komai." Ta ce. "In sha Allah, da zarar ta samu miji ma za ta kuma yin aurenta ne, tunda wannan ɗin ko idda bai ɗora mata ba, shi ne ma dalilin da ya saka auren ya mutu, na san ba ta faɗa maka ba." Ƙasa na yi da kaina ina jin kamar na nutse saboda kunya." Guntun murmushi mai ciwo Kawu ya yi ya ce. "Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya kawo mata wani na gari." Inna Habi ta ce. "Amin ya rabb, na gode sosai da amincewa, Allah ya ƙara girma da lafiya, ya bar zumunci." A hankali na amsa da Amin, Kawu ma ya amsa. Daga haka muka tashi muka shiga ciki.
Ita ta taya ni tattara kayana, duk da komai a haɗe yake da ma, ko taɓa su ban yi ba tunda aka kawo. Ko tsinke ba ta yarda mun bari ba, ta haɗa kan komai muka tafi.
Bayan mun je tana ɗiban turamen atamfofi a cikin waɗanda ban ɗinka ba ta ce. "Wallahi har yanzu ban daina takaicin mutuwar wannan auren naki ba, saboda yanzu shikenan kuɗin da kike tura mini duk wata na daina samu. Wannan shi ne samu da rashi a lokaci ɗaya." Murmushin yaƙe na yi na ce. "Allah zai kawo wani ne a gaba Inna." Da sauri ta ce. "In sha Allah, ai ke kalar masu kuɗi ce da ma tun can, bare yanzu da hutu ya ratsa ki kika yi kyau da sheƙi, talaka ko gigin biyo ki ba zai yi ba." Ban ce komai ba, don har lokacin fargabar maganganun Idonnera tana nan danƙare a cikin raina.
Kullum da zullumin tsammanin ganin Mansur ya fara cutar da ni nake kwana nake tashi, a hankali a hankali kuma sai tsoron ya fita daga cikin raina, musamman saboda yadda na dage da addu'a kamar yadda Kareema ta ba ni shawara. Burin Inna Habi kullum na tsantsara kwalliya na fita, a cewarta saboda na samo mata suruki mai maiƙo. Maganganunta da dawowar rayuwar group ɗinmu da ya yi sanyi kwana biyu su suka tayar mini da burina, na son rayuwar gidan kuɗi da hutu. Na saka a raina Alhaji Mansur ne kawai ya zo ba a na gari ba a masu kuɗin, amma sauran gidajen masu kuɗin ba haka suke ba, kamar yadda Maman Hanif ta faɗa mini. Ba ni da aiki sai hawa online mu yi ta hira a group ɗinmu bayan na gama yi wa Inna Habi aikace-aikacen gida. Kuɗaɗen da Mansur ya sako mini a cikin kayana da wanda na taho da su shi muke ci muke bushasharmu. Sai ya zamto ban da matsalar komai face tunanin su Sultan da babansu da yake manne a cikin zuciyata, sosai nake kewar su kamar na zauna nai ta kurma ihu, babu second da yake wucewa ban tuna su ba. Duk da ina yin iya yina wajen ganin na cire Anas daga raina, amma abu ya gagara, hakan ya sa na fara lissafin aure ni ma kamar yadda Inna kullum cikin tarawa da kwashewar shi take. Na san tabbas har yanzu ina son Abban Sultan, amma ko kaɗan bana tunanin komawa gidansa, don a ganina ci baya ne na can ƙarshe, na auri mai kuɗi kamar Idonnera sannan na koma gidan matsiyaci. A hankali a hankali na fara komawa Hafsan Maman Nasmah, wadda wata ƙawarta da kowa ya san su tare a group ta sanar cewa sun yi tafiya ne wata ƙasar ita da mijinta, shi ya sa aka ji ta shiru. Burina ya dawo sabo fil a cikin raina, ban da aiki sai dai na yi wanka na caɓa kwalliya na fita na ɗan zagaya ko na siyo abu. Tsabar son kuɗin Inna Habi ya sa take hulɗa da masu kuɗi, lokaci zuwa lokaci take aike na gurinsu karɓo mata abu, ko kuma na kai musu. A haka watarana da ban fi wata da fitowa daga gidan Idonnera ba wani ya biyo ni a wata lafiyayyiyar mota. Ina cikin tafiya na ji ana ta danna mini horn. Tsayawa na yi ina satar kallon shi bayan ya zuga glass ɗin motar.
"Sannu Hajiya." Ya faɗa cikin murmushi.
Fari na yi cikin son ƙara jan hankalinsa na ce. "Yawwa Alhaji." Yana faɗaɗa fara'arsa ya ce. "Idan babu damuwa ki shigo na rage miki hanya mana." Girgiza kai na yi na ce. "A'a na gode." Cikin lallami ya ce. "Haba Hajiya, ko ɗan rage ɗaukar alhakin fatar nan taki mai kyau da sheƙi da kike azabtar da ita da rana ai kya shigo." Kallon shi na yi muka haɗa ido, da sauri na janye nawa ina faɗin. "So kake mijina ya kusa hallaka mu kenan?" Wani irin abu na gani a kan fuskarsa, da na kasa tantance tsoro ne ko tashin hankali. Fuskarsa da alamun damuwa ya ce. "Tsakanin ki da Allah kina da aure?" Girgiza masa kai kawai na yi. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Amma kin ɗauki haƙƙina, ki nemi yafiyata gaskiya, don kaɗan ya rage zuciyata ba ta buga ba." Dariya na yi na ce. "Sorry, Allah ya ba ka haƙuri." Ya ce. "Wasa nake yi miki, duk wani abu da za ki aikata in dai ga ni Sani ne an yafe miki."
'Sani.' Na maimaita sunan a cikin raina, a fili kuwa zagayawa na yi na buɗe motar na shiga, saboda magiyar da ya ci gaba da yi.
Har ƙofar gidan Inna ya kai ni, muna tafe yana yi mini hira, ya faɗa mini shi ɗan kasuwa ne, yana da shaguna a cikin kasuwar wanban Kano, yana siyar da kayan kitchen. Har matakin karatunsa, da sunan ƴan gidansu duk ya sanar mini. Komai ya yi mini har da shi kansa, don dogo ne mai ɗan haske, kuma ba shi da muni, amma ba za a saka shi a cikin kyawawa ba. Abu na ƙarshe da ya faɗa shi ne ya tayar mini da hankali, cewar yana da mata da ƴaƴa uku. Daurewa na yi ban bari ya fuskanci komai ba har muka yi sallama, bayan mun yi exchanging number. Ina shiga gida na kora wa Inna bayanin komai. Ba yabo ba fallasa ta ce. "In dai yana da ɗan danshi-danshi kuma kin ga alamar za ki huta ya fito kawai a yi magana." Na ce. "To, amma sai mun gama fahimtar juna." Gudun kar a kuma kwata irin ta Idonnera, da har yanzu kullum da fargabar maganganunsa nake kwana nake tashi.
Sai da daddare Sani ya kira ni, muka daɗe muna hira, ya ba ni tarihin rayuwarsa a taƙaice, ni ma na ba shi tawa, har aure-auren da na yi ban ɓoye masa ba. Ya ce shi da gaske yake so na yake da aure, idan na ji na aminta da shi kuma zan iya rayuwa da shi a shirye yake ya turo magabatansa, na ce ya ɗan ba ni lokaci na yi tunani. Ya ce babu matsala.
Inna Habi ba ta yi amanna da shi ɗari bisa ɗari ba sai da ya fara yi mini bajinta, ni kuma duk da ina son kuɗin amma a wannan karon aure nake so na yi na dindin ba na jeka ka dawo ba, sai na tabbatar ba shi da wata damuwa sannan zan aminta a yi magana. Iya binciken da aka yi a kansa ba shi da wata matsala daga shi har iyayensa. Hakan ya sa na tura shi gurin Kawu bayan Inna ta je ta yi masa bayani. Nasiha da faɗa sosai Kawu ya yi mini a wannan karon, a ƙarshe ya rufe da fatan Allah ya sa wannan karon sai dai mutuwa ta raba mu. Sai da ya yi bincikensa shi ma sannan ya ba shi damar ya turo. Lokacin da ba mu fi wata da haɗuwa ba. Gabaɗaya watanni biyu kacal aka saka bikin.
Shiri sosai muke yi ni da Inna ba kama ƙafar yaro, tunda gidan kishiya ne dole mu dage mu fitar da kanmu kunya. Gwala-gwalaina Inna ta siyar aka siya kayan ɗaki da na kitchen, sai kuma kuɗin aure da na lefe da Sani ya ba ni, don Inna cewa ta yi ya bayar da kuɗi kawai ba sai ya kawo komai ba, tunda kaya dai na sakawa ina da su bunjum na auren Idonnera. Sosai hankalina ya kwanta da Sani, duk da ba wani hamshaƙin kuɗi ne da shi ba, amma rufin asirinsa ya yi mini, ga shi kuma gidana ni kaɗai ce ba tare za mu zauna da matar tasa ba, unguwarmu ma ba ɗaya ba.
Wannan karon kasa dannewa na yi na ce wa Kawu zan je garinsu Anas na gano ƴaƴana, ko kuma na je gidan wata cousin sister ɗinsa da take garin nan, ko zan samu labarin inda yake. Hana ni ya yi ya ce sai na yi aure, shi da kansa zai saka a je a ɗauko su. Ba don na so ba na haƙura.
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, a karo na uku na ƙara kasancewa matar aure a wata safiyar ranar Lahadi. Na so gayyatar ƴan group ɗinmu amma na fasa, Naja ce dai ko tunanin gayyatar ta ban yi ba, don har yanzu a ƙullace nake da ita.
Unguwa mai kyau da tsari aka kai ni, gidana ɗan madaidaici self contained, wanda ba ƙaramar tsaruwa ya yi ba. Two parlour ne da three bedrooms, ni na cika bedrooms biyu da parlour, shi kuma ya cike sauran gidan. Farinciki biyu nake yi da wannan auren, na farko na samu irin mijin da nake fata, na biyu kuma a tunanina auren zai saka na tsallake tarkon Mansur da nake ta zuba idon ganin ranar da zan rufta, tare da addu'ar Ubangiji ya tseratar da ni. Akwai komai na abinci da na sha a gidana, ga wayata mai tsada zan ta yin hotuna da videos. Mun ci amarcinmu son ranmu a kwanaki ukun da ya yi kafin ya koma gidan uwargida. Duk da ko kama ƙafar Anas a nuna soyayya da kulawa bai yi ba.
Sai dai me? Cikin sati biyu na fara fuskantar wata matsala da shi, ta rashin ba ni time da kulawa, idan ya dawo daga sannu da zuwa na kawo masa abinci ya ci shikenan, sai ya janyo waya ya fara latsawa, da daddare ko na yi wanka na yi kwalliya ba zai taɓa cewa na yi kyau ba, haka abinci duk daɗin da zai yi ba zai taɓa yabawa ba. And lastly sai ya zo ya yi kwana biyunsa ya tafi bai taɓa ni ba, lokacin da ya so kuma babu wani wasa ko soyayya zai yi abinsa fisha ya tashi, hakan ya sa kwata-kwata bana fuskantar komai a wannan fannin.
Yau ta kama Juma'a, bayan an sauko daga masallaci ya dawo na kai masa abinci da ruwa, ko sannu bai ce mini ba har na gama durƙusona na tashi na koma ɗaki. A gaban madubi na tsaya ina kallon kaina, na yi kyau sosai cikin rigar bubu ta lace, ga shi sai tashin ƙamshi nake, amma a ceko kallo ban ishi mijina ba? Na dinga bin bedroom ɗin da kallo, ya ji komai da ake buƙata kamar yadda nake buri, amma rashin samun abin da na yi zato ya sa ya daina burge ni. Numfashi na sauke na koma parlour, jikina a sanyaye na ƙarasa kusa da shi na zauna. Kati nake son na ce masa ya tura mini zan siya data, kwana biyu ban da ita, kuma ban da kuɗi, kuɗaɗena duk sun ƙare a hidimar biki. Cikin tausasa harshe na ce. "Sannu da hutawa." Hannu kawai ya ɗaga mini ya ci gaba da abin da yake yi. Wani yawu na haɗiye mai ɗaci na ƙara faɗin. "Magana na zo mu yi fa."
"Amma kin ga abu nake yi ko?" Ya faɗa cikin faɗa.
Kamar zan yi kuka na ce. "Ɗan lokacin da za ka ba ni da bai fi minti goma ba shi ne zai gagara? To kati ne da ma nake son ka tura mini na siya data." Wani kallo ya watsa mini tare da faɗin. "Data? Na ce ni zan dinga saka mini data ne da ma?" Da mamaki nake kallon shi, jinjina kai na yi na ce. "To idan ba ka saka mini ba wa zai sakan? Kai fa mijina ne." Tsaki ya ja ya ce. "Ke saurara! Na hana ki abinci da ruwa ne? Ko kuwa makwanci ne ban ba ki ba na bar ki kike a titin Allah? Ina su kaɗai ne haƙƙinki da yake kaina." Miƙewa na yi na ce. "Ban gane ba? Ai tunda ka aure ni komai kai za ka dinga mun." A wulaƙance ya ce. "Ko? To bari ki ji, tun wuri ma gara ki nemi mai saka miki kati ko data, amma ba ni ba. Don ba zan iya wannan shirmen ba." Daga haka ya miƙe yana yin ball da flaks ɗin gabansa ya fice daga parlour'n. Galala na bi shi da kallo ina tambayar kaina me mutumin nan yake nufi da ni? duk kuɗinsa amma banza kati ba zai saka mini ba?
"Taɓɗijan! Akwai aiki kenan." Na faɗa a fili. Komawa na yi na zauna ina jin kamar na fashe da kuka, na saba tunda na fara riƙe waya kodayaushe na ga damar hawa online zan hau, shi ya sa kwana biyun nan da ban hau ba duk na ji na takura. A ce ga gida mai kyau, da wadataccen abinci da komai amma data ta gagare ni? Gaskiya ba zan iya wannan rayuwar ba. Ina nan zaune na yi tagumi na ji an banko ƙofa an shigo, a razane na ɗaga kaina na kalli bakin ƙofar, wasu mata ne sun kai su biyar suke shigowa cikin takun taƙama da ƙasaita. Ɗaya bayan ɗaya nake bin su da kallo kamar yadda su ma suke yi mini wani wulaƙantaccen kallo. Cikin isa wata a cikinsu ta ce. "Ke ba ki ga mutane ba ne?" Kafin na yi magana wata ta riga ni da faɗin. "Bar ta, ta gama ƙare mana kallo, to mu yayyen Sani ne uwa ɗaya uban ɗaya." Murmushi na yi tare da miƙewa na ce. "Ai ban sani ba, sannun ku da zuwa." Baki suka taɓe suka nemi guri suka zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Cikin risinawa na gaishe su, ko kallo ban ishe su ba, babu wadda ta amsa. Bayan sun gama yi mini kallon wulaƙanci ni da parlourn suka tashi suka zazzaga gidan, ban san me suke ƙullawa ba na ji sun dawo suna faɗin. "Sai ta dawo wancan extra ɗakin, ya ishe ta tunda da toilet a ciki." Ban kawo komai a raina ba na shiga kitchen na fara hidimar shirya musu abinci, cikin raina ina al'ajabin waɗannan matan, da ko ba a faɗa ba ka san ƴan'uwan Sani ne saboda kamar da suke yi. Ga su manyan mata masu buɗaɗɗen ido. Ina jiyo su suna ta kushe kayana. Na yi sama da hour kafin na fito na fara jera musu abincin bayan na kwashe wanda Sani ya ƙi ci. Na haɗa musu lafiyayyen zoɓo duk da na dire musu.
"Ban da hali irin na maza, Sani yana da mace kamar Samira, mai kyau da aji amma ya je ya kwaso wannan abar, kwata-kwata ba su da haɗi da Samira, ta ko'ina ta yi mata zarra." Wata a cikinsu ta faɗa tana jifa na da mugun kallo. Ƙoƙarin barin parlour'n na yi don cin fuskar tasu ya fara isa ta. Amma tsawar da aka daka mini cikin bayar da umarnin na dawo na zuzzuba musu abinci ta sa na tsaya cak.
"Au ba za ki dawo ki zuba ba?"
Ban ce komai ba na koma na zuzzuba musu cikin daure fuska. Bayan na gama wata ta ce. "Allah ya sa ma abincin ya ciyu." Murmushin yaƙe na yi na ce. "Idan bai ba akwai komai a kitchen, sai ku shiga ku girka da kanku." Kama haɓa suka yi har suna baki gurin faɗin. "Mu za ki faɗawa baƙar magana?" Kafin na yi magana Sani ya shigo parlour'n. Bai ko kalle ni ba ya yi musu sannu da zuwa cikin fara'a, ɗaya a cikinsu ta fara rattaba masa bayanin ƙarya da gaskiya wai sai faffaɗa musu maganganu nake yi. Kamar bai taɓa dariya ba saboda yadda ya tsuke fuska ya ce. "Ba ki da mutunci da ma ko? Yayyin nawa kike faɗawa magana?" Idona cike da ƙwalla na ce. "Ka yi haƙuri." Ƙwafa ya yi ya fara nuna su ɗaya bayan ɗaya yana faɗa mini sunayensu.
Sai da suka ci abincin na kwashe kayan, na wanke sannan na koma ɗaki. Ko zama ban yi ba ya shigo ya kira ni, a ƙufule na dawo. Kallon banza Aunty Suwaiba ta yi mini ta ce. "Ɗan yi sauri ki dafa mini tuwo da miyar kuɓewa zan tafi da shi, idan na je na huta yin girki." Baki a sake nake kallon ta cikin matuƙar mamakin da ya hana ni magana.
"Ba ki ji me ta ce ba ne?" Na ji muryar Sani ya faɗi haka a cikin kaina. Numfashi na sauke na ce. "Na ji, amma babu kuɓewar ai." Ya ce. "Ki ɗora bari na siyo."
Ban huta ba sai da suka bar gidan bayan Magriba, cikin matuƙar gajiya na kwanta ina tunanin irin jarababbun dangin mijin da Allah ya haɗa ni da su. Da yake uwargidana cousin ɗinsu ce, da mamanta da mamansu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, sai yabon ta suke yi suna kushe ni. Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba sai farkawa na yi na ga har goma na dare saura. Da sauri na tashi na je na yi alwala na yi Sallah, bayan na idar na ci abinci na yi wanka na shirya cikin wasu kayan bacci masu kyau da ɗaukar ido, na bulbula turare a jikina na fito na nufi ɗakinsa, don ji na yi ina da buƙatar shi. A bakin gado na tarar da shi yana aikin irga uban kuɗaɗe, na ƙarasa kusa da shi na ce. "Sannu da aiki." Ya amsa da yawwa a ciki-ciki. Zaman jiran shi na tsaya yi, ganin abun bana ƙare ba ne ya sa na fara nuna masa abin da yake tafe da ni. Kamar wadda na ɗora masa wuta a jikinsa haka ya ja baya tare da hankaɗe ni, cikin masifa kamar zai anayar da hanjinsa ya ce. "Mene ne haka?" A dake na ce. "Haƙƙina na zo karɓa, saboda na gaji da wannan rayuwar ta sai an yi kwanaki." Kamar wadda ta yi wani sabo haka ya zuba mini ido, kafin ya ja tsaki ya ce. "Ba niyya to jarababbiya, sai ki tashi ki ƙara gaba." Zan yi magana ya daka mini tsawa da faɗin. "Get out! Ai ke ba makauniya ba ce, kina ganin abu nake yi." Zuciyata na tafasa saboda ɓacin rai na tashi na bar ɗakin ina tambayar kaina wanne irin miji Allah ya haɗa shi kuma? Ga masifa ga tauye haƙƙi, abu kaɗan faɗa, ba sakin fuska bare a yi hira da raha, gabaɗaya ya sauya kamar ba shi ne ya nuna mini soyayya a waje tamkar ya cinye ni ba. Sai da na sha kukuna sannan na samu bacci ya ɗauke ni wajen asuba.
Washegari na tashi da wani irin masifaffen ciwon kai da zazzaɓi, ina zaune bayan na idar da Sallah ya shigo ɗakin. Fuskarsa babu fara'a ko kaɗan ya dube ni ya ce. "Kin san da wuri nake fita kika zo kika naɗe a gado, ko ni zan yi wa kaina abincin karin ne?" Cikin azabtar ciwo na ɗaga kai na duba shi a wahalce na ce. "Ban da lafiya, ba zan iya aikin komai ba." Cikin ko'in kula ya ce. "Bana son rakin banza da son jiki, ki kwanta lafiya ƙalau sai yanzu za ki wani ce ba ki da lafiya, to babu abin da ya shafe ni, ki tashi ki yi mini abin da zan ci kafin ranki ya ɓaci, kuma anjima Mama za ta zo, da kin gama ki ɗora abincin rana, kar ta ƙaraso ba ki gama ba." Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin.....✍️
_Fatan mun yi Sallah lafiya, Allah ya maimaita mana_🙏🙏
*Zeey Kumurya*✍️
[5/11, 12:10 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*29.*
Ko motsi ban yi ba, don ba ni da ƙwari ko kaɗan. Jikina kamar ba nawa ba haka nake jin shi. Bayan wasu mintuna ya dawo ɗakin a fusace, daga yadda ya banko ƙofa na san ba arziƙi.
"Wai wanne irin iskanci ne wannan?" Ya faɗa cikin daka tsawa.
Ban san lokacin da na yaye bargon na tashi zaune saboda razana ba, sosai na firgita don na manta rabon da aka doka mini gigitacciyar tsawa irin wannan. Bakin gadon ya ƙaraso ya yaye bargon gabaɗaya ya cillar a ƙasa, yana huci kamar wanda ya haɗiyi garwashi ya ce. "Kar na dawo na kuma samun ki a nan, idan kika bari na yi late kuma wallahi ba ƙaramin ɓaci ranki zai yi ba." Ban ce komai ba har ya juya ya fice daga ɗakin. Saboda tarin al'ajabin da ya daskarar da ni a zaune, kullum faɗa da masifar shi ƙaruwa suke yi, na rasa dalilin hakan. A take zuciyata ta fara wani tunani na daban, don a ganina shiga tsakanina da shi aka yi, ban da haka ai kafin mu yi aure bai taɓa nuna mini makamantan halayen nan ba, haka ma farkon aurenmu.
Ina taune leɓe da yamutsa fuska na tashi da ƙyar na fita daga ɗakin ina bin bango. Kamar zan faɗi saboda jirin da nake ji amma a haka na daure na shirya breakfast, bayan na gama na fito parlour inda yake ina dafe kaina na ce. "Ga shi can na gama." Wani banzan kallo ya wurga mini ya ce. "To abincin ne zai kawo kansa gurina ko kuma ya ya?" Cikin marairacewa na ce. "Jikina rawa yake yi, ba zan iya ɗaukowa ba." Tsaki ya ja ya ce. "Ki zama mazari ma, Malama don't waste my time, ki je ki ɗauko ki kawo mini, bana son shirme." Ban ce komai ba na juya na koma na ɗauko, ina tafe tiren yana rinjaya ta kamar zan kifa. Na ɗauka zai bar ni haka amma ya ce sai na zuba masa, ban musa ba na yi kamar yadda ya ce na koma ɗaki na kifa a kan gado ina sassauke numfarfashin wahala. Wani irin hautsinawa cikina yake mun, tunda na fara girki ya fara amma sai yanzu ya fi tsananta. Ina juyi da murƙususu ya shigo ɗakin ya fita ba tare da ya ce mini ƙala akan halin da ya same ni a ciki ba, bare ya nuna tausayawar shi, sai ma warning da ya ja mini kar mahaifiyarsa ta zo ban mata girki ba.
Sai da na yi amai na samu sa'ida, ina gamawa bacci ya ɗauke ni ba tare da na shirya ba. Ban farka ba sai wajen 1, da wata irin gigitacciyar yunwa na tashi, hakan ya sa bakina kawai na wanke na fita dinning area na haɗa tea mai kauri na fara ɗiɗɗika. Ina cikin sha aka buɗe ƙofar parlour aka shigo, shi ne janye da trolley tare da wata dattijuwar mata, wadda duk da ban taɓa ganin ta ba na san ita ce Hajiya mahaifiyarsa. Da sauri na miƙe na tarɓe su tare da gaishe ta cikin girmamawa. Ba yabo ba fallasa ta amsa tare da neman guri ta zauna. Cikin sakanni na ƙare mata kallo, irin manyan matan nan ne masu buɗaɗɗen ido, ga shi da ma zaman Saudiyya take, a can take aiki. Shi ya sa ba mu taɓa haɗuwa ba, don tunda muka yi aure ba ta zo ba sai yau. Fuska babu fara'a kamar koyaushe ya dubi ya ce. "Kawo mata abin sha mana, kin tsaya sai aikin kallo kike." Jikina babu ƙwari na je na kawo mata, daga yadda take bi na da kallo duk sai na tsargu. Trolley'n hannunsa ya miƙo mini ya ce. "Kai mata can ɗakin, ki ƙara gyara shi kafin ta shiga." Na amsa cikin danne aman da ke ƙoƙarin taso mini. Allah ya taimake ni sai da na shiga ɗakin ya taho, da gudu na ƙarasa toilet na fara kelaya shi. Hannuna dafe da cikina na gyara
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 24