gane talaka nake aure su raina ni. Kowa yana taɓuka abun arziƙi a group ɗin amma ban da ni, komai ni ce koma baya. Ga shi an san ni sosai, ina daga cikin mutum biyar da suka fi kowa magana a gidan, shi ya sa ko daɗewa na yi ban hau online ba sai su yi ta cikiya ta, a yanzu ma sai da Maman Nasma da Aunty Billy mai group ɗin suka yi tagging ɗina, suka ce ni rowar abincin nake musu ne da ban turo nawa ba? Ƙaryar na je unguwa na yi musu. Tagumi na yi na fara tunanin ko tashi zan yi na yi dambu ne na tura musu? Tunda ina da gyaɗa da zogalen da ya siyo ɗazu, saboda yana son miyar zogale shi ya sa duk lokacin da zai siyo kayan abinci sai ya haɗo da shi. Murmushi na yi na miƙe ina faɗin. "Haka za a yi." Duk da ba a nan gizo yake saƙar ba, tunda ban da wayar da zan ɗauki hoton dambun ya fito ya yi tar kamar nasu, da haɗaɗɗun food flak's ɗin da zan zuba irin nasu, kuma su akan dinning suke jerawa su ɗauki hoto su turo, ni kuwa gidana ko tiles babu sai ledar tsakar ɗaki. Gwauron numfashi na ja na koma na zauna saboda tunawa da na yi shinkafar da zan yi amfani da ita ma ita kanta sai na yi zaman tsincewa, ba kamar su da sai dai kawai su saka abu su kamfata a cikin buhu su wanke su dafa ba. Takaici goma ashirin da hamsin duk suka cika mini zuciya. Tsabar tunanin ranar da mafarkina zai zama gaskiya ban san Sultan ya shigo ɗakin yana ta sallama ba sai da ya taɓa ni. A fusace na doka masa tsawa tare da faɗin. "Mene ne?" A firgice ya ɗan ja baya idanunsa cike da ƙwalla ya ce. "Abba ne ya ce ki shirya mu je gidan Kawu." Tsaki na ja na ce. "Ka ce masa bana jin daɗi." Yadda yaron ya yi sororo yana kallo na cikin hawaye sai jikina na fara yin sanyi, na ji kamar na zubar da makaman yaƙina na haƙura da batun zuwa taron gabaɗaya, na rungumi ƴaƴana da mijina kawai mu koma rayuwarmu kamar da.
Janyo shi na yi jikina cikin sanyin murya na ce. "Kar ka yi kuka yaron kirki, I'm sorry na yi maka tsawa." Cikin kuka ya ce. "Mamy kin daina son mu yanzu, kullum sai dai ki yi ta yi mana faɗa da tsawa." Kansa na shafa na ce. "Ai uwa ba ta taɓa daina son ɗanta har abada my son." Bai kuma magana ba har na share masa hawayen fuskarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin daina yi mana faɗa ko?" Ɗaga masa kai na yi ina murmushin da suka kwana biyu ba su gan shi a fuskata ba. Ta window na hango Abban Sultan tsaye yana kallon mu, ɗauke kai na yi tare da ture Sultan daga jikina. Fita yaron ya yi shi kuma ya shigo, muryarsa da alamun maɗaukakin ɓacin rai ya ce. "Duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina Hafsah, amma ban da ƴaƴana, ba za ki tusa musu damuwa a cikin zuciya tun suna ƙanana ba." Haɗe rai na yi sosai na ce. "Ai ni ba ƴa ba ce da kai kake cusa mini damuwar."
"Me nake miki? Me na rage ki da shi a zamanmu?" Ya tambaya a kaushashe.
Ɗage kafaɗa na yi tare da taɓe baki ban ce komai ba.
"Tambayar ki nake yi fa."
Numfashi na sauke na ce. "Babu komai." A fusace ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fita, na raka shi da harara.
Wayata na janyo na kunna data na ɗora daga inda na tsaya, hirar taron da za mu yi kawai ake yi a group ɗinmu, hakan ya ƙara dugunzuma hankalina, domin ranakun taron da suka rage ba su fi goma ba, ga shi abubuwan da nake yi ya sa ba mu ƙara zancen ƙaryar bikin Naja da na cewa Abban Sultan za a yi ba, bare ya ba ni ko iya kuɗin da ya alƙawarta ne, har yanzu bayan 5k ɗin taron da na tura ban ƙara wani shiri akai ba, saboda ba ni da ko sisi. Na ja tsaki ya fi cikin kwando na rashin mafita.
Bayan Magriba ina zaune a parlour ina chatting da ƙawayena na ga messages suna ta shigowa na group ɗinmu na *Zumuncinmu*, da sauri na shiga group ɗin don ganin abin da ake tattaunawa akai. Da message ɗin wata Maman Ayman na fara cin karo, ta turo video na wata tsaleliyar waya a cikin kwalinta kamfanin iphone. Ban san lokacin da na tashi zaune daga kwancen da nake ba saboda tafiya da ni da wayar ta yi. Babu abin da ya fi jan hankalina sama da cewar da ta yi mijinta ne ya siya mata saboda yadda ta ci burin taron da za mu yi, don ta je da sabuwar waya ta sha pictures. Ci gaba da bin chat ɗinsu na yi ina karantawa da saurarar voice note, congrats akai ta yi mata, daga baya kuma aka koma maganar kuɗin wayar, wanda ba ƙaramin gigita ni suka yi ba saboda yawan su da na ji.
'Wayar kawai aka siya da waɗannan maƙudan kuɗin?' Na tambayi kaina a kiɗime.
Ban kai ga samun amsa ba na ƙara cin karo da wani abun da ya ruɗa zuciyata, Maman Nasma ce ita kuma ta turo tsaleliyar mota ta ce mijinta ya siya mata a yau ɗin nan. Hannuna har rawa yake yi gurin yin zooming ɗin motar yadda zan fi ganin ta da kyau. Ko a kan titi ban taɓa ganin motar da ta tafi da imanina irinta ba. Na kwashe mintunan da ban san adadinsu ba ina aikin kallon mota da waya, sannan na haƙura ba don na gaji ba na yi musu fatan alkhairi kamar kowa. Ina ƙoƙarin fita daga group ɗin na ga Admin ta yi tagging ɗina ta ce. "Maman Sultan ke kaɗai ce ba ki siya atamfa ba fa har yanzu, ga shi lokacin abun yana ta gabatowa, kar ki rasa ɗinki fa." Wata matsananciyar kunya ce ta lulluɓe ni, lokaci ɗaya na ji gumi ya fara tsatstsafo mini kamar sabuwar ɓarauniyar da aka kama dumu-dumu tana sata, ga shi na rasa amsar da zan ba ta.
Ina nan zaune kamar an dasa dutse na ga Maman Nasmah ta ba ta amsa da faɗin. "Sorry Admin, account ɗinta ne ya samu matsala shi ya sa ba ta turo ba, ta faɗa mini da muka yi waya ɗazu. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin abin da ta ce, ko kusa tunanin faɗar hakan bai zo mini ba, to account ɗin ma ba ni da shi, ban san ya abubuwan suke ba bare na shirya maganar da za ta saka a yarda. Fita na yi daga cikin group ɗin ban ce komai ba, ina ƙoƙarin barin Whatsapp ɗin gabaɗaya na ga Maman Nasmah ta mini magana ta pc, buɗewa na yi na ga ta ce ta tura kudin atamfata, na bar shi ba sai na biya ba.
Wani irin farinciki da murna ne suka lulluɓe ni, ban san lokacin da na yi mata voice note cikin rawar jiki na dinga kwarara mata godiya ba, na manta sha'af ni ma pretending nake ni matar mai kuɗi ce kamar su, reply ɗin da ta yi mini da faɗin. "Mene abin godiya akan 15k Maman Sultan? Kamar wadda na ba wa 15 millions?" Shi ya dawo da ni cikin nutsuwata daga gigicewar murnar da na yi. Takaici ne ya lulluɓe ni na bayar da kaina da na yi, don duk wanda ya saurari voice ɗin da na yi mata zai gane ba ƙaramar ruɗewar farinciki na yi ba. Nuna mata na yi ai shi alkhairi ba ya kaɗan, don haka dole na yi murna, daga nan na kashe data ina jin zuciyata cikin yanayi biyu, na farincikin biya mini kuɗin atamfar da Maman Nasmah ta yi da kuma fargabar Allah ya sa kar abin da na yi ya sa ta gane ni matar talaka ce.
Fitowar Abban Sultan daga ɗaki ya katse mini tunanin da nake yi, ban ko motsa ba bare na nuna na san da wanzuwar shi a gurin har ya zauna a kujerar da take fuskanta ta.
"Magana na zo mu yi Hafsah." Na ji ya faɗa ba yabo fallasa.
Kai kawai na ɗaga na kalle shi ban ce komai ba. Bai damu ba don ban ga alamar hakan a fuskarsa ba ya ce. "Tun shekaran jiya nake ta son na ba ki kuɗin da kika ce za ki yi amfani da su a bikin Naja, amma ganin kin ƙi ba ni fuskar ma da za mu yi magana ya sa kawai na kira ta na ce ta tura mini account number ɗinta na tura mata kuɗin ankon sai ta bayar a kawo miki, amma sai na ji saɓanin abin da kika faɗa mini daga gare ta, ta tabbatar mini babu wani bikinta da za a yi. Hafsah me za ki yi da kuɗi da har kika zaɓi yi mini ƙarya don na ba ki? Abin da ba ki taɓa yi mini ba, me na rage ki da shi a zaman mu?" Ya ƙarashe maganar muryarsa na bayyana fusatar da ya yi da abubuwana.
Da sauri na ɗaga kai na kalle shi, wata irin kunya da takaici masu tsanani ne suka lulluɓe ni, kamar na fasa ihu saboda jin ya gano ƙarya da na yi masa. Duk yadda na so ɓoye halin da nake ciki don kar ya gane amma na kasa, haɗe rai na yi tare da ƙoƙarin yin pretending ɗin ni gaskiya na faɗa masa, ɗaga mini hannu ya yi fuskarsa ɗauke da madaukakin ɓacin ran da na jima ban gani a tattare shi ba ya ce. "Don Allah! Na haɗa ki da girman Allah ki faɗa mini Gaskiyar abin da yake damun ki Hafsah, ki faɗa mini mene matsalar da ta saka kika aro wasu sabbin halayen da ba naki ba kike aikatawa, wanda ba za su amfani rayuwarki da komai ba sai dai ma su kai ki ga hallaka? Kin canza mini kin canza wa ƴaƴanki, kin daina yi musu walwala, girki sai kin ga dama kike yi, haƙƙina kuwa an kusa sati rabon da ki ba ni, kuma da iliminki kin san hakan ba daidai ba ne, ba ki da abokin hira a kodayaushe yanzu sai wayarki, na zura miki ido na ga iya gudun ruwanki amma na ga abin naki ba na ƙare ba ne, don haka yanzu na zo masalaha nake nema, don Allah ki yi haƙuri da ko ma mene ne ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, mai cike da farinciki da ƙaunar juna." Ya ƙarashe maganar tare da matsowa daf da ni ya kama hannuna a cikin nasa ya fara murzawa, ina jin sassanyar ajiyar zuciyar da ya sauke. Ban ce komai ba sai ƙasa da na yi da kaina, bakinsa a daidai satin kunnena cikin sassanyar murya ya ce. "Please my love! Ko don su Sultan ba don ni ba." Ban san me ya ba na ji jikina ya yi wani irin yi mini sanyi ba, kai kawai na ɗaga masa don na kasa sarrafa harshena gurin furuci. Murmushi ya yi tare da rungume ni a ƙirjinsa ya ce. "Na gode sosai Ummu Sultan ɗita." A hankali na motsa leɓɓena na ce "Ni ma na gode." Ban gama rufe su ba ya ɗora bakinsa a kansu, kiran sallar isha'i ya sa ya sake ni ya tashi, har lokacin murmushi yake wanda yake bayyana tsananin farincikin da yake ciki, duk da gangar jikinsa ta daɗe da alamta mini hakan, ta hanyar yadda ya dinga sakin ajiyar zuciya da abubuwan da ya yi mini cikin rawar jiki.
"Zan je masallaci, ki yi mini tanadi kafin na dawo." Ya faɗa tare da ficewa ba tare da ya jira amsa ta ba.
Dogon numfashi na ja na sauke cikin wani irin yanayi da ban san ya zan fasalta shi ba, ina son mijina sosai so mai tsanani, kamar yadda na san bayan mahaifana babu mai so na sama da shi a duniyar nan.
Yadda ya zauna a gabana da farko cikin ɓacin rai kawai na tuno, amma cikin lokaci kaɗan ya haƙura ba tare da na ba shi haƙuri ba, ya mayar da laifin kansa duk da tarin wanda na yi masa, ya ba ni haƙuri a madadin ni na ba shi, ƙaryar da na yi masa ma da ya fahimci na ji kunya sai ya bar maganar. Anya kuwa irin mijina suna da yawa a duniya? Ba na jin akwai matar da za ta fi ni dacen miji mai kulawa da nuna tsantsar soyayya a zamanin nan, ga shi da tarin ilimin addini da aiki da shi, a kodayaushe shi mai ƙoƙarin ganin ya kyautata mana ne.
'Da ya zo a mai kuɗi da sai jin daɗi da farincikinmu ya ninka haka.' Wani sashi na zuciyata ya ce mini haka. Gyaɗa kai na yi kamar mai magana da wani na ce. "Tabbas haka ne, domin kuwa kuɗi shi ne kaso ma fi rinjaye na jin daɗin rayuwa."
Tunanin kar a ɗauke wuta ga wayata babu chaji ya sa na miƙe na soka, sannan na fita waje don yin alwala.
Ina kan darduma suka dawo shi da su Sultan, da gudu suka shigo ɗakin Sufyan ya faɗa kan cinyata yana faɗin. "Mami mun dawo." Kansa na shafa na ce. "Ka kusa karya mini cinya Babana, ko kai ba ka san ka girma ba ne yanzu?"
"Ta ina zai sani tun da kin ƙi yi masa ƙani?" Abban Sultan da ke tsaye yana kallon mu hannunsa harɗe a ƙirjinsa ya faɗi haka.
Kallon shi na yi na juya masa ido na ce. "Ai daga kai ne." Ya ce. "Ko?" Na gyaɗa masa kai kawai. Murmushinsa ya yi mai kyau bai ce komai ba.
Shi ya yi wa Sufyan wanka bayan mun ci abinci, ya kwantar da su da wuri tun kafin lokacin da suka saba kwanciya. Duk wani abu da ya kamata na yi a lokacin shi ya yi, ni dai ina zaune ina ta sana'ar tawa wato tunani.
A haka ya dawo ɗakin ya same ni, bayan ya zauna a kusa da ni ya dube ni a tsanake ya ce. "Tun ɗazu na lura da yanayinki Hafsah kamar kina cikin damuwa sakamakon abin da na faɗa miki, ko kuma kina jin kunyar abin da kika aitata. To in dai ni ne komai ya wuce, ba zan ƙara taho da maganar ba in sha Allah, ki kwantar da hankalinki ki saki jikinki mu koma kamar da, kuɗaɗen da kika tambaye ni kuma duk da ban san me za ki yi da su ba, amma na san tunda kika tambaya kina da buƙatar su, don haka da yardar Allah jibi zan ba ki 5k, sai ki yi amfanin da za ki yi da ita." Cikin farincikin samun kuɗin ɗinkin da nake ta tunanin ta yadda zan samu idan Maman Nasmah ta aiko mini da atamfar na saki ajiyar zuciya. Fuskata ɗauke da yalwataccen murmushin da na daɗe ban yi ba na ce. "Na gode sosai mijina." Yana murmushin shi ma ya ce. "Babu komai ƴar aljannatah, duk abin da kike so a duniyar nan ba zan taɓa ƙin yi miki ba matuƙar bai fi ƙarfina ba."
Daga haka muka shiga fagen da muka daɗe rabon mu da shi, sai a lokacin na gane ni ma ba ƙaramar kewar shi na yi ba. Bayan komai ya lafa ya yi bacci na ji ni ba zan iya baccin ba idan ban kunna data na ga halin da group ɗinmu yake ciki ba da abubuwan da aka tattauna, ina son group ɗin sosai, ba ma ni kaɗai ba, duk wanda yake cikinsa yana mugun son shi, saboda gida ne mai matuƙar shiga rai, kullum cikin hira muke kamar ƴan'uwan juna ba haɗuwar media ba. A hankali na zare jikina daga na Anas na sauka daga kan gadon na fita parlour na ɗauki wayata, zama na yi a kan kujera na kunna data. Messages na gani sama da goma Maman Nasmah ta yi mini, da sauri na shiga na fara dubawa. Hoton Atamfa ta turo mini ta ce ga shi har ta je gidan admin ta karɓo mun, sai kuma hotunan da suka yi a gidan admin ɗin da video. Cikin rawar jiki na buɗe na shiga kalla. Sai da zuciyata ta yi wani zillo tsabar haɗuwa da tsaruwar parlour'n da aka yi musu wani video, kusan gabaɗaya parlour'n sai da ya fito, saboda juyin da Maman Nasmah take yi da wayar tana cewa "Yau dai ga ni a gidan Aunty Billy Admin." Cikin dariya. Parlour ne wanda ya gama tsaruwa tun daga kan ginin shi da irin ƙawar da aka yi masa, da kuma kayan alatun da aka wadata shi da su, wanda kallon su kaɗai ma ya isa ya saka mutum farinciki. Wani ɗan ƙundulen abu da ya tsaya mini a maƙoshi na haɗiye tare da ɗaga kaina na bi akurkin parlourna da kallo kasancewar da akwai NEPA har lokacin, hakan ya sa na ji wani abu mai ɗaci yana yi mini yawo a ƙirji.
"Dole ne fa duk rintse duk wuya ni ma na fara rayuwa a irin waɗannan tafka-tafkan gidajen nan kusa, ko ta halin ƙaƙa." Na faɗa a fili kamar zan rusa kuka. Sauran hotunan na ci gaba da kallo, har da wanda suka yi a farfajiyar gidan, iya motocin da suke fito ta cikin hoton sun kai shida a cikin wata ƴar rumfa, ga wasu irin fitulu da suka haskaka gurin tamkar rana. Abayoyi duka a jikinsu, wanda ko ba a faɗa ba na san masu tsada ne, ga shi sun dace da jikinsu ɗan kuɓul irin na masu hannu da shin. Voice ɗinta wanda shi ne last a cikin messages ɗin da ta mun ba ƙaramin razana zuciyata ya yi ba. Idanuna na waro waje kamar zan zubar da su a ƙasa na ƙara maimaita saurara don jin ko kunnena ne bai ji mini daidai ba, amma still abin da na ji da farko shi ya ƙara mamaye masarrafar jina...✍️
*Zeey Kumurya ✍️*
[3/8, 1:36 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
6.
Gwauron numfashi na ja na sauke lokacin da nake ƙara saurarar voice ɗin a karo na uku.
"Maman Sultan ki ba ni address ɗin gidanki zan kawo miki atamfar taki da kaina." Shi ne abin da kunnuwana suke jiye mini Maman Nasmah ta faɗa. Girgiza kai na yi na ce. "Taɓ! Karen hauka ne ya cize ni da zan bari ki zo wannan akurkin gidan nawa da ko mai aikinki na san gidansu ya fi shi kyau nesa ba kusa ba." Tunanin ƙaryar da zan sharara mata kawai na fara yi. Ban kai ga yi mata reply ba na ga ta ce ko kuma na turo Driverna ko mai delivery ya karɓar mini. Ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗi, duk da hakan ma akwai yiyuwar asirina ya iya tonuwa, tunda ban da Driver bare wani mai delivery.
Reply na yi mata da duk yadda ta yi daidai ne. Ta ce tom shikenan na turo address ɗin nawa kawai ta ba wa drivernta ya kawo mini. Citson yatsa na yi na fara tunanin ƙaryar da zan shirga mata.
'Ki ba ta address ɗin gidan Shamsiyya kawai, sai ta tura drivern nata can a matsayin nan ne gidanki.' Wani sashe na zuciyata ya ba ni wannan shawarar. Murmushi na yi tare da haɗe yatsuna biyu na ɗana na ce. "Yes!" Saboda Gidan Shamsiyya babba ne sosai shi ma, duk da a yanda nake hasashen gidajen ƴan group ɗinmu ba zai kai su ba, amma babu laifi, ya fi dai wannan akurkin namu.
Jikina na mazari saboda kar Maman Nasmah ta ga na daɗe ban yi mata reply ba na yi searching numbern Shamsiyya na tambaye ta tana gida gobe? Idan tana nan zan zo. Na yi sa'a tana online, kuma ina yi mata message ta ba ni amsa da. "Ayya ba na nan, mun yi tafiya Dubai da baban su Zuhura." Tagumi na yi cikin rashin jin daɗi na yi musu fatan dawowa lafiya, a raina na ce. 'Ku kuka yi auren jin daɗi Shamsiyya, mazajenku kullum cikin ɗaukar ku, ku tafi yawon shaƙatawa ƙasashen waje suke, mu kuwa namu ƙauye ma idan za a je a ga dangi sai an yi wata ana shirye-shirye da tara ɗan kuɗin mota. Saboda rashin zuciya, kowa yana fita ya nemi kuɗaɗe masu yawa amma ban da irin mazajenmu, da ba sa burin yin tarin arziƙin da za su zama hamshaƙai, sai dai ɗan wanda za a ci abinci a kwanta a makwanci duk munin shi da rashin kyan shi.' Tsaki na ja na koma chat ɗin Maman Nasmah na ce mata ba na nan mun yi tafiya Abuja sai jibi za mu dawo, amma zan ba ta address ɗin gidansu mai aikina ta aika akai a atamfar can, idan ɗan aiken ya je ya tura yaro ya ce ga shi a ba wa Salamatu. Na tura mata da address ɗin gidana a matsayin nan ne gidansu mai aikina. Ta ce tom shikenan babu damuwa. Kamar an sauke mini wani dutse mai nauyi da ya danne mini ƙirjina haka na ji, ganin na samun mafita, don haka kawai ba za ta zo ta ga gidana ta raina ni ba, in sha Allah sai mun koma tsamfatsetsen gida irin nasu kafin wata a group ɗin ta ƙara buƙatar zuwa gidana, saboda ba wannan ne karon farko da aka buƙata ba tunda na ce ni ma ƴar Kano ce.
Mun ci gaba da chatting da Maman Nasmah, ta ce na tura mata numbern mai aikin tawa, kar drivern nata ya kasa gane kwatancen, idan ya kakare sai ya kira ta. Ƙaryar ba ta da waya na yi mata. Emogin mamaki ta tura mini tare da faɗin. "Haba Hajiya Hafsah, kamar ke a ce mai aikinki ba ta da waya? Gaskiya ki siya mata." Murmushin yaƙe na yi kamar tana gabana ta ce. "Na siya mata fa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba tana siyarwa, kin san halin mutane marasa ƙarfi, da sun ji rashi ko mene nasu ɗauka suke su siyar." Ta ce. "Haka ne, amma dai ki ƙara siya mata ko don irin haka." Na ce. "in sha Allah, kawai da ma na bari ta ɗan jigatu ne saboda kar ta kuma siyarwa."
Daga nan muka shiga hirar taron da za mu yi, ta tutturo mini agogo, ɗanƙareriyar sarƙa da ɗan'kunne na gold, haɗaɗɗen takalmi da rantsatstsiyar jakar da ta siya duka sababbi saboda taron ta ce ni ma na siya irinsu, mu yi komai iri ɗaya ranar. Jiya mijinta ya ba ta kuɗin ita ma duk ta siya. Tsam na yi a zaune ina rarraba ido, don na san ko gidan da muke zaune zan siyar kuɗinsa ba zai sai mini wannan kayan ba. Jikina a saɓule na ce mata zan siya in sha Allah, ba ta jira na tambaye ta ba ta turo mini price ɗin kowane. Kusan rikitowa na yi daga kan kujerar da nake kai saboda yawan kuɗin da na lissafa. Millions kusan biyar, a iya kayan sakawar rana ɗaya kawai. "Wanda ya ba da wannan kuɗin wanne irin kuɗi ne da shi, shi kuwa? Me yake yi yake samun kuɗi da Anas ba zai iya yi ba?" Na tambayi kaina a ruɗe. Zuciyata ce ta ba ni amsa da 'Rashin zuciya ne ya hana shi mana.' Dungurar da wayata na yi ina jin kamar na haushi bango tsabar takaicin irin mijin da na aura talaka. Da na san haka masu kuɗi suke hutawa da unguwar masu kuɗi nai ta zuwa da ina budurwa, da wani mai kuɗin ne zai gan ni ya aure, ni ma na yi rayuwar hutu da jin daɗi da kwanciyar hankali, na saka abin da nake so na ci wanda nake so a duk lokacin da na so. Dukan kaina na yi ina jin kamar na fashe da kuka. Miƙewa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 24