Reading MAR ADAMS BOOK 4 BY AYSHA BAGUDU Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata zo ta wuce dole sai kinyi tunanina tare da son kiji muryarta amman tsabar taurin"

"kai yasa kika kasa kirana ."""

A yadda yayi maganar bakaramin rikita mata lissafi yayi ba sannan gabad'aya ilahirin jikinta sun mutu

"ahankali ta motsa bakinta ""kuji min mutun wa yace maka na cigaba da rayuwa cikin rashin kwanciyar hankali ?""sannan duk second din da zata zo ta wuce sai nayi tunaninka ?""kai mai yasa da ban kiraka ba kai baka kirani ba?"" ""okey abinda zaki fad'a ma kenan ""?tai shiru tana zaro ido kar dai yaji abinda ta fad'a"

"ahankali fa tayi mganr? ta yadda ita kad'ai zataji."""

ta rasa wani irin kunnen jin magana garesa duk yadda mutun yayi magana sai yaji a wasu lokutan ma ko

"bakin mutun ya kalla ya kan fahimci abinda ya fad'a ""maryama zai fi miki alkhairi kafin kiyi magana ki dinga tattara natsuwa ajikinki, ko da yake ada ki kan natsu kiyi magana Amman a yanzu soyayya tana son"

"canza miki tunani .""yana kai wa nan ya katse kiran ransa a matukar 'bace."

"sauke wayar tayi tana kallon screen din wayar ""to menene kuma abun fushi anan daga yar wannan"

maganar idan ba bakar zuciyar irin tashi ba kai dai matarka ta gida tana da aiki mutun kamar jira yake ita kam bazata iya wani kiransa ta rarrashesa ba .ajiye wayar tayi ta cigaba da lamarin gabanta shi kuwa har kusan minti goma yana zaune rike da waya yana jiran ko zata kirasa ta bashi hakuri amman yaji shiru ya

kai yatsan hannunsa cikin bakinsa yana cizawa ahankali dakiyarta tana d'aga masa hankali duk tarin son

shi da yake gani atattare daita amman ta kan daurewa rashin ganinsa sai dai duk yadda zata boye son shi

"yana nan atare daita ."""

******

da misalin k'arfe 4:50 na yammacin ranar mr ata ya yanke shawarar da zaman da yake yaje gurin mami

"ya sameta yaji yadda sukai da yar gwal dinta ko zai ji sanyi acikin ranshi dan haka ya fara shirin zuwa wajenta sun iso abdullahi estate adaidai kofar gidan mami direbansa da masu tsaronsa suka yi parking cike da natsuwa ya fito bayan an bud'e masa murfin mota fuskar nan nashi a had'e sai dai hakan bai hana kwarjinsa fitowa ba ,ahankali yake taku har ya shigo babban parlour'n mami bakinsa d'auke da sallama sai dai bai iske mami a parlour'n ba dan haka ya nufi kofar da zata kai shi inda take cikin muryarsa mai sanyi yayi sallama a bakin kofar d'akinta wanda tun kafin ta amsa masa sallamar ta jiyo sanyayyen kamshin turarensa dake shirin fitowa take daga d'akin ta amsa masa sallama sannan ta koma"

"ta zauna a bakin gadonta tana jiran shigowarsa ."""

Ya shigo a natse ya rusuna ya gaisheta ta amsa masa cikin rashin sakin fuska ya samu waje ya zauna yana

"jin bugun da zuciyarsa ke yi gefe guda kuma yana jin haushi daga dokin takura masa data hau ,bayan kamar minti goma yace ""sweet heart nazo ne naji yadda kukayi da wacan yarinyar dan naji shiru baki nemeni ba ""au wai maryam kake nufi ?ya kalli mami kawai batare da yace uffan ba har sanda mami ta cigaba da magana ""Alhamdulillah yanzu kam maryam tasan ciwon kanta dan cewa tayi bazata iya komawa tayi rayuwa da mai bakar zuciya irinka ba ,wanda babu komai acikin zuciyarsa sai tarin mugunta da zalinci akan ya'yan mutane, bazata iya rayuwa da mutun kamarka mara yafiya ba shiyasa kaga ma ban kiraka ba yanzu dai a sauka lafiya sai kaje kayi aurenka da yar gwal ku cigaba da iskancinku da kuka saba dan bazan tursasa mata komawa gidan mutun mai bakar zuciya mara imani da tausayi ba .""tsayawa adamcy yayi tare da bin mami da kallo sakamakon jin bakar maganar data fad'a masa dan har ga Allah sai yaji aransa cewar duk fad'ar ta ce maryam bazata ta'ba bud'e bakinta ta fad'a mata haka akanshi ba yaji zafi kuma yaji sanyi acikin ranshi da bata amince ba jin farinciki rashin amincewrta ya goge tarin haushin da yaji na maganar mami ya basar da maganar kai tsaye yace ""to yanzu yaushe ne su baba"

"babba zasu je gidansu mryama so that sai na sanar mata da zuwansu ""?"

"mami ta hararesa tana kwabe baki tace ""babu ruwana da batun aurenka ka tsara komai da kanka dan"

"yanzu kaine uwar kanka kaine ubanka kanka ""inna lillahi shi kam daman mami fake love take masa ne shi bai sani ba sai a yanzu ne manufarta ta fito fili ?""ahankali ya d'ago tsuma mmun idanunshi da suka gama"

"canza kala tsabar tashin hankalin abinda maganarta ta jefashi."""

ya zubawa sweetheart yana kallonta ganin haka yasa mami ta sake had'e rai dan bata son ya kawo mata

"rainin wayonsa daya saba sannan ta cigaba da dubansa ""sweetheart ki min adalci duk abinda kike so koda banaso haka na kan yi hakuri nayi miki shi domin farincikinki shine nawa ,lamarinki lamarin ya'yanki ban ta'ba juya miki baya ba dan Allah kada kiyi min haka alokacin nawa farinciki?""menene akayi maka na rashin adalci yanzu?""ba'ayi min komai ba abinda nake so dan girman kiyi hakuri ki yafe min sannan ki fad'a ma baba babba da kanki suje su nema min auren maryma"" yayi maganar cikin wani irin yanayi mai"

"cike da ban tausayi."""

"""Bazan ce me ka ta'ba min na kyautatawa ba kayi iyakar kokarinka akanmu amman kasani duk abinda"

"kayi min bai kai d'aukar cikinka har haihu warka da nayi cikin tsananin wahala ba kasani adamcy har na mutu bazan manta tozarcin da kayi min ba, sannna ka mance na baka diyar danuwana ka wulakanta min ita ?ka mance maryam tayi zaman kunci a gidanka saboda tsabar bakar zuciya irinta taka da rashin imaninka ?"" shine yanzu zaka ce na shige maka gaba wajen auren wata can da ban san asalinta ba ""duban mami kawai yake dan ya ma rasa abinda zai ce mata ""tai shiru tana dubansa har sanda ya taso ya"

"karaso gabanta ya durkusa ya d'aura kanshi a saman cinyarta yana mai neman gafara.""sweetheart !"""

Ya Kira sunanta cikin wata irin murya wace bata da maraba data tashin hankali tana jinsa tayi masa

"banza tare da kawar da kanta ""sweetheart Ina tsananin jin damuwa araina Ina jin kamar bani da kowa acikin duniyar nan, Ina ji ajikina zan iya mutuwa akowani lokacin saboda kuncin da zuciya take ciki ,ya kara makale kanshi ajikinta ""sweetheart nifa amana ne a hannunki karki manta da amanar dady har dady ya cika yana sallati yana baki amanata dan Allah ki yafe min ko zuciyata zata samu natsuwa da"

"sausauci ."""

Nan take idanunta mami ya kad'a sosai ya cika da hawaye Allah sarki Tariq dinta mutun mai mutunci da

"son mutane da son yan'uwansa har kullum tana jimamain rashinsa Allah ya jikanka ya maka rahma kuka yaci karfin mami ya tabo mata ciwon dake zuciyarta wanda take jin bazai ta'ba warkewa ba har karshen rayuwarta tunda ta rasa wani bangaren na rayuwarta shi kuma data take ganin zai maye mata gurbin mahaifinsa yaki kwantar mata da hankali ""mr ata jikinsa yayi mugun sanyi duk iskancinsa yana gudun abinda zai saka sweetheart dinsa kuka jin kuka yake kamar ana diga masa dalma a zuciyarsa ya sake"

"matsowa kusa daita yana jin yadda zuciyarsa ke zafi da tafasa domin yasan shine silar kukanta."""

"""ki yafe min sweet heart ""ya sake maimaitawa muryarsa na rawa ""kiyi hakuri ki yafe min kuma a shirye"

"nake da in canza in zama mai faranta miki da kaunarki ,wani sanyi dadi ne ya ziyarci zuciyar mami sai dai ji take duk dan yana son ta bashi goyon baya ne yayi aurensa ya fad'a haka ."""

"Ya sake gyqra kanshi akan cinyarta ""sweetheart ki yafe min ko zan samu sausauci abinda nake ji araina"

"idan ba haka ba wallahi zuciya tana daf da bugawa zaki rasa adam dinki d'an..."" tayi saurin saka hannu ta rufe masa masa baki dan bata son rasashi shine fa da tilon da take dashi duk abinda take masa tanayi ba'a son ranta ba duk da ya sha mata laifi amman na kawo mata maryama yafi komai kona mata rai"

"kuma bata jin zata manta dashi har taso yarinyar."""

"muryarta a sanyaye ta soma magana "" na yafe maka adamcy dan bazan iya rikeka araina ba kuma na"

"barka kaje kayi aurenka kuma zan fad'a ma baba babba yaje nema maka aurenta ,kullum addua nake maka dana Allah yasa kayi aure naga jikokina na gurinka to Alhamdulillah naga khaira kuma isheni domin itace jika mafi soyuwa arayuwarta ""na gode sosai sweetheart ""ya fad'a tare da d'ago kanshi yana kallonta ya riko hannuwanta ""in sha allahu sweetheart zaki yi farinciki da zabina kuma zaki so ya'yan da maryama zata haifa min ""yayi maganar da mur mushi akan fuskarsa,itama tayi murmushi kawai ba wai dan taji dadin maganarsa ba ""ai an gama haifata mata jikar da zata so domin bazata ta'ba son maryama"

"ba bare har taso abinda zata haifa masa ."""

Har yanzu da yake gabanta zuciyarsa cike take tarin damuwa dan bai daina hango damuwa atare da

"mahaifiyarsa ba, fahimtarsa ta dai barshi yaje yayi aurensa amamn batun son maryama kwata kwata bai ga alamun haka a atattare daita .""adamcy bai bar mami ta huta ba sai daya tabbatar da ta kira baba babba tace suje masa Neman auren maryma, baba babba yace zuwa yaushe kenan ?tace ""yau muna litini kuje ranar laraba ,idan yaso banda wannan lahadi lahadi ta sama sai a d'aura auren ,taki bin raayi adamcy dan shi adamcy cewa yayi a aura a wannan lahadin koda yaji abinda tace aransa yace tun dai kin amince Allah ya kai mu"" baba babba yace mata ""to Allah yasa alkhairi ya kai mu ranar tace ""ameen ! atakaice ranta baya mata dadi da auren .adamcy ya mike ya nufi d'akinsa ya zauna shiru tare da kiran layin umma dan aganinsa ita yafi dacewa ya sanarwa ba maryama ba Kira d'aya ana biyu ta d'auka bayan sun gaisa ya sheida mata yanauwnasa zasu zo ranar laraba kuma in sha allahu lahadi ta sama za'a d'aura aure Allah sarki umma nan take ta fad'ada fuskarta da murmushi tana cewa ""Allah ya kai mu lokaci Allah kuma yasa albarka Allah ya bamu ikon gani da ranmu da lafiyarmu yace ""Ameen ya zarce da cewa umma maryama na kusa ne ?""aa d'azu nan taje gidansu subai'a amman nasan tana kan hanyar dawowa ""okay to dan Allah umma Ina neman wata alfarma a wajenki ?tace ""kayi maganar adamu !""sai daya"

"sauke numfashi sannan yace ""dan Allah karki fad'awa marayma batun zuwan yan'uwana har sai a gama"

"komai ""to shikenan an gama to ko wani abu take maka na rashin d'aa ?""yace ""no no !! ai yarinyar kirki ce"

"maryama"" akwai dai maganar da nake son muyi dake ne kafin tasan komai ""umma tai murmushi tace ""shikenan sai kazo sukai sallama dashi yayinda fuskar umma ta kasa boye tsantsar farinciki da take ciki ta"

"mike ta fito ta nufi bangaren aunty ."""

Mmn sudais

MAR'ADAMS

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan

account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa

wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina

(Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 6

"A zaune umma ta iske aunty tana kulla alawar sha ka la'be acikin farar leda ,kallo d'aya aunty tayiwa"

"umma ta fahimci acikin farinciki take haka nan itama taji ta tsinci kanta cikin tayata har sanda umma ta zauna fuskarta cike take da annuri batare da 'bata lokaci ba umma ta shiga karo mata batun zuwan iyayen adamcy ""Alhamdu lillah kawai aunty take jerowa ,kamar ta tashi ta taka rawa dan murna haka ta"

"dinga ji saboda farinciki, ba shakka tana mai tabbatarwa kanta"

"Maryamarta tayi kyakkyawan gamo mai d'auke da dumbin alkhairai, umma ta kasa zama waje d'aya"

"tace ""bari na shiga na sheidawa gali dan naga kamar yana gida ,daga nan zan je na sheida wa malam mustapha su tarbi bakin dashi ."""

"aunty tai murmushi kawai tana kallon bayanta dan tuni tayi hanyar fita ""Allah sarki umma babu abinda"

"zance miki sai dai Allah yasa kiyi kyakya wan k'arshe Allah kuma ya barmu tare da sallama umma ta fad'a bangaren baba gali taci sa'ar samunsa shi kad'ai zaune tsikar gidansa yana jin labarai .""yana ganinta yaji gabansa yayi mummunar fad'uwa dan shi yanzu da ganinta da kiranta ba alkhairi bane a wajensa sai dai ya washe baki yace ""aunty ke da kanki maimakon ki aiko akirani nazo ,sannu da zuwa aunty ga waje ki zauna ya tashi yana kokarin d'auko mata farar kujera umma tace ""ka bar shi ba sai na zauna ba nazo na fad'a maka ne jibi idan Allah ya kai mu iyayen yaron nan adamu zasu zo neman auren maryama nan"

"da sati d'aya kuma za'a d'aura aure in sha allahu ""."

"Wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa cike da matsanancin tashin hankali baba gali ya tsinci kanshi ciki,"

"inda yaji kanshi yayi masa nauyi kamar an d'aura masa dutse, dishi dishi ya soma ganinta da sauri ya bud'e idanunshi sosai dan muddin yayi sakacin da suka rufe komai zai iya faruwa dashi ""gali ina cikin farinciki bari na wuce dan ina son naje na sheidawa malam mustapha sai ku tarbi bakin dashi ,kai ma idan ka samu fita zuwa anjima ko gobe da safe sai kayi masa magana"" tana gama fad'ar haka ta juya da sauri ta barshi nan tsaye cikin mutuwar jiki yana kallon bayanta. umma na fita aunty Salma ta fito da sauri ta tsaya a gabansa ganin baya cikin haiyacinsa yasa ta d'an ta'ba shi kadan, ya maida kallonsa gareta tun dazun data tsinci maganar yake mintsininta ,taso ta fito taji sosai ""baban Aliyu auren wa za'a d'aura kuma nan da sati d'aya ?""baba gali ya kalleta a sukwane yana jin wani sabon tashin hankali na shigarsa yace ""nasan kinji komai amman bari na sake fad'a miki auren maryama za'a d'aura"" idanu"

"aunty salma ta ware sosai tana jin wani irin tashin hankali tace ""amman dai ba da wannan attijirin mai"

"kudin ba?""da shi kuwa za'a d'aura""ya fad'a mata Kai tsaye gumi na tsatsafo masa nan take jikinta ya"

"kama rawa duk sai ta kasa furta komai,babu abinda ke yawo akanta irin maganar malaminta inda yace mata ba za'a sake tada maganar ba sakamakon aikin da yayi mata a makabarta akaje akayi aikinsa yadda"

"idan mutun ya mutu bazai tashi ba haka baza'a sake tada zance auren maryama da adam ba ""."

"""kin dai ga abinda zai faru acikin gidan nan ko kuma kina raye ba wai kin mutu ba ?""saurin bubbuga"

"gefen kanta tayi da hannunta tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu tace ""Kai kuwa ka kwantar da hankalinka har yanzu fa da sauran lokaci tunda ba'a rigada an d'aura auren ba"""

"""baka san wani abu ba shi aikin zai iya tasiri aranar daurin auren ace an fasa ""kinga bazan sake"

"kuskurena yarda dake ba domin yarda da nayi dake ne duk yake kokarin janyo ciwon zuciya,ka kwantar da hankalinka bafa za'ayi auren nan ba ""dan bakisan me nake ji ba a yanzu haka ""bari ina zuwa amman wannan auren kam tabbas baza'a d'aura shi ba sai dai bayan raina sakina da tun fara maganarsu ta fito ta girgiza kai tace ""wallahi mama da kin daina wahalar da kanki akan maryama shin dole ne sai mun taka matsayi d'aya daita ?""hannayemu kad'ai sun ishemu misali ,wallahi idan Allah yaga dama sai ya barmu"

"muddin rai babu aure ba ita kuma tayi aurenta kuma ta dangwama cikin jin dadi ."""

aunty Salma ta juyo a gigice tana dubanta tace idan kika sake fad'a min haka sai na tsine miki

"""Dan ku fa nake wannna wahalar ko da yake ba laifinki ba aikin dake jikinki ne yake son lalacewa shine"

"kike son ki dawo gidan jiya amman zanyi magani ki ""karki sake d'aure min yara ""inji cewar baba"

"gali ,aunty salma ta d'auke idanunta akna sakina ta maida kanshi ""eh haka na fad'a duk kin birkita min"

"tunanin yara da shegen biye biyen malamanki na banza da wofi ""aunty salma bata sake cewa komai ta shiga d'aki ta zari mayafi ta bar gidan ."""

"Adamcy dake zaune a parlour'nsa bayan ya gama waya da umma shiru yayi ,wani irin sanyin dadi ke"

"ratsa ilahirin jikinsa,yanzu hankalinsa ya kanta maryam ba zata dawo rayuwarsa ba ga maryamarsa zai mallaka ,tsadadden murmushin nan nasa ya bayyana akan fuskarsa yana cewa ""maryama kin kusa zama tawa ta har abada Allah yasa karki min rowar kanki dan ina tsananin bukatar ki ""ya fad'a a fili yana kamo lip's dinsa na k'asa yana cizawa ahankali yana jin nishad'i mara misaltuwa wayarsa dake ajiye a gefensa ta fara ringing ya d'an waigo a natse yana kallon screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya d'aga yana ""cewa ""hello baba!"".daga can bangaren baba babban yace ""adam ya kake ?""Alhamdulillah baba"

"barka da yamma ?""barka d'an mamansa ""."

"wani murmushi ya bayyana akan fuskarsa sakamakon jin abinda baba babba ya fad'a """

"Naji dadi kwarai daka natsu ka shawo hankalin mahaifiyarka akan maganar aurenka ,ya kamata zuwa"

yanzu ka canza rayuwar da kakeyi. rayuwar da zakayi yanzu ta samu canji kabi mahaifiyarka ku rabu lafiya domin daga lokacin dakayi rakiya aka binneta daga wannan lokacin rayuwarka ta baya data yanzu ta samu canjin zahiri bazan boye maka ba daga wannan lokacin zaka shiga sabuwar rayuwar zaka zamo

"baka da karfi komai ."""

"""Kuma komai zai iya faruwa da Kai bare Kai da kake tsananin son mahaifiyarka karka d'auka wasa duk"

"wanda ya rasa mahaifiya to fa ya zama abun tausayi ,domin kuwa ya rasa halittar da take son taga rayuwarsa ta samu cigaba kuma ya rasa wacce zata dinga masa adduoin nasara a duk inda take a zaune ko kwance cikin sallah akoda yaushe,dan haka ina shawartarka kabi mahaifi yarka sosai kayi mata duk"

"abinda kasan zatai farinciki Ina maka fatan alkhairi arayuwarka ""."

"""na gode sosai baba in sha allahu zan cigaba akan yadda nake mata .""masha Allah daman Ina son naji a"

"wani estate ko wani guri zamu had'u da iyayen yarinyar dan na kira Zulai tace bata sani ba shine nace bari na kiraka naji dan mu san yadda zamu tsara tafiyar a jibi ""?shiru yayi yana tunanin mai zai ce masa Allah yasani shiyasa yaso tuntuni su maryama sun tare a gidan daya basu ba dan komai sai dan samun wata daraja da kima a idanun yanuwansa amman dai zaije suyi magana da umma gobe ""adam kana kan layi kuwa ?""numfashi ya sauke ahankali sannan ya soma masa magana a natse ""ka bani zuwa gobe zanyi magana da iyayen yarinyar naji a ina zaku had'u baba babba yace ""to shikenan Allah ya kai mu goben Allah kuma yasa albarka bari na kira babanka prof lawan ayi tafiyar dashi ko hakan bai yi ba ?""yayi sosai na gode Allah yasa yana k'asar dan gaskiya na kwana biyu rabona dashi ko a waya ""ai kuwa yana nan dan"

"mun had'u dashi a bikin diyar senater shehu mr ata yace ""okay !""sannan sukai sallama ."""

Bayan sunyi sallama da baba babba mikewa tsaye yayi ya shige bedroom Winshi yana mai manna

"wayarsa a kunnensa da wani kira ya sake shigowa daga yanda yake magana a wayar zaka fahimci yana cikin farinciki inda yake fad'a ma mb batun aurensa, mb yaji dadi sosai har yace zai zo a tsara yadda bikin zai kasance "".""aa mb abar batun biki nan tukun tunda kaga sweetheart ba wai tana son auren nan bane akan bikin nan komai zai iya faruwa ni dai babban burina maryama ta shigo lafiya.""hakan ma yayi amman gasky zamuyi biki daga baya ""babban biki a wajena mb maryama ta shigo hannuna ,mallakarta da zanyi amatsayin matar aurena wallahi ya fiyye min duk wani biki da zaayi kasan ni ba wai Ina son"

"hayani bane ""."

"mb ya kwashe da wata dariya yana cewa ""gsky abokina ka mugun kamuwa da son yarinyar nan ""yarinya"

"duk ta susuta maka lissafi haka Allah yasa ta canza mana kai gabad'aya mu sarara da iskancinka "" yayi shiru kawai yana sauraronsa yana tunanin tare da lumshe idanunshi ""?anya kuwa maryama zata iya canzasa gabad'aya?"""

"""yauwa abokina daman Ina son na maka wata magana dan nasan kai kad'ai ne zaka fad'a aji kuma ayi"

"aiki dashi ""mb yayi maganar yana sauke naunauyen numfashi ""Ina jinka!""mr ata"

"ya fad'a ba tare daya bud'e idanunshi ba ""daman akan maryam ne .""wani dogon tsaki yaja yana furzar da"

"iska mai zafi daga cikin bakinsa ""ka tsaya kaji me zance ."" ""ban san me yasa wani lokacin kake kasa gane bana son ko jin sunanta ""amman kuma ai gashi zaka auri mai sunanta ?"" ""ina daf da canza mata suna bari dai ta shigo hannuna mb yayi murmushi kana ya cigaba da magana ""adamcy rigimar duniya ""ita sukuwa ce da zata bari ka canza mata suna bayan sunanta mai ma'ana ne ?""kai ma kasani babu macen da zan ajiye a karkashina taki bin dokata da abinda nake so .""let me go to my point ,maryam ke d'aura khaira a shafukan sada zumunta na TikTok da instagram ,a gasky abun bai min dadi ba dan saboda komai ba ,sai saboda bakin mutune ,azahirin gsky banso na fad'a maka ba duk da nasan babu abinda fad'a maka din zai yi saboda rashin damuwar da kake nunawa akan yarinyar ,amman dai at least ya kamata ka duba lamarin khaira ko a yaya aka sameta diyarka wacce bayan ranka zata gajeka kuma baka sani ba ko"

"ita kad'ai ce diyarka a duniya ."""

adamcy ya ta'be bakinsa yana jin wani iri ajikinsa kafin ahankali ya bud'e tsumammun idanunshi yana

"kallon saitin shigowa bedroom dinsa yace ""wannan ai maganarku ce zaka iya mata mgana ba sai kun sakoni ciki ba "" ""ai nayi mata magana taki ji ne dana ce ma zan fad'a maka babu kunya maryam tace na fad'a maka ita yanzu ta rigada ta kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita tayi matukar bani mamaki dan sam banyi tunanin haka daga gareta ba ""dan Allah adamcy kayi hakuri kasa baki cikin al'amarin yarinyar za'a duba tayi kamara kuma abinda zai baka haushi da takaici wakar da take d'aurawa da yarinayr wai ga yar da ba'a so ta girma ,ga yar da ba'a so tai karfi,yo su barta ko dan Allah. har mb ya kai karshe maganarsa adamcy na zaune yana sauraronsa sai daya dasa aya sannan yace ""okay haka ta fad'a?""ai daman ku kuke d'aure mata gindi har kuke mata kallon macen kirki amman ni tun tin tin nasan bata da mutunci amman tunda tace ita guguwa ce ni zan nuna mata ni teku ne kuma mai wanke duk wata kurar guguwar data taso dan ubanta zan nuna mata bata isa ba,yar ma idan naga dama sai na"

"kwace gabad'aya naga ta karyar iskanci ""."

"""no karka rabata da 'yarta ka dai yi magana nasan za'aji maganarka zaka iya kiran mahaifinta yayi mata"

"magana "".kenan ma kana nufin a lalla'bata ?mb yayi shiru dan ya rasa me zai ce ""idan dai haka"

"ne ...""kaga bari kawai ma zan kira babanta muyi magana dashi ""mb ya katse mr ata ta hanyar fad'ar haka ""wannan kuma ya rage naku idan na tashi nawa kai kasan me zan iya yi.""yana gama maganarsa yayi"

hanging call din yana shafa goshinsa karo na farko da yaji wani abu mai kama da damuwa akan

"khaira,lallai jini ba karya ba ahankali ya dinga juya maganar mb acikin kwakwaluwarsa ita yanzu ta rigada"

"ta kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita ya jima zaune yana tunanin abunyi ba wai bazai iya taka mata burki ba ko d'aukar mataki akanta ba aa zatayi tunanin ko ya fara damuwa da khaira ne idan hakan ta faru kuwa zatayi tunanin wani abu akanshi wanda shi bazai so faruwar hakan ba ?""ai dole adamcy wata rana zaka damu da khaira dan ko yanzu kaji damuwa aranka har aka kira sallar magrib yana zaune yana tunanin khaira ,ahankali ya ajiye wayar a gefan gado ya mike ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya fito ya sauya kaya zuwa Jallabiya fara sol ya feshe ilahirin jikinsa da turare sannan ya nufi kofar fita zuwa

Please Login or Register in order to submit comment