na yi ina tunanin abin da zan yi kafin ranar taron na samu kuɗin siyen abubuwa irin na Maman Nasmah ko da ba duka ba. A haka na koma ɗaki na dinga zarya, a ƙarshe na samu mafita biyu kafin na kwanta. Ta farko zan takura wa Anas akan ina buƙatar kuɗaɗe, ya je ya nemo mini a duk inda suke, ai su ma mazajen su Maman Nasman mutane ne kamar shi, kuma nema suke yi ba da kuɗin aka halicce su ba, don haka shi ma dole ya samo ya ba ni. Ta biyu kuma idan ya ƙi zan ce Shamsiyya ta ara mini duk abin da zan saka ranar, sai na cewa Maman Nasmah kawai gani na yi Abban Sultan ya siyo mini su. Da wannan tunanin na samu na iya bacci, duk da na raba dare kafin ya ɗauke ni.
Washegari na tashi cikin farinciki da ɗokin kawo mini atamfar da za a yi, hakan ya sa na yi ayyukana na gida cikin walwala tare da Anas. Bayan su Sultan sun wuce tahfiz saboda weekend ne Abbansu ya yi wanka ya shirya cikin kayan da yake zuwa aikin fenti da su, sana'arsa da ma fentin ne, ranar da babu aiki kuma zaman shago yake yi wa ubangidansu. Yana ƙoƙarin fita ganin kiran da ake ta yi masa a waya na dube shi na ce. "Wai wa yake kiran ka ne?" Yana duba ƴar wayar tasa ya ce. "Su Halliru ne mana, kin san su idan za mu je aiki idan ban fito ba sun ta kira na kenan, dole su sai dai mu fita tare." Ba yabo ba fallasa na ce. "Tom shikenan sai ka dawo." Ya ce. "Za mu iya kaiwa bayan Magriba, saboda gidan da za mu yi aiki babba ne sosai, kuma duk da haka ba za mu gama a yau ba." Gyara zama na yi na ce. "Ku yi ta zuwa tafka-tafkan gidaje aiki, ba ya burge ku ne ku ji da ma ku ne kuke rayuwa a cikinsa?" Murmushi ya yi ya ce. "Ai babu wanda daula ba ta burgewa a duniyar nan, sai dai idan Ubangiji bai ba ka ba sai ka yi haƙuri ka gode masa, tare da fatan ya ba ka a lahira." Taɓe baki na yi yadda ba zai gane ba na ce. "Amma duk da haka ai za ku yi ta kallon gidan ku ce da ma ku ne a ciki ko?" Ya ce. "A'a, a saboda me? Kowa inda Ubangiji ya ajiye shi nan ya so ya gan shi fa, don wani inda kake shi kuma nan yake fatan da ma shi ne a gurin, ai mu sai dai kawai mu ce Alhamdullillah, tunda Ubangiji ya bar mu da lafiyarmu da za mu nemi kuɗinmu na halal ai ya ga yi mana komai." Kamar na rufe shi da duka tsabar takaici da baƙinciki, wato shi ko damun shi manyan gidajen ba sa yi bare ya yi burin gina su watarana, shi komai da an yi magana ya ce kaza-kaza shi sarkin tawakkali, to ai Allan da kansa ya ce tashi in taimake ka. Ban ƙara magana ba har ya fita, yana ta cewa yau babu rakiya ne na yi masa banza.
Ƙarfe goma da mintuna na ɗora girki saboda kar su Safwan su dawo 12 ban gama abinci ba. Bayan na gama na gyara kitchen ɗin ina shirin yin wanka na ji ana knocking, ganin sha biyu da mintuna na san su Sultan ne suka dawo, da sauri na nufi ƙofar na buɗe ina faɗin. "Wannan bugun ƙof...."
Maƙalewa maganar ta yi a inda ban sani ba saboda ganin wadda ko a mafarki na gan ta sai na gane ta, duk da ba mu taɓa haɗuwa a zahiri ba. Wani irin abu na ji yana yawo a cikin jinina dunƙule-dunƙule saboda tsanani mamaki, ruɗewa gami da razani. Lokaci ɗaya na ji kaina ya fara juyawa saboda matsananciyar ɗimautar da na shiga.
"Maman Nasmah!" Na furta a fili tare da dafe ƙirjina, idanuwa gabaɗaya sun yo waje kamar za su faɗo ƙasa, tsabar firgici.........✍️
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:37 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
7.
Murmushi ta sakar mini tare da faɗin. "Na'am." Ji na yi kamar babu sauran jini a jikina saboda jirin da yake kwasa ta, dafe bango na yi tare da cize leɓena cikin rashin mafita.
'Komai zai faru kar ki nuna mata ke ce wadda kuke chat, ki dage a matsayin ke mai aikinta ce kawai, tunda ba ta taɓa ganin ki ba ko a hoto.' Zuciyata ta ba ni wannan shawarar wadda na yi na'am da ita.
'To amma sunanta da kika ambata fa?' Wata zuciyar ta tambaye ni.
Numfashi na sauke tare da ƙaƙaro murmushin yaƙe don kar ta gane da wani abu na ce. "Sannu da zuwa, mu shiga ciki ko?" Har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi ta ce. "Toh." Sai a lokacin na lura da su Sultan da ke tsaye suna kallon mu, gabana ne ya faɗi don wanzuwar su a gidan tare da Maman Nasmah zai iya tona mini asiri, ban san lokacin da suka shigo ba, da tana ɗaki ma suka shigo maƙota zan tura su, har sai ta tafi sai na je na ɗauko su. Tsabar yadda ƙafata ta sage da ƙyar na iya ɗaga ta na bi bayansu, don har sun yi gaba ita da su Sultan. Mayar da ƙofar gidan na yi na rufe bayan na gama leƙen rantsatstsiyar motar da nake da tabbacin a cikinta ta zo, don ita ce ma wadda ta turo a group mijinta ya siya mata. Jikina a saɓule kamar zan fasa ihu na koma cikin gidan, na tarar da su tsaye a tsakar gida Sufyan yana nuna mata parlour yana cewa. "Nan ne inda Mami take kai baƙi, ki shiga." Kamar na janyo shi na rufe shi da duka haka na ji, na rasa mafita da abin yi, ga shi Maman Nasmah har yanzu ba ta ce komai da zai nuna ta gane ni ko ba ta gane ni ba. Ba don na so ba sai don ban da zaɓi na yi mata jagora zuwa cikin parlour'n. Gabaɗaya ƙamshinta mai daɗin shaƙa ya buɗaɗe gidan tun daga soro. Fuskarta a sake sosai muka gaisa, ko kaɗan ban ga alamar ƙyama ko raini a tattare da ita ba, hakan ya sa na ji zuciyata ta ɗan fara sanyi. Ga shi ta ja yarana sosai a jikinta, don Sufyan tunda ta zauna yake kan cinyarta. Ƙare mata kallo kawai nake ta ƙasan ido, fara ce tas kuma tana da ɗan jiki, maroon abaya ce a jikinta mai matuƙar kyau, ta yi rolling da mayafinta, yatsun hannunta guda ukun tsakiya kowanne sanye da zoben gold hagu da dama. Fatarta sai sheƙi take na zallar hutu da jin daɗi. Cikin lokaci ƙanƙani na tabbatar wa da kaina Maman Nasmah matar hamshaƙin mai kuɗin ce kamar yadda na daɗe ina hasashe. Ba don na gaji da kallon ta ba don ba ƙaramin kyau ta yi mini ba na miƙe na ce bari na kawo mata ruwa. Sosai ta burge ni, na ji da ma ni ce nake a matsayin da take. Kallon kaina na yi bayan na fito tsakar gida, zanin jikina duk ya yi baƙin gawayi, ga shi sai ƙaurin ledar da na hura wuta nake yi, gabaɗaya dai na yi kaca-kaca.
"Wannan wacce irin baƙar rana ce a gare ni da ta zaɓi mu haɗu da Maman Nasmah a cikinta? Ya Allah idan mafarki nake ka sa na farka, me ya sa sai da nake a wannan hargitsen za mu haɗu?" Na faɗa a fili tare da ɗora hannuna akai, hawayen baƙinciki da takaici na zuba daga idona. Ban taɓa jin kunya matsananciya irin wannan ba a rayuwata. Kitchen na yi saurin nufa jin kamar za ta fito, abinci nake son zuba mata amma ina kunyar ba ta abin da na dafa, don taliyar Hausa ce da manja da yaji, sai salad da na yanka.
"Bari na ɗauko kaya a mota." Na ji muryarta ta faɗi haka, saurin share hawayena na yi na ce. "To."
Kafin ta dawo na shiga ɗakina na sauya kaya a gaggauce, wani lace na saka wanda Abban Sultan ya ɗinka mini sallar da ta wuce, shi ne ƙarshen ƙurewar adaka a cikin kayana. Na bulbula turare na ɗan yi ɗaurin ɗankwali mai kyau. Amma duk da haka da na fito sai na gan ni kamar almajira a kanta. Fahimtar tana jin zafi saboda babu nepa ya sa na ɗage labulen window da na ƙofa. Ta ba ni atamfar da wasu tarin kayayyaki a leda ta ce na ba wa yara, a ɗarare nake da ita, ko haɗa ido na kasa yarda mu yi. Ban taɓa sanin haka ƙarya take da kunya ba idan aka kama mutum sai a yau, duk da ita ba ta nuna mini komai ba, sai ma hira da take ta ja na, kuma ko da wasa ba ta kama sunana ba ko na su Sultan, kuma ba ta yi mini maganar group ɗinmu ba kwata-kwata balle na taron da za mu yi. Amma duk haka a ruɗe nake, Allah -Allah nake ta tafi ko na samu nutsuwa na yi tunanin mafita, tsabar rikicewa ko ruwa ban ba ta ba. Abinci da ma ba zan iya ba ta wanda na yi ba, saboda kar abin kunyar ya yi mini yawa.
Tana kokarin tafiya na ji an buɗo ƙofar gidan an shigo, wata mummunar faɗuwar gaba ce na ji ta ziyarce ni, saboda na san Anas ne kawai yake da wannan ikon, idan kuwa shi ya dawo na shiga uku na kaɗe har ganyena. Domin ba zan so Maman Nasmah ta gan shi a matsayin mijina ba, abin kunyar sai ya yi mini yawa ai.
"Ƴar aljannatah!" Na ji muryarsa da ba ta da maraba da saukar dalma a kan ƙirjina a wannan yanayin da nake ciki yana kira na." Ban amsa ba har ya yi ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi. Tun daga kansa har tafin ƙafarsa kalolin fenti ne kamar wanda ya yi birgima a cikinsu. Satar kallon Maman Nasmah na yi na ga ta ƙura masa ido. Na san a cikin ranta tana ta cewa wannan abin ne mijina? Na san ko almajirinta ya fi shi kyan gani, ga shi sana'arsa ta bayyana kanta a jikinsa, yanda ko mahaukaci ne ya shafa shi sai ya sani.
'Ni kam na ga ta kaina, yau ruwa ya ƙare wa ɗan kada.' Addu'a nake ta yi Ubangiji ya sa mafarki nake, don ganin Anas da ta yi ya fi zuwan gidan da yadda ta same ni saka ni a cikin tashin hankali. Na gama tsara ƙaryar da zan shirga mata bayan ta tafi, amma dawowar shi ta wargaza komai, domin ban ga uban abin da zan ce mata ta yarda ba kuma, tunda ta ga mijina da sana'ar yake. Duk yadda ya so control ɗin kaina kar na nuna komai amma na kasa, zuciyata cunkushe da baƙinciki na dube shi na ce. "Me ya dawo da kai?" Idanunsa a kaina yana mun wani irin kallo ya ce. "Tunaninki ne ya addabi zuciyata ya hana ta sukuni, fahimtar ba zan taɓa samun nutsuwa ba idan ban gan ki ba ya sa tilas na bar aikin na zo na gan ki na koma." Ya ƙarashe maganar tare da kashe mini ido. Wani irin ƙululun takaici ne ya ƙara cika ni, maganganunsa ko kaɗan ba su burge ni ba, kamar ya watsa mini garwashi haka na ji su. Harara kawai nake banka masa ƙasa-ƙasa lokacin da suke gaisawa da Maman Nasmah. Tsabar bayar da kai a tsakar gida ya zauna maimakon ya shiga ɗakin su Sultan ya ɓuya. Ƙwafa na yi a ciki-ciki na miƙe ina ƙaƙalo murmushi ganin Maman Nasmah ta miƙe ita ma, ƙoƙarin danne kukan da yake son kwace mini na yi na ce. "Har za ki tafi? Ki bari na gama abinci ki ci mana." Sai a lokacin na tuna ko ruwa ban kawo mata ba. Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai wallahi, na gode ma a hakan." Ina gaba tana bi na a baya, har da rusunawarta da za ta yi wa Abban Sultan sallama. Ni kwa ko kallon shi ban yi ba, duk da ina jin shi yana mun magana. Har ƙofar gida na raka ta, na ga ashe tare da driver suke. Shi ya fito da sauri ya buɗe mata bayan motar ta shiga. A raina na ce. 'Kuɗi kenan, mai saka ai ta bauta maka ko da ba ka da sarauta.' Sai da suka bar layin na koma cikin gida bayan na saki ajiyar zuciya, ina cika ina batsewa na nufi kan Anas kamar zan fashe. Kafin na yi magana ya riga ni da faɗin. "Wace ce wannan?"
"Ban sani ba." Na faɗa a zafafe kamar zan kai masa duka.
Cikin mamaki ya ɗago yana kallo na baki buɗe. Kukan da yake ci na tun ɗazu na saki na ce. "Mene na dawowa yanzu bayan da ka ce sai Magriba? Kawai ka zo ka zubar mini da mutunci da ƙima a gabanta, jibi kayan jikinka da yadda kake, kowa sai ya san mijina fenti yake!" Miƙewa ya yi fuskarsa a haɗe ya ce. "Kunya kika ji don ta gan ni a haka Hafsah? Shi ne har da kuka?" Harara na zabga masa na ce. "Idan kunya ce kaɗai ma ai da sauƙi." Numfashi ya sauke ya ce. "A tunanina abin alfaharinki ne a gan ni a wajen neman halal ɗina ba haram ba, yanzu a misali a ce faɗowa gidan na yi da gudu ana bi na ana na yi mini ihun ɓarawo fa? Za ki so ta ga haka?"
"Eh wallahi! In dai a cikin kyakkyawar shiga kake da ba za ta bayyana talaucinka sosai ba, idan ya so na ce mata sharri aka yi maka." Na faɗi haka ina ƙara rushewa da kuka tare da shigewa ɗaki, duk da ba na kallon shi amma na san bi na ya yi da na mujiya.
Tsayawa Anas ya yi sakato kamar wani shashasha yana kallon ƙofar ɗakin kamar tana gurin, mamaki da al'ajabin Hafsah sun hana shi magana, ya rasa ma abin da zai ce mata. Ba ya jin tana cikin hayyacinta gaskiya, don waɗannan abubuwan ba halinta ba ne. Girgiza kai ya yi tare da kama haɓa ya ce. "Anya ba zan kira a yi mata roƙiyya ba kuwa? A gani ko aljanu ne suka shafar mini ita, don wannan lamuran nata sun wuce hankali." Bin bayanta ya yi don ƙara tabbatarwa da kansa koma mene ne yake damun matar tasa.
Maman Nasmah tana shiga mota ta fashe da dariyar da take ta cin ta cikin rashin damuwa da kallon da drivernta yake mata, ba ƙaramin dauriya ta yi ba da ba ta ƙyaƙyace a gaban Hafsah ba. Ta daɗe da gano ita talaka ce, saboda in dai za a yi maganar wani abu na gayu ko masu kuɗi ba ta saka baki, kuma ta gwada ta da abubuwa da yawa da suka ƙara tabbatar mata da zargin ta. Amma duk da haka ba ta yi tunanin talaucin nata ya kai haka ba, don a lokacin da suka yi parking a ƙofar gidan ta kalli gidan da unguwar ta yarda gidan masu aiki ne, saboda ita a tarihin rayuwarta ma ba ta taɓa shigowa irin unguwannin nan ba, idan ta yi sa'a direbanta ya san unguwar sosai. Ta inda ta gane gidan Hafsah ne tun kafin ta shiga, su Sultan ta gani sun dawo daga makaranta, ta tambaye su sunansu suka faɗa mata, ta ce mamansu tana cikin gidan suka ce eh, kuma farkon sanin ta da Hafsah hoton Sufyan ne akan dp ɗinta, hakan ya sa tana ganin su ta gane su.
Tana sane ta ƙi nuna wa Hafsah ta gane ta ko ba ta gane ta ba, ta bar ta a cikin duhu don ta ji idan sun yi chatting anjima me za ta ce mata. Dariya ta ƙara kwashewa da ita saboda tuno yadda Hafsah ta yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwan zafi, tana lura da yadda take ta share zufa a goshinta, da dibibicewar da ta yi. Kasancewar Hafsah talaka ba zai saka ta rabu da ita ba, don haka kawai Allah ya haɗa jininsu, ta ji tana son ta. Amma a yau da ta gan ta a gidanta sai ta gane dalilin da ya sa ƙaddara ta haɗa su tun farko. Numfashi ta sauke tare da lumshe idonta tana tuno Anas da murmushin da ya yi wa Hafsah lokacin da ya shigo, irin namijin da ta rayu da burin samu mai cikar zati da kamala. Tun daga sallamar da ya yi kafin ta gan shi gabanta ya faɗi, da ta gan shi kuma sai komai ya kwance mata, ta kasa ɗauke idonta daga kansa. Babban abin da ya ƙara fizgar ta a kansa soyayyar da ta ga ya nuna wa Hafsah. Kashe idon da ya yi wa Hafsah da kallon da yake bin ta shi kuwa sai da ya saka tsigar jikinta ta tashi. To a hakan ma jikinsa duk da fenti ina ga ya kintsa ya yi fes? Ta san sai ta kusa zaucewa. Lafewa ta yi a jikin kujera tana hasaso ita yake yi wa wannan kallon, tabbas ta san sai ta kusa sumewa. A rayuwarta tana bala'in son namjin da ya iya soyayya da kulawa, amma ita nata mijin da shi da katako ba su da maraba, don tana iya yin watanni ma ba ta saka shi a idonta ko ta ji muryarsa ba. Amma in dai dukiya ce yana da ita har da ta hauka, a iya kuɗin da ya mallaka mata in za ta yi kyautar 10 million ko motsi ba za su yi ba, balle kuma shi uban gayyar. Ban da kadarori da ya mallaka mata. Ta gane Hafsah ba ta so ta ga mijinta ba, ita kuma ganin shi kawai da ta yi ba ƙaramin tsintar dami a kala ba ne a gurinta. Wata irin zazzafar soyayyar shi ce ta ji tana mamaye zuciyarta. Ta yi haƙurin zama da mijinta na shekara takwas, amma a wannan karon dole za ta rabu da shi, domin ba irin mu'amalar da take da sauran maza ta ji tana son yi da Anas ba, son shi take, so take su yi rayuwa a matsayin miji da mata, ko ta samu farinciki da cikar burinta a rayuwa ita ma. Kuma sannan ta bar mummunar hanyar da take kai, ta bin wasu mazan da aurenta bisa sahalewar mijinta, kasancewar shi ɗan luwaɗi da bokansa ya haramta masa mu'amla da mace sai dai namiji ɗan'uwansa. Kuɗaɗen da ta mallaka sun ishe su yin duk irin rayuwar da take so ita da Anas.
Dogon numfashi ta ja ta sauke a karo na barkatai, matsaloli biyu ne za su yi mata katanga daga samun cikar burinta nan kusa, na farko ta a yadda za a yi ta samu kan Anas ya amince da ita, na biyu kuma yadda za ta raba su da Hafsah, don a matsanancin son shi da ya yi mata kamun farat ɗaya ba za ta iya sharing ɗinsa da wata ba, nata ita kaɗai take son ya zama har ƙarshen rayuwarta. Kuma ko mene za ta yi don ganin ta mallaki Anas, saboda ita kaɗai ta san me take ji a game da shi, daga lokacin da ƙwayar idonta ta sauka a kansa zuwa yanzu......✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:37 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
8.
Ina durƙushe na kifa kaina a jikin gado ina runtumar kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwar uwarta na ji ya shigo, ƙara volume na yi ba tare da ɗago ba balle ya saka ran zan saurare shi. Ina jin shi yana zauna a gefen gado kusa da kaina. Matsawa na yi tare da ƙoƙarin tashi na bar ɗakin na ji ya ruƙo ni, ƙoƙarin ƙwacewa na yi amma ya nuna mini shi namiji ne, ya riƙe ni gam ya mayar da ni na zauna a fusace. Cikin taushin murya ya ce. "Ki yi shiru don Allah Hafsah mu yi magana, mene ne haka? Wannan kukan na mene?" Tsaki na ja na ce. "Don Allah, don darajar iyayenka ka ƙyale ni Anas, ba na son magana a yanzu." Ya ce. "Na ji zan ƙyale ki, amma don Allah ki bar wannan kukan da kike yi mara amfani, ko dan su Sultan da suke jin ki." Na ce. "To." Kawai, tare da share hawayena, duk da na san dole wasu sai sun zuɓo. Ni kaɗai na san halin baƙinciki da takaicin da nake ciki, kamar nai ta zunduma ihu haka nake ji. Babban tashin hankalina ban san me zai biyo baya ba a gurin Maman Nasmah da yadda ta zo ta gan ni, ina tsoron ta faɗa wa wasu ƴan group ɗinmu.
Wunin yau gabaɗaya haka na yi shi sukuku, zuciyata a cunkushe da jin haushin Anas. Tun bayan da na dawo daga rakiyar Maman Nasmah na kashe wayata, har dare ban kunnata ba, duk da yadda zuciyata take ta azalzalata na kunna na ji me Maman Nasmah za ta ce mini, na ji matsayin da ta ajiye ni, na Salamatu mai aiki ko kuma Hafsah Maman Sultan. Tsabar abin duniya ya bi ya dame ni ko ruwa ban kai bakina ba. Hakan ya sa nake ji na wani iri kamar mai cuta, ƙirjina har zafi yake mini.
Maman Nasmah kuwa bayan ta koma gidanta ta ci gaba da saƙawa da warwarar hanyar da za ta bi ta mallaki Anas, a ƙarshe ta yanke wasu shawarwari, abu na farko da za ta fara yi shi ne ta raba shi da Hafsah, na biyu kuma za ta saka a yi mata binkice akan shi, sai ta fara da bin iyayensa da ƴan'uwansa ta yi musu alkhairi, bayan ta tabbatar ta karɓu a gurinsu sai ta bayyana masa manufarta, yadda ko da ya ƙi amincewa wani nasa zai yi masa dole ya amince, fatanta kawai ya kasance mahaifansa suna raye, don idan da su komai sai ya fi tafiyar mata daidai. Tun yamma take kiran wayar Hafsah a kashe, don ta fara aiwatar da aikinta a kanta, domin da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, ba za ta tsaya kuma garin kallon ruwa kwaɗo ya yi mata ƙafa ba.
Ina kwance a kan dardumar da na yi sallar Magriba Anas ya dawo. Ban ko kalle shi ba, har ya yi wanka ya je masallaci sallar isha'i ya dawo. Da kansa ya zuba abinci ya ci, na dinga kallon shi ina jin kamar na je na samu fuskarsa nai ta mari, ya na cin taliya da manja da yaji amma kamar mai cin wani haɗaɗɗen abincin da ya ji nama, sai wani lumshe ido yake yana zurƙuma lauma. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba. Bayan ya gama ya dube ni ya ce. "Wace ce ta zo ɗazu?" Kamar na share shi, amma yadda na ji ya yi magana babu alamun wasa ya sa a ƙufule na ce. "Sai yanzu za ka tambaya? Me ya sa tunda ka gan ta ba ka tambaye ta, ta ba ka amsa da kanta ba?"
"Saboda ke nake da hurumin tambaya, ke kika kawo ta gidana."
Tashi zaune na yi cikin tsiwa na ce. "Ina gidan yake? Har kake wani ƙafafa kana cewa gidanka?" Na ƙarashe maganar ina keɓe baki. Girgiza kai ya yi ya ce. "Ki ba ni amsa kawai, kar ki tunzura ni, na yi miki abin da ba ki taɓa zato ba."
'Ka yi mana' Na faɗa a cikin raina, amma a fili sai na ce. "Ƙawata ce." Ya ce. "Ya yi, amma ya aka yi ban san ta ba tunda muke da ke?" Na ce. "Allah ne bai yi ba." Daga haka na tashi na shige ɗaki.
Anas ya bi ta da kallo, har yanzu tantama yake akan anya Hafsah ita kaɗai ce kuwa? Saboda tun sanin da ya yi mata bai san ta da irin waɗannan halayen ba, ya san dai tana da fushi idan aka yi mata abu, amma bayan wannan bai san wani hali nata mara kyau ba. Kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 24