abin da za a dafa ba, ƙeta ce kawai ta saka ba za tana ba ni abincin ba. Ni kuma ban damu ba tunda Allah ya rufa mini asiri, kuma ba jimawa zan yi a gidan ba zan tafi gidana na alfarma.
Kawu kuwa da kallon tausayi ya bi bayan Hafsah har ta fice, ya yi alƙawarin duk inda ta tambaye shi za ta je ba zai hana ta ba, amma ba wai zai bar ta tai ta gantali ko'ina ba ne. Saboda ya san fitar ce take ɗan ɗeɓe mata kewar halin ƙuncin da take ciki.
Da sallama na shiga gidan Inna Habi, na tarar da ita a zaune a tsakar gida tana dakan daddawar miya. Ba yabo ba fallasa ta amsa mini, don ba wani kula Kawu take ba saboda talaka ne, don ita indai kaga ta shigewa wa mutum to yana da maiƙon da za ta lasa ne. Tsugunnawa na yi har ƙasa na ce. "Ina yini Inna?" Ta ce. "Lafiya ƙalau, ya Baban naki da jiki?" Na ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Ta ce. "Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi. Har kin yi idda ko?" Na ce. "Eh, tun wancan satin ma." Ta ce. "To Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya kawo miki wani mijin na gari, ga tabarma can je ki zauna, bari na kawo miki ruwa." Na ce. "To Inna." Bayan an yi la'asar na share mata tsakar gida da ɗaki, ta gama abinci ta zuba mini muna ƴar hira. A lokacin na sako mata zancen Mansur, ina kallon wayata da message ɗinsa ya shigo na ja tsaki. Inna ta ce. "Ke kuma lafiya kike jan tsuka ke kaɗai?" Ɓata fuska na yi na ce. "Wani ne ya dame ni wallahi, wai dole sai ya zo mun haɗu yau." Ta ce. "Wane ne? A ina kuma kuka haɗu?" Yadda na faɗa wa Maman Sabir haka na zayyana mata ita ma." Haɓa ta kama ta ce. "To shi ne me? Mene abin damuwa? Ki tsaya ki saurare shi, ki bar shi ya zo. Ki cire wancan tsohon mijin naki daga ranki ki fuskanci abin da yake gabanki." A shagwaɓe na ce. "Inna yana da kuɗi daga gani mutumin, ni kuma gaskiya ba na son irin masu mahaukatan kuɗin nan." Dundu ta ɗaka mini ta ce. "Ku ji mini sakarar yarinya kai, Allah ya kawo miki tsuntsu daga sama gashashshe za ki butulce masa, wa yake ƙin kuɗi? Ai kuɗi abin so ne, tashi ki je masa ki share seat room ki ƙara gyara shi, ki zo ki karɓi turaren wuta ki saka, sai ku yi zancen a can." Ina murmushi na tashi cikin farincikin haƙata ta cimma ruwa, da ma na san ina cewa mai kuɗi ne za ta goya mini baya, kuma da ma a gurinta kaɗai nake tunanin samun haɗin kai cikin ruwan sanyi. Address ɗin gidan na tura masa, da ma text ɗin da ya yi mini kafin na yi mata maganarsa akan yana jiran address ɗin ne.
Sai da ta saka na sake sabon wanka na yi kwalliya, ta ba ni turare na fesa. Bayan Magriba ya yi mini text ga shi a ƙofar gidan, inda Allah ya taimake ni mota tana shiga cikin layin. Da zan fita ta ce. "Ki sakar masa fuska fa, kar ki cukule ki yi dinkum, kin ji na faɗa miki." Na ce. "To Inna."
Da na fita na yi zaton zai fito daga motar ne, sai ga bai yi hakan sai horn ma da ya danna. Ina murmushi na ƙarasa gurin motar na buɗe front seat, zuciyata cike da kewar shi, don yau kwata-kwata ba mu yi waya ba sai dai chat, saboda yana cikin hayaniya ya jejje companies ɗinsa don ganin yadda abubuwa suke tafiya.......✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:43 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*21.*
Idanunsa ƙir a kaina fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce. "Welcome Madam, ban san sunan da zan ba wa ranar yau ba saboda tsananin farincikin da nake ciki." Ban ba shi amsa ba har sai da na zauna na rufo motar sannan na ce. "Ya na ji muryarka a dashe? Ba dai mura ce ta kama mini kai ba?" Ya ce. "Ita ce mana, wannan zirga-zirgar da na yi ce ta saka." Na ce. "Sannu Allah ya ƙara sauƙi." Ya ce. "Amin ya rabb, ashe Camera rage miki kyau take yi, a fili kin fi kyau sosai." Fari na yi masa da ido na ce. "Kai ma haka ai, Ina yini? Ko gaisawa ba ka bari mun yi ba." Ya ce. "Ana ta kai wa yake ta kaya? Gabaɗaya ni kin ruɗa ni ne ai, gaskiya dole na samu wata gwaggwaɓar kyauta na yi wa Maman Nasmah, saboda haɗa ni da tauraruwar matan da ta yi." Na yi dariya kawai ina ƙare masa kallo, ƙamshinsa mai daɗi da sanyin AC na ratsa ni.
Mun daɗe muna hira, da zai tafi ya raka ni har bakin soro, ya ce na kira Inna ya gaishe ta, bayan sun gaisa ya ba ta kuɗi, ni ma da zai wuce ya ba ni bandir ɗin ƴan ɗari biyar. Da murna Inna ta rungume ni bayan na koma, tana dariya ta ce. "Yanzu kika yi miji, ai irin waɗannan kullum su muke addu'a da fatan ku samu, rabon arziƙi ne ya sa kika baro gidan wancan matsolon." Na ce. "Haka ni ma na ce, amma ni Inna Kawu kawai nake ji, don shi Alhajin ya ce ba ya so bikinmu ya kai azumi." Dafa kafaɗata ta yi ta ce. "Kwantar da hankalinki, saboda yanzun nan ma na kira shi na ce masa a nan za ki kwana, gobe da kaina zan je na yi masa bayani, na gama shirya duk abin da zan ce masa, ke ma anjima zan faɗa miki, yadda bakinmu ba zai zama biyu ba, yanzu bari na siyo mana tsire mu ci, wancan tuwon a ba wa almajirai shi kawai." Ina murmushi na ce. "To Gwaggo sai kin dawo."
Kusan raba dare muka yi muna tsara yadda abubuwa za su kasance, ni kuwa zuciyata fes na yi amanna da duk ƙaryar da Inna za ta faɗa wa Kawu, don ko ban yi bincike akan Mansur ba na san ba zaɓan tumin dare ba ne, saboda na yi amanna Maman Nasmah ba za ta taɓa haɗa ni da wanda ba ta aminta da shi ba.
Washegari wajen ƙarfe goma muka koma gida tare da Inna, bayan mun gaisa da Kawu na shige ciki na bar su tare, cikin raina ina addu'ar Allah ya sa kar ya ba mu matsala a cikin auren nan, don na san halinsa tsaf zai ce a'a idan ya ji irin kuɗin da Alhaji Mansur yake da shi. A tsanake Inna ta dubi Kawu ta ce. "Ɗan'lami magana nake tafe da ita mai muhimmanci fa." Kawu ya ce. "To ina sauraren ki Yaya Habi." Ta ce. "Yawwa, yarinyar nan Hafsah jiya da ta je wani ƙanin mijin maƙociyarmu ya gan ta ya ce yana so, babban mutum ne mai hankali da kowa yake yabon shi, matarsa ce ta rasu shekara ɗaya da suka wuce, bai sake aure ba har yanzu kuma bai taɓa haihuwa ba." Gyara zama sosai Kawu ya yi ya ce. "A ina yake? Mene ne kuma sana'arsa?" Inna Habi ta ce. "Ɗan kasuwa ne, sauran bayani kuma idan ya zo duk zai yi maka da bakinsa, don shi a yadda muka yi magana jiya a ƙage yake, kafin azumi yake son a yi komai idan mai duka ya nufa." Jinjina kai ya yi ya ce. "Amma Yaya kamar ya yi kusa yarinyar nan ta sake aure kafin azumi, don har yanzu tana cikin damuwar mutuwar wancan auren nata, da bari muka yi ta huta sosai, radadi da zafin abun ya bar cikin ranta." Da sauri Inna ta ce. "Wanne hutu kuma? Ai ba ta buƙatar wani hutu, idan ta yi auren ai shi ne abin zai fi saurin barin cikin ranta ta manta da wani Anas, kai dai kawai ka yi mata addu'a, ƙila rabon wasu ƴaƴan da ba na wancan ba ne ya fito da ita. Kuma ita ma fa ta amince da na yi mata magana." Kawu ya ce. "Hafsan da kanta?" Ta ce. "Ita fa." Numfashi ya sauke ya ce. "To Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ki ce ya zo mu zanta, idan har ta amince da shi kuma ba shi da wani aibu da za a hana shi aure shikenan, sai a yi." Cikin farinciki ta ce. "Yawwa, ko kai fa, ai ita bazawa ba a buƙatar yin jinkiri a lamarin aurenta."
Da Inna ta sanar mini yadda suka yi ba ƙaramin murna na yi ba, a lokacin Kawu ya kira ki ya tambaye ni zan iya yin aure yanzu? Kuma ina son wanda Inna ta zo masa da batunsa? Tun kafin ya gan shi gara ya ji ra'ayina. Kaina a ƙasa na amsa da na amince. Ya yi mana addu'a tare da fatan alkhairi.
A ɗokance na kira Alhaji Mansur bayan na koma cikin gida na ce. "Kawu ya ce duk lokacin da ka shirya ka zo yana son ganin ka." Muryarsa ɗauke da farinciki ya ce. "Kai amma na ji daɗi, Alhamdulillah! Ai ni a shirye nake, anjima da daddare in sha Allahu zan zo." Ina murmushi na ce. "Sai ka zo, zan sanar masa, amma don Allah zan roƙe ka wata alfarma." Ya ce. "Faɗi kanki tsaye darling." Na ce. "Yawwa, idan ka zo gurin Kawu don Allah kar ka ba shi ko taro har ku tafi, hakan zai fi sakawa ya fi amincewa da kai." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Shikenan, duk da abin yana da matuƙar wahala a gurina, don ni ban san me ya sa ba hannu har ƙaiƙayi yake wajen yin kyauta, bare kuma Babana guda na je har gabansa na kasa ba shi kuɗi, anya zan iya kuwa?" A shagwaɓe na ce. "Please my Man." Cikin marairacewa ya ce. "Ya zan yi, yadda kika ce ai haka za a yi." Na ce. "Yawwa thank you."
Inna Habi ce ta sanar wa Kawu zuwan Alhaji Mansur Idonnera, har dare kuma ba ta tafi ba, ta ce sai sun zo ta ji yadda aka yi. Gwaggo dai da ido kawai take bin mu.
Kamar yadda ya alƙawarta bayan isha'i suka zo, na ce masa su shiga soron kawai, don kunya nake ji na tsallake Kawu da sunan na fita zance. Hakan ya sa har suka tafi ba mu haɗu ba, sai waya muka yi ya mun sallama, yana ta yabon yadda Kawu ya tarɓe su. Shi ma Kawun yabon nasu ya yi ta yi, ina jin shi yana cewa Inna. "Ma sha Allah, yaron akwai tarin ilimin addini sosai, magana da komai nasa cikin nutsuwa da ilimi yake yi." Washe baki ta yi ta ce. "Ka gani ba, ka ga abin da nake faɗa maka ai." Ya ce. "Na gani kam, yanzu mun gama magana na ce ya turo manyansa neman izini kafin ta fara fita gurin shi, sai su fahimci juna." Inna ta ce. "Hakan ya yi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum."
Kwana uku a tsakani Mansur ya turo magabatansa suka kawo kuɗin aure da sadaki, Kawu da wani abokinsa da maƙotanmu guda biyu ne suka karɓa, duk da Kawu bai so haka ba, don shi tambaya kawai suka ce masa za a yi ban da kawo kuɗi, ya yi niyyar ƙin karɓa amma ragowar suka ce a karɓa kawai, yarinya ta samu miji ba a toshe ta ba. An sanya biki sati biyu kacal, wanda ya kama saura kwana uku azumi a lokacin. Duk wanda Kawu yake da tabbaci a kansa ya saka ya yi masa bincike akan Alhaji Mansur, kuma Alhamdulillah ta ko'ina sakamako mai kyau ake kawo masa. Hakan ya sa hankalinsa ya kwanta ya bi abin da addu'a kawai.
Sosai nake shirin bikina, duk da ban da ɗan tayi sai Maman Nasmah da Inna Habi. Don Naja tun ban fi kwana biyu da dawowa gida ba na yi blocked ɗinta a ko'ina da na san za ta same ni, don wani irin haushin ta nake ji. Na kuma ƙudurce a raina ba zan nema ta ba har sai na yi aure, na kira na sanar mata ta zo ta ga irin mijin da na aura da gidan da nake. Ƴan group ɗinmu babu wanda ya san aure na ya mutu bare ya san zan sake wani auren, da ma haka muka tsara ni da Maman Nasmah, ba za su taɓa sani ba, shi ya sa babu wanda na gayyata, haka ma ƙawayena da ƴan unguwar da na zauna, duk ban faɗa musu ba. Kuɗi sosai Idonnera yake tuttula mini na hidimar biki, amma ko sau ɗaya ban taɓa bari Kawu ya sani ba. Na je an yi mini gyaran jiki, na haɗa wa kaina lefe a gidan Inna, na sissiya abincin da za a dafa ranar bikin. Kayan ɗaki da na kitchen da ma ko tsinke ba zan tafi da shi ba, ya riga da ya siya komai. Amma Kawu bai san da batun ba, don wata gonarsa ya ɗaga ya siyar ya ba wa Inna Habi kuɗin ya ce a yi mini komai da su. Ta nuna masa kuma an siya suna nan a gidanta, har jeren ƙarya ta ce masa an tafi ana i jibi ɗaurin auren. Tun daga zuwan da Mansur ya yi na farkon nan sau ɗaya ya ƙara dawowa, saboda ayyuka da abubuwa da suka sha masa kai. Ina ta hidima amma zuciyata cike take da kewar ƴaƴana, na so zuwa har ƙauyen su Anas na kwaso abuna, amma sanin Kawu ba zai yarda ba ya sa na bari sai na tare bayan na gama cin amarci na je na ɗauko su ko ta halin ƙaƙa. Ranar Juma'a ɗaurin auren ya kama, ranar Alhamis na je aka yarfa mini kitso tare da rangaɗa mini ƙunshi. Bayan an gama na tura masa da hotunansu, sai ya ce ba su fita ba sosai, Camerar da na yi amfani da ita ba ta da kyau, bari ya turo a kawo mini waya, da ma yana ta son ya sauya mini kuma ya sha'afa. A daren ya aiko wani yaronsa ya kawo mini sabbin wayoyi, keypad da iphone. Ita kanta keypad ɗin ban taɓa ganin irinta ba, mai kyau ce sosai kuma daga gani babu tambaya da kuɗi mai yawa aka siye ta. Ban yi amfani da su ba na ce sai Allah ya kai mu gobe bayan na tare a gidana.
Washegari ta kasance rana mafi girma da tarihi a rayuwata, rana mai ɗumbin farinciki da murnar cikar burina. Duk da ban yi gayya ba amma gidan cike yake da mutane, don ita Gwaggo ta yi, ƴan'uwanta da na Kawu da maƙota. Dangin mahaifiyata kuwa babu wanda ya zo, sun ce abun ya zo a ƙurarren lokaci, sai aike suka yi mini tare da alƙawarin daga baya za su zo su ga gidan nawa.
Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura aurena da Alhaji Mansur Ibrahim Idonnera, a babban masallacin juma'ar unguwarmu. Bakina ya ƙi rufuwa saboda farinciki, na je aka yi mini makeup mai kyau, na shirya cikin wani tsadadden lace milk color. Maman Nasmah ta zo amma ba ta jima ba ta tafi, saboda za ta je gidansu Ango, don su a event ma suke yinin ba a gida ba. Mansur ya so na je, amma na ce masa a'a don na san Kawu ba zai taɓa bari ba. Yadda nake cikin nishaɗi da walwala haka ma ango yake, bini-bini ya kira ni ya ce ya rasa ina zai saka kansa saboda farinciki, kamar ya zauce haka nake ji. Murmushi kawai nake yi masa. Saboda yadda ya nuna ya ƙagu a kai ni ya sa ana yin sallar la'asar aka tafi kai ni, bayan Kawu ya yi mini doguwar nasiha mai ratsa jiki. Mota ɗaya kacal ya kawo kamar yadda na ce masa, saboda har yanzu Kawu bai san mai kuɗi ba ne sosai, sadaki da kuɗin aure duk kuɗi kaɗan na ce masa ya bayar.
Daga Inna Habi sai wata ƙanwarta da wata maƙociyarmu aka tafi kai ni, unguwar da nisa daga tamu, hakan ya sa sai daf da Magriba muka ƙarasa. Tun daga farkon unguwar muka fara cin karo da tafka-tafkan gidajen, wanda tsabar tsaruwar su kamar za su yi magana. Ta cikin mayafi nake ƙare wa ko'ina kallo. Layinka unguwar kowane shafe yake da titi luwai-luwai, a bakinsa kuma an saka gate. Future house ɗin da nake fata dai nan aka kai ni. Ban san ta yanda zan iya fasalta girma, kyau, da haɗuwar gidan da aka kai ni ba, don duk tunanin mai tunani ya wuce nan. A wani ƙaton ɗaki na alfarma da ke hawa na uku a gidan aka ajiye ni, su Inna suna yin sallar Magriba suka yi mini sallama suka tafi suka bar ni daga ni sai halina.........✍️
*Zeey Kumurya ✍️*
[3/8, 1:43 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
FREE BATCH
*22.*
Yaye mayafin fuskata na yi ina murmushi na shiga bin ɗakin da nake da kallo. A hankali na miƙe na fara shafa ƙaton gadon da duk girman shi a ɗan gefen ɗakin yake. Daga baya na koma gurin wardrobe da madubi, na daɗe a tsaye kafin na fita ƙaton parlour'n da ya ji komai na more rayuwa. Wani tsalle na doka cikin tsananin farinciki, yau ni ce a gidan da nake mafarkin kasancewa a cikinsa matsayin mallakina? Tsabar zumuɗi har wani irin tsiko nake jin jikina yana mun. Ɗayan bedroom ɗin da ke manne da wanda na fito na shiga, shi ma kamar shi yake a komai da komai, banbancinsu kawai kowanne furnitures da kalar shi. Ban wani jima ba na fita, ƙofar da na gani tana facing ɗina na shiga, haɗaɗɗen dinning area na yi tozali da shi. Cike da ƙauyanci na je na fara tattaɓa abubuwan ina sunbatu ni kaɗai. Daga nan da na fita hawa na biyu na sauka, shi kuma ƙaton parlour ne kawai da ya ji komai, sai kitchen da toilet a cikinsa. Sai da na leƙa ko'ina sannan na sauka ƙasa. Shi kuma kamar hawa na uku yake, parlour, da two bedrooms kowanne da toilet a cikinsa, sai kitchen da dinning area. Gabaɗaya komai na gidan sabo ne, ko'ina kuma kalarsa daban. Ta window na leƙa na hango wasu apartments ɗin daban daga can nesa, amma duk da ban je na gani ba na san wanda nake ciki duk ya fi su girma. Sai da na gama kalle-kallen nawa zan koma can saman na ga wata ƙofar daban ta cikin parlour'n, da sauri na je na buɗe, sai na ga wani parlourn ne daban shi ma, mai kyau amma bai kai sauran girma ba, da toilet a cikinsa. Ban jima ba na koma saboda kar Ango ya shigo ya tarar da ni a ji kunya. Bayan na zauna na ɗauko jakata na ɗauki wayata na duba time, sai na ga ƙarfe goma na dare ma ta wuce. Cikin mamakin abin da ya hana Mansur zuwa har lokacin na kira shi. Har missed call uku na yi masa amma bai ɗauka ba. Ban kawo komai a raina ba na ci gaba da santin gidana, sai wajen 11 na tuna ko sallar Magriba ban yi ba. Da sauri na miƙe na shiga haɗaɗɗen toilet ɗin ɗakin don ɗauro alwala, da ƙyar na iya kunna fanfo na yi na fito. Bayan na idar na ciro sabbin wayoyina daga kwali na jona su a chaji. Tsohuwar kuma hoton shi na lalubo na shiga kalla don ya ɗebe mini kewa. Abin da ya fi burge ni da shi yadda bai taɓa kyara ta ko nuna mini ƙyama ba kasancewata talaka, da kuma tunda muke da shi bai taɓa yi mini maganar banza ba, duk da ya san ni bazawara ce, kamar yadda aka ce wasu mazan suna yi ko da auren mace za su yi. Hakan ya ƙara mini ganin girman da darajar shi, na tabbatar so na tsakani da Allah yake yi mini. Har sha biyu ta wuce ina zaune a gurin, zuwa lokacin na fara fargabar ko ba lafiya ba? Yadda ya nuna mini ya matsu a kawo masa ni, amma fiye da awa biyar da kawo nin babu shi babu dalilin shi, sannan ina ta kiran shi bai ɗauka ba, shi kuma bai kira ni ko ya yi mini text ya sanar mini abin da yake faruwa ba. Sai da gyangyaɗi ya fara ɗiba ta sannan na tashi na koma kan gadon na kwanta, gabana na dukan tara-tara. Tun ina ɗaukar abin wasa har na ga ya wuce hankali ganin har 2 bai shigo ba. Na dinga kiran shi da tura masa text amma shiru. Duk da tarin gajiyar da ke addaba ta amma sai na kasa bacci, sai wajen asuba wani wahalallen bacci ya kwashe ni, wanda cikinsa na dinga mafarkai wai wani mugun abin ne ya samu mijina. A firgice na farka ina faɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Gabaɗayana na yi sharkaf da gumi. Jin kamar ana buga ƙofar ɗakin ya sa na tashi sauri na je na buɗe, cikin raina ina addu'ar Allah ya sa shi ne. Saɓanin abin da na yi zato na tarar, wata yarinya ce tsaye a bakin ƙofar, kanta a ƙasa ta ce. "Ina kwana Hajiya?" Ina zazzare ido na ce. "Lafiya ƙalau." Cike da ladabi ta ce. "Mu ne masu aikinki da alhaji ya ce a samo, sauran suna ƙasa, mun kammala abin kari ne na ce bari na zo na sanar miki." Kallon ta na yi na gan ta a tsabtace take babu ƙazanta a tattare da ita, numfashi na sauke na ce. "Ok, a cikin gidan nan kuka kwana ne?" Ta ce. "A'a yau muka zo, amma maigadi ya nuna mana ɓangarenmu da za mu dinga kwana mun kai kayanmu can." Gyaɗa kai na yi na ce. "Ya sunanki?" Ta ce. "Laure." Na ce. "To sannun ki, je ki na gode." Har ta juya na kira ta, ta dawo tare da rusunawa, umarni na ba ta akan ta kira mini maigadin.
Sai da na yi sallar asuba don lokacin kusan goma saura sannan na sauka ƙasan, na tarar da shi zaune akan carpet. Kamar zai yi sujjada saboda duƙawa ya ce. "Barka da fitowa ranki ya daɗe." Hakan ya fasa mini kai, na zauna a kan kujera tare da harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ban amsa masa ba na ce. "Maigidan nan ya shigo jiya ne?" Ya ce. "A'a, ai da ma ya sanar mini ba zai kwana a gidan ba, wani uzuri ne ya tasar masa ya yi ƴar tafiya, amma ba zai jima ba zai dawo, na ɗauka ya sanar miki ne ma." Ajiyar zuciya na sauke jin yana lafiya ƙalau, amma me ya sa ni bai faɗa mini zai yi tafiya ba? Kuma wanne irin uzuri ne da har ya fi kasancewarmu a daren farkon aurenmu muhimmanci? Ya zaɓi ya je ya yi shi, ni kuma ya bar ni na kwana ni kaɗai ƙwallin ƙwal, babu waya babu komai? Rashin mai ba ni amsa ya sa na sallami maigadin. Hankalina ya ɗan kwanta da na ji lafiya lau yake, hakan ya sa na saka masu aiki suka kawo mini abinci na karya. Bayan na gama suka kwashe kayan. Wajen sha biyu na yi wanka na shirya na fita harabar gidan don ba wa idona abinci, duk yadda na dinga ganin girman gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wannan ya fi shi, don kafin na gama zagaye shi sai da ƙafafuna suka yi liƙis da gajiya. Part ɗin masu aiki maza daban na mata daban, ɗakin gateman da toilet ɗinsa shi ma daban, sai wasu extra parts guda biyu. Ga swimming pool da garden mai kyau da ya ƙawatu.
Har bayan azhar ina ta kiran layin Idonnera ba ya ɗauka, tun ina yi masa uzuri har abun ya fara damu na, don abincin rana ma kasa cin shi na yi. Duk tasirin farinciki da murnar kasancewa ta a gidan da na daɗe ina mafarkin kasancewa a cikinsa sai na neme su na rasa.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 24