Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Maman Nasmah masoyiyata ce ta haƙiƙa, don ta gama yi mini komai, tunda ta fitar da ni kunyar zuwa taron nan. Sai da na gama tsallena da rawar murnar daɗi na kira ta don na yi mata godiya, har lokacin kuma Anas bai dawo ba. Bayan mun gaisa ta ce. "Ya aka yi ya bar ki kika je kuma?" Ina murmushi na ce. "Shawararki na bi ai, na nuna masa bai isa ba, shi ne har da cewa idan na fita a bakin aure na." Maman Nasmah ta ce. "Gara da kika yi masa haka, ki ci gaba da ƙwatar wa kanki ƴanci, kar ki bari takaicin Namiji ya kar ki, namijin ma wani banza talaka da ko ɗawainiyarki bai gama iya ɗaukewa." Shiru na yi don ba na jin daɗin yadda take yawan zagin Anas da aibata shi, duk da wani lokacin idan na yi nazari gaskiya ta faɗa, amma mijina ne duk lalacewar shi, kuma ina son shi a haka. "To da kika dawo me ya ce kuma?" Ta katse shirun nawa da faɗar haka. Na ce. "Ba ya nan na dawo, har yanzu kuma bai dawo ba." Ta ce. "To kar dai ki raga masa, ni shawara nake ba ki wadda za ta fishshe ki, don so nake na ga kina rayuwa mai inganci, idan ya faɗa miki ɗaya ki mayar masa da goma zafafa, kar ki ƙara yarda ki kuma irin rayuwar bayan da kuka yi da shi, wani ladabi da biyayya duk ki zubar da su a gefe, ki daina wannan aikin wahalar da na zo na tarar da ke kina yi kin yi ciɗin-ciɗin kamar wadda aka haƙo daga rami, yadda kika ga na zo gidanki haka nake zama kodayaushe a gidana, ina daga kwance masu aiki ne suke yi mini komai. To akan me zan kashe kaina? Haka kawai na yi baƙi watarana su gan ni a ƙazance, ai abin kunya ne." Na ce. "Haka ne, na gode sosai, zan yi duk yadda kika ce." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Kayan ciye-ciyen da ta kawo jiya shi muka ci ni da su Sultan, na yi musu wanka na kwantar da su, sai murna suke yau na ja su a jiki kamar yadda muka saba a da. Har wajen sha ɗaya Anas bai dawo ba, har na kwanta na ji na kasa bacci, don ba ya taɓa kaiwa haka a waje, bare kuma ya fita ba na nan ya bar yara kaɗai a gidan. Ina ƙoƙarin kiran shi a waya ya shigo. Kamar babu abin da ya faru na ɓacin rai a tsakaninmu kafin na fita haka ya mun magana, ya sanar mini jiran shagon dare ya yi wa mai gidansu tunda bai samu ya yi na rana ba. Ganin haka na nuna masa kayan da Maman Nasmah ta ba ni, amma ban da sarƙar gold ɗin, saboda kar ya yi magana. Bai nuna ɓacin ransa ba ya ce Allah ya sanya alkhairi. Na yi mamakin shi sosai, don na ɗauka zai yi mini bala'i ne. Washegari da na ce masa zan koma gidan gyaran jikin bai hana ni ba, ya dai roƙe ni akan kar na yi dare irin na jiya, na ce masa in sha Allah. Sai da na yi abincin rana na kai maƙota da uniform ɗin islamiyyar su Sultan sannan na tafi. Tun ƙarfe bakwai na ga Maman Nasmah tana ta kira na, amma saboda aiki ban samu sukunin kiran ta ba, sai da na hau napep. Ta na ɗagawa ta ce. "Ya kuka yi da faƙirin mijin naki? Shi nake ta kiran ki na ji amma ba ki ɗauka ba." Cikin mamakin yadda yanzu kullum muka yi waya ko chat sai ta ji me yake wakana tsakani na da Anas na ce. "Me ya sa kika damu ne?" Ta ce. "Saboda ina son na ji halin da kike ciki mana na ba ki shawarar da za ta fishshe ki, ni fa tamkar ƙanwata da muke ciki ɗaya haka na ɗauke ki, kullum da ke kwana nake tashi, wannan mulkin mallakar da yake yi miki ji nake kamar ni ake wa wallahi." Cikin jin daɗi da ƙara yarda da soyayyar ta a gare ni na ce. "Allah Sarki ƙawata, to ki kwantar da hankalinki, don komai ya wuce a tsakaninmu ni da shi, ba ki ga yadda ya mun jiya ba, faran-faran, yau ma tare muka fito, bai hana ni ba." Kamar wadda ta firgita haka na ji ta yi magana da faɗin. "Ban gane ba! Bai ce miki komai akan daɗewar da kika yi ba?" Na ce. "Bai ce ba, kawai dai ya ce kar na daɗe yau." "Kuma kin nuna masa kayan da na ba ki?" Na ce. "Eh." Shiru na ji ta yi na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Kin ga shawarar da nake ba ki ta yi aiki ko? Da kin ci gaba da yi masa lako-lakon nan da tuni jiya ya ƙare miki tijara, amma abin da nake so da ke kar hakan ya sa ki koma masa kamar da fa, idan ba haka ba zai ci gaba da juya ki kamar waina ne, yanzu kin saka masa tsoron ki a cikin zuciya, ya gane ko babu shi za ki iya rayuwa, tunda har ya yi miki barazana da saki kuma kika shallake, to haka ake yi wa maza a zauna lafiya da su, idan kuma kika ce za ki raga musu sai su mayar da ke baiwa, dabba ma ta fi ki daraja a gurinsu." Cikin gamsuwa da maganganunta na ce. "Tabbas haka ne, don da a da ne Anas ya hana ni abu na yi sai ya saɓa mini sosai, amma jiya har da haƙuri ya ba ni, ai na faɗa miki yana tsananin so na, ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba." "Yawwa, to ki yi amfani da wannan son ki gara shi kamar taya, ke ma ki shigo samun mu manyan mata isassu a gidajensu, za ki ga yadda zai na rawar jiki a kanki da yi miki biyayya." Bayan mun gama wayar na yi shiru ina nazartar maganganun ta, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, na yi kuma amanna da su, duk da na yi niyyar mu koma kamar yadda muke a da ni da Anas, don da ma dalilin da ya saka nake yi masa duk wani rashin mutunci saboda ba zai fitar da ni kunya ba ne, amma tunda na samu duk wani abu da nake buƙata na fitar taronmu ban da wata sauran damuwa. Kasa zaune ko tsaye Maman Nasmah ta yi bayan sun gama wayar, ko kaɗan ba haka ta so ji ba, ta so a ce Anas ya na dawowa ya yi wa Hafsah fata-fata ya kore ta a daren, hakan ya ƙara tabbatar mata ba ƙaramin so yake yi wa Hafsan ba kamar yadda ta faɗa. Dole ne ta ƙara ƙaimi da dagewa gurin ziga Hafsah da nuna mata mijinta ba kowa ba ne face talaka mara daraja, za ta yi amfani da son rayuwar kuɗin da Hafsah take da shi ta cimma burinta. Wani murmushi ta saki lokacin da wata idea ta to mata cikin kwanyarta kamar an zira mata ita. A fili ta ce. "Duk rintsi duk wahala dole na mallaki mijinki Maman Sultan!" Da daddare da muka kuma waya da Maman Nasmah ta ce na takura wa Anas ya siya mini sabuwar waya kafin ranar taro, kowa yana turo abin da mijinsa ya yi masa a group amma ban da ni, saboda nawa mijin ya fi kowa fatara sai ya kasa tsinana mini komai. Ya na dawowa ko bari ban yi ya zauna ba na ce. "Abban Sultan taron da na ce maka za mu yi fa saura kwana biyar, kuma gaskiya ni ina buƙatar sabuwar waya kafin ranar." Ya ce. "Ba mun gama wannan maganar ba Hafsah?" A harzuƙe na ce. "Ba wani mun gama, ni kawai ka siya mini." Ya ce. "Zancen kike so." Masifa na shiga surfa masa kamar wata uwarsa, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba. Na dinga jifan shi da kausasan kalamai. Bai ce mini ƙala ba har na gaji don kaina na yi shiru ina huci. Ina hawa online a lokacin na ga an ci gaba da turo abubuwa, kowacce ta na cewa mijinta ya siya mata kaza, ya ba ta kaza, ya kawo mata kaza. Hakan ya ƙara tunzura ni, na dinga Allah wadai da auren Anas, don da na san haka masu kuɗi suke bauta wa matansu da ko sama da ƙasa za su haɗe ba zan auri talaka ba. Ga shi ana ta tagged ɗina ana cewa ni ina nawa abubuwan? Rashin abin cewa ya sa ba na yi musu reply. Duk wata tijara da rashin mutunci babu wadda ban yi wa Abban Sultan ba akan ƙin siyo mini wayar da ya yi, na daina aikin komai a gidan, tsakani na da su Sufyan sai hantara da zagi, musamman idan yana gidan, amma duk da haka ko ɗaga kai bai taɓa yi ya kalle ni ba bare ya tanka, duk da ina ganin tsantsar ɓacin rai a kan fuskarsa. Yau ya kama saura kwana biyu taronmu, da daddare bayan na dawo daga gidan gyaran jiki ina zaune a gefen gado ina kallon fatata yadda ta yi wani irin kyau da sheƙi abun gwanin burgewa. Kallon yadda jikina ya koma kaɗai ya na saka ni a cikin matuƙar nishaɗi. Kiran Maman Nasmah ne ya shigo wayata, da murmushi na ɗaga tare da yin sallama, bayan ta amsa na ce. "Ya shirye-shirye?" Ta ce. "Shirye-shirye Alhamdulillah, ai mu mun gama komai, rana kawai muke jira." Na ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana wannan rana dai da rai da lafiya, mu sha shagali mu mori bidirin tanadin da aka yi mata." Ta ce. "Amin, amma dai ya kawo miki wayar?" Na ce. "Hmm, ina fa! Ai da ƙyar ya siya mini, ko tanka ni ba ya yi fa." Ta ce. "Taɓ, kowa kuwa da sabuwar waya zai je gurin nan, daga mai ta million sai mai ta sama da haka, ke kaɗai ce za ki tashi da jagwal." Cikin yaƙe na ce. "In sha Allah ni ma da sabuwa zan zo, bari ya dawo gidan." Ta ce. "Allah ya sa, ki san dai duk yadda za ki yi ya siya miki atou." Na ce. "In sha Allah." Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar. Miƙewa na yi na fara zarya a ɗakin, ina tunanin hanyar da zan bi na samu waya mai tsada irinta ƴan group ɗinmu, na ƙulla na ƙunce amma ban da wata hanya sai Anas ɗin dai. Citson yatsa na yi na ce. "Oh Allah, ni Hafsah wacce ƙaddara ce ta kai ni auren mara zuciyar da ba zai iya nemo kuɗin da zai wadata ni da shi ba? Ya mayar da ni zarra a cikin mata ni ma kamar su Maman Nasmah." Tsaki na ja na koma na zauna tare da rafka tagumi. A haka ya dawo ya same ni, na tarɓe shi da kallon banza tare da jan dogon tsaki. Bayan ya rage kayan jikinsa ya na ƙoƙarin barin ɗakin na yi tsalle na sha gabansa, ina bin shi da wulaƙantaccen kallo na ce. "Anas don Allah wai kai wanne irin mutum ne? Ko babu zuciya a ƙirjinka ne da za ka yi amfani da ita ka nemo kuɗi a duk inda suke ka yi mini abin da nake da muraɗi?" Numfashi ya sauke tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefena ya fita amma na ƙara tare hanyar, ina hawaye na ce. "Wai mahaukaciya ka mayar da ni a gidan nan ne da sai nai ta maka magana ka ƙi Kula Ni?" "To ai ba ki da maraba da ita." Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai jira amsata ba ya ci gaba da magana da faɗin. "Duk abin da za ki yi da cin mutuncin da za ki mun na yi wa kaina alƙawarin ba zan kula ki ba, bare na biye miki, har ki yi ki gama." Ƙugu na riƙe a harzuƙe na ce. "Ai ban da ranar ganawa idan har ba za ka yi mini abin da nake so ba, na gaji da zama sai dai na ga a yi wa wasu abubuwa ni ba a min, alhalin su ma mazajen nasu mutane ne kamar kai, ba fin ka suka yi da komai ba, abin da suke yi suke samun kuɗi kai ma za ka iya." Girgiza kai ya yi cikin tsantsar takaici ya ce."Allah ya ganar da ke Hafsah, amma ba zan gajiya da yi miki wannan addu'ar ba." Ina ƙoƙarin ƙara yin wata maganar ya hankaɗe ni ya fice, ƙwafa na yi na koma na zauna ina jijjiga jiki. Sabbin wayoyi da motocin da ƴan group ɗinmu suka tutturo mazajensu sun siya musu sai gizo suke mun a cikin kaina, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duk wadda ta turo abu wani sashi na gidanta ya fito sai na gan shi haɗaɗɗe ginin zamani, wani parking space ma kaɗai sai a saka gidana a ciki ya zauna har da ragowa. Gabaɗaya Anas da duk wata kyautatawa, kulawa da soyayyar da yake min sun fice mini a rai, rayuwar gidan kuɗi da jin daɗi kawai nake hange. Na tabbata yadda nake kwana da wuni da tunanin ranar da mafarkina zai zama gaske idan aka auna jinina ba ƙaramin hawa za a ga ya yi ba. Duk yadda na so mu yi fitina da Anas a daren nan amma ya ƙi biye mini, ƙarshe ma ficewa ya yi ya bar mini ɗakin ya koma nasu Sultan. Da Asuba ina tashi na ɗora daga inda na tsaya, na dinga watsi da kayan ɗakina ina jifan shi da shi, tare da gasa masa duk maganar da ta fito daga bakina. Don hankalina a matuƙar tashe yake na ganin har ana i gobe taronmu amma ban mallaki sabuwar waya ba, kuma kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa duk kyawun da zan yi a gurin, da tsadar kayan da zan saka a banza za su tashi idan ban da rantsatstsiyar waya, saboda akwai video da za a yi mana wanda kowa zai ɗaga wayarsa a ciki, so ake mu tashi kan media a taron nan namu, ai ta yawo da videos da pictures ɗinmu, mu zama topic of discussion a ranar, shi ya sa aka ce kowacce ta sako gold. Don haka duk rintsi duk wahala ba zan bari na zamo takashin baya ba, dole duk abin da za a yi ya zamto ina gaba-gaba. Yau idan na je gidan gyaran jiki shi ne za a mun lalle, amma saboda zullumin rashin waya ya sa har 8 ta wuce ban fara shirin tafiya ba. Ina kwance ina aikin kallon hotunan wayoyin da fiye da rabin ƴan group ɗin suka turo a tsakanin shekaran jiya da jiya Abban Sultan ya shigo ɗakin. Kamar an tsikare ni na tashi zaune na dirga daga kan gadon a haukace na je gabansa na haska masa rakwaɓaɓɓen screen ɗin wayata na ce. "Kalli yadda ake abin arziƙi, kalli irin wayoyin da mazajen wasu suka sissiya musu, ni kam Anas anya ka na so na kuwa? Gobe ne abin nan amma ka fitar da ni kunya abu ya gagara." Tankwaɓar da wayar ya yi ya ce. "Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba Hafsah sai yanzu, kin taɓa ganin mutum ba shi da gashin wance ya ce sai ya yi irin kitsonta? Kin san kuɗin da mazajen nasu suke da shi ne?" Ina huci na ce. "Ai ba da kuɗin suka zo duniya ba, nema suka yi, kai ma sai ka fita ka nemo a duk inda suke." Murmushin takaici ya yi ya ce. "Kin yi nisa my love, ba za ki taɓa jin kira ba, abu ɗaya nake fata shi ne Allah ya sa ki je ki ga mazajen nasu ba su da wani abu da suke nema ido rufe, wanda ni kuma ina da shi, na san daga nan za ki dawo cikin hayyacinki." Wulaƙantaccen kallo na bi shi da shi, ina keɓe fuska kamar na ga kashi na ce. "Har akwai wani abu da talaka yake da shi da mai arziƙi zai rasa? Ai kuɗi babu abin da ba sa samar wa mutum a duniya." Girgiza kai ya yi ya ce. "Kamar yadda Ubangiji yake raba arziƙi ga wanda ya so haka yake raba lafiya da sauran baiwa ga bayinsa, don ka na da kuɗi bai zama lallai ka na da lafiya ko kuma wani abu mai muhimmanci a rayuwarka ba, na san ba za ki taɓa gane duk wani abu da zan faɗa miki ba a yanzu, balle ki yarda da ni, saboda nausawar da kika yi a cikin wani tunani na banza da wofi. Shi ya sa na tattara ki na watsar na zuba miki ido ki yi duk abin da za ki yi ki gama, zan dai ci gaba da yi miki addu'ar Ubangiji ya ganar da ke cikin gaggawa." Wawan tsaki na ja tare da galla masa harara, ina jin kamar na kikkifa masa mari. Bai ko kalle ni ba ya ɗauki abin da zai ɗauka ya fice. Rashin sanin abin yi ya sa na tafi inda na ajiye kayan da Maman Nasmah ta ba ni don na ɗauka na tasa su a gaba na kalla kamar yadda nake yi kullum ko zan ji sanyi a raina. Sai dai me? Neman duniya babu wanda ban yi ba amma babu su babu alamar su, gabaɗaya na ƙara hargitsa ɗakin, na yi wa komai filla-filla, amma ko alamar abu mai kama da su ban gani ba. A haukace na fita parlour ina sharce zufa na duba amma nan ma babu, kitchen, toilet, ɗakin su Sultan, soro babu inda ban duba ba amma ban gan su ba, har bokitin da nake zuba shara sai da na zazzage a ƙasa na duba. Amma kaya suka ce ɗauke mu inda kika ajiye....✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:39 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *11.* Cikin matuƙar gigita da ɗimauta na koma ɗaki kamar wadda ta rasa duk danginta, na ƙara duba ko'ina har inda kayan ba za su shiga ba amma still ba ta sauya zani ba. Tamkar ledar da ke narkewa a wuta haka na zube a tsakar ɗakina na baje a kwance ina sakin numfashin wahala. "Na shiga uku! Su kuwa kayan ina suka shige? Idan har ta tabbata ɓata suka yi na gama kaɗewa har ganyena!" Na faɗi haka a fili ina ɗora hannuna akai daga kwancen da nake. Kamar ɓeran da ya hangi kyanwa haka na miƙe zumbur na fara laluben inda na cilla wayata, da ƙyar na gano ta a cikin kayan sawarmu da na yi musu ɗaiɗai a tsakar ɗakin kamar na rabon gado. Wani farfar na ga tana yi, a hakan na lalubo numbern Anas na yi Dialing. Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama. Ban bari ya ƙarasa ba bare na amsa na ce. "Anas ka ɗaukar mini kayan nan da matar nan ta ba ni ka sauya musu gurin ajiya ne?" Ajiyar zuciya na ji ya sauke bai ce komai ma. A harzuƙe na ce. "Magana fa nake yi maka." Yana sauke numfashi ya ce. "Relief nake samu, don yadda kika yi magana cikin tashin hankali na ɗauka mutuwa za ki faɗa mini an yi." Cikin ƙufula na ce. "To ba gara mutuwar da wannan rasa kayan da na yi ba, kayana fa Anas wanda zan yi fitar kunya da su gobe? Don girman Allah da darajar su Inna idan ka gan su ko kai ɓoye ka dawo ka ba ni! Don Allah ba don ni ba, wallahi idan ta tabbata kayan nan sun ɓata zuciyata za ta iya bugawa." Na ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka. Cikin lallami da son kwantar mini da hankali ya ce. "Ki nutsu dai ki duba su da kyau Hafsah, don ni tun ranar da kika nuna mini su ko ƙyallin ledar da suke ciki ban ƙara gani ba, don haka suna gidan, tunda babu mai shigowa bare ya ɗauka." A ruɗe na ce. "Ba sa nan, wallahi na duba ko'ina har toilet da cikin bola ban gan su ba, ba sa nan fa Abban Sultan, don Allah ka taimake ni ka zo ka taya ni dubawa, ko idona ne ya makance daga ganin su." Ya ce. "Tom shikenan gani nan." Na ce. "Yawwa, ka yi sauri." Daga haka na kashe wayar. Duk da gajiyar da na yi sai da na ci gaba da bincike kafin ya ƙaraso. Ina cikin yi tunanin kiran Maman Nasmah na sanar mata halin da ake ciki ya faɗo mini, da sauri na ɗauki wayar na kira ta, kamar mai dakon kiran ta ɗaga da sauri, don ni ko ringing ban ji ta yi ba. Ina share hawayen da ya yi male-male a kan fuskata na ce. "Takwara ina cikin tashin hankali, ban ga kayan da kika ba ni ba gabaɗayansu." Cikin mamaki ta ce. "Kamar ya ba ki gan su ba? Wanne kaya ma tukunna?" Na ce. "Wanda zan saka gobe mana? Komai da komai ɗin da kika aiko mun da shi fa, har sarƙar gold ɗin!" Numfashi ta sauke ta ce. "To ai ni ban ga abun damuwa ba a nan tunda kin san wa zai ɗauka?" Da sauri na ce. "Sai dai in aljanu ne, amma ko Abban Sultan bai san inda na ajiye su ba, saboda ɓoyo nake yi musu kamar na ganin mutuwa." Ta ce. "To ko na ganin ƙiyama ne ga shi nan mijinki ya gani ya sace." "Sata kuma?" "Eh mana, to idan ba shi ba wa zai ɗauka? Su Sultan ƴaƴanki ƙanana ko kuma kin yi wani baƙon ne a gidan ban sani ba?" Cikin ɗaurewar kai na ce. "Babu wanda ya shigo gidan ma tunda kika kawo kayan bare baƙon zama, daga ni sai mijina da ƴaƴana a gidan, kuma na kira shi tun ɗazu na tambaye shi ya ce ko ganin su bai yi ba, balle ya ɗauka, Abban Sultan ba ya ƙarya, da ya ɗauka zai faɗa mini wallahi, ko da wasa yake mini yadda ya ji hankalina ya yi mugun tashi zai ce shi ya ɗauka." Dariya na ji ta sheƙe da ita kamar sabon kamu, tana dariyar ta ce. "Lallai Namecy har yanzu da sauran ki a karatun ɗa namiji, to bari ki ji, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba shi ya sace kayan zai je ya siyar, ƙila ma ya daɗe da cin kasuwarsu, ke kina nan kina cewa ba zai ɗauka ba." Girgiza kaina na fara yi cikin tantamar abin da ta ce, don ko kusa ban kawo Anas zai ɗauki kayan nan da niyyar sata ba, saboda shi mutum ne da kayan wani bai dame shi ba kwata-kwata, tun farkon aurenmu idan zan samu duniya ba ta gabansa, kuma ba ma ni ba, naturally ɗinsa kayan wani ba ya gabansa, ban taɓa jin ya mun zancen abin wani yana burge shi ba, bare ya roƙa, mutum ne shi mai wadatar zuci, abinsa na karan kansa kawai ya sani, da shi yake amfani. Zan shaide shi a wannan fannin. A sanyaye na ce. "Anas ba zai mun sata ba Maman Nasmah." A zafafe ta ce. "Ke kika sace abinki kenan ko kuma kayan su suka ɗauke kansu? Wai ke wacce iriya ce ne? Ina ganin ki kamar mace mai wayo ashe ba haka ba ne? Ki nemi abu ki rasa a gida kuma daga ke sai shi amma ki dinga cewa ba shi ya ɗauka ba, ki yi tunani da ƙwaƙwalwarki mana, kin ce babu wanda ya shigo gidan ma tunda na ba ki kayan bare a ce ko shi ya ɗauka. Ina nuna miki Annabi kina runtse ido, ga abu a fili amma shegen son miji ya sa kin baɗa wa idonki toka kin ƙi gani. To ki karkaɗe kunnanki ki saurare ni da kyau, mijinki shi ya ɗauke kayan nan ya siyar babu ko tantama, ko ki yarda ko kar ki yarda. An faɗa miki ana yarda da maza ne yanzu, idan da

Chapter 6 of 24