Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akwai abin da ya fi komai rashin tabbas l a duniyar nan to namiji ne. Kin faɗa mini inda kike ɓoye kayan can bayan wardrobe ɗinku ne, idan ba wanda ya san da gurin a ɗakin ba ta yaya za a ɗauki kayan? Aiko ɓarawo ne ma duk ƙwarewar shi a sata ba zai yi tunanin da abu a gurin ba, sannan kuma a yadda kika faɗa mini mijin naki ya ƙyale ki kina yin abin da kike so ya isa ya sa ki gane wata gadar zaren yake shirya miki, ya yi miki lumbu-lumbu ya kwashe kayan. Kin san tsadar kuɗin sarƙar nan kuwa? Ya na ganin shi bai mallaki kuɗinta ba ke kin mallaka ai ko don baƙinciki da hassada ya ɗauke. Na san halin mazaje irin naki talakawa da yawa, kullum matansu cikin kawo mana complain suke idan sun zo neman taimako, talaka akwai baƙar zuciya da mugun hali, ba sa so su ga matansu sun fi su cigaba, don haka tun wuri gara ki farka daga mummunan bacci da kike ki san abin yi." Shiru na yi ina nazarin maganganunta, wani ɓarin na zuciyata ya yarda da ita, wani kuma ya na jaddada mini ko duniya da abin da yake cikinta na mallaka Anas ba zai taɓa ɗaukar mini ko tsinke ba, idan ban ba shi ba. Cikin rashin sanin wanne ɓangare na zuciyar tawa zan bi na ce. "Bai taɓa ɗaukar mini abu ba fa, gaskiya ba shi ya ɗauka ba, sai dai in....." "To waye?" Maman Nasmah ta katse ni cikin kufula. Ban ba ta amsa ba ta ci gaba da faɗin. "Da kike cewa bai taɓa ɗaukar miki abu ba kin taɓa mallakar abun miliyoyi ne? Million ai ba dubu ba ce, da zan faɗa miki price ɗin sarƙar nan sai kin riƙe baki, mantawa na yi ma ban haɗo miki da receipt ɗinta ba. Ni gaskiya nake faɗa miki, saboda na ga so ya rufe miki ido, mutum ba ya son cigabanki ya ga kin samu abin duniya ya sace amma kina yabon shi, just common waya ya siya miki ya kasa saboda maƙo amma kike tunanin ba zai ɗauki abin miliyoyi ba, wa ya sani ma ko ya daɗe da yin cinikinta sai yau ya fake ki ya ɗauka ya kai aka ba shi kuɗin, ina nuna miki haske kina ƙara luluƙa kanki cikin duhu. Amma tunda kin ƙi ganewa bari na ƙyale ki, gaba idan ya kuma tafka miki wata babbar satar kya yarda don dole a lokacin da dare ya yi miki, tunda na nusar da ke tun farko don ki yi wa tufkar hanci amma kin ƙi fahimta." A razane na miƙe tsaye daga zaunen da nake, don zuwa yanzu na fuskanci gaskiya Maman Nasmah take faɗa mini, idan na yi la'akari da yadda yau Anas bai dawo gida ba daga kai su Sultan tahfiz, alhalin ko karyawa da wanka bai yi ba, kuma hakan ba ɗabi'ar shi ba ce, tabbacin ya tafi siyar da kayan kenan. Jijjiga kai na yi ina jin kamar zuciyata za ta fashe na ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Me ya sa Anas zai mun haka? Sai ana i gobe taronmu zai mun wannan tozarcin?" "Baƙin halin talaka kenan, ke kuwa kya fita a gan ki fess sanye da ɗanƙareriyar sarƙar gold shi kuma yana fama da kaya duk fenti?" "To wallahi bai isa ba! Bari ya dawo gidan sai ya fito mini da kayana." Maman Nasmah ta ce. "Atou, ki zage ki zabga masa rashin mutunci da tijara ya fito miki da kayanki, kar ki sake ki raga masa ko na sisi, wannan miji naki ai jaraba ne, ga tsiya ga sata, ban da ƙaddara ai kin wuce ajinsa, yadda kike Black beauty ɗin nan ai da manyan alhazawa kika dace, kwata-kwata ba ki yi dace da miji ba." Rasa abin cewa na yi saboda tsabar baƙinciki da takaici, cikin kuka na ce. "Na gode sosai Maman Nasmah, zuwanki cikin rayuwata alkhairi ne, tunda ga shi kina fayyace mini abubuwan da ban taɓa tunanin za su faru ba, na gode da nusar da ni ɗin nan kika yi." Ta ce. "Haba, mene na godiya, ai na faɗa miki tamkar ƴar'uwata ta jini haka na ɗauke ki, don haka babu godiya a tsakaninmu, abin da nake so da ke kawai duk wani abu da ya shige miki duhu ki faɗa mini zan ba ki shawara in sha Allah." Na ce. "Na gode, zan kira ki anjima na faɗa miki duk yadda muka yi da shi." Ta ce. "Allah ya kai mu, ina ƙara jaddada miki dai kar ki raga masa fa, ki buɗe masa wuta ya fito miki da kayanki." Na ce. "In sha Allahu." Tare da kashe wayar na yi cilli da ita cikin ƙunar zuci kamar ita ce Anas ɗin. Wani irin tafarfasa da turirin bala'i ne kawai yake kai kawo a cikinta. Maganganun Maman Nasmah sun yi zaman kafaffen rodi a cikin zuciyata, na yi amanna da yarda da su ɗari bisa ɗari, don a yanzu ko tantama ba na yi Abban Sultan ne ya sace mini kayana. Rasa inda zan saka kaina na ji daɗi na yi, na dinga safa da marwa daga tsakar gida zuwa ɗaki kamar zautacciya, filin zuciyata cike da tanadin tulin buhunhunan tijara da rashin mutuncin da zan zazzage a kan Anas. Ina bakin ƙofar soro na haɗa kaina da bango na ji an buɗe ƙofar gidan an shigo, kamar wadda ta ga abin tsoro haka na ɗago kaina da sauri na bi shi da mugun kallo, ban amsa sallamar da ya yi ba na fara magana cikin ɗaga murya. "Ina kayana? Kar ka ce mini komai kawai ka fito mun da kayana." Sororo ya yi yana kallo na cikin rashin fahimta, fuskarsa ɗauke da maɗaukakin mamaki ya ce. "Rashin kayan ne ya zautar da ke haka kike sunbatu marasa kan gado?" A fusace na ce. "Idan akwai abin da ya fi mahaukaciya ka kira ni da shi ma Anas bai dame ni ba, abin da na sani kawai wallahi sai ka dawo mun da abuna, ka je duk inda ka kai ma ko ka siyar da ka sata ka karɓo k...." "Sata kuma? Ni kike alaƙantawa da sata yau? Me zan yi miki da kayanki? Me za su ƙare ni da shi?" Ya yi maganar yana nuna kansa cikin ɓacin rai. Ɗage kafaɗa na yi na ce. "Oho maka, ka na tsammanin ba zan gane kai ba ne ka sata? Daga ni sai kai a gidan idan ba kai ba wa zai ɗauka?" Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Wallahi Hafsah inda kika ajiye kayanki ma ban sani ba bare na ɗauka, rantsuwa ba ɗabi'ata ba ce kin sani, amma na rantse miki da zatin Allah ba ni na ɗaukar miki kayanki ba, ki dai tuna ko kin cilla su wani gurin kin manta, ban da haka wa zai ɗaukar miki? Wa ma ya shigo gidan?" "Kai mana!" Na faɗa ina zabga masa harara. Numfashi ya sauke ya ce. "Da farko na ɗauka da wasa kike da kika nuna kike zargi, amma yanzu ban ga alamar hakan a tattare da ke ba, ban taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo a rayuwarmu ki alaƙanta ni da sata ba, kin fi kowa sani na da abin da zan aikata da wanda ba zan yi ba, ban san me na yi miki ba Hafsah kika zaɓi ki ta ɓata mini rai, kar ki kai ni bango na yanke hukuncin da duk ba zai mana daɗi ba." Baki na taɓe na ce. "An yi walƙiya na ga duk wasu mugayen halinka da a da son ka ya rufe mini ido ba na gani, don haka ko me za ka yi ka daɗe ba ka yi ba, ƙarƙari ka ce za ka sake ni ko? To idan ba ka sani ba ma ka sani shi na fi buƙata a yanzu, don in na rabu da kai wanda ya fi ka komai da komai zan aura." Taune leɓensa ya yi yana hucin ɓacin rai ya ce. "Huɗubar da suke yi miki kenan?" Na ce. "Oho maka, ni dai yanzu ba dogon surutu na nema ba, kawai ka fito mini da kayana, don ba ka siya mini ba, ba ka isa ka ɗauke wanda aka ba ni ba wallahi." Ya ce. "Sai ki yi ta yi, Allah ne shaidata kuma shi zai bayyana gaskiya." Cikin zaƙalƙala na riƙe ƙugu na ce. "Aikin banza, gayyar tsiya kawai da rashin zuciyata, ban da mugun hali babu abin da mutum ya iya, ko da yake an ce gado ba karambani ba ai, tunda ba ka tashi ka ga ana yi a gidanku ba ai kai ma ba ka yi a gidanka ba." Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shiga ɗakin da yake, ya juyo ya zuba mini idanunsa da suka yi jajir ɗin bacin rai, muryarsa na rawa ya ce. "Hafsah! Me kike nufi?" Ba tare da tsoro ko dogon nazarin sakamakon da maganata za ta janyo ba na ce. "Abin da yake akwai shi nake nufi, wanda ya kasa riƙe ɗansa ya turo shi almajiranci ta yaya zai iya kula da matarsa har ya yi mata duk abin da take so? Ka ga kenan ba a ƙasa ka ɗauka ba." Jikinsa har tsuma yake saboda tsananin fushi da ɓacin rai, don da farko na ɗauka duka ne zai yi idan ya ƙaraso inda nake, amma sai na ga ya kama hannayena ya damƙe a cikin nasa, muryarsa kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce. "Cin mutuncin har da iyayena da suke ƙasa Hafsah? Kar ki fara don Allah! Kar ki fara abin da zuciyata ba za ta ɗauka ba wato sako iyayena a cikin sabgar mu, don ba zan jure ba, zuciyata za ta iya tunzura ni na aikata abin da ban yi niyya ba, kar ki bari mu yi asarar juna saboda wasu can da ba ki san su ba, ba ki san da alkhairi suke nufin ki ko da sharri ba. Please na roƙe ki ko dan su Sultan, ina son ki, ban shirya rabuwa da ke. Kuma kar ki manta yanzu igiyar aurenmu saura biyu, furucin da na yi a baya na idan kika fita a bakin aurenki ya riga ya tabbata saboda kin fitan, na shiga tashin hankali a sanadin hakan, amma ke na ga ko a jikinki, to don girman Allah kar ki bari saura biyun ma su tsinke mana." Dogon tsaki na ja tare da fizge hannuna, ko kaɗan ban ji tausayinsa ko kuma na ji kalamansa sun ratsa ni ba, sai ma wani irin haushin shi da ya ƙara rufe ni, musamman da na tuno gobe ne taronmu, kuma shi nake zargi da sace abubuwan da za su saka na zama tauraruwa a taron, da kuma baƙincikin ƙin siyo mini wayar da ya yi, alhalin matan group ɗinmu komai suke so mazajensu suna yi musu cikin gaggawa. Ga uwa uba huɗubar Maman Nasmah, da ta dinga jaddada mini na tabbatar na matuƙar ɓata masa rai, ya ji babu daɗi shi ma kamar yadda na ji. Cikin son ƙara ƙona masa rai na ce. "Ai da ma wanzami ba ya son jarfa, to tunda ba ka so in dinga taɓa maka Iyaye, ka sake ni na je na auri wanda zai so ni, ya gatanta ni, ya yi mini duk abin da nake so a duniya, mai kuɗi ba faƙiri irinka ba." Bai ce komai ba ya juya kamar zai tashi sama alamun ba ya son ci gaba da jin maganganun da nake yi. Jikinsa sai kyarmar tsantsar ɓacin rai yake. Da sauri na bi bayansa na riƙo rigarsa, cikin fitsara na ce. "Na gaji! Na gaji da wannan takaicin naka! Ka sawwaƙe mini idan ka cika ɗan halak a cikin Binta da Musa!" Ban san lokacin da ya juyo ba sai ji kawai na yi ya ɗauke ni da wani wawan mari da ya saka ni kifawa. Da sauri na dafe kuncina tare da ɗaga kaina na kalle shi ina hawaye. Sai na ga shi ma nasa idanun da suka kaɗa suka yi jajir cike suke da ƙwalla, muryarsa a dashe saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai ya ce. "Ki je na sake ki Hafsah!".......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:39 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) 12. Tamkar saukar aradu da ka haka na ji furucin nasa a tsakiyar kaina, wani irin abu mai zafi da zugi ya baƙunci zuciyata. Lokaci ɗaya na nemi zafin marin da ya mini na rasa, saboda wanda nake ji a cikin zuciyata sakamakon sakin da ya mun ya ninninka shi. Da ma haka sakin yake? Haka mata suke ji idan aka yi musu shi ko da su suka nema? Ji na yi duniyar tana juya mini, na daina fahimtar komai na wucen gadi. Sama-sama na ji muryar Naja ƙawata da ban san lokacin da ta shigo gidan ba tana rafka salati, tare da ƙarasowa ta kama ni a inda na ƙame kamar mutummutumi ta shigar da ni parlour ta zaunar a kan kujera. Ko da wasa ban taɓa tunanin ko me zan yi wa Anas zai iya saki na ba, na ɗauka ko da zan dinga yankar naman jikinsa ina gasawa saboda azabtarwa ba zai iya rabuwa da ni ba, saboda matsananciyar soyayyar da na san yana mini. Numfarfashi kawai nake yi. Naja da ke riƙe ni har lokacin tana sallallami ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah me ya faru? Me ya haɗa ku da Abban Sultan? Don Allah ki ce abin da suka ziyarci kunnena lokacin da na shigo gidan nan ƙarya ne, kunnen nawa ne bai ji mini daidai ba." Girgiza kaina na yi ina hawaye na ce. "Daidai ki ji Naja'atu, kuma ni na buƙaci hakan da kaina." Ja baya ta yi a ruɗe ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi har haka ke kuwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da na san abin da zan tarar kenan da wallahi ba zan zo ba." Gimtse baki na yi tare da share hawayena na ƙwace daga riƙon da ta yi mini na dafe kaina tare da lumshe idona. A hankali a hankali na ji zafin sakin yana raguwa daga cikin raina, ina kallon Naja da ta ishe ni da tambayar sanin ba'asi na ce. "Me ya sa kika damu ne haka? Mene a ciki don na rabu da Anas?" Kallon mara hankali ta mun ta ce. "Ba don na gan ki fes kin ƙara fresh da kyau ba da sai na ce kina cikin mayen hauka ne, na zo na tarar da ku cikin tashin hankali ke da mijinki har ya sake ki sannan kuma ki ce me ya sa zan damu?" Murmushi na yi don a yanzu ba ta Anas da sakin ya yi mini nake ba, duk da ina jin ɗacin abun matuƙa a cikin raina, taron da za mu yi gobe da abin da zan saka shi ne kawai danuwata. "Me ya sa idan na kikkira ki ba kya ɗagawa? Idan na yi miki magana a Whatsapp ba kya dubawa bare ki mun reply?" Hararar ta na yi na ce. "Saboda kin gama kunce mini zani a kasuwa mana, na yi ƙarya da ke amma kika ce wa Anas ba ki san zancen ba." Gyara zama ta yi ta ce. "Shi ne dalilin da ya sa nake ta kiran naki ai, na ji dalilin da ya sa kika aikata hakan." Baki na taɓe na ce. "Ya riga ya wuce ai." Na ƙarashe maganar ina miƙewa don fara haɗa kayana na bar wa Anas akurkin gidansa. Naja da har lokacin na lura a cikin ruɗu take ta kamo hannuna kamar za ta yi kuka ta ce. "Hafsah kin bar ni a cikin duhu fa, don girman Allah ki faɗa mini abin da yake faruwa, na ga kin ware kamar ba wadda take cikin zullumi ba." Komawa na yi na zauna don na labarta mata duk abin da yake faruwa, saboda Naja ta wuce ƙawa ko aminiya a gurina, ta zamo ƴar'uwa da ba zan iya ɓoye mata komai nawa ba. Cikin takaici na ce. "Naja Anas ba so na yake yi ba kamar yadda yake pretending, na yi da na sanin auren shi." A zabure ta ce. "Kamar ya? Ban gane ba?" Tsaki na ja na ce. "Matan da mazajensu suke son su, suke yi musu duk abin da suke so a lokacin da suke so bayan wadata su da suka yi da komai na more rayuwa suna can daban, amma ni ko kusa ba na cikinsu, ba na cikin mata masu sa'a da ake kwatance da su, ake sha'awar su, ake burin samun mazaje irin nasu." Na ƙarashe maganar kamar zan fashe da kuka. Galala ta yi tana kallo na ba ta ce komai ba. Numfashi na sauke na ce. "Ba ki gane me nake nufi ba ko? Yanzu zan ganar da ke." Ban jira amsarta ba na kwashe labarin komai na faɗa mata. A matuƙar gigice na ga ta miƙewa kamar wadda na faɗawa ranar mutuwarta, tana nuna ni da hannu ta ce. "A'uzubillah! Hafsah da ma ba ki da hankali? Ashe mahaukaciya ce ke ban sani ba?" Haɗe rai na yi na ce. "Haukan uban me na yi?" A fusace ta ce. "Ban sani ba, wallahi ba don na kai zuciyata nesa ba da sai na kikkifa miki mari, kamar na rufe ki da duka haka nake ji, I'm speechless! Na rasa me zan ce miki, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ƙarashe maganar tare da dafe kanta. Tsaki na ja ban ce komai ba. Komawa ta yi ta zauna tana bi na da wani irin kallo, idanunta cike da hawaye ta fara magana da faɗin. "Ko a mafarki aka ce mini za ki aikata wannan tafkeken haukan da jahilcin ba zan taɓa yarda ba, yaushe kika haukace Hafsah? Yaushe kika daina amfani da ƙwaƙwalwarki wajen yin al'amuranki? Ina iliminki na addininki yake? Kin watsar saboda son duniya da hangen dala ko?" Shiru na yi ban ce komai ba. Kamar za ta rufe ni da duka ta ce. "Kin ba ni matuƙar mamaki da kunya, akan wani banzan group kika bari salihin miji irin Anas ya yi miki har saki biyu? Saura igiya ɗaya fa a tsakaninku yanzu? Saboda wasu tsinannu Hafsah!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji. Kallon banza na yi mata na ce. "Saboda sun haska mini abin da ban sani ba na rayuwa shi ne suka zama tsinannu? Ki yi mini duk zagin da za ki mini amma ban da su, don ni sun gama yi mini komai a rayuwa." "Sun gama kam, tunda sun cuce ki sun kashe miki aure, su kuma suna can zaune lafiya ƙalau da mazajensu." Naja ta faɗa tana jifa na da wani mugun kallo. Cikin tsagalgala na ce. "Ai su mazajensu ba talakawa ba ne, kuma da ma irin gidajensu ai ba a fatan a fita." Ta ce. "Haka ne, duk da na ga alamar kin yi nisa amma ba zan ƙi faɗa miki gaskiya ba, da tunatar da ke abin da gidahumar ƙwaƙwalwarki ta mantar da ke ba. Hafsah tun kina ƴar ƙarama a zanin goyo mahaifinki ya rasu, mahaifiyarki kuma bayan kin ɗan girma ba ki fi shekara uku ba ita ma ta bi bayan shi, daga lokacin aka dawo da ke gurin Kawu ya riƙe ki. Kawu ya yi miki riƙo na tsakani da Allah tamkar ƴar da ya haifa a cikinsa, kuma ya nuna miki soyayya saboda bai taɓa haihuwa ba, sanadiyyar hakan Gwaggo matarsa ta tsane ki, ta gana miki azaba. Ba sai na tuna miki irin uƙubar da kika sha a gurinta ba, saboda kin fi kowa sani. Yanzu idan kika bar nan kika koma gida a matsayin bazawara ya kike tunanin zamanku zai kaya ke da Gwaggo? Kina budurwa ma ba ta so ki ba balle a yanzu? Ko kin mata da wannan? Kuma idan ba gidan ba, ba ki da gurin zuwa, tunda dangin mahaifiyarki suna can Lafiya, tsakaninki da su waya ce ko chat, ba ki taɓa zuwa ba, su ma ban da lokacin bikinki ba su taɓa zuwa kun haɗu ba, can kike tunanin za ki je ki yi zawarcin a haka? Ba su saba da ke ba, ba ki taɓa zuwar musu ba, kawai sai su gan ki rana tsaka ki ce musu aurenki ne ya mutu kika koma? Ki yi aiki da hankalinki ki yi tunanin abin da zai fishshe ki, takamaiman gurin da za ki je ki zauna ma ki ji daɗi ba ki da shi idan kin bar nan ɗin, amma a haka kika kashe aurenki?" Shiru na yi don maganganunta sun fara ratsa ni, amma duk da haka ba su saka na ji zan saduda ba. Ganin haka ta ci gaba da magana da faɗin. "Abu na biyu kuma, samun mijin da yake son ka tsakani da Allah ma kamar yadda Anas yake son ki a wannan zamanin wahala yake, ya so ki tun kina ƴar ficiciyarki, ba ki san kanki ba, bare ki yi kwalliya da za a ce ita ta ja hankalinsa gare ki, kuma a lokacin ko alamar zama budurwa ba ki fara ba, bare ya ce ya ga kyanki ko jikinki ya so ki don su, hasalima a cikin rayuwar wahala da ƙuncin rayuwa ya gan ki, ya fara da jin tausayinki daga nan ya rikiɗe ya koma soyayya. Babu gatanta kin da bai yi ba tun kina gida har zuwa aurenku daidai ƙarfin ikonsa. Soyayya, kulawa, darajawa, babu wanda bai nuna miki ba. Ya taya ki aikin gida, ya kai ki unguwa da kansa, ya ɗauke miki dukkan wata ɗawainiyarki, da kika haifi ƴaƴa bai canza miki ba kamar yadda wasu mazan suke yi, ya rungume ku ke da yaranki kuka ci gaba da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Anas bai taɓa ragar ki da komai ba, to me kike nema a gurin miji da ya fi wannan? Me kike da buƙata? Ke ba matsalar kishiya, ba ta uwar miji, ba ta ƙannensa ko yayye ba, miji ba ya dukanki, ba ya cin mutuncinki bare zagi. Amma saboda hauka ki dinga hangen na wasu can da ba ki san irin taskun rayuwar da suke ciki ba, wallahi Maman Sultan daɗi ne ya yi miki yawa, da kuma kin samu Anas ɗin mai haƙuri. Da ma an ce samu mai saka hauka." Baki na zunɓura na ce. "Hmm, duk waɗannan bayanan naki kin san dai na fi ki sanin da su ko?" Ta ce. "Eh, amma ba kya duba su ai." Na ce. "Eh, saboda ni yanzu ba su ne a gabana ba." Naja da take jin kamar ta rufe ni da duka ta ce. "Ƙaton gida da hawa manyan motoci su ne a gabanki ko? Ki faɗa mini matar da kika sani da always mijinta ne yake saka mata data da katin da za ta yi waya, idan za ta je unguwa ko'ina ne ya ba ta transport, na tabbata da za ki cikiya kafin ki samu ɗaya sai kin samu 50 da ba a yi musu. Ke fa tsabar daɗi ko sana'a ba ki taɓa gwadawa ba, saboda ba ki da buƙatar komai, yi miki ake kina daga kwance ƴar gata. Kuma ko ma ba wannan ba, kwanciyar hankali ya fi komai a rayuwar nan, ka ci ka sha, ka yi ibada ba wani tension ka yi baccinka, me ya fi wannan daɗi? Anas shi ne gatanki, shi ne suturarki, shi ne rufin asirinki, ko kaffara ba zan yi ba idan kika rabu da Anas ba za ki taɓa samun miji kamar shi ba, don irinsu a yanzu ba su da yawa, sun yi ƙaranci." Da sauri na ce. "Zan samu wanda ya fi shi mana, sosai ma." Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ban san lokacin da kika koma mayyar kuɗi ba, idan kuɗi kike nufin za ki samu wanda ya fi Anas za ki samu sosai ma, amma samun mai nagartar shi ne zai yi miki wahala. Ana cewa mazan aure sun yi ƙaranci, ba ƙaranci suka yi ba, samun nagari nagartacce ne ya yi wahala. Kin gan ni nan, ban rasa mijin

Chapter 7 of 24