ce. "To." A shaƙe.
Ina gungunin daga zuwa na za a fara takura mini na tashi na fitar tsakar gidan da ya yi buɗuɗu da ƙura da ledodi. Da ma kafin na yi aure ni nake komai na gidan, saboda Gwaggo irin matan nan ne masu mugun son jiki, ba ta son motsa jikinta ko kaɗan, ta fi son kullum tai ta jibgewa kamar kayan wanki.
Ina toshe hanci saboda ƙura na share tsakar gidan da wata ficiciyar tsintsiya da ta sagar mini da hannu. Bayan na gama na wanke toilet, masan gargajiya ce kuma ta cika ta yi hani'an kamar kashin ciki zai fara malala, ga shi a buɗe take fayau babu ko ɗan murfi. Ina gamawa na dinga kwara amai, saboda ƙyanƙyami da uban warin da na shaƙa. Kallo na kawai Gwaggo take ta na taɓe baki, ba sannu bare na gode. A ranar na ce wa Kawu a samo masu kwasar masai su kwashe zan biya, don ba zan iya rayuwa da wannan toilet ɗin ba. Ya dinga saka mini albarka tare da tarin addu'oi. Saboda kullum da takaicin lalacewar banɗakin yake kwana yake tashi, ba shi da halin gyarawa ne kawai ya saka bai gyara tuntuni ba. Amma sai da ya tambaye ni ina na samu kuɗin? Bayan na ce har abinci Anas daina ba ni ya yi. Ƙarya na yi masa na ce wani abu na siyar a cikin kayan ɗakina, sai jiya aka kawo mun kuɗin na taho da shi. Washegari da safe na je na kwaso barguna da zanin gado saboda shimfiɗa, don ba zan iya kwanan kan tabarma zalla ba. Daga yadda na ga gidan na gane bai dawo ba tun fitar da ya yi, tabbacin ƙauyen ya tafi kenan.
Haka rayuwa ta ci gaba da garawa, kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan Kawu saboda Gwaggo, ga shi komai ni nake yi da kuɗina, hakan ya sa duk kuɗaɗen hannuna suka ƙare karaf.
Yau da safe bayan na gama duka aikin gidan da tulliƙar wankin kayan Gwaggo na je soro gurin Kawu. Bayan mun gaisa na marairace na ce. "Kawu ina son zuwa asibiti anjima, kwana biyu ciwon kai da na ƙirji ya dame ni." Cikin jimantawa ya ce. "Subhanallahi! Hansatu kar ki bari damuwa ta saka miki wani ciwon fa, ki yi haƙuri ki daure ki fawwala wa Allah komai, na san abin da ciwo, kuma dole ki damu ko don ƴaƴanki da ba sa gabanki." Hawayen ƙarya na fara ban ce komai ba, ya dinga yi mini nasiha sannan ya ce na tashi na tafi. Cikin farinciki da murna na shirya na fita. Direct gidan wata dilalliya a unguwarmu na je, na faɗa mata ina son zan siyar da kayana. Ta ce mu je ta gan su. Bayan ta gani ta yi musu kuɗi, ban tsaya ciniki ba na ce ta bayar kawai duk da tayin wulaƙanci ta yi musu, ga shi kuma sun sha jiki da ma kuɗin ba na kirki ba ne. Rabin kuɗin ta ba ni ta ce za ta cika sauran daga baya. Gidan gabaɗaya ya yi ƙura ya fice daga hayyacinsa, na dinga tambayar kaina ni kaɗai ina Anas ya tafi da har yanzu bai dawo ba? Ina ya kai mini su Sultan da kewar su take ta damu na? Rashin amsa ya saka ni taɓe bakina, na ci gaba da sabgogina. Har katifata na siyar, saboda babu amfanin da za ta mun, tunda wanda zan aura yana da arziƙi shi zai yi komai kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa. Kawu kuma da ma na riga na yi masa ƙaryar na siyar komai nawa. Sai yamma lis na koma gida cikin farincikin samun ƴan kuɗaɗe. Sai dai kuɗin ba su fi sati ba suka ƙare, ciyar da kai da su labulun wanka da na wanki ba wasa ba ne. Ƙara komawa gidana na yi na tsitstsinci wasu abubuwan na ƙara siyarwa. Wasa farin girki, kafin na gama idda sai da na siyar da kusan komai nawa, kayan sakawa da ɗan abin da ba za a rasa ba ne kawai suka yi saura. Ƙarshe har wayar hannuna na siyar na siya wata ba kamfanin iphone ba, shi ne ma na ɗan samu kuɗi masu tsoka a hannuna.
Yau Juma'a, wadda ta yi daidai da gama iddata. Cikin tsananin farinciki na tashi ina jin zuciyata fes kamar an yi mini bushara da gidan aljanna. Kafin Kawu ya fita soro ya janyo ƙafa ya zo ƙofar ɗakina ya ce. "Hansatu yau lafiya ba ki fito ba har yanzu?" Na ce. "Lafiya ƙalau Kawu, ina kwana?" Ya ce. "Lafiya lau, yau kin kammala idda ko?" Na ce. "Eh, kwana ɗari ba goma ya tabbata." Cikin jimami ya ce. "Kullum da lamarin nan nake kwana nake tashi, har yanzu zuciyata rawa take yi, gani nake kamar mafarki nake zan farka. Ga shi ina ta kiran shi Anas ba na samun shi, bare na roƙe shi ya taimaka ko da sau ɗaya ne ya kawo miki yaranki ki gan su, raba uwa da ɗa ba daɗi." Ban ce komai ba na fara sheshsheƙar ƙarya, irin abin yana damuwa ɗin nan sosai. Cikin tausayawa ya ce. "Ki ci gaba da haƙuri ki ta addu'a, in sha Allah hakan alkhairi ne, Allah ya kawo miki wani mijin na gari wanda ya fi shi." Ina jan hanci na ce. "Ai ni Kawu ba zan sake wani auren ba, a haka zan ta zama, na haƙura, saboda ban san ƙalubalen ƙara fuskanta ba a cikinsa." Da sauri ya ce. "Ashsha! Kar ki ce haka, ai komai ya faru da bawa da sanin Ubangiji, za ki ji daɗi ki yi farinciki a gaba in dai ba ki da haƙƙin shi. Ke dai ki ta addu'a kawai, amma kar ki kuma faɗar haka." Na ce. "To Kawu."
Bayan ya tafi na kira Maman Nasmah, bayan mun gaisa na ce. "Yau Allah ya yi aure da mara kwabo, na kammala idda, da ma a addinance tun last week na yi jini uku na gama, na bari na cikashe kwanakin ne saboda lissafin mutane." Ta ce. "Bar kan ki, na taya ki murna." Na ce. "Bari ke dai, ya maganarmu?" Ta ce. "Hmm, abu fa ya lalace." Cikin faɗuwar gaba na ce. "Ban gane ba!" Ta ce. "Hmm, ashe tuntuni Alhaji Kyauta ya gaji da jira ya yi auren shi, yanzu haka suna can honeymoon ma shi da amaryar tasa." Wani irin jiri na ji yana kwasa ta daga zaunen da nake. Cikin matuƙar razani gami da firgici na ce. "Na shiga uku! Yanzu sai da na kashe auren nawa shi kuma zai ce a'a, da can me ya sa bai faɗa ba?" Cikin son kwantar mini da hankali ta ce. "Mene abin damuwa to?" Kamar zan fashe da kuka na ce. "Akwai mana, don Allah ki roƙe shi ko a ta uku ne ya daure ya aure ni, wallahi ko kaɗan ba na jin daɗin zaman gidan nan namu, ga yarana ina son na ɗauko su." Ta ce. "Ai kin fi ƙarfin zama da kishiyoyi biyu, ɗayar ma a plan ɗina kina shiga za ki fitar da ita. Rasa Alhaji Kyauta ba abin ɗaga hankali ba ne, maza masu kuɗi hamshaƙai suna nan da yawa a duniya, akwai wani abokin mijina matarsa ta rasu last year, yana ta damu na, na samo masa mata amma na mayar da abun wasa, har yanzu kuma bai yi aure ba. Don haka yanzu sai na haɗa ku, don ko shekaran jiya ma ya yi mini maganar, ba shi da matsala ko kaɗan, kuma yana da bala'in kuɗi."
"Ya kai mijin Aunty Billy?" Na katse ta da faɗin haka.
Tsaki ta ja ta ce. "Ya ma fi shi, ki bari na haɗa ku za ki gasgasta ni, yanzu zan tura masa hotunki da lambarki, ke ma na tura miki nasa." Cikin zumuɗi na ce. "Na ji daɗi amma, gaskiya ban san da bakin da zan gode miki ba, kin gama yi mini komai a duniyar nan." Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu ƙawata, matuƙar ina raye ba za ki taɓa zubar da hawaye ba. Abin da ba ki sani ba ma, wallahi ko mijina ne zan bar miki ki aure shi, ni dai ki yi farinciki kawai shi ne burina." Cikin mamaki na zaro ido kamar tana gabana tare da faɗin. "Mijinki fa kika ce?" Ta ce. "Eh, mene ne a ciki, kin wuce haka a gurina ai, kuma kar ki ji zancen wasa, ko a yanzu kika ce kina son shi wallahi za ki aure shi, idan kuma ba ki yarda ba ki gwada ki gani." Jinjina kai na yi na ce. "A'a, ko a mafarki ba zan taɓa auren mijinki ba har abada, mu ma bar wannan maganar." Dariya ta yi ta ce. "Kin ji an ɗaga taro sai bayan Sallah ko? Saboda azumi ya ƙarato." Na ce. "Eh, ai na ji daɗin haka, saboda kafin lokacin in sha Allah ina gidana na alfarma." Ta ce. "Ko tantama babu tawan."
Mun daɗe muna tattaunawa akan yadda abubuwa za su wakana sannan muka yi sallama, zuciyata cike da so da ƙaunar Maman Nasmah, tamkar ƴar'uwata da muka fito ciki ɗaya haka nake jin ta, tunda da za ta iya sadaukar da komai nata saboda ni. Bayan na gama duka ayyukan gidan saboda sababin Gwaggo na yi wanka, ina shiryawa na ji ƙarar shigowar message. Da sauri na janyo wayar na duba, don a zatona lambar mutumin Maman Nasmah ta turo mini. Amma sai na ga lambar Anas ce. Ban san me ya sa ba na ji zuciyata ta doka, jikina na mazari na buɗe amma sai na ga babu komai, ba abin da aka rubuta. Umarnin kiran shi zuciyata ta ba ni, bijire mata na yi cikin takaicin yadda na damu, cikin haushi na ja tsaki tare da taɓe baki ina faɗin. "Goge lambarsa ma zan yi, kar zamanta a cikin wayata ya shafa mini salalan tsiyar talauci."
Bayan Azhar na karɓo wayata daga chaji na ga an kikkira ni da baƙuwar number har two missed call. Bin bayan kiran na yi, tana shiga na ji an katse an kira. Kafin na yi magana na ji wata irin murya mai sanyi da kamewa ta yi sallama. Amsawa na yi tare da faɗin. "Wa ke magana?" Bai amsa ba ya ce. "Da fatan ina magana da tauraruwa mai hasken da ya haskake zuciyata tun kafin na gan ta a zahiri?" Shiru na yi ina maimaita kalamansa a cikin raina, sai da ya ƙara magana sannan na ce. "Ai gabaɗaya ka sani a duhu ne, har na fara tunanin ko wrong number ka kira." Murmushi ya yi mai sauti wanda na ji shi har cikin kaina ya ce. "Ai zuciya ba ta taɓa mistake akan dukkanin abu mai muhimmanci a gare ta, ke ce wadda nake nema Hafsah." Ya yi shiru na wasu sakanni alamar ba ya iya dogon zance sannan ya ci gaba da magana. "Sunana Mansur Ibrahim Idonnera, ƙawarki takwararki ce ta ba ni numbernki, tunda ta tura mini hotunki na gani na rasa sukunina gabaɗaya, tun lokacin har yanzu ina kwance ina ta tunaninki ne kawai, sai yanzu da kika ɗaga na ji wannan zazzaƙar muryar taki na ji na fara samun nutsuwa." Ƙaƙƙarfar ajiyar na sauke, da ma ina ta addu'a Allah ya sa shi ne wanda Maman Nasmah ta ce za ta haɗa mu, don muryarsa kaɗai ta tabbatar da yanayinsa, yadda yake magana a kasalance yana jan numfashi ba ƙaramin burge ni ya yi ba, daga ji babu tambaya jiƙaƙƙe a can ƙasan tekun kuɗaɗe, ga sunansa kuma da ya ƙara tabbatar mini da haka. Murmushi na yi tare da kwanciya don wayar ta fi armashi na ce. "Duk wannan yabon ni kaɗai?" Ya ce. "Kin fi gaban haka ma zinariyar mata, yanzu dai ki sanar mini na karɓu ko sai na ƙara zage damtse kar zuciyata ta buga." Siririyar dariya na saki tare da ƙanƙame wayar ban ce komai ba.
"Dariya mai daɗi da saka nishaɗi." Ya faɗa ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Hakan ya haifar mini da tashin tsigar jiki. Lumshe idona na yi na ce. "Idan akwai abin da ya fi karɓuwa ma ka yi shi a gurina." Ya ce. "Wow, thank you, dole na bayar da tukuicin amsar nan." Murmushi na yi na ce. "Ai kai ne tukuicin." Ya ce. "Bayan ni ma akwai buƙatar wani, ki tura mini account number ɗinki na saka mini tukuicin, ko kuma ki faɗa mini wani abun da kike so na saka a kawo miki." Cikin jin daɗi na ce. "Na gode, amma account ɗina ba ya aiki yanzu." Don ba zan ce ban da shi gabaɗaya ba ya raina ni." Ya ce. "Zinariya guda ba account kuma nake zaune, bari na kira wani na haɗa ku, sai ki je bank ɗinsu ya buɗe miki duk lokacin da kike so, ni yanzu ba na Nigeria ne amma da ni zan zo na kai ki da kaina." Na ce. "Babu komai, hakan ma ni ce da godiya." Daga haka muka yi sallama bayan ya ce zai tura mini kati. Ina ta rawar murna na samu irin mijin da nake so message ya shigo wayata, ina dubawa na ga credit ne na 20k, murza idona na yi don ƙara tabbatarwa ko shi ne bai ganar mini daidai ba, amma still haka na gani. Waro ido na yi na yi tare da dafe ƙirjina na ce. "Katin dubu ashirin? Katin waya na kira kawai!" Gabaɗaya sai na ruɗe na susuce, na kira Maman Nasmah na sanar mata ba ta ɗaga ba. Sai na hau online na shiga chat ɗinmu, na ga ta tuttura mini hotunan Mansur, cikin azarɓaɓi na buɗe cike da matsuwar son ganin yadda kamanninsa da komai nasa za su kasance........✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
FREE BATCH
*20.*
Ƙura wa hoton farko da na buɗe ido na yi, ina bin kowacce gaba ta jikinsa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Baƙi ne amma mai haske ba mai duhu ba, kuma yana da ƙiba, sannan ba matashi ba ne kamar yadda na yi tunani don ya fara manyanta, amma a muryarsa da yadda yake magana na ɗauka bai fi matashi ɗan 35 years ba. Hannunsa da ya fi fuskarsa haske sosai tabbacin hutu na kalla ina murmushi. Daga yanayin suturar jikinsa da gurin da aka yi masa hoton kaɗai ma ya gamsar da ni. Ci gaba da kallon sauran na yi, wasu ma duk a ƙasashen waje ya ɗauka. Reply na yi mata da thanks kawai na fita daga chat ɗin. Wani irin fayau nake jin zuciyata kamar an wanke mini ita da tsintar wannan dami a kalan da na yi.
Da yamma na je gurin masu siyar da kati na yi musu transfer ɗin na 15k suka ba ni kuɗin, daga nan shagon masu siyar da mayuka na je na siya mai ɗan kyau da sabulu da turare, dan so nake na fara gyara jikina kafin ya zo mu haɗu. Ina son na je gidan Maman Nasmah saboda mu fi tattauanawa yadda yakamata amma ina tsoron Kawu, don ɗan nan da can idan na ce za ni da ƙyar yake bari na.
Tun wayar da muka yi da Mansur ba mu kuma waya ba har sai washegari da safe, ya kira ni ya ce ayyuka ne suka yi masa waya, muna gama wayar shi ma kamar jiya ya turo mini da credit na 20k. Da ma jiya da muka yi chat da Maman Nasmah na faɗa mata ta ce ai shi bai mayar da 20k kuɗi ba, indai Idonnera ne yanzu na fara ganin ɓarin kuɗi.
Ranar Monday na yi wa Kawu ƙaryar zan koma asibiti, ciwon kai da na ƙirji sun ƙara dawo mini, ya dinga yi mini faɗa da nasiha akan na cire damuwa a cikin raina, na zama mai tawakkali, don shi duk a zaton shi damuwar sakin ce take sanya mini ciwon. Na ce masa in sha Allah zan rage, sannan ya bar ni na tafi. Banki na je aka buɗe mini account, ina zuwa ban wani tsaya bin layi ba, saboda wanda Mansur ya haɗa ni da shi, shi ya zo ya shigar da ni ya yi mini komai. Bayan an gama na kira shi, bai ɗaga ba kamar yadda na yi zato ya katse ya kira da kansa.
"Ranki ya daɗe." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa. Murmushi na yi na ce. "Tare da naka, an kammala komai shi ne na kira na sanar maka." Ya ce. "Ma sha Allah, yanzu na ji ni daidai, amma da Madam babu account babu hanyar da zan tura mata kuɗin da za ta siya kayan kwalliya ta mun ai ba kanta." Dariya na yi na ce. "To dole kai sai ka tura mini kuɗi?" Ya ce. "Mene amfaninsu idan ban ba ki ba? Kin ga kwana ukun a takure na yi su saboda ban tura miki kuɗi ba, don haka yanzu turo mini account number ɗin kawai na fara tura miki kuɗin powder kafin na zo." Cikin farinciki na ce. "An gama." Tare da katse kiran na tura masa. Tabbas sai yanzu na samu namiji irin wanda ya dace da ni, mai buɗaɗɗen hannu ba irin Anas matsolo ba, tsabar so da tarin dukiya har matsuwa ya yi ma ya tura mini kuɗi. Ƙarar shigowar message ya saka ni saurin duba wayata, yawan kuɗin da na gani ya saka ni zaro ido ina ƙara bitar zirukan, idan ba idona ne yake yi mini gizo ba one million na gani. Ban gama tantacewa kiransa ya shigo. Cikin azarɓaɓi na ɗaga, na ce. "Na ga alert, Ranka ya daɗe ai kuɗin sun yi yawa." Cikin dariya ya ce. "One million ɗin? Ai ni kira na yi na ji idan ba za ta isa ba na ƙaro." Na ce. "A'a, ta yi yawa ma na go...."
"Babu godiya a tsakaninmu, don haka daga yau kar ki kuma, million kuma ki shirya tarɓar ta, don kin kusa fara kyautar ta nan kusa ba ma a ba ki ba, don haka ki daina cewa ta yi yawa." Ya katse ni da faɗin haka.
Ƙara dashare bakina na yi don tun ɗazu ya ƙi rufuwa na ce. "Tom shikenan my dear, Allah ya ƙara arziƙi da wadata." Ya ce. "Amin, ki jira a nan bank ɗin yanzu zan turo ɗaya daga cikin yarana ya kai ki shopping Mall ki zaɓi duk abin da kike so, kafin na dawo mu je tare." Danne ruɗun da nake ciki na yi na ce. "To." Daga haka muka yi sallama.
Ni kaɗai na dinga murmushi, na manta a cikin mutane nake, don gabaɗaya na kasa control ɗin gigicewar da kuɗin suka saka na yi.
Har yaron nasa ya zo muka tafi ban daina kallon alert ɗin ina murmushi ba. Ƙara ruɗewa na yi bayan na shiga cikin motar da ya zo da ita, don ba ƙaramar haɗuwa ta yi ba. Wani haɗaɗɗen guri ya kai ni, ya ce na ɗauki duk abin da nake so, Oga ya bayar da maƙudan kuɗaɗe. Na yi dariya kawai ban ce masa komai ba. Zagewa na yi ban yi wa kaina ƙauro ba na jibgi kaya, ina ganin na loda da yawa amma yaron ya ce sun yi kaɗan ya ƙara ɗibar mini wasu. Da muka je gurin biyan kuɗi na ji kuɗin kayan ba ƙaramin girgiza na yi ba, amma shi ko a jikinsa ya zaro ATM ya ba da aka zara muka taho. Rashin sanin ta yadda zan shiga gida da uban kayan ya sa na ce ya kai ni bayan layinmu, na kai su ajiya gidan wata mata da muke mutunci da ita.
Bayan mun ƙarasa na shiga na yi mata bayani ta ce. "Inyee, su Hafsah har an fara zaurawan ne?" Murmushi na yi tare da ƙirƙirar abin da zan faɗa mata, don ba zan nuna ina son shi ba a ce da ma muna tare tun da, ko kuma a gane plan ɗina. Cikin ɓata rai alamar ba na so na ce. "Wallahi kuwa Maman Sabir, daga na je asibiti wani mutumi yay ta bi na da naci da magiyar na ba shi lambata, bayan na ba shi kuma ya ƙi ƙyale ni wai sai ya kawo ni gida, shi ne ya tsaya a wani guri ya yi mini siyayya, na ce ba zan karɓa ba amma ya nace, har ƙaryar ni matar aure ce fa na yi masa amma ya ƙi yarda." Ta ce. "To ai abin farinciki ne wannan, sai ayi ta addu'a Ubangiji ya sa da shi za a yi idan da alkhairi." Na ce. "Gaskiya ni ban shirya aure yanzu ba, ko zan ƙara aure ba yanzu ba." Ta ce. "A'a kar ki yi wannan gangancin, domin kuwa dama ce Allah ya ba ki, ai haka abin yake da ma, mace tana yin idda za ki ga maza sun fara tururuwar zuwa mata, kamar waɗanda ake sanarwa." Na ce. "To Allah ya kyauta, bari na je na dawo." Cikin tsokana ta ce. "To ki gaishe shi ki ce in ji surukarsa." Na yi dariya kawai ban ce komai ba.
Mun ci gaba da shan soyayya ni da Alhaji Mansur Idonnera, idan muka fara waya har mantawa nake yi kati ake zara saboda daɗewa, ga shi kuma ya ce mini ba ya ƙasar, wani tsari yake yi da duk ƙasar da ka je da sim ɗinka za ka yi amfani, amma ba ƙaramin kuɗi ake ɗauka ba. Idan mun gama wayar mu ɗora da chatting. Sati ɗaya da haɗuwarmu amma kullum sai ya tura mini credit ɗin 20k ya ce na saka data. Hakan ya sa ni kasancewa a cikin nishaɗin da ban taɓa riskar kaina a ciki ba, tare da ƙara mantawa da Anas, su Sultan ne kullum sai na tuna su, amma shi ma ban bari yana damu na ba. Na ƙara tabbatarwa kuɗi su ne jin daɗin rayuwa, su ne gishirin zaman duniya kamar yadda ake yi musu kirari, su ne farincikin komai a rayuwa.
Yau Friday yau muka yi da shi zai zo mu haɗu, duk da ina murnar ganin shi amma da fargabar yadda zan sanar da Kawu batun shi na tashi. Ba na so ya yi zargin wani abu ko ya saka ayar tambaya a kaina, don mutum ne shi mai zurfin tunani da nazari. Ina zaune bayan an sakko daga masallaci na samu mafita, akwai wata kamar Yaya take a gurin shi, zan ce masa zan je gidanta na gaishe ta, idan ya so sai Alhaji Mansur ya je can mu haɗu. Don na san ita ba za ta hana ba, musamman idan ya zo ta ga mai kuɗi ne, don irin matan nan ne masu azababben son kuɗi. Cikin murna na shirya, bayan na rufe na ɗakina na yi wa Gwaggo sallama na fita. Na tsugunna a soro na ce. "Sannu Kawu, ya jikin?" Ya ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Na ce. "Allah ya ƙara afuwa." Ya ce. "Amin ya rabb." Kaina a ƙasa na ce. "Da ma gidan Inna Habi nake son zuwa na gaishe ta." Ya ce. "Da kuwa kin kyauta, ga shi kuwa Juma'a ce ga ladan Zumunci, ki je Allah ya kiyaye, ki gaishe ta." Na ce. "Za ta ji." Har na miƙe ya tsayar da ni da faɗin. "To kina da kuɗin mota?" Na ce. "Eh Kawu." Ya ce. "Kar fa ki yi tafiyar ƙafa, idan ba ki da shi ki faɗa na ba ki." Na ce. "Ina da shi wallahi." Ya ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya, kar ki dare amma." Na ce. "To." Duk ci da kaina ɗin da nake yi Kawu bai sani ba, don shi duk a zaton shi Gwaggo ce take ciyar da ni a cikin abincin siyarwarta, saboda duk ƙi na da take yi da muguntar da yi mini a baya ba ta taɓa nunawa a gabansa, yi take kamar za ta lashe ni saboda soyayya idan a gaban idonsa ne, shi ya sa har yau bai gane makircinta ba, ni kuma ban taɓa faɗa masa ba. Na san ko da ba kullum ba zai taɓa zama bai ba ta kuɗin cefane da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 24