daita zai zo ba sannan yazo yana wani cika yana batsewa ""."

umma dai bata ce komai ba ta zuba masu ido sai dai ta lura yanayin maryama kamar bata so zuwansa

"ba,shima kuma yayinsa ya nuna bai ji dadin fitar da tayi ba ,jiki a sanyaye ta nufi d'akinta .""ahankali ta cire hijab dinta ta ninke ta zauna abakin gado tai shiru idanunta na kokarin zubar da hawaye tayi saurin gogewa ita kam wannan halin nasa yana matukar damunta dan dai Allah yasa tana da dauriya ne, data yarda ta bayyana masa yadda take son shi da bata san irin wulakancin da zata sha a hannunsa ba a yanzu ma da shine yake bukatarta yana mata iskancin daya ga dama Ina ga ita ke bibiyarsa .""shi kam mr ata bayan ya kar'bi number baba gali tashi yayi bai nemi maryama ba yyiwa umma sallama ya"

"wuce .sosai maryama taso tasan me ya kawosa dan har dare tana tunanin umma zata yi mata magana akan zuwan shi amman ta share ta kasa hakuri ta tambayeta ""umma wai zuwan me mr ata yayi d'azu?"" umma tace"" babu komai zuwa yayi mu gaisa ""gaisawa kuma umma ""?eh mana ko akwai wani laifi"

"ne ?""aa ""!maryama ta fad'a tana girgiza mata kai sai dai tai tsai da ranta tana tunani dan a lissafinta ya kwana biyu bai kirata ba gashi yau yazo yayi mata banza ""to ke me zai dameki tunda Allah ya saukaka miki idan ma fasa aurenki yayi ai kin huta ,amman kuma ya zakiyi da son shi da sharadin yan'uwansa har washegari ranar laraba mr ata bai nemeta ba canji da mr ata yayi mata shi ya kara d'aga mata hankali ya"

"kusan haukatata dan gabad'aya ta gama amincewa zuciyarta ta rasa shi ."""

******

A yau ne su baba babba zasu samu ganawa da baba gali tare da malam mustapha a babban masallacin

"malam mustapha dake kan sabon titin agege had'add'un motoci jeep guda biyu tare da motocin masu tsaronsu guda hud'u wad'an da daman sun san unguwarsu maryama mr ata ya had'asu dasu ,karfe d'aya daidai suka baro estate dinsu mota d'aya baba babba ne tare prof lawan shu'aib aminin mahaifin mr ata yayinda d'ayar motar baba k'aramin ne tare da uncle jay zaune aciki sai motocin masu tsaro biyu a gaba biyu abayan da jiniya suka karaso unguwar diribobin suka yi parking a gafen titi inda mutanen unguwar suka zubawa motaocin ido suna kallon jami'an tsaronsa dake cike da kowannesu rike da bindiga .kai tsaye baba babba ya soma neman number baba gali, daga baba k'aramin har baba babba da uncle jay har ma prof lawan zance zuci suke acikin ransu da mamakin a irin unguwar da adamcy ya kawosu nema masa aure wata hargi tsatsiyar unguwa,mai cike da adarawa kala kala da 'yan cirani iri iri da 'yan sikiraf, shi kam prof lawan kasa hakuri yayi yace ""kaddara aure kenan babu inda bata kai bawa,shi kuma adamcy duk tarin ya'yan manya mutane dake cikin kasar nan birjiki bai ga wacce tayi masa ba sai anan"

"kaddararsa take ?"""

numfashi baba babba ya sauke kawai dan bai san ma me zai ce ba sai dai ya shiga cikin wani yanayi mai

"tsarkakkiya babu abinda yazo zuciyarsa kamar nuzlarsa yadda tai kulafucin son shi haka ma hindu wacce har yauzu tana mutuwar son shi dan ko bayan fitowarta daga kurku sai data samesa da maganar ya shiga cikin lamarin sai dai hakuri ya bata tare da bata misali da nuzla da yana da wannna karfin ikon to tabbas da tun lokacin da nuzla ta haukace akanshi ya dace ya bashi umarnin ya aureta .""""ubangiji yasa albarka ""!prof lawan ya fad'a yana jinjina kai baba babba ya amsa da""ameen !""daga haka bai k'ara cewa"

komai ba ya kai hannunsa baki yana shafa farin gemunsa batare da 'bata lokaci ba baba gali ya turo

"ataho dasu suka fito a natse kowannensu cikin shiga ta alfarma suna taku ahankali kallo d'aya zaka masu ka tabbatar da cewa wad'an din manya mutane ne ."""

baba gali dake tsaye a bakin massalaci cikin tsananin tashin hankali da firgici tsayuwar jiran karasowarsu

tun daga nesa yake kallonsu tare da yaron daya tura idanunshi ya zuba masu gaba d'aya kwakwaluwarsa motsin kirki bayayi tun kafin su Kai ga karasowa inda yake ya tabbatar da lallai ba komai yasa maryama tayi wannan babban kumun ba sai hasaadar da suke mata hawaye ne ya cika idanunshi yayi saurin

"daukewa ahankali suka karaso yayinda jami'an tsaron ke biye dasu ."""

"a mutunce ya kar'besu yana cewa ""sannuku da zuwa ku biyuni ya fad'a yana juyawa da sauri sauran"

kad'an yayi tuntu'be dan jikinsa har rawa yake suka biyo bayansa a natse Inda kowannen su ganin yake kamar a mafarki ne wai auren adam shararren d'an kasuwan nan da kasa da duniya tasan da

"zamansa ne suka zo nema acikin unguwr irin nan kuma a massalaci irin wannan abun kamar almara , amman lamarin ubangiji kenan yafi gaban haka waje suka samu suka zauna ,doguwar gaisuwa suka yi fuskar malam mustapha cike da annuri yayinda fuskar baba gali take cike da matsanancin tashin hankali haka ma baba k'aramin zuciyarsa kuna take ganin Inda adamcy ya kawosu bayan sun gama gaisawa suka fara da abinda ya kawosu wato nemawa d'ansu auren diyarsu maryama ""baba gali ya fara magana ""ni yayan mahaifinta ne uwa d'aya uba d'aya na baku auren maryma sai dai wani hanzari ba guda ba maryama fa ta ta'ba aure kuna ganin babu wata matsala ""eh to mu bamu san da wannan zance"

"ba amman bari mu kira shi yaron muji ko yasan da zaman haka .""baba babba ya fad'a tare da ciro wayarsa ya soma kokarin Neman number adamcy kira d'aya ya d'aga yana gaishesa baba babba ya amsa sannan ya saka wayar a handsfree ta yadda kowa zai ji ""adam gamu mun samu karasowa, gamu tare da yayan mahaifinta sai dai yayi wata magana ko kasan da zaman yarinyar ta ta'ba aure ?""adamcy yayi shiru zuciyarsa na dokawa da sauri sauri sai dai yayi matukar mamakin jin abinda yayan mahaifin maryama yayi to ma me kawo wannan maganar,?""adam kana jin kuwa ?""ina jinka baba maryama ko aure dubu"

"tayi ina son aurenta haka ""."""

Mmn sudais

MAR'ADAMS

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan

account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa

wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 7

baba babba yana gama jin abinda adamcy ya fad'a ya dubi baba gali a tsanake sannan ya maida hankalin

"sa ga wayar da yake yace""shikenan idan mun gama zan kiraka"" adamcy yace ""tom!""ka ji abinda yaro yace da alamun yasan da zaman komai sai muyi fatan Allah yasa albarka, ai auren bazawara ba wani abun aibu bane yana daga cikin baiwa ta mussaman matukar zata tsare mutuncinta tasan ciwon kanta ai shikenan ."" ""wannan haka ne maryama kam yarinyar kirki ce wacce ta tsare mutuncin kanta ga"

"hankali ."" ""Dan tana da hankalin da wata budurwa bata dashi nasan shi d'an naku shi yasan abinda ya"

"gani atattare daita da har ya zabeta ta zamo abokiyar rayuwarsa .""inji cewar malam mustapha ."""

"murmushi baba babba yayi"" yadda kuke da tabbas akan yarinyarku haka d'anmu adam yake domin"

"kuwa Allah yayi masa baiwa iri iri cikin farinciki sukai murmushi hannuyensu damke da juna da malam mustapha baba gali kam zuciyarsa kamar ta buga tsabar bakinciki yaso ne lokacin daya fad'a masu ta ta'ba aure daga nan komai ya rushe sai gashi abun yazo masa da bazata ""ganin baba gali bai da niyyar basu ruwan sha yasa malam mustapha ya janyo katon din ruwan roba ya soma zarowa yana ajiye ma"

"kowa a gabansa."""

"Baba babba yace ""mun gode idan zai yuwu yaron yana son a d'aura auren a lahadi ta sama ""ji baba gali"

"yayi kamar ya mutu a gurin domin kuwa da zarar an d'aura auren shikenan ta faru ta kare basu da wani sauran dabara amman dai zai nemi su d'an daga masu kafa ko nan da wata biyu ne masu zuwa alabashi kafin zuwa wannna lokacin salma tayi nasarar ruguza komai sai dai kafin yayi hanzarin yin magana ya tsinkayo dariyar malam mustapha tare da cewa ""ai tunda mun bada auren maryama ga adam aure kam za'a d'aura shi in sha allahu Allah ya kai mu lahadi ta sama ,Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi yasa muna raye za'ayi wannan auren Allah yasa auren ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuriarku "".Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun baba gali ya shiga furtawa daga zaunen da yake .""amman dai malam mustapha"

"da karambani tsiya yake wannan zakewa haka kamar shine shakikinta?"""

maimakon ya zuba ido ya barshi yayi magana akan komai amman sai wani zakewa yake yana bare bare

"da rawar kai .""ameen ya hayyu ya qayyum cikin farinciki mutane dake zaune a wajen suke amsawa sannan suka ajiye wata takarda mai ruwan kasa a gabansu ""."

baba babba tsaf ya fahimci baba gali kamar akwai hassada atare dashi dan a zahiri ake iya hango tarin

"bakincikinsa wanda Ke nuna alamun bai so faruwar wannan abun alkhairin ba .""a natse suka mikawa juna hannu sukai musabaha sannan sukai sallama baba babba ya kai hannu ya d'auki roban ruwan da'aka ajiye masa wanda hakan yasa suma sauran suka d'auka suka rike har bakin inda motocinsu suke"

"pake suka rakasu .""fuskar baba gali babu yabo babu fallasa ya kalli malam mustapha dake tsaye kusa"

"dashi yace ""kai malam mustapha haka akeyi ?""da mamaki malam mustapha ya tsaya yana kallonsa ""kasani ko mu a shirye muke daga jin sunce a d'aura aure ranar lahadi ta sama sai kayi tsigil ka amince halan kai zaka yi mata kayan d'aki da sauran abubuwa ?""da wani sabon mamaki malam mustapha yake dubansa sai dai yace ""ayya kayi hakuri malam gali na maka shishshigi ashe ?sai dai ina mai baka hakuri tare da neman yafiya amman na d'auka kai ma hajiya tai maka bayanin komai akan batun zuwansu da kuma bukatarsu kamar yadda ta min amman dai kayi ...""fuuuuuu baba gali ya wucesa tare da karya kwana ya nufi hanyar gida hankalinsa a matukar tashe batare daya tsaya ya karasa jin abinda malam"

"mustapha zai fad'a ba "" ."

"Tafiya kawai yake yana surutu ""ko ya salma zata yi da rayuwarta dan tun shekaranjiya da taji batun"

"auren nan bata sake kwantar da hankalinta ba .""?yanzu haka bata gida tun safe data fita bata dawo ba bai san inda ta nufa ba .""cike da matsanancin tashin hankali ya shigo gidan kai tsaye bangaren umma ya shiga ya samu waje ya zauna akan kujera yana mata bayanin yadda sukai da iyayen adam sannan ya mika mata takarda da suka kawo yace ""kudin wata kasa ne masu yawa sosai sai dai ban san ko na wace kasa bane ga shin nan na gaisuwar iyaye ne ""umma tasa ta kar'ba ta d'an bud'e ciki tace ""masha Allah lallai maryama tayi kai kudi ne kuwa masu yawa nima ban san ko kudin wace kasa bane hakika yau muna cikin tsananin farinciki domin kuwa abun farinciki ya samemu Alhamdulillah Alhamdulillah umma ke jerowa tana taka rawa gabad'aya ta kasa zama waje d'aya saboda tsananin farinciki."" maryma kinyi hakuri kin sha wuya yau ga irin kyakkwan sakayyar da Allah yayi miki ,gali bari naje gurin auntynta kai ma dan Allah ka kira 'yan'uwanka ka sanar masu abun alkhairin daya same mu .""maryama dake zauen a d'akinta tun awanin biyu tana zaune tana zana fuskar mr ata da shigar da ya zo daita jiya

Please Login or Register in order to submit comment