Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rayuwa cikin kwanciyar hankali, sun dinga addaba musu kenan da ƙwarzaba, Aunty Samira ce kaɗai take jin sauƙin su, duk da ita ma idan suka so ba sa raga mata." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Matansa kuma? A bayaninki fa kamar kina nufin a baya ba a yanzu da ya auro ni ba?" Ta ce. "Eh, ai ya auri mata biyu kafin ke duk sun fita, saboda ba za su iya da mulkin mallakar da ake yi musu kamar bayi ba, cikin matan har da ƙawata, a gurinta na samu labarin komai na halayyarsa." Ta ƙarashe maganar tana waige-waige. Tsabar ruɗu kasa magana na yi, na dinga tambayar kaina me ya sa ya ɓoye mini ya taɓa rabuwa da wasu matan? Ƙasa ta yi da murya ta ce. "Ba na faɗa miki don ki shiga cikin damuwa ba ne, na faɗa miki ne don ki san irin matakan tsaron da za ki ɗauka na ƙwatar ƴancin kanki." Cikin sarewa na ce. "Wanne mataki zan ɗauka? Me zan iya yi?" Ta ce. "Addu'a, ba dare ba rana." Girgiza kaina na yi tare da dafe shi, me ya sa abubuwa suke jagwalgwale mini haka ne? Duk da inda nake tunanin zan huta, na ji daɗi na yi farinciki, sai na tarar da tashin hankali fiye da na baya. Kamar zan yi kuka na ce. "Da ma akwai maza irin haka ne?" Ta ce. "Fiye da haka ma, mazan yanzu ɗaiɗai ne na Allah." Taune leɓena na yi na ce. "Yanzu sai a samu wanda ya fi Sani tijara?" Ta ce. "Dubu nawa ma, ai kowacce mace da kika gani haƙuri kawai take yi, amma ita kaɗai ta san me take ƙunsa a gidanta, kuma kowa da tasa matsalar daban-daban." Runtse idona na yi ina jin kamar kaina zai fashe, ban saba da damuwa ko matsala ba, shi ya sa yanzu da ta riske ni nake jin kamar zan haukace. A sanyaye na fara magana da faɗin. "Ni mijina na farko duk ba shi da irin waɗannan mugayen halayen, mutum ne mai tausayi da sanin darajar mace, ba faɗa, ba zagi, ba duka, sai tarin kulawa da soyayya, ga addini da sanin yakamata, kuma duk wani haƙƙi da yake kansa yana ƙoƙarin saukewa, ga girmama sirukansa, ban san ya zan fasalta miki shi ba, amma duk inda ake neman miji na gari ya kai."  Cikin jimantawa ta ce. "Allah Sarki, Allah ya yi masa rahama." Da sauri na buɗe idona na ce. "Ba rasuwa ya yi ba fa, yana nan a raye." Cikin waro ido ta ce. "To ai yadda kika fasalta shi babu macen da za ta same shi ta yi gangancin su rabu, shi ya sa na yi tunanin mutuwa ya yi. Ke kuma me ya raba ku?" Cikin ɗacin rai na ce. "Ƙaddara." Ta jinjina kai tare da faɗin. "Amma kuwa akwai baƙar ƙaddara, don samun irin tsohon mijin nan naki ba ƙaramar wahala zai yi ba." Ban ce komai ba don ba ni da abun cewar. Bayan ta tafi na ƙule a ɗaki ina tunanin maganganun mutum uku akan Anas, da Naja, da wata maƙociyar Inna da na ba ta labarinsa da kuma Binta. Dukkansu maganganunsu ɗaya ne a kansa, na fara tunanin anya ba gaskiya suke faɗa mini ba? Amma idan na tuna yadda su Maman Nasmah da sauran ƴan group ɗinmu suke yabon nasu mazajen sai na ga kamar akwai maza burjik irin Abban Sultan, har ma da wanda suka fi shi a kyautatawa da komai da komai. A haka Sani ya shigo ya same ni, ba kunya ba lallami bare wata soyayya ya yi abin da zai yi ya fita, ya bar ni da jinyar ciwon da ya famo mini kuma ba iya yi mini maganinsa zai yi ba. Sosai na azabtu, na fice daga hayyacina cikin sati biyu saboda wahalar aiki da rashin kwanciyar hankali, ga ciwo da nake yi a tsaitsaye, wanda na yi na yi Sani ya kai ni asibiti amma ya ƙi. Yau na tashi da farinciki saboda ziyarar da Aunty Kareema da Maman Hanif suka ce za su kawo mini. Duk da bana jin daɗin jikina haka na tashi da wurwuri na yi aiki, bayan sun zo sai da na tabbatar na yi wa Hajiya duk wani abu da za ta buƙata sannan na tafi gurinsu muka sha hira. Na ji daɗin zuwan nasu sosai, ya saka ni nishaɗi, har na ji damuwar da ke damu na ta ragu. Bayan Magriba ina idar da Sallah Sani ya banko ƙofa, fuska a haɗe kamar an aiko masa da saƙon mutuwa ya dube ni a wulaƙance ya ce. "Ke zo." Cikin faɗuwar gaba na miƙe na bi bayan shi, don daga gani babu tambaya kiran ba na alkhairi ba ne. A tsaye muka tarar da Hajiya tana kaiwa da komawa, kamar baiwar da ba ta galihu haka na samu gefe na rakuɓe tare da yin ƙasa da kaina. Cikin ɗaga murya ya nuna ni da yatsa tare da faɗin. "Waɗan ne ƴan iskan ne suka zo ɗazu gidan nan?" A tsorace na ce. "Ƙawayena ne." Yana jifa na da wani mugun kallo ya ce. "Shi ne kuma har suka fi mahaifiyata ko?" Cikin rashin fahimta na kalle shi na kalle ta. Kamar ba ta san magana saboda ƙasaita ta ce. "Kya kalle ni mana, kin tafi gurinsu kin bar ni tashe-tashe, ba wannan ne ma ya fi ƙona mini rai ba kamar kiran da dinga ƙwala miki kika yi banza da ni, kuma kina ji kika ci gaba da shewarki." Da sauri na ce. "Wallahi ban ji ba, kuma na ga na gama yi miki duk wani da za ki buƙata, shi ya sa ma na je na zauna, amma ki yi haƙuri don Allah." Kama ta yi ta ce. "Innalillahi! Ƙarya na yi miki kenan ƴar nan?" Saurin girgiza kai na yi. Ta ce. "To ga shi na faɗi magana kin ce ba haka aka yi ba, idan ba ƙarya kike nufin na yi ba me kike nufi? Tunda har zan faɗi magana ki ce ba haka aka yi ba." Na buɗe baki zan yi magana na ji ta maƙale, sakamakon wawan marin da Sani ya ɗauke ni da shi. A gigice na dafe kuncina, kafin na gama watstsakewa daga zafin marin ya ƙara mini wani a ɗayan kuncin tare da faɗin. "Mahaifiyata za ki ƙaryata saboda ba ki da mutunci ba ki da kirki? To wallahi ba ki isa ba, kin yi kaɗan, ban haifi matar da za ta wulaƙanta mini uwa ba." Na yi zaton zai ƙyale ni haka, amma sai na ji ya ci gaba da dukana ko ta'ina, kuma da dukkan ƙarfinsa kamar ya samu garjejen ƙato ɗan'uwansa. Ya zage ya jibge ni son ransa, har da naushi da hauri da ƙofa. Tun ina iya kare kaina har na kasa, na yi yunƙurin guduwa amma ban da ko ƙwarin tashi. Ina kwance male-male bayan ya gama yi mini laga-laga na ji wani abu mai ɗumi yana bin tsakanin cinyoyina, daga nan ban ƙara sanin me yake faruwa ba...✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [5/11, 12:13 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRING PENS* (FREE BATCH) *31.* A hankali nake ƙoƙarin buɗe Idanuna, amma saboda nauyi da ciwon da kaina yake yi mini da ƙyar suka buɗe. Dishi-dishi na fara gani, kafin su washe yadda zan iya gani da gane komai. Saman ɗakin da nake na ƙura wa ido na wasu sakanni, daga fara na sauke shi ƙasa na fara bin ko'ina da kallo. Cikin sakanni na gane a bedroom ɗina na gidan Sani nake a kwance a kan gado. Yunƙurin tashi zaune na yi amma na kasa, saboda sarawar da kaina ya yi mini, hannuna da na ji kamar ya riƙe na kalla, drip na gani sanye a jikinsa. Cikin raunin zuciya na mayar da idon na rufe ina tunano abin da ya faru. Jin an turo ƙofa ya saka ni buɗe ido da sauri, wata matashiyar mata na gani hannunta ɗauke da wasu tarkace da ban gane mene ne ba. "Ma sha Allah, kin farka kenan?" Ta faɗa tana ƙarasowa bakin gadon tare da dafa kaina, wanda hakan ya sa na ji kamar dutse ta ɗora mini. Cikin kulawa ta ce. "Ya jikin naki?" Ban iya ba ta amsa ba sai da wasu sakanni suka shuɗe, saboda yadda shi ma bakin ya yi mini nauyi, da ƙyar cikin numfarfashi da rawar leɓe na iya cewa. "Da sauƙi." Ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, yanzu ina ne kike jin ya fi miki ciwo sosai?" "Ko'ina da ko'ina." Na faɗa wasu hawaye masu ɗumi suna gangarowa daga idona. Cikin tausayawa ta ce. "Ki yi haƙuri, za ki samu sauƙi in sha Allah, ni doctor ce, matar abokin Sani, tun a jiya da daddare ya kira ni na zo na ba ki taimakon da zan iya, don ba zai iya kai ki asibiti ba a yanayin da kike ciki, saboda ba za karɓe ki ba sai da police. Ni ma ba don mawuyacin halin da na tarar da ke a ciki da tausayin ki ba da ba zan taɓa ki ba gaskiya." Ban iya cewa komai ba sai bin ta da ido kawai na yi. Tana duba ruwan da ta saka mini Sani ya shigo, da sauri na runtse ido, wata irin tsanar shi nake ji ta cika mini zuciya, ko ganin shi bana son yi. Ba tare da ta amsa sallamar da ya yi ba ta ce. "Sai yanzu?" Ya ce. "Eh." Ta ce. "Hmm, yanzu kana da wannan patient ɗin da kai ka yi sanadin shigar ta mawuyacin hali amma ka iya tsallakewa ka tafi ka bar ta, ta kwana ita kaɗai? Kuma maimakon ka yi asubanci ka zo sai ka bari har rana ta fito? Ina ganin na yi late ɗin zuwa ashe ma na riga ka." Muryarsa babu alamun rusina ya ce. "To idan na zauna me zan yi mata? Na ga ta samu lafiya har tana bacci shi ya sa na tafi." Numfashi ta sauke ta ce. "Ga magunguna nan na rubuta ka je ka siyo, don ana buƙatar su da gaggawa, sannan za a yi mata ƙarin jini don ta zubar da jini sosai a ɓarin da ta yi, ga jininta ya hau sosai, kuma za a yi mata wankin ciki, duk kauce-kaucenka dole dai sai mun je asibiti." Ya ce. "Ni duk wannan lissafin gaskiya ba kowanne zan iya yi ba, don na san ba ƙaramin kuɗi za a ci ba." A ƙufule ta ce. "Sani ka ji tsoron Allah, ka yi mata wannan mahaukacin dukan sannan kuma ka ce ba za ka tsaya wajen ganin ta samu lafiya ba? Kar ka manta kai ma fa kana da ƴaƴa matan nan ka haifa, kuma abin da ka yi shi za a yi maka." Bai ce komai ba ya karɓi takardar ya fice. Cikin tashin hankalin jin na yi ɓari na buɗe idona na ce. "Da gaske na yi ɓari? Da gaske ina da cutar hawan jini? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Saurin zuwa ta zauna a kusa da ni ta yi, cikin lallami ta fara magana da faɗin. "Ki yi haƙuri, don cuta kam an gama cutar ki, an zalunce ki, wallahi ban taɓa sanin haka mijinku yake ba sai jiya da na zo, idan da labari aka ba ni ba zan taɓa yarda ba, ko shi mijina da yake abokinsa bai san haka yake ba, ba ƙaramin shock ya shiga ba shi ma da ya aika-aikar da ya yi, duk da ya ce wai mahaifiyarsa kika zaga, bai san sanda zuciya ta ɗeɓe shi ya aikata miki haka ba." Girgiza kaina na fara yi duk da nauyin da ya yi mini, cikin kuka na ce. "Don Allah likita ki taimake ni ki mun allular da zan mutu, na gaji! Na gaji da zaman gidan nan, tsabar tashin hankalin da nake ciki ban ma san ina da ciki ba, gara na mutu kawai na huta da wannan rayuwar." "Subhanallahi! Ki daina faɗar haka, kar ki yi saɓo, kowane tsanani yana tare da sauƙi, watarana sai labari." "Ban da tsananin gidan nan, kullum abun gaba yake ƙara yi, daga wulaƙanci da cin zarafi an koma duka, nan gaba kuma ban san me zai faru ba." Na ƙarashe maganar ina jin numfashina kamar zai bar gangar jikina, tsabar raɗaɗin da zuciyata da ciwon da gaɓɓan jikina suke yi mini. Don maganar ma dauriyar yin ta kawai nake, saboda shi kan shi bakin ciwo yake mini, kuma na ji ya yi mini wani irin burɗunɗun alamun a kumbure yake. Sosai likitar da ko sunanta ban sani ba ta ba ni baki gami da tarin kulawa kamar wata ƴar'uwata. Ita ta kai ni asibiti, ta tsaya tsayin daka wajen ganin an yi mini duk abin da ya dace. Na sha wahalar da tunda uwata ta kawo ni ban taɓa shan irinta ba, zan iya cewa tunda na mallaki hankalina ban taɓa jinyar da na sha azaba kamar wannan ba. Ban taɓa yin ɓari ba, shi ya sa ban san haka wankin ciki yake ba sai a wannan karon. Amma duk da haka ko kaɗan Sani bai nuna ya tausaya mini ba, sai ma mitar na saka shi asara da kashe kuɗi da ya dinga yi. Na yi kuka kamar idona zai faɗo. Kwanana uku amma ko kare bai zo duba ni ba, ni a ƴan'uwana babu wanda na faɗawa, saboda ko inda wayata take ban sani ba bare na kira su. Hajiya kuma da abin ya faru a gabanta ita ma ko leƙe, balle ƴaƴanta. Daga nurses sai Dr. Zainab ke kula da ni. Ranar da aka sallame ni ji na yi kamar na wuce gidan Kawu, amma da na tuno ba shi da lafiya, kuma idan na je a yadda nake ba ƙaramin ɗaga masa hankali zan yi ba sai na fasa. Gabaɗaya Sani da gidansa da aurensa sun fice mini a rai, don ko muryarsa na ji sai wani ƙunci mara misaltuwa ya lulluɓe ni. Ina kwance a kan gadona ina ƙullawa da saƙawa na ji an shigo ɗakin, idona a lumshe yake hakan ya sa ban san wane ba. Bayan mintuna biyu na ji muryar Hajiya cikin isa da taƙamar ta, ta ce. "Sannu hamshaƙiya, ki dawo gidan amma ban isa ki zo kin gaishe ni ba ko?" Tsananin mamaki da al'ajabin ta ne ya hana ni magana, bayan na ci uwar jinyar da ɗanta ne ya yi sanadi kamar ba zan rayu ba, ba ta je duba ni ba amma ta zo tana yi mini ƙorafin ban je na gaishe ta ba? Ƙarfin hali zan kira wannan abun nata ko kuma fin ƙarfi? Ji nake kamar na juya na wawwanke fuskarta da mari, ko zan ji sauƙin abin da nake ji a cikin raina. Na dinga tambayar kaina da ma akwai mutane marasa imani da tausayi irin haka? A ce ka ga mutum cikin tsananin ciwo har da suma amma ko sannu ta kasa haɗa ku? A yadda na zuciya a lokacin zan iya zazzagin ta, hakan ya sa ban tanka mata ba har ta gama tsaiwarta ta fice bayan ta ja ƙwafa. A hankali na miƙe don har yanzu ban daina jin jikina ba ƙwari ba, na je gaban madubi na tsaya ina kallon kaina. Goshina da leɓena da suka kumbura har yanzu ba su gama sacewa ba, gefen idona kuwa ya yi baƙi sosai bayan gurin ya yi ƙullutu, gabaɗaya na sauya na zama wata dodo-dodo, fuskar babu kyan gani ko kaɗan. Numfashi na sauke tare da jingina bayana a bango. Anas ne ya faɗo mini a rai, mutumin da bai taɓa kai hannunsa jikina da sunan duka ba, sai don soyayya da kulawa da rarrashi. Zuwa yanzu na fara gasgata maganganun Naja da abin da take guje mini a rabuwa da Anas, saboda kwata-kwata ba su da haɗi a mu'amala da halayya shi da Sani, duk abin da na kwatanta su sai na ga Anas ya yi masa zarra nesa ba kusa ba, kuɗi kawai Sani zai nuna masa, wanda zuwa yanzu na gane ba kowanne ne yake samar da kwanciyar hankali ba. Duk wani abu da nake nema da burin na samu na samu a gidan Sani, amma na rasa nutsuwa da sukunin zuci, har ta kai a yanzu ba sa burge ni, ba sa gabana. Babban burina a yanzu shi ne na rabu da Sani, ya sake ni ya raba ni da wannan wahalallen jarababben auren nasa. Na gaji, ba zan iya ci gaba da wannan rayuwar kamar dabba ba. Ina nan tsaye ina matsar ƙwalla ya shigo yana huci, na yi kamar ban san da zuwansa ba na ci gaba da kukana. A fusace ya nuna ni da hannu tare da faɗin. "Daga dawowar ki har za ki fara ɓata mata rai saboda ba ki da mutunci da hankali? Mahaifiyata za ki ce za ki raina saboda ba ki da tarbiyya ba a ba ki ba a gida?" Zagaye shi na yi na wuce na je bakin gado na zauna, saboda kukan da na yi har kaina ya fara juyawa, na fara jin jikina wani iri. Hakan ya ƙara ƙular da shi ya buga mini tsawa da faɗin. "Ok, ni ma rashin ɗa'ar za ki gwada mini kenan?" Wani kallo na yi masa don ba ta shi nake ba bare na bi ta kansa, ta lafiyata kawai nake yi. Ban san lokacin da ya ƙaraso bakin gadon ba sai kawai ji na yi ya ɗauke ni da mari fau!.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [5/11, 12:13 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *32* A firgice na kalle shi cikin son tabbatar da mafarki nake yi ko gaske? Ina cikin jinya da ɗanyen jikin ɓari yake ƙoƙarin kwata dukan da ya yi mini? Yadda yake huci da zazzaro ido ya sa na miƙe hannuna dafe da ƙuncina na bar kan gadon na koma ƙarshen ɗaki ina sheshsheƙa cikin ɗacin zuciya. Muryata a raunane na ɗaga kaina da ke sara mini na kalle shi, cikin kuka da raunin zuciya na ce. "Me kake son mayar da ni ne? Jaka ko baiwa?" Cikin izgili ya ce. "Ai duk ita ce, duk sunan da aka kira ki da shi daga cikin waɗanda kika ambata sun dace da ke." Taune lip ɗina na yi cikin jin zafi da raɗaɗin maganganunsa. Magana nake son yi amma na kasa saboda wani irin abu mai tuƙiƙi da ya turniƙe mini maƙoshi, hakan ya haddasa mini tarin bazata mai ƙarfin gaske. Bai damu ba ya ci gaba da faɗin. "Wallahi tallahi wannan ya zama na ƙarshe a saɓawa mahaifiyata da ɓata mata rai da kike yi, matuƙar ta ƙara kawo mini ƙarar ki sai na ɓaɓɓalla ki." Ina sauke numfarfashi cikin dashewar murya na ce. "Ka ji tsoron Allah, ka tuna ni amana ce da Allah ya ba ka, idan ka ci gaba da zalunta ta wallahi haƙƙina ba zai taɓa barin ka jin daɗin rayuwa ba." Ɗora ƙafarsa ya yi a kan gado ya ɗora hannunsa a kai, cikin tsantsar tijara ya ce. "Ki fara yi wa kanki wa'azi kafin ki yi wa wani, banza jahilar kawai, kuma daga rana mai kamar ta yau, kar na ƙara ganin wata mata a gidan nan da sunan ta zo gurinki, ko da kuwa ƴar'uwarki ce balle kuma wata ƙawa, idan kunne ya ji jiki ya tsira." Daga haka ya juya ya fice. Kuka na rushe da shi ko zan ji sauƙin abun da yake raina, amma tamkar ana rura garwashi haka ya ci gaba da naso a cikin raina. Ban san adadin lokacin da na kwashe a haka ba, kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ni. Cikin baccin na ji ana sheƙa mini ruwa mai bala'in sanyi. A firgice na farka ina faɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Tare miƙewa cikin kyarmar jiki. Hajiya na gani tsaye a kaina da ƙaramin bucket a hannunta. "Uban wa zai dafa mana abinci da kika zo kika kwanta?" Ta faɗi haka cikin daka tsawa. Galala na yi ina kallon ta tare da wartsakewa ba tare da na shirya ba, ni take jira na dafa abinci kenan? Ban ce komai ba na tsugunna saboda jirin da yake ɗiba ta na yunwa. Cikin karyar da harshe na ce. "Ban da lafiya, ba zan iya girki ba." Wani kallo ta yi mini da na kasa tantance ma'anarsa ta juya ta fice. Ajiyar zuciya na sauke na lallaɓa na hau gado na kwanta idona cike da ƙwalla. Ban taɓa tunanin zan tsinci kaina a irin wannan rayuwar ba ko da a mafarki, ba na son ɗaga wa Kawu hankali, amma da tabbas yau sai na yi yaji na bar gidan nan, ba zan zauna baƙinciki ya sa zuciyata ta buga ba, daga Hajiya har Sanin ba su da asara, sai dai a yi wa ƴaƴana asara ta. Juyi na yi na dawo rigingine na ƙura wa saman ɗakin ido, na rasa ina zan saka kaina, ina zan tsoma zuciyata na ji sanyi, har nauyi-nauyi na ji ƙirjina yana yi mini. Ba na abin da nake so da buƙata a yanzu sama da na yi ido huɗu da ƴaƴana. Wata irin kewar su nake ji, musamman a yanzu da nake cikin wannan tashin hankalin, na rungume su a jikina ko zan samu sauƙin abin da nake ji. Lumshe idona na yi, hakan ya ba wa hawayen da ya cika idona damar fara zuba yana ɗiga a kan pillow'n da nake kai ta gefen idona. Rayuwarmu da Anas da kusan kullum sai na tuna ta nake ƙara tisawa, na dinga hasashe da laluben wani laifi ko ta inda ya gaza amma ban samu ba. Zuwa na tabbatar wa kaina na yi rashin adalin mijin da ba zan taɓa samun kamar shi ba, na gane wauta da ɗanyen kan da na yi na YI WA KAINA sagegeduwa, na cuci kaina na jefa rayuwata a cikin ƙunci da hannuna. Babu abin da ya fi tayar mini da hankali sama da idan na tuna yanzu aure na har uku, shi ma wannan ɗin addu'a nake Allah ya raba ni da shi, sai dai idan na rabu da shin ban san me gaba za ta haifar ba, ban san wa zan kuma haɗuwa da shi ba. Wahalallen numfashi ina jin kamar mafarki ne abubuwan da suke faruwa, ban san sunan da kiran rayuwata da shi ba, ƙaddara ko ganganci ko kuma wauta da hauka? Gabaɗaya kuɗi da wani rayuwar jin daɗi sun fice daga kaina, farinciki, walwala da kwanciyar hankalin da nake ciki a da su kawai nake da buƙata. A yadda nake jin azaba a cikin raina ba don yarana ba da na ta addu'a ba dare ba rana Allah ya ɗauki raina a yau, don wannan rayuwar da na tsinci kaina a cikinta ba ta da amfani, ƴan group ɗin namu da nake son burgewa da haɗa kai da su yanzu ga shi mun rabu, tun kafin na yi offline ya yi sanyi, aka daina magana kamar ba shi ba, shikenan har an yi an gama, ni kuma na jefa kaina a bala'i sanadinsa, ga shi na rabu da mutanen cikinsa. Jan majina na yi tare da tashi zaune na goge hawayen fuskata. Fuskata da idona har wani zafi suke mun saboda gajiya da kuka. Ina dafa bango na ja ƙafa da ƙyar na je toilet na watsa ruwa, bayan na fito ina cikin shiryawa na ji an banko ƙofa an shigo, da sauri na ɗaga kaina cikin faɗuwar gabar da a rana ba zan iya ƙirga adadin wadda nake yi ba. Kafin na gama tantance komai na ji saukar belt a gadon bayana. A ƙufule na fara ƙoƙarin kare kaina tare da riƙe ta, amma ya murɗe hannuna ya fizge ya ci gaba da zaula mini. Tsugunnawa na yi cikin ƙarfin hali na riƙe ƙafarsa da nufin na yar da shi, amma ko motsi bai yi ba sai ni na faɗi ƙasa ƙeya ta, ta bugu saboda rashin ƙwarin jiki. Tsayawa ya yi a kaina yana huci ya ce. "Ba ki ji abin da na faɗa miki ba ko? Ki tashi ki je ki ɗora girki ko na lallasa ki, wannan shafa na yi miki, ba ki ga komai ba ma, tunda kunnen ƙashi gare

Chapter 20 of 24