ne." Ya ce. "Amin Ummu Hafsah." Don kamar yadda ya yi alƙawari tun suna tare da Hafsah in dai ta haifi mace ita zai yi wa takwara, bai canza ra'ayi ba har yanzu.
A nan gidan na yi sallar magariba na ɗan ci abinci bisa takurawar Naja, don Alhamdulillah maganganun Anas ba ƙaramin sanyaya mini rai suka yi ba, na samu relief sosai da kwanciyar hankali. Ta raka ni na zazzaga na ga gidan, ma sha Allah ya yi kyau sosai, ya fi wanda muka zauna a ciki komai da komai, don shi kowane ɗaki da toilet, kuma ginin ya fi wancan zamanantaka, ga shi ita ma Najan an yi mata kaya sosai da suka ƙara ƙawata gidan. Nai ta santi a cikin raina. Da su Sultan na koma gida, ban ɓoye wa Kawu komai ba na faɗa masa abubuwan da suka faru waɗanda na yi wa Anas na rashin kyautawa. Nasiha sosai ya ƙara yi mini tare da faɗa, ya ce da ma da walakin goro a miya Anas ya shafe wannan tsawon lokacin bai zo ya gaishe shi ba. Ya ji daɗin ganin su Sultan sosai yay ta nan nan da su.
Na ɗauka zan iya dangana da auren Naja da Anas ya yi, amma da na zo bacci sai abun ya yi ta dawo mini a rai, na kasa bacci, na dinga tunanin duk wannan kulawar da soyayyar yanzu ta koma kan wata ba ni ba, duk abin da yake mun yanzu ita ma haka zai yi mata? Na yi nadama mara iyaka, na ji aure da duk wani ɗa namiji sun fice mini gabaɗaya daga rai, tunda wanda nake da yaƙini a kansa ya yi mini nisa.
Haka rayuwa ta ci gaba da garawa da ni, yau fari gobe baƙi, inda na ɗan samu sauƙi na fara sana'a, hada-hadarta sai yake ɗauke mini hankali daga yawan tunane-tunane, da kuma fara samun lafiyar Kawu, don an haɗa shi da wani mai magani kuma ana samun ci gaba sosai da sosai. Duk weekend Anas yake Kawu su Sultan su kwanar mini biyu. Ranar ina zaune aka aiko ana sallama da ni, ina fita na ga Sani duk ya fice daga hayyacinsa, wai ya zo a mayar da aurenmu, ko tanka masa ban yi ba na koma gida duk da jama'ar da yake ƙoƙarin tara mini saboda magiya. Da na kira Binta cousin ɗinsa na sanar mata sai take ce mini ai ya ƙara aure bayan rabuwarmu, ya auro ƴar hau dangin bala'i, tana nan ta zame musu alaƙaƙai, ita take juya su tun daga kan mahaifiyar tasa har shi da ƙannensa, duk bautar da na yi wa Hajiya to yanzu ita take yi wa matar, don ana zargin asiri ta yi musu duka ta mallake su, saboda uwar biyayyar da suke mata daga gani ba a banza ba, wasu kuma suke cewa haƙƙin matan da ya zalunta ne, don hatta kuɗi ita yake kawowa da ya ciro daga banki, sai abin ya ta gama ta yaga ta ba shi, shi ne rabonsa. Na dinga mamaki ina cewa da ma akwai matar da za ta iya juya Sani da Hajiya duk uban mulkinta?
A bakin Maman Humairah nake jin group ɗinmu ya tarwatse, bayan an yi faɗa kaca-kaca, wai mijin wata yana soyayya da wata bazarawa a group ɗin, wasu kuma sun yi munafurci ya fasu, aka dinga tone-tonen asiri da bankaɗen-bankaɗen sirrin juna. Na ce Allah ya kyauta, su ƙarata su kaɗai, don ni na tabbata babu wanda group ɗin nan ya yi wa illa kama ta, ya janyo mini asara da haifar mini da ciwon da ban san ranar warkewar shi ba.
Muna zumunci sosai da Naja, duk da na so ja baya da ita saboda ba ƙaramin kishi da raɗaɗi nake ji a cikin raina ba idan na lalle ta na tuna mijina take aure. Ita kuwa baiwar Allah kullum cikin kwantar mini da hankali take, tare da nanata Alƙawarin Anas na cewa zai mayar da ni idan Ubangiji ya yalwata shi. Zan so hakan kuma zan fi kowa farinciki idan ya kasance, amma ina tunanin yadda za mu yi rayuwa da ita a matsayin kishiyoyi. A duk lokacin da muka haɗu na kalle ta sai na ƙara tabbatarwa da kaina na YI WA KAINA da rayuwata babbar cuta, saboda da an ga ta an ga wadda take rayuwa cikin kwanciyar hankali da rufin asiri, duk da ban sani ba ko zan koma gidan tsohon mijin nawa kamar yadda take faɗa mini ya alƙawarta zai mayar da ni da zarar ya samu sarari, ni dai kawai na bar wa Allah zaɓi, duk abin da ya zaɓa mini shi ne mafi alkhairi a gare ni, kuma zan karɓe shi hannu bibbiyu..........✍️
_*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH! komai ya yi farko yana da ƙarshe, na gode sosai masoyana da kuka yi jimurin bibiyata, abin da na rubuta daidai Allah ya haɗa mu a ladan, wanda na yi kuskure kuma ya yafe mana bakiɗaya. BRIGHT PENS na godiya sosai da sosai, da fatan za ku jiraye mu a second batch.*_
*Ƙofa a buɗe take ga masu gyara, sharhi ko ƙorafi. 09047871750.*
_*Zeey Kumurya*_✍️
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 24