Reading MAR ADAMS BOOK 4 BY AYSHA BAGUDU Chapter 28 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sonki Ina sonki !!!har na kan rasa kofar da zan shigo miki da kyauta dan dinbin farinciki dana kasance adalilinki na rasa me zan baki duk kyautar dana miki ganin nake ban baki komai ba me zan miki wanda zaki kasance acikin farinciki har karshen rayuwarki?""tayi shiru kawai tana cgb da kallonsa, kalamansa sunyi matukar kashe mata sansar jiki sai dai mamakinsa take yadda wani lokaci yake iya kwnatar mata da kai ya tausa sa kalamansa agareta ya dawo mata tamkar wani bawa wanda hakan yasa soyayyarsa take sake bin jinin jikinta har take jin son da take masa ya zarta wanda yake ikirarin yana mata ita dai tana iya boye nata ne, yadda ya tsura mata idanunshi yasa take jin soyayyarsa na sake ratsata ""burina a kullum na kyautata miki"

"maryama."""

"Taso wa tayi da kyar ta tsaya a gabansa ""bani da abinda nake bukata daga gareka da kyautatawa"

zuciyata face kaunarka mijina ka cigaba da sona kaine farincikina da samunka ne na samu yaye war damuwar komai arayuwarta kaine muradin Raina kaine farincikina bani da komai sai kai kana tattalina ka bani matsayi mai girma acikin zuciayarka ni da kai mutu ka raba zan dangwama cikin maka dagwamamkiyar biyayya bazan gaza ba in har hakan shine zai zama farincikinka Ina sonka mijina ta

"k'arasa maganar tana sunkuyar da kanta saboda tsananin jin kunyar maganrta .."""

Ya matsota sosai ya rungumeta ajikinsa tsam suna shafa sansar jikin juna shauki da kaunar junansu na

"sakè mamaye zuciyarsu ji suke tamkar su had'e guri d'aya .""fad'a me kike son na mallaki?ya tambayeta yana kamo ha'barta yana kallon face dinta ""ai na rigada na fad'a maka tunda ka soni a matsayin da nake ka gama min komai sukai shiru suna kallon kwayar idanun juna so take tai masa magana akan shan sigari duk da kwana biyu taga baya sha amman tana jin tsoron zai iya canzawa daga farinciki da yake ciki zuwa"

"damuwa dan haka zata bari sai zuwa wani lokaci."""

"ahankali ta zare jikinta tana duba agogo ""yalla'ba ya kamata ka shiga wanka ka fito lokacin na tafiya"

"kuma nasan taru takardu na can na jiranka shima agogo ya kalla sannna ya nufi hanyar bathroom yasa hannu ya bud'e sannna ya juyo tana tsaye tana kallonshi ""bana tsamanin zamu wuce wata biyu a kasar nan dole idan zanje england dake zani kiyi renon ciki acan"". yana k'arasa magana ya fad'a bathroom har ta bud'e baki zata masa tuni da adduar shiga ban d'akin sai taji mgnr daya sakar mata shi kuma har ya rufo kofar abun shi ta girgiza kai kawai tana kallon kanta ""wani irin ciki kuma ana zaman kalau duka yaushe akayi auren ?.""sakè girgiza Kai tayi tace ""yalla'ba kenan Allah ya bar min kai Allah ya kara maka lafiya yasa kayi tsawon rai mai albarka tana zaune tana tunnain irin soyayyar dake wakana a tsakaninsu dashi a kullum .a dan lokacin da sukai tare jinsa take kamar sun d'auki tsawon shekaru tare dan ya iya"

"soyayya ."""

bata ankara ba sai ganinsa tayi akanta ya fito daga wanka lallai tayi nitso cikin tsananin tunaninsa mai

"tarin yawa, ahankali ta d'ago ta kallesa domin tasan yana nan ya tsareta da wad'an nan tsumammun idanun nan shi masu karyar mata da zuciya, gabanta ne ya shiga fad'uwa ganin launin yanayin su ya sauya kamar ba daga wanka ya fito ba gabad'aya hankalinta a tashe yake kar yace zai yi wani abu daita gani tayi yanayin fusakrsa ta gauraye da murmushi wanda bai bayyana akan fuskashi sosai ba amman ita ta fahimci murmushi ne."" tafiya yayi da baya da baya yana kokarin sakin towel din dake d'aure a kugunsa tai saurin sunkuyar da kanta kasa tana jin fad'uwar gaba mai tsanani .""har ya gama shirinsa bata d'ago ta kallesa ba kamshin turarensa ne da ya doki hancinta yasa ta d'an d'ago kanta taga ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya yana tsaye ya zuba mata idanunshi yana kallonta kamar wani maye kafin ahankali ya tako ya zauna kusa daita batare daya d'auke idanunshi akanta ba ita kam tuni kanta yayi kasa"

"tana kallon kasan kafet ""."

"""har ka gama shiri ?""ta fad'a tana cigaba da kallon kasa bai amsa mata ba yace ""ki taso ki shirya mijinki"

"shima ya zama abun kunya a wajenki ?ta d'ago a natse ta kallesa da shayayyun idanunta ""yaushe nace abun kunya ne ?""ta fad'a tana masa wasa da idanunta ya d'an yi murmu shin gefen baki ""idan ba haka bane mai zasa da zan shirya kikayi saurin yin kasa da kanki?""Tayi shiru kawai domin ganin ya ranfota bata da ta cewa dan gaskiya tana jin kunyarsa sosai ""me zai sa ki dinga jin kunya ta haka nifa mijinki ne bai kamata ki dinga jin kunya ta haka ba komai kikayi min daidai ne haka nima komai na miki ke din tawa ce bata kowa ba still dai bata ce masa komai ba sai dai ta aro murmushi tace ""nifa ba kunyar ka nake ji ba kawai abun nan ne nake jin...""sai tayi shiru ta kasa k'arasa maganrta tana jin wani irin fad'uwar gaba"

"""wani Abu kenan ?""."

"tai shiru tana kawar da fuskarta gefe aranta tace ""wannan maganar tafi karfin bakina ""Ina jinki!""allah ya"

"gani bazan iya fad'a ba""ya jinjina kai yana dubanta ""look at me !ya fad'a cikin wata irin murya mai kashe"

"sansar jiki da kyar ta waigo ta zuba masa idanunta kamar yadda shima yake kallonta ""Ina bukatar acire kunyar nan a dinga kula dani yadda ya kamata ."""

"""kayi hakuri wata rana zan daina ""ya gyara zamansa ya matso sosai kusa daita hakan yasa ta sakè"

"sunkuyar da kanta hannunta ya kamo ya rike ya had'e da nashi ""idan ina kallonki bana iya rike kaina Ina son naga kin cire kunyar nan ya fad'a yana k'ok'arin had'e fuskokin su kafin tayi wani abu har lip's dinsa sun sauka akan nata tana kallonsa ya fara tsotsan lip's dinta lumshe idanun ta tayi tana kallon cikin kwayar idanunshi sai daya tsostsa son ranshi sannna ya tashi makale daita a parlour'n ta zame hannunta cikin nashi tana masa fatan alkhairi da dawowa lafiya ""ban gane nufinki ba !""sarai ta fahimcesa dan"

"haka tace ""kayi hakuri anan zan tsaya "". yace saboda me !?"

"""Ka fahimta mana""! tayi maganr cike da shagwa 'ba ya dawo kad'an ya janyota jikinsa ""ban gane ba ki"

"ganar dani na fahimta ,fuskarta ta manna a k'irjinsa tana boye fuskarta .""ya fahimceta sarai saboda yanayin tafiyar ne ""idan saboda tafiyrki ce zuwa anjima zaki dawo normal ta d'ago ta kallesa tana hura"

"masa hanci batare da tace masa uffan ba ,"" muje kici wani abu ""ta girgiza masa kai"" for now bana jin cin"

"komai idan ina bukatar wani abu zan sauka ""duk yadda yaso tabisa taki binsa anan sukai sallama ya kamo bakinta yana tsotsa da kyar ta samu ta cire bakinta acikin nashi ya tsaya yana dubanta tare da kai hannunsa ya kamo kuncinta yana kashe mata idonsa d'aya kamar wata sokuwa haka ta tsaya tana kallonsa ya kai bakinsa daidai kunnenta ya sakar mata zazzafan kiss, saurin d'auke numfashi tayi tana"

"lumshe idanunta bata san tsawon minti nawa ya d'auka kafin ya cire bakinsa ba sai ji tayi ya fice ."""

Tunda ya fita suna makale a waya ko kiransa akayi zai ce ta rike wayar da zai shiga metting ne yace ta

"shiga d'akinsa ta duba durowa da system dinsa take kai zata ga wani book ta d'auka ta karanta kafin ya fito tace ""okay tare da mikewa ta shige d'akinsa ta d'auko ta fito zuwa parlour tana zaune tayi zurfi sosai cikin karatun book din soyayya ne sai ga tabawa tana nemi izinin shigowa. bayan ta shigo ta gaidaita cike da girmama wa tace ""hajiya tace kizo !"" tai tsam da ranta tana tunanin kafin ahankali tace mata ""okqy ganin nan zuwa ""tabawa ta juya ta fice bayan fitar tabawa ta mike ahankali tana jin fad'uwar gaba dan bata san dalilin kiran ba kuma jikinta tuni ya bata kiran bana alkhairi bane "".ahankali ta koma d'akinta ta d'auko hijab ta sanya ta fito tana taku a natse har ta sauko babban parlour'n gidan sai dai bata ganta a parlour'n ba ta tsaya shiru tana tunanin shiga parlour'nta na biyu dan haka ta samu waje ta zauna akan kujera tare da had'e hannuwanta tana wasa dasu bata jima da zama ba sai ga tabawa ta fito daga hanyar parlour'n mami ,d'an murmushi tayi tace ""ranki ya dade ai hajiya tana wan can parlour'n ki"

"k'arasa can .""tana gama fad'ar haka ta shige kitchen."""

jikin maryama da muryarta a sayayye ta nufi hanyar parlour'n gabanta na matsanancin fad'uwa da

"karfin gaske ,aiko tana gama shiga parlour'n tayi mugun gani domin kuwa aunty khadija,aunty shahida zabiba da auta ne zaune sai mami dake zaune a tsakiyarsu suna tautauna wa ,nan take jikinta yayi sanyi haka gabanta ya cigaba da fad'uwa da yake bata san lokacin data soma karanto adduar da zata kare mutun daga duk wani abinda ya tunkarosa( allahumma inna na'uzubika min jadil bala'i wadarki shaka'i wasu 'il kad'a'i wa shamatatil ahda'i ) da kyar ta dinga d'aga kafafunta tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki ta cigaba taku inda gabad'aya suka zuba mata idanu suna mata kallo mai d'auke da tsana da kaskanci ,bata tsaya akoina ba sai a gaban mami ta durkusa har kasa ta gaisheta a tsorace ""mami ina yini ""!?da kyar mami ta bud'e baki ta amsa mata da ""lafiya !""atakaice sannan ta juya ta gaishe da yayyen mijinta da zabiba batare data gaishe da nana hauwa'u ba zabiba ce kawai ta amsa mata gaisuwarta"

"itama babu wani sakin fuska ,ta maida hankalinta ga mami tace ""mami gani !"""

"Kafin mami tayi yunkyrin yin magana aunty shahida tace ""ita nana hauwa'u sa'arki ce da ba zaki gaishe"

"daita ba ko kuwa rashin mutuncin da kike wa shi wancan shayayyen sokon mijin naki zaki kawo ma mutane ?""maryama tai shiru tana dukar da kanta kasa azahirin gasky taso ta gaishe daita amman ganin"

"yanayin yadda take jifanta da mummunar kallo yasa taki gaisheta""idan shi kin shanyesa kin gama dashi"

"mu baki isa ki gama damu ba, idan ma ba shi ba me ne ne abun so a wajenki ?""wallahi idan na kalleki"

"kullum dariya nake fashe wa dashi saboda ba inda ya kamata soyayyarsa ta kare ba kenan amman munyi masa uzuri tunda ba haka aka barshi ba an rigada an dabaibayesa da mugayen asiri wallahi rayuwarsa is so pity kin d'auki kaya kin d'aurawa kanki kiji tsoron Allah abinda kikayi kika rufe wa d'an uwamu ido dashi ki kwancensa""ke da iyayenki kunyi shirka kun mallake sa idan ba haka ba ina shi ina ke bare wannna tsinanniyar unguwar taku da ko masu aiki a karkashinaa bazasu zauna acikinta ba bare macen da yake aure .""ahankali maryama ta d'ago kanta tana kallon aunty shahida dake magana cikin"

"nuna isa da mata kaskanci ."""

"""Wallahi ina namiji bazan ta'ba had'a iri dake ba ko ba dan komai ko dan zuriar da zan had'a dake na"

"kaicewa aurenki wai fa ashe ubanta d'an giya ne kuma acikin giyar ya mutu uwarta kuma sai da suka gama hole warsu da ubanta akayi auren wallahi tur da aurenki ""aunty shahida ta k'arasa maganar tana zabga mata harara""inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa tana runtse idanunta tana danne damuwarta da hawa yen daya cika idanunta dan karsu ga raunita bayan aunty shahida tayi shiru itama aunty khadija ta Kama hakan yasa mami ta mike ta shige d'akinta tana goge hawayen bakinciki abinda adamcy yayi mata uba dan gida uwa karuwa wani irin zuriar zata hanfo masa tashin mami ya bawa maryama kwarin gwaiwar yin magana "".tace kuyi hakuri duk abinda zakuyi ya tsaya iya kaina amman karku ta'ba min mutuncin iyayena sai maganar asiri da kuke ta faman mgan akai kusani ni ba jahila bace inada ilimi bazan yiwa namiji asiri dan ya soni ba dan banga ribar me zan samu akan haka ba""yanzu ku amatsayin ku na iyaye iyaye wad'an da suke da ya'ya mata ..""""ke dan ubanki waye sa'anki"

"anan nana hauwa'u ta fad'a tana katse maryama ta hanyar fad'ar haka ."""

wani kallo maryama ta d'auketa dashi wanda hakan yasa nana hauwa'u ta mike tsaye tana k'okarin

"rufeta da duka maryama tayi sauri ta mike ta nufi kofar fita da sauri nana hauwa'u tana biye daita tana zaginta sauran taku uku tsakaninsu ta cafko maryama ta shige ta banko kofar da karfi kofar ta rufe kanta aiko tayi tayi ta bud'e kofar ta kasa dan haka tsaya a bakin kofar tana buga kofar da karfi ""wato ke gaki yar iska yau sai dai karki fito yunwar cikinki ma kad'ai ta isheki amman muddin kika fito sai kin ci ubanki ""maryama dake tsaye a tsakiyar parlour hawaye take zubar wa jikina na rawa "" wai ke har kin isa aunty shahida tana fad'a kina fad'a wai gaki shegiya zaki fito ne yar gidan matsiyata matsefa"" can sai ga aunty khadija tace ""auta kofar a rufe take ne ?""shegiya matsiyaciyar yarinya ta rufe kofar amman zata ci uwarta sai dai karta fito ""wallahi zaki sani tunda kika yi silar rabamu da d'anuwanmu kema zaman gidan nan sai yayi miki zafi zamuyi addua kam ya dawo haiyacinsa amman kema zaki ci ubanki "".inji cewar"

"aunty ."""

"khadija."""

"Aunty khadija ta numfasa tace ""auta na baki wannan aikin ki tabbatar kin lakadawa wannan yar gidan"

"matsiyatan mugun duka ""ai karki damu aunty bani kad'ai zanyi wannna aikin ba tare da sister zamu ci"

ubanta ai wallahi adamcy ya cucemu daya auro mana wannan yarinyar aunty khadija taja hannun nana

"hauwa'u suka sauka suka koma parlour'n mami alokcin mami ta fito tana cewa ""ai ni ba aurenta bane damuwata a yanzu kamar yadda kuka ce ubanta d'an giya ne uwarta kuma karuwa ce wallahi wannna shine babban tashin hankalina ""asalinta kenan sai dai mu d'age da addua kuma muyi maganinta Allah sarki maryama kam tana can ciki tsananin tashin hankali hannunta rike da waya tana son ta kira adamcy tana jin tsoron abinda zai biyo baya jin sun wuce yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya.""Duk wuni ranar a storace maryama tayi sa acikin d'akin da ta d'an ji motsi jikinta zai Kama rawa har most especially kasan mararta ta kai hannu ta dafe kasan mararta da take wani irin karkarwa shiyasa bata sauka dan karta had'u dasu daga d'akinta sai parlour'n ko abu take bukata hakura take har sanda zai dawo ta"

"kwanta flat akan kujera dafe da mararta tana zubar da hawayen cin mutuncin iyayenta da sukai ."""

Karfe biyar daidai ya dawo gidan kallo d'aya yayi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta dan ko kusa

"dashi bata zo ba yayi mata tambayr duniya tace babu komai kanta ke ciwo ""shine ba zaki kira ki fad'a min ba?"" ya fad'a yana janyota ya had'eta da jikinsa ya kai hannunsa daidai kanta normal yaji kanta sannan ya zarce da hannunsa kasan mararta yana shafawa ahankali ""me kika bawa baby nah yaci ?""tai masa narai narai da idanun tana had'e fuska ""nifa bana da komai ""ai bazaki san kina da ba amman ni naji alamun kina da akan jijiyata ""Allah bani da komai karki min mutsu mana dan rashin wayonki bazai bari ki fahimta ba, ya kai bakinsa yana tsotsa karan hancinta ta zare jikinta ta koma can nesa dashi ta tsaya .""ahankali ya taka ya sake janyota jikinsa gabad'aya ya rungumeta tare da matseta gam ajikinsa wani iri taji ajikinta nan take gabad'a ya tsigar jikinta suka mike hatta numfashinta sai daya nemi ya"

"d'auke sakamakon irin rungumar da yayi mata ""Ina son ki haifa min yara da wuri."""

"""Bayan kana da wata !""naki nafi so !ya fad'a yana shafa mata sansar jiki ""bari na baki maganin ciwon kai"

"kafin lokacin sallah yayi wani kallo tayi masa tana shagwabe masa fuska ""naki wayon tunda ka fita kaina da marata ciwo suke ""yarin yar nan fa na gano ki babu abinda ke damunki so kike ki doje min kuma baki isa ba haka yayita jagwalgwalata har sai da yaji kiran sallah daga massalaci dake cikin estate din sannna ya barta ya shiga bayi .""da daddare da misalin karfe goma adamcy na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda maryma ke zaune a tsakkiyar gado ta cigaba da karatun novel din d'azu , madadin tayi murmushi saboda kashi hamsin na damuwarta ta kau amman taki sakin fuska yanzu ma tana karatun ne dan samun sausaucin abinda ke damunta sai tayi kamar ta fad'a masa sai ta danne .""shi kuwa lokaci lokaci ya kan d'ago idanunshi ya kalleta saboda gaba d'aya"

"hankalinsa yana kanta ."""

shiru yayi na second biyar yana kallonta cikin rigar bacci fara sol iya gwiwarta ahankali ya d'auke

"idanunshi ya maida kansa ya cigaba da aikinsa da yakeyi ,sai dai kasa cigaba da aikin yayi ya taso daga shi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon inda take rigingine itama sai ta tashi zaune sosai tana"

"kallonsa ya zauna a gefenta tare da ajiye mug d'in hannunsa akan bed side d'in, laptop d'in kuma a"

"saman gadon d'ayan gefensa. hannusa ya miko mata alamar tazo garesa .bata musa masa ba ta matso ya janyota gabad'aya ya had'e ta da jikinsa tare da makaleta a tsakkiyar k'afafunsa.ahankali ta zame ta kwanta ta d'ora kaina a cinyarsa daman wajen da ya fi son ta kasance kenan ya kar'bi book d'in hannuna ya ajiye a gefe, ya d'ora hannusa a saman cikinta yana sakè maimaita tambayarta damuwarta ""wai meke damunki ne ?""cike da sanyin jiki ta shafa sajensa shi kuma ya d'an ciza lips dinsa na kasa ""miyasa wataran kike da miskilanci ne ?""tace ""ni d'in?"". 'ta fad'a tana nuna kainta da kallonsa'.sai wani"

"basar dani kike inata tambayrki meke damunki ?"".."

"""Me ka gani ne kake ta faman tambayata?"" yace ""abubuwa dayawa""tace to babu komai kasan wani"

"lokaci yanayin mutun yana canzawa haka dai na yini yau ban sani ba ko dan kaina da marata dake ciwo ne ""ta fad'a tana gyara kwan ciyarta ajikinsa wanda yasa shi Lumshe idanun shi , ya duk'o a hankali ya manna mata kiss mai kyau a goshinta .sannan ya dauko novel d'in yana duba shafin da take kallon kasan ido yayi mata sunkuyar da kanta tayi tare da kai hannu ta Shafa sumar kanta ta kai hannu zata kar'bi book din ya hanata yana furta sunan book din how I love to be loved,a lokuta dadama waanan book din ke debe min kewarki most especially wannan page din ya damk'a mata book din a hannu yana shafa sumar kanta aranta tace dole kaso page din tunda iskanci ne zalla amman a zahiri murmushi ta sakar masa very interesting novel ""wow!""ya fad'a da d'age mata girarsa d'aya bakinta ta turo masa tana girgiza masa Kai yace kina son ki tashi kaina kenan ?""ta sake girgiza masa kai tana mur mushi shi din ma fuskarsa a sake take ta fahimci sai lokacin ya samu natsuwa , ya jawo lap top d'insa ya cigaba da aikinsa ita kuma ta zuba masa ido yana cigaba da aikinsa batare da ya kalleta ba, idonsa na kan system d'insa"

"yace, ""kallon fa ko kina bukatata ne ?"""

"ahankali ta d'auke idanunta tana tabe baki a ranta tace ""aikin ka kenan!""shima ta'be baki yayi alamar"

"me yayi . karatu ta cigaba shima ya cigaba da aikinsa yana shan coffee time to time yayi aiki mai tsawo kafin ya saki wani ajiyar zuciya, ya kalli maryama da barci ya kwasheta hannunta rike da novel fuskarta ya shafa yana sake sakin ajiyar zuciya bayan ya gama ya duba camerorin gidan shiru yayi tare da kai yatsan hannunsa kan hakorinsa ahankali yaga duk abinda ya faru a gidan mamaki ya cika zuciyarsa hankalinsa yayi matukar tashi ganin irin gudun da maryama tayi domin ceton kanta daga nana hauwa'u ya ALLAH wannan irin tashin hankali ne haka ?""ya furta a fili yana kallonta baiwar Allah shiyasa yanayinta ya sauya zuwa damuwa amman kuma taki fad'a masa abinda aka mata ""nan take zuciyarsa ta dinga masa tuttukin bakinciki ya duba agogon wayarsa karfe d'aya da wasu mintuna ta wuce Amman bazai iya hakuri har garin Allah ya waye ba number mijin aunty shahida ya kira kiran na shiga ba'a d'aga ba haka zalika ta mijin aunty khadija kira uku yayi ana na hud'u ne ya d'aga cikin bacci yace ""adamcyn ..""adamcy ya katse shi da sauri ta hanyar furta sunansa ""kabir!wanda aka kira da haka ya mike zaune yana damke wayar hannunsa da kyau ""kabir!! sau nawa na kiraka ?"" yace sau biyu ""ka jawa matarka kunne ta fita a"

hanyar matata idan ba haka ba zan d'auki mummunar mataki akanta yana gama fad'ar haka ya katse

kiran ya kira hisham shima cikin sa'a ya d'aga abinda ya fad'a wa kabir shi ya fad'awa hisham ya katse

"wayarsa yana dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi ."""

Ya d'auki kusan mintuna talatin yana dafe da goshinsa sannan ya cire hannusa yana ciza lip's dinsa

"ahankali ya soma motsa bakinsa ""idan kunsan wata baku san wata ba idan na daukeki muka bar kasar gabad'a ya zan ga yadda zakuyi ya k'arasa maganar yana sumbatar goshin maryama,kwanciya ya gyara mata ya ja bargo ya lullu'ba mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala kamar yadda ya sabar ma Kansa kafin ya kwanta sai yayi alwala bayan ya fito ya kwanta a gefenta zuciyarsa na cike da tausayinta addu'a ya musu sannan yasata a jikinsa yana shafa jikinta tana jin motsinsa a jikinta ta share ta cigaba da baccint""Washegari bai nuna mata yasan komai daya faru ba sai dai bayan yayi breakfast ya gargad'eta da"

"karta sake ta fita duk abinda take so da zarar ta danna bell masu aiki zasu zo su kawo mata ."""

tai shiru tana jin bayaninsa har ya gama ya riko hannunta suka fito tare zuwa bangaren mami koda suka

"shiga tana bayi tana wanka wankata kuma yana d'aukar lokaci amman haka ya zauna jiranta ,itama haka ta zauna ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa yace ""ko dai zan tafi dake ne !""kamar tace masa!eh!sai kuma ta girgiza masa Kai ."""

"""me yasa yanzu bakya son cigaba da zane naga ko a gida bakya yi ?""zan cigaba mana hutun wata nawa"

"aka bani domin nasan ranar komawa aiki ?""""ba maganar komawarki aiki nake yi ba ai aiki kin gama dashi har abada sai dai idan ina bukata zaki min a gida""ya fad'a yana kissing din hannunta yana matseta da jikinsa tare da kai bakinsa daidai kunneta tayi saurin zame jikjnta daga nashi ""yalla'ba mami fa karta fito ya sake matseta yana harararta yace""ni fitowarta nake so ai ""naunauyen ajiyar zuciya ta sauke ita dai Allah ya had'ata da gamonta babu jimawa mami ta fito kafin yayi wani abu ta zame ta durkusa kasa tana gaisheta ""ta d'an yi shiru tana dubansu dan ta ga yanayin da suke harara ta buga ma maryama tana nuna mata hanyar waje da hannunta ta d'an yi shiru tana dubanta duk da ta fahimci abinda take"

"nufi .""""Sweetheart kina nufi maryama ta fita?"" ya tamabyeta yana had'e fuska tamkar an aiko masa da"

"sakon mutuwa ""idan bata fita ba me zata min ?""."

"""haba sweetheart me yasa ?""idan bata fita ba yanzu zan bar maku d'akin d'an bazan kasance tare da"

"makiyiyata ba domin duk mutumin da yayi silar rabaka da d'anka babban makiyinka ne bakinciki ya kama maryama zuciyarta kamar ta Kama da wuta ""bana son gaisuwarta bana buka tar ganinta kai ma idan bazaka zo kai kad'ai ba na yafe amman karka k'ara shigo min da wannan abar tunda bayan asiri data maka yan uwanka ma ka bata damar ta rainasu wai har wannna yarinyar shahida zata gaya ma magana saboda ta samu d'aurin gindi a wajenka taci

Please Login or Register in order to submit comment