shi abin da yake ƙara ɗaure masa kai rashin sanin dalilin da ya sa take masa hakan, a iya sanin shi bai san ya yi mata wani laifin ba, bare ya ce ko shi ne dalili. A ɗazu bayan ya koma gurin aiki yay ta tunane-tunane, shi mutum ne da ba ya son zargi ko ƙala wa mutum abin da ba shi da tabbas a kan shi. Hakan ya sa ya ƙi alaƙanta abubuwan Hafsah da matar da ya gani ɗazu, duk da wani sashe na zuciyarsa yana ta faɗa masa wataƙila ya na da nasaba da hakan, ya dinga tambayar kansa wacce mata ce ita da har Hafsah take kunyar ta gan shi a matsayin mijinta. Numfashi ya sauke cikin rashin sanin abun yi, makamancin haka bai taɓa faruwa a tsakaninsu da Hafsah ba tunda suka yi aure, shi ya sa abin ya dame shi matuƙa, ya rasa tudun da zai dafa wanda zai taimaka masa ya gano hasken da zai fitar da shi daga duhun da yake ciki. Yana son matarsa so mai tsanani, ba ya son abin da zai shiga tsakaninsu ko yaya yake. A parlour'n ya goce ya kwanta, don so yake ya ga iya gudun ruwan Hafsah.
Duk yadda na so yau ba zan kunna wayata gabaɗaya ba amma na kasa, wajen tara da mintuna na ɗauko na kunna cikin dokawar zuci. Bayan na kunna data direct Whatsapp na shiga na duba group ɗinmu. Duk yawan messages ɗin da na tarar sai da na bi ɗaya bayan ɗaya na ga babu inda aka yi maganata, kuma da Maman Nasmah aka sha duk hirar da aka yi. Ƙaƙƙafar ajiyar zuciya na sauke, don ni duk a tunanina za ta faɗa musu ta zo gidana ta ga ni matar talaka ce. Fita na yi ba tare da na ce ƙala ba, duk da na gagga an yi cikiyata.
Ta private na ga Maman Nasmah ta mini saƙo har uku, cikin faɗuwar gaba na buɗe. Na ga ta ce. Ta kikkira ni a kashe, da fatan lafiya. Na ce mata lafiya ƙalau. Ina mamakin yadda kodayaushe tana online, ko dan su ƴan gata ne komai sai dai a yi musu? Ba kamar mu da muke wuni cikin wahalar ayyukan gida ba. Ta mun reply da. 'Masha Allah.' Danne zuciyata na yi na ce mata da fatan ta je gida lafiya? Ba ta ba ni amsa ba, sai ta kira ni. Na ɗaga cikin mutuwar jiki, ji na nake kamar wadda ta yi wa Sarki ƙarya aka kama ta. Sallama ta mun na amsa Idanuna cike da hawaye.
"Allah ya sa ba kya tare da baban Sultan na kira ki da daddare."
Na ce. "Eh ba ma tare." Ta ce. "Har Salamatu ta faɗa miki na kai mata atamfar kenan? Don ni tun kafin na ƙarasa gidan nata nake kiran wayarki a kashe, ko tana da wani layin naki ne?" Maimakon na yi murna Maman Nasmah ba ta gane ni ce ba sai na ji saɓanin haka, wato tsabar a mawuyacin halin da ta gan ni da mai aiki na yi mata kama? Cikin danne kukan da ya taho mini na ce. "Ai ni kika tarar ba Salamatu ba." Ban san me ya sa na ji na zaɓi kawai na faɗa mata gaskiya ba. Kamar za ta fasa mini dodon kunne saboda ƙaraji na ji ta ce. "What? Ke kuma Namecy? Ke ce wannan matar duk a yagule a wahale?" Hawaye na zuba daga idona na ce. "Ni ce."
"Taɓ! Amma gaskiya jin ki ya fi ganin ki, muryarki mai daɗi da sanyi babu wanda zai yi tunanin a wannan gidan kike rayuwa gaskiya, I'm sorry idan kin ji babu daɗi, mamaki ne ya kusa kashe ni."
"Babu komai, shi ya sa na kasa bayyana muku wace ce ni saboda kar a raina ni." Na faɗi haka cikin son wanke kaina.
Ta ce. "Kin yi farar dabara kam, don aka gane haka kike ba ƙaramar wulaƙantacciya za a mayar da ke ba, Allah ya taimake ki mun haɗu kafin ranar taro." Na ce. "Taimakon me? Ai yadda kika gan ni su ma haka za su gan ni ranar." Ta ce. "Haba, never kina da ni ki je a haka, zan aiko miki mayukan shafawa masu tsada wanda za su gyara miki fata kafin ranar, da turaruka da sabulan wanka, da jaka da mayafi da takalmin da za ki saka ranar, ke har da sarƙa da ɗan'kunne gold da kuɗin da za ki yi liƙi a gurin. Kina da ni ai ba za ki taɓa kunyata ba ƙawata." Wani tsalle na doka daga zaunen da nake ina jin kamar an yaye mini duka damuwata na ce. "Gold fa kika ce?" Ta ce. "To mene ne a ciki? Me aka yi aka yi wani gold? Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki tawan, har gurin makeup zan kai ki a yi miki." A rikice na ce. "Wayyo daɗi, kamar kuwa kin san tunda aka fara maganar taron nan tunanin yadda zan yi na fito fes kawai nake yi, na god..."
"Babu godiya a tsakaninmu ai Namesy, kin fi ƙarfin komai a gurina, da kin faɗa mini ma tun da ai da ba wannan zancen ake ba, wani tunani ne ma ya faɗo mini yanzu a rai, kawai zan haɗa ki da mai mun gyaran jiki ta yi miki na amare na sati ɗaya, yadda za ki fi yin kyau da sheƙi ranar taron, har ƙunshi ma za ta yi miki." Ƙasa jurewa na yi na tashi da wayar ƙare a kunnena na fara taka rawar murna, da na san haka Maman Nasmah take da kirki kuma take so na da tuni ba na faɗa mata gaskiya ba. Tsabar farinciki rasa abin cewa na yi. Sai da ta ce ko ba na jin ta sannan cikin dariya na ce. "Farinciki ne ya hana ni magana." Ta ce. "To za ki je gyaran jikin na kira ta yanzu na sanar mata?" Na ce. "Me zai hana? Ubangiji ya so ni da rahama na butulce." Ta ce. "Okay, amma tun safe sai dare za ki koma gida fa." Da sauri na ce. "Kai! Duka satin kuma?" Ta ce. "Eh, mene a ciki?" Na ce. "Baban Sultan ne da ƙyar ya yarda gaskiya." Ta ce. "Saboda ba ya son ci gabanki? Bai ba ki kuɗi kin yi ba kuma za ki yi ya hana ki? Idan kika yi kyan ai shi ma zai ji daɗi, ki ce masa gyaran jiki ne ba wani abu ba." Na ce. "Duk da haka, da ƙyar ya bari, na san halin shi, zai ce ga yara ga kula da gida ba zan fita na wuni a waje ba." Ta ce. "Caɓdijan! Gaskiya matan talakawa kuna ƙoƙari, ko da yake da ma an ce talaka akwai baƙar zuciya da mugunta. Ni mijina duk inda na ce masa zan je ba ya hana ni, kuma ya ba ni kuɗin da zan yi amfani da shi ko nawa ne. Sorry sis, amma kuna ƙoƙari fa, ga talauci ga mulkin mallaka." Numfashi na sauke kamar zan yi kuka na ce. "Hmmm, to ya za mu yi?" Ta ce. "Ai ni ba zan iya ba, kuma ku ma har da laifinku, ku kuke nuna musu lako-lako tun farko, miji ba wata uwar yake muku ba, amma ku yi ta yi musu biyayya, yanzun dai duk yadda za ki yi ki samu ki je gyaran jikin nan gaskiya, idan ba haka ba ranar taro ki tashi kamar almajira a cikinmu, idan kuma ki ka ƙi zuwa kowa zai gano ki, saboda da ma ana ta complain kwana biyu kin ja baya a group, ni kankaro miki mutunci nake son yi. Da safe zan faɗa miki yadda muka yi da mai gyaran jikin na tura miki address ɗinta." Daga haka muka yi sallama ta katse wayar.
Tagumi na rafka ina bitar maganganun Maman Nasmah, musamman na ƙarshe. Wato mu matan talakawa mu ne a wahale? Mu mazaje suke takurawa, su kuwa komai suke so barin su ake yi su yi, ga kuma rayuwar ƴanci da wadata. Na san Anas da bala'in kulle, abu in ba na dole ko na dangi ba bai fiya bari na zuwa ba, ya fi son duk inda za ni mu je tare saboda kishin tsiya, shi ya sa nake ta tunanin ta yadda zan faɗa masa zuwa wannan taron namu, ga kuma gyaran jiki da ya kunno kai, amma dai zan fara tambayar shi na ji abin da zai ce, idan ya hana ni na yi ficewa ta, don gaskiya Maman Nasmah ta faɗa, mu muke yi musu lako-lako, shi ya sa suke mana yadda suka so.
A ɓangaren Maman Nasmah kuwa murmushi ta yi ganin cikin sauƙi ta fara samun nasara, za ta ƙara jan Hafsah a jikinta ta nuna mata ita mai ƙaunar ta ce tsakani da Allah, tare da yi mata tarin alkhairi wanda zai saka ta ƙara sakin jiki da ita. A hankali a hankali tai ta bugar cikinta tana faɗa mata abubuwan da Anas yake so da wanda ba ya so, ta tunzura ta, ta yi masa wanda ba ya so ta hana ta yin wanda yake so. Tunda a iya wayar suka yi yau ta lura ƙaramar ƙwaƙwalwa ce da ita, ban da haka ta yaya don ta ce mata ta gan ta a yagule a wahalce za ta yarda? Ai ko makaho ya shafa su ita da ƴaƴanta zai gane babu wahala a tattare da su, don babu yadda za a yi a ga Hafsah a ce a gidanta take rayuwa. Ana ganin ta an ga mai rayuwa cikin rufin asiri, kuma babu inda za ta shiga a raina ta, don daga gani mijinta yana da kula, ba sa tare da yunwa ko rashi na daidai ƙarfinsu. Amma ita saboda kidahuma ce ba ta fuskanci hakan ba, don haka za ta yi amfani da son kuɗin da dogon burinta ta cimma nata burin........✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:38 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
9.
Washegari na tashi cikin tsananin farinciki mara misaltuwa, ni kaɗai na dinga sakin murmushi ina imagining rawa da murnar da zan yi idan saƙon da Maman Nasmah ta ce za ta kawo mini ya ƙaraso. Ga ni nake kamar a mafarki, idan na tuna wai har da sarƙar gold za ta haɗo mun, sarƙa fa? Ba ma ɗan'kunne ko zobe ba. Gaskiya watan arziƙina ne ya tsaya. Na dinga kallon kaina ina hasaso ni sanye da ɗanƙareriyar sarƙa tana zuba walwali.
Ƙarfe bakwai na safe na ga ta mun text na address ɗin gidan mai gyaran jikin, ta ce na je ƙarfe tara tana jira na. Cikin zumuɗi na koma parlour inda Anas yake shirya su Sultan na zauna a kan kujera, fuskata ba yabo ba fallasa na ce. "Abban Sultan zan fara zuwa gyaran jiki yau, na ga fatata duk ta yanƙwane." Kallo na ya yi cikin mamaki sannan ya ce wa Sultan. "Ɗauki abincin naku ku je ɗakinku ku ci." Suka amsa tare ɗauka suka fice suna satar kallo na. Anas ya maido da hankalinsa gare ni tare da faɗin. "Ina jin ki, ban gane me kike nufi ba?" Kaina tsaye na ce. "Cewa na yi zan je gyaran jiki anjima, za a yi mini na sati ɗaya." Cikin rashin fahimta ya ce. "Wai wanne irin gyaran jiki? Da ma kina zuwa ne ban sani ba? Har yanzu ban fahimce ki ba Hafsah?" Cikin hasala na ce. "Da Hausa fa nake yi maka maganar nan, gyaran jiki dai wanda ake yi wa mata su yi kyau fatarsu tai ta sheƙi da fitar da ƙamshi, da kake tambaya kuma da ina yi, ba na yi, yanzu zan fara." Wani kallo da ban taɓa ganin ya yi mini irinsa ba ya wurga mini tare da faɗin. "Shi ne kuma sai a yau ɗin za ki je za ki faɗa mun? To ban shirya ba gaskiya." Tsaki na ja a cikin raina na ce. 'Sarkin tsiya aminin talauci, to ba cewa zan yi ka ba ni kuɗin ba.'
"Ba kai za ka biya ba ai, ni zan biya da kaina." Na faɗi haka ina huhhura hanci.
"A ina kika samu kuɗin?"
"Allah ne ya ba ni."
"To ba za ki je ba." Ya faɗa a fusace tare miƙewa ya bar mini parlour'n.
Da wani matsiyacin kallo na raka shi, ƙwafa na ja na miƙe kamar zan kifa na ɗauko wayata na kira Maman Nasmah, ringing biyu ta ɗaga, muryarta da alamun bacci ta ce. "Kin ga saƙona kenan?" Na ce. "Eh, ki yi haƙuri na tashe ki a bacci." Ta ce. "Ba komai, Kin tambayi mijin naki?" Na ce. "Hmm." Tare da faɗa mata duk yadda muka yi da shi. Cikin kwakwazo ta ce. "Wannan miji naki ba dai baƙar zuciya ba wallahi, ni fa tunda na gan shi yana yi miki wani murmushin gefen baki na san mugu ne, ban da haka mene na hana ki wani fita?" Kamar zan yi kuka na ce. "Kulle ne da shi da ma, ko bayani ban gama yi masa ba ya tashi ya bar ni, in dai ba tare za mu fita ba bai fiya bari na fita ba, wai shi kishi."
"Kin gani ba, muguntar kenan ai, shi yana fita yana watayawa kullum amma ke yana barin ki a gida a dunkume, saboda kar ki fita ki....." Jin motsin shi na yi saurin katse da faɗin. "Ina zuwa, ga shi nan." Ban jira amsar ta ba na datse kiran.
Murmushin mugunta Maman Nasmah ta yi ta ce. "Jaka, haka zan ta zura ki na kai ki na baro, miji irin naki ai abin so ne, mai kishin iyalinsa da tsare mutuncinsu, ban da mahaukaciya ce ke da ma wanne mijin arziƙi ne za ka ce masa za ka fara fita wani gyaran jiki rana tsaka ya bar ka? In sha Allahu kafin taron nan sai na yi sanadin da zai miki ko saki ɗaya ne, daga nan na fara plan B ɗina." Ta lumshe idonta tare da rungume pillown da yake ƙirjinta, wani irin son Anas sabo na fizgar ta, mutumin da ko sunansa ba ta sani ba, amma soyayyar shi ta mata mugun gamu, saboda yadda tunaninsa ya addabe ta ko lokacin yin wasu abubuwan ba ta samu yi ba a daren jiya, raba dare ta yi tana ta juyi a gado tare da hasaso irin soyayyar da take fatan su yi. Tana ganin ɗaya daga cikin mazan da take hulɗa su yana ta kiran ta amma ta ƙi ɗagawa, domin daga lokacin da ta yi tozali da Anas duk mazan duniya suka koma mata tamkar mata ƴan'uwanta, shi kaɗai take gani a Namiji. Fatanta kawai Allah ya sa mijinta ya dawo a cikin satin nan, ta rura masa wuta ya ba ta takardarta, ta yi ta yi ta gama iddarta a ɗaura mata aure da masoyinta. Komai take yi fuskarsa kawai take gani a cikin idanuwanta da murmushin da yake yi wa Hafsah. Numfashi ta sauke tare da mirginawa tana murmushi ta ce. "Ina son ka sosai mijin Hafsah Maman Sultan a yanzu, nan gaba kaɗan kuma mijin Hafsat Maman kyawawan ƴaƴan da za ta haifa maka masu kama da kai."
Ido na bi shi da shi bayan ya shigo ɗakin, cikin tsoron ko ya ji wayar da nake yi, don babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da wani abu ya faru a tsakaninmu na faɗa wa wani, mutum ne shi mai son sirri sosai. Shi ya sa tun da muke da shi bai taɓa kai ƙara ta gida ba da sunan na yi masa wani laifin. Yana cire jallabiyar jikinsa na ƙarasa kusa da shi fuska a murtuke na ce. "Wai don Allah Anas me ya sa kake mun irin wannan abubuwan ne? Akan me za ka hana ni zuwa gyaran jikin nan?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Saboda na isa." Kallon sama da ƙasa na yi masa na ce. "Yanzu kai ba abin jin daɗinka ba ne zan je a gyara ni?" Ya ce. "Ba shi ne damuwata ba, inda kika samo kuɗin zuwan nake son sani." A wulaƙance na ce. "Oh, saboda ga ƴar matsiyata dangin matalauta ko? Wadda wani nawa ba zai iya ba ni kuɗi ba." Kallon takaici kawai ya mun ya juya ya fita, na bi shi da harara. Kiran Maman Nasmah na ƙara yi na faɗa mata komai. Cikin faɗa ta ce. "Wai wannan mijin naki shi ne autan maza ne da kike ta lallaɓa shi haka? Maman Sultan kar dai ki ce mini ke ma mata kika rako duniya?" Na ce. "Ban gane ba?" Ta ce. "Ai ba za ki gane ba, ni kawai ki faɗa mini idan gyaran jikin ne ba kya so na saka ta dawo mini da kuɗina." Cikin rawar baki na ce. "Wallahi ina so, kawai ban san fita ba da izninsa ba ne." Ta ce. "To sannu doluwa, idan akan maganar kuɗi ne ki ce masa ƙawarki ce kuka haɗu a social media ta ba ki, ba shikenan ba ya ji abin da yake so?" Shiru na yi, don na san hakan ma wata sabuwar fitinar ce. Fahimtar hakan ya sa Maman Nasmah ta ce. "Ko me zai yi ki faɗa masa haka, don maza ba a yi musu lako-lako, ni ban ma taɓa ganin mace mai tsoron miji irinki ba ko a labari, ko a cikin group ɗinmu ai za ki ga kowacce tana faɗa watayawarta take yi son ranta a gidanta, ke kaɗai ce fa kike cikin wannan rayuwar ƙuncin, ki zage ki ƙwatarwa kanki ƴanci, idan ba haka ba taron ma hana ki zuwa zai yi. Don haka duk abin da zai ce ki yi ficewarki, kar ki raga masa, ba a raga wa maza yanzu ko kaɗan." Cikin rashin mafita na ce "Toh shikenan." Daga haka muka yi sallama. Zama na yi ina bitar maganganun Maman Nasmah, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, su da mazajensu ma suke hamshaƙan masu kuɗi ba sa tsoron su sai ni matar talaka. Yanda matan group ɗinmu suke watayawarsu abin ba ƙaramin burge ni yake ba, sai na ji suna cewa duk inda suke so zuwa suke. Don haka ni ma daga yanzu na ɗaura ɗamarar yin duk abin da na ga dama, na daina shayin Anas, bari ya dawo daga kai su Sultan school, zan nuna masa wargi ce ni daidai ƙugunsa. Da wannan tunanin na tashi na fara shirin tafiya gidan mai gyaran jikin. Har na sha tea ɗin da ya tafasa da bread na yi wanka bai dawo ba. Ina cikin shiryawa ya shigo, sai da kammala komai na ɗauki jakata da mayafi na nufi ƙofa fuskata a murtuke, ba tare na ce masa ƙala ba.
"Babu inda za ki je fa wallahi Hafsah." Ya faɗa yana tare hanya. A haƙiƙance na ce. "Wai saboda me? Idan kuɗin ne dole sai ka ji wa ya ba ni to ƙawata ce da ta zo jiya." Yana ƙara babbake hanya ya ce. "A ina take? Mene ne alaƙarki da ita?" Kaina tsaye na ce. "A group na Whatsapp muka haɗu." Cikin matsanancin ɓacin rai ya ce. "Ban san ta ba, ban san irinta ba, ban san wace ce ita ba, ba zai yiwu haka kawai ta ɗauki kuɗi ta ba ki ni kuma na bar ki, ki yi amfani da shi ba, don haka ki mayar mata da abinta!" A zazafe na mayar masa da raddi da faɗin. "Wallahi ba zan mayar ba, kai ba ka ba ni ba, ita da yake mijinta mai zuciya ne da son faranta wa iyalinsa ya ba ta har ta sammun a ciki sannan kuma ka ce na mayar saboda mutunta? Su mazansu ga kuɗi ga ba matsi, sai kai talaka ne za ka hana ni rawar gaban hantsi? To wallahi bari ka ji Anas, ban ga abin da zai hana ni zuwa gyaran jikin nan ba, saboda taro za mu yi a group ɗinmu, kowacce mijinta ya ba ta kuɗi don ta fito fes sai ni ce zan tafi a duƙun-duƙun? To ba zai yiwu ba." Na ƙarashe maganar kamar zan kai masa duka, zugar Maman Nasmah na ƙara tunzura ni na ci gaba da faffaɗa masa maganganu ya gane ba na tsoron shi a yanzu, amma na danne na ƙyale shi haka ba don halin shi ba. Tsananin mamaki da al'ajabi su suka saka Anas sandarewa a tsaye, ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi, hakan ya ba ni damar raɓawa ta gefen shi na fice. Na kai tsakiyar tsakar gida na ji muryarsa cikin matsanancin ɓacin ran da ban taɓa jin shi a cikinsa ba, don muryarsa har rawa take yana faɗin. "Wallahi! Wallahi! Wallahi idan kika ɗaga ƙafa kika fita daga gidan nan a bakin aurenki!".......✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:38 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
10.
Cak na tsaya kamar an kafe ni, don furucin a bakin aurenki da ya yi ba ƙaramin dukan zuciyata ya yi ba. Kamar na koma na fasa fitar, amma sai na ji ba zan iya ba, hakan ya sa kawai na ci gaba da tafiyata ba tare da na waiga ba, duk da na ji motsin fitowarsa tsakar gidan. Idan akwai abin da nake da tabbaci cikakke a kansa to shi ne son da Anas yake mini, na san ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba, wannan maganar tasa ma ya yi ta ne kawai a matsayin hargagi, amma na san ba har cikin zuciyarsa take ba. Idan ma har cikin ran nasa ne matsalar shi ce ba tawa ba, don kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa idan ina nuna ba na tsoron shi sai ya fi shayi na.
Na shafe kusan mintuna talatin kafin na ƙarasa gidan mai gyaran jikin saboda akwai nisa daga unguwarmu, ina zuwa babu ɓata lokaci ta fara gudanar da aikinta, ta na yi tana ba ni labarin kuɗin Maman Nasmah da na mijinta, don akan wannan gyaran jikin nawa ma sai da ta ninka mata kuɗin sau uku akan yadda take yi. Sai na ji ina ma ni ce ake labarin kuɗina da na mijina, na dinga addu'ar Allah ya nuna mini ranar ni ma zan zama irin haka, a dinga labarina da kwatance da ni. Sai yamma lis na baro gidan, matar tana ta yabon kyan fatata, ni kuwa gani nake murnar kuɗin da aka ba ta ne kawai ya sa take ta koɗa ni, babu wani kyan fata da nake da shi kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa.
Yau Anas ko fita bai yi ba, takaici da mamakin Hafsah sun saka ya zauna yay ta tunane-tunane, hakan ya haifar masa da ciwon kai. Bai taɓa zaton zai ce wa Hafsah idan ta yi abu a bakin aurenta za ta aikata ba. Shi ya dafa musu abincin rana ya yi sauran aikace-aikacen gidan.
Sai bayan Magriba na koma gida, na tarar ba ya nan sai su Sultan kaɗai a parlour suna homework. Da gudu suka taso suka rungume ni, Sufyan ya ce. "Mami ina kika je? Muna ta neman ki, kin tafi kin bar mu." Kayan hannuna wanda Maman Nasmah ta aiko mini da shi na ajiye a kan kujera na ce. "Unguwa na je, ku ƙarasa aikin naku na ba ku kayan daɗi." Da murna ya koma ya ci gaba. Sultan ya ce. "Mami na zubo miki abinci? Abba ya dafa mana macaroni." Na ce. "To bari na shiga na ajiye kayan nan na fito." Sufyan ya ce. "Za ki biya mana karatu yau ko Mami? Idan mun iya ki yi mana tatsuniya irin na ranar nan." Na ce. "To." Kawai.
Sai da na yi Sallah sannan na baje kayan na dudduba, duk abin da ta lissafa za ta ba ni babu wanda ta manta ba ta sako ba, har da kuɗi 30k wai na transport zuwa gidan gyaran jiki, kuma ta ce gobe na tafi da atamfata za ta aiko a karɓa akai mini ɗinki. Ina ɗaga sarƙar gold ɗin da na shafe mintuna ina lailaya ta na ce. "Allah ka saka wa wannan mata da alkhairi, ka ba ni ikon faranta mata kamar yadda ta faranta mini a yau." Kamar zan zauce haka nake ji tsabar farinciki, na ƙara tabbatarwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 24