aure wanda zai aure ni ba, amma na rasa nagartacce wanda nake da yaƙiyin zai riƙe ni saboda Allah ya kyautata mini, wanda ya san ma mene ne auren, don matsalar da take damun mu yanzu majority ana auren ne kawai ba don an san mene ne shi ba, ba don an ɗauke shi ibada ba, ana yin shi ne don wata buƙata, ko a bi kyau, ko kuɗi, ko neman ɗaukaka, ko dan a ce mutum ya yi auren shi ma, gabaɗaya ba ga matan ba, ba ga mazan ba, duk an daina aure saboda Allah da bauta masa, ƙalilan ne masu yi don haka. Wasu kuma ilimin zaman auren ma da yadda za su tafiyar da junansu a zamantakewar auren ne ba su da shi. Rimi-rimi za ki ga mutum ya zo mini da gaske da niyyar aure, amma daga mun yi dogon zama zan gane ba za mu zauna inuwa ɗaya ba, masu kuɗin da masu kyan da talakawan duk suna zuwa, amma samun nagartaccen a ciki ya yi wahala, saboda Juma'ar da za ta yi kyawu tun daga Laraba ake gane ta. Maza na gari sun yi wahala Hafsah, ki riƙe mijinki gagam wallahi, idan ba haka ba za ki yi da na sani mara amfani, za ki yi nadama a lokacin da time ya ƙure miki, za ki yi saki na dafe. Yanzu da za ki yi shela ki fadi halin Abban Sultan ki ce idan da mai son shi za ki bari ta aure shi sai kin ga mata dubu sun zo, kuma da kike ta cewa talauci ai shi ba talaka ba ne, yana da rufin asirinsa, bai taɓa gazawa ba tunda kuka yi aure. Na ga gidan hayar da kuka fara zama kafin Allah ya hore masa ku yi naku, abokan hayar taku sha'awar ku suka dinga yi, yadda yake kula da ke da tattalin ki, ya ba ki lokacinsa. Mama kullum cikin sam barka take yi miki, kullum aka tashi zance aka ce maza sun zama ƴan kansu yanzu sai ta bayar da misali da ku, ta ce ƙawar Naja kuwa ta yi dace da mijin marainiya, Allah ka ba wa ƴaƴanmu irinsa." Baki na taɓe don ni gabaɗaya hankalina yana kan yadda za a yi na fito fes a taronmu na ce. "Sai faɗar alkhairinsa kike amma ban ji kin faɗi aibunsa ko ɗaya ba, mutumin da yake zuba mun uban kulle, kamar wata kayan kadara." Numfashi ta sauke ta ce. "Alkhairin nasa ne ya fi aibun yawa, kulle kuma tabbas na san yana da shi, kuma da ma ai ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, amma duk da haka ai ba ya hana ki zuwa biki ko sunan dangi da na maƙota, duk abin da ya faru na jaje yana barin ki, ki je, fita ce haka barkatai babu dalili yake hanawa, ko so kike ya bar ki kina wuni a maƙota da gantali a unguwa?" Hararar ta na yi na ce. "Ban sani ba, tunda ba ke ake turkewa a gidan kamar akuya ba ai dole ki ce haka. Nan gidan Maman Sadik ga baki ga hanci, jikin gidana amma sai na yi watanni ban je mata ba, tun suna shigowa su har sun gaji sun daina saboda ba na zuwa."
"To me za ki je ki yi musu? Na ga Asma'u cousin ɗita da suka zuna a bayan layin nan yabon ki ta dinga yi, lokacin da aka yi wani faɗa har da zuwa police station, a saboda irin yawon gulmace-gulmacen nan da ake yi na bin gidan maƙota kullum, ta ce kin huta abinki, ko me za a yi na tashin hankali babu ke a ciki, asirinki a rufe. Amma ke kin raina hakan ko?" Na ce. "Ai shi saboda kar na fita na ga halin da duniya da take ciki ne ya sa yake kullen, kar kuma na ga yadda maza suke bauta wa matansu tunda shi ba ya yi." Naja ta ce. "Ko? To kar ki nutsu ki san inda yake yi miki ciwo, duk da zan yi miki uzurin rashin sanin halin da duniya take ciki, na rayuwar ƙarya da packaging da mutane suka ɗaura wa kansu, shi ya sa kike ganin kamar su waɗancan matan komai gaskiya suke faɗa. Tunda babbar wayar ma ba ki daɗe da fara riƙe ta ba." Cikin ƙosawa da jawabanta na ce. "Su fa ba maƙaryata ba ne, saboda sun sassan gidajen juna suna zumunci, idan ƙarya suke ai ba za su bari a je inda suke ba." Jinjina kai ta yi ta ce. "Ni fa ban ce ba masu kuɗi ba ne, amma ba zai yiwu a ce duka group ɗin ke kaɗai ce talaka kamar yadda kike faɗa ba, kuma masu kuɗi wanda suka tashi a cikinsa ba za su yi irin wannan banzar rayuwar ba, ta komai naka sai ka tura a group an gani, ka yi son a sani, sai dai ko ƴan taka haye ne ƴaƴan Malam Shehu suka auri masu kuɗi, shi ne ba a saba da rayuwar ba ake nuna wa duniya, ko kuma duk packaging ne kashe kai ake a yi abin ƙaryar. Kuma ko da ma masu kuɗin ne kina da tabbacin kowacce tana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali kamar ki? Wata ƙila mijinta mai duka ne, wani ɗan shaye-shaye, wani mai bin mata ko maza, wani ma kuɗin ba na halak ba ne, ba ki san ta yadda suke samun su ba." Ɗaga mata hannu na yi na ce. "Kar ki yi musu mugun fata kuma." Murmushi ta sake yi ta ce. "Misali kawai nake ba ki, ba wai ina nufin hakan ba ne, kawai dai ina faɗa miki ne don na san ba za a rasa ba. And lastly yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi, idan kina tunanin za ki kashe aurenki ki fita ki auri mai kuɗi to kin yaudari kanki, don kowa ɗan'uwansa yake aure, talaka sai talaka mai kuɗi sai mai kuɗi, sai dai ikon Allah da tsananin rabo ne yake saka mai kuɗi ya auri talaka." Miƙewa na yi a fusace na ce. "Ya ishe ki haka wannan cin fuskar da kike mun!" Ita ma miƙewar ta yi ta ce. "Idan na ci miki fuska ai kaina na ciwa Hafsah, gaskiya nake faɗa miki, kuma da ma an ce ɗaci gare ta, ki zauna, ki nutsu, ki yi nazari da kyau don Allah, ko don ƴaƴanki da ke kanki. Zan kira Anas mu yi magana da shi idan na koma gida, zan ce masa ni na hana ki tafiya, na san ba zai ƙi mayar da ke ɗakinki ba in sha Allah. Duk da na ga ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan nan lokacin da na shigo, don ba na jin ma ya lura da ni. Please ƙawata ki watsar da mutanen can, ki manta da su, ki bar group ɗin ki goge numbers ɗinsu, ke ki canza sim ma gabaɗaya yadda ko sun kira ba su same ki ba, idan ba haka ba wallahi za su kai ki su baro." Na ce. "Na ji na gode." Bi na kawai ta tsaya tana yi da kallo na wasu sakanni. A sanyaye ta ce. "Idan kika bar Anas ba shi kaɗai kika butulcewa ba, har da ubangijin da ya tsamo ki daga cikin jarrabawar rayuwa, ke kuma kike ƙoƙarin siyen ta da kuɗinki. Kina da iliminki na addini daidai gwargwado, kin san arziƙi da talauci duk na Allah ne, a kullum Ubangiji cikin raba arziƙi yake da ƙwace shi, babu wanda aka haifa da dukiya, kowa da kika gani a nan gidan duniya ya samu kuma a nan zai bar shi. Don haka wannan kaɗai ya ishe ki darasi a rayuwa. Ƴaƴa da miji na gari da lafiya su ne babban arziƙi a duniyar nan, kuma duk Ubangiji ya ba ki su, maimakon ki gode masa sai ki raina?" Shiru na yi don zuwa yanzu maganganunta sun fara ratsa ni sosai, ganin haka ta dafa kafaɗata ta ce. "Zan tafi, ina fatan za ki yi amfani da dukkan shawarwarin da na ba ki, sannan kuma don girman Allah kar ki ƙara kwatanta haukan zagin Anas, bare ki taɓo iyayensa, ina jiye miki siyen ticket ɗin wutar jahannama da hannunki, tunda kin san hukuncin mai aikata abubuwan da kike yi a musulunci. Don haka idan kunne ya ji jiki ya tsira!" Daga haka ta ɗauki jakarta ta juya ta fice. Kasa kataɓus na yi na bi bayanta da kallo kawai cikin mutuwar jiki, gabaɗaya ta gama ɗaure ni da jijiyoyin jikina. Na shafe kusan mintuna biyar kafin na ja ƙafata na shiga ɗaki. Ringing na tarar wayata tana yi, na ƙarasa na lalubo ta na duba na ga har kiran ya katse, missed call sama da 10 na tarar na Maman Nasmah. Ban yi yunƙurin bin ta ba don na san ban da ishashshen katin da za mu yi doguwar magana. Wani kiran nata ne ya ƙara shigowa, tsayawa kawai na yi na ƙura wa wayar ido, zuciyata na kokwanton na ɗaga ko kar na ɗaga? Na bi shawarar Naja na fita daga group ɗin na manta da su na ci gaba da rayuwata kamar da, ko kuma na ci gaba da zama a cikinsu da burin kasancewa kamar su ko ta halin yaya?........✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*13.*
Ban gama yanke shawara ba shi ma kiran ya katse, ko 1 second ba a yi ba wani ya ƙara shigowa. Ɗagawa na yi cikin son jin dalilin wannan uban kiran da take zabga mini. Cikin faɗa kamar wata uwata ta ce. "Ina kika ajiye wayar ne nake ta kiran ki ba ki ɗauka ba?" Ba yabo ba fallasa na ce. "Ina parlour ne, wayar kuma tana ɗaki." Ta ce. "Okay, ya kuka yi da shi? Ya dawo miki da kayan naki?" Numfashi na sauke na ce. "A'a, ya ce ba shi ya ɗauka ba, na haƙura kawai na bar wa Allah." Cikin zuzuta ta ce. "Kin ce gobe ya ƙara ɗauka kenan? Shikenan kin buɗe masa ƙofar jidar miki abubuwa, ina nan na kasa sukuni saboda tunanin halin baƙincikin da kike ciki ashe ke har kin ware? Tsabar yadda na damu da abun ko abinci ban iya ci ba tunda kika faɗa mini." A sanyaye na ce. "To ya zan yi? Na yi bala'in na yi masifar, ƙarshe har saki na ya yi fa."
"Saki kuma?" Na ji ta faɗa a yanayin da na kasa tantance na murna ne ko kuma na ruɗu ne, saboda yadda ta yi kamar za ta fasa mini dodon kunne.
Na ce. "Eh, kin ga ya zama biyu kenan, da na farkon nan da ya ce idan na fita a bakin aure na, na ɗauka baraza ce kawai ya yi, ashe da gaske yake." Cikin karsashi ta ce. "To shi ne me? Ai akan gaskiyarki kike, kuma duk abin da ya faru shi ne ya janyo da ya ƙi kula da ke ya yi miki dukkan abin da kike so, ƙarshe ya ƙara miki da sata." Shiru na yi ban ce komai ba, don na rasa abin faɗi. Cikin sassauta murya ta ce. "Amma ki kwantar da hankalinki, ki zo gidana yanzu, ga ɗinkinki nan an kawo ki zo ki karɓa, duk abubuwan da aka sace kuma zan ƙara ba ki sabbi, har wayar ma duk zan siya miki sabuwa dal, idan da wadda kike so sai ki faɗa a kawo ta, idan kuma ba ki da choice zan ce a kawo miki irin ta hannuna." Cikin farinciki na ce. "Da gaske za ki ƙara ba ni kayan, har da sarƙar gold ɗin?" Ta ce. "Mene a ciki? Yanzu ina yi wa Hubby waya zai saka a kawo komai, wannan ba komai ba ne ai a gurinsa, kuma ko me na ce masa ina so babu ɓata lokaci yake mun, so kar ki wani damu. Ina son ki fito fes kamar kowa ke ma a gobe." Dogon numfashi na ja na sauke na ce. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ya bar ƙauna tsakaninki da mijinki." Ba ta amsa ba ta ce. "Ki yi maza ki zo, yanzu zan tura miki address ɗin."
A gaggauce na shirya cikin doguwar rigar atamfa cikin zumuɗi. Jikina har tsuko yake saboda farinciki. Na yi niyyar bin shawarar Naja, amma sake ba ni kayan da Maman Nasmah ta ce za ta yi ya sa na manta da wata Naja'atu da batunta ma gabaɗaya. Ban damu da rashin dawowar su Sultan ba har biyu saura na fice daga gidan. Na samu mai napep muka tsadance ya kai ni har ƙofar gidan Maman Nasmah.
Tun daga farkon unguwar tasu na tabbatar wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, saboda maka-makan gidajen da na fara tozali da su, sakin baki na yi ina ba wa na mujiyata abinci. Gabaɗaya sai na ƙara raina kaina. Muna tafe ina waya da ita tana faɗa mini inda zan na cewa mai napep ɗin ya bi. A bakin wani ƙatoton gida muka tsaya. Da sauri na zuro kaina kamar zan faɗo ina ƙare masa kallo, ban san lokacin da bakina ya furta. "Aljannar duniya." Ba. Sai da drivern ya mini magana sannan na dawo cikin hayyacina na fita na sallame shi. Ban san ya zan iya fasalta girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ba tun daga waje ma. Don ko tantama ba na yi idan na ɗaga kaina na ce zan hango ƙarshen tsayinsa sai ɗankwalin kaina ya faɗi. Ina nan tsaye da baki a buɗe aka buɗe ƙaramar ƙofar makeken gate ɗin gida, wani matashi ne ya ƙaraso inda nake ya ce. "Ke ce baƙuwar Hajiya?" Ɗaga masa kai na yi don ruɗewar da na yi ta hana ni magana. Ya yi gaba na bi bayan shi ina tuntuɓe saboda kalle-kalle. Mun yi tafiyar mintuna biyar kafin mu kai inda part ɗinta yake. Ya danna wani abu da ban san mene ne ba, babu jimawa aka buɗe ƙofar da ita ma ɗaukar ido take ya ce na shiga. Zan cire takalmi yarinyar da ta buɗe ƙofar ta ce na shigo da shi. Duk yadda na so sakaya ƙauyancina amma sai da ya bayyana kansa, saboda tsintar kaina da na yi a wani tsamfatsetsen parlour, wanda ya wadatu da fitilu masu wasu wani irin ƙyalƙyali da haske. Ajiyar zuciya na sauke na lumshe idona tare da ƙara baza hancina, don sake shaƙar sassanyan ƙamshin da yake tashi a parlourn a wadace. A iya tunanina ban taɓa tsammanin za a samu kamar wannan falon a Nigeria ba sai dai a ƙasar waje. Sai da muka wuce faluka uku, a na huɗu wanda yake upstairs muka tarar da Maman Nasmah. Fuskarta ɗauke da fara'a sosai ta taso ta rungume ni tare da yi mini sannu da zuwa. Na amsa cikin yaƙe, don ko mai aikinta da ta yi mini jagora ta fi ni kyan gani, don daga gani suturar jikinta ma ta fi tawa tsada. Ta zaunar da ni bayan ta baya wa yarinyar umarnin ta kawo mini drinks. Tana ta jana da hira amma na kasa sakin jikina, satar kallon parlour'n kawai nake ina faɗin. "ALLAHUMMA ARZUƘUNI" A cikin raina. Ita kanta sai na ga ta ƙara yi mini kyau fiye da ganin farko da yi mata, yadda ta hakimce a kan kujera cikin shiga ta alfarma tana latsa waya a gayance ba ƙaramin burge ni ya yi ba. Hakan ya ƙara girmamar burina na son rayuwar kuɗi da hutu. Ta wata ƙofa da ke cikin parlour'n ta shigar da ni inda dinning yake shi kaɗai da zan ci abinci, haɗuwar gurin da tsaruwar shi da kyawun dinning ba za su faɗu ba, food flaks ɗin da aka zuba abincin ma kaɗai abin kallo ne. A taƙaice dai duk yadda nake tunanin girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ya wuce nan, don tamkar rainon daji haka na koma saboda ƙauyanci. Bayan na yi Sallah ina zaune a bedroom ɗin da ta kai ni ta shigo ta ce. "Kamar kina cikin damuwa ko?" Na ce mata. "A'a babu komai." Baki ta taɓe ta ce. "Ai ko kin ɓoye fuskarki ta fallasa ki, kuma na san ba zai wuce akan wancan mijin naki ba ne, da zuwa yanzu ya kamata a ce kin gane ba son ki yake ba, tunda har akan abu ƙanƙani ya iya sakin ki." Girgiza kai na yi na ce. "Wallahi ba shi ba ne, don yanzu da shi da babu duk ɗaya ne a gurina." Murmushi ta yi ta ce. "Ko ke fa, anjima za a kawo kayan naki, yanzu mai lalle ta zo tana parlour, mu je ta yi mana ko iya baƙi ne, tunda time ya ƙure ba damar yin ja." Na ce. "Tom shikenan."
Ana yi mini lallen Maman Nasmah tana ƙara kushe Anas da aibata shi, da nuna mini ko ya dawo ya ce na koma kar na yarda, ni dai na yi shiru ban ce komai ba, don har yanzu zafin sakin bai bar sukar zuciyata ba.
A ɓangaren Maman Nasmah kuwa wani irin farinciki da annashuwa take ji, duk da a plan ɗinta saki uku take so Anas ya yi wa Hafsah kafin ta shiga cikin rayuwarsa, ta yadda babu aure a tsakaninsu kenan bare ya ce zai mayar da ita. Tana lura da yadda ta ɗimauce da ganin gidanta, ta dinga murmushi a ranta tana faɗin. 'Kina burin kasancewa a cikin irin wannan daular, ni kuma ina burin kasancewa da mijinki da kike ganin shi a banza, wanda duk wannan daular da nake ciki ta kasa gamsar da ni da sanya ni a cikin farinciki, saboda rashin samun abokin rayuwa kamar shi.'
Sai da Naja ta koma gida ta huta sannan ta kira Anas, duk da halin tashin hankalin da yake ciki da zazzaɓin da ya rufe shi lokaci ɗaya amma da sauri ya ɗaga yana fatan Allah ya sa zancen Hafsah za ta yi masa, saboda duk da abin da ta yi masa ko kaɗan son ta bai ragu a cikin zuciyarsa ba. Bayan Naja ta yi sallama ya amsa ta ce. "Abban Sultan idan babu damuwa ina son don Allah mu yi wata magana ne da kai, idan kana free yanzu, in kuma kana abu idan ka gama sai ka kira ni." Ya ce. "A'a babu abin da nake yi, ina sauraren ki." Ta ce. "To Masha Allah, ɗazu na zo gidanka na riski wani mummunan al'amari da bai mun daɗi ba ko kaɗan wallahi, ya kuma saka ni a cikin tashin hankali mara misaltuwa, kana nan ma na zo, amma saboda yanayin da kake ciki na san da ƙyar idan ka gan ni. Hafsah ta faɗa mini komai da yake faruwa, na yi mata faɗa sosai tare da ba ta shawarwari, kuma na ga alamar ta ɗauka daga yanayin yadda jikinta ya yi sanyi. Shi ya sa na kira na roƙi alfarmarka, akan don Allah ka yi haƙuri ba don halinta ba, ka mayar da ita ɗakinta, saboda tana gidan ma a can na baro ta, na hana ta tafiya." Numfashi ya sauke ya ce. "Anya kuwa Hafsah za ta risina? Don abubuwanta sun daina ba ni mamaki yanzu sai dai tsoro. Don da farko ma na yi tunanin ba ta cikin hayyacinta ne, sai daga baya na gane tsantsar iskanci ne da burin shirme da ruɗin shaiɗan." Naja ta ce. "In sha Allahu ba za ta sake ba, ka yi haƙuri, ta faɗa mini komai babu abin da ta ɓoye mun, amma ni na yi mata uzuri, saboda rashin mai ba ta shawara da ƙarancin wayewa sun taka muhimmiyar rawa a wajen habbaƙa al'amarin nan, amma komai ya zo ƙarshe in sha Allahu, zan kawo Mama da kaina har gidan ta ƙara yi mata faɗa, ba na son Kawu ya ji zancen nan, don kansa duk son da yake yi mata sai ya kusa balla ta." Ya ce. "Tom shikenan Naja, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, amma da na so na bar ta, ta je gida ta huta, idan ta gaji da zaman gidan ne." Naja ta ce. "A'a fa, da yardar mai duka komai ya zo ƙarshe, kuma kai ma da ka sani ka ƙwace wayar tata ka karya sim ɗin da ka fuskanci inda matsalar take. Da may be abun bai yi tsamari haka ba." Ya ce. "To ai ba ta bari mun yi magana ma ta fahimta ba bare na gane inda matsalar take, sai dai kawai ɗan abun da na fahimta daga maganganunta na baya da gugar zanan da ta dinga mun, da zuwan wata ƙawarta gidan." Cikin takaici Naja ta ce. "Allah ya kyauta ya ƙara ganar da ita, Da iliminta amma na rasa inda ta ajiye shi ta ɗauki kishiyarsa." Ya ce. "Ni ma mamakin da nake yi kenan, don ban taɓa zaton za ta iya ambaton sunan mahaifana ƙarara ta haɗa kuma da cin mutunci ba."
"Ka yi haƙuri, na san ta yi hauka da wauta, kuma ta ɓata maka rai matuƙa, amma ka taimaka ka mayar da ita, ba na son na ga kun rabu wallahi, ba na son ta yi asarar miji irinka."
Runtse idonsa ya yi don har lokacin muryar Hafsah ba ta daina yi masa kuwwa a kunne ba, a sanyaye ya ce. "Shikenan na mayar da ita, Allah ya sa ta yi nadamar abubuwan da ta aikata har cikin zuciyarta." Ajiyar zuciya Naja ta sauke ta ce. "Amin ya rabb, na gode sosai da ka fahimci ni da kuma wannan alfarmar da ka mun, Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya kaɗe fitina a tsakaninku da sharrin shaiɗan, ya sa makamancin hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, ke ma Allah ya ba ki miji na gari." Murmushi ta yi ta yi masa sallama ta katse wayar. Shiru ya yi yana tunanin rayuwarsu ta da shi da Hafsah, ya so rabuwa da ita na har abada ko don ya nuna mata daraja da ƙimar da iyayensa suke da shi a wajensa, amma darajar su Sultan da kyautatawar da ta yi masa a da su saka sanya ya amince ya mayar da ita. Amma ba zai koma gidan ba a yau, su Sultan ma ba zai mayar da su ba, don da ma da ya ɗauko su ɗazu daga tahfiz gidan wani abokinsa ya kai su, ya ce musu Hafsan ta je unguwa ne. Ya san Naja za ta kira ta, ta faɗa mata duk yadda suka yi, zai gani idan za ta neme shi, inda da gaske ta yi nadamar abubuwan da ta yi masan.
Bayan Magriba na ce wa Maman Nasmah zan koma gida, don na san zuwa yanzu Naja sun yi magana da Anas kamar yadda ta alƙawarta, kuma na san ba zai ƙi mayar da ni ba, duk da ba ni da tabbas, don ban taɓa yi masa irin ko da makamancin irin wannan laifin ba na taɓa mahaifansa. Ga shi wayata ta ɗauke ta ƙi kunnuwa gabaɗaya, bare na kira ta ko ita ta kira ni. Hana ni tafiya Maman Nasmah ta yi, ta dinga yi mini faɗa kamar za ta ari baki, wai shi bai neme ni ba, bai mayar da ni ba amma zan komar da kaina saboda zubar da aji da rashin sanin ciwon kai, ta takura sai na kwana a gidanta, gobe inda an gama komai sai na tafi. Don dole ba don son raina ba na amince. A daren muka je saloon aka yi mana wankin kai da na ƙafa, aka kuma kawo mini kayana da sabuwar waya kamar yadda ta faɗa, har da kuɗin liƙi sabbin ƴan ɗari biyar-biyar. Farinciki, murna da ɗoki suka saka na manta da Anas da babinsa, na ci gaba da shirin taronmu da za mu cashe mu raƙashe a gobe.
Kallon Hafsah kawai Maman Nasmah take tana yi mata murmushin mugunta a zuciyarta, saboda ita kaɗai ta san me ta shirya mata a wannan kwanan da za ta yi a gidanta.......✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*14.*
Har sha biyu na dare ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 24