Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gurin na fito ina sauke numfashi. Tarar da su na yi suna hira hankali kwance. Ba tare da ya damu da yadda ya gan ni a hargitse ko ya tambayi jikina ba ya ce. "Ga Hajiya nan Hafsah, za ta zauna a nan gidan tare da mu, can gidan Samira babu space." Ji na yi gabana ya yanke ya faɗi, kafin na yi magana ta riga ni da faɗin. "Sai ka ce mata wani gidan Samira babu space? Nan kai yi niyyar kawo ni, za ta hana ne ko me kai da gidanka?" Kansa ya shafa ya ce. "Haka ne fa." Tare da mayar da kallon shi gare ni ya ce. "Kin yi girkin?" A raunane na ce. "Ban jima da tashi daga bacci ba, ka san ban da lafiya, wallahi ba zan iya aiki ba a yanzu, jikina duk ya mutu, ga shi har sau biyu ina yin amai." "Idan asibitin Murtala da Malam ne a kanki babu abin da ya shafe ni, don tsabar iskanci ciwon bai tashi zuwa ba sai da mahaifiyata ta zo? To ba zai yiwu ba, ko za ki mutu sai kin yi girkin nan wallahi." Ya faɗa cikin ɗaga murya. Kallon Hajiya na yi ko za ta saka baki ya ƙyale ni amma sai na ji ta ce. "Ki yi abincin da yawa, don su Bilki duk za su zo yanzu." Da sauri na ɗago kai na kalle ta a wahalce, ko makaho idan ya shafa ni sai ya gane ban da lafiya, balle mai idon da zai ganar masa yadda na yi firkai-firkai, amma saboda rashin imani wani aikin ma take cewa a ƙara mini. "Kina ji ai." Ya faɗa yana zazzaro mini ido waje. Idona cike da ƙwalla na ɗaga masa kai kawai. Kamar sabuwar jaka haka na wuni ina aiki, ga ciwo da yake ƙara baibaye ni. Kafin na gama girkin na yi amai ya kai sau biyar, bayan na kammala na dinga jigilar kai wa da komowar kai musu abincin. Babu wanda ya ce mini sannu bare na gode, sai ma tukuicin mugun kallo da harare-harare. Sai da na tabbatar na kai musu duk wani abu da za su buƙata sannan na koma ɗaki na kwanta bayan na yi wanka da sallah, don wani irin azababben bacci nake ji. Ga yunwa ina ji amma ko yunƙurin cin wani abu na yi sai na ji amai, hakan ya sa tilas na haƙura na kwanta ba tare da na ci komai ba a gabaɗayan wunin yau. Gajiyar da na yi ta ƙara mini zazzaɓi da ciwon kai da wani irin ciwon gaɓoɓi, don kamar ba a jikina ba haka nake jin su. Ban yi nisa a baccin ma na ji ana yarfa mini ruwa a fuska. A firgice na tashi ina salati. Sani na gani a kaina da robar ruwa a hannunsa. Yana jifa na da matsiyacin kallo ya ce. "Kin ajiye bawan da zai gyara gidan nan ne?" Kuka na fashe da shi saboda yadda nake jin jikina na ce. "Haba Sani! Ba ka ganin halin da nake ciki ne? Ban da lafiya fa, taɓa jikina ka ji mugun zafin da ya yi." "To ina ruwana da rashin lafiyarki? Auro ki na yi don ki bauta mini ko kina da lafiya ko ba ki da ita, kin sani sarai ba ma shiri da ƙazanta, ki tashi ki je ki tsaftace gidan nan, ga ɗakin Hajiya can ma ki gyara mata, don wulaƙanci ashe ɗazu da na ce ki gyara ƙin gyarawa kika yi ma?" Ƙara fashewa na yi da kuka na ce. "Me ya sa ka zama mara tausayi ne? Me ya sa ka canza daga Sanin da na sani? Don Allah ka bar ni na huta mana, wallahi tsabar yadda nake ji na rasa ina zan saka kaina na ji daɗi." Jijjiga kai ya yi ya ce. "Haka nake da ma can ni ba sauyawar da na yi, mace don ta yi mini bauta na aure ta, ba don ta na zuba mata ido ta kwanta kawai ta huta ba." Ina goge hawayen fuskata na ce. "To mene bana yi maka? Kuma yanzun ma ai ka ga ban da lafiya ne." Bai ce komai ba ya juya ya fita, ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗin ya ƙyale ni na koma na kwanta, ko mintuna biyu ba a yi ba ya dawo tare da watsa mini sachet ɗin magani a jikina ya ce. "Ga shi nan, ki tashi ki sha ki je ki yi abin da na saka ki." Bai jira amsata ba ya juya ya fice daga ɗakin. "Taɓɗijan!" Na faɗa tare da tashi, don zuwa yanzu na fara jin tsoron shi, gabaɗaya gani nake wani daban aka ajiye mini ba Sanin da sani ba ne. Ko wata biyu ban cika ba amma har na fara fuskantar irin wannan matsalar da ban taɓa zaton akwai maza masu irinta ba? Ina kuma ga tafiya ta yi tafiya an yi shekaru? Ina kuka ina aikin gyaran parlour'n da suka yi dama-dama da shi, ga shi har an yi Magriba ma ban sani ba ina can bacci. Sai wajen goma na gama tulliƙar uban kayan wanke-wanken da suka ɓata, a kitchen ɗin na zube a kan tiles ina numfarfashi kamar raina zai bar gangar jikina. Daga nan ban ƙara sanin me ya faru ba sai farkawa na yi na gan ni a parlour a kan carpet. Da rarrafe na je na buɗe fridge na ɗauko ruwa mai sanyi da na ji shi kawai nake so na fara kwankwaɗa, sai da na shanye tas na cillar da jarkar sannan na tashi ina sakin ajiyar zuciya. Direct kitchen na nufa na lalubo guntun abincin da suka rage na fara ci hannu baka hannu ƙwarya, saboda azababbiyar yunwar da take nuƙurƙusar hanjina. Allah ya taimake ni wannan karon ban yi aman ba, na lallaɓa na koma ɗakina na sha maganin da ya cillo mini na kwanta. Da ma yau ya gama kwanansa a gurina zai koma gurin uwargida ne. Da safe na tashi jikin da sauƙi amma ba wai na warke sumul ba ne, tun sassafe Inna Habi take yi mini flashing, ba ta san ni ma ba katin ne da ni ba. Ina gama morning azkar ɗina na tafi ɗakin Hajiya na gaishe ta, cike da shan ƙamshi ta amsa tare da faɗin. "Don makirci jiya shi ne kika baje a kitchen ba tare da kin girka mini abin da zan ci ba ko?" Kaina a ƙasa na ce. "Ki yi haƙuri Hajiya, wallahi ban da lafiya ne, kuma na ga akwai ragowar wanda na dafa." Taɓe baki ta yi ta ce. "Bana cin abinci kala ɗaya sau biyu a rana, da rana, da safe da daddare duk fresh nake ci. Ina fata kin gane?" Gyaɗa mata kai na yi na ce. "Eh, in sha Allah kuma zan kiyaye." Ba ta kuma magana ba ta ɗauke kanta, duk a maganganunta na fahimci ita ta kai ni parlour daga kitchen ko tambayar jikin nawa ba ta yi ba. Sai ma aiki na babu gaira babu dalili da ta dinga saka ni. Wannan rana ita ma ban huta ba, wuni na yi ina abu ɗaya, da na zauna za ta tashe ni na yi mata wani abun. Ina son na yi bacci amma ban samu dama ba, ga aman da na fara jiya yau ma sai da na yi shi sau biyu. Duk na galabaice na fita daga hayyacina na yi zuru-zuru. Da ya zo da safe kafin ya wuce kasuwa shi ma bai mun sannu da jiki ba. Takaici ya sa na ƙule a ɗaki na ci kukana na ƙoshi. Bayan Magriba ina zaune a kan darduma Inna Habi ta dame ni da flashing, checking balance na yi a account ɗina na ga ina da ɗari da wani abu, cikin murna na siya katin na kira ta. Tana ɗagawa ta ce. "Hafsah daga samun duniya har kin fara wulaƙanci ko? Ni zan ta kiran ki, ki ƙi kira na?" Murmushin da ya fi kuka ciwo na yi na ce. "Ki yi haƙuri Inna, bana kusa da wayar ne." "Tun safen?" Ta tambaya cikin faɗa. Na ce. Eh, babarsa ce ta zo, ina gurinta." Ta ce. "Tom shikenan, da ma ce miki zan yi ko ƴar dubu biyar ce a kuɗin da kika tara ki turo mini." "Wanne kuɗin Inna?" Na tambaye ta cikin mamaki. Ta ce . "A'a, ku ji mun yarinya, guntun na cefane mana da wanda yake ba ki." Girgiza kai na yi na ce. "Inna ai shi yake siyo komai nasa, ko biyar ba ya ba ni." Da sauri ta ce. "Wannan zancen ƙanzon kurege ne, kina kamar wannan gidan, kuma mijinki da halinsa ba ba shi da shi ba ki ce ba ya ba ki, sai dai in rowa za ki mun." Numfashi na sauke na ce. "Tom shikenan, zan kawo miki in sha Allah." Ta ce. "Yaushe?" Na ce. "A cikin satin nan." "Allah ya kai mu, ina nan ina zuba ido, saura kuma na ji shiru, kawunki ma ya kamata ki je ki gano shi, don ƙafar tasa ta tasar masa kwana biyu." A ruɗe na ce. "Subhanallahi! Bari na kira shi." Daga haka muka yi sallama na kashe wayar. Kawu na kira da guntun kuɗin da ya rage, na yi masa ya jiki? Ya ce da sauƙi ma sosai tare da tambaya ta da fatan komai dai lafiya na ce masa eh. Ba mu wani jima muna magana ba kati ya ƙare. Jujjuya wayar na shiga yi a hannuna, yau kwana uku ban da data, ko da nake gidan Anas da ba shi da shi ban taɓa yin irin kwanakin nan babu data ba. Lumshe idona na yi tare da ajiye wayar ina tuno rayuwarmu, yadda yake taya ni aiki da tarairaya ta kamar ɗanyen ƙwai, idan ban da lafiya ya ruɗe ya rasa inda zai saka kansa, amma nan ko sannu ta gagara a yi mini. Ga shi da ya ga alamar ban da kuɗi zai ɗauka ya ba ni ko da babu yawa. Ban ankara ba na ji hawaye yana bin kuncina ba tare da na san dalilin su ba. Tuno Hajiya tana can tana jiran abincin dare ya sa na miƙe ina share hawayena na nufi kitchen na fara kiciniyar ɗora girki. Ga kayan abinci nan birjik da lemuka amma duk sun fita a kaina, ji nake gidan ya yi mini zafi duk na ƙuntata. Ina cikin aikin ya shigo yi mini sallama, a ladabce na dube shi na ce. "Don Allah ina so gobe na je na duba Kawu, jikinsa ya tashi." Cikin isa ya ce. "Idan kin gama aikinki da wuri sai ki je, kuma kar ki yi dare." Na ce. "To na gode." Har ya juya zai fita na ce. "Don Allah idan babu damuwa kankana nake son ka siyo mini, yau ma na kasa cin abinci ita kawai na ji ina sha'awa." Wani kallo ya yi mini ya ce. "Ki siya da kuɗinki mana." Kafin na yi magana Hajiya ta shigo kitchen ɗin tana faɗin. "Me kake yi a nan har yanzu kuma? Ka san yara da Samira suna can suna jiran ka." Ya ce. "Eh yanzu zan tafi, sallama na yi mata." Baki ta taɓe ta ce. "Ka ƙara tsayar da ita dai, da ma ta bar ni yunwa tana damu na sai yanzu ta ga damar ɗora girkin." Nuna ni ya yi da hannu ya ce. "Daga yau ki tabbatar kafin Magriba kin gama girkin dare, ya za ki dinga barin mahaifiyata da yunwa bayan komai na siyo na ajiye?" Kaina a ƙasa na ce. "Zan kiyaye da yardar Allah." Tsaki ya ja ya mayar da duban shi kanta ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah Hajiya, ba za ta sake ba." Ta ce. "To, ga kayan da na cire jiya da yau can, idan ta gama sai ta wanke mini." Cikin rashin daraja ya sune ni ya ce. "Kin ji ai, sai ki hanzarta." Da ido kawai na bi su har suka fice tana kwarara masa addu'a........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [5/11, 12:12 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *30.* Jingina na yi a jikin cabinet saboda jirin da yake ɗiba ta, tarin da gajiyar da ta addaba ta na kwanciya na huta kawai nake buƙata, amma tsabar rashin tausayi wani aikin ma ake tula mini a daren nan. Da kukan da ba zan ce ga dalilinsa ba na ƙarasa girkin. Na shirya komai na kai mata har bedroom ɗin da take, sannan na shige toilet na fara wanke mata kayan da ta ce. Ina cikin yi ta leƙo ta ce. "Idan kin gama ki ƙara wanke toilet ɗin, sannan na ga kitchen duk a hargitse, ki tabbatar kin gyara shi tsaf kafin ki kwanta, don ba za a dinga bar mini gidan yaro da datti ba. A wahalce na dube ta na ce. "Ki yi haƙuri Hajiya a bar shi da safe na gyara, wallahi kamar ana zare mini numfashina haka nake ji, ba ni da lafiya sosai." Wani kallo ta yi mini cikin hura hanci ta ce. "Shi ya sa na gan ki ga ki nan shame-shame a kwance ai." Ban kuma magana ba na ci gaba da abin da nake yi. Sai wajen 12 na kwanta, gaɓoɓina kamar an sassara mini su, ga yunwa da nake ji, kuma ko ƙamshin abinci bana son ji bare na zuba na ci. Kankana kawai zuciyata take da muradi, na duba kuma ko ina da kuɗi na ba wa maigadi ya siyo mini ban ga ko biyar ba. Hakan ya sa baccin ma ya ƙi zuwa gabaɗaya, na dinga juyi a gadon ina jin kamar zan ci babu. Wajen 3 na kasa jurewa na tashi na je na haɗa tea mai yawa na kwankwaɗe. Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba saboda jin daɗin sauƙin da na samu. "Ke! Ke!" Na ji ana kwaɗa kira a kaina. A tsorace na buɗe ido da ƙyar saboda baccin da yake ci na. Hajiya na gani tsaye a kaina, da sauri na yunƙura na tashi zaune ina ƙare wa inda nake kallo. Ba ta ce mini ƙala ba ta bar gurin, ajiyar zuciya na sauke, ban ma san a parlour bacci ya ɗauke ni ba. Ƙyallin rana na hango ta window, a gaggauce na tashi na yi ɗaki na yi alwala na yi Sallah na fice kitchen, saboda ganin har takwas na safe ta wuce. Ina tunanin abin da zan yi Hajiya ta shigo kitchen ɗin fuska a cuskune, tana bi na da wani matsiyacin kallo ta ce. "Sai yanzu kika ga damar tashi kenan? Har kusan ƙarfe tara ba ki yi komai ba sai yaushe za ki gama kenan? Sai yunwa ta ci ta cinye ni ko?" Cikin girmama na tsugunna na ce. "Ki yi haƙuri Hajiya, wallahi ban san safiya ta yi haka ba, kuma jiya ban kwanta da wuri ba." A shaƙe ta ce. "Ki daina bari kina yawan saka ni magana da ƙorafi, dududu yau kwanan mu nawa tare amma kullum sai kin ɓata mini rai, kar fa ki kai ni bango na yi miki abin da za ki zo kina da na sani." Kaina a ƙasa na ce. "In sha Allah ba zan kuma ba, ki yi haƙuri." Tana ƙoƙarin barin kitchen ɗin ta ce. "Sannan kuma kafin ki yi girki a kodayaushe ki riƙa zuwa kina tambaya ta abin da za a girka, ba wai ra'ayin kanki za ki dinga yi ba." Da sauri na ce. "In sha Allah." Ta ja dogon tsaki sannan ta fice. Ajiyar zuciya na sauke tare da miƙewa ina sauke numfashi, wacce ƙaddara ce ta janyo ni gidan nan? Ni kam na ga ta kaina da wannan wahalalliyar rayuwar, uwar miji bala'i, miji bala'i, ƴan'uwansa bala'i. Ko bacci nake na farka idan na tuno Hajiya sai gabana ya faɗi, ga shi na koma kamar jakar baiwar da aka siya da duka saboda uban aikin da nake sha, ko lokacin kaina ba ni da shi yanzu, sallah ma sai na yi mugun dagewa zan dinga yin ta akan kari, matuƙar aka ci gaba da tafiya a haka. Tunawa da na yi ban ta faɗi abin da za a dafa mata ya sa na fice da sauri na je ta tambaye ta. A wulaƙance ta ce. "Mintuna nawa da fitowa amma sai yanzu za ki biyo ni ki tambaya?" Cikin mamakin yadda komai na yi mata laifi ne na ce. "Na ɗan tsaya gyara kitchen ɗin ne." Ƙwafa ta yi ta ce. "Haɗo mini tea, sai ki soya ƙwai da dankali." Na ce. "Tom, da rana fa." Kamar ba za ta amsa ba sai daga baya ta ce. "Idan ranar ta yi kya ji." Ban ce komai ba na juya na fita, cikin raina ina jinjina sarauta da mulkin matar nan. Da ta faɗa da ma da ɗorawa zan yi da wuri saboda na yi na gama na je na dubo Kawu. A parlour na shirya mata abincin, bayan na gama gyaran gidan ina ƙoƙarin zuwa na yi wanka Sani ya shigo, mata da yara uku da na ga suna bin shi a baya ya sa gabana faɗuwa, don ko ba a faɗa ba na san matarsa ce, tunda ba ta cikin ƴan'uwansa. Da azama na yi nufin shiga daƙi don na kimtsa kar kishiya ta gan ni a hargitse amma Hajiya ta tsayar da ni da faɗin. "Ke Hafsah, miƙo mini wayata a ɗaki." Ban da zaɓi ban da bin umarninta, amma kamar na zunduma ihu haka na ji. Kafin na dawo har sun zazzauna, yadda matar take ta bi na da kallon ƙasan ido ya tabbatar mini da hasashena. Cikin takaicin ita tana fes ni kuma ta same ni a yarkace na gaishe su, ba yabo ba fallasa ya amsa, ita kuma kamar an yi mata dole. Fuska a haɗe kamar kodayaushe idan Hajiya za ta yi mini magana ta ce na je na sake sabon girki na kawo musu, ta tambayi yaran da ko gaishe ni ba su yi suka faɗi abin da suke so na je na yi na kawo musu, a taƙaice dai sai wajen sha biyu na karya na yi wanka na shirya, da zummar ina gama abincin rana na fice. Sai da na yi zarya uku kafin ta faɗa mini abin da zan girka da rana, idan na je sai ta ce ba yanzu ba, lokacin cin abinta bai yi ba. Sai wajen uku na kammala komai na kai musu, a lokacin shi ma yana gidan, har sannan kuma ita ma kishiyar tawa ba ta tafi ba. Ina son na yi magana da shi amma na rasa ya zan yi, don tunda ya zo bai shiga ɗakinsa ko nawa ba bare na bi shi mu keɓe. Ganin lokaci yana tafiya kuma sai na dawo na yi girkin dare ya sa na yi ƙundunbala na je ɗakin Hajiyar na ce masa ina son magana da shi. Banza ya yi mini kamar bai ji abin da na ce ba, su kuma duk suka yi tsit suka zuba mini na mujiya, sosai na muzanta, musamman da na tuna a gaban kishiya ya yi mini wannan wulaƙancin. Danne kukan da ya taho mini na yi na ƙara maimaita masa. A wulaƙance ya ce. "Me ya faru?" Cikin dakiya na ce. "Na gama aikin ne da ma, shi ne na ce zan je na dubo Kawun yanzu." Kallon Hajiya ya yi ya ce. "Hajiya kina ji fa, wai gida za ta je, ko kawunta ko ba ya jin daɗi ko me oho?" Yatsina fuska ta yi ta ce. "Fita kuma a yanzu? To ta dawo yaushe?" "Ana yin la'asar in sha Allah." Na faɗa cikin fatan ta bar ni na je ɗin. Girgiza kai ta yi ta ce. "Sai dai wani lokacin, yamma ta yi yanzu, idan ina buƙatar a mun wani abun wa zai mun idan kin saka ƙafa kin fice?" Ban san lokacin da na ɗaga kai na ƙura mata ido, cuta fa na ce babana yana yi zan je na dubo shi, amma saboda mugun hali ta hana. "Ko ba ki ji me aka ce ba ne?" Na ji ya faɗa cikin ɗaga murya. Kai kawai na gyaɗa na fice daga ɗakin daga kamar sabuwar munafuka. A parlour na zube a ƙasa na fashe da kuka, hana nin da aka yi bai kai nuna ba ni da darajar da suka yi a gaban abokiyar zamana saka ni a cikin takaici ba. Ya nuna da ni da banza duk ɗaya ne a gurinsa, tunda ko kallon arziƙi ban ishe shi ba tun da suka shigo. Jin ana knocking ƙofar parlour ya sa na goge hawayen fuskata na je na buɗe. Wata mata ce cikin shiga ta kamala, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce. "Sannu amarya." Na ba ta hanya tare da faɗin. "Yawwa." Tare da gaishe ta cikin fara'ar da na ƙaƙalo ni ma. Ta amsa tare da faɗin. "Na zo gaishe da Hajiya ne, na san ba ki san ni ba, ni ƴar ƙanwarta ce." Na ce. "Allah Sarki, mu je na raka ki inda take." Ko shiga ban yi ba na nuna mata kawai na koma ɗakina, kuka nake son na ci gaba da yi ko zan samu sauƙin abin da yake damun raina. Sosai wannan ɗabi'ar da rashin sanin darajar mace ta mijina ta fara saka mini tashin hankali mara misaltuwa. Ban san haka rashin kwanciyar hankali yake ba sai yanzu ba, don ji na yi gabaɗaya komai na duniya ya fice mini a rai. Ina zaune ina tunanin Kawu da jikinsa da ƴaƴana da nake cikin matsananciyar ƙishirwar ganin su na ji ana bubbuga ƙofa. Sunan Allah na ambata saboda faɗuwar da gabana ya yi, don ko sunan Sani da Hajiya na tuno sai razani ya baibaye zuciyata. Jiki a saɓule na tashi na buɗe, ganin baƙuwar da ta zo ce ya saka ni sakin ajiyar zuciya. Da fara'a kamar ɗazu ta ce. "Yaya Sani yana ta ƙwala miki kira ki kawo mini ruwa, shi ne na ce masa bari na je na ɗauka da kaina, ai ni ba baƙuwa ba ce a gidan." Murmushi na yi na ce. "Gaskiya dai kam." Tare muka fita na zuba abinci ta ci, tana ci muna hirar duniya. Babu ruwanta, ga ta da kirki, ta sanar mini sunanta Binta. Da zan yi aikin abincin dare tare muka shiga kitchen ta taya ni, duk da na hana ta amma ta dage sai ta yi. Bayan mun gama muna zaune mu kaɗai a parlour ta ce. "Aunty Amarya kamar ba ki da lafiya ko? Na ga ɗazu kamar amai kika yi, kuma fuskarki ta nuna alamun hakan." Na ce. "Eh, gaskiya kwana biyu bana jin daɗin jikina?" Ta ce. "Kin faɗa masa kuwa? Saboda ku je asibiti a ga abin da yake damun ki." Cikin takaici na ce. "Ya sani, har magani ma ya ba ni." Girgiza kai ta yi ta ce. "Yaya Sani ba zai taɓa canza halinsa akan mace ba, tunda na ji an ce ya yi aure, tun kafin na gan ki na fara tausayin ki." Da sauri na ce. "Me ya sa?" Ta ce. "Ki yi haƙuri mijinki ne, amma kwata-kwata ba shi da mu'amala tsakanin shi da iyalinsa, ko ita Aunty Samira ba wani daɗin shi take ji ba, duk da tana ƴar'uwarsa, zai sauke wa mace komai na haƙƙin da yake kansa, amma fa faɗa da masifa kullum cikin yin su yake." Cikin mamakin yadda take rattabo bayani ba tare da na tambaye ta ba na ce. "Hmm." Kawai. Gajeren murmushi ta yi ta ce. "Kin yi mamaki kawai na fara ba ki labari ko? Duk da na san zuwa yanzu ya fara bayyana miki halinsa, amma ina sanar miki ne don ki san irin ɗamarar da za ki ɗaura, don ba ki ga komai ba a yanzu. Ga shi dai mutum har mutum, ga addini daidai gwargwado, a waje babu mai ganin shi ya ce shi yake irin wannan abubuwan, kuma Babbar matsalar ma ba shi kaɗai ba ne abin jin, da shi ne kawai da sauƙi, to har da familynsa, duk ba sa barin matansa su yi

Chapter 19 of 24